Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

01 HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI
This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
A wani dadadden zamani da ya wuce, a cikin birnin Misira, an yi wani attajiri da ake kira da suna Shamsuddin. Mutum ne mai gaskiya da rikon amana, ga shi da saukin kai, ga kuma hakuri sai ka ce kasa. Yana da rumfuna da yawa a cikin kasuwar Misira, dukkan rumfunan nan nasa cike suke da haja iri daban-daban. Yana da bayi da kuyangi, bakake da farare, masu yawan gaske. Saboda halayensa na kwarai da kuma yawan rumfunansa a cikin kasuwa, aka nada shi Sarkin Kasuwar Misira.
Shamsuddin yana da mata daya, wadda suke matukar son juna. Sai dai babbar damuwarsa shi ne, shekarunsu arba'in da aure amma ko batan wata matar tasa ba ta taba yi ba, don haka Allah bai nufe shi da samun da ko diya ba.
Wata rana, ranar Juma'a da hantsi, Shamsuddin na zaune a cikin rumfarsa ta kasuwa, sai ya lura da cewa, kusan kowane dan kasuwa yana zaune tare da dansa, wasu 'ya'ya biyu, wasu fiye, a cikin rumfa, suna koya musu sha'anin kasuwanci. Ya zauna yana ta tunani. Da lokacin sallar Juma'a ya kusa, sai ya nufi gidan wankan da ke cikin kasuwar, domin yin wankan Juma'a da kuma alwala. Bayan ya fito daga gidan wanka, a bakin kofar gidan wankan, sai ya amshi mudubin wani wanzami yana duba fuskarsa, yana cewa, "na shaida babu sarki sai Allah, na kuma shaida Annabi Muhammadu bawan Allah ne kuma Manzonsa."
Ya dubi gemunsa ya ga ya cika da furfura, sai ya raya a cikin ransa, furfura fa alama ce ta sakon mutuwa. Da ya tuna ba ya da magaji, sai hankalinsa ya dugunzuma. Bayan an gama sallar Juma'a, sai Shamsuddin ya nufi gidansa. To, da ma matarsa ta san a daidai wannan lokaci yakan dawo gida duk ranar Juma'a, don haka kafin ya shigo ta riga ta yi wanka ta caba kwalliya. Ta shirya masa abinci da abin sha bisa shimfidarsa.
Yayin da ya shigo gida sai ta tare shi da fara'a, ta ja hannunsa ta zaunar da shi bisa shimfida. Ta ce masa, "barka da wannan yammaci, mai albarka."
Shamsuddin ya harare ta, ransa a bace, "ni ban ga albarkar da ke cikin wannan yammaci ba!"
To, da ma ta san abin da ke damunsa a rai kullum, sai ta kyale shi. Ta jawo akussan abinci ta ajiye a gabansa, ta ce, "ci abinci, ya maigidana." Ya sa kafa ya shure akushin abinci, "ni ba zan ci abincinki ba."

Matar ta tambaye shi, "me ya same ka yau, maigida? Menene sababin damuwar ka?"
Shamsuddin ya amsa mata, "ke ce sababin damuwa ta” Matar ta ce, “me ya sa ka ce haka?” ya amsa mata ya ce, “na buɗe rumfata yau da safe na ga kowanne Bafatake yana da ɗa guda ɗaya ko fiye da haka a tare da shi suna zaune a rumfar tamkar mahaifinsu. Ni kuma na gan ni haka babu kowa, sai na ce a raina, “mutuwar nan da ta ɗauki mahaifinka ba za ta bar ka ba kai ma.” To ke kuma tun haɗuwa ta da ke da farko kin sa na rantse cewar ba zan yi mata ta biyu ba bayan ke, kuma ba zan yi kuyanga ba, ‘yar Habasha ko Barumiya ko ma wata k’abila daban. Kuma kika sa na rantse cewar ba zan kwana a ko’ina ba sai tare da ke. Ga shi ke kuma juya ce ba kya haihuwa, kuma zama da ke tamkar zama ne da kurman dutse.” Matar ta ce, “wallahi ba haka ba ne, Allah shi ne shaida ta cewar laifin daga wajen ka ne, domin maniyyinka rarrauna ne, ba zai iya samar da ciki ba ballantana ‘ya’ya.

Sai ya ce mata, “to menene zai kaurara shi? Faɗa min na tafi na sayo shi domin ya kaurara min nawa.” Matar ta ce, “ka tafi wajen masu magani.” Ya kwana da ita a wannan daren. Washegari ya tashi yana mai nadamar kaushin harshen da ya yi mata a jiya, ita ma ta yi da-na-sanin martanin da ta mayar masa. Ya tafi kasuwa yana neman masu magani har ya dace da wani mai maganin ya yi masa sallama ya amsa sannan ya tambaye shi, “yalla kana da maganin da ke kaurara maniyyi?” mai magani ya amsa, “na wajena ya k’are, sai dai ka tambayi mak’wabcina.” Ya tambayi na gaba shi ma ya ce babu. Haka ya yi ta zagaya masu maganin nan kaf yana tambaya babu wanda ya ce akwai sai dariya suke masa. Da ya gaji sai ya koma rumfarsa yana cike da damuwa. A gefen rumfarsa wani babban dillali yana faɗin amfanin ganyen shayi da zoɓorodo da kuma taba. Shi wannan mutumin ana kiransa Sheikh Muhammadu Samsami, matalauci ne, kullum yana yi wa Shamsuddin addu’ar fatar alheri. Bayan ya gama tallar ya zo bisa al’adarsa ya gaishe shi, ya lura cewa yau Shamsuddin na cikin damuwa sai ya ce masa, “ya shugabana, yau me ya ɓata maka rai?” Shamsuddin ya faɗa masa dukkan abin da yake damun sa da yadda suka yi da matarsa, ya k’ara da cewa, “yau shekara arba’in kenan da aure na amma ba ta taɓa haihuwar namiji walau mace ba. Kuma an ce wai dalilin rashin haihuwar ta saboda maniyyina ne bai yi kauri ba.
Na zagaya wajen masu magani kaf ban samu dacewa ba.” Sheikh Muhammadu ya ce, “ya shugabana, ina da maganin da ke kaurara ruwan halitta ɗa namiji, amma me za ka ce ga wanda ya yi sanadin matarka ta haihu bayan tsawon shekaru arba’in bata yi haka ba? Shamsuddin ya ce, “idan ka yi min haka zan maka tagomashi mai yawa.”
“To ba ni dinari.” In ji Sheikh Muhammadu. Shamsuddin ya ce, “ɗauki waɗannan dinarai biyun. Sannan ya nemi a ba shi tasa da kasko, duka Shamsuddin ya ba shi. Ya ɗauka ya tafi zuwa wajen mai sayar da hakukuwa ya awo bibiyu na albasa da tafarnuwa da zanjabilu da citta da kaninfari da masoro da farin barkono da sauran kayan yaji. Ya daka su gaba ɗaya sannan ya tafasa su cikin man zaitun sannan ya k’ara ganye uku na gamji da ararraɓi da ruman. Sannan ya cika kaskon da garin alkama. Sannan ya cuɗa da zuma, ya rufe cikin wannan tasa ya kai wa attajiri ya ce masa, “ga maganin da ke kaurara maniyi.” Ya faɗa masa yadda zai yi amfani da shi. “ka rik’i wannan a matsayin ruwan sha. Amma da farko ka samu naman rago ka ci, kuma a dafa maka ‘yan shila da yaji mai zafi ka ci. Sannan idan zafin yaji ya dame ka sai ka haɗa da nono da sukari domin su ne ke hana yaji zafi.” Attajiri ya haɗa dukkan abubuwan da ake buk’ata har da naman da tattabarun ya aika da shi ga matarsa ya ce a sarrafa su kafin ya dawo.
Da ya dawo da yamma ta kawo masa girkin ya buɗe ya cinye gaba ɗaya sannan ya sha haɗin maganin. Ya ji daɗin maganin sosai. Bayan ya kammala ya kwanta da matarsa. A wannan dare Allah ya k’addara ta ɗauki ciki, bayan wata uku sai ta ga al’adarta ba ta zo ba, a nan ta fahimci ta samu juna biyu. Yayin da ciki ya girma ya isa haihuwa, ciwon nak’uda ya kama ta, ta kasance tana k’ara saboda farin ciki da kuma wahalar haihuwa. Aka kirawo unguwarzoma ta taimaka mata tana ambata sunayen Allah da na Annabi Muhammadu da na sahabbai sannan tana kabbara har ta haifi ɗa namiji. Aka yi masa kiran sallah da kalmar shahada a kunnuwansa. Sannan unguwarzoma ta naɗe shi cikin zane ta mik’awa uwarsa, ta karɓe shi ta ba shi nono. Bayan ya k’oshi ya mik’a da barci abin sa. Unguwarzoma ta zauna tare da ita har kwana uku, aka shiryawa mai jego kayan k’anshi da nama mai kyau, kuma bayan kwana bakwai aka rabawa jama’a alawa da dabino. Sannan aka barbaɗa gishiri a k’asa wai maganin mugun ido. Attajiri Shamsuddin ya shiga wajen matarsa ya taya ta murnar haihuwa lafiya sannan ya ce mata, “ina ajiyar Allah ɗin yake?” Aka kawo masa jaririn kyakkyawa bisa cikakkiyar surar mahalicci wanda yake tabbatacce har abada ba zai gushe ba. Kodayake kwana bakwai kenan da zuwan jaririn duniya, amma ga wanda bai sani ba sai ya yi tsammanin ya shekara guda, saboda girman da Allah ya ba shi
Uban ya dubi fuskarsa na haske da k’yalk’yali kamar wata ɗan daren sha huɗu, ga kundukukinsa ja mai k’ayatarwa. Ya ce da matar, “wanne suna kika kira shi?” ta amsa da cewa, “da a ce mace ce sai na ba ta suna, amma tunda namiji ne babu mai ba shi suna sai kai mahaifinsa.” A wancan lokacin kuwa mutane sun kasance suna raɗawa ‘ya’yansu suna bisa faruwar wani al’amari a lokacin da aka haife su, attajiri da matarsa suka kasance suna tambayar sunan da ya kamata su raɗa wa ɗansu. Can sai wani daga mahalarta ya ce, “Allah ya raya Alaldini!” Sai kuwa attajiri ya ce, “to sunansa Alaldin Abul Shamatu.”
Sannan ya mik’a yaro ga masu shayarwa, ya sha nono na tsawon shekara biyu sannan aka yaye shi. Yaro ya rik’a girma har ya kai shekara bakwai, sannan uban ya ɗauke shi ya ɓoye a cikin gida domin tsoron idanun mahassada, ya ce, “ba zai fito waje ba har sai ya yi gemu.” Ya sa kuyanga da bawa su rik’a kula da shi; kuyangar na shirya masa abinci, bawan kuma yana ɗaukarsa a bayansa. Daga nan aka yi masa kaciya ya shirya k’asatacciyar walima. Bayan nan ya samo malamin da ya rik’a koya masa rubutu da karatu da alk’ur ani mai girma da sauran ilmi har dai ya samu ilmi mai yawa. Rannan bayan an kawo masa abinci sai bawan ya manta ya bar k’ofar gidan da yake a buɗe bai rufe ta ba. Saboda haka Aladdin ya fito ya tafi wurin mahaifiyarsa tana tare da wasu matan suna hira. Yayin da suka ga ya shigo sai suka yi tsammanin farin bawa ne wanda ya yi sha don tsananin kyawonsa. Yayin da suka gan shi gaba ɗaya sai suka rufe fuskokinsu da mayafi suka ce da uwarsa, “yaya za ki bari farin bawa ya shigo mana nan wurin? Ba ki san cewa kunya na daga sashen imani ba.” Ta ce musu, “ku ambaci sunan Allah da bismilla! Kada ku sa mini laifi Wannan ɗana ne furen zuciyata kuma magajin falke kuma attairi Shamsuddin mai dukiya a birnin nan, wanda uwar goyonsa ta yalwata da tufafi da abinci da abinsha.” Suka ce, “mu kam tsawon zamanmu da ke ba mu taɓa sanin kina da ɗa ba.” Sai ta ce, “haka ne, domin mahaifinsa ke tsoron sharrin idanun mahassada ya ɓoye shi a gidan k’ark’ashin k’asa, yanzu ma watak’ila bawa mai kula da shi ne ya manta k’ofar a buɗe shi ya sa ya fito. Ba ma nufin fito da shi yanzu sai ya soma gemu tukunna.

Matan suka nuna jin daɗin su game da shi, saurayin ya tafi k’ofar gida ya zauna, sai ga bayin babansa haye da alfadararsa. Ya tambaye su, “wannan kuma fa daga ina?” suka ce masa ta babanka ce, mu raka shi kasuwa ne muka dawo da ita.” Sai ya ce musu, “menene sana’ar babana?” Suka ce “mahaifinka falke ne na k’asar Misira, shine ɗan sarkin ‘ya’ya a zamaninsa.” Daga nan ya tashi ya tafi wajen mahaifiyarsa ya ce da ita, “mecece sana’ar mahaifina?” Ta ce masa “mahaifinka tajiri ne mai alheri, mafificin tajirai na k’asar Masar, shi sarki ne a kan ‘ya’yan Larabawa, ko bayinsa ba sa yi masa magana a harkar cinikin da ya gaza dinari dubu. Duk wanda yake da kaya na kamar dinari ɗari ko fiye, zai sayar ne kurum gwargwadon aniyar sa. Su tafi zuwa garuruwa masu su saro kaya su sayar ba tare da tuntuɓar sa ba saboda amincin sa da su. Yana da dukiya mai yawa a hannun mutane suna jujjuya su bai kula ba yana ta sha’anin sa. Wani abu na daga dukiya bai taɓa damun sa ba balle ya sa tsone masa ido, Allah ubangiji ya hore wa mahaifinka dukiya mai yawan gaske.”

ZANCI GABA GOBE INSHA ALLAH02 HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI

Da ya ji haka daga bakin mahaifiyarsa sai ya cika da farin ciki, ya ce, “ya uwata, yabo ya tabbata ga Allah wanda ya k’addara mahaifina shi ne sarkin ‘ya’yan Larabawan Masar kuma falke mai dukiya. Amma me ya sa kuka sa ni k’ark’ashin k’asa kuka tsare ni sai ka ce ɗan kurkuku?” Ta ce, “haba ɗana, ba mu saka ka ko tsare a ciki ba face saboda tsoro idandunan mutane. Domin kambun ido gaskiya ne, mafi yawan waɗanda suke ga kaburbura daga ido suka tafi.” Ya ce mata, “to yaya za ku yi da hukuncin Allah? Tsoro ba ya hana k’addara aukuwa. Abin da aka rubuta gudu baya hana zuwansa, wanda ya ɗauki kakana ba zai bar mahaifina ba ballantana.

Wanda ya rayu yau ba lallai ya rayu gobe ba. Idan mahaifina ya mutu ya rage saura ni na mutu kenan, ni Aladdini ɗan Shamsuddini bafatake, idan na ce wa mutane ni ɗansa ne na san babu wanda zai gaskata ni saboda kun ɗauke ni ku ɓoye babu wanda ya san cewa Shamsuddini yana da ɗa. Bayan ransa ba za a bar min komai ba za a ɗauke dukkan dukiyarsa da mallake – mallakensa a zuba a baitalmali. Ni zan rik’i gaskiya na bar k’arya. Wanda ya ce saurayi na mutuwa saboda idanun mutane wannan bai gaskata hukuncin Allah ba. Yanzu abin da za a yi ke uwata ki faɗa wa mahaifina ya tafi da ni kasuwa ya buɗe min rumfa ya zuba min kaya, na zauna tare da fatake da dillalai ya rik’a koya min yadda ake saye da sayarwa da karɓa da bayarwa.” Uwar ta ce, “an jima kaɗan mahaifinka zai dawo zan faɗa masa wannan buk’ata.

Yayin da Shamsuddin ya dawo sai ya tarar da Aladdini a zaune yana hira da mahaifiyarsa, ya ce da ita, “don me kika bari ya fito waje?” ta ce da shi, “ya ɗan baffana, ba ni ce na fito da shi ba, bayin ne suka manta k’ofa a buɗe ya samu ya fito lokacin ina tare da mata sun hallara gare ni daga manyan wannan gari, ya shigo gare mu.” Ta habarta masa yadda suka yi da shi. Da ya ji haka sai ya ce, “ya ɗana gobe idan Allah ya yarda zan ɗauke ka zuwa kasuwa. Amma ka sani zaman rumfa yana buk’atar ka zam mai ladabi ga abokin ciniki da tausasa masa domin akwai jama’a mabambamta a kasuwa. Ana buk’atar natsuwa da kwantar da hankali a kowanne al’amari mutum ya gani a kasuwa.” Aladdini ya yi barci a wannan dare yana mai farin ciki bisa wannan alk’awari na mahaifinsa. Da gari ya waye attajiri ya tafi da ɗansa ɗakin wanka, bayan ya fito ya ba shi tufafi masu daraja da tsada. Bayan sun karya kumallo ya ɗora shi a kan alfadara shi kuma ya hau wata suka tafi kasuwa, mahaifin yana gaba ɗan na biye da shi a baya.
Yayin da mutanen suka ga falke mai alheri tare da saurayin nan fuskarsa na haske kamar wata ɗan daren sha huɗu, sai suka rik’a faɗi a tsakanin su, “ku dubi yaron nan da ke biye da shugaban fatake, muna tsammanin akwai alheri tare da shi. Yadda fuskarsa take kyakkyawa haka ma zuciyarsa take mai kyau.” Dattijon nan Sheikh Muhammadu Sansami wanda muka ambata a baya ya ce da dillalai, “ba za mu taɓa yarda wannan yaron ya kasance ɗa ga Shamsuddini ba. Ko mu da ba mu kai shi a shekaru ba, ba mu da yaro mai k’uruciya kamar wannan ba!”
Ya kasance bisa al’adar tajiri duk lokacin da gari ya waye ya zo kasuwa ya buɗe rumfa fatake na zuwa gare shi su zauna, a karanta surar Fatiha sannan a yi addu’a. Sai ya yi musu kyauta su kuma su yi masa fatar alheri kowa kuma ya shiga sabgar gabansa. To amma yau da ya zauna a rumfa babu bafataken da ya zo gare shi. Da ya ga haka sai ya kira mataimakin dilallai ya ce da shi, “yau me ya sa fatake ba su zo mun yi addu’a ba?” Muhammadu Samsami ya ce, “ban san yadda zan fada maka labarin ba, amma matsala ce gagaruma ta tashi. Duk fatake sun hada kai domin su tube ka daga wannan muk’amin naka. Shi yasa suka k’i zuwa gare ka a yau.” Shamsuddini ya ce, “to menene dalilinsu na aikata haka gare ni? Laifin me na yi musu?” Mataimaki ya ce, “menene sha’anin wannan yaron da ke zaune kusa da kai? Ka tuna kai ne zababbe shugaban fatake. Menene sha’aninsa? Bawanka ne ko hadiminka ko kuwa dan uwan matarka ne? Mu muna ganin kamar kana karkata bisa ga k’ananan yara kana begensu.” Attajiri ya tashi bisa gare shi ya yi kururuwa ya ce, “ka yi shiru ya kai Nak’ibu, Allah wadan wannan zato da kake siffantawa a ranka! Wannan dana ne!” Mataimaki ya zabura ya ce, “ba mu taɓa sanin ka haihu ba a rayuwarka.” Shamsuddini ya ce, “ka manta shekarar da ka ba ni maganin kaurara maniyyi na hada na sha? A wannan lokacin matata ta samu ciki ta haifi wannan yaron. Na raine shi a boye domin gudun miyagun idanu, ba nufina ba ne ya soma fitowa waje ba har sai ya samo ajiye gemu tukunna.

Mahaifiyarsa ce ba ta yarda da maganata ba, ta amince da buk’atarsa cewar na fito da shi zuwa kasuwa na koya masa kasuwanci da saye da sayarwa.” Mataimaki ya tashi zuwa ga ragowar fatake ya fada musu dukkan abin da ya faru. Da suka ji haka suka taso gaba dayansu suka je gaban rumfar Shamsuddini suka karanta fatiha kamar yadda suke yi bisa al’adarsu. Daga nan suka nuna farin cikinsu da yaron suka yi masa fatar alheri. Suka ce da Shamsuddini, “ko da wanda ya kasance mafi tsananin talauci a cikinmu, idan ya samu yaro ko yarinya yakan tara mu ya sanar mana, sannan ya ba mu goro da alewa domin mu shaida Allah ya albarkace shi da zuri’a, amma kai ba ka yi mana haka ba.” Shamsuddini ya ce, “kun bi ni bashi, mu taru a gona domin na sauke bashin' haihuwa aladdin Da gari ya waye ya aika da bayi zuwa gona ɗauke da shimfida biyu, daya nasa, daya domin ɗansa. Sannan ya sa aka kai kayan dahuwa; raguna da shinkafa da man shanu da duk abubuwan da ake buk’ata a girki. Sannan ya shirya dansa suka tafi gona, ya ce da dansa, “idan mutum babba ya zo mai furfura ni zan tarbe shi na zaunar da shi a shimfidata, idan kuma saurayi ya shigo maras gemu sai ka tarbe shi ka zaunar da shi shimfidarka.”
Aladdini ya ce, “menene hikimar bambanta shimfiɗa haka?” Ya ce, “saboda yaro marasa gemu zai ji kunyar cin abinci cikin manya masu gemu.” Dan ya gamsu da wannan jawabi. Yayin da fatake suka hallara, Shamsuddini ya tashi ya tarbe su ya zaunar da su a shimfidarsa yayin da Aladdini ya rik’a tarbar samari a shimfidarsa.
Sannan aka hallarar da abinci ga bak’i suka ci suka sha suka yi farin ciki suka ji dadi, suka kwana suna sha suna shafa turare. Manya suka rik’a tattauna al’amuran da suka shafi ilmi da kasuwanci da sauran hirarraki da nasihohi. A cikinsu akwai wani bafatake sunansa Mahmudu Balhi, shi ya kasance a sarari musulmi ne, amma a zuciya tasa Majusi ne mai bautar wuta. Yana da dabi’ar barna a zuciyarsa ga yara. Yayin da ya dubi Aladdini duba daya asara dubu ta tabbata gare shi, shaidan ya k’awata masa jauhari a fuskarsa ya ji zuciyarsa ta cika da k’auna da sha’awarsa, ya ji ba zai iya daurewa ba tare da ya aiwatar da nufinsa a kan sa ba. Shi kuwa Mahmudu Balhi ya kasance yana karbar kayayyaki a wajen Shamsuddini yana sayarwa ya kuma dawowa ya debi wasu. Ya tashi daga wurinsa ya tafi wajen yara suka mik’e domin taryensa. Shi kuwa Aladdini a lokacin sai matsuwa ta same shi, ya tashi domin ya je ya biya buk’ata ya dawo. Mahmudu Balhi ya juya ga ragowar yara ya ce musu, “idan kuka rinjayi Aladdini ya yarda zai yi tafiya da ni, zan ba wa kowannenku riga mai tsada ta alfarma.” Sannan ya juya sashin manya ya zauna. Yaran na zaune sai ga Aladdini ya dawo suka tashi suka tarye shi sannan suka zaunar da shi a tsakaninsu suna masu girmama shi. daya daga cikin yaran ya ce da na kusa da shi, “ya shugabana Hassan, ina so ka fada min idan ka samu jari me za ka yi na kasuwanci?” Yaron ya amsa ya ce, “idan na girma na zama munzalin namiji zan ce da mahaifina ya ba ni dukiya da kaya, shi kuma sai ya ce min ba shi da wannan kayan, amma na tafi ga wani bafataken domin na koyi saye da sayarwa. Sai na tafi wajen wani bafataken na ari jarin dinari dubu guda na sayi kaya na tafi Dimashk’a na sayar a nan na samu riba biyu a bakin daya. Daga nan sai na sayi kaya daga Dimashk’a na tafi Halbiya na sayar a nan ma na ci riba mai yawa, idan na sari kayan Halbiya sai na tafi Bagadaza na sayar a nan ma na ci riba kamar a baya. Haka zan yi ta saye ina sayarwa a birane
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI
avatar
saidou

7 months ago

Reply

Tyhfhhhjg

avatar
ummitah

7 months ago

Reply

Wow

Please Login or Register in order to submit comment