Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA...._*馃崄馃崄

馃崄

*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*馃挕


Na Feedohm馃挒

*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS_


1 to 2


_*Assalamu Alaikum ...na canza wannan littafin daga A DALILINSU ...to ...A DALILIN YAYATA....Saboda naga sister jannah tayi littafin mai irin Sunan.......馃崄*_


Duk da bana da wayau amma nasan duk lokacin da wannan mai bakaken kayan yazo dole sae mamana tayi kuka ranar ....baya da maganar da ta wuce ta babanmu duk da yayi shekara daya da rasuwa...Mugun haushinsa ya turnukeni ...ji nake da ina da karfi babu abunda zai hana ban mashi jajjagen kasa ba abaki...

..Kai maman tamu bata nan kuma ba yanzu zata dawo ba.....na saka hannu na tare bakin kofar ina mazurai ...

Yaushe zata dawo ...ya fada fuskar a murtake kamar yarda yake kullun ...

Ohon maka ....kullun kai kazo sae ka saka mamanmu kuka kai kana so kaga maman taka tana kuka ....na fada tare da rike kugu...


Yayata dake cikin gida tana wanke waken da zatayi awara ta kwala man kira ....

Na kalleshi duk na bata rai ina fadin ...matsa zan rufe gidan saboda barayi.. ....ban jira komae ba na turo gidan da karfi ...ina jin lokacin da ya sake tsaki mai karfi ....nayi saurin dawowa na bude kofar ...lokacin har ya bude motarshi zaya shiga ....

Da karfi na kwala mashi kira kamar yarda naji mamana na kiranshi .....Lauya ...

Ya juyo yana kallona ....Maman tawa ta dawo Ashe ban sani ba....na sake dariyar shakiyyanci ...

Karamin tsaki ya dan ja sannan ya dawo cike da bacin rai ....na bashi hanya ya shiga ni kuma na koma kusa da motarshi na tsaya ....


Ina ganin ya fito na tattare siket dina na kwasa a guje ...don nasan mamar tawa batta nan ...tsakin da ya man ne ya bani haushi ...

Ban dawo lungun ba sae da na tabbatar ya bar unguwar sannan naje kiran da yayata keman ...

markade ta bani na kai mata sannan ta tace awarar ta daura saman wuta ...


Mamana ta dawo rike da ledar gari yayi zafi ....nayi saurin karba ina dariya ....sae da ta dauko tabarma ta shinfida sannan ta fito da kayan dake ciki .....

Irin kayan kwancen nan ne da ake bata inda take aiki ....ta miko man dae dae nawa sannan ta mikawa yayata wanda zasu mata ...nan na dinga murna tare da godiya .....


鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�

Tunda na fito daga gida yaron dake zagaye da kaskon tuyar awarar yayata suka fara watsewa .....bana dagawa kowa cikinsu ....don duk yawancinsu masu cima yayata zalun ne ...basa bata kudinta idan sun dauka ita kuma ba mai yawan magana bace ...sae dae ta kyalesu ....amma idan ina gurin ko karkashin gadon uwarka ka boye sae na bika na karbo kudina .....bana jin komae idan ka daukar wa yayata awarar naira goma na je har gidanku na kwanto akuyarku idan ma baku da ita zan iya dauko tukunyar ku na taho da ita ..kuma idan duk duniya zata hadu baran ce ga inda na kaita ba har sae anbiyani kudin sannan zan bayar ...don bana ajeta gidanmu gudun kar mamana tace na bayar ...


Shafi'u dan makwabtan mu na gani sae dauka yake yana ci ba tare da ya kirga ba ....na kafe shi da ido har na zauna bai san da zuwana ba ....sae da ya koshi sannan ya mike yana kakkabe riga ya fito da naira goma ya aje bisa kwandon yana fadin ...Saa ga kudinki nan kin biyoni sha biyar ...


Kam ubancan ...Ashirin da biyar fa ...na fada tare da rike kugu..

Yayi saurin kalloni yana washe baki kafin yace ...Haba Hudata ina nufin saura naira Sha biyar aljihuna yanzu zan fito mata da ita sae ta biyoni Hamsin ...

Nace ...owo ai na dauka ta ashirin da biyar kaci ...

Ya washe baki ...aa ina ni ....ai ina lissafi ...ya lalubi aljihu ya fito dasu ya mika mata ...ya tafi yana kakkabe hannu tareda kalloni ....

Gurin na koma na zauna ....Yayata ta Bini da kallo tana so tace na tashi amma tana shakkata ...tasan in har na zauna ba ciniki zatayi ba sossae ....Mutane na son zuwa amma Ni suke tsoro ...



Feedohm馃挒
馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA..._*馃崄馃崄

馃崄


*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*馃挕

Na Feedohm馃挒


*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._


3 to 4



Barister Shehu abunda kake niyar aikatawa sam bai dace ba ...wannan zaluncine tare da yaudara ...matar data amince da kai ta baka amanar dukiyar mijinta yanzu kuma ta fito kana so ka zalumcesu ...idan har kai baka taimakesu ba to bai kamata ka zaluncesu ba ....


Ya kife wayar tare da juyowa a firgice yana kallon Mahmud daya kafeshi da ido harde da hannayensa a kirji ...

Cikin borin kunya yace ...so what dan naci amanarta kanwar babata ce ...kai Mahmud zan iya komae akan kudi ...

Ni kuma Barister Mahmud nace indae har ina raye bara ka taba wannan cin amanar ba ....

Wae me ya shafeka ne da rayuwata ....kaga ka fita wannan maganar ...meyasaka tunda mijin nata ya rasu baka je ka taimakesu ba sae yanzu zaka zo kana man wani waazi ...

Sabida ta yarda da mutumin da bai kamata ta yarda dashi ba....yana gama fadar haka ya matso kusa da table din shi ya dauki takardun da zai dauka tare da briefcast dinshi ya fita ...

Tsaki Barister shehu ya sake kafin shima ya tattara nashi nashi ya bar office din ....daga nan gidansu Huda ya nufa kai tsaye ...


Cikin lungun ya hango ana dambe da huda ...ta haye ruwan cikinshi sae jibgarshi take yara sae kara zugata suke ....yayi kwafa ...yana tunanin da itace ake duka haka to babu abunda zai kaishi rabasu ...yafi kaunar a kasheta kowa ya huta don da alamun yarinyar tana neman shigar mashi hanci ....da wannan tunanin ne ya isa gurin ...tare da fincikota ya dagata daga yaron da karfi sannan ya dauketa mari .......

Marin ya shigeta sossae ta dago tare da zuba mashi ido kafin ta dauki katon dutse ta jefawa glass din motarshi ta gama ......nan take glass din ya fashe ...ya juyo da azama amma kamar walkiya ta bace .....yayi kwafa tare da sake murmushin mugunta yayi sallama gidan ...da yake baida katanga da gidan ya fada ciki ba tare da shamaki ba ....


Bayan sun gaisa yake fadawa mamanta cewa ....kudin sallamar aikin babansu Huda malan Ibrahim sun fito ...yanzu haka gobe yake shirye shiryen fito dasu banki sae ya kawo masu zuwa jibi ...

Tace ...ka barsu hannunka lauya ...idan ka kawo mana ina zamu ajesu ...na tabbata bara ka cucemu ba ...don haka ka barsu hannunka ..sae dae ka dan bamu abunda zamu kara jari dashi dan Allah ..


Murmushi yayi yace ...aa hajiya zan kawo maki su ki gani bayan kwana biyu sae nazo na karba ...don yanzu haka ina shirye shiryen saya maku da gida wanda zaa zuba yan haya a ciki duk shekara sae su dunga baku kudin ...idan na kawo kudin jibi to wanshekare zanzo da mutanen da zaku sayi gidan gurinsu sae a karbi kudin a basu ....

To Amma ina tunanin inda zamu aje su Lauya ...

Murmushi yayi yana fadin ...Allah zai karesu Umma ....ya mike yana fadin zan tafi idan huda ta dawo a ja mata kunne bata jin,magana yanzu daga rabasu fada ta fasa man glass din mota ...

Ta hau sallallami tana bashi hakuri tare da fadin idan kudin sun fito dan Allah ya sayi glass din dasu ...


Yace mata to ...tunda dama haka yakeso .....

鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�


Barister Mahmud indae kana bukatar wani abu cikin kudin ka fada man bawae ka dinga man wani waazi ba na daban ....

Wani kalan murmushi ya sake yana fadin ...nawa ne kudin nasu ...

Yauwa dan gari ...10m ...ne ...zan baka 1m .....shikenan ko ...

Dariya ya sake mai cike da maanuni daban sannan yace ...zan baka 10m ka bar masu nasu please

Barister Shehu ya sake dariya yana fadin ....Am not a kid Barister baran taba cin kudinka na zauna lafiya ba ....nasanka sossae ...don haka kabar wannan uwar watsin ...


Suma wannan sae ka basu kayansu ...

Dariya yayi yana fadin gobe karfe biyar na marece zan kiraka na basu agabanka barister ....ya juya ya shige motarshi ...


鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�

Karfe biyar dae dae ya kira Mahmud ya mashi kwatancen gidansu Huda sossae yace yazo lungun gidan ya iskesu ...ko minti talatin bai cika ba ya shigo lungun ....


Feedohm馃挒
馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA馃崄馃崄_*


馃崄

*_HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕_*


Na Feedohm馃挒


_*DEDICATED TO*_
_EXCLUSIVE WRITERS.._


5 to 6


Motar Barister shehu da ya gani ya tabbatar mashi da yana gurin ...ya fito ya jingina da motarshi tare da harde hannaye ....kafin ya ciro wayarsa ...ya hango Huda janye da tunkiya da gudu ....yana gani ta shiga wani lungu sannan ta fito babu tunkiyar ta cire dan kwalinta ta daure a kugu .....


Wata tsohuwa ta shigo lungun da sauri janye da hannun wani karamin yaro ....

Ke diyarnan yanzu akan naira shabiyar zaki kwanto man tunkiyar dubu sha biyar dan rashin mutunci.....tsohuwar ta fada tare nuna huda da Hannu ..


Me ya saka da nace ki biyani kudina baki bayar ba ....idan kina son tunkiyarki wallahi sae kin bani kudina ...idan ba haka naje na sayar da ita na baki canjinki ....ta fada cike da tsiwa ...


Tsohuwar ta kwantar da murya ...Haba Hudalliya ....na rantse maki da Allah da fatse ta dawo daga talla zan bashi ya kawo maki kudinki ..dan Allah karki sayar man da tunkiya ..

Ta juya baya tare da dage kitsonta tana fito keya ...Nifa Innarsu Fatse dan karki ga na maki rashin kirki amma gaskia sae kin biyani kudina tukun na bada ...

a ranta tace ...rashin mutunci kuma har nawa Hudalliya.....amma a fili cewa tayi ...iyakar mutunci kin man shi Hudalliya yanzu dae alfarma nake nema yar albarka ...

Barister Mahmud dake kallonsu yana dariya har da rike ciki ya matso ya kama hannun Huda yana fadin ...nawa ne kudin naki ..

Sarkin neman suna zaka biya mata ne ...ta bashi amsa tare da mashi kuri da ido .....sannan tace ...hala ba nan unguwar kake ba don ban taba ganinka waccen majalisar ba ta sa ido ....

Naira Ashirin ya fito ya mika mata yana fadin ...karba ki sakar mata tunkiya ...


Tsohuwar ta kalla tace ...Allah ya soki da na maki rashin mutunci ..

Da dae taga an biya kudin sae cewa tayi
.....rashin mutunci har na wana shegiyarnan ......

Oho dae ...huda ta fada tare da shigewa lungun ta janyo mata tunkiyarta ta koma ....

Barister Shehu ya kira ya fito daga cikin gidan suka shiga tare ....gabanshi ya mikawa Mamansu Huda duka dukiyarsu a cikin jikka sannan ya mika mata makullen suka tafi akan gobe zai dawo da masu gidan da zaa saya ..


da Suka fitone Mahmud ya mika mashi hannu cikin jin dadi da bai ci amanarsu ba sannan suka rabu .....


Wajen karfe goma na dare Wayar Barister mahmud ta fara kara ...lokacin suna zaune da family dinsu suna dinner ...ganin number barister Shehu ce ya saka ya dauka tare da sallama ....


Barister Shehu yace ...Please ka sameni gurin gidansu wannan yarinyar akwae matsalane yanzu please ....

okey ...ya fada tare da daukar keys ya fita da sauri ....yana isa lungun gidan yaga ba motar Shehu ya kira wayarshi ringing daya ya dauka sannan yace gashi nan ....da yake lokacin sanyine mutane duk sun shige gidajensu ....kofar gidan su Huda ya matsa ya zauna saman dakalin dake wajen ....


Kaya yaga an watso mashi a jiki ....yayi saurin mikewa tare da daga tsumman da aka jeho mashi ....bindiga ya gani a ciki nannade ...da saurin ya daga cikin rashin fahimta ....ba dae wani abu akawa wadannan mutanen ba ..
ya fada da karfi tare da kara daga bingidar .....


Flashlight din da ta dinga haskashi tare da karar daukar hoto ya sakashi sakin bindigar kasa .....


Feedohm馃挒
馃挧馃挧 _*A DALILIN YAYATA..馃崄馃崄*_


馃崄

*_HASKEN WRITERS ASSOCIATION馃挕_*


Na Feedohm馃挒


_*DEDICATED TO*_
_EXCLUSIVE WRITERS..._


7 to 8


Weldon Barister ...ba dae kace zaka hanani aikata abunda nake so ba ....good gashi yanzu zaayi komae da kai ...
Barister Shehu ya fada lokacin da yake takowa kusa dashi ...



Bai san lokacin da ya sauke mashi mari ba tare da shakarar wuyan rigashi ...
wadanda suke tare sukayi saurin banbareshi tare da maida hannunshi baya suka rike ...

Shehu ya sake dariyar mugunta yace ..

Kayi abunda kake so Barister ....zaka bimu gidan mu karbi abunda nake bukata sannan ka tafi ....ko kuma na watsa wadannan pictures din a duniya na rubuta bayan na kaiwa Marayu Hakkinsu ...baristern duniya yaje da yan fashi sun karbe asirinsu ya tonu ...kayi tunanin makomar baristoci sannan kayi tunanin mutuncin mahaifinka sannan da son da yake maka ....na tabbata daga rannar da ubanka ya sami wannan labarin bara ya kara motsi ba ...kana sane da yana da hawan jini ....amma rufe wannan zancan shi zaya saka na goge wannan pictures din bayan wasu shekaru ....na lura kana so ka tuna man asiri ...
don haka zabi ya rage naka ...


Idanuwanshi suka ciko da kwallah ....tabbas indae har mahaifinshi yaga wannan labarin ya tabbata bakinciki zai zama ajalinsa .....ba tare da yace komae ba ya nuna kofar gidan da hannu ...alamun su tafi ...

Mask suka saka sannan Barister Shehu ya sakawa Mahmud suka shiga .....kauren an turoshi da alamun haka suke rufeshi dan an kangeshi da dutse ta ciki ......


Baka jin motsin komae sae kukan kaji dake tashi cikin ....suka kutsa kai suka shiga ciki ...kamar rakumi da akala haka Barister Mahmud ke binsu .....


Barister shehu ne ya saka kafa ya naushi mamar dake bacci ....tayi firgigi ta mike tana tasbihi ....


Nan da nan ya canza murya yace ina kudin da aka kawo masu ....

Bamu da kudi Wallahi dan Allah kuyi hakuri ....ta fada tana hawaye .

Karyane shegiya ....wani ya fada da karfi ..

Kaine dae Shegen munafuki ....Huda dake bacci ta farka tare da bashi amsa ....ya kai mata uban duka da yake dama ba kaunarta yake ba ....


Ta sake uban kara tana fadin ....Allah ya isa shege mugu ....ka bugi Uwarka na kashi .......

Bata rufe baki ba ya kara daga hannu da niyar dukanta ....Saa ta rungumeta tana kuka tare da bashi hakuri ....

Mahmud dake tsaye kamar gunki ..yace ...No.........kayi abunda ya kawoka amma banda duka ....ya karashe maganar da karfi ...


Gurin Uwar ya dawo yace....kina son ranki Hajiya ....ki fito man da kudin da aka kawo maki yau naira million goma da marece ko kuma na kasheki anan ...


Wallahi hakkin marayune kuyi hakuri dan Allah ....ku barmu hakkinsu ...ta fada cikin kuka ...


Duka ya kai hannu zai mata saa ta rarrafo tare da rike mashi hannu tana kuka ...Dan Allah karku dakar mana Umma wallahi inda kudine zan fito maku dashi ...ku barmu dan San Allah .....




Karkashin gado ta leka ta janyo jikkar bakko....ta fitar da tsumman dake ciki sannan ta janyo masu jikkar ta aje gabansu tana kuka ....

Huda tayi tsalle tare da dira saman jikkar ta cire kallabinta ta daure a kugu tana kuka tana fadin ....Wallahi ko uwayenku zasu zo nan bara ku fita da jikkar nan ba ....


Barister Shehu ya hankadata gefe guda ta fada jikin mahmud ....rikeshi tayi gam tana fadin ....karku tafi da ita Dan Allah ...da itane Mamana zata sakani Js One ....ku bar mana don Allah ....

Lumshe ido yayi ya banbareta daga jikinshi ya fita daga dakin da sauri ..

Motarsa ya fada ya cire Mask din dake fuskarshi ya jefar sannan ya data motar ya fita da ita daga lungun da gudu ....ko da ya koma gida Dad dinshi na zaune baki gate yana jiranshi ...yana ganshi ya taso tare da rungumoshi yana fadin ....

Lafiya dae ko .....

Dauriya ya saka a ranshi ya sakar mashi murmushi yana fadin ....Alhmd dad ....me kake anan har yanzu ..

hannunshi ya kama yana fadin ...taya hankali zai kwanta banga ka kwanta ba har 12 .....

Baice komae ba sae dae ya bishi da kallo suka shige ciki ...sae da Dad din ya rakashi har part dinshi sannan ya dawo ya kwanta ....


Feedohm馃挒
馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA...馃崄馃崄_*


馃崄


*_HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕_*


Na Feedohm馃挒


_*DEDICATED TO*_
_EXCLUSIVE WRITERS..._


9 to 10



Tunda suka tafi mutanen gidan suka hade guri guda suna kuka ...mamarce ke karfin halin lallashinsu amma sam Huda taki shiru sae ma abunda yaci gaba .....bawae yawan kudin takewa kuka ba ...wae Mamarta ta mata alkwarin idan har aka samu kudi ta kaita Js one zata dinga bata naira Hamsin na break to shi takewa kuka ....


Saa kadae ta fahimci abunda Huda kewa kuka ...don sae da mama ta fita sallar asuba sannan ta rarrafa tare da kwanciya saman cinyar Saa tana fadin ....Yanzu Shikenan Yaya Saa tunda an dauke kudin mama bara ta dinga bani naira hamsin din da tace ba ta tara .....ta saka bayan hannu tare da share hawayen tana fadin ...Allah ya isa ban yafe ba ...kullun naira hamsin in kashe ashiri na saka talatin asusu ..don Allah nawa zan tara yaya Saa ...


Saa tayi shiru tana jinjina rashin wayau na Huda ...bawae kudin suka dameta ba ...aa hamsin din da zaa bata takewa wannan ihun dama ....share mata hawayen tayi tana fadin ...Allah zai kawo wasu Huda kinji ..

Karfe 9:30 na safe barister shehu yazo gidan karbar kudin wae zaa kaiwa wadanda zaa sayi gidan gurinsu ....


tunda ya fara magana ...maman huda ke kuka har sae da ya dasa aya .....sannan ta fada mashi duk abunda ya faru .....

Salati ya fara yana dafe kai .....har da hawaye ..yana nuna yama fisu damuwa da dauke kudin da akayi .....don cewa yayi daga gidan police station ya nufa zai kai report dole a nemo wadanda suka sace kudin ......

Tace .. kawae ya barsu police babu abunda zasu iya yi a kae ...su sun barsu da Allah ko su waye ...

Cemata yayi zaya je ya dawo in Allah ya yarda yanzu ...sannan ya mike ya tafi .....cikin kudin da ya sace ya dauko dubu dari biyar ya kawo mata ....yace tayi jari da su ......

Godiya ta dinga mashi har da kukanta ......Huda ta shigo dakin tayi saurin dukawa gurin mamarta ta ...

Mamana me aka maki ....dan Allah kiyi shiru idan ma naira hamsin da zaki dinga bani kikewa kuka ...wallahi na yafe ki dinga bani arba'in idan kin samu ......ta karashe maganar kamar zatayi kuka ...

Huda Lauya ya bamu taimako ...banda bakin gode mashi ....ku tayani godiya ....ta share hawayenta ...


Mamana dama ya kawo ya sace.. kuma ya sake kawowa zai kuma sacewa ne .....ta fada tana kallonshi....

zumbur ya mike yana fadin ....Huda waye ....nan da nan zuba ta fara keto mashi ....

Da hannu ta nunashi tana fadin ...eh mana banda kai waye yasan muna da kudi ....

Mamanta tayi saurin buge mata baki tare da korata ta fice waje tana kwalla ...
tana fita gurin motarshi ta nufa ....ta samu kwalba duk ta bula tayoyin gaban motar sannan ta bar unguwar ...


Maman tata ta dinga ba barister shehun hakuri tana fadin ...Huda yarinyarce karda maganar ta bata mashi rai ....sun gode sossae Allah ya basu abunda zasu saka mashi dashi .....Yaya Saa ta shigo har kasa ta gaidashi ....ya amsa cikin faraa da yake ita yana shiri da ita ...ta mike ta fita ...yabi bayanta da kallo yana wani irin murmushi .......


Sun dan taba hira da mamar sannan ya tashi ya tafi .....da yake weekend ne gurin mutanen da sukayi aiki tare ya nufa ...su hudu ya basu 1m suka raba ....sannan ya tafi da
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment