Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naƙudar Sadeeq to ko zan yi yawo tsirara bai isa ya haɗa jini da jinin Halimatu ba domin na tsaneta na tsani ahalinta baki ɗa....." Wani irin bugu ya kaiwa bakinta yana huci,cikin zallar ɓacin rai ya ce, "Ashe ko zaki yi yawo tsiraran,domin kuwa aure babu fashi in kinga Sadeeq bai auri Raudah ba ita ce ta ce bata son sa, ko kuma ƙasa ne ya rufe idanuna!" Ya kai ƙarshen maganar yana ficewa a fusace ya bar mata ɗakin.

Yaya Sadeeq kuwa suna fita ɗakunansu da ke cikin zauren sasan nasu kowanne ya nufi ɗakinsa,kowanne a cikinsu zuciyarsa babu daɗi.Yaya Sadeeq ɗin ya yi kwance bisa katifar ɗakin nasa yana kai hannu ya dafe kansa,kalaman Inna Karimatu ke yawo a kansa,yana lalubo dukkain halayyar Umma dana su Raudah domin ya gano aibu ko kasawarsu a nagartattun halaye amma ya gaza samun nakasu a tattare dasu.Tun tasowarsa yake son sanin wani irin laifi ko saɓani ne ya shiga tsakanin Innarsa da Umma har take mata irin wannan ƙiyayyar,amma har kwanan yau ya gaza gano wani laifi ko saɓanin da ya janyo wannan kalar ƙiyayyar.Abinda ya fahimta kawai shi ne,Innarsa mugun hali ne da ita da kuma muguwar hassada akan irin yadda Umman ta fita komi na rayuwa.Ya dafe kansa da ke tsananin sara masa yana jin ƙarin ƙaunar Raudah a cikin zuciyarsa mai tsanani,ko kaɗan baya ji akwai barazanar da zai sanya shi ya janye daga neman aurenta domin idanunsa basu taɓa gane masa wata ƴa macen da ta mallaki cikar halitta irin wanda yake so ba sai a jikin Raudah.Tunawa da ya yi basu sama shiga kowani sasa ba tun shigowarsu gidan ya sanya shi ya miƙe ya lalubi wayarsa ya fito daga ɗakin,ya kulle ɗakin nasa ya fito daga zauren yana nufan sasan Hajiya Kakah domin fara miƙa gaisuwa zuwa gareta.

"Amincin Allah ya tabbata a gareki ƴar tsohuwa mai ran ƙarfe!" Daddaɗar muryar Yaya Sadeeq ya furta hakan lokacin da ya isa ga ƙofar ɗakin Hajiya Kakah.Daga ciki ta amsa da wani irin ɗoki ta ce, "Ameen ya masoyin Manzo! Barka da sauka,sannunku da isowa." Yaya Sadeeq ya ɗage labulen ɗakin ya sanya kansa ciki fuskarsa na haskawa da maɗaukakin murmushi.Idanunsa ya sauka akan Hameedah da ke wa Hajja Kakah gyaran falon,ta gaida shi cike da ladabi kamar yadda suka ba.Yaya Sadeeq ya amsa mata fuska babu walwala sosai,domin kaf gidan babu mai ganin haƙoransa a waje sai sahibar tasa Raudah,ita ma ba kasafai ta faye gani ba domin miskili ne shi mare son raini ko ƙanƙani.Shiyasa sam bayi wasa dasu bare su raina shi,iyakarsa dasu gaisuwace sai idan ya yi niyyar yi musu alkhairy ya siya musu wani abin ko ya raba musu kuɗi idan sun zo ganin gida daga Kaduna.Kusa da Hajjah Kakah da ke zaune saman kafet ɗin da ya mamaye tsakiyar ɗakin ya zauna,cikin murya mai cike da karsashi da jin daɗin ganinta ya shiga gaidata a ladabce.Ta amsa cikin farin ciki tana faɗin, "Madallah da amsar sakamako,nayi farin ciki nayi murna ƙwarai,Ubangiji yasa albarka ya kawo aiki mai tsoka ka riƙa kai ni Hajji da Umrah duk shekara Sadeekuna!" Yaya Sadeeq ya saki murmushi ya ce, "Ameen Hajjah Kakah,Allah ya zaɓa mana abin yi mafi alkhairy tsakanin aikin ko kasuwanci." Hameedah tana kammala goge saman TV stand ɗin Hajjah Kakah ta sulale ta fice daga ɗakin,domin sam ta san ba za ta kuma sukuni idan yana cikin ɗakin ba.Hajiya Kakah ta dubi jikan nata mafi soyuwa a zuciyarta sakamakon yawan kyauta da alkhairynsa gareta,ta buɗe baki cike da ƙauna ta ce, "Ameen Sadeeku,sai maganar aje Iyali idan abin yi mai ƙarfi ya samu,duk da cewa wannan sana'ar ta ɗinki kaɗai ya isheku ku ci da Iyali dashi,ina aka kwana,shin ka samu wacce ka ke so ne ko kuwa?" Sadeeq ji yayi gabaki ɗaya Hajjah Kakah ta famo masa mikin kalaman Innarsa akan abinda zuciya da gangar jikinsa ke so da kuma kwaɗayin mallaka.Ya turɓune fuska cike da nuna zallar damuwa ya soma da faɗin, "Hajiya Kakah na samu wacce nake so,kuma ƴar gida ce jinina Raudah,amma Inna tayi rantsuwar ba zan haɗa jini da Umma ba matuƙar tana raye,ni kuma nan duniya banga macen da nake so,nake kuma burin mallaka ta zama matata ba sai Raudah." Ya dakata yana kallon yadda fuskar Hajjah Kakah ya fara tsukewa da matsanancin fishi.Yana dasa aya ta ce cikin karaɗi, "Ita Karimatun ne har tayi kaurin wuyan da za ta furta ba za ka auri jininka ba? To ita kuma a suwa daddawa a kunu ni Zuwairah? Ka kwantar da hankalinka ka ji ko,indai har Raudatu na sonka,kai koma bata son ka tunda kai dai ita ce zaɓinka to zan kuwa nuna ƙarfin ikona wajen ganin anyi wannan auren nan bada jimawa ba." Hajjah Kakah tayi maganar tana huci kai ka ce tana da wani say ne akan Inna Karimatun da akan idanunsu bata iya katabus,amma a yanzu a bayan idanunta gashi ta maze tana yanko zance kamar za ta iya cika masa alwashin da ta sha.Shi ko Yayah Sadeeq kalaman Hajiya sai suka kwantar da hankalinsa,domin yafi kowa sanin halinta na nuna iko akan su jikokinta da bata haɗa soyayyarsu da kowa ba.Cikin nuna farin ciki ya ce, "Allah ya ja kwana Hajjah Kakah,Raudah tana sona ba ma sai kin nuna ƙarfin iko akanta ba,tana baya-baya dani ne sabida tsoron irin ƙiyayyar da Inna ke gwada musu su da Ummansu,abin na min ciwo Kakah tun daga randa na fahimci Umma nagartacciyar uwace da ta ɗaukeni tamkar su Raudah a zuciyarta,bata taɓa min koda kallon banza ba duk da irin yadda Inna bata ƙaunarta,bata taɓa nuna min cewa ina da bambamcin da ƴaƴanta ba,ta ɗaukeni tamkar ɗanta ne ko kaɗan ban ga wani dalili guda ɗaya da Inna zata kafa hujja dashi wajen zurfafa ƙiyayyarta ga Umma ba." Ya dakata da kalamansa yana jin tsananin ɗaci da ciwon yadda Innarsu ta fito a wata iriyar bahaguwar mace mai tsananin hassada da son kanta.Hajjah Kakah ta sake ƙanƙance idanu ta ce, "Baka kaini takaici ba Abubakar,domin nafi kowa sanin bakomi ne a zuciyar Karima game da Halimatu ba sai tsabar hassada da ƙyashin yadda ta fita samun duniya,tana adawa da cigaban da kullum ke samun rayuwar Halimatu na iya sarrafa sule ya zama sisi,gashi kuma ta fita kyawawan halaye da zuciya mai kyau,na sha gwada yiwa Karimatu karatun ta nutsu akan Halima amma da zaran na haɗa idanu da ita duk sai na ji tsoro ya cika zuciyata,daga ita har Safiya na rasa kalar asirin da suka banko mini da duk jarabata bana iya katabus a kansu,amma akan maganar aurenka da Raudah dole in nuna ƙarfin ƙwanjina,in kuma dage da sadaka domin na garara daga dukkanin sharrinsu har Ubangiji ya tabbatar da wannan lamari." Hajiya Kakah ta kai ƙarshen kalaman tana narkewa Sadeeq tamkar za ta saki kuka.Ya dinga rarrashinta tare da bata shawaran yadda yakamata ta bullowa lamarin har ya samu su rinjayi Inna Karimatu burinsa ya cika akan mallakar Raudah.Ya jima sosai a sasan Hajjah Kakan kafin ya yi sallama da ita ya fito ya nunfi sasan su Raudah,yana tafe zuciyarsa na ayyano masa kyakykyawar fuskarta da ya yi kewar gani tsayin watanni kusan uku da basu shigo Zaria ba.Ya doka sallama daga cikin tsakar sasan nasu idanunsa na yawo cikin muhallin da tsafta ya wadacesa,ko'ina a share tsaf simintin tsakar sasan na ɗaukar idanu kamar kullum sai an saka kilin an wanke tsakar gidan.Maimunatu ce ta fito daga ɗakinsu tana amsa sallamar tasa,ta ɗan rusuna kaɗan ta gaida shi tana ƙin kallon fuskarsa domin tana tsanani shakkarsa fiye da Yaya Usman da ke jansu a jikinsa.Ya zuba mata idanu babu ko ƙirfawa yana mamakin irin hasken da ya ga tayi tashi guda,cikin matuƙar tsare gida da tsuke fuska ya ce, "Ke! Uban me ki ke shafawa kika yi irin wannan farin tashi guda? Bleaching ki ke yi sabida baki da hankali ke daƙiƙiyace ko?" Maimunatu ta zumɓuri baki ƙirjinta na dukan uku-uku,cikin aro jarumta ta bashi amsa da faɗin, "Yaya nifa ba bleaching nake ba mayuka ne kawai na samu da suka amshi fatata." Ya maka mata wata uwar harara yana kausasa murya ya ce, "To daga yau kada ki sake shafasu domin kuwa mayukan bilicin ne,idan kuma na cigaba da ganin wannan farin na sake wanzuwa akan fatarki saina ɓallaki a cikin gidannan idiot!" Ya ƙare maganar da tsawa sosai a muryarsa.Hakan ya sanya Maimunatu saurin yin gaba ta suri buta ta nufi banɗaki,dama ta fito da zummar zuwa banɗakin ne ta ji sallamarsa har ta amsa tare da gaida shi ɗin.Cike da ɓacin ran banzayen halayen da tun watannin bayan baya ya fara kula dasu game da Yarinyar ya isa bakin ƙofar ɗakin Umma yana sallama,daga ciki muryar Ummance ta amsa masa sallamar tana masa lale da zuwa.Ya sanya kansa cikin falon yana wadata fuskarsa da murmushi,yayinda idanunsa suka shiga zagaye falon da daddaɗan ƙamshin turaren wuta ke tashi.Cike da ladabi ya gaida Umman,ta amsa da fara'a tana ɗaurawa da faɗin, "An ce sai kun amsa sakamako za ku dawo,har an amsa kenan Sadeeku? To Allah ya sanya albarka yasa yawan rai aka yiwa,Allah ya kawo babban rabo ya tsare manaku a kowani mataki na rayuwa." Yaya Sadeeq ya amsa cikin matuƙar jin daɗin addu'o'in Umma.Shiru ya ɗan ratsa a tsakani kafin Yaya Sadeeq ɗin ya kasa haƙuri ya dubi Umma ya ce, "Umma su Suhailah basa nan ne na ji sasan tsit?" Umma tayi murmushi tana gano dukkanin take-takensa akan Raudah,cikin sanyin muryarta ta furta, "Suhailah na wajen Gwaggonta Salamatu,su Sumayyah na ɗakinsu suna faman zuzzuba tuwan madara a mazubin da suke packaging ɗinsa za a kai shago." Daga haka ta ciri murya tana kiran sunan Sumayyah,cikin seconds ta bayyana a cikin falon idanunta na sauka akan Yaya Sadeeq ɗin.Da wani maɗaukakin murmushi da murnar dawowarsu garin take gaida shi,ya amsa da kulawa yana sake zubawa ƙofar ɗakin nasu idanu.Burinsa kawai idanunsa su sauka akan kyakykyawar fuskar Raudah,Sumayyah tayi masa fatan alkhairy akan kammala karatunsu da amsar result ɗinsu da suka yi cikin nasara.Ya amsa yana sake yaba nutsuwa da hankali irin na ƴaƴan Umman,domin ko Hameedah da take tsarar Raudah bata san tayi tunanin yi musu fatan alkhairy akan kammala karatun nasu ba.Ta juya ta koma ɗakinsu tana sanar da Raudah cewa Yaya Sadeeq sun dawo gashi can a falo,Raudah da zuwa lokacin tayi wanka tana sanye cikin wata straight gown na atamfa pich colour da ya amshi jikinta.Ta ɗago daga manna sticker ɗin RAUDAH'S CUISINE a jikin pack ɗin gullisuwa da tuwan madara da suka gama packaging,ta ɗaura idanunta akan Sumayyah tana faɗin, "Ma Sha Allah! Barkansu da dawowa,bari na ƙarisa manna stickers ɗin in fita mu gaisa." Yadda tayi maganar cike da basarwa ya sanya Sumayyah sakin murmushi,cike da tsokana ta dubi Raudah ta ce, "Kai ke ko Yaya Raudah,duk ya ƙagu ya ganki ne fa, baki ga yadda yake faman kallo ƙofar ɗakinnan ba,wallahi Yaya Deeku ba ƙaramin kamuwa ya yi a sonki ba." Raudah ta harari Sumayyah tana faɗin, "Au kema kin zama ƴar saka idanu ce da gulma Sumy?" Sumayyah ta saki dariya tana faɗin, "Daga faɗan gaskiya kuma Yaya Raudah? Ai kowa ya kalli yadda yake kallonki ya san soyayyarki ce fal a cikin zuciyarsa,ke ma kuma daga yadda ki ke amsa wayarsa kaɗai za a fahimci kina son sa Yaya Raudah,kuma wallahi za ku dace da juna." Raudah ta jinjina kai ta ce, "Duk ba wannan bane Sumy, ina jin tsoron halayyar Inna Karima da sam ba ƙaunar Umma take ba bare kuma mu,shiyasa a koda yaushe nake ƙoƙarin danne duk wata soyayyarsa da nake ji a cikin zuciyata domin bana son duk abinda zai saka Inna Karimatu ta samu hanyar ɗagawa Umma hankali ko cin mutuncin mu." Sumayyah ta jinjina kai jikinta na mutuwa da kalaman Raudah,domin tabbas ita ma tana hango ƙura idan har Inna Karimatu ta gano irin soyayyar da Yaya Deeku da Raudah ke wa junansu......✍🏻



_Hello my luvly fans!😍Shin labarin ya fara shiga zukatanku ko har yanzu da saura dai? Me ku ke shinshinowa ne cikin wannan tafiyar da kuma rayuwar ahalin Hajjah Kakah? Mu haɗu comment section_ 😍
[10/8, 2:29 PM] Aysha Dansabo😍: 📱 *RAYUWA DA ƘADDARA* *Arewabooks@ayshadansabo*

*Paid book 08167768704*

*Free page*

*Chapter 6*

Tunda ta fito daga ɗakin nasu ya kafa mata idanunsa babu ko ƙiftawa,wani irin sassanyan kyawu ya ga ta sake ƙarowa.Zuciyarsa ta sake narkewa cikin ƙaunarta yana sake zurfafa ganinsa akan kyakykyawar fuskarta da kalar ƙaramin hijab ɗin da ta saka ya hasketa matuƙa,kalar baby pink ne da ya fiddo asalin hasken fatarta ya kuma yi mata kyau sosai.Cikin takunta mai cike da nutsuwa ta ƙarisa bakin seatern da ke facing ɗinsa ta zauna,tana mai jin nauyin kaifafan idanunsa da basu daina yawo a kanta ba.Da wani irin sassanyar muryarta ta gaidashi a ladabce tare da kwararo masa addu'an fatan alkhairy game da kammala deegree ɗinsu,ya amsa da wani irin fara'a yana sake jin matsananciyar ƙaunarta na kewaye jininsa.

"Habeebty kin amince a yau na nemi izinin fara keɓewa da ke da sunan zance a wajen Baba Mai Itace?" Yaya Deekun ya jefawa Raudah tambayar idanunsa a kanta yana kallon yadda tayi ƙasa da idanunta.Ta ɗago ta dubeshi da manyan idanunta masu haske tana wani narke fuska,da shagwaɓa a cikin muryarta ta ce, "Da wuri haka Yaya Sadeeq? Me zai hana ka fara gabatar dani a wajen Inna kafin ka tunkari kowa da wannan batun?" Yaya Sadeeq zuciyarsa sai tayi wani irin kaɗawa da jin kalaman Raudah, "Kenan ita ma ta san za a iya samun matsala da Mahaifiyarsa sabida irin ƙiyayyar da take gwada musu?" Ya tambayi kansa yana kallonta da wani irin yanayi da idanunta suka kasa jurewa gani akan fuskarsa,sai ta sake yin ƙasa da kanta lokacin da yake faɗin, "Habeebty Inna ba za ta hana aukuwar dukkanin abinda Allah ya hukunta ba,ni dai burina ki bani goyan baya na fara neman izinin Baba Mai Ice,domin na riga da nasar da Babanmu ke ce zaɓina." Ya ƙare maganar cikin wani irin sanyin muryar da ya sanya Raudah ɗago kanta ta dubesa,ya kashe mata idanu guda tare da karyar da kansa ya ce, "Please Raudah!" Raudah sai ta samu kanta da sakin masa sassanyar murmushi kafin ta furta, "Shikenan Yaya Deeku na baka dama." Da wani irin farin ciki ya furta, "Thank u Habeebty,i luv u!" Raudah tayi saurin kai bakin hijab ɗinta ta rufe idanunta wani irin kunya na lulluɓeta.Sai dai kalmar tayi mata daɗi tare da sake jefa wani ƙaƙƙarfan feeling a cikin zuciyarta,ba yau ne karon farko da ya fara furta mata kalmar ba,amma wannan ita ce karon farko da ya furta mata kalmar gaba da gaba kamar hakan.Ya saki wani lallausar murmushi yana sake faɗin, "Ni ba idanu nake so ki rufe ba Habeebty,so nake ki ce u luv me too Baby!" Yadda ya faɗi kalmar Baby ɗin yana kwaikwayon salon yadda take magana ba ƙaramin dariya ya bata ba,ta sake rufe idanu tana dariya ƙasa-ƙasa cikin hijab ɗinta kafin ta furta, "Kai Yaya Sadeeq! Ni fa kunya nake ji!" Sai ya saki lallausar murmushi yana miƙewa tsaye ya ce, "Soon zan fara rage wannan kunyar domin tayi yawa Raudahta,bari na je na ɗan huta a ɗaki kafin Baban ya dawo na same shi da maganar,domin na ƙosa ki zama mallakina tun kafin wani ya kutso ya zame mini barazana." Raudah ta dubeshi wani irin abu na dukan zuciyarta,cikin sanyin murya tayi masa fatan hutawa lafiya tana riga shi shigewa cikin ɗakinsu.Ya bi bayanta da kallo yana jin yadda ƙaunarta ke sake rassa a cikin zuciyarsa,gangar jikinsa na cigaba da amsar wani irin gagarumin feeling da bai taɓa jin hakan akan kowace mace ba sai Raudan.Ya juya ya fito daga ɗakin yana baza idanunsa a tsakar sasan ko zai hangi Umma,ganin babu alamunta sai ya fice ba tare da ya nufi ɗakin Anty Amarya ba.Sam matar bata kwanta masa arai ba,kuma ko kaɗan baya ƙaunar alaƙarta da Innarsa tunda ya fahimci cewa ita ɗin ba ƙaramar hatsabibiya bace,wacce ke taka rawa wajen sake lalata Innarsa da banzayen ɗabi'u da shaiɗana kala-kala.

Yana fitowa daga cikin sasan sukai kaciɓus da Baba Lawal a waje,dawowar daga ƙofa kenan ya je duba wasu awakai da aka kawo masa daga Nijar.Yaya Sadeeq ya gaidashi da ladabi sosai,Baba Lawal ya amsa gaisuwar da fara'a yana ɗaurawa da faɗin, "Sannunku da zuwa Abubakar,Allah ya yi albarka ya kawo babban rabo da kuma abokiyar rayuwa ta gari." Yaya Sadeeq ya amsa yana sadda kansa ƙasa kaɗan ya ce, "Baba zuwa anjima idan kana free akwai maganar da nake so muyi da kai." Baba Lawal ya jinjina kai ya ce, "To shikenan Saddiku babu damuwa,Allah ya kai mu lafiya ina nan daga nan har la'asar babu inda zan sake fita In Sha Allah!" Daga haka Yaya Sadeeq ya wuce zuwa ɓangarensu shi ma Baba Lawal ya shige sasan nasa yana tunanin wata magana ce Sadeeq ɗin ke son yi masa?

"Baban Raudah baka bada kuɗin karin safe ba,yanzu ina so nayi mana tuwan shinkafa ne ka bani kuɗin cefanen rana don Allah!" Umma ce ke wannan maganar tana zaune daga bakin ƙaramin gadon da ke ɗakinsa.Ya ɗago kai ya dubeta ya ce, "Halimtu ki yi haƙuri ki ranta a aljihunki ku yi cefanen,kuɗin jikina na kwashe na sallami wanda suka kawo mini awakan dana faɗa miki za a wuto dasu daga maraɗi,ragowar dubu ɗaya ce kuma na ba Safiya suyi cefane tunda na san ke kina da abin yi da za ki iya juyamin kuɗin kafin na samu." Umma ta jinjina kai ƙasan zuciyarta na mata wani irin zafi da ƙuna,amma a zahiri murmushi ta sakar masa tana faɗin, "Shikenan babu damuwa,Allah ya cigaba da rufa asiri." Daga haka bata ƙara tofa koda kalma guda ba ta baro masa ɗakin.Tana tafe zuwa ɗakinta ne zuciyarta na mata zafi ainun,domin wannan ɗabi'ar da ya ɓullo da ita na rashin bata kuɗin cefane ya fara damunta.Baya cikin mazan da suka rasa, ko basu da sana'ar da zasu iya ci da Iyali,daidai gwargwado Allah ya gama hore masa domin ba ƙaramin samu yake yi da sana'ar Itace da sayar da Dabbobinsa ba.Ita ce kaɗai yake ganin ƙwanjin ya ɗauki ƙwandala ya basu kuɗin cefanen da zasu ci abinci ita da Yaranta,kullum sai dai ya bai wa Safiya ita kaɗai,su kuma ya kawo uzurinsa ya ce bayi dashi a ranta masa.Rancen da ba zai taɓa sake tada zancen ba bare aje ga maganar biya,ta mance rabon da ya ɗauki naira biyar ya basu suyi cefane bare kuma abin karin safe.Duk daga aljihunta take yi,idan bata dashi Raudah da ke da sana'ar yi ita ce mai bayar da kuɗi a sayi abin karin safe ko ta fita da kanta tayo musu cefanen da zasu girka abincin rana.Da zaran ya raba hatsin ya basu daidai da tauraruwar zuciyar tasa shikenan su ya gama dasu,duk wani kuɗi da za a kashe wajen sarrafa hatsin sai dai su gani a hannun Anty Safiya amma ba dai su ba.

Da wani irin ɓacin rai ta nufi ɗakinta tana mai zama daga bakin gadonta hawaye na cika idanunta,ba kuma hawayen komi bane sai na tausayin ƴaƴanta mata.Tabbas bata so a rama dukkanin rashin adalcinsa da zunubansa akan ƴaƴansa,domin haka Ubangiji ya faɗi cewa,duk abinda ka aikata akan ƴar wani tabbas kai ma zai zo ga taka ƴar.Ta janyo jakarta domin duba ƴan canjin da ke ciki sabida bata da wadatan kuɗi duk ta kashe cinikinta a hidimar asibitin Raudah,dama kuma ciwon yazo ne a daidai lokacin da ta kwashe dukkanin kuɗin hannunta ta saro kayan masarufin da take siyawar.Ɗan cinikin da suka yi ta tattaru suka nufi asibitin dasu,kuma cikin hukuncin Allah kuɗin duk suka wuce ba tare da Baban Raudah ya biya sisin kwabon sa ba.Naira ɗari biyar ta zaro cikin jakar,baya ga ita babu komi sai naira ashirin.Ta kasafta kuɗin tas ta ga ba zai ishesu cefanen ba,duba da yadda komi ya tsauwala a halin yanzu.Kayan miyan girkin kansa wuya yake yi,ta yadda cin miya ma sai mai hali da rufin asiri.Ta fito daga ɗakin riƙe da kuɗin ta nufi ɗakin su Raudah,ita kaɗai ta samu a ɗakin Sumayyah na can bayan ɗakunansu tana wankin kayan makaranta da za a koma hutu a ranar monday.Ta dubi Raudah da ke kwance tana danna waya ta ce, "Raudah tashi zaune." Raudah ta aje wayar tana tashi zaune tare da maida dukkanin hankalinta kan Umman.Umma ta ce, "Za a samu ɗari biyar a wajenki?" Raudah ta jinjina kai wani abu mai nauyi da danne zuciyarta,domin tunda ta ji Umma tayi tambayar ta gane yau ma ɗin dai bai basu kuɗin cefanen ba kenan.Da wani rawar murya ta ce, "Akwai dubu ɗaya Umma,bari na baki kawai ki riƙe a hannunki." Umman ta girgiza kai tana faɗin, "Sai dai ki amshi ɗari biyar ɗin ki bada dubu ɗayan Raudah,ki saka hijab ki je ki yo mana cefane tuwo nake son muyi na farar shinkafa saiki haɗo da ledar rufe tuwan." Raudah ta jinjina kai ta ce, "To Umma,bari na tashi na gani ko zan iya fita a ranan nan." Umma da shaf ta manta cewa Raudah ragowar ciwo ce da bata jima da samun sauƙi ba sai tayi saurin dubanta ta ce, "Na manta ne Raudah,kawo kuɗin Sumayyah ta tafi,idan ta dawo ta kammala yin wankin,ko kuma idan ta kammala sai ke ki daure ki shanya muku tunda na ga har da hijaban da ki ke fita da su zuwa makaranta." Raudah ta jinjina kai ta ce, "To Umma bari na zaga bayan na gani." Daga haka ta miƙe tana gyara zaman ɗankwalinta da ya zame,sassalkan gashinta irin na Umman baƙi mai cika da tsayi ya bayyana a sarari.Ta maida ɗankwalin ta ɗaura sosai tana saka silifas ɗinta ta fito daga ɗakin,can bayan ɗakunansu na duka gidan ta nufa.A nan ne da rijiya da kuma manyan igiyoyin shanya da suke shanya kaya idan sun wanke,babban fili ne sosai a wajen da ko kiwo aka so yi za a iya yi ba tare da takura ba.Daga gindin rijiyar mai albarka da idon ruwa sosai ta hangi Sumayyah nata faman ɗauraye musu kayan da ta kammala wankewa,Raudah ta isa wajenta tana faɗin, "Sannu Sumy,Allah baki miji nagari,gaskiya kin yi saurin kammala wankin." Sumayyah ta kashe Raudah da smiling tana faɗin, "Ameen Yaya Raudah,ke ma Allah barki da masoyinki Yaya Deeku." Raudah ta rausayar da kai tana faɗin, "Riƙa cewa idan da alkhairy Sumayyah,domin soyayyah ba shi ne ba, alkhairy muke nema da kuma zaɓin Allah ba abinda zukatanmu ke so kaɗai ba." Sumayyah ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce, "Hakane Yaya Raudah,Allah ya yi mana zaɓi mafi alkhairy Ameen." Raudah ta ce, "Sumayyah je ki Umma na kira za ki yin cefane,ni zan ƙarisa ɗaurayan na shanya." Sumayyah ta kammala ƙarisa ɗauraye hijab ɗin ƙarshe wanda yake mallakin Raudah ne,sannan tayi mata sai ta dawo ta baro wajen."

A hankali Raudah ke cigaba da ɗauraye ragowan kayan har ta kammala,tana yi tana tunanin yadda za ta shiga FCE ranar monday da wannan jikin nata da sam take ji kamar bata da ƙwari.Aji huɗu suke a kwalejin FCE da ke Zaria ita da Aliya da Zainab,domin dukkaninsu basu amince su zauna da jahilcin rashin zurfafa karatu kamar yadda su Baba Lawal suka yi sakaci ba.Shiyasa Baba Auwalu da ya yi zurfin ilimin yafi su sanin daɗinsa,shi ya jajirce wajen ganin anbar su Raudah sun ɗaura karatunsu bayan kammala sakandiri.Da fari aure Hajjah Kakah ta so ayi musu ya soke wannan maganar,ya nusar da ita cewa duka nawa suke da za a ce za a yi musu auren wuri ba tare da sun samu abinda suka samu a bokon da muhammadiyan baki ɗaya ba.Da yake a kwalejin FCE ɗin yake ya kuma kai wani matsayi shi ya shiga ya fita ya samo musu admission,ita kuma Gwaggo Shatu ta ce ta ɗauki nauyin biya musu kuɗin registration har su kammala.Tana da wannan ƙoƙarin da aikin zumunci ba tare da ƙyashi ko duba ga baƙar halayya da tsanar da Hajja Kakah ta nuna musu a baya ba,ko kaɗan idan tayi nufin alkhairynta yi take kai tsaye

Please Login or Register in order to submit comment