You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
k'asa daza'ayi gobe a fadarsa, kowanne hukuma taza6i mutane uku dazasu wakilceta, sannan annad'a Wanda zaizama kwamitin shugabancin wannan zama baki d'aya.
Mudai anan J! Yana ciki, sannan kuma shine shugaban wannan kwamiti gaba d'aya dazai jagoranci wannan zama har fadar shugaban k'asa.
Nanma aka d'auki tafi gaba d'aya, kowa yayi na'am da hakan, saidai fuskar mutum biyu babu alamar sun amshi zancen, kuma koda khaleel yake bayani babu alamun jindad'in bayanan nasa, babu Wanda yakula da hakan sai khaleel da hankalinsa ke akan kowa, tunda dama yana zargin wasu manyansu acikin k'ungiyar, akwai guns kusan 6 acikin wad'anda suka kar6a duk Na jami'an tsarone, sannan ankama wasu acikinsu masu kaki.
Haka sukaita tattaunawa, kowa yana kawo albarkacin bakinsa, da hanyoyin dazasubi domin dak'ile ta addacin da'akeyi acikin gida da k'asashen k'etare ana zubarma da Nigeria mutuncinta.
Har 1:30pm suka kai ad'akin taron sannan aka tashi, amma khaleel yariga kowa fitowa, bama arufe taron dashiba yanemi excuse saboda time d'in sallah yayi, wad'anda suke musilmai awajen sai kunya Takamasu, dansu ko alamar tunawa da za'a shiga time d'in ibadarsu basu nunaba, saima k'ara 6ararrajewa suke suna sakin bayanai.
Shi dai khaleel yamusu sallam yafito, akan idan basu kammalaba har aka idar da sallah to zai dawo, idankuma sun tashi shikenan.
๐๐๐ปirinku mukeso khaleel masu girmama addininsu samada uzurorinsu Na duniya, wad'anda basa shakkar gudanar da ibadar aduk Inda suka tsinci kansu, masu kishin bautar ALLAH.
(Bawai ta addanci bane addini, Adinin musilinci ba addinin 'yan ta'adda baneba kamar yanda duniya take fad'a ahalin yanzun, duk Wanda kagani musilmi d'an ta adda to tabbas baya cikinmu, yana amfani dahakanne kawai domin kansa, sannan shid'in ru6a66en musulmine, mukuma maba d'aukarsa d'aya daga cikinmu, addininmu zaman lafiya da adalcin k'yautatawa junanmu yakoyar damu, yanunamana muhimmancin adalci gawad'anda bama addinimu d'ayaba, addinin musilinci adalin addinine, dake koyar damu k'yawawan ayyuka, sannan addinine mai sauk'i, danhaka duk wani d'an ta'adda dazai kira kansa musilmi munce k'aryane, shiba mabiyin addininmu baneba, ISLAM IS THE BEST RELIGION๐ช๐ญ.
Wlhy iyaye Ku kula sosai akan films da 'ya'yanmu suke kallo, musamman wad'anda ake nuna Muslim's amatsayin 'yan ta'adda, yaranmu kwakwalwarsu k'aramace, komai suka gani zasu iya d'auka hakane dai-dai, ALLAH yasa mugane.๐ค๐ปโ๐ป๐ญ
_____________
Koda aka fito sallah yaga sunfito saiya wuce office, zamansa babu dad'ewa youseef yay knocking d'in k'ofar, izinin shigowa yabashi.
Ya k'ame tareda yin salute Na ya khaleel.
Kansa ya jinjina masa sannan yamasa alamar ya zauna, bayan ya zauna khaleel yamik'o masa hannu sukayi musabaha๐ค๐ป.
Takardun dake hannunsa yamik'a masa, sir! ga wad'annan bayanan, mun tattarasu duka, insha ALLAH komai zaka samu. Maganar Munner kuma munata bibiyarsa ta number d'insa, haryanzu kuma yana cikin abujarnan. Saidai yayi wata waya damukayi recording ". 'Yay maganar yana mik'a masa k'aramar wayarsa.'
Kar6a khaleel yayi yakunna record d'in yana saurara. bayan yagama saurare yamik'ama youseef wayar yana furzar da isaka.
" naji youseef, shima zaibi jirgin 6:30pm ne zuwa Kano, kiramin Adams".
''OK sir".
Babu dad'ewa saiga Adams, cikin girmamawa yace, "gani sir".
''Ok, uhm dama inason naji katanadar mana jirginne?".
" yes sir!".
"Uhm Na k'arfe nawa?".
" 6:30pm".
"OK, bama saimunje kanoba, zamu kamashi a airport kawai. youseef kiramin Joseph, kace yayi shiri kune zakuje kama Munner, zuwa 6pm kaidashi Ku tabbatar kunzagaye airport, kaga insha ALLAH kafin akira sallar magriba kun gama da matsalar".
" babu damuwa sir, barama naje nasamu Joseph d'in a office, amma sir danazone please akan hajia, kadaure muje ka ganta, kullum saita ambaci sunank.........
Kasa k'arasawa youseef yayi, saboda wani mugun kallo da khaleel ya watsa masa.
๐๐ป" ALLAH ya huci zuciyarka sir".
Khaleel baice komaiba ya kauda kansa daga kallon youseef d'in.
Jiki a sanyaye youseef yamik'e, yay salute nashi sannan yafice.
Adams natsaye baice komaiba dai, amma shima yanason yarok'eshi akan yaje d'in, saidai yana shakka.
d'ago ido khaleel yay ya kalleshi, "akwai damuwane". 'Ya tambayi Adams yana maida idonsa a kan computer dayake latsawa'.
" a'a sir!, amma........
......Amman mi? Indai akantane karkacemin komai".
Yak'atseshi da Sauri.
Wani yawu Adams ya had'iye tareda girgiza kansa, shima saiyayi salute nashi yafice.
Binsa da kallo khaleel yayi, ya sauke numfashi tareda dafe kansa, ahankali yafurta momy kingama da rayuwata, ALLAH ne kawai kerik'e da zuciyata, amma datuni ta tarwatseโนโ๐ป.
Agurguje inji Perty๐
********
Alhmdlh aranar su Youseef sunsami nasarar cafke Munner, kuma cikin sauk'i da nasarori.
****
Kusan 8pm khaleel yakoma gida, saida yafara shiga cikin gidan, Dan yanaso su gaisa dasu Anty Mamie, yau yafita da wuri basu gaisaba.
K'annensa suna falon, harsu Hasnah, fira suketayi, su Affan naganin khaleel suka taso da gudu sukamasa oyoyo, rungumesu yayi shima yana farincikin ganinsu, d'ai-d'ai yabisu ya sumbaci kumatunsu, shima duk haka suka sumbaceshi.
Manyan kuma suka gaidashi. Da 'Yar sakin fuska ya amsa, yabisu da kallo d'ai-d'ai amma babu Aysha.
"Su mamafa?". 'Yay maganar idonsa akansu'.
" mama sunfita itada baffah, ummi Amarya kuma kanta ke ciwo ta kwanta, Anty Mamie tana d'aki itama."
Batareda yace komaiba yanufi d'akin Anty Mamie, saida yay knocking tabashi izinin Shiga sannan yatura k'ofar yashiga da sallama.
Da Aysha yafara cin karo zaune kusada Anty Mamie tana bata dambu abaki.
Suduka idonsu nakansa, duk suka masa sannu da zuwa.
A sanyaye ya amsa yanamaijin k'aunar mahaifiyarsa har cikin ransa. K'arasowa yayi ya zauna d'ayan gefen Anty Mamie shima.
"Babana andawo?".
Kansa ya jinjina mata, ya d'ora kan nasa agefen kafad'arta yana kallon Aysha, yace, " Mamie kidaina shagwa6a yarinyarnan, jiyafa ta6ara taitamin iri-iri."
Aysha tad'an murgud'a masa baki, tana fad'in "jealousy kawai".
Anty Mamie kam 'Yar dariya tayi, " babana aidolene Na shagwa6ata, bakaga ba ita kad'ai baceba, yanzu hakama abinci taci tayi amansa, shine matar zunnurain tayi dambu takawo mata, inad'an lalla6atane tanaci".
Rankwashi khaleel yamata agefen kanta, takuwa kware baki ta zabga k'ara tareda dafe kanta.
Da sauri Anty Mamie ta rungumota jikinta, shima tamasa rankwashi biyu akansa.
Dafe wajen yayi yana fad'in "uchhhh, dazafi wlhy Mamie".
" oooh kasan dazafin amma kama yarinyata? duk wata mugunta ka iyata babana salo-salo ko?".
"ALLAH Anty Mamie yarinyarnan batada kunya, kigafa murgud'en takemin harda gwalo? kibarni kawai Na caskalata".
Cikin 'Yar dariya Anty Mamie tamik'e daga tsakkiyarsu, ''kunga kutashi kuje 6angarenku, bazan iyaba dawannan rikicin, kuje wajan Ammah Tamuku shari'a".
" uhm tab, lallai Anty Mamie, yanzu naje wajan jar wuya aii bakina saiyaje gate, dama haushina takeji nak'i saya mata mota.
"Hhh kunfi kusa aii".
Jakkarsa Aysha tad'auka tafita tana dariya, tabarsu dansud'an gana.
Binta khaleel yayi da kallo yana murmuahi da jinjina hankali irin nata, yamaido kallonsa ga mahaifiyar tasa, wadda itama ayshan tabi da kallo murmushi d'aukeda fuskarta.
Khaleel yamatso kusada Anty Mamie, hannunta Na dama yakama ya sumbata, sannan yad'auki hannun yad'ora bisa kanta, murya amarairaice yace, " Mamie Na kisamin albarka, a office an za6eni cikin wad'anda zasu gana da shigaban k'asa gobe idan ALLAH ya kaimu, kuma nine shugaban dazai jagoranci kwamitin ma, wlhy duk fargaba tacikani, tunda safe naketa tattara bayanan dazanyi agaban shugaban k'asa ina kwancewa, narasa wanne zan d'auka, gashi inason kai kukana akan manyanmu danake zargi da hannu a k'ungiyar su momy."
Murmuahi Mamie tayi, tashafa fuskarsa da d'ayan hannunta, murya a sanyaye tace, ''karkakji tsoro babana, nasan kaid'in jarumine kuma jajurtacce, kasaka aranka CIKI DA GASKIYA, WUK'A BATA HUDASHI, shugaban k'asa mutumne kamar kowa shima kuma yanada sauk'in kai, danhaka karkaji tsoro ko shakkar ganawa dashi, katuna bayaune kafara ganawa da shugabannin k'asashen duniyaba."
"Duk inda kake addu'ata nabiye dakai, ALLAH ya albarkaci rayuwarku, yatsareminku aduk inda kuka tsinci kanku, kaje kayi wanka kahuta danka samu isashshen lokacin kanka".
" idonsa cikeda kwallah yace amin Mamana, farincikina, haske mai haska rayuwata, ALLAH yak'ara tsawon rai mai amfani da ingattacciyar lafiya", 'yak'are maganar da sumbatar hannunta'.
Jiki a sanyaye yamata sallama yafice.
Hawayenta tashare, tana murmushi, ahankali tace, "ALLAH Na gode maka".
6angarensu yanufa, dan baiga Aysha ananba, yasan tawuce.
Agurguje๐
___________________
Washe gari su khaleel suka samu damar ganawa da shugaban k'asa, sunsami tarba mai k'yau daga fadar shugaban k'asa, sunkuma tattauna muhimman abubuwa dazasu kawo cigaban k'asa, dakuma yanda za'a dak'ile ta'addancin dake faruwa ak'asarnan.
Sund'au tsawon awanni kusan 5 taredashi, tarema sukayi lunch da president da tawagarsa, yamusu jinjinar bangirma tareda k'yaututtuka masu k'yau, musamman ma khaleel saboda k'ok'arinsa, sannan suka gana da 'yan jaridu Na awa d'aya.
Sunyi sallama da shugaban k'asa suka tafi, bayan khaleel yabama wani makusancin shugaban k'asar short note domin yabashi.๐๐๐ป
________________
Akwana atashi babu wahala wajen ubangiji, kwanaki Na Sauri sati Na gudu, watani tamkar sati ya koma.
Acikin wannan gudun fanfalak'e da suniya takeyi yau ga cikin Aysha yashiga watanni takwas.
Abubuwa masu yawan gaske sunfaru awannan tsakanin, ciki harda kammala bautar k'asa da Aysha tayi, (Nysc) Alhmdlh tagama cikin nasarori.
Rufaida da sadiya duksun haihu, Aysha kuma taje har Kano suna, kwannta 8 a can, saboda khaleel baya k'asar alokacin, amma da k'yar yabarta taje.
Matar youseef ma ta haihu baby boy itama, hakama bishirah, ta haihu, da k'yar khaleel ya yarda Aysha tabi gwaggo bintu sukaje suleja suka mata barka.
Mufeedah ma baiwar ALLAH, anata Jan ciki, ita harma tashiga watan haihuwarta.
Ansaka bikinsu hasnah, watanni hud'u kacal, harda musleem dasu maleekah ma, baffah yace gwamma ya aurar dasu kawai yahuta baki d'aya, yazauna da 'yan k'ananun 'ya'yansa su ummunoor.
*******
Momy dai ana nan anata shan jinya, amma jikin NATA da sauk'i, saboda tana samun kulawa, Idan tayi magana anaji yanzu, sannan tana motsa hannunta kad'an-kad'an.
da k'yar khaleel ya yarda yashiga ya ganta tana barcima lokacin, danhaka batasan yajeba, yafad'ama su baffah suma sunje sun ganta.
Babu wanda bai zubar mata da kwallaba ganin yanda duk ta lalace, ta canja kamanni kamar ba itaba, k'ibarnan dukta zube.
Hawaye taita zurarrwa saboda ganinsu, magana take amma basajin mitake fad'a, dole suka hak'ura.
Saida Baffah yayta lallashi daban magana sannan khaleel yayarda yasakko innah jummai, amma da yasaka anyi rammm da ita a station d'in su, yace anan zata k'are sauran rayuwarta.
Saida k'yar da lallashi yayarda yasakota.
Rasa inda zata nufa tayi kuwa, doledai tadawo gidan mak'iyar tata Ammah, suna zaune awani yammaci kawai saigata tamkar an jehota.
ALLAH Sarki d'an uwa mai dad'i, saiga Ammah takar6eta da hannu bibiyu, suka rungume juna suna kuka, daneman yafiyar juna.
Annan innah jummai tazauna sabodama batada isashshiyar lafiya, ciwon k'afa da hawan jini.๐
____________
Su khaleel duksun gama shirye-shiryen kai k'ungiyar su momy kotu, sunsami nasarar cafke sauran mutanen dasuke zargi, dakuma kar6o Na k'asashen k'etare, ciki harda manya-manyan mutane wad'andama bazaka ta6a tunanin akwai saka hannunsuba............โ๐ป
๐คธ๐ปโโ๐คธ๐ปโโkumuje zuwa yanda zata kaya a kotu, dolene masu laifi su kar6i hukuncinsu ahannu๐๐๐ฝ.
๐คyanzu saboda buk yazo k'arshe, ankama muku hajia babba shine babu comments ko, aiko zan ajiye nak'i k'arasa typing d'in๐, rashin comments d'inkuma yasakani jin gandar typing d'in wlhy,โน.
Idan naga ruwan comments yau, kwaji yanda takaya gobe, idan naji shiru, nima nawuni barci abuna yafimin dad'i๐๐.
Yawan comments, yawan girman hukuncin su hajia babba๐๐๐๐ฏโโ
*_I love you all_*๐๐๐๐
[10/26, 4:29 PM] Aysha Galadima: *_Typing๐ฒ_*
๐คฐ๐ป
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{๐ชwuk'a bata hudashi๐ก}_
*_Bilyn Abdul ce๐ค๐ป_*
*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_
*_part 2_*
_(littafi na biyu๐)_
_ina kike *Asy khaleel*?, wanga page nakine, babanki khaleel namik'o gaisuwa ta musamman, taredani bilyn Abdul๐._๐๐ป
Kuma banmanta dakuba wlhy.
Fatima Abubakar, Ummi Alhassan, Rabi Sanusi, Aaliyah, Fatima, Zainab Ahmad, Xeety, Sameera Bello.
Alkairin ALLAH ya iso gareku๐๐๐๐โค๐ค๐ป
4โฃ9โฃ
*_Monday morning_*
_Cote_.
A yau ranar litinin 8/9 aka shiga shari'arsu momy, abbabban kotun k'asa da k'asa ta Abuja.
Anyi zammne misalin 10am, tareda lauyoyi masu kare gwamnati dakuma lauya mai kare 'yan ta'addar wannan k'ungiya.
Bayan Alk'ali ya saurari k'arar dakuma jawabai abakin lauyoyin guda biyu.
Am fafata sosai, amma ba a yanke hukuncinba, sai azama Na gaba insha ALLAH.
Ran khaleel yad'an 6aci, soyayi ayita kawai yau ta k'are, amma babu komai, ALLAH ya kaimu randa alk'alin yasaka.
Aysha Na zaune afalo zama da k'yar tashi da dabara, dukda cikin nata bawani uban girma yayiba, kunsan cikin fari dama bakowanne keyin k'atoba.
Sallamar ya khaleel yasakata d'ago ido ta kalleshi.
Cikin murmushi tace, "sannu da zuwa sadauki na, yau da wuri haka?".
Kusada ita ya zauna yana murmushin shima, yadurk'uso ya sumbaci cikinta, " babies na inafata kuna cikin k'oshin lfy? Injidai maah-maah tabaku abinci?".
"Tab abinma dariya, ALLAH Sadauki idan kana wannan abun dariya kake bani, waya gayamaka yara biyune to?."
Matsawa yayi sosai, ya mannata da jikinsa, acikin kunne yarad'a mata abinda nima banjiba.
Aysha ta tureshi tana fad'i ''kai kai ALLAH nidai babu ruwana, saima Na fad'aka da Ammah".
"Hhh dubeta kamarma zata iya".
" OK haka kake zaton bazan iyaba ko? Kajira sammaci". 'Tayi maganar tana komawa k'asa'.
K'afarsa takamo tafara k'ok'arin cire masa takalman.
Shikuma yana fad'in "kibari kawai, kinma tunamin wlhy, wai shegen alk'alinnan dukda hujjoji da lauyanmu yabayar yad'aga zaman kotun nan harsai next week".
" to aii babu komai sadauki, dayau da wani satin duk d'ayane, insha ALLAH za'a yanke musu hukunci dai-dai dasu, wahalarmu bazata tafi abanzaba aii, mugodema ALLAH ma da nasarorin daya bamu duk aka kamasu".
"Hakane kuma sholyna, su john ma k'asarsu hukuncin kisa ta yanke musu".
" woow! Dan ALLAH da gaske sadauki!?".
"I'm telling you".
" kai alhmdllh, amma naji dad'i sosai wlhy, nasan Anty meerah saitafi kowa farinciki dahakan, tsinanne, dama dukmasu hali irinnasa k'arshensu kenan, sugama tara dukiyar kuma daga k'arshe tazama mara amfani agaresu, saidai wasu suci kuma".
"Hakane wlhy sholyna, gadai su momy nan inda suka k'are, ita wannan ciwonma data tsinci kanta kad'ai ya isheta, munyi magana da Anty zuwairah akan dukkan kud'ad'e da kaddarorin momyn, kawai zamu kaisu gidan marayu, danbanga amfaninsuba, baffah yace babu Wanda zaiyi amfani dasu agidannan".
''Hakan shine dai-dai aii sadauki, to Amma su Lola fa? naga suma sakasu akayi bashiga sukayiba".
" eh, hakane, amma kinsan mutanenmu da bushewar zuciya, dukda sunga an hukunta wad'annan bazaisasu dainaba suma, sunrigada sun saba da iskancin, dakuma kama kud'ad'e masu nauyi, yanzu koda an sakesu suma tasu dabar zasuje su kafa. Amma dai munan muna tattaunawa akansu, sauran yaran kuma duk mun maidasu hannun iyayensu".
"Aii kunyi dai-dai wlhy, jaridun k'asarnan gaba d'aya wannan satin labarinkune kawai aciki, nasan gaba d'aya idanun al'ummar Nigeria Na kanku yanzu, kai duniyama baki d'aya, jira kawai akeyi aji irin hukuncin daza'a yankema wannan k'ungiya".
"Hakane wlhy, yanzufa da k'yar Na kufto daga hannun 'yan jarida, Taheer nabar musu nagudo, saiya bar wajen yayta tsinemin azuciya d'an iskan".
Dariya Aisha tayi, tace, " aiini wlhy birgeni kukeyi, yanda kuke tafiya da rayuwarku a tsari, idan fannin aiki kuke komai cikin girmamawa suke makashi, basa kallon kaid'in abokinsune, hakama idan aka dawo fannin abota kashige cikinsu kuyita barkwanci, baka kallon kai ogansune awajan aiki, lamarinku daban dana sauran jama'a sadaukina."
"To miye duniyar Sholyna, watarana komai saikiga yazama tarihi, saidai atuna sunanmu badai mud'inba, su Youseef mutanene masu kwazo, kinga tunda nabasu shawarar mukafa k'ungiya taimakon matasa babu musu suka amincemin, yanzu haka nake fad'a miki mun samama matasa kusan 200 aiki wlhy, banda wad'anda muka samama sana'oi, dakuma wad'anda suka koma makaranta, aikinga wannan nasarace, watarana basaikiji sunkai irin dubu biyar d'innanba, inaga hakane yakamata masu kud'in k'asarmu sunayi, musamman ma 'yan arewa dan mutanan kudancin k'asarnan tuni sun waye da irin wad'annan taimakon, amma 'yan arewa ina, kowa burinshi akirashi wane, zakiga kowanne banki mutum yanada kud'i, gawasu agida, motocin hawa Na alfarma, saka manyan kaya masu tsada, agogo wannan saikiji Na million d'aya ahannunsa, 'ya'yansa kowanne yanada account nakansa, ga hannun jari a ma'aikatu daban-daban, shin dukmi zakayi dasu?, kasan dai baza'a gina rami arufeka dasuba ko?, kiga mutum yak'are rayuwarsa kaf aneman dukiya, babu kwakwkwarar ibadar dazai rik'e tazame masa guzurin shiga kabari, wlhy kaiconmu dawannan makauniyar rayuwa, bazakasan kana cikin babbar asaraba sai mala'ikin mutuwa yazo kanka, lokacin babu tsumi babu dabara kuma?".
"Wlhy hakane Sadauki, ai gaskiyafa 'yan arewa muna cikin halin hau, kowa dagashi sai 'ya'yansa, shiyyasa kullum kuma mune abaya, masu k'aunarmu da gaskiya dason dawomana da martabarmu irinsu BUHARI kuma toshewar basira tahanamu ganewa, munfison awatsa mana tsaba mu tsatstsage alokacin, batareda munyi tanadi wa gobenmuba, inhar za'a cigaba da tafiya haka aii wataran sai'an shafe tarihin arewa da al'ummar cikinta, shiyyasa nake tausayin 'ya'yanmu wlhy".
" dolene subaka tausayi, ayanzuma jibi yanda duniya take walagigi, inaga nanda shekaru 20 masu zuwa, ALLAH ka gafarta mana dai kawai."
"Ameen to". 'Aysha tafad'a tana yunk'urawa zata tamik'e'.
Saida ya taimaka mata sannan tasamu tatashi.
"Sannu sholyna kinji, insha ALLAH saura kad'andai ki juyomin babies d'ina ki huta muma mu huta".
"ALLAH ya kaimu, dama nagaji nikam, tashige kichin".
Shima mik'ewa yayi yana dariya dafad'in ''k'ya gaya musu yarinya, kina juyewa zankuma ajiye wani aii".๐๐
******
Rana bata k'arya.......
Yaukam kotu tacika dank'am da jama'a, su Kansu 'yangidansu ya khaleel kwansu da kwarkwata sun halarci zaman, harda innah jummai datak'i komawa Jigawa har yanzun๐คฃ, saboda tsoron dariyar mutane, da anamusu fafa su masu kud'i.๐คช
Tunda hajia babba taga gayyar 'yan gidansu taketa zubda hawaye, tama kasa had'a ido da kowa awajen, su kansu duk hankalinsu nakanta, ko kad'an Aysha bataji tausayin kowaba acikinsu, musamman ma hajia babba da hajia khaltum, glory, kubrah. Saima d'an karan dad'i dake ratsa zuciyarta da ruhinta, yauga mak'iyanta gurfane agaban kotu, abinda bata ta6a zaton zai faruba ko a mafarki, dantasha jin labarin makamanta wannan cases d'in natafiya abanza, batareda ankama koda masu laifinbama bare agurfanar dasu gaban kotu.
Kotu tayi tsit ana sauraren jawabi daga lauyoyin na 6angarori biyu, lauyan gwamnati yakawo kwararan hujjoji, tareda manyan shaidu irinsu ya khaleel, wad'anda ganaune ba jiyauba.
Shiru nawani lokaci Alk'ali yana bincika hukuncin dazai yanke.
Alfarma hutun mintuna talatin aka d'auka, Alk'ali da jama'arsa suka shiga wani d'aki domin tattaunawa.
Kusan mintuna talatin saigasu sun shigo, alk'ali ya zauna, bayan wasu 'yan mintuna yad'ago idonsa dake sakaye acikin glass yana kallon jama'ar kotu, yay gyaran murya tareda gyara zamansa.
"Wannan kotu mai alfarma tayankema wad'annan mutane hukuncin dai-dai da laifinsu, saboda fasa kaurin miyagun kwayoyi dasukeyi, dakuma safarar yara mata, tawani fanninma harda makamai, laifinsu yahad'u dayawa, wannan yasaka bamuda kwakwkwaran hukunci, bisa nazari dawannan kotu tayi, da taimakon manyan lauyoyi anyankema dukkan wani dake cikin wannan k'ungiya hukuncin d'aurin shekaru 40 babu Tara, sannan babu wani dakeda lasisisn fitar dasu koda wata gewamnati tazo annan gaba, akwai horo mai tsananin gaske da azabtarwa da'aka tanada musu agidan kaso.
Mutun uku acikinsu basuda isashshiyar lfy, d'aya tasamu sauk'i, za'a wuce da ita gidan kaso, amma akwai alfarmar idan anga ciwonta yatashi amaidota asibiti tacigaba da kar6ar magani, idan tasamu sauk'i sai'a maidata cikinsu.
Guda biyukam abarsu a asibiti sucigaba dashan magani harsu sami sauk'i sannan asakasu cikin 'yan uwansu.
Akwai jami'an tsaro 26 acikinsu, wannan kotu tamik'a nasu case ga hukumominsu, zasumusu hukunci a cotes nasu, ga sunayensu kamar haka.........
Tsaf Alk'ali ya lissafoau, harda Ak'ilu Abbas, dakuma wani ogan khaleel Wanda khaleel yata6a fad'a masa saiya binciko dukmasu hannun alamarin, dawasu k'ananun ma'aikata.
Sai tsine musu akeyi, khaleel yay murmushin jin dad'i tareda fad'in Alhmdllh, yakai dubansa ga momy wadda itama shid'in take kallo, idonta cikeda kwallah, kasa jurar kallonta yayi, domin haryanzu tanada kima a idonsa, dukda tareneshi akan wata manufa tata tadaban, shi kallon uwa yake mata har gobe.
Daganan kotu tatashi.
Bayan duk an fito khaleel yaja tawagar 'yan gidansu har inda hajia babba take akan keke ana turata, saboda bata iya tafiya.
Cikin takun k'asaitarsa da jarumta tareda izzar kwarjini Na nutsuwa da cikar kamala yake nufota, kallonsa takeyi wani tuk'uk'in bak'inciki Na azabtar da ruhinta, saidai babu damar koda magana.
Baice komaiba yaja gefe yatsaya, tareda jingina da bango ya hard'e k'afafunsa da hannayensa ak'irji.
Baffah ne yake magana cikeda 6acinrai, tunda abinnan yafaru saiyau bakinsa zai furta wani Abu kuwa.
"Laure kinga k'arshen mutum mara godiyar ALLAH ko? Kinga yanda rayuwar mutum mai buri da hassada take k'arewa, komi katara, komin k'arfin ikonka saika dawo k'asan k'asa, mutum mak'ask'anci, shin miye ribar
Book Chapters
Chapter 36
Chapter 37Chapter 38Chapter 39