Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikinta na rawa ta fara ja baya,tsill magen na kara biyota,ganin tabbas wajanta take son yasa tayi wani tsalle ta faɗa shimfiɗar ABDALLAH wanda yake fitar da numfashi a hankali sabida wani zazzaɓi daya rufe a lokacin,tana faɗa tayi saurin shigewa jikinta tare dasa hannu ta ƙanƙameshi,kanta nakan hannunsa,ido ta ɗago karaf suke haɗa ido da ABDALLAH kallonta yayi lokacin da yaga face ɗinta daf da tasa yayinda lips ɗinta ke gogar nasa.


Sosai suke kallon juna babu ko giftawa wajan 20min ya janye idonsa ya rufesu ruf ba tare daya ce komai ba,wata ajjiyar zuciyar ta sauke mai ƙarfi yayinda ta ƙara tura kanta saman faffaɗan ƙirjinsa
****** ******

LOKOJA

Da gudu ta tashi daga jikin YARIMA,dai² wajan ƙofar taje tare da sauke numfashi tace.

"Uhm"

Daga wajan ƙofar akace.
"ranki ya dade ana nemanki"

Zaro ido OMEHI tayi tare da dafa ƙirji,ɗan numfasawa tayi tare da gyara tsaiwa tace.


"i'm coming.. but not now..,i'm not felling well.. ok"


Tayi maganar a rarrabe,daga waje akayi magana cikin sauri.


"Allah ya taimaki GIMBIYA Allah ya ƙara maki Lafiya"

Shuru tayi bata ce komai ba,wajan YARIMA ta koma wanda yake kwance flat kamar baya da rai,ya nayin saukar numfashinsa shi zai tabbatar he still a life.


Wajan 11pm notification ya shigo wayar YARIMA saurin ɗaukan wayan tayi domin duba abinda akace.


_naga antashi a FADA masarauta tayi shuru me ake ciki?_


Hannunta na karkarwa ta shigayi masa replay.


_kayi parking motar kashigo ta ƙofar baya gani nan zuwa_


Kasan cewar daga ƙofar baya zuwa ɗakin OMEHI babu nisa yasa tayi saurin ɗaukan Alƙyabba ta saka a jikinsa,kofar ɗakin ta buɗe ta fita zuwa ƙofar baya,tafiya kaɗan tayi duwa inda take tunanin zata ganshi,wasu fadawa ta gani suna kai kawo alama tayi masu da hannu zuwa inda take,da gudu suka ƙarasu inda suke haɗe da rusunawa suna kwasar gaisuwa,ɗan jinjina kai tayi sannan ta basu uwarnin dukkan suje su duba mata DAWAKANTA kai suka jinjina tare da barin waje.


Da sauri ta ƙarasa tana ganinsa tsaye yana kai kawo ga kofar mota a buɗe,a hankali tayi masa magana,ƙarasuwa yayi tare da rusunawa,ɗakinta tayi masa nuni dashi da azama ya ƙarasa shiga ɗakin nata.


A kwance ya ganshu harya mirgino ƙasa yana ƙoƙarin faɗuwa,cikin sauri ya ƙarasa wajansa,ɗauke kai YARIMA yayi lokaci da sukayi ido 4 da abokin nasa,sannan ya lumshe ido.

Tattare hannun rigarsa yayi tare dayin bisimillah yasa hannu ya saɓi YARIMA aka faɗa,cikin sauri yabar ɗakin tare da nufar ƙofar waje inda yayi parking a waje.


Huce GIMBIYA yayi ya nufi side ɗin baya na motar ya shimfiɗe YARIMA yana ƙoƙarin rufe motar yaji an riƙe hannunsa ɗan juyawa yayi yaga YARIMA ne kallonsa SUDAS yayi sannan ya maida idonsa ya kalli GIMBIYA wacce kanta yake ƙasa da alama kuka take,bayan ya kalleta sai maida kallonsa cikin motar,nan take ya fahimci abinda YARIMA yake nufi hannu yasa ya shafi gashin YARIMA sannan yace.


"kayi haƙuri ba dai² bane tafiya da matar da ba taka ba,komai yana da lokacinsa ka ɗauki hakan matsayin ƙaddararka"


Yana faɗin hakan ya nufi side ɗin drever yayiwa motar key da gudu yabar wajan.


Durƙoshewa tayi a wajan tana rusa kuka kamar ranta zai fita,ji take ina tabishi suyi rayuwa tare,inama mahaifinta zai amince da YARIMA koda bai yadda ya aureta ba,shin yaushe zasu ƙara haɗuwa da juna inane garinsu?wannan tambayoyin da take dasu amma babu amsa,kamar daga sama taji muryar SARKI a bayantace



_kika karanta min littafi baki biya ba ko sweether😍😍kije ni ba zance komai,just 200 naira🤟🏻_



"why are you cry tunda sun tafi ko zaki bisu ne?"


Last free page na ƙara ne sabida wasu🤞🏻




Sarauta👸🏻👸🏻ce


7
IDU (sarki)ne tsaye akanta ya ƙura mata ido yana karantar ya nayinta,yana son tilon ƴarsa amma son da yake mata bazai saka ya amince ya aura mata wanda zai cuceta ba,babu shakka dole OMEHI tabar wannan garin domin hakan shi zaisa ta manta da wannan ƘABILAN,dole ne OMEHI ta ziyarci garin KANO.

Fadawan data aika ne suka dawo daga gudanawar da Gimbiya hidima,sune suka ƙarasu tare da rusunawa suna kaiwa sarki gaisuwa,jin jina kai kawai yayi baice masu komai ba dan bayajin zai iya magana sabida ɓacin rai da kuma takaicin abinda ƴartasa tayi.


Ace wai ƴar cikinsa daya haifa bata ɗauko IZZA DA ƘARFIN MULKINSA ba,ji yake kamar bashi ya haife taba,doba da yadda take gudanar da aikinta cikin sanyi, akwaita da saurin ya fiya da kuma yarda da mutum.


Tun a daren jiya ya tabbar akwai ƙaddara a cikin rayuwarta,ya shiga halwar tsafinsa ya bincika ya ganu abubuwa da yawa,amma abu mafi ciwo da kuma ɗaurewar kai akwai wanda yake son ganin bayan ƴartasa,amma ya kasa samun dama sabida wani haske daya gewaye rayuwar ƴar tasa zuwa yanzu hasken ya fara jada baya,yayinda mutumin yake ƙara kusantu rayuwar OMEHI sosai ya shiga tashin hankali koda ya fiya bincike akai nan take madubin ya tarwatse.

Jikinsa na rawa ya fito daga ɗakin yayo waje yana share gumin fuskarsa,da sauri yake takawa zuwa wajen Fada turus yayi ganin wani matashin mutum mai cikar zati da haiba ga kuma kwarjini,kallo ɗaya yayi masa ya gane ba ƘABILAN EGBURA bane shi,ido ya zuba masa yana karantar ya nayinsa,sanye yake da kayansu komai da yayi irin shigar sune.

Da sauri Fadawa suka tashi za suyi kansa,hannu IDU(sarki)yasa ya dakatar dasu can ya hangoshi yana magana da wani wajan 3min a tsakani ya fara takawa zuwa flat ɗin Gimbiya.

Ɗan murmushi IDU(sarki) yayi tare da jinjiga kansa,juyawa yayi ya koma cikin Fada,wajan 30min ya aiki ɗan Aike zuwa flat ɗin Gimbiya.

Ɗan aiken ne ya shaida masa Gimbiya tace ba tajin daɗi murmushin takaici yayi,wai ƴarda ya haifa ya koyarda ita IZZA da kuma yadda zata juya mutane da ƙarfin ikonta da mulkinta,amma yau itace da kawo wata ƙabilan ɗakinta.

Ɗan lokaci kaɗan idonsa ya sauya kala daga fari zuwa red, Fadawa ya bawa umarni kowa ya tashi ya tafi makwancinsa masu tsaro suje inda suke zaune.

Wajan 1hour da tafiyarsu ya tashi ya fara tafiya domin barin Fada,yana fita yaci karo da wasu Fadawa,nan suka shaida masa aiken Gimbiya zuwa duba Dawakanta,kallonsu yayi tare da juya manyan idonsa irin na Omehi,hakan ya tabbatar masu tambayarsu yake inda Gimbiyar take,nan suka shiga labarta masa inda take.

A wajan ya tsaya wajan shadow wanda ba lallai kasan da mutum a wajan ba,yana kallon sanda wani ya shiga flat ɗin Gimbiya sannan akan idonsa aka ɗauko YARIMA a kafaɗa har zuwa ƙofar baya,har lokacin da suka ja motar suka bar waja.


Numfasawa yayi sannan ya ɗauke kansa daga gareta yace.


"kin ɗauka ni shasha ne?tayaya kike tunanin zan ɗauke kaina daga gareki bayan ban yarda dake ba,you are mad Omehi ƙarya kike ki sauyawa zuciyata ra'ayi akan abinda batai niya ba.

Kishirya a gobe zaki bar wannan garin.


Da gudu yake jan motar har zuwa gidan da YARIMA ya sauka,parking yayi ya fito tare da rufe murfin motar,wasu mutane biyu ne masu kula da flowers ya kira domin su taimaka masa yakai Yarima cikin gida.


Ƙara suwa sukai wajan suka rusuna domin girmamawa,nan ya shiga gaya masu abinda ya keso,juyar da kansa yayi zuwa wajan Yarima wanda yake kwance.

"Yarima bari mukaika ciki nida waɗanan"

Kallonsa yayi sannan ya kalli masu aikin haka nan su ƙara shafa masa wani abun,tabe baki yayi sannan ya lumshe idonsa,sosai abokin nasa ya gane bayason ma'aikatan sun taɓa shine,haka ya shiga rarrashi da ban baki da kyar ya yarda suka ɗaukesa zuwa cikin gidan.

Ƙarfe 3 na dare JET ɗin mai Martaba ya sauka a garin,babu wastin time aka shiga shirya Yarima cikin kaya na alfarma idan ka ganshi ba zaka taɓa cewa a halin cuta yake ba,fuskarsa ta faɗaɗa da murmushi babu wanda yake kallo sama da mahaifinsa ko idonsa baya son ɗaukewa,su yake ya tambayeshi meke damunsa yaga babu walwala akan face ɗinsa amma babu hali,domin bakinsa bazai taɓa buɗewa da niyar yin magana ba.


Ƙarfe 4 sun gama komai nasu,aka saka Yarima a Jet Mai Martaba ya shiga,nan Jet ɗin ya fara tashi a hankali sai ƙasa mai tsarki garin Annabi Muhammad S.W.A MAKKAH.


****** ****** ******
Washe gari da safe Abdallah ne ya fara tashi daga bacci,ɗan tsaki yaja ba tare da yace komai ba,hannu yasa yakai shoulder ɗinta,numfashi ta sauke mai ƙarfi lokacin da skin ɗin Abdallah ya sauka akan nata skin ɗin.

Shoulder ɗinta yaja ya zameta daga jikinsa,tashi yayi ya shiga wani ban ɗaki na ƙasa lokacin kaɗan yayi wanka ya ɗora alwala.

A gaggauce ya shirya ya gita daga ɗan ƙaramin gidan na ginin ƙasa,daret Masjid ya nufa domin gabatar da sallah.

10 dai² ya shigo gidan,lokacin ta sauya kayan jikinta,farin yadi ne a jikinsa mai manyan zane har ana ganin siglet ɗinsa ta jiki sabida farin yadin.

A kasalance yace.

"fito"

Yana faɗin hakan yayi ficewarsa waje.


To zaune suke akan wani babban Fillow irin na masarautar nan,kallon matar tasa SARKI KHALEFA yayi fuska babu annuri yace.


_beby kika karantamin book baki biya ba ko☹️ni bazan maki Allah ya isa ba_


"Fulani ina tunanin lokaci yayi da Gimbiya Sultana zata san komai"


Comments pls


8
A razane fulani ta ɗago kai tana kallonsa fuskarta ɗauke da mamakin abinda ya faɗa mata,ko a farki bata taɓa tunanin zai gaya mata wannan abun ba,hannu tasa ta shiga goge gomin da yake ƙaryo mata,kallonsa tayi ta ɗan kwaɓe fuska alamar shagwaɓa tace."my man amma inaga not now idan tasan komai yanzu ai kaga rabin burinka bazai cika ba,kasan cewa munason gudanar da komai ba tare da tasan wacece ita ba"ta faɗa tana kwantar da kanta a ƙirjinsa, numfashi ya sauke tare dayin wani killer smile domin ya riga daya hango nasara na ƙara kusantuwa gareshi,babu shakka ƙarfin mulkinsa da kuma izzarsa zasi ta dauwama har abada dole magoya bayansa su duƙawa izzarsa dole ne ya zama sarki mai ƙarfi iko wanda zai shafe ko wanne sarki dake duniyar nan,babu shakka burinsa bazai taɓa cika ba harsai cimma shariɗan da ɗalatsiman tsafinsa suka bashi ta hanyar cimma burinsa akan SULTANA DA OMEHI,ji yake lokacin daya ɗiba kamar yayiwa dan hakan yayi saurin tashi tsaye tare yin wata kururuwa nai ƙarfin gaske,da sauri ta diro akan koshin ɗin da take zaune tasha gabansa tace."what now?"kallonta yayi sannan ya jinjina kai yace."Fulani just waiting for me,yau zan cika muradin zuciyata akan SULATNA"jikinta ne ya shiga rawa zuciyarta ta shiga bugawa da ƙarfi shin wacce hanya zata bi wajan ruguza wannan plan ɗin nasa,what should i do? ganin ya fara tafiya zai bar wajan tayi saurin shan gabansa,hannunsa ta riƙe ta shiga murzawa a hankali ɗan lumshe ido yayi jin mood ɗinsa ya fara sauyawa,ɗan kwantar da kanta tayi a ƙirjinsa tace."babu shakka da naji daɗi kuma nayi alfahari da kai amatsayin miji mai taƙama da izza da kuma ƙarfin iko"takai ƙarshan maganar tana shafa gashin ƙirjinsa,hannu yasa ya fisgota suka faɗa saman koshin ɗin da suke daga nan labari yasha banban.
Saurin zamewa tayi daga cikinsa ganin ya samu bacci,da sauri ta fito tayi flat ɗin GIMBIYA SULTANA,tana shiga taga flat ɗin tsaf sai zabga ƙamshi yake,ɗaki wanda yaji kaya royal masu kyan gaske komai na ɗakin light blue ne,a gaggauce ta shiga kwala mata kira amma babu Sultana babu labarinta,babu inda bata shiga ba a flat ɗin amma babu Sultana,a kifime ta fito har al'ƙabbatar na shirin faɗuwa,nan tayi wajan Jakadiya mai kula da flat ɗin Sultana,nan ta shiga tambayarta inda Gimbiya take babu ɓata lokaci ta shiga labartawa Fulani abinda ya faru daman Sarki ne ya umarcesu da kada su gaya mata,tana gama faɗa Fulani tasa hannu ta shiga zabgawa jakadiya mari tare da faɗin.

"nida gidan mijina har wani abu ya faru da Gimbiya amma aƙi gayamin,wallahi sai kinyi ladamar aikatamin abinda kikai" tana gama faɗin hakan tayi saurin barin wajan ta koma flat ɗinta.

****
A dai² wani matsaikin gida mai napep ɗin yayi parking,a hankali ABDALLAH ya fito da santala² legs ɗinsa waje yana fitowa itama ta biyo bayansa ta fito sallamar mai napep ɗin yayi sannan yasa hannu ya murza key a ƙofar gidan,ɗan matsawa yayi gefe tare da ɗauke kansa wajan 5min bata motsa ba,tsakin yaja sannan yasa hannunsa mai laushi ya riƙo nata hannun ya turata cikin gidan,sannan yabi bayanta a hankali take takawa duk wani action ɗinta akan idonsa,waist ɗinta ya zubawa ido ganin yadda yake juyawa a hankali cikin abayar daya bata ta saka,ɗan tabe baki yayi a zuciyarsa yace."duniya ta lalace tunda Sultana ta fara ɗaukan kanta matsayin budurwa"da wannan tunanin suka ƙarasu parlour'n ɗakin,zama tayi akan sofar parlour'n shima wata duguwar sofa taje ya zauna hannu yasa ya zare farar rigar jikinsa ta yadi ya ajjiyeta gefe guda,nan take faffaɗan ƙirjinsa ya baiyana wanda yake cike da gashi baki siliƙ sai gyalli yake,kwanciya yayi tare da lumshe idonsa yana sauraron heartbeat.

Lumshe ido tayi bayan ta gama kallon kyakkyawar fuskarsa,ɗan ƙara waro ido tayi sannan ta motsa baki a hankali kamar bata son magana tace.

"zaka aure ni"?



Afuwa bana jin daɗi,tobe continew soon,inama barka da shagayowar shekara musulunci.


Comments


9

_🌹IZZAR SO Littafina na kuɗine kada kiyi tunanin zaki siyi Littafin nan domin ki watsawa media🙏🏻ga dukkan wanda zai siya 200 kacal katin mtn zaki ɗauki picture nasa ki turo ta wasapp no 08119237616🤟🏻kota Btu accout no 0116886423 Na'ima sulaiman s,unioun bank,idan zaki haɗa da ducoment ɗin SAI NA AURETA zaki biya 300 kawai domin samun duka book ɗin guda biyu🥰_



Shuru yayi mata ba tare daya ce komai ba, tashi tayi a hankali ta fata tafiya zuwa inda yake kwance,zama tayi kosa tashi tare da sauke numfashi mai zafi tace.

"Babu shakka ni nasan bana da gata kuma akwai ƙaddara a cikin rayuwata,bana da wani wajen jin daɗi face wajanka,nasan akwai wani abu mafi muni a rayuwata tunda mahaifina da kansa yasu yimin fyaɗe,a koda yaushe idan na tambayi zuciyata wanda ya dace da ita,sunanka take kira"

Lumshe idonsa yayi ya najin ya heartbeat ɗinsa na,ƙaruwa mai yasa ba zata fahimci baya sonta,ta riƙa data zubar da ƙimarta akan idonsa,bai taɓa sonta ba haka kuma bazai auri wacce baya soba,yasan daman wata rana dole ne ta duƙawa izzarsa domin yasan meye wekness nata,ware idonsa yayi sannan ya tashi zaune kusa da ita har numfashinsu na haɗuwa waje guda,kanta ta sunkuyar ƙasa,ɗan murmushin taƙaici yayi sannan yasa lallausan hannunsa ya riƙe habatar sannan ya juyo da face ɗinta zuwa wajansa,cikin idonta yake kallo yayinda itama take kallon nasa zuciyarta na ƙara bugu da sauri,ɗan motsa lips ɗinsa yayi yace.

"sunana zuciyarki ke kira?to meye sunan nawa THE POOR MAN ko?idan hakane zuciyarki kam tayi maki ƙarya"

Yana kaiwa nan ya tashi ya shige ciki abinsa hankali kwance,bayansa tabi da kallo yayinda hawaye kebin kuncinta,hannu tasa ta dafe saitin zuciyarta inda yake mata zafi,ɗan lumshe ido tayi tana tunanin mahaifinta mafi soyuwa a gareta.



****Makka***
Dukkan wani bin cike daya kamata ayiwa YARIMA anyi masa amma babu wani cigaba,yayinda duk wani result na binciken da akai masa yake nuna lafiyarsa ƙalau,sosai hankalin TAKAWA ya tashi ganin tilon ɗansa na shirin rasa ransa,dan haka ya yanke shawarar daga nan zasu huce EXGPHAT domin yi masa binciken gaggawa,wani Dr ne ya nemi da sukeɓe da TAKAWA.

Dr ne ya kalleshi sannan ya cire glass ɗin face ɗinsa yace.

"am sorry to say ranka ya daɗe,duk inda zaku kai YARIMA ba za'a samu yadda ake suba,tuna nina yaban wannan aikin MAGIC ne domin munsha karɓar problmes irin wannan,a shawarce gwara a koma gida a fara yi masa na hausa da kuma addu'ar karya duk wani tsafi da kuma sihiri"


Jinjina kai TAKAWA yayi tare da faisar da numfashi mai zafin gaske,babu shakka da ace yasan wanda ya aikatamawa yaronsa haka,wallahi saiya nuna masa bashi da wayo kuma baisai ƙarfin mulki da izzar saba,kallon Dr yayi tare dayi masa murmushi alamar ya gamsu da wannan suka shirin komawa Garinsu wanda ni kaina bansan ko wanne gari suke ba.

***KANO****
Kano birnin damu koda me kazu anfika,yau kwanan GIMBIYA OMEHI 5cif a garin kano,wanda ta sauka wajan ONKWO (kawu)ta sosai ta samu nutsuwa a wajansa domin baya ta kurata komai takeso yana mata,yayinda ya gargaɗe ta koda wasa kada ta sake ta nuna wata ƙabila ce ita.

Tare suke zuwa wajan aikin kawun nata,ba wani waje bane face gidan SARKIN KANO inda yake kula da dawakan SARKI yayinda ita kuma take jire masa dawakan idan zaije wani waje anan suke yini sai yamma suke tafiya gidansu.

A kullum tana tsintar kanta da tunanin YARIMA tana ji inama zata ganshi da babu abinda zai hana tabishi domin ta fahimci shine rayuwarta shine dukkan wani farin ciki nata,gashi zuciyoyinsu sun rabu da juna,amma babu shakka bugun zuciyarsu nayi ne lokaci ɗaya.

Wasu hawaye ne suka shiga zubuwa daga cikin idonta,sannu a hankali bugun zuciyarta ke ƙaruwa.

Haya niya taji tana tashi a hankali tare al'gaita mai daɗi da kuma ratsa zuciya,ɗan tashi tayi ta ɗeka,a dai² lokacinne taga an turo wata kujera kamarta gurago daɓe baki tayi lokacin da akazu hucewa dashi,ƙara leƙawa tayi amma bata iya ganin kowa waye akan kujerar.

***KATSINA***

Kwanan su 4cif babu wanda ya ƙara ganin kowa,ita ta gujeshi ne akan soyyayarsa da taji ƙarfinta,yayinda shi kuma ya daina fitowa sabida wani zazzafan zazzaɓi daya rufesa,ko tashi baya iyawa.

Wanka tayi ta saka wata duguwar abaya mai bin jiki,cikin sauri ta fito da niyar zuwa ɗakin da yake domin ta gaji da zama babu shi,tana shirin barin ɗakin nata taji wata iska na kaɗawa a ɗakin nata mai karfi kafin taji wata kururwa da ihu na karaɗe cikin ɗakin nata.

Wajan 10min iskar ta ɗauke idonta ta buɗe a hankali a razane tayi baya tare da dafe ƙirjinta ganin mahaifinta SARKI KHALEFA a gusa da ita,cikin takun isa da gadara yayin kanta gadan²,yana zuwa yasa hannu ya fisgota ta faɗa saman bed ɗin kafin..


200 naira kacal,domin jin yadda zata kaya tsakanin UBA DA ƳARSA,SHIN SARKK KHALEFA KOWA ZAI SAMU CIKAR MURADIN RANSA?amsar sai kun biyoni zaku jita.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment