Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shape mai kyau da diri. Fuskarta ɗauke yake da dara daran idanu, bakinta ɗan ƙarami ne pink color, sai dogon hanci da yayi tsini har baka, in tayi dariya dimple ɗinta sai ya lotsa, gashin giranta tamkar anyi mata kabin, Basma tanada yalwataccen gashi har gadon baya, mai silɓi da baƙi sosai, Basma ta haɗu domin ko ba makeup fuskarta a haɗe take, Allah ya gama halitta anan. A fili in ka ganta za kayi zaton za tayi nauyi amma ana ɗaukarta shagwal take, kyau dai ta haɗa na Barebari da kuma Fulani. Masu karatu ya kuka hango kyawun Basma, abin ba acewa komai lol😃.

A hankali take taku, saboda dogon takalmin dake ƙafarta, a haka ta isa part ɗin su Yaya Ahmad, ta same shi yanata waya ganinta ne ya sashi saurin kashe wayar, galala yayi yana kallon halittar Allah, haɗiya miyau yayi a zuciyansa yace
"gaskiya Basma kin haɗu, dole in fara lasar zumanki kan muyi aure, dan bazan jure ganinki haka ba" a fili kuma yace
"walcome my Baby" ya buɗe hannu domin taje tayi hugging ɗinshi, rungume hannunta yayi ta gyara tsayuwa, domin ba zata iya abinda yake nufi ba, miƙewa yayi ya isa gab da ita kamshin turarensu ya gauraye gurin, kama hannunta yayi sai ta runtse ido, ƙoƙarin rungumeta ya shiga yi, da sauri ta janye tace
"miye haka Yaya Shureym, ka bari kaci abinci mana" dariya yayi yace
"afwan gimbiyata ganinki ne duk ya ruɗani, muje ki zuba min" suka je suka zauna, ta zuba masa abincin ya soma ci, yana santi duk a haukansa ya ɗauka ita tayi.

Bayan ya kammala ci, saiya miƙe yaje ya wanke bakinsa ya dayo, ita kuma ta zauna akan kushum tana jiran dawowarsa, daya dawo saiya zauna kusa da ita, hannunta ya kama yace
"Basma ina sonki sosai, gobe ina son zamu fita zaki rakani wani guri da yamma" tace
"ok Allah ya kaimu".
Wasa ya farayi da yatsun hanunta, yana mata magana rad'a-rad'a, janye hannun tayi tace
"haba Prince ka bari mana" sosa k'eya yayi yace
"haba my Basma ya kike yi kamar baki waye ba, ina ce a England kika yi karatu, ai nasan duk kin waye da irin wannan ai" gaban tane ya fad'i tana tambayar kanta
"shin me wannan yake nufi?" a ranta, bata ankara ba taji ya rungumeta yana kokorin yi had'a bakinsu guri d'aya, ai da sauri ta fara kiciniyar kwatar kanta, shi kuma ya rik'eta gam, Sallaman da Yaya Ahmad yayi ne ya shigo, shine yasa yayi saurin sakinta, ita kuma ta mik'e da sauri tayi k'ok'arin barin d'akin da gudu, Shureym ne yake kiranta amma ina ta fece a guje, haka ta isa part d'in Ammi tana haki, Allah yasa bata tadda kowa a falon ba, saita wuce d'akinta ta fad'a kan gado, runtse idonta tayi tana mai ambaton Allah, tsanani damuwa ta shiga, yanda Yaya Ahmad yazo ya gansu shine matsalanta.

Acan kuma Yaya Ahmad yace
"haba Shureym wallahi ba girmanka bane yin haka, iskancin da kake yi a can America sai kace zaka gwada a kan k'anwarka, kuma akan matar da zaka aura?" shafa kansa yayi yace
"to meye? ai aurenta zanyi, kuma ma kasan duk abinda zanyi bazan wuce gona da iri ba" tsaki Yaya Ahmad yayi yace
"Allah ya shiryeka" bai jira Mai zaice ba ya fice a falon. Bayan Basma yabi, yasan tabbas tana part d'in Amminsa, can ya wuce ya sameta a d'akinta ta kwanta, jin an shigo mata d'aki ne yasa tayi saurin d'agowa ta zauna, Yaya Ahmad ya rufe d'akin, ya jawo wata kujera ya zauna ya fuskanceta, sunkuyar da kai tayi k'asa tana wasa da hannunta, kiran sunanta yayi yace

"Basma, ban sanki da hali haka ba, ko da yake nasan shaidani ne shi, amma kuma duk da haka da laifinki Basma, kinje har d'akinmu a wannan shigar kuma ba mayafi, sannan kuma daga ke sai shi, kin san cikon na ukun ku shaidan ne, Basma mace da Namiji ba aso suna keb'ewa haka, in dai ba mata da miji bane, ki daina d'aukar Shureym a matsayinmu, domin mu jininki ne, shi kuma aure zai shiga tsakaninku, dole kiyi taka tsan-tsan dashi domin na fiki sanin waye Shureym".

Dago jajayen idonta tayi tace
"Yaya kayi hak'uri ba laifi bane, shine ya matsamin, ina k'ok'arin kwacewa ne kazo ka samemu a haka"

"eh, Nagani ai, ina so in dai zaki sashinmu, tofa ki tafi da su Na'im da Anwar, karki yarda kina keb'ewa dashi ke kad'ai" tace
"to Yaya Ahmad, insha Allah zan kiyaye"
"yauwa k'anwata" nan yayi ta mata nasiha har ta saki jiki sukayi barkwanci, kana yayi mata saida safe ya wuce.
Basma ji tayi duk Shureym d'inma ya sire mata a rai, bata zata haka yake ba, amma ta d'auki alkhawari za tayi maganinsa.

*Washe gari*
Da misalin k'arfe 4:30pm na yamma Basma ta shirya cikin riga da sket na kanti, ta sanya lafaya, ba k'aramin kyau tayi ba, yau ta fito a 'yar Maiduguri sosai, fitowa tayi su Anwar da Na'im suna biye a bayanta, suma sunyi shigan kananan kaya sunyi kyau, shekarunsu zai kai 16yrs, har motan Prince suka isa, sai ga shi ya tawo, tun daga nesa yake washe baki harya k'araso, ganinsu twins ne yasa yace
"My Basma kin ga yanda kika yi kyau kuwa" murmushi tayi ba tace komai ba, yace
"ba dai da su twins zamu tafi ba?" da murmushi a fuskanta tace
"tare Zamu tafi, ko akwai Matsala ne?" bata rai yayi yace
"amma ai kinsan ba haka mu kai dake ba ko?" kafin ta bashi amsa twins suka ce
"Haba Yaya Shureym me mukayi da ba za'a damu ba, mu gaskiya sai munje" Basma ma tace
"in ba zamu dasu ba sai dai a fasa tafiyan" k'ara tsare gira Shureym yayi, sai ya bud'e mota bai ce komai ba, haka su ka tafi tare badan ransa ya so ba, har suka dawo Prince bai saki fuska ba. Siyayyan kayan kwalama yayi musu suka dawo, Basma ko a zuciyarta sai dariya take yi.

Bayan Sallan Isha'i, Yaya Ahmad ya shigo falon Ammi, bai sameta a falon ba, saiya wuce wurin Basma ya sameta tana danna system d'inta, rufewa tayi suka gaisa, ya samu guri ya zauna tace
"Yaya Ahmad kasan yanda nayi yau da mutuminka kuwa?" cikin dariya yace
"wa kenan?" tace
"Yaya Shureym mana" nan ta kwashe yanda suka yi ta bashi labari, aiko sai ya kwashe da dariya yace
"good k'anwata, yanzu ma ko yace kije side d'inmu karki je, kice yazo falon Ammi kuyi hiran, kinga ai ba zai yi shakiyanci anan ba" dariya itama tayi tace
"sosai ma kuwa, ai ba zai yi ba, maganinsa zanyi ai tunda shi shaid'ani ne" dariya yayi yace
"Mijinki ne dai ba ruwana, yauwa gobe ne fa zaki kawomin patient d'ina ko?" Tace
"eh, insha Allah gobe ne zanje har gida na d'aukota,
"to Allah ya kaimu"
"Ameen". Nan suka yi sallama ya wuce.

*Washe gari*
Da misalin k'arfe goma na safe, Basma ta shirya ta fita cikin shigar doguwar riga na atamfa ya kamata daga sama k'asa ya bud'e, babu wani kwalliya a fuskanta, ta shiga motanta sai d'aya daga bodyguard d'inta yazo zai yi magana tace
"yau ni ka d'ai nake jin fita ba dad'ewa zanyi ba" daga wannan bata sake magana ba ta tada mota tayi gaba.

Yau ak'ofar gidan tayi parking ta shiga a nutse, ta samu Deeja tana wanke-wanke, da sallama ta shiga, Deeja ta mik'e da sauri tace
"sannu da zuwa Anty Basma" Basma ta amsa cike da fara'a, tabarma ta d'auko ta shinfid'a mata ta zauna, tace
"Deeja ina Umma" tace
"Umma ta fita mak'ota dubiya yanzu zata dawo, bari na k'arasa wanke-wanke kan tazo" Basma ta mik'e tace
"bari na tayaki" da sauri Deeja tace
"a'a ki barshi nagode" ai sai ta b'ata rai tace
"baki so na samu lada ne nima?"
"a'a inaso ki samu, gani nayi daga nin ki baki saba da wahala ba" dariya tayi tace
"haka dai kika gani" haka ta sanya mata hannu tana d'auraye kayan tana kifewa a kwando suna kuma hira.

Yaya Aryan ne yayi sallama ya shiga, ai sai gaban Basma ya fad'i, da sauri ta waiga aiko tsaraf suka had'a ido nan take gabansu ya fad'i dukansu, mamaki ne ya kama Aryan, sai da suka yiwa juba kallon tsayin minti uku, kana ya je ya zauna kan wata kujera, Deeja ce tace
"Yaya ba kaje kasuwan bane?" yace
"naje, wani Abu nazo amsa gun Umma"
"ok, aiko ta fita amma bazata dad'e ba" a sanyaye Basma ta k'arasa taya Deeja wanke-wanke, ta koma ta zauna, Deeja ta d'au kayan ta kai kicin ta dawo ta zauna gefen Basma, tace Basma ga Yayana Aryan"
"ok" tace, Deeja ta kai dubanta ga Yaya Aryan tace
"Yaya Aryan ga Basma nan, wanda na baka labari, yanzu ma tazo muje asibity ne a k'ara dubani" murmushi yayi na gefen baki yace
"ok na ganta" sai Khadija taji abin yayi mata wani iri yanda Yaya Aryan yace, Basma tace
"ina kwana" tayi maganar a sanyaye, amsawa yayi a dak'ile, sai ya mik'e yace
"Deeja zan koma, anjima zan dawo, dan yau ba zan dad'e ba a kasuwan"
"To adawo lafiya" Basma ta bi bayansa da kallo.

Saita juya tace
"dama wannan ne Yayan naki?" da murmushi Deeja tace
"eh" Umma ce tayi sallama sai duk suka amsa, nan Basma ta gaishe ta, ta kuma bayanin komawansu asibity, Umma tayi godiya tace
"to sai kun dawo" Deeja ta d'auko hijabi ta sanya suka wuce. Umma da mamaki tace
"ikon Allah, Basma sam bata kyamarmu".

*Rahma Ce*
[8/3, 5:01 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *7.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

Basma da Deeja suna tafe a hankali a cikin mota, Basma ta kalli Deeja tace
"Deeja dan Allah ina son ki bani tarihinku a tak'aice in ba damuwa" murmushi Deeja tayi tace
"ba damuwa Anty Basma" nan ta fara bata labarinsu tas a takaice, har suka isa Asibiti zancen suke yi, Basma tana girgiza kai alaman tausayawa sosai.

Bayan sun isa Asibiti, suka tadda Yaya Ahmad a office d'insa,  ya duba Deeja ya k'ara bata wasu maganin kana ya sallamsu yace
"an gama ba zata k'ara dawowa ba" Basma ce tace
"ok Yaya godiya muke" murmushi yayi mata yace a cikin harshen yaran barebari,
"Basma, Khadija tana da kyau, ko kin lura da haka kuwa?" da murmushi a fuskanta ta mayar masa cikin yare,
"sosai ma kuwa, haka Yayanta yake kuma yama fita kyau, ita tafi kama da Ummansu" murmushi yayi yace cikin sigar wasa
"to kina ganin inna zab'eta tayi?" zaro ido tayi waje tace
"Yaya talakawa ne fa, amma kana ganin su Ammi zasu yarda?" dariya yayi sosai yace
"mai zai hana suk'i yarda, damu dasu duk d'aya muke a gurin Allah, face wanda yafi wani imani, kawai ke zaki wayar da ita sosai ta zama kamar yanda kika waye, sannan zan sata a makaranta tayi karatu, kinga ai shikenan ba mai hanani aurenta" murmushi tayi tace
"hakane Yaya Ahmad, ni ai wallahi ka sani farin ciki sosai, dama kuwa kasan abin da nake shiri kenan na maidata makaranta" dariya yayi yace
"to na rigaki buk'atar samun Ladan" itama dariya tayi tace
"yauwa Yaya Ahmad, ya za ayi ka samar ma Yayanta aiki a company Abbanmu, yana da diploma a computer science, kaga in an d'aukeshi sai ya koma karatunsa, yayi digree da masters, kuma yana aiki ana biyansa salary mai kyau" murmushi yayi yace
"shawara mai kyau, kinga mun taimaka su, tunda suna cikin buk'atan haka, kuma dama amfanin Arzikin kenan, in ka samu ka bama na k'asa da kai, zansa ma a k'ara yiwa unguwarsu titi, zamu d'auki matasan unguwan marasa k'arfi mu sanya su a makaranta, dan naga unguwar akwai mabuk'ata sosai" tace
"da kyau Yaya Ahmad, wannan shawaran yayi, Allah ya bamu ikon yi" yace "Ameen" duk wannan hiran cikin yaransu na barebari suke yi, Deeja tayi shuru tana saurarensu amma bata fahimtar me suke cewa, computer science d'in da Basma tace, shine ya bata damar fahimtar k'ila hiran da sukayi da ita ne, take gaya masa.

Mik'ewa Basma tayi tace
"Yaya bari mu tafi" murmushi yayi yace a cikin harshen labaraci
"ki kulamin da Matata, karki sake ki gaya mata ba yanzu ba tukun, kuma ina so ki b'oye musu asalinmu, saboda su samu damar sake jiki damu" murmushi tayi tace itma cikin larabci,
"ai Yaya bazan fad'a ba, zance musu Mom d'nmu da Dad basa k'asarnan suna Canada, muke Nigeria da sauran family d'inmu, kuma gidan hutuna shine gidan iyayenmu, kaga bazasu gane ba" Cikin harshen turanci yace
"good girl" tana dariya suka fita, Deeja dai jinsu  takeyi, tad'an so ta fahimci hiran amma bata gane ba saboda batajin labarci sai kalmomi kad'an take iya tsinta.

Suna tafe a hanya suna hira a yanzu Deeja ta saki jiki sosai da Basma, koda suna kusan sa'a amma akwai girmamawa na musamman da Deeja kewa Basma, Basma tace
"Deeja samu shiga kasuwa siyayya" tace
"to Anty Allah ya kaimu lafiya".

Sunje Babban shago na saida kayan kanti, side d'in maza suka fara shiga, riga da wando ta siya kala biyar k'ananun kaya, sai manyan kaya shadda da material na maza kala biyar d'inkakku,  sai su singilet da gajeran wando guda biyar-biyar, sai takalmi kala hud'u, huda kala biyu, da kuma turare masu k'amshi har kala Hud'u, sai a gogo kala biyu. Aka sanya kowanne a jaka, ta bada kud'i aka sanya musu a mota.

Suka shiga side d'in mata nanma kaya ta sanya Deeja ta zaba kananu da kuma lesshi da atamfa, hatta gyale, takalma da d'an kunne duk ta siya mata, sannan ta siyawa Umma nata kayan kala uku da mayafi, takalmi da d'an kunne da sarka, harda turare, Siyayya suka yi sosai kana suka wuce gida.

Suna isa suka fara shiga da kaya, Umma ai bud'e baki tayi tana kallon kayan cike da mamaki, saida suka shigo dashi tas, Basma ta ware na Yaya Aryan tace
"Deeja ina d'akin Yaya Aryan yake?" Deeja tace
"shine can da yake kallonki" tace
"d'akin abude yake?"
"Eh a bud'e yake kullun" Umma kallonta take kawai ta kasa magana, Basma ta nufi d'akin ta bud'e, ba laifi d'akin ba wari yana k'amshin turaren wuta na tsinke, sai dai d'akin akwai datti da tarkacen kaya, aiko shiga tayi ta bud'e k'ofar, ta fara kauda kaya kana ta samu tsintsiya ta share d'akin, har wani gumi ta had'a abinda ba'a saba yiba, Deeja tazo zata tayata tace ta barshi itama zata iya, tana gama sharan ta kakkab'e zanin katifar ta gyara kana tazo ta kwashi kayan data siya masa ta aje gefe guda, ta fito tana sharce zufa, Umma ne tace

"Sannu da k'ok'ari Basma Allah ya miki albarka, ya baki miji nagari, yasa ki gama da duniya lafiya" ta k'arasa maganar tana matsar kwalla, Murmushi Basma tayi ta k'arasa kusa da Umma, zama tayi gefenta a kan tabarma tace

"Umma na d'aukeki Uwa a gareni, duk abin da na muku na yiwa kaina ne domin Uwata nayi mawa, kuma Umma meye amfanin kud'in da za'a tara a aje ba'a yi taimako dashi ba, ki d'auka tamkar ke kika haifeni Umma, domin Allah ya riga ya had'amu, iyayena basa nan suna k'asar waje dagani sai Yaya na Ahmad da kuma sauran danginmu, lokaci-lokaci suke zuwa nan domin mu munk'i zama dasu, munfi son zama a k'asarmu, Umma iyayenmu suna bamu kud'in wanda bamu san me zamu yi dashi ba saboda yawansu, kinga kuwa danna bayar wa Alumman Annabi bamu
Fad'i ba"

Da murmushi a fuskan Umma tace
"kwarai kuwa Allah ya saka da alkhairi"
"Ameen Umma, kuma nayi magana da Yaya na yace zai mai da Khadija makaranta, yace in gaya muku kafin yazo" Umma cike da farin ciki mara misaltuwa ta rungume Basma, Deeja kuwa tsalle tayi ta dawo kusa da Basma, godiya ta shiga zuba mata sosai tamkar ta biya mata saudiya.

Haka sukaita murna suna zuba mata godiya, Basma ta d'auko takadda a jakarta ta shiga rubuta short note, ta bama Yaya Aryan hak'uri akan abinda tayi masa. Tana gama rubutawa ta mik'e ta je ta sanya letter a cikin d'aya daga cikin jakukunan kayan data siya masa, kana ta fito ta d'auki Jakarta tayiwa su Umma sallama, Umma har k'ofar gida ta rakota tana shi mata da albarka tare da addua, Deeja kuwa har mota taraka ta.

Basma na isa gida wanka ta yi ta dad'e cikin ruwan zafi tana gasa jiki domin yau ta kwaso gajiya, tana fitowa ta shirya ta wuce part d'in Momynta, ta same ta zaune bisa dadduma ta idar da sallan La'asar, zuwa tayi ta kwanta ajikinta cike da shagwab'a tace
"Momy kin jini shuru yau baki nime ni ba?" murmushi tayi tace
"ai kwanakin nan naga kamar kinyi hankali ne, kodan basu Leema ne k'ila" dariya tayi tace
"kai Momy, dama can ma haka nake, hala su Na'im suna islamiya?"
"eh suna can, wai ke kuwa yaushe rabon naga kina karatun al'Qur'ani?" murmushi tayi tace
"Momy ina karantawa bayan sallan Magrib da kuma in zan kwanta barci, a wata sau biyu nake saukewa fa"
"Masha Allah haka nake so ki rik'a kula da ibadarki sosai"
"tom Momy zan kula insha Allah, Momy dama ina son muyi magana akan yarinyar dana bige rannan, sunan ta Khadija" nan ta shiga bama Momy labarinsu kaf da kuma abubuwan da tayi musu, da ma taimakon da take shirin yi musu ita da Yaya Ahmad, Murmushi Momy tayi na farin ciki tace
"Basma ban tab'a tunanin kinyi hankali irin haka ba sai yau, wannan abu da kike yi tunani ne mai kyau, nima zan bada tawa gudun mawar akai, sai muyi tarayya a cikin Ladan gaba d'aya, zanga Ahmad saimu tattauna akan gyaran unguwar da taimakon mutanan unguwar, Allah ya bamu ikon yi da iklasi" tace
"Ameen Momy, kin amince in cigaba da taimaka musu kenan?"
"sosai kuwa na amince, ai in dai wannan ne sai inda k'arfi na ya k'are wajen baki goyen baya, kuma mun taimaka wa Abbanku ne, tunda shike Mulkan k'asatar nan"
"hakane Momy"

kamar zata gayawa Momy k'udirin Yaya Ahmad akan Deeja saita fasa, saboda ta d'aukar masa alkhawari akan bazata gayawa kowa ba. Haka suka cigaba da hira na 'Ya da Uwa har barci ya d'auke Basma, Momy kuma ta cigaba da lazumi, sai gabda sallan Magrib ta tasheta, sannan duk suka nufi d'aki.

Yaya Aryan ya dawo da yamma lis, ya samu Umma tana tuka tuwo, ya gaisheta kana ya nufi d'akinsa, yana tura k'ofa ya shiga yaga daki fes an gyara, bai k'ara tsinkewa ba saida ya hango jakukuna a gefe, da sauri ya juyo ya kalli Umma yace
"Umma waya shigan min d'aki kuma jakukunar waye a ciki?" Murmushi tayi tace
"ka shiga ka duba akwai sak'on bayani a ciki" Deeja ce tayi tsaraf tace
"Yaya Aryan kayanka ne da" bata k'arasa ba Umma tayi mata dak'uwa tace
"yi min shuru a wurin nan, ya shiga ya gani mana da kansa, ya tsaya yana tambaya" jikinsa a sanyaye ya koma d'akin, zama yayi dirshen a ledan d'akin, ya shiga fidda kayan dake jakukunan d'aya bayan d'aya, harya isa jakan da huluna da agogo ke ciki, yana ciro hula sai letter ya fad'o, da sauri ya aje hulan ya shiga bud'e letter, gyara zama yayi ya soma karantawa kamar haka

*Assalamu Alaikum*

*"Yaya Aryan nasan zaka yi mamakin ganin sak'o na, da farko ina mai baka hak'uri akan duk abin da na yi maka kwanaki, hak'ik'a nayi kuskure, kuma naji kunya d'azu sosai, saboda bansan kaine Yayan Deeja ba."*

*"Yaya Aryan wannan kayan naka ne, a matsayina na k'anwarka na siya maka, karka d'aukesu a matsayin na raina maka ne, wallahi nayi maka dan Allah ne, domin a yanzu ka zama Yaya a gareni."*

*"Dan Allah kar kace ba zaka sanya kayan ba, domin in kayi amfani dasu, hakan ne zai nuna min ka yafemin akan abinda ya faru tsakanin mu, kuma ka d'aukeni k'anwarka. Hakan zai sanya ni farin ciki sosai Yaya Aryan."*

*Kanwarka Basma Bulama.*
Nagode.

Wani irin yanayi Yaya Aryan ya tsinci kansa a ciki, komawa yayi ya d'aura kansa bisa katifa, ya kuma karanta sak'on, yayi ta maimaitawa kusan sau biyar, mamaki ne ya cika shi, zuciyarsa yana harbawa a hankali, ji yayi duk kasala ya rufeshi, lumshe idonsa yayi ya shiga tariyo abinda ya faru a tsakaninsu, nan take yaji ta burgeshi yanda take nuna isa kamar wata *'YAR SHUGABA* salonta ya bashi mamaki yanda tayi saurin sakowa ta bashi hak'uri, sai yaji zuciyansa ya wanke babu sauran jin haushinta da yake yi, hakanan ya tsinci kanshi da k'ara son ganin ta, yana kissima ya salon zai sauya tunda yanzu sun shirya ba fad'a, murmushi yayi wanda ya k'ara bayyana kyawunsa, a bayyane yace

"nima naso na baki hak'uri, saboda irin k'ok'arin da kika yi akan Deeja, baki cancanci mari a guna ba Basma,  kawai dai munyi abun a cikin rashin sani ne, koda ke kika rafa tsokana ta, amma duk da haka zan ja aji, domin ki gane ni d'in Namijin gaske ne"

Dariya yayi wanda ya bayyana fararen hak'oransa, ya tashi zaune ya k'ara duba kayan, duk sun kwanta masa arai, godiya yayi ma Allah, kana ya mai da kayan mazauninsu ya fita zuwa masallaci dan gabatar da sallan Magrib.

*Rahma Ce*
[8/3, 5:02 PM] Rahma Kabir🌺: *'YAR SHUGABA*👑

_page_ *8.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

*Bayan mako guda*

Yaya Aryan yanata zuba ido yaga zuwan Basma amma shuru, wani lokacin har tashi yake a kasuwa da wuri domin yazo ko zasu had'u, cikin da bara yake tambayan su Umma akan Basma tazo? sai suce bata zoba, wasa-wasa har aka shafe sati d'aya, sai rashin zuwan nata ya fara sa shi damuwa, Addu'a yake Allah yasa lafiya.

Ta b'angaren Basma kula kalau take, domin a cikin satin Yaya Shureym yazo, sun sha soyayya shiyasa bata samun lokaci sosai ba na zuwa gidansu Deeja, domin kullun yamma suna fita da Yaya Shureym dasu Na'im, sai Magrib suke dawowa.

Hakan yasa bata samu damar zuwa ba, amma fa tana tunaninsu da kewar Umma sosai, ta d'auki aniyar siyan musu waya, in bata samu zuwa ba ta rik'a kirasu.

Yau ya kama ranar Juma'a, bayan Sallan La'asar Basma da Yaya Ahmad suka shirya zuwa gidansu Deeja, Basma tayi shigan lafaya mai kalan fari da green, Yaya Ahmad kuma ya sanya sky blue na shadda hula bak'in dara da takalmi bak'i, sunyi kyau sosai. suka kama hanya suka tafi a mota ba tare da escot ba, hira suke cikin nishad'i tare da kwanciyar hankali, a haka suka isa gidan.

Bayan sun isa Basma, ta fito tace
"Yaya bari na gaya musu tukunna saika shigo" ya kalle ta da murmushi yace
"ba damuwa ina jira".

Cikin natsuwa ta Shiga gidan, duk kan su suka amsa, cike da fara'a Umma ta tarbeta, Deeja kuwa tasowa tayi ta amshi jakan hannunta tana mata sannu, Yaya Aryan kuwa basar da ita yayi tamkar bai ganeta ba, Amma fa a zuciyansa yana yaba kyawun da tayi, dauriya kawai yayi ya matse, zama tayi a kan tafarma sai da suka gaisa da Umma kana suka gaisa da Deeja, ta kai kallonta wajen Yaya Aryan tace
"ina yini Yaya Aryan?" farin cikin ne ya mamaye zuciyansa jin yanda ta kira sunansa yayi masa matuk'ar dad'i, a fili kuma ya amsa fuska ba yabo ba fallasa a dak'ile, daga nan bata k'ara cewa komai ba domin jikinta yayi sanyi yanda taga ya amsa mata, sai duk ta jita a takure, Waigawa tayi wurin Umma tace
"da Yaya Ahmad muke yana waje, nace bari na sanar muku kafin ya shigo" Umma ta fad'ad'a fara'an fuskanta tace
"Allah Sarki ai da ya shigo tunda duk gida ne, Kai Aryan tashi ka shigo dashi" da sauri ya mik'e ya fita, cikin minti uku saiga su sun shigo, ya zauna a tabarman da Yaya Aryan ke zaune shima ya zauna gefensa, cikin natsuwa ya gaida Umma, ta amsa cike da farin ciki, Deeja ne ta fito daga d'aki sanye da gyale ta kawo masa ruwan pure water a cikin plet ta aje a gabansa, sannan ta gaishe shi, cikin kulawa ta amsa, Basma na satan kallonshi, taga sai wani kallon Deeja yake kamar zai had'iyeta, ita ko Deeja batasan yana yiba, nan ya shiga yiwa su Umma bayanin zuwansa, yace

"Umma kan zancen makarantar Deeja ce, insha Allah ranar Monday zasuje tare da Basma tayi mata registration, saboda yanzu ana farkon fara d'aukan sabbin dalibai, sannan

Please Login or Register in order to submit comment