Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aalimah da ke tahowa, Basma da Khaleesa sun sako ta a tsakiya har gabansa, sun bi sun rirrike hannunta, bakinsu kamar zai tsage don farin ciki, kan kujerar suke kokarin zaunar da ita kusa da Daddyn, amma sai ta zame ta zauna a kasa daura da kafafunsa ta soma gaishe shi cikin harshen Hausa.
Cewa yake, “Tashi-tashi ‘yata ki zauna a kujera, kin sha hanya. Ki yi hakuri I couldn’t make it taking you from airport, I went to California for a meeting, dawowata kenan. Ina fatan kin ci abinci kin huta?�
Murmushi ta yi, ta ce,
“Babu damuwa Daddy, kuma na ci abinci�.
Ya kalli Basma ya ce, “ Basma bani jakar can�.
Ta dauko jakar ta kawo masa babu ko russunawa kamar ta mikawa sa’anta, Aalimah ta ji wani iri a ranta. Budewa ya yi ya fiddo wasu takardu ya mika wa Basma, ya kuma mika wa Aalimahn wasu irinsu. Ya bawa kowaccensu biro ya ce ta sanya hannu karkashin dokokin jami’ar da za su je. Sai a lokacin ne Aalimah ta ga admission letter dinta da kwas din da Babanta ya zaba mata.
Zukar numfashi ta yi ta fesar, tana rokon Allah ya fidda ita kunyar iyayen ta, ta sha ji a bakin Yayanta Aboubacar how complicated pharmacy is (tsaurin kwas din harhada magunguna) lokacin da Daddy ya ce ya karanta shi don shine abinda Kakansa Prof. Kashim ya karanta ya kuma zauna akan (proffessorial chair) dinsa har mutuwar sa, ko don ya farantawa Mama, Aboubacar ya fitittike ya ce shi ba zai iya ba, Accounting yake so.
Nasiha sosai Daddyn ya yi musu a kan su tsare mutuncinsu, su maida hankali kan abin da ya kai su. Bai yarda da yin saurayi ko friendship da maza ba, duk kuma ranar da ya ga hakan zai cire kowaccensu ne ya yi mata aure. A karshe ya yi musu addu’a, ya gaya musu jibi za su fara registration.

3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Price 1&2 N400
6/28/21, 7:31 AM - Buhainat: 🌹 *Aalimah* 🌹
*
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*

FREE PAGES 6


Ta jima a jikinsa tana ba shi hakuri, sannan ya ce ya hakura, amma in tana son zaman lafiya ta daina kawo masa wadannan sababbin halayen da ta billo da su, kuma ta zauna lafiya da Aalimah don zamanta daram a gidansa, tunda ba tare suka hada kudi suka sayi gidan ba. Duk ta ce ta yarda, sannan suka yi dan gajeren romancing dinsu suka fito, suka tadda yaran duk sun sha wanka sun shirya gwanin sha’awa. Daga Basma har Khaleesat kayan Aalimah ne a jikinsu. Sun dan matse su sabida duk sun fita garin jiki. Don ma dai manyan riguna ne dinkin Nijar. Ta hadiye wani abu da ya tokare ta a wuya, ta kama hannun Yesmin suka fita. Ta dauka motarsa zai nufa ya shiga ya tafi inda za shi, sai ta ga ya ce duk su shigo tashi motar.
Mummy kamar ta yi kuka don ya rushe duk wani plan da ta shirya. Ta shirya a ranta ba wani traditional wears da za ta saya musu, kuma ba za ta sai wa Aalimah wani abin kirki ba, kwancen su Basma za ta dawo ta tattara mata. Ta san ba shi da sanya ido, ba abin da zai fahimta. Amma yanzu ta san ya ruguza komai.
Chevrolet din Daddy suka shige dukkansu. Ya zauna a mazauninsa ya sanya belt, sannan ya tsaya yana dan duba abu a wayarsa,da alama adireshin inda zai je yake dubawa a yanar gizo. Sannan a tsanake ya dauki hanya. Aalimah sakin ido da baki da hanci ta yi sosai tana shan kallon birnin Boston, don tunda ta zo ban da makaranta, babu inda ta ke zuwa.
Su Khaleesa na ta hira a tsakaninsu ba ta sa musu baki ba, wani lokacin ma ba sosai ta ke fahimtar maganganunsu ba, sabida yanayin accent dinsu. Sun iya Hausa, amma ba sa janta da nisa, wato jefi-jefi suke yinta. Ta lura Mummy ba ta da walwala sosai tunda suka taho duk da Daddy na yi mata hira. Tafiya suke sosai kamar za su bar cikin gari, kafin Aalimah ta ga sun hau wani titi da aka rubuta Newbury street Boston. Sun yi tafiya sosai a cikinsa kafin su karkata ya yi parking a kofar wani katafaren shago a samansa an rubuta Riccardi. Tunda Mummy ta fahimci shagon African Germents ne na maza da mata ta sake gyara zamanta cikin motar tana duba Ipad dinta.
Daddy ya dan dube ta ya ga ba ta da alamar fita sai ya mika mata hannu ya ce,
“Give me the credit card�.
Ba musu ta dauko a jakarta ta ba shi abinsa.
“Ba kya bukatar komai?� Ya sake tambaya cikin kwantar da murya.
Ba tare da ta dube shi ba, ta ce,
“A nan dai babu, su shiga su fito�.
Ya kada kai ya bi bayan yaransa wadanda har sun shige shagon sun hau elavator. Abubuwa kadan suka tsitstsinta a Riccardi don kayan maza na Africa sun fi yawa. Basma ta ce, Daddy ya kai su wani shagon again. A cikin mota ya zauna ya kira waya ya yi magana da wani abokinsa dan Nigeria, mutumin ya hada shi da matarsa suka yi magana, sai ya ja motar. Wannan karon kan titin Harrison Ave Daddy ya shiga.
Tun daga nesa Aalimah ta hango dogon ginin da ya tabbatar mata wannan karon su Basma za su samu har ma fiye da irin kayan da suke so. Daddy ya yi parking a parking lot suka firfito, wannan karon ma banda Mummy, Aalimah, ta daga kai tana karanta sunan shagon, ‘ZAINAB SUMU PRIMITIVE MODERN’. A cikin shagon nan su Basma sun yi siyayyar kaya da jewelleries har da na banza. Da ta ga Aalimah ta ki daukan komai ita da kanta ta dinga daukar mata duk abin da ta daukar wa kanta. Sai dai tana bambanta colour. Ta fahimci Aalimah na son ‘dark colours’ sabida kalar fatarta don haka komai ta daukar wa Aalimah mai turuwa ne sosai, sai ta daukar wa kanta lighter one. Hatta Yesmin sun gwangwajeta da kayayyaki daidai jikinta, sun samu kaya iri-iri, na Nijar, na Najeriya, na Senegal, na Arab da na D’jbouti. Daddy shi yake nuna musu wasu ma ya ce su kara. Sai da Khaleesat ta ji tausayin creditcard dinsa, ta ce su barshi haka, amma shi ko a jikinsa. Ya basu suka zare kudin komai, za su fito kenan wani Bature ya biyo su da gudu ya ba su wani littafi yana tallata musu malldin The Germent District, ya tabbatar musu za su samu shagon beyond their expection, za su ji shi kamar suna cikin Africa in dai batun tufafi ne. Basma ta ce a je, Khaleesat ta ce, sai dai wani lokacin, Aalimah ta ce su tausaya wa Daddy su barshi haka. Hannu ya dora a kan kafadunta ya bubbuga.
“If you like atamfa, lets go Aalimah, kada ki ji tausayin wannan Daddyn he loves you more than his money�.
Dariya suka yi suka shiga mota suka tafi. Aalimah dai ta kafe a barshi haka sai wani lokacin. Ganin ta dage suka yarda.
Sai da suka yi nisa Mummy Zulaiha ta yi gyaran murya, su kam har sun manta Mamansu na cikin motar saboda rashin motsinta. Daddy ya dan dube ta ya maida idonsa kan titi. Duk kokarinsa na fahimtar matarsa ya kasa. Ta zame masa ‘alqibla-less’. Ta dan motsa dan kyakkyawan bakinta tana magana, “Mu shiga kasuwa daBURLINGTON MALL zan yi cefane da tawa siyayyar�.
Bai ce komai ba ya karkata kan motar ya nufi kasuwar da ta fada, su suka taya Mummy da tura sayayyar da ta ke yi a shopping bag, har ta gama cefanen kayan abinci kala-kala nau’i-nau’i suka sa a bayan mota. Daga nan sai suka wuce Burlington Mall din ta yi ta sayayyar kayan gayunta, su ma ba a barsu a baya ba duk wani abin amfani na mata na tsaftar jiki da kayan shafa da kamshi sun saya, Daddy na ta biya, sannan suka taho gida.
Kafin su iso gida Mummy ta saki rai sosai tana ta jan mijinta da hira, su ma yaran tana kula su har Aalimah. Shi dai kallonta yake yana mamakinta. Ta zame masa kamar wata mai ‘Multi personality disorder’ yanzu ta ke daidai anjima za ta koma wata majanuniya. He loves his wife as such! Wato yana son matarsa a duk yadda ta ke. Take-away suka yi na KFC kafin su shiga gida don already dare ya yi, kuma duk yunwa suke ji mai girkawar ma Mummy ta gaji tibis. Tun a lokacin ta soma regrettingkorar Easther da yanzu kafin su dawo sun tadda komai yana jiransu a kan dining. To wai ma da ta yi gaggawar korar Easther how sure is she (wane tabbaci ta ke da shi na cewa) Aalimah ta iya girkin da za su iya ci har mijinta? Damuwa karara ta bayyana a kan fuskarta har suka shiga gida.
Kafin su kwanta, suna zaune a falo tare da yaran, Daddy ya ce, “Zulaiha ina tunanin daukar wa yaran nan driver, Basma ba ta kai shekaru sha takwas baballe ta dinga tuka su. Duk da Aboulkhair is coming for his holiday next month bana jin zai juri jigilar kai su da dauko su da wannan baccin safen nasa. Hanya ta da tasu are parallel (sun baude) ina makara most often (sau-tari)�.
Da sauri Mummy ta ce, “Ka san bana son strangers Daddy, ka bar zancen daukar driver din nan don Allah. Ni zan dauki nauyin kai su da dauko su dukkaninsu. Na gama course din da office suka sanya ni yi a Worcesterkarfe hudu zan dinga dawowa, kuma zan zauna wata guda a gida kafin na koma office so I will take care of their transportation�.
Cike da gamsuwa ya gyada kai sannan ya dago ya dube ta yana murmushi.
“Promotion in progress… Ummu Mu’az, wannan karon ya kamata a cire min parcentage, kudi sun yi miki yawa matar nan kuma ba mai ci, ke kanki ban ga kina ci ba�.
Dariya ta yi cikin nishadi ta kada masa kyawawan idanunta,
“Kai ma ka san wa nake tarawa.
I want him to own a lodge in one of the America’s most expensive luxury condos. Be it in San Francisco, Miami, Los Angels, Dallas, Seattle, New York, Oahu, Ohio, Chicago, nan Massachusetts, or wherever he like. A penthouse; irin wanda ko a garuruwan nan dana ambata sai dan gata zai iya mallaka. Ka san Allah Daddy ba don kaina nake wahalar aikin nan ba. I’m doing it for “MU’AZZAM� da lafiyarsa, tunda na lura shi in don ta shi bai damu ya tara komai ba.
Abin da ya sani kawai shi ne, ya yi ta bautawa wannan aikin nasa, yana karar da kudin a gidan haya, bayan wannan ban san me Mu’azzam ke yi da kudin da yake samu ba. I’m sometimes wondering he belongs to CHEVRON (wani lokacin ina tababar kasancewarsa ma’aikacin CHEVRON)�.
Murmushi sosai Daddy yake yi yana sauraronta da mamaki. Ba tun yau ba ya sani, Mu’azzam is her favourite childcikin ‘ya’yanta, amma bai taba sanin abin ya kai haka ba. Ta ci buri mai girma a kansa.
Wato duk tsayin shekaru goman nan da ta dauka tana aiki da JP Morgan Chase yana mamakin me ta ke yi da kudinta, tunda duk bukatunta babu wanda ta taba dauke mishi, sannan ya san ba iyayenta ta ke kaiwa ba, don shi ne ya gaji da ganinsu cikin tsohon gidan da suke ciki ya sauya musu, hatta petir din da za ta zuba a mota yana wuyansa, ashe this is her dream! Gyara zama ya yi sosai ya fuskance ta, ya kira ta da sunanta na yanka,
“Zulaihatu!�
Wannan ya tabbatar mata maganar da zai yin is highly sensitive. Bai damu da amsawarta ba, ya ce, “Ki fidda ZAKKAH, ki yi sadaka, ki kai iyayenki Hajj da duk wanda ya kamata cikin ‘yan uwanki. Sannan ki ninka kyautatawarki gare su.
Ba’a san gawar fari ba, amma use your opportunity when it is in your hands (wani lokaci na zuwa da za ki so ganinsu ko sau daya, amma zai zamo ba sa raye, ki yi amfani da damarki a lokacin da ta ke hannunki). Mu’azzam baya neman agajin ki a halin yanzu, domin ya riga ya tsaya a kan duga-dugansa. Abinda yake bukata daga gareki shine kawai ADDU’A da sanya albarka. And thank Allah the exalted for making you two alive together,which is his foremost success in life(kuma ki godewa Ubangiji Mabuwayi da ya raya ku tare, wannan shine babbar nasarar sa a rayuwa). Wannanita ce shawara ta gare ki a matsayina na mijinki, uban ‘ya’yanki,wanda ya fi kowa kaunarki in an cire iyayenki. Besides, this boy is making a lot of money beyond your expection (ta wani gefen, wannan yaron yana samun kudi fiye da tsammaninki). Yarage naki ki dauka ko kada ki dauka. Ina kara maimaita miki cewa(Mu’azzam ba ya bukatar kudinki don ya tsaya da kafafunsa, abin da yake bukata shi ne, KE din kanki a raye, da addu’o’inki.
Yana gama fadin hakan ya tashi ya hau sama ya barta a nan tana ta karanta wasikar jiki. Tana analysing kalamansa filla-filla.
*****


Kamar kullum washegari suka yi wanka suka shisshirya. Mummy Zulaiha ta zo har dakinsu ta yi kiran Aalimah. Tare suka fita ta nuna mata duk yadda ake amfani da injinan cleaning din gidan, da yadda ake tsaftace shi. Sannan ta tambaye ta ko ta iya girki? Ta ce ba abin da ba ta iya girkawa ba. Sai ta ce, har English meals? Ta ce, ta iya wasu a wurin Mamanta. Sai ta ce, to shi kenan daga yau ita za ta dinga girki da cleaning, mai aikinta ta yi tafiya. Tana kuma son kullum ta gama abincin dare kafin dawowar Daddy. Tana kuma son wannan zancen ya tsaya a tsakaninsu. Incase su Basma za su tambaye ta wani abu a kan hakan, ta ce, ita ta sa kanta.
Aalimah ta yi motsi da bakinta tana so ta tambaye ta makarantarta kuma fa? Amma ganin ba fuska dole ta hadiye. Tun a lokacin ta fara girkin rana bayan MummyZulaiha din ta nuna mata yadda ake amfani da komai.
Ta yi cleaning, ta yi girkin rana, ta yi na dare. Ko na minti biyu ba ta huta ba. Da suka tambaye ta ko me ta ke yi haka tun safe? Ta gaya musu yadda uwarsu ta gaya mata. Ta kara da cewa, Easther ta yi tafiya shi ya sa ta ke taimaka wa Mummyn. Allah ya so tun farko Mamansu ta hore su da komai, ba ta da son jiki ko kankani.
Ranar litinin, wato washegarin ranar,Mummy Zulaiha ta kwashe ‘ya’yanta ta kai makaranta, ta bar Aalimah a kitchen. Mamaki ya kama su har hada baki suke wajen tambayarta,
“Aal, will not go to school Mum?�
Ta lailayo ashariyar da ba su san ta iya ba ta antaya musu, ta kuma ce duk wanda ya kara yi mata zancen wata “Aal� ubansa za ta ci ciki da waje. Ta cire ta daga makarantar don ubansu, su je su gaya wa ubansu su ga yadda za ta ci mutuncinsu. Duk suka yi lakwas. Zaginta da balbalin bala’inta ya fi karfi a kan Basma, ta ce ta san ta fi kowa firirita a kan wata Aal, to in ta isa ta je ta gaya wa ubanta RAAZEE ISHAQ ta cire Aalimah daga makaranta.
Hatta abokan karatun Basma sun fahimci yau ba ta cikin walwala. Wadanda suka damu har tambayarta suke yi, me ke damunta? A gajarce ta ke cewa, “Headache�.
Da yamma motar makaranta ta bi ta koma gida, Mummy ta ce su Khaleesat kawai za ta dinga maidawa gida, she’s old enough ta kula da kanta (Basman).
Ko da suka dawo a kitchen suka tadda Aalimah ko wanka ba ta samu ta yi ba saboda aiki. Har wanki Mummy ta jibga mata don ma dai da inji ne. A ranta ta ce, in kin ji wuya za ki koma inda ki ka fito.
Idanu narai-narai da hawaye Basma da ke tsaye a bakin kofa ta ke kallon Aalimah, wadda duk ta yi gumi ta yi maiko, ta takarkare sai kankarar tukunya ta ke da cokali tana ci, abinci cokali daya wannan Mummy ba ta bata ba, duk da ita ta yi girkin. Tazo ta kwashe shi tsaf ta kai ‘dining’ kuma ta kasa-ta-tsare a falon tana ta ayyukan ta cikin system dinta, bata bari Aalimah ta ganta ba ta bar wurin da sauri ta yi sama da gudu, ta fada gadonta tana hawaye. Me za ta iya a kai banda fada wa Daddy? Babu!
Haka suka wuni dukkansu sukuku da su cikin damuwa da mamakin Mummy. Su dai sun san ko a cikin iyaye tasu uwar is exceptional wajen kyautata wa ‘ya’yanta. Yaushe ta canzazuwa maketaciya?
Rayuwar da suka yi ta yi kenan har tsayin wata guda, sai Daddy zai dawo ta ke cewa ta je ta yi wanka, sai za a zauna cin abincin dare za ta samu ta ci. Amma ba ta da breakfast ba ta da lunch. Sai karshen mako kuma, shi ma don Daddy na gida tana da freedom duk da haka komai ita ta ke yi, bai taba lura ba. Yanayin abincin gidan ne kawai ya lura ya canza, kuma ya fi jin dadinshi a kan na baya. Kuma da yake Allah ya yi shi mutum mara sa ido ko bin kwakkwafi, bai taba tankawa ba. Sakin ciki yake ya ci iyakar cinsa.

Karatu fal! Ya yi wa Aalimah fintinkau, ya wuce ta, an bada assingments har ba adadi ba ta yi ko daya ba. Absentness dinta da ya yi yawa shi ya sa coordinator dinsu da wasu daga cikin course tutors suka ankara. Makarantar ta yi tracingguardian phone number dinta a file dinta suka yi mishi phone call officially.

Ina kwalin digiri da masters din Mummy Zulaiha ya je ta manta da hakan zai faru? Oho! She’s blindly chasing a way to push poor Aalimah from her house. Ta manta an ce rana dubu ta barawo, rana daya ta mai kaya.
Karfe biyu na rana Aalimah tana kwashe abincin da ta gama girkawa a warmers, Mummy Zulaiha tana sama bedroom dinta tana barci abinta hankali a kwance. Kuka ta ke yi mara sauti tana share hawaye da hanci da gefen mayafin da ke kanta. Ba tana kuka ne don aikin da Mummy ke jibga mata ba wanda ko makaho ya shafa ya san ya fi karfinta ita kadai, ko kukan yadda ta kasa treating dinta kamar ‘ya’yan da ta haifa ba, tana kuka ne na tausayin kanta da iyayenta. Sun hana idonsu barci, sun yi fafutuka sun kawo ta don ta yi karatu an raba ta da shi a banza a daidai lokacin da ta fara fahimtarsa, kwakwalwarta ta bude ya soma shiga kanta, an maida ta boyi-boyin gida on no reason. Ba ta son zama sanadin kawo commution tsakanin ma’auratan, amma da ta ce da kawunta ya maida ita hostel tunda ita ta fahimci Mummy Zulaiha zamanta a gidan ne kawai ba ta so.
Ba zato ba tsammani sai ganin Daddy ta yi a tsaye a bakin kofa, ya dogara hannunsa na dama da kofar kicin din. Ta yi nisa a kukanta, shi ya sa ko motsin motarsa ba ta ji ba.
Daddy ya jima a tsaye a bakin kofa yana kallon Aalimah ba tare da saninta ba, ba kuma tare da sanin shi kansa mintuna nawa ya ba ta a wurin yana nazarin abubuwan ba. An ce four weeks rabonta da school, ya zo ya same ta tana girki a kitchen. Wannan na nufin duk abincin da suke ci tsawon sati hudun da ya fahimci canzawarsa ita ce ke girka shi? Wannan ne dalilin Zulaiha na korar mai aikinta, ta kuma hana shi daukar driver da ya ce zai daukar musu? Ba ya so ya yardar wa zuciyarsa Zulaiha ta aikata hakan da gan-gan, kuma za ta iya cin amanarsa har haka.
Ba zai yi saurin yanke hukunci ba sai ya ji daga bakin kowaccensu. Shigowa kicin din ya yi ya kama hannunta ya ja ta suka fice daga gidan, kafarta ko takalmi babu. Da fari ta tsorata, amma da ta ga Daddy ne sai ta yi shiru. Kukan ma bakidaya ya dauke. Ta san yau dubun Mummy ce ta cika tunda yanzun ba lokacin dawowarsa ba ne. Za ta yi amfani da wannan damar ta roke shi ya maida ita hostelno matter what. Yau da a ce zama ne ya kawo ta gidan ba karatu ba, she’s willing to do beyond what Mummy wants from her… ita ma uwa ce a gare ta kuma uwarta ma tana sa ta aiki, amma ba ta hora ta da yunwa. Daddy murfin chevrolet dinsa ya bude ya sanya ta a gaban motar, ya zagayo ya shiga mazauninsa a nitse ya fita daga compound din gidan nasa suka hau titi.
Sun yi tafiya mai nisa ba tare da ya ce komai ba, ita kuma ta yi kokari ta daina kukan da ta ke yi ta tsane hawayen idanunta tsaf! Amma kallo daya za ka yi mata ka fahimci ta ci kuka ta koshi, abinka da farar mace, fuskar nan ta yi jazur kamar jini zai fito. Sai daya yi nisa da unguwar su ‘Martha’s Vineyard Real Estate’ sosai sannan ya gangara ya sauka a gefen titi.
Yadda fuskarta ta yi jajawur saboda kuka haka tashi ma ta yi, duk da shi ba kukan ya yi ba. Tsananin bacin rai ne ya maida shi hakan. Ba Zulaiha kadai ya ji matukar haushi ba, har ita Aalimahn. Cikin fada ya soma yi mata magana cikin harshen su Temachek. Ga abinda yake cewa.
“Me yasa baki gaya min ba ta kai ki makaranta ba?�
Shiru ta yi, don ba ta san amsar da za ta ba shi ba. Mummy ba ta bata damar hakan ba, ‘ya’yanta ma sun kasa gaya masa balle ita? Idan ya dawo Mummy kasawa ta ke ta tsare har sai ta tabbatar ya shiga dakin barcinsa ya kwanta. Ko ba don wannan ba baza ta iya hada shi fada da matarshi da ta zo ta same su suna zaune happily da ‘ya’yansu, sannan tun washegarin ranar da Mummy ta ce zata dinga driving dinsu ta karbe wayarta data bata daga cewa za ta debi wasu muhimman contacts dinta da ke ciki, ba ta dawo mata da ita ba, and she lacks the courage to ask her again (bata da karfin gwiwar sake tambayar ta) tunda ta san wayarta ce.
Ko iyayenta da Yaya Aboubacar ba ta kira ba a tsayin kwanakin nan kusan talatin. He trust his wifeso much(ya yarda da matarsa sosai) ta yadda har ya daura mata alhakin kai su da dauko su.Howcould she told him that his wife is a green snake? (Ta yaya zata iya gaya masa cewa matar tasa macijin sari-ka-noke ce?�.
Jin ta yi shiru,sai ajiyar zuciya kawai take yi, sai kuma ya sassauta daga fadan da ya ke yi mata.
“Gaya min kin ji ‘yata Aalimah, me ke faruwa a gidan da ban sani ba? Ya ya aka yi kowa yana zuwa makaranta banda ke? Kada ki ji tsoro ki gaya min ba abin da zai same ki. Sai na ji gaskiya daga bakinki ne zan san matakin da zan dauka�.
Sosai ya ke lallashinta, yadda Daddynta ke yi in yana so ya ji cikinta. Kuka ne ya kufce mata, ta soma yinsa sosai.
“Na roke ka da Allah Daddy ka maida ni hostel, Daddy da Mama zuciyarsu za ta karye, in na kasa yin karatun nan. I’m not here to stay at home. I’m here to study, don Allah Daddy �.
Shiru ya yi zuciyarsa har barbawa ta ke yi sabida bacin rai. Daga bisani ya ce,
“Ina wayarki? Me ya sa ko text ne ba ki yi min ba in kin kasa kira na?�
Cike da fargabata ce,
“Ta karbi wayarta�.
Wuta ta dauke masa na dan lokaci, kafin ya ce cikin sanyin murya.

“I’m sorry my daughter, I failed to fulfill my responsibilities as a father. But that doesn’t mean negligence, it’s because I trust my wife so much on everything, (ki yi hakuri ‘ya ta, na gaza wajen cikasa hakkokina na Uba a gareki cikin gidana,

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

1 Comments On AALIMAH
avatar
nusaibah-2

11 months ago

Reply

I like dis book wllh

Please Login or Register in order to submit comment