Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyu zuwa uku kamar yadda ya jero
min tambayoyi.” Khalifa ya ce, “an ba ki
iznin.” Ta dubi malamin ta ce, “ina so ka
amsa min tambayoyina da hanzari idan ka
kasance malami.” Ya ce, “yi tambayar ki, a
shirye nake.”
Ta ce da shi “menene kibiyoyin addini.”
Ya amsa mata da cewa “kibiyoyin addini su
goma ne; na farko kalmar shahada ita ce
addini, na biyu sallah ita ce, abinci. Na uku
zakka da sadaka domin samun tsarki. Na
hud’u azumi shi ne garkuwa. Na biyar aikin
hajji shi ne shari’a. Na shida jihadi a bisa
tafarkin Allah, na bakwai da na takwas su ne
umarni da kyakkyawa da hani da mummuna,
wad’annan su ne darajar d’an Adam. Na tara
jama’a su ne alheri. Na goma neman ilmi shi
ne tafarkin abin godewa.”
Ta ce, “ka fad’i daidai. Yanzu ina da wata
tambayar, “menene al’amuran addini?”

ZANCI GABA05 HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGAR SA TAWADDUD

Ya ce “al’amuran addini guda hud’u ne;
ingancin k’uduri da gaskiyar nufi da cika
alk’awari da nisantar iyaka.” Ta ce haka
batun ya ke, ga wata tambayar ta k’arshe,
idan ba ka amsa ba zan tub’e rigar ka.” Ya
ce, “fad’i ko menene.”
Ta ce “menene rassan Musulunci?” Ya yi
shiru bai amsa ba har lokaci ya yi nisa.
Kuyanga ta ce, “tub’e min rigarka tunda ba
ka amsa ba.” Khalifa ya ce, “amsa mu ji su
ya kuyanga, ni zan karb’e tufafin daga gare
shi na ba ki.”
Sai ta ce da su “rassan Musulunci su ashirin
da biyu ne, ga su: rik’o da littafin Allah
mad’aukakin Sarki, koyi da manzanninsa,
tsira da aminci ya tabbata a gare su. Kiyaye
aikata alfasha, cin abu daga halali. Nisantar
abin da yake haramun, da mayar da kayan
da aka karb’a cikin zalunci. Tuba, da neman
sanin ilmin addini da shari’a da k’aunar
abokan arziki da bin mutanen kirki da ban
gaskiya ga annabawa da jin tsoron jinkiri da
zumunci da shirin guzurin barin wannan
rayuwa da yafewa a lokacin da ake da ikon
d’aukar fansa, da hak’uri yayin ciwo da
hak’uri a lokacin jarrabawa da neman sanin
Allah mad’aukakin Sarki da abin da
Manzonsa ya sanar da mu da gujewa Iblis
la’antacce da jayayya da rai bisa sab’awa
mahalicci da kwad’aituwa bisa bautar Allah
Makad’aici.”
Yayin da Khalifa ya ji jawabinta sai ya umarci
malamin da ya cire alkyabbarsa da
rawaninsa da sandarsa ya fita yana mai jin
kunya gare ta, ya zama abin dariya ga
Khalifa.
Daga nan wani mutum daga malaman ya
mik’e tsaye ya ce, “ya ke kuyanga ga wasu
tambayoyina gare ki.” Ta ce, “ina jin ka.”
“Menene sharad’in cinikin bashi?”
Ta ce “tamanin kayan ya zama sananne,
kayan su zama sanannu kuma lokacin da za
a biya ma ya zama sannanne.”
“Menene sharud’d’an cin abinci?”
“Sakankancewa Allah mai girma da d’aukaka
shi ne ya azurta mu da ci da sha. Don haka
wajibi ne mu gode masa bisa ga haka.”
“Menene godiya?”
“Komawar bawa zuwa ga Allah da abin da
Allah ya yi a gare shi zuwa ga Allah da abin
da ya halatta domin sa.”
“Menene sunnonin cin abinci?”
“Wanke dukkan hannaye yayin farawa da
ambaton bismillah kafin a soma cin abincin.
Da zama bisa sashen hagu da cin abincin da
hannu da yatsu uku. Da kuma cin abincin da
yake daidai da mutum. Kada a ci abinci fiye
da k’ima.”
“Menene ladubban cin abinci?”
“Yankar loma k’arama da cin gabanka da
k’aranta kallon abokin zamanka.”
“Wannan haka ya ke.” In ji malami mai
tambaya.
A nan asuba ta riski Shaharzad, ta katse
zancenta mai dad'in saurare.
DARE NA 444
A dare na d'ari hud’u da arba’in da hud’u,
Shaharzad ta ce, na samu labari ya kai
wannan hamshak’in Sarki, yayin da kuyanga
ta amsa tambayar malamin game da
ladaban cin abinci sai ya ce, “kin kyauta,
haka yake.” Sannan ya ce da ita, “fad’a min
game da k’udurce – k’udurcen zuci.”
“K’udurorin su uku ne da kishiyoyinsu guda
uku; Na farko k’udurin imani kishiyarsa ita ce
jayayya. Na biyu k’udurin sunna, kishiya tasa
ita ce bidi’a da dangoginta. Na uku k’udurin
biyayya, kishiyarsa kusata da aikata sab’o.”
“Haka yake. Fad’a min game da sharad’an
alwalla.”
“Sharad’an su ne, Musulunci, rarrabewa
tsakanin abu mai kyau da mara kyau da
tsarki da tsarkakken ruwa da gusar da
abubuwan da ba na addini ba.”
“Menene imani?”
“Imani shi ne, yarda da Allah da mala’ikunsa
da manzanninsa da littafansa da ranar lahira
da kuma yarda da k’addara ta alheri da ta
sharri.”
“Menene abubuwa uku da ke kyautata
abubuwa uku?”
“Safiyanus Sauri ya fad’i cewa abubuwa uku
masu gusar abubuwa uku su ne;
takatsantsan ga waliyai yana kyautata
rayuwar lahira, takatsantsan ga sarakuna
yana kyautata rayuwar duniya, takatsantsan
a wajen b’arnar kud’i na kyautata dukiya.”
“Menene mabud’an sama, kuma k’ofofi nawa
gare ta?”
“Allah mad’aukakin Sarki ya fad’i cewa, ‘wa
futhatus sama’u fa kanat abwaba.’ Ma’ana
‘Kuma, aka bud’e sama, sai ta kasance
k’ofofi.’ Babu wanda ya san adadin k’ofofin
sama sai Allah wanda ya halicce su, haka
nan babu wani d’an Adam face yana da
k’ofofi biyu a sama, d’aya wadda arzikinsa ke
saukowa, d’aya inda ayyukansa ke hawa.
K’ofa ta farko ba ta rufewa sai ranar da ya
bar duniya, k’ofar aikinsa kuma ba ta rufewa
sai ranar da aka tsayar da shi gaban Allah.
Domin ko da mutum ya mutu akwai
ayyukansa da ke samun sa walau na alheri
ko na sharri.”
“Haka ya ke,” in ji malami mai tambaya, ya ci
gaba da cewa, “fad’a min game da wani abu
da rabin wani abu da kuma abin da babu
shi.”
Ta ce da shi “wani abu shi ne Musulunci,
rabin abu shi ne Munafunci, abin da babu
kuma shi ne kafirci.”
“Fad’a min yadda zuciyoyi suke.”
Ta ce “akwai cikakkiyar zuciya da zuciya
maras lafiya da zuciya mai zargi da zuciya
mai alk’awari da kuma zuciya mai haske.
Cikakkiyar zuciya ita ce ta Annabi Ibrahima
mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi. Zuciya maras lafiya ita ce zuciyar kafirai,
zuciya mai mai zargi ita ce irin zuciyar
waliyan Allah, zuciya mai alk’awari kuwa ita
ce misalin zuciyar shugabanmu Annabi
Muhammadu tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi da ta mabiyansa, sannan
zuciya mai haske ita ce misalin zuciyar
malamai. Haka nan zuciyar malamai ta rabu
zuwa gida uku; akwai zuciyar da ke k’aunar
wannan duniyar da abin da ke cikin ta. Da
zuciyar da ta rataya ga zuwa rayuwar gaba
watau lahira. Da zuciyar da ta rataya wajen
son Ubangiji mahaliccin Sarki. Haka nan an
ce zuciya ita kanta ta kasu zuwa gida uku;
wadda ta mutu irin ta kafirai da wadda babu
ita irin ta munafukai da wadda take tsaye cif
babu rawa, misalin ta muminai.
Sannan an ce tsayayyiyar zuciya ta rabu
kaso uku; zuciyar da take cike da haske da
imani, da zuciyar da ke raunata da tsoron
karkacewa. Sai zuciyar da take jin tsoron
kub’ucewar rabo.

ZANCI GABA06. HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGARSA TAWADDUD

malami mai tambaya na biyu ya ce, “kin kyauta ya ke
kuyanga.” Ya koma ya zauna.
Kuyanga ta dubi Sarkin Musulmi ta ce, “ya
Sarkin Musulmi, ya yi min tambayoyi da
dama, yanzu zan yi masa nawa ‘yan
tambayoyi idan ya amsa shi kenan, idan
kuma bai amsa ba zan amshe alkyabbarsa.”
Khalifa ya ce, “wannan daidai ne.” Ta juya ga
malamin ta ce, “me za ka fad’a game da
imani?” Ya mik’e tsaye bisa dugadugansa
sannan ya ce, “imani shi ne mik’a wuya a
bayyane bisa ga abin da Annabi mai tsira da
amincin Allah su tabbata gare shi ya zo da
shi. Imanin mutum ba ya cika sai ya tabbata
a bisa halaye biyar, su ne; dogaro ga Allah,
mik’a al’amari ga Allah, rashin mamaki game
da sha’anin Allah da yarda da hukuncin
Allah, sannan al’amarunsa duka su zama
domin Allah.”
Ta ce, “haka zancen ya ke. To ina so ka fad’a
min menene farillar farillai da farillar cikin
farkon kowace farilla da farillar da kowace
farilla ta dogara gare ta da farillar da ke
dulmiya kowace farilla da kuma sunna mai
shiga cikin farilla da kuma sunnar da farilla
ba ta cika sai da ita.” Nan take ya d’auki
lokaci bai ce komi ba, ya yi shiru na wani
lokaci. Ganin bai tanka ba sai Khalifa ya
umarce ta da ta fassara su, sannan in ya
kasa zai sa ya tub’e alkyabbarsa, ya ba ta.
Ta ce, “ya malami, ka sani farillar dukkan
farillaiita ce tabbatar sanin Allah mad’aukakin
Sarki, amma farillan farkon dukkan farillai ita
ce shaidawa babu abin bautawa da gaskiya
sai Allah, kuma Muhammadu manzon Allah
ne. Farillar da kowace farilla ke buk’ata ita ce
alwalla. Farillar da ke dulmiya kowace farilla,
ita ce wankan janaba. Ita kuwa sunna mai
shiga cikin farilla ita ce tsettsefe yatsu da
gemu mai kauri. Ita kuwa sunna wadda farilla
ke cika da ita, ita ce aske gashin gaba da
fisge gashin hammata da kaciya.” A nan
gajiyawar malamin ta bayyana, ya tsaya
gaban Sarkin Musulmi ya ce, “Allah ya sani
ya Sarkin Musulmi cewa wannan kuyanga ta
kasance mafi sanin ilmin furu’a da waninta
fiye da ni.” Ya juya ga barin ta yana mai
k’ask’antacce. Ta juya ga ragowar malaman
da ke zaune ta ce, “ya ku manyan malamai, a
cikin ku akwai gwani a kan rubutu da karatun
Alk’ur’ani mai girma, wanda ya nak’alci
ruwaya bakwai da nahawunta da lugga da
furuci?” Wani malami ya mik’e tsaye ya dube
ta ya ce, “yalla ke kin karanta littafin Allah
mai girma, kin haddace surorinsa, kin san
yawan ayoyinsa da juzu’o’insa da shafaffun
ayoyi da wad’anda aka shafe su da su da
k’ira’o’i da surorin Makka da na Madina? Kin
san tafsirinsa da musabbaban saukar ayoyi?”
Ta amsa, “na’am.” Ya ce, “nawa ne adadin
surorinsa da yawan kurinsa da yawan
ayoyinsa da yawan kalmominsa da yawa
haruffansa? Nawa ne adadin ayoyin sujjada
da yawan annabawan da aka ambaci sunan
su a ciki? Nawa ne adadin surorin da aka
saukar a Makka da yawan wad’anda aka
saukar a Madina? Tsuntsaye nawa aka
ambata a cikin sa? “
Ta ce, “ya shugabana ka sani adadin surorin
Alk’urani mai girma guda d’ari da goma sha
hud’u ne. Saba’in daga cikinsu an saukar da
su a Makka, arba’in da hud’u kuma an
saukar da su a Madina. A cikin sa akwai kuri
guda d’ari shida ashirin da d’aya. Akwai
ayoyi dubu shida da d’ari uku da talatin da
shida, sannan ya k’unshi kalmomi dubu
saba’in da tara da d’ari hud’u da talatin da
tara. Haka nan ya k’unshi haruffa dubu d’ari
uku da ashirin da uku da d’ari shida da
saba’in. Game da wanda ya karanta kuwa,
duk harafi za a ba shi lada goma. Ayoyin
sujjada su goma sha hud’u ne.”
A nan asuba ta riski Shaharzad, ta katse
zancenta mai dad'in saurare.
DARE NA 446
A dare na d'ari hud’u da arba’in da shida,
Shaharzad ta ce, na samu labari ya kai
wannan hamshak’in Sarki, yayin da malami
gwanin Alk’ur’ani ya tambayi kuyanga sai ta
cigaba da ba shi amsa ta ce, “amma game
da annabawan da Allah ya ambata a cikin
Alk’urani mai girma su ashirin da biyar ne. Su
ne; Adamu, Nuhu, Ibrahima, Isma’ila, Ishak’a,
Yakubu, Yusufu, Lud’u, Yunusa, Salihu, Hudu,
Shu’aibu, Dawuda, Sulaimanu, Zulk’ifil, Idrisu,
Iliya, Alyasa’u, Yahaya, Zakariyya’u, Ayuba,
Musa, Haruna, Isah da Muhammadu tsira da
amincin Allah ya tabbata a gare su duka!
Amma tsuntsaye da aka ambaci sunansu a
littafin Allah su tara ne; sauro da k’udan
zuma da k’uda da tururuwa da hudahuda da
hankaka da fara da alallaka da tsuntsun
Annabi Isah Amincin Allah ya tabbata gare
shi, watau jemage.” Malami ya ce, “kin
kyauta, fad’a min wacece mafificiyar sura a
K’ur’ani?”
Ta ce “suratul Bak’ara.”
“Wacce aya ce ma fi girma a cikin ta?”
Ta ce da shi “Ayatul kursiyu, ta kuma k’unshi
kalmomi hamsin, kowace kalma tana d’auke
da albarka hamsin.”
“Wace aya ce take d’auke da ayoyi tara a
cikin ta?”
Ta ce “wurin fad’in Allah mad’aukakin Sarki
ke cewa, ‘Inna fil khalk’is samawati wal
ardhi…’ har zuwa k’arshen ayar.”
“Wace aya ce ma fi adalci?”
Ta ce “wajen fad’insa Mad’aukakin Sarki,
‘Innallaha ya’amuru bil ma’arufi. Wa yanha
anil fahasha’i wal munkari wal bagyi…”
“Wace aya ce ma fi kwad’aitarwa?”
Ta ce “tana cikin suratul Ma’arij, inda Allah ke
cewa, “A yad’ ma’u kullun ri’in minhum an
yad khala Jannata na’im.”
“Wace aya ce mafi sa wa mutum ya yi
tsammani?”
Ta ce “ita ce wadda ke cewa, ‘K’ul ya
ibadiyallazina asrafu ala anfusihim, la
tak’nad’u min rahmatillah. Innallah yagfuruz
zunuba jami’a. Innahu huwal gafurur rahim.
“Ke da wace k’ira’a kike karatu?”
Ta amsa “ina karatuna da irin yadda ‘yan
aljanna suke yi bisa ruwayar Nafi’u.”
“A wace aya ce aka ambaci k’arya bisa ga
annabawa?”
Ta ce “a cikin Suratul Yusuf, inda Allah ke
cewa, “wa ja’u ala k’amisihi ba damin kazib.”
“A wace aya aka gaskata kafirai a cikin ta?”
Ta ce “fad’insa mad’aukakin Sarki, “wa
qalatil yahudu laisatil Nasara ala shai’in
waqalatil Nasara laisatil Yahudu ala shai’in
wa hum yatlunal kitab.’ Dukkansu sun fad’i
gaskiya.”
“Wace aya ce Allah ya fad’e ta ga kansa?”
Ta amsa “inda yake cewa, “wa ma k’alak’tul
jinna wal insa illa li ya’abudini.”
“A wace aya ce Mala’iku ke magana?”
Ta ce da shi “ayar da ke cewa, ‘wa nahnu
nusabbihu bi hamdika wa nu k’addisu laka.”
Cikin suratul Bak’ara.”

ZANCI GABA INSHA ALLAH07 HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGAR SA TAWADDUD

Me za ki fad’a game da neman tsari a kan
shaid’an yasasshe da abin da ya zo a cikin
ta.” Ta ce, “neman tsari daga shaid’an wajibi
ne, Allah ya yi umarni da haka a lokacin da
za a soma karatun K’ur’ani. Akwai dalili
game da haka wajen fad’arsa mad’aukakin
sarki, “fa iza k’ara’atal k’ur’ana fas ta iz
billahi minasshaid’anir rajim.”
“Fad’a min yadda lafazin neman tsarin yake.
Kashi nawa ne? Akwai sab’ani a ciki?”
Ta ce “wasu na cewa ‘A’uzu billahis sami’ul
alim, minasshaid’anir rajim. Wasu kuma na
cewa ‘A’uzu billahis zulquwwa
minasshaid’anir rajim. Amma duka abin da
ya fi shi ne abin da Alk’ur’anin ya yi furuci da
shi watau, ‘A’uzu billahi minasshaid’anir
rajim. Manzon Allah mai tsira da amincin
Allah ya k’ara tabbata a gare shi ya kasance
idan zai fara karatu yana ambaton haka.
Kuma an rawaito daga Nafi’u, ya karb’o daga
mahaifinsa cewa mai tsira da amincin Allah
ya k’ara tabbata a gare shi ya kasance idan
ya tashi sallah cikin dare yana cewa, ‘Allahu
Akbar Kabiran Subhanallahi bukratan wa
asila. Daga nan sai ya ce, ‘A’uzu billahi
minasshaid’anir rajim min hamazihi wa nafa.
An rawaito daga d’an Abbas Allah ya yarda
da shi ya ce, “farkon abin da Mala’ika Jibrilu
ya sauko da shi bisa ga Annabi shi ne neman
tsari, sannan ya ce fad’a masa bismillah,
sannan ya fad’a masa ya yi karatu da sunan
Allah wanda ya halicce shi ya bai wa d’an
Adam sani.”
Yayin da gwani ya ji zancenta ya yi mamakin
lafazinta da fasaharta da ilminta da fifikonta.
Ya ce da ita, “ya ke kuyanga, me za ki ce
akan fad’ar Allah mad’aukakin sarki,
Bismillahir rahmanir rahim?” Ta ce, “wannan
aya ce a cikin K’ur’ani mai girma cikin suratul
Namli. Kuma ana sanya ta a farkon kowace
sura, amma akwai sab’ani tsakanin malamai
cewa ita aya ce a kowace sura ko a’a.”
Ya ce, “kin kyauta.”

kuyanga ta cigaba
da ba wa gangaran game da sab’anin
malamai a kan Basmala. Ya ce da ita, “kin
kyauta, fad’a min me ya sa ba a rubuta
basmala a farkon suratut Tauba?”
Ta ce “yayin da surar ta sauko bisa
sakankancewar alk’awarin da ke tsakanin
Annabi Muhammadu mai tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi da kafirai, sai ya
gabatar da ita ga Sayyadina Ali d’an Abi
D’alib, Allah ya girmama fuskarsa. Ya tafi
zuwa Makka ya karanta ta gare su a ranar
salla, amma bai karanta masa da bismillah
ba.”
“Fad’a min falalar Basmala.”
Ta ce “an fad’i cewa Manzon Allah ya ce,
babu wani abu da za a ambaci basmala a
kansa face ya yi albarka. Haka nan an
rawaito hadisi daga gare shi cewa, ‘na rantse
da ubangijin d’aukaka ba a ambaton
basmalah a kan mara lafiya sai ya samu
lafiya.’ Haka nan an ce yayin da Allah
mad’aukakin Sarki ya halicci gadon al’arshi
sai ya raurawa, raurawa mai girma, sai
ubangiji ya rubuta Basmala a jikinsa, sai ya
daina raurawar. Yayin da aka saukar da ita
sai ya ce, “na samu aminci daga abubuwa
uku; girgizar k’asa da shafe k’asa da kuma
ambaliyar ruwa.’ Darajarta mai girma ce,
albarkarta na da yawa, zance a kanta zai yi
tsawo idan aka fad’ad’a.
Ta ce an fad’a daga Ma’aiki cewa za a zo da
wani mutum a ranar lahira idan aka yi masa
hisabi sai a yi umarnin a kai shi wuta. Sai
mutumin ya yi k’ara wajen Allah ya ce, “yaya
za a yi min haka?” sai Allah ya ce, “don me
ka ce haka?” sai mutumin ya ce, “Ya
ubangijina ka ambaci kanka Arrahmanu
kuma ka ambaci kanka Arrahimu amma ga
shi za ka sa a kai ni wuta.” Sai Allah
mad’aukakin sarki ya ce, “ni na ambaci
zatina da Arrahamanu, kuma Arrahimu, ku kai
wannan bawan nawa zuwa aljanna, domin
rahamata domin ni ne mai yawan rahma, mai
yawan jink’ai.”
“Haka yake, fad’a min menene asalin
Basmala?”
Ta ce “yayin da Allah ya saukar da Alk’ur’ani
an rubuta shi da sunan Allah mad’aukakin
Sarki. Yayin da Allah ya saukar da cewa
“kiraye ni Allahu ko Arrahmanu duk yadda
kuka kira suna da martaba, kyawawan sun
tabbata gare shi.” Sannan ya ce, “ku rubuta
su da cewa mun fara neman albarka da
sunan Allah, magamin kyauta a duniya.”
Yayin da aka saukar da cewa, ‘Ubangijinku
makad’aici ne, babu wani Sarki sai shi,
magamin kyauta a duniya mai keb’ab’b’en jin
k’ai a lahira.” Sai suka rubuta, ‘da sunan
Allah Mai Rahma Mai Jin k’ai.’” Yayin da
gwani ya ji kalamanta sai ya sunkuyar da
kansa yana cewa a ransa, ‘wannan shi ne
babban abin mamaki! Ta yaya wannan
kuyanga ta san asalin Basmala? Wallahi sai
na hilace ta, na d’aukaka bisa kan ta, na
rinjaye ta.’ Sannan ya d’ago kai ya dube ta
ya ce, “shin Allah ya saukar da Alk’ur’ani
gaba d’aya ne ko daban-daban?”
Ta ce, “Mala’ika Jibrila amintaccen Allah,
Allah ya k’ara yarda a gare shi, shi ya sauko
da shi daga wajen Ubangijin talikkai bisa ga
Manzonsa, shugaban ma’aika, cikamakin
annabawa, Annabi Muhammadu, tsira da
aminci su tabbata a gare shi. Allah ya ba shi
umarni da hani da wa’adi da tsawatarwa da
labarai da buga misali cikin shekara ashirin
da uku da ayoyi mabambanta bisa
gwargwadon aukuwarsu.”
Ya ce, “kin kyauta, fad’a min farkon surar da
ta sauko bisa ga manzon Allah.”
Ta ce “Abdullahi d’an Abbas ya fad’i cewa
surar farko da ta soma sauka ita ce suratul
Alak’, Jabiru bin Abdullahi kuwa ya ce, suratul
Mudassir ce ta soma sauka, sannan aka rik’a
saukar da ayoyinsu a mabambantan lokuta.”
“Fad’a min ayar k’arshe da ta sauko.”
Ta ce da shi “k’arshen ayar da ta sauko ita
ce ayar riba. Sannan an ce, “iza ja’a
nasrullahi wal fatah.”

ZANCI GABA INSHA ALLAH08 HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGAR SA TAWADDUD

yayin da kuyanga
ta shaida wa gwani bayani game da ayar k’arshe da ta sauka sai ya ce, “haka yake, ki
fad’a min sunayen sahabban da ke karb’ar ayoyin K’ur’ani a zamanin Annabi.” Ta ce da shi “su hud’u ne; Ubayyu d’an
Ka’ab da Zaidu d’an Sabitu da Abu Ubaida Amir bin Jarrah da Usmanu d’an Affan yardar
Allah ta tabbata a gare su.” “Su waye makarantan da ake karb’ar karatu
daga wajen su?”
Ta k’ara da cewa “ su ma su hud’u ne; akwai
Abdullahi d’an Mas’ud da Ubayyu d’an Ka’ab
da Mu’azu d’an Jabal da Salim d’an
Abdullahi.”
“Menene ma’anar fad’in Allah da yake cewa,
kada ku yanka ga kafaffu?”
Ta amsa masa da cewa“kafaffun nan su ne
gumaka, wad’anda aka kafa ana bauta musu
daga barin Allah makad’aici, muna neman
tsarin Allah bisa ga haka.”
“Menene ma’anar fad’in Allah cewa, ‘ka san
abin da ke cikin raina, ni ban san abin da ke
cikin ranka ba?”
Ta ce “fad’ar Annabi Isah ce lokacin da
mutanensa suka ce shi da mahaifiyarsa su
ne Allah, dalilin haka ya ce da Allah kai ka
san abin da ke raina, ni ban san abin da ke
cikin naka ba, kai ne masanin abubuwan da
ke b’oye.”
“Me za ki ce game da fad’in Allah cewa, ‘Ya
ku wad’anda kuka ba da gaskiya, kada ku
haramta halal, abin da Allah ya halatta a
gare ku.”
Sai ta ce da shi “Malamina Allah ya ji k’ansa
ya fad’a min cewa, wani sahabi Zahhaku ne
ya ce, “akwai wasu mutane musulmi da suka
ce, ba za mu ci abu kaza ba don ba shi da
tsarki, sannan za mu tufata da gashi.” Sai
wannan ayar ta sauka. Amma K’atadata ya
ce an saukar da ayar ne a kan wasu
sahabban ma’aiki mai tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi, wato Aliyu d’an
Ubayyu da Usmanu d’an Mus’ab da wasun
su da suka taru suka ce mu keb’e kanmu, mu
yi tufafin gashi, mu bar cin abinci mai dad’i
sai wannan aya ta sauko.”
“Me za ki ce game da ayar da Allah ke cewa
ya rik’i Ibrahima Badad’i?”
Ta ce da shi “an ce shi Badad’i ne
kasancewar sa masoyin talakawa, a wata
fad’ar kuma aka ce kasancewar sa mai
ciyarwa ne domin Allah. A wata fad’ar kuma
aka ce saboda kasancewar sa mai mik’a
wuya ga Allah, zuciyarsa ba ta yankewa
daga ambaton Allah da tuna ayyukansa.”
Yayin da Gwani gangaran ya ji wannan
jawabin nata tamkar zubar ruwa daga girgije
babu tsayawa, kuma gamsasshe, sai ya
tsaya bisa dugadugansa ya ce, “ya Sarkin
Musulmi wannan kuyanga ta fi ni ilmin k’ira’a
da wanin sa.” Sannan kuyangar ta ce, “ina
neman iznin in yi maka tambaya d’aya, idan
ka kawo jawabinta ni ce fansarka idan ba ka
kawo ba zan cire alkyabbarka.”
Sarkin Musulmi ya ce, “tambaye shi mu ji.”
Ta dubi gangaran ta ce da shi “wace aya ce
ke d’auke da Kaulasan ashirin da uku da
ayar da ke k’unshe da Minjaye goma sha
shida da ayar da ‘ayn’ d’ari da arba’in a cikin
ta?” Gwani ya yi shiru bai amsa ba, tambayar
ta zo masa a bazata. Ta ce, “cire alkyabbar
ka.” Ya cire. Sannan ta juya ga Sarkin
Musulmi ta ce, “ayar da ke k’unshe da
Minjaye goma sha shida tana cikin suratul
Hudu inda Allah ke cewa, “K’ila ya Nuhu ihbid’
bisalamin minna wabakatin. Ayar da ke k’unshe da Kaulasan ashirin da uku kuwa ita
ce ayar bashi da ke cikin suratul Bak’ara,
inda Allah ke cewa, ‘Ya ayyuhal lazina amanu
iza tadayantum bi dainin ila ajalin
musamman faktubuhu... har zuwa k’arshen
aya. Aya kuwa mai d’auke da ‘ayn’ d’ari da arba’in tana cikin suratul A’arafi inda Allah ke
cewa ‘Wakhtara Musa k’awmahu saba’eena
rajulan limee k’atina…” wuraren da babu
kalmar girmama kowa a ciki sun had’a da
surorin ‘iqtarabas sa’atu wan shak’k’al
k’amar’ da surar Arrahmanu da surar
Izawak’a.” Yayin da Gwani gangaran ya ji haka, sai ya cika da mamaki ya ajiye
alkyabbarsa gare ta ya juya yana mai
tsananin damuwa.
sai wani malami, likita masanin cututtuka ya tashi tsaye ya ce da
ita, “tunda kun gama da zancen sanin addini
ga ni na zo da zancen sanin jikin dan Adam.
Fad’a min game da mutum, yaya aka halicce
shi? Jijiyoyi nawa ne gare shi? K’ashi nawa
gare shi? Nawa ne fak’onsa? Wacece jijiyar
farko, kuma me ya sa ambaci dan Adam da
wannan suna na watau Adam?”
Kuyanga ta gyara tsayuwa ta ce, “an ambaci
Adam da wannan suna na Adama saboda
rasuwar da mabambantan kamanninsa. An
ce an halicce shi daga marashiyar k’asa,
watau kenan mabayyaniya. K’irjinsa an yi shi
daga k’asar Ka’aba, kansa kuma daga k’asar
gabas, k’afafunsa daga k’asar yamma. Allah
ya halicci k’ofofi bakwai a kansa wad’anda
suka had’a da k’ofar idanu da hanci da
kunne da baki. Sannan da wasu k’ofofin
zarcewa biyu daga k’asansa; wato dubura da
zakari ko farji.
Idanu an yi su domin gani, kunnuwa domin
jin sauti, hanci domin sunsuna, baki domin
d’and’ano. Allah ya sa harshe domin ya yi
furuci daga abin da ke zuciyar mutum. Ya
halicci Adam bisa abin hayarwa guda hud’u,
su ne; ruwa da k’asa da wuta da iska. Ya
kasance wad’anda suke launin rawaya daga
mutane suna da d’abi’ar wuta, kasancewar
ta mai zafi, busasshiya. Bak’ak’e kuwa suna
da d’abia’ar k’asa, kasancewar ta
busasshiya, mai sanyi. Majina kuwa ta fito ne
daga ruwa kasancewar ta mai sanyi, mai
danshi. Jini kuwa daga iska kasancewar sa
mai zafi, kuma mai danshi.
A jikin dan Adam an halicci jijiyoyi guda d’ari
uku. Sannan akwai k’asusuwa guda d’ari
biyu da arba’in da rayuka uku; na numfashi
da na tafiya da na d’abi’a. Allah ya sanya wa
kowannensu hukunci da irin aikinsa. Haka
kuma Allah ya halicci zuciya ga mutum da
saifa da huhu da hanji guda shida da tumbi
guda uku da hanta da k’oda guda biyu da
mazawari da matsina da k’wak’walwa da
k’ashi da tsoka da fata da kuma sanya masa
hak’ori domin magana da tauna. Haka nan
Allah ya halicci d’an Adam da kafafen ji guda
biyar; ji da gani da sunsuna da d’and’ano da
tab’awa da ji a jiki. Ya sanya zuciya ta zama
a sashin hagu na k’irji, ya saka tumbi gaba
ga zuciya, ya sanya matsarmama kusa da
hanta, wani lokaci tana matsowa kusa da
zuciya, kodayake hanta tana daga gefen
dama, idan ta cika ta zubo bisa ga hanta sai
mutum ya ji tashin zuciya. Allah ya halicci
wasu abubuwan da ba su kai wannan aiki ba
suna k’asa da inda tumbi yake. Sannan a
tsakanin k’irji akwai hak’ark’ari da sauran
abubuwa wanda ya had’a da huhu domin
tace iskar numfashi.”

ZANCI GABA INSHA ALLAH

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment