Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[1/10, 11:05 AM] Nordin: *JIRWAYE....*






*DAGA ALK'ALIMIN NABEELA DIKKO*






*AUREN DOLE!*





_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM..._


*Shimfid'a:Da farko dai Aure shi ne Alak'ar zaman tare tsakanin namiji da mace,A bisa yardar juna da Amincewar Dangi,Ta hanyar cika wasu ka'idoji,Na Al'ada da Addini.*





*Shi kuma Auren Dole:Shi ne tilasta yaro ko yarinya auren Wanda kowa acikinsu baya so,ko kuma baya kauna mafi yawa iyaye da kakanni ne ke tilasta shi."*







*SHAFI NA D'AYA*




"Zaune take a gaban kakanta, mallam Buba mak'eri,Banda k'arajin kuka ba abinda takeyi!"



"A fusace mallam Buba,Ya ce "Kinji dai na gaya maki...Wato ke gaki gagarau Ma'u!"Ni zan gindiya sharad'i kice ki shure ki wuce!"Saboda kin raina ni,Ke da muguwar uwarki!"To daga ubanki!Har uwar taki nafi karfinsu!"Aure ba fashi!Ko da ki amsa ki yarda kiyi Auren soyayya ko kuma ki karbe shi a matsayin *AUREN DOLE*"




"Cike da firgici!Ta dago kanta!Tana kallon Baba mallam(Kakanta)Hawaye ke zuba a idonta kamar an bud'a famfo!"




"Rik'e kafarsa tayi tace "Dan Allah kaka kayi min rai!Wallahi na tsani tsohon nan yafa tsofewa Babana!"Ka taimake ni!Ka had'ani da wani Kaka....!"



"Marin da Kaka ya watsawa Ma'u ne ya katse maganarta..."Tasbahar da ke hannunsa ya dinga zuba mata ta ko'ina!"Kururuwa!tah ta fito da ilahirin jama'ar gidan mai d'auke da lungage..."Suna kallon Ma'u da ke kuka!Babu halin cetontah!"Saboda gudun b'acin ran Kaka."




"Ta da muryarsa yayi sosai!"Ya ce, Yoo....Duk gidan nan akwai mai yimin musu sai ke!Ma'u to kinci gidanku kin qara tunzura ni nadawo da ranar aurenki kusa,idan yaso ki mutu agidan Alh.Kalle nafi farin cikin hakan da in barki ki auri shashashan yaron nan da kike so Kamalu!"Me yake da shi!me ya ajiye ke in kinsan asalin talaucin su baki kaunar ki aure shi!Saboda talauci n su na gadi ne!A jinin su yake..!"



"Ma'u tashi tayi cikin kunar rai!Ta nufi sashen su jikin Innarta ta fad'a tana rusa kuka!"Kamar ranta zai fitaa!"



"Kaka ahasale ya bar kofar dakinsa da ke gabas din gidan...butar da yasamu ajiye a hanyar fita waje,yayi shuri da ita,yace munafukan banza!To ku koma tsayin me kukeyi anan!?"Yana hararar sarakunan nasa da suka fito gulma.."Sum-sum kowacce ta fice sashenta domin sun San kaka sarai da masifa!!!"





"Lami ta kalli 'yartah rai!Babu dad'i!"Ta ce Kiyi hak'uri Asma'u ki yarda da zab'in Baba mallam shi ne mafita agare mu,kinsani sarai ni ko Babanki bamu isa muja da shi baah!"


"Duk gidan nan ba mai karya dokarsa!Kar ki bari zuciyarki ta rud'eki akan ki karyata,Ki barwa Allah komai!Kin sani sarai, " *AUREN DOLE* A gidan nan Ba akanki aka fara ba!Bare ak'are kanki!"





"Asma'u ta tashi zaune,Ta kalli Inna tare da kama hannayenta,Ta ce"Yanzu Inna kuna kallo Baba mallam zaiyi min *AUREN DOLE!?"* Saboda yana son cimma wata manufa tasa!"Tare da kwad'ayin Abin Duniya!"




"Wallahi na tsani!Alh.kalle,Inna bana sonsa,ba zan iya rayuwa da shi ba!Yafa tsufa!Yaransa duk sun girmeni!"Aure na zaiyi kawai, saboda budurwar zuciya!Da son zuciya!"Shi ne ya zubawa kaka kud'i domin yabashi Ni,A dole!"Shin meye haka!Addini ko Al'ada!!?"Na rasa amfanin wannan baqin aure da ake mana agidan nan......Wani Sabon kuka!Asma'u ta ke rerawa...."Inna Lami ma hawayen tausayi 'Yarta ke zuba a kyakkyawar fuskarta,Tare da cigaba da rarrashin Asma'u,da ido yayima luhu-luhu saboda kukaah!!!!"
[1/10, 11:05 AM] Nordin: *SHAFI NA BIYU*




*ALK'ALAMIN NABEELA DIKKO*








"A cikin jihar kebbi akwai wata qaramar hukumar mulki da a ke kira Argungu,"Babban gari ne,Mai cike Al'umma,Ga su da manyan yan boko maza da mata,kuma ma'aikatan gwamnati ne a kowanne fanni,Bugu da qari Albarkokin Allah sun yawaita A garin,Domin Allah ya albarkace su da manyan rafi masu dauke da Kifaye naji, na gani na fad'a,kuma mafi yawa daga cikin su asalin su D'aya ne akwai Kabawa,Lekayawa,Fulani,Zabarmawa da kuma gobirawa, noman shinkafa,da kayan lambu ne,da na masarufi sune Ayyukan su,Mutane ne masu rik'e da Al'ada ko kuma sana'ar gidan su ta gado!"Argungu gari ne na kabawan Asali wad'anda sukayi fice ciki da wajen Nigeria."Akwai cigaba mai yawa da suka samu,sunyi suna dalilin bikin kafun kifi(Fishing Festival) da akeyi aduk k'arshen shekara."Acikin wannan gari akwai wata unguwa da ake kira Gobirawa,yawancin mazauna unguwar ada caan baya zabarmawa ne,Daga baya hausawa suka yawaita acikinta."Gidan Mallam Aminu yana daga cikin unguwar layi na uku,Gabas da masallaci Sheik Bashir."Da ke Unguwar."




"Mallam Aminu,mutumen kirki ne,Wankan tarwada mai tsayi da jiki,yana cikar zati da haiba daka ganshi kaga irin malamman nan masu Da'awa,Sannan kuma ya fito daga gidan sarkin mallaman garin,Duk gidan su malammai ne kuma shi ne magajin gidan, ya kasance babban malamin da akeji da shi a jihar kebbi da kewayenta."Allah ya albarkace shi da samun ilimi mai yawa,ya na ba mutane da yawa karatun addini."Yana da mata d'aya malama juwairiyya itama tana da islamiyya ta kanta,mace ce mai kyau,ga kirki abin burgewa tana da ilimin addini,mutunci da sanin girman Dan Adam,Sai yaran su akwai Muhammad Yaseer da yaseera sai qaramin Abdul raheem."Yaran su sun taso acikin rayuwa mai kyau wato ilimin addini da na zamani."Tare da tarbiyya."Muhammad Yaseer yana karatun aikin likita,A jami'ar Danfodio Sokoto."Sai Yaseera da ta kammala karatun sakandaren mata a wannan shekarar,Abdul kuwa zai tafi aji d'aya a sakandare."Dukkan yaran kan su a had'e yake suna da zurfin ilimi mai yawa,kowannen su ya haddace Alqur'ani mai girma tare da wad'an su littafan sa ni,"Suna da kyau matuka,ga biyayyah da kamun kai da nutsuwa."




"Kamar kullum matukar mai gidan yana gari ko baya nan hakan ke faruwa agidan,wato karatu tun kafin sallah Asuba har zuwa wayewar gari, Mallam ne acikin iyalansa,Suna ta karatu ya fadiwa matarsa da yayansa,daga bisani Addu'a sukayi kowa ya shafa,Daga nan suka cigaba da fira kowa na fadin ra'ayinsa ko buqatun su da abinda suke so."Kasancewar Yaseera da Abdul ne kawai agida domin yaseer yana makaranta."




"Mallam ya tambaya Abdul na tambayeka ba ka bani amsa ba!?"



"Abdul ya ce"Abbu daman ni inason idan nagama karatuna na sakandare ka kaini jami'ar nan ta madina ina so nayi karatun likitan musulunci."




"Dariya mallam yayi tare da miqawa Abdul hannu sukayi musabaha yace masha Allah,



"Allah ya cika maka burin ka Abdul raheem,Amma kasan tufin Asirin Allah ne,muke da shi idan Allah ya kaddari hakan zanji dadi Allah yaqara tufa mana Asiri."




"Ameen ya rabbi,Umma ta itada Yaseeara suna dariyar Abdul."



"Naga bakin ki na motsi ke kuwa me kike buqata?.Umma ta tambayi yaseera tana murmushi."



"Abbu ni yaushe zan tafi makanta!?"Yaseera ta tambaya."




"Amsa ya bata na gaya maki makaranta ba yanzu ba!Ki k'ara hakuri akwai tunanin da nikeyi akai!"Inji Abbu.


"Yanayin yaseera ya sauya!Domin tana son cigaba da karatun ta wataqila Abby bazai barta ba!Tace acikin zuciyarta!"A cewa fili cewa tayi to Abbu,Nagode." tashi tayi ta nufi madafar Abinci domin hada abin Karin safe."





"Abdul ma yasan aikin falon Abbu yaje ya share tare da harabar gidan,sannan ya fara wanke motar Abbu da yake yau Assabar ba makaranta sai goma suje islamiyya su dawo sha biyu,su koma karfe biyu,su komo shidda na yamma."




"Abbu ya kalli Umma yace"Juwairiyya ina ganin kamar lokaci yayi da zan fadawa yaseera mijin da na zaba mata,saboda naga tana son karatu ni kuma sai anyi auren su nikeson ta tafi makaranta tana gidan mijinta,ba wai saboda na raina kamun kanta ba!"Wannan shi ne ra'ayi na amma me kike ganin ya race!?"



"Umma Ta numfasa tace Mallam nima,In bayanka gwara kawai tayi karatunta bayan auren,sai dai wani hanzari ba gudu ba!"Ya kamata tasan da maganar Aurenta da Najibullah shi yafi cancanta."



"Hakane In sha Allah an juma da dare zan sanarda ita!"Inji Abbu."




"To Allah ya yarda yasa mudace saboda kowacce uwa tana alfahari da samun suruki kamar n
Najibullah...Umma tace tana kokarin tashi,Bari naje na duba me ake hada mana na kari,Abbu yace to kuyi himma Ku gama Ina son nafita yanzun nan."




"In sha Allah,mallam yanzu za'a gama.."Umma tace ta nufi hanyar madafa."







*GIDAN MAK'ERA*

"Babban gida ne,Mai dauke da lungage da dama,Mallam Abubakar wanda akafi sani da (Malam Buba)shi ne shugaba agidan,Yana da mata biyu Inna Karime wato uwar gidansa wacce ta rasu shekarun baya!tanada 'ya'ya tara maza biyar,Umar,Nasiru,Aliyu,Badaru da sani sai mata,lubabatu,sahura,sai Mariya da sakina dukkan sunyi aure har da yaran su wasu kuma sunada jikoki,Sai matarsa ta biyu Amina wacce suke kira da (Anna)Da dadewa suka rabu da ita akan masifar sa,yanzu hakan shi kadai yake rayuwa sai halinsa,Anna tana da 'ya'ya shidda,Tare da Malam Buba,Mata biyar,Zainab,Ruqayya,Hassana da usaina,Aysha,sai namiji d'aya kuma shine babba acikin su wato Yusuf Mahaifin Asma'u."Tunda Anna tabar gidan malam tayi aure a kauyen felande yanzu hakan scan take rayuwa da yaranta biyu maza da ta samu Idirisu da mustafa."






"Dukkan gidan kowa na tsoron Baba mallam,Saboda mutum ne,mai akida da dokoki,Shi ke hada aure shi ke saki harkar gargajia ta yalwatu arayuwarsa Duk yaransa maza agidan suke zaune da iyalan su kowa da nashi lungu."


"Gidan mallam Buba,Babban gida ne,Wanda 'ya'yansa da jikoki har tantab'a kunne ke rayuwa acikin gidan,Sana'ar gidan tun kaka da kakanni ita ce Kira, kamar irinsu(Wuk'a,Adda,b'ota,gatari,da kwasa,tsinke da sauran su,)Shiyasa akafi sanin gidan da gidan mak'era."Suna bayarda taimakon wuta hakan da sauransu."




"Duk 'yammatan gidan da sun tasa mallam Buba ke zab'a masu miji,suyi aure,tun kan diyansa mata da maza har izuwa kan jikoki,"Gulma da hassada ta yawaita acikin gidan saboda kowa naji da kansa."Ba komai bane yakawo haka saboda bawani ilimi ne da su ba bare matansu da Baba mallam ke nemo musu."




"Lungun yusuf,shi ne daban agidan saboda yasa mu mata mai kirki,Wato sadiya (Lami)yar gidan limin,Haka yaranta uku Asma'u,Sauda,da Baraka,sunada tarbiya sosai."



"Duk gidan suna jin haushin lami wacce suke kira da uwar mata!Wai batada d'a namiji!Sun tsaneta bata jin sanyi kowa agidan sai Baba mallam domin shi ba ruwan shi da bambanci,Duk Wanda ya taka dokarsa takashi yake! ,Kaf mazan gidan,kyashi da shin yusuf Saboda shi kadai ne namiji dakin su,sai qannansa mata da yake taimakawa kuma suna masa biyayya, Akai kai suna zuwa garin da Anna ke aure su dubata tare da mata sha tara na arziki,Su Asma'u suna son kannen babansu domin sune masu kaunar maman su,komaina yusuf shi kadai yake yinsa sai qannan sa mata,shiyasa aka fitarda shi daban agidan haka matarsa lami batada shaqat acikin matan saurinta(facaloli)shiyasa suke hade mata kai,Kullum cikin tuggu gulma da shirya mata munafunci sukeyi agidan,Mijinta Yusuf ko duk acikin yayan malam babu yafisu tufin asiri,Shiyasa yake sakewa Baba mallam kudi,shi kuma yana sonsa da diyansa sosai."Kuma wataran yana auda kai!A al'amuran su saboda akwai kwadayi da son abin duniya,Abu daya ya hadasu nacewar Yusuf yayi akan sai yaransa sunyi karatun boko,Wanda al'adar gidan Arabic kawai ake,Asma'u kawai ce tauraruwar da tayi nasarar gama sakandare,daga kanta mallam yayi rantsuwa ba Wanda zaiyi boko sai bayan ransa! shiyasa mallam ya tilasta mata aure yanzu,domin ya zaba mata miji mai arziki."Duk gidan sunji bakin cikin auren da Ma'u zatayi."Amma agefenta ita da Iyayenta baso sukeyi ba!Hakuri kawai zasuyi saboda gudun zuciya da masifar Baba mallam,A ganin Yusuf ya karya dokar Mahaifinsa Asma'u tayi karatun boko,yanzu kuma taya zai karya auren hadin da za'ayi mata,Saboda koshi din dan yayi dace da tagari ne,Amma yana bakin cikin Asma'un sa yarinya mai ladabi da biyayya mai kyau da ilimi ta auri jahili kamar Alh.kalle,Wanda aqallah zai girme masa,Gashi da mata har uku da yaran da shi kanshi bazai san adadin su."





"Cikin sati d'aya Asma'u duk ta rame!tayi baqi damuwa ce,A zuciyarta abubuwa da dama take ayyanawa aranta!Ko ta gudu tabar gidan...kuma tana tausayin rayuwarta da ta iyayenta!"Domin kuwa barin gida babbar illa ce ga rayuwar 'ya macce."




"Ta rasa ya zatayi an rabata da Wanda takeso matashi dai-dai aurenta!"Za'a yi mata *AUREN DOLE* da sa'an mahaifinta!"Kuma babu Wanda taga alamar zai takawa Baba mallam burki!"




"Duk mutunci da tarbiyar Asma'u ta dauki aniyar ajiye su gefe domin idan Alh.kalle yazo gidan tatas take masa,Amma dariya yake mata ko tausayinta bayaji aganin kurciya ce,ke damun ma'u."





"Ana hakan har akasa ma'u ruwa saura sati d'aya ayi aurenta Alh.kalle an kawo kayan lefe akwati biyu,Wanda shi aganin sa ya nuna bajinta...haka agidan sai nuna baqin ciki sukeyi tare da kyamar su Asma'u."




"Gidan Gwaggo Hassana kanwar Yusuf,Asma'u ta tafi abinta,Rarrashinta gwaggo,keyi...Domin ta hakura da zabin mahaifinsu,Suma haka akayi musu auren gashi har yanzu sun zauna lafiya harda yara."




"Shirye shiryen aure akeyi ta kowanne fanni Alh.Kalle ya gyare gida an fente ko ina,Matansa sai dariyarsa sukeyi suna kiransa da mijin yarinya."
[1/10, 11:05 AM] Nordin: *SHAFI NA UKU*







*ALK'ALAMIN NABEELA DIKKO*




*BABI NA BIYU*






*GIDAN MALLAM AMINU*



"Bayan sallar isha,Mallam ne zaune acikin qayataccen falon sa mai kyau da tsari,da yake yana da tufin asiri,yana da shaguna magungunan musulunci,ga makarantu sannan yana aikin gwamna gidan marayu."Shiyasa yake da tufin asiri dai-dai gwargwadou."Fira yakeyi shi da matarsa,Suna kallon wa'azin sheik Daurawa,A sunnah t.v, daga bisani umurni ya bata da takira masa yaseera."



"A dakinta ta sameta tana karatun Alqur'ani mai girma."




"Bayan ta kai aya,juyowa tayi ta kalli ummanta tare da gaita."




"Umma ta ansa sannan tace"Idan kin gama Abbunku yana kiranki."




"Yaseera tace"yawwa Umma daman nagama kuma yunwa nikeji abinci zanci muje!"




"Tare suka jira ita da ummata sai da suka kai kofar falon yaseera ta dawo baya Umma ta fara Shiga sannan yaseera ta biyo bayanta,aqasan lallausan kafet din,ta zauna dai dai kafafuwan Abbu tare da gaida shi."




"Umma ko agefensa tayi mazauni saman kujerar nan ta zaman mutim uku,"




"Amsa gaisuwar yayi,fuskarsa asake."



"Sai dai yaseera jikinta yayi sanyi!"Duk gabban jikinta rawa ya ke saboda wata fargaba da taji ta ziyarci gangar jikinta."




"Gyaran muryar Abbu,ya dawo da ita hankalinta.."



"Ya ce, ''Yaseera dazu naji kinyi magana akan kina son ki koma makaranta ko?"



"Eh,Abbu tace da sauri!tare da ajiyar zuciya."



"Ya ce,Masha Allah."Zaki tafi makaranta amma da sharad'i d'aya...sai nayi miki aure,Idan mijinki ya amince sai kitafi kina a matsayin kamilar macce,Hankali yafi kwanciya kina gidanki kina karatu saboda ina tsoron wannan zamani mai cike da abubuwan tashin hankali da al ajabi."Na sanki da hankali da nutsuwa kuma ina da kamun kai,Amma ita rayuwar nan da kike gani komai yana iya canjawa ko dole,ko ta wuya ko kuma ta dadi!"




"Dan haka nayi tunanin zab'a maki miji nagari!Wanda zai iya riqeki da gaskiya da Amana wato Najibullah Dan gidan Alaramma Usman..."



"Tunda Abbu ya ambaci kalmar aure yaseera ta sadda kanta aqasa zuciyarta nayi mata tafarfasa!Domin sam batasa aure agabanta yanzu ba!Karatu takeso shiyasa ba ta kula duk wanda zaice yana sonta,kwallah!ke kokarin gangaro akan lafiyayyar fuskarta mai kyau kallo,kokarin hadiye kukan take!"Sai taji Abbu na cewa..."




"Nasan zakiji maganar kamar a mafarki!To gaske ne,Tun kina makaranta mukayi zancen auranku da najibullah,ni da mahaifinsa,kin sani sarai mu abokan juna ne duk wa'Azi tare muke zuwa,Alfarma ya nema gareni ni kuma na amince saboda nasan irin tarbiyar da na baki Yaseera."




"Sannan Najib yaro ne mai zirfin ilimin addini da na zamani,shi kan shi Alaramma ne,yana da hakuri,ga shi ya san girman manya,yana da mutunci,Hakika na tabbata rayuwarki zata inganta agidansa,yana da abinda zai ciyarda ke yayi miki sutura sannan ya kula da lafiyarki dan kuwa yana aikinsa da 'yan Sana'oi,sannan zai cigaba da baki ilimi har karsheb rayuwarki."




"Yanzu hakan ya tafi madina yayi wani kwas,na wata shidda,tun kina makaranta,in sha Allah munasan ran zai dawowarsa akarshen watan nan na muharram sai kuka juna sannan ayi buki,bayan nan idan yabarki kiyi karatun idan kuwa bai barki ba sai ki hakura!"



"A karshe ina rokon ki alfarma yaseera idan har zabin da nayi maki baki gamsu da shi ba!Kina da damar zabin wnda kike so kike ra'ayi domin *AUREN DOLE* ba aure bane matukar matsaloli zasu dinga kunno kai!"Ni dai amatsayina na mshaifinki kinga ya dace in san waye zanba aurenki,"Kuma hakkina ne nazaba maki miji nagari mai nagarta,Wanda Addini sa da dukkan halayensa sunyi dai-dai da fadar Allah (SWT) da manzon rahma Annabi (SAW)"

"Amma kuma Allah yace"Muji tsoronsa muyi muku adalci shiyasa nace idan baki ra ayinsa ba komai nasan yadda zanyi na sanarda su!Farin cikinki shi namu."




"Ya kalli umma ya ce,"juwairiyya ko ba haka ba!"




"Umma ta ce"Hakane Abbu,Hakika yadda kayi shi yafi cancanta ga kowane uba nagari yasan wa yarsa zata aura meye addininsa,muhallinsa da kuma aikin yinsa,yadda yarinya bazata shiga acikin wani hali ba!"Yaseera nasanki da nutsuwa to ki nutsu kiyi tunani mai kyau akan ra'ayin Mahaifinki ba wai ya tilasta ki bane ko zai maki *AUREN DOLE* A'ah idan baki sonsa ki fada mana!Mu hakki da Allah ya daura mana akanki mukeson saukewa saboda Yadda muke da hakki!Akanki hakan kema kinada hakki akanmu yaseera!"


"Saboda haka wajibi ne,agaremu sauke Hakkin ki da ya rataya awuyan mu,saboda Annabi (SAW) ya ce,Hakkin D'a akan iyayensa,sune :"Na farko,Ya sanarda shi karatu,da rubutu."
"Abu na biyu,Ya kyautata sunan sa,
Sai Abu,na uku Ya aurar da shi idan ya balaga."

"Yaseera mu baki ilimin addini da na zamani,kinsan yadda zaki iya bautar Allah kuma kinsan yadda zaki kare kanki daga wuta.. "Domin Allah (SWT) ya ce "Acikin Alqur ani mai girma,"Yaku wad'anda kukayi imani,ku kame kanku da iyalanku daga wuta,wadda take makamashinta mutane da duwatsu ne!"Allah ya karemu."



"Ameen Abbu yace"cikin jin dadin kalaman matarsa,azuciyarsa yana alfahari da samun mace mai ilimi amatsayin uwar yayansa..."Muryarta ta katse masa tunani.."



"Inda ta ce"sannan kinga Abbunki ya sanyawa maki suna mai ma'ana irin na addinin musulunci,"Kina ganin sunaye,da yawa agari maras ma'ana wasu iyayen ko da za'a kashe su baza su iya fad'in ma'anar sunan da suke kiran yaransu da shi ba,To ki godewa Allah yaseera saboda ke da kanki kinsan meye ma'anar sunanki!kuma kinsha karanta alqur'ani,Kina ganin yaseerah aciki."




"Kinga anan kowanne daga ciki munyi iya kokarin mu wurin yi maki biyun na ukun ne mukeson mu cika da yardar Allah."



"Ni da Abbu saida mukayi shawara da juna kafin mu sanarda ke, Saboda haka ba wata shawara da zakiyi daman dai nice babbar qawarki kuma abokiyar shawararki,Sai ki fad'a mana ra'ayinki muna saurare..."Umma ta qarashe zancenta tana kallon 'yartah da sadda kai tana sauraren jawabinsu."





"Duk da ba hakan taso aranta ba,Amma ahankali tunani ya fad'ou mata arai!"Cikin sanyin murya ta motsa labban bakinta da sukayi mata nauyi,domin wata kunya da nauyin iyayenta taji ya kama jikinta.."



"Numfashi tayi sannan tace ahankali"Abbu!"Umma"Ba abinda zance da Ku sai dai godiya!"Ina rok'on Ku da kada kusake tambaya ta abu,idan zakuyi min,Ku iyaye na ne bai kamata Ku nemi wata alfarma awurina ba,domin yi maku biyayya wajibi,Nasan Baku kaini inda zan nakasa ba!kuna sona!Hakika kunyi min komai rayuwa,fatana Allah yaqara maku rai da lafiya,yasa ayi karshe mai kyau."




"D'ago fuskarta tayi ta kalli,iyayenta Wanda hasken annuri da farinciki ya bayyana afuskokin su,itama murmushi tayi tace,Ina alfahari da Ku,A kullum ina rokon Allah yasa inyi rayuwa irin taku,Wadda dole sai nasamu miji,nagari hakan zata kasance Alhamdulilah Abbu ya zaba min Alaramma najibullah,mai addi,mai ilimi,mahaddacin Alqur ani,Nagode Abbu,na yadda na amince koda za'a iya kiran aurena da *AUREN DOLE* na tabbata agurina aure ne Wanda iyayena sukaga yadace da ni dan haka agefena babu *AUREN DOLE!*."


"Umma,Tabbas ina da hakki akanku,Amma naku yafi yawa akaina,saboda duk abinda yakamata kuyi mana kunyi mana shi.."Bazan manta Acikin suratul Isra'i,Allah (SWT)Ya ce"Kuma ubangiji ya zartar da hukunci kar abautawa kowa sai shi,kuma dangane da iyaye biyu Ku kyautata musu,ko da dayansa yakai ga tsufa to karkace dasu tir!"Kuma karka tsawace su,sannan kuma ka gaya musu magana mai karamci."

Sannan Manzon Allah (SAW) yana cewa yardar Allah tana tare da yardar iyaye,kuma fushin Allah yana tare da Fushin iyaye,"




"Dan haka umma
...Abbu nabi Allah da manzonsa,kuma na biku,kuma in shaa Allah zan cigaba da bin umurninku tare da yimuku biyayyah har karshen rayuwata..."Yaseera tace cikin ladabi.."





"Ajiyar zuciya Abbu ya sauke yace Alhamdulillahi Alaa kulli haliin..Tabbas nasamu mata,kuma uwa tagari wacce tayima yarana tarbiya tagari,Juwariyya nagode abisa namijin kokarinki akan yaran nan,Domin kece mai kula da su tare da sanya ido akansu da duk wasu lafuzza dazAsu fito daga bakinsu..."



"Umma tayi murmushi tace"Mallam kenan, ai Kaine ka karantar da ni har nike sanarda su,karfa ka manta Kaine jigon gidannan...daga ni har su muna bisa turbar inda ka ajiye mu,wannan tsarinka ne,kuma kokarinka ne,Domin ko kana gida ko baka gida,ka tsara yadda za a tafiyarda rayuwa da kuma mu'amulat agidanka."Sai dai mu godewa Allah nida yarana da yabamu garkuwa mai kyau,mai kuma inganchi amatsayin jagoran mu."





"Dariya Abbu, yayi yace Masha Allah, Ya kalli yaseera da ke wasa da zoben azurfa dake yatsanta,Ya ce Yaseera....."



"TaceNa'am,Abbu tare da dagou kanta.."




"Ya ce,Allah yayi miki,Albarka kinji,Kuma yadda kikayi mAna biyayya Allah ya ba ki wadanda zasuyi miki,Hakika akullum ina alfahari da Samun 'ya macce irinki!"Allah ya sanya alkhairansa da albarka a lamarin nan."




"Ameen,Ameen."umma tace tana murmushi.."




"Yaseera murmushi tayi cike da kunya,sai Abbu yace zaki iya tafiya abinki.."Aykuwa da gudu yaseera tabar falon."





"D'akinta ta fad'a,da yake cikin dakin falon umma yake,A falon,akwai dakuna uku, biyu da falo na umma,dayan nata,Shi kuma Yaya yaseer nashi na daga waje,Abdul kuma nashi na daga cikin falon Abbu,na shi daga gabas na Abbu daga yamma."Haka suke rayuwarsu kowa da dakinsa daban agidan,mazan ba ruwansu da harkokinta itama bata shiga lamarin su,wannan tsarin yasamo asaline daga iyayen su,Kuma wannan bai hanasu so da kaunar junansu ba,tare da sanin girma da kimar kansu Sam babu raini atsakaninsu."



"Yaseera saman gadonta da ke dakin tafada wasu hawaye masu zafi da ta kasa bambance ko na meye, ke zuba afuskarta!"Abincin da bataci ba!kenan adaren, duk da kasancewar tanajin yunwa,Tashi tayi,bayi ta fada domin dauro alwala,sallah ta tada bayan ta fito,sai da tayi Nafilfili,tare da azkharul naumy,sannan tayi shafa'i da wutiri,Akarshe addur ar istihara, ta karanto tare da fatan wannan zabi yazamo mata nagari,sannan ta tashi, kwantawa"Har kasan zuciyarta taji sanyi da nutsuwa yana yatsa dukkanin jikinta..."





*WANENE ALH.KALLE*

"Alh.Kalle babban dan kasuwa ne,da yayi suna agarin Argungu,Yana kantina da dama na kayan masarufi."Yana da arziki kwarai da gaske amma kuma kowa yasan jahili ne,ba boko babu mahammadiya,yana da mata uku

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment