Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin rashin chajin chaji yake sabida jin kid'a,ita da dankwalli kuwa dama sai dai in zata je unguwa,itama tunani ta hau yi yanzu akan wayanan 'yan dalilan sai aljana ta sako ta agaba,bata ga arna dake yawo ba dankwalli ga Karin gashi da suke da chineke suke Shiga band'aki su fito da chineke sai ita aljanar zata takurawa,ita bata yarda akan haka Aljana ke takura mata ba,To Abdulmajeed da ta takura wa fa shi kidan yake ji ko dankwalli shima zai sa ya d'aura kansa,sam bata yarda wanan dalilin ne yasa aljanar take bibiyarsu ba,mugunta ce kawai,Nasiha shima Mallam Hashimu yayi mata na inta San duk abinda ya zayyano tana yi to ta daina Dan duk hanyo yi ne da aljanu zasu iya takura mutum.








B'angaren Abdulmajeed kuwa yana zuwa gida ba zarce ko Ina ba sai band'aki Dan Allah Allah yake ya k'araso gida,sai da ya samu Minti goma aband'aki kafin ya fito,wajen Mahaifiyarsa ya nufa dake Palo a zaune tana kallo,,sallamar da ya yayi ta amsa ta zuba mishi ido har ya zauna,ganin shi tayi awani hargitse, jiran tace " Abdulmajeed lafiya kuwa naganka haka yasu Muhibbar,"?

"Umma ina fa lafiya Aljana ta sako ni agaba na rasa mai nayi mata,yanzu ma da naje gidansu Muhibba sai da ta biyoni,bansan mai nayi mata ba,ni bani na bud'e mata k'ofa ba amma ni ta sako agaba, yanzu a haka zan na fita tana tsorata ni sai dai kawai aga ina gudu,sai kace mahaukaci Dan babu Wanda yake ganinta sai ni kadai"',Abdulmajeed yace cikin tsanin damuwa da tashin hankali,Hafsa shiru tayi ta kasa Magana Dan abun yanzu ya wuce tunaninta,to wai mai yasa aljanar ta daina bibiyar Muhibba ta koma tana Bibiyar Abdulmajeed,kwantar masa da hankali tayi tace ya bari Abbansa ya dawo zasu nemi mallami suyi mishi bayanin abinda ke faruwa.






Abu kamar wasa ya zama gaske,Dan babu dama Abdulmajeed yafita sai anga ya dawo da gudu,Dan Duk inda yayi sai yaga aljanar,dai dai da makaranta da ya shiga Dan ya koyar da dalibai sai da ta bi yo shi,yana tsaka da koyar da Maths ya hangota acikin dalibai wanan Karin a sifar yara ta bayyana,Abdulmajeed bai San lokacin da ya wurgar da chalk d'in hanunsa yasa gudu ba,daliban kuwa ganin Mallaminsu ya diba aguje yasa suma suka rufa mishi baya, makaranta tuni ta hautsine dalibai suka ringa tik'ar gudu a bakin titi,Jamaar gari hankalinsu ya tashi da su ka ga yanda dalibai da mallamai ke zuba gudu a bakin titi,Abdulmajeed da k'yar ya k'arasa gida, yana shiga gidan yaga aljanar abakin k'ofa a tsaye,ja da baya ya fara yi yana " wai mai nayi miki kike bibiyata?,mai kikeso awajena? Mai yasa kike San ki cutar dani?






Wani mahaukacin dariya ta kwashe dashi cikin yanayinta na ban tsoro ta fara nufar shi tana " Abdulmajeed Baka ga komai ba tukuna ba dai ka iya wulak'anta mutane ba,zan koya maka hankali,gobe Idan kaga wani bazaka k'ara marmarin wulak'an ta shi ba, ahaka zan ta bibiyarka har sai ka kusa zaucewa",




Abdulmajeed fad'uwa yayi kasa sumamme sakamakon ganinta da yayi akusa dashi.






Readers wai shin wane wulakanci Abdulmajeed yayiwa aljana take bibiyarsa Ku biyoni sadnaf kusha labari apage 10 kuma na karshe insha Allahu kunsan na gaya muku labarin bashi da tsayi.
[9/22, 12:18] Sadnaf: πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭





*Written by*
πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž






PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l



*TRUE LIFE STORY*


πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭





*Written by*
πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž






PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l



*TRUE LIFE STORY*



Aunty Fannah kisa



*#[email protected]*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


PAGE 10
πŸ”š



*Wanan shafin na sadaukarwa dumbin masoyana masu K'aunar novel d'in daga taimako hakika naji dadin irin k'aunar da kuka nuna min Allah ya barmu tare,kamar yanda na fad'a muku labarin daga taimako ba labari bane mai tsayi,gajeran labarine Wanda yake k'unshe da fadakarwa da kuma Nishadi,ba tsayin novel ke nuna had'uwarsa ba abinda yake kunshe dashi shi ke nuna novel ya had'u,Alhamdulillahi anan nazo Karshen novel d'in daga taimako kuskuren da nayi a ciki Allah ubangiji ya dubeni da idon rahama ya yafemin,darasin dake ciki Allah yasa Al umma su amfana*❀❀❀❀❀❀





*Whuuuuuuh Pure moment of life writers,takun ku daban yake Dana kowa ina mugun ji daku,domin da bazarku nake rawa Allah ya d'auka ka wanan Kungiya tamu ya k'ara had'a kawanunmu,kai kubani kid'an 'yan pure Asama,because they don't just entertain they touch,educate and melt the heart of the readers love you oll* ❀❀❀❀❀❀❀❀ _up up up pure moment may the sky be your limit_πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ








*Aunty sis* πŸ’žKai kai kai kai kaiπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Ni *Auntysis*πŸ’žnayi daria harda ciwon ciki

Masha Allahu

*Sadnaf* writer daya tamkar da dubu

Ya salam
Gaskia na dade banyi ma novel daria irin haka ba tin daga zamanin iffatu har zuwa yanzu..

*Sadnaf* mai salo kala kala
Kinzo mana da sabon salo ma wannan karan.
Farko munji tsoro sosai da sosai sbd yadda kike firgitamu har cewa nayi na dena karantawa sai daga baya kuma abun ya zama na daria ba kadan ba..gaskia kin samu daria kin sakamu nishadi mara misaltuwa..jz bil jannah



All hakika yawan page na novel ba shi bane dadin littafi ko maanarsa ba, novel na maana da dadi akan abinda ya kunsa ne kuma ya koyar da al-umma wani muhimmin darasi na rayuwa. Komin kankantarshi kuwa.

*Aljanu gaskia ne sbd Allah ne ya haliccesu harda surarsu cikin Al Qurani mai girma(suratul jinn)* *_sannan suna shiga jikin dan Adam musamman jikin da babu kariyar al-qurani da ambaton Allah._*

_Ya kamata mu kiyaye duk wata hanya da jinnu zasu iya shiga jikinmu har su firgita mana rayuwa_

Duk da lbrn nan true life story ne amma nayi imani *Sadnaf* ta baje basirarta wajen tsara shi don yayi dadi kuma sakon da take son Isar ma jamaa ya iskesu ta hanyar da zasu ji dadin fahimta.


Tabbas dunia makaranta ce, Abdul Majeed ya hadu da babban karatu mai kyakkyawan darasi na sharrin *wulakanci* dama haka rayuwa take,ka zauna kana wulakanci babu ji babu gani,insha Allahu wata rana sai Allah ya hadaka da gamonka tun a dunia.
Allah ubangiji ya karrama dan Adam a cikin dukkan halittun da yayi na dunia. *Kai waye da zaka wulakanta shi kuma kayi tunanin Allah zai barka a haka* ??????????

Ya kamata mu saka hattara a rayuwarmu musamman haduwar nan da muke ta social media wadda ba sanin juna mukayi ba,bamu san dawa muke zaune ba, wata rana wani zai maka yanzu ko nan gaba,ina Allah zai hadaka da mutun nan gaba,wace irin alfarma zaka nema ko a nema a wajenka. Wadan nan duka abun dubawa ne idan mukayi laakari da cewa duniar kanta is a small place. Ya kamata mu rage wulakanta juna, mu fahimci juna mu zauna lfy kodon rashin sanin dawa muke zaune, *idan ba haka ba mutum yayi irin na Abdul Majeed*

Sakaci da addua shine babban matsalarmu a yanzu tsabar yadda muka sa dunia a gaba.
Ya kamata mu dage da Azkar na safe da marece don neman tsarin Allah akan dukkan wata azzalumar halitta.

Zama ba kallabi,shiga bayi anyhow, yawan kide kide a cikin gd daga safe har marece duk hanya ce ta gayyatar aljanu,maraba da su da basu kyakkyawan wajen zama a gdnka da jikinka.


Fatan alkhairi nake maki da zuriarki baki daya
Allah yasa kifi haka
Allah ya kara baseerah da kaifin ido.


*Much luv daga Auntynki*πŸ’ž




K'arar fad'uwar Abdulmajeed dasu Mallam isah suka ji ne yasa suka yo hanyar waje dagudu,abakin k'ofa suka ga Abdulmajeed akwance,sallati suka yi Mallam Isah yayi Sauri ya d'agoshi yana k'iran sunansa,Hafsa da sabida gigicewar da tayi bokitin ruwa ta kinkimo,ta fara watsa mishi,dogon ajiyan zuciya Abdulmajeed yaja ya bud'e idonsa ahankali,kuka ya fashe dashi yana " na shiga uku na lalace Abba aljanar nan tana so ta zautar dani,ni da mai tab'in hankali babu maraba,tace na mata wulak'anci haka zata yi ta bibiyata Abba Dan Allah Ku taimaka min Ku rabani da ita " Abdulmajeed yace yana k'ara fashewa da kuka,Hafsa da tunda Abdulmajeed ya fara magana itama take kukan Dan Tausayin d'anta take ji jarumi irin Abdulmajeed yabi ya rame ya susuce kamar bashi ba, Magana ta fara yi tana " Mallam Dan Allah mu kai Abdulmajeed gun wani Mallamin ba sai mun jira dawowar Mallam Saminu mai Rukiyya ba, idan muka ce zamu yi ta jiransa bamu San ranar dawowarsa ba gashi aljanar nan kullum sai ta tsorata shi,ba dama ya fita sai ya dawo da gudu,in bai suma ba zai tafi band'aki,wanan Masifar da mai tayi kama," Hafsa tace tana k'ara fashewa da kuka,



"Hafsa bazaki gane ba,Mallam Saminu mai Rukiyya shi kadai ne zai iya raba Abdulmajeed da Aljanar dake bibiyansa Dan yana aiki da aljanu,amma duk inda zamu je sai dai aci kud'inmu yanzu kinga Mallam Jamilu da ya zo cemin yayi na kawo dubu ashirin ya rabashi da aljanar Dan ta aureshi,kiji fa,amma idan wajen Mallam Saminu mai Rukiyya muka kai shi kud'in sadaka kawai zamu bashi,ya kuma rabashi da aljanar,tunda kinsan shi yayi wa Ainau addu'a ta samu sauki" Mallam Isah yace cikin tsanin damuwa



" Hafsa share hawayen da ya zubo mata tayi tace " to shikenan Mallam yanzu yaushe zaka koma Gidan Mallam Saminu mai rukiyyar,ka duba kaga ko ya dawo"?



"Ai basai naje gidansa ba inada Numbers zan kirashi naji yaushe zai dawo,Abdul tashi mu Shiga ciki kaji Insha Allahu,zamu rabaka da aljanar",Mallam Isah yace yana mik'awa Abdulmajeed Hannu daya yi Shame shame akasa yana zubar hawaye,Abdulmajeed Mik'ewa yayi,suka shiga ciki,jin ana kiraye kirayen sallah ne yasa yaje yayi alwala ya nufi massallaci Dan tun daga lokacin da aljana ta sako shi agaba ya daina wasa da sallah




Muhibba kuwa tundaga lokacin da Abdulmajeed yazo gidansu ya tafi take ta kuka gabad'aya ta rasa mai ke mata dadi,ta rasa mai yasa aljana take bibiyar ita da Abdulmajeed,laifin ne Dan ta taimaka mata,ahaka Muhibba ta wuni tana kuka,sai da ta ga ba kukan shine Mafita agare ta ba,addua ya kamata ta dage ta ringa yi Na Allah ya rabasu da aljanar ya karesu daga sharrinta,Da wanan tunanin Muhibba ta dage da addua ba dare ba rana akan Allah ya rabasu da Aljana dake bibiyarsu,ayau kwana hud'u kenan rabonta da Abdulmajeed ko awaya bata samunsa,hakan kuwa ba k'aramin damunta yake ba,shawara ta yanke zata je gidansu taji ko Lafiya.






K'arfe uku na rana ta nufi band'aki tayi wanka ta d'aura alwala,tafito tazo gaban mudubi ta fara shiryawa Dan so take tana idar da sallar la'asar ta tafi gidansu Abdulmajeed,tana cikin shafa hoda ta hango wanan aljanar abayanta ta zuba mata ido tana kallonta,Muhibba duk da ta tsorata adduoi ta ringa yi azuciyarta ta d'aure ta fara magana Dan ta sha alwashin indai aljanar ta k'ara bayyana bazata gudu ba,zata tsaya ta tambayeta mai takeso awajensu take bibbiyarsu,cikin jarumta da rashin tsoro Muhibba bakinta d'auke da ayatul kursiyyu ta juya abun mamaki bata ga aljanar ba amma da ta juya ta kalli Mudubin aljanar na nan a tsaye,bata tsorata ba ,tace "mai yasa kike bibiyar ni da mijina? Mai muka miki ? Laifine Dan na taimakeki?


murmushi aljanar tayi da ya k'ara sa ta zama abun tsoro hak'oranta mai kama da na allura ya bayyana cikin Muryar da tafi kama da sauk'ar aradu ta fara magana " baki min komai ba Muhibba,laifin mijinki ne ya shafeki,banida niyyar in cutar dake,hasali ma sanki nake yi,Dan gashinki na burgeni,wak'ok'in da kike sawa awaya yana sani nishadi,Dan abinda ke kawoni gidanki kenan,ba abinda yafi burgeni dake kamar in kika shigo band'aki naga kina d'an wak'a gashinki a bud'e ,ni sanki nake yi ,Mijinki ne dai ya min laifin domin ya wulak'antani,ya mareni akan nace ina sansa ,ya koreni Dan naje bara,ya zageni Dan naje gidansu neman taimako ,Dan haka sai na rama abinda yamin,"



Muhibba da jikinta ke rawa sabida muryarta ba k'aramn tsoro ya bata ba,tambayarta ta ke so tayi mai Abdulmajeed ya mata ta b'ace,addua tayi,ta cigaba da kwalliyarta,k'arfe hud'u saura ta fito daga gida ta nufi gidansu Abdulmajeed.

Atsakar gida ta samesu a zaune Abdulmajeed na kwance akan tabarma,yana jin karatun Qurani,Mallam Isah da Hafsa na daga gefensa,sallamar da tayi suka amsa,Abdulmajeed ya d'ago yana kallonta,Dan ayanzu haka ita yake tunani Dan yayi missing d'inta sosai amma ba dama yaje gidansu Dan yana fita aljanar zata kunya ta shi ta sa shi gudu abakin titi ko ta sa shi sakin fitsari a wando,Muhibba durk'usawa tayi tana gaishe da su Mallam Isah idonta akan Abdulmajeed da ya tsura mata ido,gani tayi yabi ya rame kamar ba shi ba ,take taji hawaye na Neman zubo mata sabida tausayinsa da ya rufeta,Wai Abdulmajeed d'inta da baya tsoro ba yasan wargi,shine ya zama haka abun tausayi,amsa gaisuwarta su Mallam Isah sukayi suna tambayarta ya mutanen gidan,ce musu tayi lafiyarsu kalau,dama taji Abdulmajeed shiru ne kwana biyu shine tace bari tazo taga ko Lafiya,ashe ma bashi da Lafiya,Dan duk a tunaninta Abdulmajeed bashi da Lafiya,Hafsa cewa tayi ina fa lafiya Aljana ta sako Abdulmajeed agaba tana Neman zautar dashi,bashi da aikin da wuce gudu, da zuwa band'aki,tausayin Abdulmajeed ne ya k'ara rufe Muhibba tace musu ba abanza Aljanar ke bibiyar Abdulmajeed ba,laifi yayi mata,zaro ido suka yi suna kallonta, Abdulmajeed yayi sauri ya zauna yana tambayarta wane laifi yayiwa Aljanar da zata sako shi agaba,ajiyar zuciya ta sauke ta fara basu labarin abinda Aljanar ta gaya mata,ak'arshe tace " Abdulmajeed zaka iya tuna wacce ka mara Dan tace tana sanka,zaka iya tuna wacce tazo bara gidanku ka koreta?zaka iya tuna wacce tazo Neman taimako ka zageta"? Shiru Abdul majeed yayi,yana tunanin wa ya tab'a Mara dan tace tana San shi,sai da yayi tunani mai zurfi kafin ya tuna,ya tab'a zabgawa wata mari da ta dage tana sanshi,



*WAIWAYE*

Lokacin da Abdulmajeed ke zuwa high institution ,Dan gayu ne na k'arshe yana mugun ji da kansa gani yake yafi k'arfin ,yan matan makarantar,Dan aganinsa babu ajinsa a cikinsu,Dan ba laifi 'yan mata suna sanshi, hakan ne yasa ya d'orawa kansa Girman kai yake wulak'anta 'yanmata,abokanansa suyi ta mishi wa'azi,watarana suna zaune ak'arkashin bishiya suna hira da abokanansa,d'aya daga cikinsu yake basu labarin yarinya da yakeso a ajinsu,Abdulmajeed dogon tsaki yaja yace wa abokin na shi, yayi asara ya rasa wacce zaiso sai wanan bak'ar hallitar mumuna, Aljana da tafito shawaginta tana saman bishiya tana jinsu,jin abinda Abdulmajeed yace ne yasa ta rikid'e ta koma mutum, a mumuna siffa,Wanda sabida muninta bazaka so ka k'ara ganinta ba,gata bak'a wuluk,taho wa tayi daga nesa ta nufi inda suke,abokanan sa kuwa dama suna da kallon mata,hangota da suka yi daga nesa ne yasa suka fara gulmarta suna cewa basu tab'a ganin mai muninta ba,duk abinan da suke Abdulmajeed bai d'ago ba yana dai jinsu,ganin da suka yi wajensu ta nufa yasa suka ja bakinsu su kayi shiru suna mamakin wajen wa zata zo,tana isa wajensu ta saki murmushi tana gaishe su kasa amsawa sukayi sakamakon tozali da suka yi da hakoranta jajjaye da ya k'arawa fuskarta muni,Sagir ne yayi k'arfin hali ya amsa gaisuwarta yana tambayarta mai take nema awajensu,murmushi ta k'ara yi tace wajen Abdulmajeed tazo,Abdulmajeed d'agowa yayi da sauri Dan duk abinda ake kansa a sunkuye yake,tozali da yayi da fuskarta ne yasa yaji wani zafi a zuciyarsa,Dan arayuwarsa ya tsani munana,gani yayi ma ta raina mishi hankali yama zaayi tace wajensa ta zo,cikin had'e rai yace mata lafiya tak e nemanshi,batare da wani b'ata lokaci ba tace mishi sanshi take yi,abokanan Abdulmajeed k'yalk'yale wa suka yi da dariya da suka ji abinda tace,Dan sun San Abdulmajeed ya tsani mumunar mace,dariyar da suka yi ne ya tunzura Abdulmajeed ya zabga mata lafiyayyun mari guda biyu,yace shi sa'arta ne da zata ce tana sanshi,in taga level d'inta bata sani ba,zagi ya rufeta dashi,Aljana ta durk'ushe akasa tana kuka,zaginta ya cigaba da yi kamar zai daketa Dan ma abokanansa na rikeshi,mik'ewa tayi ta goge hawayenta ta ce Dan ta ce tana sanshi shine zai mareta,d'aga hannu zai k'ara marinta su sagir suka yi sauri suka rik'e mishi hannu,girgiza kai tayi tace yaje zai gani,da zagi ya bita har tabar gurin,tun daga lokacin Aljanar nan ta ringa zuwar wa Abdulmajeed a siffar mutane,yana wulak'anta ta,a almajira taje gidansu,yana tsakar gida yana cin abinci,Almijira ta ringa zabga bara tana a taimaketa Dana abinci yunwa take ji,sai da ta kai minti talatin tana bara,Abdulmajeed ko d'agowa bai yi ya kalleta ba,ganin da yayi ta cika mishi kunne da bara ne yasa ya mik'e afusace ya koreta yana ce mata mayya sai kace dole,Aljana kuwa ta k'ara zuwa gidansu daddare yana zaune a k'ofar gida wata tazo Neman taimako wai bata da kaya ataimaka mata,ganin Abdulmajeed bai kulata bane yasa ta fara k'ok'arin shiga gidan,tsawa ya daka mata yace mata ajiya ta bawa mutanen gidan zagi ya rufeta dashi na uwa na uba ya koreta,Aljana kuwa tana tafiya ta sha alwashin sai ta rama abinda Abdulmajeed ya mata itama ta zautar dashi,wanan kenan.
Da sauri Abdulmajeed yace ya tuna wacce ya tab'a zabgawa mari,girgiza kai Muhibba tayi tace mishi


"To ba mutum bace Aljana ce,sallati su Mallam Isah suka yi suna sun shiga uku Abdulmajeed kuwa jikinsa ya fara rawa Dan ya tuna tace yaje zai gani,

Muhibba k'ara tambayarshi tayi ko ya tuna almajirar da tazo bara da kuma wacce tazo Neman taimako,?Abdulmajeed sai da yayi tunani mai zurfi yace ya tuna,nan ma Muhibba tace mishi Aljanar ce,,


Abdulmajeed hankalinsa ba k'aramin tashi yayi ba,ya ringa kuka yana Dana sani,Mallam Isah kuwa jin fad'a ne tsakanin mutum da aljan ne yasa ya suri wayarsa ya k'ira Mallam Saminu mai Rukiyya,Mallam Saminu mai Rukiyya yace mishi dawowarsa kenan daga kauye,ai da sauri Mallam Isah ya ajiye wayarsa yace musu su zo su tafi wajen Mallam Saminu mai Rukiyya basu ga ta zama ba,ahaka suka dunguma suka nufi gidan Mallam Saminu mai Rukiyya ,basu samu ganinsa ba sai wajen Magriba,suna zama,yace suje suyi alwala su dawo,dukansu Alwala suka yi Muhibba kuwa sai addua take Allah yasa ya iya masu tsakani da Aljanar,bayan sun zauna yabi Abdulmajeed da kallo,gyaran murya yayi yace yasan mai ke tafe dasu, Dan Aljanar tariga su isowa wajensa ta gaya mishi duk abinda yafaru,Dan haka tace ya cire hanunsa a lamarin,Dan sai ta d'au fansar wulak'ancin daya yi mata,Sallati Suka yi gabad'aya Abdulmajeed kuwa ya saki tusa,kuka yasa yana ya taimaka ya bata hakuri ya daina ya tuba bazai sake ba,Mallam Isah da Muhibba ma rokon Mallam Saminu mai Rukiyya suka ringayi suna ya taimaka musu,ya bata hakuri,Mallam Saminu bai ce komai ba ya tashi ya shige d'akin sai da ya samu minti arbain kafin ya fito,ce musu yayi ya samu ta hakura dak'yar amma tace bata hakura gaba d'aya ba,zata rama nan gaba yanda masu hali irin nashi zasu daina,amma tace insha Allahu bazata k'ara bibiyarsu ba,Abdulmajeed hankalinsa ba k'aramin tashi yayi ba daya ji abinda Mallam Saminu yace,magana yake so yayi,Mallam Saminu ya dakatar dashi yace ya yi iya yinsa Dan haka yaje su dage da addua wanan kuma ya zame masa darasi,adduoi ya basu da shawarwari na hanyar da zasu bi su nisan ci kansu da aljanu,Godiya Mallam Isah ya mishi ya bashi sadaka suka fito.


A takaice washegari Abdulmajeed yaje gidansu Muhibba ya d'auketa bayan dogon nasihan da iyayen Muhibba suka musu,Dan Muhibba ta gaya musu komai suka nufi gidansu,suna isa Muhibba ta duro daga kan machine ta nufi gidan Surayya Dan tayi missing d'inta sosai,Surayya dake band'aki tana wanka ta bar k'ofar band'akin a bud'e dan tunda daga lokacin da su Muhibba suka tafi gidansu take cikin matsancin tsoro ko an kwankwasa k'ofa bata bud'ewa sai kayi magana tasan wanda ke kwankwasa k'ofa da yake Muhibba ta kagu taga Surayya buga gidan ta ringa yi da k'arfi, tuni Surayya ta wurgar da soson hanunta ta diba aguje,tayi d'aki ta ma manta tsirara take ta fara wa innahu Sulaimanu,sai da taji muryar Muhibba tana ta bud'e mata sanan ta d'aura zani taje ta bud'e k'ofar,rungume juna suka yi,suna murnar ganin juna atsaitsaye Surayya ta ringa bata labarin abubuwan da suka faru da bata nan,da irin gudawan da Abdulmajeed yazo yayi a gidansu, Muhibba in banda dariya babu abinda ta ringa yi tana rik'e ciki,anan itama ta bata labarin abinda yasa Aljanar take bibiyarsu,Surayya tsoro ne ya kamata tana Allah ya karesu daga sharrinsu.



A Daren Abdulmajeed a ango yake sak, Dan ya dirje Muhibba kamar kayan wanki to an kwana biyu ba ahadu ba, tun daga lokacin Abdulmajeed baya wasa da sallah da tashin dare,Muhibba kuwa kullum kanta a d'aure tana jin karatun Qurani.




Bayan shekara biyu Muhibba na asibiti tana nakuda,Abdulmajeed hankalinsa yabi ya tashi,sai kai da kawowa yake Dan tun cikin Muhibba na karami Allah ya jarrabce shi da San cikin,bayan awa d'aya da rabi da aka shigar da Muhibba nurse ta lek'o tace Abdulmajeed yazo yaga jaririya matarsa ta sauka lafiya,da saurinsa ya nufi d'akin,har yana Neman yayi tuntub'e Surayya na biye dashi abaya,Gani yayi Muhibba ta kau da kanta, bata kallon inda jaririyar ke kwance,bai kawo komai aransa ba,ya nufi inda aka kwantar da jaririyar,abinda yagani ne yasa yaja da baya,jaririyar bak'a ce irin k'irin d'inan,gata katon kai ne da ita, muni iya muni wanan jaririyar ta had'a,cikin tashin hankali,ya d'ago zai yi magana,Muhibba tayi sauri ta ce yayi shiru,anan ta tuna mishi abinda Aljanar tace na zata rama,shiru yayi bai ce komai ba.



A takaice duk Wanda yaga jaririyar da Muhibba ta Haifa sai ya girgiza,ahaka aka lallaba akayi suna Muhibba ta cigaba da kula da jaririyarta Dan ita bata k'i jaririyar ba,Abdulmajeed kuwa shima haka ya ringa ririta jaririyar Dan yasan abinda ya shuka shi ya girba.



Ahaka Muhibba ta k'ara haihuwar yara hud'u amma kyawawa Zainab ce dai ta banbanta acikinsu wato ta farin, Dan muni kamar ayanka a b'oye,Abdulmajeed kuwa tunda ga lokacin ya daina wulak'anta mutane,duk wanan zafin kan babu.




Anan na kawo karshen daga taimako kuskuren Dana yi aciki Allah ya yafemin.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment