Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

💞💕
💕💞💕
💕💞💕💞
💞💕💞💕💞


*_💋 TRIPLETS 💋_*
     *_( ROMEO )_*




*Story & Written*
           ⬇️
     *Star Lady*



The writer of
*DUK KARFIN IZZATA*    
And now
*_💋 TRIPLETS 💋_*       
     *_( ROMEO )_*


_Assalamu alaikum warahmatullahi taala wa barkatuhu masoyana masoyan *DUK KARFIN IZZATA* masoyan Hiyana da Brigadier general Safras ina muku fatan alkhari da godiya mai tarin yawa ba zan taɓa mantawa da kuba har kullun kuna rai na ya Allah ya tsaremin ku daga sharrin duk wani abun halitta_.

Da farko dai wanna littafi book 1 sadaukarwa ne ga My dear Amira My sister kuma my P.A😹ina kaunar ki lodi lodi 🥰


BOSS BATURE!!!much kauna 💖 masoyiya munarh much love ❤️

Kamar Yadda na fara littafin nan lafiya ina rokon Allah subhanahu wata'ala daya bani ikon Kammala shi lafiya Allah ya bani ikon faɗakarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaɗantarwa Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abunda bazai amfani al'ummar Annabi ba.

🤲Ya Allah ina rokon da ka tsaremum alkalami na daga rubuta abun da zai lalata tarbiyyar ƴa'ƴan mutane Allah ka bani ikon isar da sakon da nake son isar wa

*Gargarɗi*

_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a haɗamun document ko amin Edit Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_


San nan ina jiran daɗaɗan comments naku masu karamin karfin gwiwa ta hanyar daddaɗar comments naku ne zan iya gane ya kuka ɗauki littfin Ina godiya Allah ya bar zumunci 🥰

Share fisabilillah👏👏

Mai neman karin bayani ya min magana ta wan nan number 09162620621 or 09075846926 Please iya WhatsApp ban da kira



💋THE BEGINNING 💋

Let's get started


Episode 1

KATSINA STATE

Unguwar farin yaro

Misalin karfe 4 na yamma anguwar tayi shiru babu wani motsin kirki kyakkyawar yarinya ce Chocolate colour doguwa tana da kyakkyawar fiska ɗan ma dai dai ci mai ɗauke da dogon kyakkyawar hanci mai tsini har baka ga manya manyan dara daran idon ta masu design na kifi farare ne tas kamar madara masu ɗauke da dogayen gashin ido kamar wadda tasa eyelashes bakin ta ɗan karami dai dai da face nata lallausan laɓɓan ta launin pink color, lips nata nasama design of heart ne tana da baƙi lallausan saje kwance a gefen lalausan kumatun ta lallausan kwantaccen bakin gashi siɗif a goshin ta kamar na larabawa tana da gogayen yatsun kafa masu ɗauke da kunba (farce) farare tas kamar madara sanye take cikin blouse gown pink color mai bala'i kyau ta sanya ɗan karamin hijabi baki a kanta a shekaru bazata wuci 13 years ba kallon ɗaya zaka mata ka san tafito daga gidan hutu da jin daɗi amma sai dai ga fuskar ta ɗauke da bushesshen hawaye alamar tasha kuka. Rike dake da matches (ashana) a hannun ta kyakkyawar kafar ta na sanye cikin kyakkyawar flat shoe baki kalan hijabin ta kyakkyawar gaske ce dan idan nace zan tsaya zayyana muku kyan yarinyar nan to sai mu kwana mu wuni bamu gama ba dan ta ko ina ta haɗu.

Sauka tayi daga kan titin da take tafiya ta keta ta cikin wani lungu taci gaba da tafiya tana tangal tangal alamar ta gaji.
Dai dai zata shiga wani kwana wani matashin saurayi yace "Jimana ƴanmata" Juyowa tayi tana kallon sa zaune yake cikin motar sa kofar motar a buɗe ya zuro kafafunsa waje, Ji tayi kamar kar taje sai kuma ta tuna da zancen mum ɗin ta in da take cewa "Ba kyau wulakan ta ɗan adam dan baka san in da zaka haɗu da shi gaba ba" tuna hakan ya sanya ta nufesa tana ɗaure fuska.
Da ga ɗan baya ta tsaya da zazzakar voice nata tace "Gani nan" tayi maganar rai a ɓace fitowa yayi daga cikin motar ya juya gabas ya juya yamma lungun babu kowa shiru cikin sauri ya zaro handkerchief daga aljihun sa ya kaɗa mata a fuska, nan take ta yake jiki zata faɗi cikin zafin nama ya taro ta ya turata cikin mota gidan baya, ya shiga gidan gaba ya tada motar da gudun gaske ya fito daga lungun ya miƙi hanyan. Gudu yake zubawa sosai kamar zai tashi sama yara uku ne a cikin bayan motar da ita 4 dukkan su a sume kuma dukkan su mata ne.

Agogon Nigeria karfe 4:30pm ta buga.

Gidane ɗan ma dai dai ci mai ɗauke da ɗan ƙaramin kofar shigowa, bazaka kira gidan da gidan talakawa ba haka zalika bazaka kirashi da gidan masu kuɗi ba, za dai a sashi a layin gidan masu rufin asiri sai dai duk anguwar gidan tafi kyan gani da tsari da fasali. Ɗakuna biyu ne a cikin gidan sai yar karamar kitchen dake tsakar gidan ta ɓangaren hagu, daga gefen dama kuwa toilet ne awajen, gidan yana da ɗan filin tsakar gida mai ɗan girma.
Kyakkyawar mace ce zaune a tsakar gidan saman tabarma, kallo ɗaya zaka mata kaga jikin hutu ta mike kafa tana tsintar shinkafa a bai bai kana kallon yadda take tsintar shinƙafar kasan bata iya ba sanye take cikin dankareriyar lace baki mai ratsin ja hannun ta da wuyar ta sanye suke da sarkan gold mai matukar kyau da tsada farace tas kyakkyawa ajin farko, cikin sanyin murya ta ɗago kai tace"Jehan!! Jehan!!!"daga cikin ɗaki wata zazzakar murya ta amsa da "na'am Mum" "Kizo ki je ki dubamin Rimsha tun ɗazun da ta fita siyo matches bata dawo ba kin san dama ba wani sanin hanya sosai tayi ba, kiyi sauri dan mu samu mu ɗaura girkin nan yamma tayi sosai" "Mum ni gaskiya na gaji shekaran jiya fa tare da ita mukaje shagon na nuna mata hanya ba daman kince tafini ƙwaƙwalwa ba to sai ta gane hanya da kan ta ba sai na nemota ba ta dawo gida" tayi maganar cikin harshen turanci ta kai karshen maganar tare da fitowa waje daga cikin ɗakin.

```Jehan```
Kyakkyawa ce ajin farko farace tas doguwa mai kyakkyawar fuska dake ɗauke da dogon hanci har baka ga manya manyan idanun ta masu design na kifi farare tas kamar madara gashin idon ta dogaye a tsai tsaye bakin ta ɗan ma dai dai ci tana da lallausan laɓɓa pink color,sanye take cikin blouse gown pink color kanta ba ɗankwali ta zubo gashi har baya bakin kirin mai tsantsi da laushi an mata kananan kalba a kan nata a karshen kitson an sanya mata bit manya manya kowani kitso ɗaya bit uku aka sa idon ta abushe yake bata da tsoro ko kaɗan a shekaru ba zata wuce 15 years ba. Jehan yarinyace shagwaɓaɓɓiya a jin farko ga rashin tsoro iyayi rashin kunya rashin ji izza ba'a mata ta kyale rashin hakuri saurin fushi rashin son mutane.

***** "Ina ɗankwalin ki Jehan?" Cewar mum tayi maganar da ɗan karfi, turo baki Jehan tayi cikin shagwaɓa tace "Mum nifa nagaji da sanya ɗankwalin nan ni yanzu ma Mum fruits nake son sha" tayi maganar da harshen turanci "Jehan!! Jehan!!! Saunawa na kira sunan ki? Ki wuce kije ki sanya hijabi kije ki nemomin Rimsha kin san yarinyar nan ba in da ta sani tun da muka dawo nan bata taɓa fita ba sai shekaran jiya idan kika bari na mike Allah sai jikin ki ya gaya miki" "Kai Mum ni wlh kin takuramin yanzu fa mun kai 5 days da zuwa garin nan idan ma ban da dakikanci irin na Rimsha ko ba'a taɓa nuna miki waje ba ba zakije ki dawo ba bare mun taɓa zuwa to ni waye ma ya nunamin ba da kai na naje ba?" tayi maganar cikin kwaɓaɓɓiyar Hausar ta, Shiru Mum tayi bata sake cewa komai ba, ita kuwa Jehan waje ta samu saman dakalin soak away dake kusa da windon toilet ɗin ɗakinta ta zauna tana tura baki.

Wata kyakkyawar farar mata ce mai ɗan kiba ta fito daga cikin ɗaya ɗakin tana faɗin "Haba Jehan ɗin daddy yi hakuri kije ki dubo yar uwarki kinji idan ta ɓata fa? Ya zaki yi?" Tsaki Jehan taja kafin tace "Goggo ni fa I can't go anywhere ta ɓata mana ni ina ruwana da ita? Please Mum let's go back to our real house I don't like this house it's too local, I want to see my dad I miss him" Ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta nufi ɗaki tana faɗin "Tunda kun dame ni na shige ɗaki" kallon mum goggo tayi, yayin da mum ta ɗaure fuska tana zancen zuci "Koma me Jehan tayi baku kuka batata ba baku kuka mai data hakan ba" wucewa goggo tayi tabi bayan Jehan dan taje ta rarrashe ta miƙewa Mum tayi ta nufi kitchen tare da shinkafar da take tsinta.

Shiru shiru har karfe 6 na yamma gari ya fara duhu Rimsha bata dawo ba Mum ta fara tsorata ta ɗauko mayafinta ta fito wajen gidan dan ta dubo Rimsha kallon gabas tayi ta kalli yamma ita kan ta bata san ko ina ba a unguwar dan tun da suka zo bata leka ko kofar gida ba. A hankali ta zuro kafafunta ta fara takawa ta rasa ina zata bi Jehan ce kawai ta san unguwar chan ta hango majalisan samari suna zaune suna hira cikin sauri ta karisa wajen tare da yi musu sallama, cikin fara'a uku daga cikin su suka amsa mata Sallamar har suna haɗa baki, sauran ukun kuma fiska a ɗaure
"Dan Allah bayin Allah baku ga ƴata ba wallahi tun ɗazun na aiketa siyo ashana shiru shiru har yanzu kuma bata dawo ba mu sabbin zuwa garin ne batasan ko ina ba sai shagon shima sau ɗaya ta taɓa zuwa" ɗaya daga cikin sune ya miƙe yana faɗin "Kai subhanallah yadda siyasa ta gabato dinnan satar yara ake sosai kamar me ya Allah yasa ba gaba da ita akayi ba bari mu duba miki ita Mama ya take yarinyar ina nufin tsawon ta da kalar kayan da tasa tayu ko ta ɓata hanyane tun da sabon zuwa garin ne ku" da sauri Mum tace "Chocolate color ce shakarun ta 13 tana sanye cikin dogon riga pink color da karamin hijabi baki sunan ta Rimsha" "Yusuf, Sha'aban kuzo mu rabu mu duba ta ko Allah zai sa mu ganta Mama ke kuma ki koma gida idan mum ganta zamu kawota har gida kinji?" Mum bata da zaɓi dan in tace ba zata koma gida ba bata san ko ina ba bata san ta ina zata fara neman Rimsha ba dole tabi maganar Sadiq hakan yasa ta gyaɗa masa kai ala'mar to sanna ta wuce jiki ba kwari ta nufi gida zuba mata ido Sadiq yayi har sai da ya ga gidan da ta shiga sanna yace "Sha'aban Yusuf muje mu duba mata ƴar nata mana" a tare Sha'aban da Yusuf suka mike kallon sauran Sadiq yayi yana faɗin "Hafeez kufa muje mana me kuke jira" a gatsale Hafeez yace "babu in da zamuje gayyan soɗi neman gindin zama daga ganin baki har ka fara shishshige musu to dai kabi a hankali dan da ganin matar nan wlh batayi kama da talaka ba me ya kawota anguwar talakawa?" Shiru Sadiq ya yi bai sake magana ba ya wuce tare da Sha'aban da Yusuf suka kutsa cikin anguwar neman Rimsha.

Lokacin da Mum ta koma gida an fara kiraye kirayen Sallar Mangariba, a tsakar gida ta isko Jehan da goggo suna zaune wuce su tayi zata shiga ɗaki goggo tayi saurin cewa "Maryam lafiya ina Rimsha ɗin take?" Mum na kokarin yin magana Jehan ta rigata da cewa "Mum I'm feeling hungry I want to eat something very soft" Kallon Goggo mum tayi kafin tace "Aunty Aisha ya kamata ki sanar da Jehan yanzu fa mum shiga halin rayuwa ko mutuwa ne dan na lura tafi jin maganar ki batun Rimsha kuma bamu ganta ba yaran unguwar nan sun fita tayani neman ta" kallon Goggo Jehan tayi dan ita ba wani jin Hausa sosai take ba iya mum ce ka ɗai ke musu magana da Hausa sai kuma goggo da take musu kaɗan kaɗan time to time Daddyn su turanci da Larabci kawai yake musu" goggo where is Rimsha? I'm seeing like Mummy is not happy why is she talking like this everyday she's shouting and abusing me?" "Jehan you have to be very very careful now kina jina? Our life now and before is very very different" cewar goggo shiru Jehan ta ɗan yi kafin tace "okey na gane kaɗan now ina Rimsha take nake son sani kafin na tambayi Daddy" Hararar wasa Goggo ta mata kafin tace "Ba tun ɗazun akace kije ki nemo taba kika ki maybe ta ɓata hanya ne" Mikewa Jehan tayi ta nufi waje tana faɗin "Bari nayi checking nata mu gani ko zan ganta amma fa sai ta sha very very good slap idan na ganta dan ta ɓatan rai" ita dai Goggo bin ta da ido kawai tayi har ta fice.

Tana fita sukayi karo da su Sadiq suna kokarin shiga gidan "Who are those peoples kuma?" ta tambayi kan ta tare da ruke haɓa da hannu ɗaya ta tsaya a bakin kofar shigowa ta tare musu hanya, cikin nitsuwa sadiq yace "Sannun ki bari mu wuce" a wulakan ce ta masa kallon uku goma kafin tace "From where to where?" kallon su Sha'aban dake bayan sa yayi san nan ya dawo da kallon sa kan Jehan dake tsaye ta rike kugu tana musu kallon banza "Yi hakuri ni bana jin turanci kiyi magana da Hausa" cewar Sadiq dogon tsaki taja kafin tace "daga ina? kuma ina zaku je?" tayi Hausar a kwaɓe kallon ta Sadiq yake a ransa yana mai mai ta yadda ta kwaɓa hausar wai ita a dole tayi magana "wajen mamanki muka zo" cewar Yusuf, kallon wulakanci ta masa kafin ta musu nuni da hanyar komawa da hannu ta a wulakance tace "Ku wuce ku bani waje wasu dirty Boyz daku ne zakuce wajen Mum kuka zo to Mum ta muku me please leave this place before I open my eyes" ta kai karshen maganar tare da jan dogon tsaki tana tofar da yawu. Har ga Allah yadda take magana ba karamin tafiya da Imanin Sadiq tayi ba dan shi a rayuwar sa yana son mace mai izza tana burge shi sosai.

```Sadiq```
Sadiq matashin ne mai jini a jiki wadda ba zai wuce shakara 24 ba ba laifi yana da kyau dai dai gorgodo yana da hali mai kyau baki ne amma irin bakin nan mai shegen kyau yana da ɗan ma dai dai cin hanci da manya manyan ido

Fusata iya fusata Yusuf ya fusata da abun da Jehan ta musu yarinya yar karama zata tsaya tana faɗa musu magana cikin kunan rai yace "Yaya Sadiq muje dan Allah idan ba haka ba zan iya sumar da yarinyar nan" kallon banza Jehan ta watsawa Yusuf ba tare da tayi magana ba, juyawa Sadiq yayi yana kokarin yin magana, Mum ta fito dan duba su tun da taji shiru shiru gashi har an gama sallar mangariba, ganin mum yasa Sadiq ya ɗan sunkuyar da kan sa kasa dan tun da yaga Jehan ya ji ya fara jin kunyar mum "Mama wallahi mun duba bamu ga yarinyar nan ba" Salati Mum tasa tana kokarin yin magana Jehan ta rigata da cewa "They are lying Mum ina zata je da za suce basu gan taba" Yusuf ji yake kamar ya kwashe ta da mari dan haushi ita kuwa sai kallon rai ni take musu ko shakkan su babu a idon ta bare tsoro "Bayin Allah ina ne police station na ku bari na kai Report tun wuri, cikin nitsuwa da girmamawa Sadiq yace "Mama kiyi hakuri zuwa da safe sai muje amma da zakiji shawara ta da baki je police station ba dan last 2 weeks aka sace wata yarinya a nan kin san zaɓe ya kusa haka iyayen ta sukayi ta yawon zuwa police station ƴan sanda suna anshe musu kuɗi basa masu aiki kin dai san yadda kasan nan ya zama yanzu sai a hankali ba talakawan ba ba masu kuɗin ba kowa baya son gaskiya mafi yawancin su kan su kawai suka sani amai ma kon ki kwashi kuɗi ki kai wa yan sanda gwara ki ɗau kuɗin ki kai masallaci a sayi buta ayi sallah ayiwa yar ki addu'a sanna ki biya kuɗi a miki saukan Qur'ani mai girma dan Allah shi ka ɗai ne mafita, a yan kwana kin nan an sace yara zasu kai 3 a layin nan" Jin haka yasa hankalin Mum ya kara tashi sosai dan atunanin ta Rimsha sai dai ta kauce hanyar gida ta sauya hanya bata taɓa tunanin za'a iya sace ta ba amma jin bayanan Sadiq yasa hankalin ta yayi mugun tashi cikin ruɗu da fargaban in da Rimsha take tace "Yaro muje yanzu nan afara yi mata addu'a ka kai ni in da malaman ku suke mu baki ne a garin nan bamu san kowa ba" "Mama ki bari sai da safe mu kara dubata zuwa azahar tun da ku baki ne tayu ba sace ta akayi ba ɓata hanya tayi idan mun dubata gobe zuwa azahar bamu ganta ba sai mu fara rabawa malamai kuɗi su fara addu'a" shiru Mum tayi kamar mai tunani zafafan hawaye ne suka fara bin kuncin ta da yake wajen ya fara duhun mangariba su Sadiq basu lura da hawayen da take ba, ita dai Jehan sai kallon ban za take musu a duhu tana yamutse fuska tare da ɗage dogon hanci tan nan dan bata gane abubuwan da su Sadiq ke tattaunawa da Mum ba dan ba wani jin Hausar kirki take ba sama sama ta iya shi ma sai idan ita tayi kayan ta take gane me take faɗe idan Hausa ta wuce zo tafi zauna ina zuwa zansha ruwa da sauran kananan word to ba wani ganewa take ba. Da kyar mum ta iya cewa Sadiq "Bawan Allah ya sunan ka? kuma inane gidan ku dan gobe nazo muje neman nata tare" Murmushi Sadiq sarkin murmushi yayi kafin yace "Ga gidan mu can mai kofar kwanon nan sunana Sadiq wayan nan biyun kanne nane Yusuf da Sha'aban Yusuf Maman mu ɗaya Sha'aban kuma ɗan kanin Baban mu ne" "Na gode kwarai da gaske Babana dan sunan babana gare ka Allah ya biyaku da gidan Aljanna" murmushi Sadiq yayi yana faɗin "Ba komai Mama sai da safe" ya kai karshen maganar tare da juyawa suka bar wajen, Hannun Jehan Mum ta riko dan su koma cikin gida "Where are we going mum?" harara cikin duhu Mum ta wurga mata kafin tace "cikin gida" "Mum which kind cikin gida kuma? Where is Rimsha what about her?" Shiru Mum tayi dan bakin ciki ji take kamar ta wanke Jehan da mari haka Allah ya kaddara amma ko mai ya faru Jehan da Goggo ne sila "Mum please talk to me now" "Jehan wallahi ki fita ido na idan zaki rabu da wanna shegiyar yaren turawan ki kama Hausa gara miki ki kama yaren ki kina yar fulani shuwa arab Daddyn ku cikakken bafulatani ni cikakkiyar shuwa arab amma dan iskanci baki iya yaren mu ko ka ɗan ba sai aron yare ki bi ki addabi mutane to wallahi tun wuri ki fita harkan yaren yahudawan nan ki kama yaren uwar ki da uban ki kai kaji min ƴa" "Mum what are you saying? why are you shouting anytime everyday" Dogon tsaki mum taja ba tare da ta sake magana ba ta ja hannun ta suka wuce cikin gida dan tasan idan ta biyewa Jehan haukata ta ta zatayi.
A tsakiyar gida suka isko Goggo na alwala sallar issha sakin hannu Jehan Mum tayi tare da wucewa ɗaki abun ta kallon Goggo Jehan tayi tace "My Goggo please where is Rimsha" da sauri Goggo ta ɗago kai tana faɗin "What are you saying Jehan? You mean up til now they didn't see Rimsha?" gyaɗa mata kai Jehan tayi ba tare da tayi magana ba ta nufi cikin ɗaki "Jehan kizo kiyi alwala" cewar goggo "No goggo ba yanzu zan yi sallah ba sai an jima" daga cikin ɗaki mum tace cikin harshen turanci "Wannan ne kuma wane uwar ki baki isa ba wallahi ko ki wuce kije kiyi alwala kizo kiyi sallah a gaba na ko kuma na fito na same ki a wajen" Shiru Jehan ta tsaya ta kasa cigaba da tafiya dan mum bata taɓa mata magana a irin wanna sigar ba juyowa tayi ta kalli goggo "Ni ma dai Jehan awan nan gabar ba zan bi bayan ki ba duk wanda baya sallah bai da wata amfani a duniya da kuma lahira sanna idan baki sallah a kan lokaci idan kin mutu kunama da maciji ne zasu yi gadin ki a cikin gabari ki kuma wutar jahannama zaki tafi saɓanin mai sallah akan lokaci da Mala'ikun rahma ne zasuyi gadin sa a kabarin sa su buɗe masa kofar aljanna ya rinƙa shakan kamshin aljanna sanna ya shiga aljanna" Ta
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment