Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

DARE DUBU DA DAYA (187)
HIKAYAR ANASIL WUJUDI DA MASOYIYARSA ALWARDI FIL AKMAM
A cikin wani dad’ad’d’en zamani da ya shud’e an yi wani babban sarki mai girman sha’ani da sarauta. Yana da waziri ana kiransa Ibrahimu wanda ke da wata ‘ya wadda ta kai matuk’a wajen kyawo da kwarjini da cikar halitta. Tana da baiwar fasaha da yalwar harshe. Sai dai tana yawan sha da son wasanni da wak’e – wak’e da son jin labarai. Irin baiwar da take da ita ne ya sa jama’a ke mata wak’a suna cewa:
Na je wajenta mai fitinar Turkawa
Har da Larabawa duk ba ta kyale ba
Tana jan hankalina zuwa a gare ta
Tana cewa ni zam mata ba wasa ba
Na ce mata raina fansa ne wurinki
Ba ki san zamani ba shi da sabo ba?
Idan yau kin zama kin haskawa
Gobe zai zamanto ba ke ce ba
Sunanta Alwardi, sunan ya biyo bayan irin kyawonta da cika da kwarjinin da ke gare ta. Sarki ya kasance yana son ganin ta saboda kyawonta. Ya kasance duk shekara sarki kan shirya wani taro wanda ake had’uwa a yi wasanni a motsa jiki a yi farin ciki. Da ranar da ta zo jama’a suka taru da dukkan manyan sarakunan k’asar, ‘yar waziri ta lek’o ta taga tana kallo, ana tsakar wasan sai ta hangi wani saurayi kyakkyawan gaske a cikin masu tsaro wanda ba ta tab’a ganin kyakkyawa kamar sa ba. Ga shi cikin kayan aiki masu kyau sun dace da shi, ga shi da fuska mai ban sha’awa, mai fararen hak’ora da wushirya daidaitacciya yana da yawan fara’a. Mai dogon wuya da faffad’ar kafad’a. Ta dube shi ta sake dubar sa har ta ji ba za ta iya daina kallon sa ba. Da aka jima sai ta cewa uwar goyonta, “wanene wancan saurayin mai kyawon gani haka?”
“Wanne kenan kike nufi?” Uwar goyon ta tambaye ta.
“To bari ya zo wucewa ta nan zan nuna miki shi.” In ji Alwardi
Ta d’auki tuffa ta daidaice shi ta jefe shi da ita, ya waiga da sauri ya d’aga kai inda ya ji jifa, sai ya had’a ido da ‘yar waziri tamkar wata a lokacin da dare ya yi duhu. Ya kalle ta ya sake kallon ta, ya kasa d’auke kai daga kallon ta, yayin da ita ma ta kasa daina kallon sa har sai da ya ji son ta na kwarara cikin zuciyarsa, ya rera wad’annan baitoci:
Kin jefe ni da baka ta idonki,
Kibiya ta harbe ni da ganinki
Ganinki ne ya kashe ni ta taga
Ko kuwa kibiyar da kika harbe ni?
Yayin da aka gama wasa kowa ya kama gaban sa, sai ta ce wa uwar goyonta, "yaya sunan wannan saurayin da na nuna miki?" Ta ce, "sunansa, Anasul Wujudi." Daga nan Alwardi ta tashi ta zauna a kan kujera, zuciyarta na huruwa da wutar bege. Ta yi ajiyar zuciya tana rera wadannan baitoci:
Wanda ya gan ka bai tab'e ba,
Ya Anasil Wujudi kyakkyawa
Na tsinkayi fuska tasa a taro
Ya zamto wata mai haskakawa
Taro ya yi kyau da zuwansa
Ya sa taro armashi shi ne dan baiwa
Yayin da ta gama wak'ar ta rubuta a wani siliki mai kyau ta ninke ta ajiye k'ark'ashin matashinta. Da uwar goyonta ta ga haka sai ta zo kusa da ita tana ba ta magana har ta samu ta yi barci sannan ta sace wannan takardar ta karanta abin da ke ciki ta fahimci lallai ta auka cikin kogin son Anasil Wujudi. Sannan ta mayar da takardar inda take ta koma mazauninta. Da yarinya ta farka sai ta ce da ita, "ya shugabata kin san ni ce mai shawartarki a wasu lamura, nakan shiga damuwa saboda ke. Ki sani shi so shu'umi ne, kuma b'oye shi ba ya k'ara komai sai sake narkar da zuciya tamkar yadda k'arfe ke narkewa idan ya sha wuta, ni ba zan shiga tsakanin so ba." Alwardi ta ce, "menene maganin bege da ciwon so." Uwar goyon ta ce, "maganinsa shi nesaduwa da masoyi."
"To yaya hakan zai samu?" Ta ce, "hakan na samuwa ta hanyar aike tsakanin masoya da tattausan zance da yawan gaisuwa. Wad'annan ke had'a kan masoya abu mai wahala ya zame musu mai sauki. Ni na cancanci na kiyaye sirrinki, kuma a shirye nake na zama 'yar aike tsakanin ku." Da yarinya ta ji haka sai zuciyarta ta cika da farin ciki amma ta yi shiru da maganar ta k'I fad'awa kowa. Ta ce a ran ta. 'Babu wanda zan fad'awa komai kuma babu wanda zan amince wa a wannan lamari tukunna. Wannan d'in ma sai na jarraba ta." Tsohuwa ta ce mata, "ya shugabata, ni na gani a cikin mafarki cewa wani mutum ya zo gare ni ya ce min, 'uwargijiyarki da Anasil Wujudi suna son junansu, ki tashi ki zama jakadiya tsakaninsu, ki b'oye lamarinsu alheri mai yawa zai faru gare ki idan kin aikata haka.' To kin ji mafarkin da na yi. Yanzu al'amari na gare ki. Alwardi ta ce bayan ta ji irin mafarkin da tsohuwa ta yi.
A nan asuba ta riski Shaharzad ta katse zancenta mai dadin saurare.
DARE NA 372
A dare na d’ari uku da saba’in da biyu, Shaharzad ta ce na samu labari ya kai wannan hamshaƙin sarki, Bayan yarinya ta ji bayanin tsohuwa game da mafarkin da ta yi, sai ta ce da ita, “da gaske kike za ki b’oye sirrina ya uwar goyona?” Tsohuwa ta ce, “ ta yaya zan kasa b’oye sirri alhali ina daga ‘ya’ya tsarkaka?” Sannan yarinyar ta d’aga matashin kanta ta d’auko takardar nan da ta rubuta ta, ta da ka wa tsohuwa ta ce ta tafi ta kai wa saurayi Anasul wujud. Sannan ta ce ta tsaya ta karb’o amsa. Tsohuwa ta d’auki takarda ta tafi zuwa wajensa ta ba shi, ya karanta ya fahimci abin da ta k’unsa sannan ya rubuta a bayan takardar amsa kamarhaka:
Ina maimaita begenki a zuciyata,
Amma na kasance ina b’oyewa
Halin da nake ciki yana fassara
Hawayena suna ta faman zubowa
Idanuna na ciwo da gudun zargawa
Ni na kasance mai yawan kewarki
Tun lokacin nan da muka zam ganuwa
Zuciya na cikin duhu k’warai da ita
Begena da kewar ki kullum na k’aruwa
Ya ninke takardar ya sumbace ta, ya ba wa tsohuwa ya ce, “ki isar min da gaisuwata ga Gimbiya.” Ta juya ta tafi ta kai mata sak’o. Bayan ta karanta ta fahimci sak’on sannan ta rubuta a k’arkashin takardar baitoci kamar haka:
Ya mai k’unar zuciya da ganinmu,
Yi hak’uri ka rabauta daga gunmu
Mun yi sanin cewa son ka gare mu
Yana nan kamar yadda yake wajenmu
Zuciyarka tana cikin k’aunarmu
Ka jira dare ya zo domin had’uwarmu
Sharad’in kenan mu hadu ni da kai
Domin kashe wutar begen ranmu
An zuba k’aya a wurin kwanciyarmu
Hak’ark’arinmu ba maraba da jikinmu02 HIKAYAR ANASIL WAJUDI DA MASOYIYARSA ALWARDI FIL AKMAM

Ta ninke takarda ta ba wa magoyiyarta ta tafi domin zuwa wajen saurayi. Tana isa k’ofa ta had’u da mai tsaron k’ofa wani baba ne mai girman jiki. Ya daka mata tsawa yana cewa, “ina za ki?!” Ta ce, “gidan wanka za ni.” To amma yadda ta ba shi amsa jikinta na rawa ba ta san lokacin da ta jefar da wasik’ar ba. D’aya daga babanni ya gan ta a k’asa ya d’auka. Yayin da uwar goyon ta fita waje ta duba babu takarda, sai ta juya baya ta shaida wa uwargijiyarta abin da ya wakana.
Waziri na zaune a kujera cikin zaurensa sai baba ya shiga wajensa ya dank’a masa wannan takardar ya ce “na tsinta a nan waje yanzun nan.” Waziri ya karb’i takarda ya karanta, ya duba ta sosai ya gane hannun ‘yarsa. Ya fashe da kuka sannan ya tashi ya tafi wajen uwar yarinyar yana kuka duk ya jik’a gemunsa. Ta ce masa, “me ya faru kake kuka haka?” ya ba ta amsa ya ce, dubi wannan takarda ki gani.” Ta karbi takarda ita ma ta gane cewa wasik’ar soyayya ce daga ‘yarta zuwa ga wani mai suna Anasul Wujudi, ita ma sai ta kama kuka, amma daga bisani sai ta dangana ta natsu duk da hawaye na kwarara a idanunta ta ce da mijinta, “ya shugabana kuka ba zai mana amfani ba, abu ma fi muhimmanci shi ne yadda za ka kiyaye martabarka da mutuncinka game da al’amarin ‘yarka.” Ta ci gaba da ba shi magana har zuciyarsa ta d’an yi haske daga k’uncin da ya shiga. Ya ce da ita, “tsoron da nake game da wannan yarinyar saboda ban san halin yaron ba. Kuma shin kin san cewa sarki na matuk’ar son ta kuwa? Tsorona guda biyu ne, na farko game da ni kaina, na biyu kuma saboda sarki yadda Yake ji da Anasul Wujudi idan wannan zancen ya je kunnensa kashinmu ya bushe. Me kike gani za mu yi?”

Waziri ya tambayi matarsa game da al’amarin ‘yar su ya ce, “Me kike gani za mu yi?
Ta ce masa, “yi hak’uri tukunna har na yi istikhara.” Ta d’aura alwalla ta yi sallah raka’a biyu sannan ta yi addu’ar istikhara kamar yadda ma’aiki mai tsira da aminci su tabbbata a gare shi ya koyar. Bayan ta kammala ta ce da mijinta, “a cikin tsakiyar bahar kogin taska akwai wani dutse ana kiran sa dutsen sakla. Dalilin ambatonsa da wannan sunan shi ne babu wanda zai je gare shi face ya sha wahala. Ka yi mata wurin zama a can.” Waziri da matarsa suka amince za su gina fada a can su kai ‘yarsu da dukkan abubuwan buk’ata. Za a rik’a kai mata komai na shekara guda tare da dukkan kuyanginta da babanni da sauran hadimai. Ya samu masasska’a da magina da masu zane suka gina wani babban gida wanda ba a tab’a ganin irin sa ba. Sannan ya sa aka shirya dukkan komai aka yi shirin tafiya, waziri ya shiga wurin ‘yarsa cikin dare ya ce ta fito domin su tafi yawon bud’e ido. Ta fito ta ga an kammala shiri tsaf ana jiran ta. Zuciyarta ta yi k’unci saboda rashin sanin wajen da za a je, ta ji kewar rabuwa da mutanenta. Ta yi ta kuka mai tsanani, ta rubuta wad’annan baitoci a k’ofar gidan domin sanar wa Anasil Wujudi halin da ta tsinci kanta. Tana mai fatar idan ya zo wucewa ko ya yi nufin ganin ta ya ga wannan abin da ya zagwanye mata zuciya, ya yank’wane mata fata, ya narkar da nama gami da sanya kwararar hawaye. Ga abin da ta rubuta:
Domin Allah mutan gidanmu,
Idan masoyina ya zo wajenku
Ku gaishe shi da kyau da kyau
Daga gu na ku fad’a da kanku
Ku fad’a masa na tafi wurin nesa
Ban san inda za a kai ni ba gare ku
An d’auke ni cikin dare mai duhu
Hatta tsuntsaye tuni sun barcinsu
Ku ce masa da sannu hali zai samar
Da had’uwar masoya biyu a ranaku
Na gani an cika kaskon nisantar mu
Amma hali da sannu zai bar shakku
Ni kam na da’u hak’uri sai wata ran
Kai ma ka yi hakuri da sannu ma sadu
Yayin da ta gama rubuta wak’ar ta hau bisa abin hawan da aka tanadar mata suka d’unguma suna wucewa da keta jazirori da fak’uk’uwa da jigayi da kwaruruwa da wurin tudu da burji har suka sadu zuwa ga kogin gab’ar taska. Suka sauka a nan suka kafa laima suka huta sannan suka shigar da ita wani babban jirgi suka tuk’a zuwa dutsen sakla. Waziri ya umarce su da idan sun kai ta gidan da aka gina a shigar da ita da jama’arta sannan a dawo a karya gadar da ke sadar da mutum zuwa gidan. Jirgin kuma a d’auke shi daga kogin. Suka aikata umarninsa sannan suka dawo suna kuka. Wannan kenan game da al’amarinsu.
Amma Anasul Wujudi kuwa da ya farka da asuba ya yi sallah sai ya shirya ya hau dokinsa ya tafi wurin aiki, a hanyar dawowarsa ya biyo ta k’ofar gidan waziri bisa zummar ko zai samu yin ido hud’u da abar k’aunarsa ko kuwa wani abokin aikinsa domin ya zauna nan wurin sa. Da ya iso gidan bai ga kowa ba, ya d’aga kai k’ofar gidan da ya ga rubutu ya karanta. Yana gama karantawa ya ji hanjin cikinsa ya d’auki zafi, zuciyarsa ta yi tsanani. Ya juya zuwa gidansa bai san halin da yake ciki ba, ya kwanta bai fad’awa kowa halin da yake ciki ba. Da al’amarin ya tsananta gare shi, wutar soyaya ta ruru a zuciyarsa, sai ya tashi ya yi shigar masu bara ya fita daji bai san ininda yake tafiya ba cikin dare. Ya yi ta tafiya a wannan daren har gari ya waye da tsakar rana bai fasa tafiya ba. Zafin rana ya tsananta, duwatsu suka zama tamkar wuta, ga gajiya da yunwa da k’ishirwa na gallabarsa. Can ya hangi wata bishiya wadda ruwa ke gudana a k’ark’ashinta. Ya tafi ya zauna k’ark’ashin inuwarta ya yi nufin shan ruwan amma ya rasa mad’ebi hannunsa bai kai ba ballantana bakinsa. Tuni yanayin fuskarsa ya sauya, ya motse, ga k’afafunsa sun kumbura saboda tafiya da wahala. Ya karkata kai yana rera wad’annan baitoci:
Masoyi ya sha giyar begen masoyi,
Wanda ya dogari da shi a farin ciki
Soyayya ta azabtar da mu k’warai
Mun yi nisa ba ruwa balle abinci
Yaya rayuwa za ta yi dad’i babu ke,
Masoyiyata kin tafi tamkar mafarki
Na k’one da wutar so kewar Gimbiya
Ga ni nan tafe ko’ina ina neman ki
Da ya gama wak’ar ya fashe da kuka, ya yi ta kuka har k’asar inda yake zaune ta jik’e da hawayensa. Daga nan ya tashi ya bar wannan wuri ya yi ta tafiya yana keta daji da tudu da kwari har gab’b’ansa suka gaji, gashin kansa ya jik’e da gumi, idanunsa suka yi rauni. Yana wannan hali sai ga wani zaki ya b’ullo mai ban tsoro, gashinsa kamar mashi, kansa kamar k’ubba, bakinsa kamar k’ofar d’aki, hak’oransa kuwa kamar na giwa. Yayin da Anasil Wujudi ya ga wannan dabbar ta taso gare shi haik’an sai ya sakankance da mutuwa, ya kalli ka’aba yana maimaita kalmar shahada. Ya karanta a littafi cewa duk wanda ya gamu da zaki a daji idan ya yi masa ladabi, ya yi masa zance cikin k’ask’anta kai za su rabu lafiya. Saboda haka ya tausasa harshe yana cewa, “ya babban zaki, zakin zakoki, zakin dukkan dabbobi daji kai ne babbansu ko sun k’i ko sun so. Ya kai babbar halitta uban samari da tsofaffin dabbobi. Sarki mai mulkin dabbobi. Ka sani ni mai bege ne wanda na rabu abar begena, na karkata ga barin kyakkyawan halina, na bar muhallina mai dad’i na taho nan. Ka ji tausayina, ka dubi wahalata da begena. Yayin da zaki ya ji wannan maganar sai ya jinkirta gare shi ya zauna tsugunne a kan kafafunsa ya d’aga kansa sama kamar yana sauraren wani abu. Can an jima sai ya rik’a kartar k’asa da daginsa, daga nan ya rik’a wasa da su. Yayin da Anasil Wujudi ya ga haka sai ya rera wad’annan baitoci:
Ya zakin daji kana son kashe ni
Tun kafin na ga mai wahalshe ni?
Ni ba naman daji ba ne babu k’iba
Kuma kewar ta ta sake ramar da ni
Ban wuce ‘yar siffa cikin likkafani ba
Ya uban daji zakin yak’i ka ji da ni
Kada ka bari masu zargina su samu
Nasara a kaina su da zubar hawayena
Kada ka bari wahala da yawan kewa
Neman masoyina su halakar da ni
Ban kula da duhun dare ba tamkar ka
Ba ka kula da dare balle ka yi razana.03 HIKAYAR ANASIL WAJUDI DA MASOYIYARSA ALWARDI FIL AKMAM

Ya watan tsuntsaye shin kai ma kar ni kake?
To ka rok’i Mamallakin kowa ya zam amsawa
Wa ya gani cikin kukanka akwai faranta ciki
Ko kuwa kukanka na bak’in ciki ne da rabuwa?
Idan na yi kukan rashin saduwa da masoyina
Zan zamo hak’urin da na d’auka ya zam k’arewa
Ya Allah ka kiyaye amincin masu begen juna
Ba zan daina neman ta ba ko da zan zam mutuwa
Bayan ya k’are wannan wak’ar ya sake suma, da ya farfad’o ya nufin shek’a ta biyu ya ga mai jira a ciki. Da ya gan shi sai ya yi kuka kamar yana cewa, “ya matabbaci sannunka.” Ya yi ajiyar zuciya ya rera wad’annan baitoci yana cewa:
Majirayi ya ce min mutum kake ko aljani?
Na gode fad’ar Abidi zan samun abin biya
Yalla ko Allahu ya kusata ni da baiwa tasa
Ya biya min buk’atata domin burin zuciya
Da yawa zuma kan yi harbin domin ruwa,
Idan ka ga wuya sauk’i na zuwa daga baya
Wuta ta k’one zuciyata ta maida ruwa jini
Na kwarara a kuncina na b’ata a soyayya
Ya matsa shek’a ta uku ya samu cakwaikwaiya, yayin da ta gan shi sai ta soma tsalle tana kuka. Shi kuma ya rera wad’annan baitoci:
Cakwaikwaiya ta yi al’ajabi daga sautina
Tamkar sautin mai bege lokacin begensa
Na ce ku ji tausayinsa ya ‘yan uwa gare shi,
Da yawa akan mutu bisa so da bege na kusa
Tamkar an samu bege cikin dare babu barci
Babu wayewar gari babu kula da al’amarinsa
Kilishi ya zame masa kurkuku da ya jib’ince ni
Ya dabaibaye ni da begen so da tsabar sonsa
Na ce da su gudun hawaye ya tsawaita gare ni
Hak’urina ya tafi tilas ne na zagaya nemansa
Ya tafi zuwa shek’a ta hudu ya tarar da Alallak’a na zaune su biyu, da ganinsa suka yi tsalle suna wak’a suna nishi. Da ya ga haka sai hawaye suka kwararo masa ya rera wad’annan baitoci:
Alallak’a sun gan ni suna gaisuwa gare ni
Suka ce ya Anasil Wujudi sannu da tsanani
Hawayena suka zubo domin tsabar so
Sautinsu mai dad’i yana matuk’ar tsuma ni
Na zamto mabeganci na shagala da kyau
Ina cikin son ta da nema cikin dukan zamani
Ya tafi gaba kad’an zuwa ga wata kyakkyawar shek’a wadda babu wanda ya kai ta kyau a wurin. Ya lek’a ciki ya tarar da kurciya tana nishi irin na bege, wuyanta da k’udurin jauhari sabo. Ya dube ta da kyau ya ga ta fi kowanne tsuntsu kyawon gani a wurin. Ya skhekar da hawaye sannan ya rera baitocin nan:
Ya kurciya na tunkare ki da gaisuwa,
Ya ‘yar uwar bege da masu begen girma
Ni ina cikin son barewa mai d’an wuya
Amma ganinta ya fi saran takobi girma
A yadda ta haramta mini jin dadin barci
Ruwa ya zame min d’aci babu zuma
Yayin da Anasul Wujudi ya k’are wannan wak’ar.

Yayin da Anasul Wujudi ya k’are wannan wak’ar sai kurciya ta juya jikinta cikin alamun jin maganar ta ratsa ta na game da bege. Ta karkad’a kai tana kuka irin nata kamar dai tana ba shi labarin wasu lamura na rayuwar masu bege. Bayan wannan Anasil Wujudi ya dubi Baban nan ya ce masa, “yalla wannan wurin wanene ya gina shi?” Baba ya ce, “Waziri wane shi ya gina wannan waje domin tsaron ‘yarsa yana tsoro kada ta shiga matsala a lokacin rayuwarta, ya kawo ta nan tare da hadimanta duka. Ba a bud’e wajen sai sau d’aya a shekara lokacin da ake shigo da kayayyakin buk’ata.” Ya ce a ransa, ‘da sannu zan samu cimma burina amma zan jima ina sauraro.’ Wannan kenan game da al’amarinsa.
Amma game da Alwardi ta kasa jin dad’in komai ta daina ci ta daina sha, ta kasa zama ballantana kwanciya ko barci. Tsananin bege ya sake k’aruwa cikin zuciyarta. Ta fita tana yawo cikin k’ubbar nan tana gewaywa tana kuka da wak’e – wak’e. Ta yi ajiyar zuciya tana cewa, “an d’aure ni da kewar barin masoyina, sun jefa ni kurkuku wai shi soro an k’one mini zuciyata da wutar so tunda aka juyar da ganina da masoyina. An d’aure ni cikin soro mad’aukaki a cikin dutse wanda aka halicce shi cikin zurfin ruwan kogi. Su burinsu hana mini cimma burina, babu ragi sai don kawai su halaka ni. Ta yaya za a hane ga zuwa wajensa….”
Tana gama fad’ar haka ta nufi wajen taga ta bud’e sannan ta k’uk’k’ulla zannuwanta na alfarma masu tsada sannan ta d’aura sark’ar jauhari a wuyanta. Ta zura wannan d’aurin zuwa waje sannan ta kama a hankali ta sauka k’asa ta tafi cikin daji har ta isa zuwa gacin kogin ta hango wani masunci iska ta kado shi wannan wuri. Yana hango ta sai ya firgita ya yi tsammanin aljana ce, ya tura da gudu zai tafi. Ta yi k’ara gare shi tana masa ishara da hannu tana cewa, “ya kai masunci, ni fa mutum ce tamkar ka ka daina jin tsorona. Addu’a ce na yi kuma aka amsa addu’ata domin na kasance cikin bak’in ciki da rashin kwanciyar hankali. Ka saurari zancena ka ji tausayina sai Allah ya tausasa maka.” Ta d’aga murya tana mai shaida masa halin da take ciki.” Masunci da ya ji halin da take ciki sai ya yi ajiyar zuciya saboda tausayi ya tuno abin ya wuce gare shi lokacin yana k’uruciya. Lokacin da son zuciya ya rinjaye shi, bege ya tsananta gare shi. Bak’in cikinsa ya k’aru da b’acin zuciya. Wutar bege ta ruru cikin zuciyarsa, ya wak’a wad’annan baitoci:
Tsananin k’auna ta yanke mini hanzari
Gab’ob’ina sun raunana hawaye na ta zuba
Idanuna sun daina barci duk tsananin duhu
Zuk’ata na tafasa wutar so na ci da ta jaraba
Na samu jarraba a lokacin k’uruciyata
Har mun sayar da rayukanmu babu riba
Yayin da masunci ya k’are wak’arsa sai ya gurguso da jirginsa kusa da inda take tsaye ya ce, “shigo na kai ki inda kike son zuwa.” Ta shiga ciki shi kuma ya tura jirgin cikin ruwa, iska ta yi musu kyau ba ta hargitsa su ba. Suka tafi har suka daina ganin k’asa, watau inda suka baro. Shi masunci tafiya kawai yake yi bai san inda yake nufa ba, iska kuma na tura su da hanzari ba da katsewa ba har kwana uku. Yayin nan iska ta ruma da yardar Allah mad’aukakin sarki, jirgi bai gushe ba yana tafiya da su har suka sadu zuwa
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment