Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

01. HIKAYAR TUFFA UKU

Allah shi ne Sarki ma fi daukaka daga dukkan Sarakuna, shi ne ma fi tsarki daga dukkan abubuwa.
Wata rana da dare, daga cikin ranaku,

a cikin birnin Bagadada, lokacin da Halifa Harun Al'Rashid da Wazirinsa Ja'afarul Barmakiyi ke mulki, Halifa ya aika cikin dare aka kira masa waziri Ja'afaru da sarkin fada Masruru.

Ya ce musu, "Ina so a cikin wannan dare mu canja kama, irin ta fatake, mu shiga cikin birni, mu tambayi talakawa a kan yadda suke ganin mulkinmu a kansu, duk wani hakimi, ko wakili ko mai unguwa da muka ji talakawa na kuka da shi, sai mu tube shi."

Ja'afaru da Masruru suka ce, "Mun ji, mun dauka!"

Suka yi shiga irin ta fatake, suka shiga cikin birni. Suna cikin tafiya cikin wani kwararo, sai suka ga wani tsoho, shekaru sun yawaita a kansa, yana dauke da wata

tsohuwar koma ta kamun kifi, yana tafe yana wake-wake. A cikin wake-waken nasa sai suka ji yana cewa: "Koyaushe mutum ya kai kara zuwa gare su, sai su wulakanta shi, koda shi yake da gaskiya. Idan haka ne kuwa,

kasancewar ran talaka a cikin kabari shi ne ma fi kyawon zama."
Yayin da Halifa ya ji wannan waka ta dattijo, ya dubi Ja'afaru ya ce, "Dubi wannan talaka, ka ji wannan waka tasa? Lalle akwai abin da ke damun sa a cikin zuciyarsa."

Halifa ya gabata a gaban tsoho ya ce, "Ya kai wannan tsoho, mene ne sana'arka?"

Tsoho ya ce, "Ya shugabana, su ce sana'ata. Ni talaka ne, na fita daga gidana tunda tsakar rana na nufi kogi kamun kifi, har zuwa wannan lokaci da na dawo, Allah bai nufa na kama wani abu da zan ci ni da iyalina ba, domin bakin cikin wannan abu, nake gurin mutuwata."

Halifa ya ce da shi, "Ko za ka koma tare da mu zuwa ga kogin Dujillati, ka jefa komarka a ciki, bisa ga arzikina, komai komarka ta debo a cikin kogin zan saye shi dinari dari, ka sami abin da za ka ci da iyalinka?"

Tsoho yayi farin ciki da jin wannan magana ta wannan farke. Baisan sarkinsa bane' Ya ce, "Na yarda, ya shugabana."

Suka dunguma suka nufi kogin Dujillati, da suka isa, tsoho ya warware komarsa, ya jefa bisa ruwa, ta nutse kasa, ya jirkita ta, sannan ya jawo ta. Koma ta fito da akwati dake sarki me cika alkawarin saiya biya' kudin wannan akwati babba mai nauyi. Yayin da Halifa ya gan shi, ya dubashi shi, ya same shi nannauya. Ya ba masunci dinari dari, ya tafi yana murna.

Masruru ya dauki akwati tare da Ja'afaru suka nufi gidan Halifa. Da suka isa, suka kunna fitila, aka ajiye akwati saiya ciro mab'alli Halifa. Ja'afaru da Masruru suka karye murfin akwati suka tarar da kubba a ciki, an rufe ta da jan gashi. Suka yaye gashin, suka tarar da mayafi karkashinsa,

suka yaye mayafin, suka tarar da shimfida karkashinsa, suka yaye shinfidar, sai ga yarinya a kwance, kai ka ce narkakkiyar azurfa ce don kyau. An yanka ta gunduwa-gunduwa, ta kasance matacciya.
Yayin da Halifa ya ga wannan yarinya da irin kisan da aka yi mata, sai hankalinsa ya tashi, hawaye ya karyo masa yana gudana a kan kundukukinsa.

Ya waiwaya zuwa ga Ja'afaru cikin fushi mai tsanani, fushin da bai taba yin irinsa ba, ya ce da shi, "Ya karen wazirai, Wallahi ka cancanta da na kashe ka a cikin wannan lokaci. Kana wazirina har a kashe mutum, a saka a cikin akwati a jefa cikin kogi cikin zamanin mulkina. Kuna so wannan laifin kisa ya ratayu a kaina? Wallahi!

Babu makawa in bincika al'amarin wannan yarinya, duk wanda aka samu ya kashe ta, in kashe shi, in saka mata hakkinta."

Hankalin Ja'afaru ya tashi, domin bai taba ganin fushin Halifa kamar irin wannan ba. Halifa ya dube shi ya ci gaba da cewa, "Da girman saduwata ga dangin Halifofi na daga Banu Abbas, idan ba ka zo mini da wanda ya kashe wannan yarinya ba, in saka mata gare shi, Wallahi sai na rataye ka a kofar gidana, kai da mutum arba'in na daga 'yan uwanka!"

Ja'afaru ya ce, "Ka jinkirta mini zuwa kwana uku, ya Sarkin Musulmi!" Halifa ya ce ya jinkirta masa.

Ja'afaru ya fita daga gidan Halifa, ya nufi cikin birni yana mai bakin ciki, yana cewa a cikin ransa: Ina zan san wanda ya kashe wannan yarinya, har in hallara shi gaban Halifa? In na hallara masa wani wanda ba shi ya aikata laifin ba, aka kashe shi, alhakinsa ya ratayu ga wuyana ke nan, ni yanzu ban san abin da zan aikata ba. Ya nufi gidansa.

Ja'afaru ya yi zaune gidansa har kwana uku suka wuce. Rana ta hudu Halifa ya aika zuwa gare shi, yana nemansa. Yayin da ya zo gaban Halifa, sai ya tambaye shi, "Ina wanda ya kashe yarinya?"
Ja'afaru ya ce, "Ya Sarkin Musulmi, ni na san abin boye ne, ballantana na san wanda ya kashe yarinya?"

MUHADU GOBE DOMIN CIGABA02. HIKAYAR TUFFA UKU
(TALE OF THE THREE APPLES)

Halifa ya juya wurin dogarawa ya ba su umurni
su rataye Ja'afaru da 'yan uwansa. Tausayi ya
kama mutane, wasu suka fara kuka. Dogarawa
kuwa suka zabura domin cika umurnin Sarkin
Musulmi
Daga nan sai ga wani saurayi kyakkyawa, mai
kyawawan tufafi, ya keto daga cikin mutane da
gaggawa, ya zo ya durkusa a gaban Halifa. Ya
ce, "Ya Sarkin Musulmi, ni ne na kashe wannan
yarinya da kuka gani a
cikin sunduki. Kashe ni a madadinta, domin
daukar mata fansa."
Yayin da Waziri Ja'afaru ya ji zancen wannan
saurayi, da abin da ya bayyana daga zancensa,
ya yi farin ciki da kubutar ransa da na 'yan
uwansa, sannan kuma ya yi bakin ciki da
hukuncin da za a yi wa wannan saurayi. Halifa
ya yi umurni da a rataye wannan saurayi tunda
ya yi ikirari. Dogarawa suka cafe saurayi za su
rataye shi.
Daga nan sai ga wani tsoho mai yawan shekaru,
ya ratso ta cikin mutane yana kuka. Ya zo ya
durkusa a gaban Halifa ya ce, "Ya Sarkin
Musulmi, kada ka kashe wannan saurayi ba da
alhakinsa ba. Ni ne wanda ya kashe yarinya, a
kashe ni maimakonta."
Saurayi ya ce, "Ya Halifa wannan tsoho ya tsufa
da yawa,rudewar tsufa
ce ta sa shi yin wannan magana. Ni ne na kashe
yarinya, a kashe ni maimakonta, ku biya
alhakinta da ni."
Tsoho ya ce da saurayi, "Ya dana, kai yaro ne
kankane, yanzu ka fara sha'awar duniya. Ni na
girma na koshi da duniya, na fanshe ka na
fanshi Waziri Ja'afaru da 'yan uwansa, babu
wanda ya kashe yarinya sai ni. Domin Allah na
roke ku, ku gaggauta kisasi da ni."
Halifa ya dubi saurayi da tsoho ya ce, "Wanene
daga cikinku ya kashe yarinya?"
Saurayi ya ce, "Babu wanda ya kashe ta sai ni,
don haka a kashe ni."
Tsoho ya ce, "A'a, ni ne na kashe ta, don haka ni
ne ya kamata a kashe."
Da Halifa ya ji haka, sai ya ce a rataye su duka
su biyun. Waziri Ja'afaru ya ce a'a, mutum daya
ya yi kisan kai kuma a rataye biyu, wannan
zalunci ne ya Halifa.
Saurayi ya ce, "Da girman wanda ya daukak
sama, ya shimfida kasa, ni ne na kashe yarinya,
na sanya ta a cikin sunduki, na jefa sundukin a
cikin kogin Dujillati." Ya siffanta abin da aka
samu a cikinsundukin
majeranta. Halifa ya gasgata saurayi, ya kuma
tabbata shi ne ya kashe yarinya. Halifa ya yi
al'ajabi a kan wannan al'amari, ya tambayi
saurayi dalilin kisan yarinya.
Saurayi ya ce, "Ka sani ya Sarkin Musulmi, cewa
wannan yarinya matata ce, 'yar baffana. Wannan
tsoho shi ne ubanta kuma baffana ne. Na aure
ta tana budurwa, na sami zuri'a da ita 'ya'ya
uku, dukkansu maza. Ta kasance tana so na,
matsanancin so, tana yi mini biyayya iyakar
biyayya, da dai ba ta taba bata mini rai ba.
Ranar farko ta wannan wata, sai ta kwanta
rasahin lafiya mai tsanani. Na nemo masu
magani kala daban-daban, suna ba ta
magunguna har ta fara samun sauki. Ran nan
na shiga dakinta, sai ta ce da ni, tana son wani abu, domin tana
marmarinsa. Na tambaye ta menene shi? Ta ce
da ni, tana marmarin cin tuffa. Na ce zan siyo
mata.
Da fita ta daga dakinta, ban zame ko'ina ba sai
kasuwa wurin neman tuffa. Na zagaye kasuwa
duka amma ban samu ko daya ba. Na dawo
cikin gari ina cigiyar tuffa koda daya ta kasance
dinari daya in siya, amma ban samu ba. Na
kwana cikin wannan dare ina mai tunani.
Da gari ya waye na kara fita cigiyar inda zan
sami tuffa. Na hadu da mai sayar da 'ya'yan
itace, na tambaye shi tuffa, ya ce mini, tuffa ta yi
karanci yanzu, ba lokacinta ba ne, ba a
samunta ko'ina sai a cikin gonar Sarkin Musulmi
ta Basara.
Da na dawo gida, na shiga wurin matata, sonta
ya daukaka a gare ni. Na yi nufin tafiya Basara
wajen neman tuffa, daga nan Bagadada kuwa
tafiyar kwana goma sha biyar ne, amma ban
gaya wa matata ba, sai dai na fada mata zanyi
tafiya ta kwana talatin. Muka yi bankwana da
ita.
Na shirya na kama hanya, ina ta tafiya ba dare
ba rana, har kwana goma sha biyar, na isa
Basara. Na tafi wurin
mai kula da gonar Sarkin Musulmi, na siyo tuffa
guda uku, kowace daya a kan dinari daya. Na
juyo zuwa gida, na yi wasu kwanaki goma sha
biyar kafin na iso.
Bayan na iso gida, na shiga dakin matata na ba
ta tuffar guda uku, na fada mata inda na samo
su, da kuma kudin da na siyo su. Ba ta nuna
alamun farin ciki ba ko kadan da wannan kokari
da na yi. Ta karba ta ajiye su yashe a kasa.
Bayan 'yan kwanaki kadan ta warke sarai daga
rashin lafiyarta.
Ran nan na fita kasuwa, ina zaune a cikin
rumfata ina cininki. Daga nesa, sai na hango
wani bakin mutum a cikin rana, da tuffa a
hannunsa. Da ya zo ta
gaban rumfata zai wuce, sai na ce a zuciyata,
ina wannan bakin mutum ya sami tuffa a cikin
wannan gari wanda na zagaye ko'ina ban samu
ba? Bari in tafi ya fada mini inda ya siyo, idan na
tashi saye nan gaba ba sai na sha wahala ba.
Da ya zo dab da rumfata, sai na yi sauri na fito
na tare shi, na ce abokina ina ka siyo wadannan
tuffa, idan na tashi siya in tafi can in siyo?
Sai bakin mutumin nan ya yi dariya ya ce mini,
"Masoyiyata abar begena ce ta kai mini su har
gida. Ta ce mini lokacin da ba ta da lafiya,
sakaran mijinta ya tafi har Basara ya siyo mata
su, guda ukun nan a kan kudi dinari uku."
Lokacin da na ji zancen wannan bakin mutum,
ya Sarkin Musulmi, duniya ta yi mini baki kirin,
na ji babu wanda na tsana a raina kamar
wannan mutum da matata, maciya amana.
Amma ita ce mai babban laifi tunda har gida
take isko shi. Nan take na rufe shagona, na nufi
gida a fusace.
Da zuwana na tambayi matata, "Ina tuffar da na
siyo miki guda uku?" Ta ce da ni, ba ta sani ba,
ba ta kuma san inda suke ba. Tun daga nan
na gasgata zancen
bakin mutumin nan, bana tsaya na yi wani
dogon bincike ba. Idanuna suka rufe da
tsananin fushi da kiyayya.
Na tashi na dauki wuka, na hau bisa ga kirjinta,
na yanka ta da wukar. Na yanke kanta da
gabobinta, na yi mata gunduwa-gunduwa. Na yi
gaggawa na rufe ta da mayafi, na kunsheta a
cikin shimfida, na sa ta cikin kubba na rufe, na
sa kubbar a cikin sunduki. Da dare ya yi na
dauki sundukin na dora shi a kan alfadarata, na
tafi na jefa shi a cikin Bahrul Dujillati, babu
wanda ya sani, domin lokacin 'ya'yanmu sun tafi
gidan baffana.
Bayan na jefa sundukin a cikin kogi na dawo
gida,sai na tarar da a cikin 'ya'yana daya ya
dawo gida yana kuka. Na tabbata bai san abin
da na yi wa mahaifiyarsa ba, sai na tambaye shi, me yake yi wa
kuka? Ya ce mini, "Na dauki tuffar da ka siyo wa
mama, lokacin da ta shiga wanka, na fita ina
wasa da su a hannuna zan je gidan kaka, sai na
hadu da wani bakin mutum ya kwace su daga
hannuna ya ce ina na same su? Na fada masa
babana ne ya siyo wa mamata su lokacin da ba
ta da lafiya, duk daya a kan dinari daya, kuma
har Basara ya tafi neman su saboda sonta da
yake yi. Ya mangare ni, ya tafi da su. Ina jin
tsoro kada mama ta gane ni ne na dauke su ta
buge ni."
Yayin da na ji zancen dana, sai na tabbata lalle
bakin mutumin nan shi ne ya yanka zancen
karya game da matata. Na kashe ta a kan
zalunci, ba tare da ta yi mini wani laifi ba. Na yi
kuka, kuka mai yawa.
Ina cikin wannan hali, sai ga wannan tsoho,
mahaifin matata, ya rako sauran 'ya'yanmu. Na
labarta masa ga abin da ya kasance ga 'yarsa,
ya zauna a gefena yana kuka, ba mu gushe ba
muna kuka har tsakar dare. Muka yi zaman
makoki a wannan dare.
Bayan kwana hudu sai muka ji ana shelar
ratayewar Waziri Ja'afaru da 'yan uwansa, shi
ne muka zo, sai muka samu wannan labari. Ina
hada ka da girman Allah, ya Halifa, ka gaggauta
sa a rataye ni, domin biyan kisasi ga matata, ni
ina jin tsoron yin shari'a da ita ranar lahira."
Koda saurayi ya gama labarinsa, gaba dayan
jama'ar dake wurin idonsu ya cika da hawaye,
hatta Halifa sai da ya zubar da hawaye. Halifa
ya ce, "Na rantse da Allah ba ni kashe kowa face wannan bakin
mutum, funafuki, annamimi."
Halifa ya juya ga Ja'afaru ya ce, "Na ba ka
kwana uku, ka kawo mini bakin mutumin nan,
idan ba haka ba zan rataye ka, da 'yan uwanka
mutum arba'in." Jama'a duk suka watse.
Waziri Ja'afaru ya koma gida yana mai bakin
ciki, yana cewa a ransa, "Ta yaya zan iya nemo
wannan bakin mutum cikin dubban mutanen da
ke wannan birni? Na rantse da Allah ba zan fita
daga gida na neman kowa ba, Allah da ya kare ni daga halaka yanzu
shi nake roko ya kara yi mini mafita." Ya yi
zamansa gida har tsawon kwana uku bai fita
ba.

Zanci gaba03. HIKAYAR TUFFA UKU (TALE OF THE THREE
APPLES)

Koda saurayi ya gama labarinsa, gaba dayan jama'ar
dake wurin idonsu ya cika da hawaye, hatta Halifa
sai da ya zubar da hawaye. Halifa ya ce, "Na rantse
da Allah ba ni kashe kowa face wannan bakin
mutum, funafuki, annamimi."
Halifa ya juya ga Ja'afaru ya ce, "Na ba ka kwana
uku, ka kawo mini bakin mutumin nan, idan ba haka
ba zan rataye ka, da 'yan uwanka mutum arba'in."
Jama'a duk suka watse.
Waziri Ja'afaru ya koma gida yana mai bakin ciki,
yana cewa a ransa, "

Ta yaya zan iya nemo wannan
bakin mutum cikin dubban mutanen da ke wannan
birni? Na rantse da Allah ba zan fita daga gida na
neman kowa ba, Allah da ya kare ni daga halaka
yanzu shi nake roko ya kara yi mini mafita." Ya yi
zamansa gida har tsawon kwana uku bai fita ba.
A cikin kwana na hudu, Waziri ya kira alkalai da
shaidu, ya yi wasiyya ga 'ya'yansa da iyalansa, ya yi
bankwana da su, yana kuka suna kuka. Daga nan
sai ga manzon Halifa ya zo da sakon Halifa na
nemansa yanzu-yanzu. Manzon ya ce da shi, "

Halifa
ya yi fushi mai tsanani, kuma ya rantse wannan rana
ba za ta wuce ba face kana ratayayye, kai da 'yan
uwanka arba'in, muddin ba ka zo masa da bakin
mutumin nan ba."
Yayin da Waziri ya ji wannan sako na manzon Halifa,
sai ya sake fashewa da kuka, 'ya'yansa ma suka
fashe da kuka. Da ya gama bankwana da su, sai ya
gabata a gaban 'yarsa karama, 'yar autarsa mai
kimanin shekaru shida, domin ya yi bankwana da
ita. Ya kasance Waziri na son 'yar nan tasa fiye da
sauran 'ya'yansa. Ya jawo ta zuwa ga kirjinsa domin
ya rungume ta, sai ya ji wani abu mai tudu a cikin
aljihun rigarta. Ya sa hannu cikin aljihunta ya fito da
abin da ke ciki, sai ya ga tuffa ce.
Nan take kamannun Waziri suka canja, ya tambayi
'yarsa ina ta sami tuffa? Ta ce da shi, "Bakin bawan
nan ne namu Raihanu ya ba ni ita tun kwana hudu
da suka wuce. Tuffa uku ce, na cinye biyu saura
wannan daya, ita ma yau zan cinye ta."

Lokacin da Waziri Ja'afaru ya ji ambaton bakin bawa
da tuffa uku, ya yi farin ciki ya ce, "Ya mai kusata
farin ciki, ubangijin sammai da kassai, ina kara
godiya a gare ka, da ka kubutar da ni da 'yan uwana
daga halaka kashi na biyu." Ya yi umurni da a kira
masa bawa Raihanu.
Da aka hallaro da bawa Raihanu, Ja'afaru ya
tambaye shi ina ya sami tuffa uku? Bawa ya ce, "Ya
shugabana, tun kwana takwas da suka wuce, ina
tafiya cikin wani kwararo na wannan birni, na ga
wani yaro yana wasa da tuffa guda uku, na kwace su
a hannunsa, bayan ya fada mini cewa na
mahaifiyarsa ne da mahaifinsa ya tafi har birnin
Basara ya siyo mata, lokacin da ba ta da lafiya, ya
fada mini duk daya an siyo ta a kan dinari daya. Na
tafi suna rike a hannuna, har na shiga cikin kasuwa.
Wani saurayi ya gan su a hannuna ya tambaye ni
inda na same su, ni kuwa na yi masa karya na ce,
masoyiyata ce ta kai mini su har gida, na tafi ina
masa dariya. Bayan kwana hudu sai shugabata ta
gan su a hannuna ta ce tana so, ni kuwa na ba ta
su duka."

Yayin da Ja'afaru ya ji wannan labari na bawa
Raihanu, ya yi al'ajabi domin duk wannan fitina ta
kashe yarinya da aka saka cikin sunduki, aka jefa a
kogi, ta faru ta sanadiyyar wannan bakin bawa nasa.
Ya yi umurni da a daure bawa. Ya kara yi wa Allah
godiya da ya kubutar da shi. Sannan ya rera
wadannan baitoci, ya ce:
"Wanda masifarsa ta kasance manisanciya,
Rai ba ya da ikon sa shi fansarta,
Kai mutum za ka sami bayi da yawa,
Amma ranka ba ka samun waninsa."
Ja'afaru ya umurci wasu bayinsa da manzon Halifa
su tafi da bawa Raihanu wurin Sarkin Musulmi,

yana
isowa yanzu. Suka tafi da bakin bawa yana daurarre.
Amma 'yar Ja'afaru da ba ta san abin da ke faruwa
ba, da ta ga an fita da bawa Raihanu a daure, sai ta
fashe da kuka tana cewa a dawo musu da bawansu.
Ja'afaru ya lallashe ta, ta yi shiru, ya yi mata
alkawarin za a dawo da shi.
Bayan Waziri Ja'afaru ya shirya, sai ya nufi fadar
Halifa. Da ya isa, ya kwashe duk abin da ya faru ya
fadawa Halifa. Halifa ya sa aka kira masa saurayi
wanda ya kashe yarinya, da dattijo uban yarinya.
Bayan sun zauna ya nuna wa saurayi bakin bawa ya
ce, "Wannan shi ne bakin mutumin da ka gani da
tuffa a hannunsa?" Saurayi ya ce shakka babu, shi
ne.

Waziri ya bayyana musu yadda aka sami tuffa a
hannu 'yarsa wadda ita kuma ta ce bawa Raihanu ne
ya ba ta su. Shi kuwa bawa Raihanu sai a lokacin
ma ya san abin da ke faruwa na kisan yarinya
sanadiyyar karyar da ya yi.
Ya durkusa a gaban saurayi da tsoho, yana kuka
yana tumurmuza fuskarsa a kasa, yana ba su hakuri
a kan karyar da ya yi wa saurayi, yana cewa, "

Ya
shugabana, ka gafarce ni, wallahi ban fada maka
waccan maganar ba domin in hada ka fada da
matarka, ban taba sanin ta ba, kai ma ban san ka
ba, sai ranar da muka hadu da kai a kasuwa.
Wannan maganar na fade ta ne kawai domin in yi
dariya. Ina neman gafararku."
Halifa ya yi mamaki a kan wannan al'amari da ya
faru matukar mamaki. Ya ce, "Da dai ban taba jin
labari mai al'ajabi da mamaki ba kamar wannan."

Ya
juya wurin bawa ya ce babu makawa sai an rataye
ka a kan wannan karya da ka yi." Sannan ya ba da
umurni a rubuta wannan labari a ajiye shi a dakin
ajiye littattafai domin na baya su karanta su karu da
darussan da ke ciki.
Waziri Ja'afaru ya ce, "

Hakika wannan labari abin
mamaki ne, amma ko kusa, ko alama, bai kai labarin
Waziri Nuruddin da dan uwansa Shamsuddin ban
mamaki da tausayi ba. Amma ba zan fada wa Halifa
wannan labari ba sai idan ya yi alkawri labarin zai
zama fansar rayuwar wannan bawa nawa."

Halifa ya amince da haka, amma da sharadin idan
labarin bai kai wannan ban mamaki ba, to za a
kashe bawa Raihanu. Waziri Ja'afaru ya yarda da
haka. Ya gyara zama ya fara bayar da labarin Waziri
Nuruddin da dan uwansa Shamsuddin.

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment