Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gayamani
shashasha...ta buga uban tsaki mtswww...
Sannan ta kalli driver Wanda yake zaune shi
betafiba kuma bece uffan ba, cikin d'aga murya
tace dallah Malam mutafi kana 6atamin lokaci.
Jiki na 'kyarma driver yaja mota suka d'au hanya,
dan yasan akan ilham ze iya rasa d'an Albashin
dayake samu, kuma gashi dashi ya dogara.
Montocin da basu wuce sha biyuba suka sadasu
da gida, sukayi horn megadi ya bud'emasu get
suka shige. Bayan ya ajiye motar inda aka
tanada domin ajiye motoci, ilham ce tafara
bud'ewa tafita, d'akinta ta wuce kai tsaye tafad'a
toilet tayi wanka sannan ta canja 'kaya, ta
kwalama Ameeno kira, saida gaban Ameeno yayi
mugun fad'uwa danjin ilham a gida yanzu, kuma
tasan indai taje school ba yanzu bane lokacin
dawowarta, jiki na 'kyarma ta isa ta dur'kusa
tace gani, ilham tace jeki kawomin lemu da cake
yauba saikin yimin girkiba, cike da farin ciki
Ameeno tabar d'akin zuwa kitchen dan kowoma
*_YARINYAR BABA_* abinda ta bu'kata. Saida ta
kammala sannan tafita zuwa d'akin momynta,
bata isketa d'akiba sai motsi dataji a kitchen
saboda haka nan tanufa dan tasan yanzune
lokacin da Momy ke shiga kitchen domin
had'ama daddy abinci. Ranta yayi fari dan ganin
Momy zaune kan kujera a kitchen tana yanka
d'anyar ku6ewa, domin yau abinda zata had'ama
megidan kenan tuwom semo da miyar d'anyar
'ku6ewa. Love u all Zee Elkaseem


YARINYAR BABA
[07:16 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR*
*BABA*
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```*
*Page* 101-110
cikin ladabi ilham ta rissina "Momy sannu da aiki,
cike da mamaki Momy ta d'ago ta kalleta ta
girgiza kai tace "yauwa, tare da tambayarta "ya
akayi kika dawo yanzu Alhalin kuma nasan
lokacin tashinku beyiba,?
Ilham tad'an 6ata fuska tadafe kanta cikin
marairaicewar murya tace "Kaine ne yakemun
ciwo shine na dawo amma nasha magani, Momy
ta tausayamata tace "ayya Allah sauwa'ke ilham
ta Amsa da "Ameen,
daga nan suduka ba wanda ya'kara magana
Momy ta maida hanakalinta kan yankan ku6ewar
datakeyi.
Wani shu'umin murmushi ilham tayi sannan takai
dubanta ga hannun Momy dataketa ayki da
sabuwar wu'ka sai wal'kiya take, tsawon minti
biyar tana kallon wukar tare da hannun Momy ko
'kiftawa batayi, wani haske yafito daga idanunta
yafada kan wu'kar hakan yayi dai-dai da fad'uwar
'ku6ewar da Momy ke yanakawa 'kasa tare da
shigewar wukar cikin tafin hannunta, wani irin
mugun 'yanka wu'kar tayimata, aiko kamar jira
take jini yafara kwarara ba tsai-tsayawa.
Momy ta ri'ke hannunta dake zubar jini tanata
salati, cikin rud'ewa ilham takama momy tana
tambayarta lafiya, Momy kasa yimata magana
tayi saboda tsabar rad'ad'in da gurin keyimata,
ga jini sai zuba yake ba tsai-tsaiyawa.
Cikin rud'ewa ilham tad'auki waya takira dadynta
tagayamshi halin da Momy keciki dan ganin
datayi Momy ta galabaita, numfaahinta na niyyar
d'aukewa.
Da sauri daddy yabaro office d'insa dukda
d'umbum jama'ar dake jiransa hankalinshi tashe
yake tu'kin bako sallama yashigo gidan kwance
ya iske momy tsakiyar falon ba Alamar numfashi
tattare da ita, gefe kuma ga ilham da 'yan biyu
sai faman kuka suke.
Cikin kuka ilham tanufi dadynta tafad'a jikinsa
tana kuka "daddy ka taimakemu kada Momy ta
mutu, wayyo nashiga ukku wayyo daddy....
Cikin tsananin rud'ewa daddy yacire ilham daga
jikinsa yanufi inda momy take kwance ba Alamar
numfashi tattare da ita, ga kuma hannunta har
yanzu jini na zuba, cikin tsananin rud'ewa
yacema ilham "taimakamin musata mota mukaita
asibiti,
Haka kuwa akayi da taimakon ilham akasa Momy
mota suka nufi asibiti ilham sai kuka take duk ta
wani firgice ta fita hayyacinta yanda kasan
batada masaniya akan ciwon Momyn.
Sun Isa asibiti emergency aka nufa da ita, nan
likitoci suka taru kanta, sun gano tarasa jini sosai
ajikinta saboda haka idan ba'ayi gaggawar
'karamata jiniba za'a iya rasa rayuwarta.
Ilham kuwa yanzu nadamar gaske tayi datasan
hakane da bata amince da zama cikin 'kungiyar
_*JIN DADIN RAYUWA*_ ba dan gashi tana gani
zata rasa momynta.
Daddy kuwa cewa yayi a d'ebi jininsa a'karama
Momy, cikin sa'a aka auna jinin akaga ze iyabata
cikin 'kankanin lokaci aka eba aka 'karamata.
Kwanan Momy biyar asibiti aka sallamota, duk
ilham tabi ta rame saboda fargaba, tana gudun
kada wataran awayi Gari Momy ta mutu.
Cikin sati Momy ta warware kamar batasha
jinyaba, sannan hankalin ilham yadawo jikinta,
Sosai daddy ke kula da Momy tun ranar datayi
rashin lafiya, ba'karamar Shiga damuwa yayiba,
yanzukam Alhmdlh sunkoma normal Kowa yasaki
jikinsa suncigaba da rayuwa kamar yanda suka
saba.
Love u all
Zee Elkaseem

YARINYAR BABA
[07:21 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR*
*BABA*
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```*
*Page* 111-120
A yau 'kungiyar *Aji dad'in rayuwa* tayi bikin
karrama ilham akan namijin 'ko'karin datayi gurin
kawo jinin momynta, hakan ba 'karamin cigaba
yakawoma 'kungiyarsuba, dan tsafi ya nuna cewa
shigowar Ilham wannan 'kungiya babban
cigabane agresu.
Saboda haka Abigael ta tabbatarma ilham daga
'yau batada sauran 6acin rai danagane da wani
d'an Adam adoron 'kasar nan, kuma daga yau
zata fara jin dad'in rayuwarta batare da momynta
ta takurataba, dama batada matsala da daddy,
Hakeem kuwa sai Kallon ilham yake yanamata
murmushi, itama murmushin take tare dajin dad'i
acikin ranta.
***********************
Tun daga wannan lokacin ilham tari'ka yin abinda
taga dama fita kuwa idan zatayi Momy bata isa
tahanataba, kaya sai wanda taga dama take
sanyawa, mini siket da body hug, da wando
pencil sune kayan fitar ilham zuwa unguwa
daddy kuwa yana gani beta6a hanataba, saima
duk abinda take bu'kata ya sakarmata mukullin
ma'ajiyar kud'insa kullum ta eba yanda takeso
bedamuba domin kud'in akwaisu.
Mota ilham ta gayama daddynta tanaso
yasiyamata, gaban momy suka ajiye magana ta
fad'amashi irin wacce takeso yayimata
Al'kawarin zuwan motar cikin wannan satin,
Momy kuwa data yun'kura zatayi magana tanaso
tahana amma bakinta sai yakasa furta kome
kamar ansa kwad'o da makulli an rufemata baki.
Saida suka gama maganarsu daddy yacema
ilham taje ta shirya ze kaita shopping, aiko cike
da murna tanufi d'akinta shima nashi d'akin
yawuce.
Sunfito cikin shiri daddyn ilham sanye cikin jaket
masu ruwan 'kasa ilham kuma wani matsiyacin
wando tasanya wanda yafito da duk wani shape
na jikinta, sai wata riga wacce batada maraba da
bes, kanta bako d'an kwali tayi parking d'in
gashinta, sannan suka wuce momy tana zaune
tana kallonsu tanason magana amma takasa.
Sai bayan fitarsu wani kululun ba'kin ciki
yatokaremata a wuya, da sauri tashige d'aki
tafad'a gado tafashe da kukan ba'kin ciki.
Kuka tayi sosai sannan tatashi jikinta duk ba
kwari tafad'a toilet tayo Alwala ta kabbara sallar
nafila, bayan tagama ta dad'e zaune tana addu'oi
sannan taji sau'kin ba'kin cikin dake damunta.
Cikin satin motar ilham ta 'karaso had'ad'iyar
mota 'kirar camry dunkulalliyar kalar ja me duhu,
ilham tayi farin ciki sosai, tun daga lokacin
ta'karo wulakanci tacigaba da baza tsiyarta.
Momy kuwa ta du'kufa da addu'a kullum ba dare
ba rana, saboda tayi imanin addu'a itace takobin
mumuni.
Love u all
Zee Elkaseem

YARINYAR BABA
[07:23 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR*
*BABA*
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```*
*Page* 121-130
Haka rayuwa tacigaba da tafiya da ilham, dan
yanzu ilham ta wuce duk 'yanda me karatu ke
tunani yau kimanin shekarunta hudu cikin
'Kungiya likafa taci gaba, dan yanzu 'kungiya
tafara sakar masu kud'i suna fantamawa a gari,
sa6anin da, da ba'a basu kud'i saidai suna abinda
sukaga dama batare da wani ko wata ya takura
rayuwarsuba.
Yayinda kullum 'kungiyarsu ta _*AJI DADIN
RAYUWA*_ take 'kara ha66aka dan yanzu Abigael
ta'kara samo masu salon tsafi, Inda arana sai
susha jinin mutum a 'kalla biyu ko ukku.
Ilham tasaki jikinta cikin 'kungiya, fantamawa
take cikin Gari tana yanda taga dama batare da
wani ya takurataba, dan yanda ilham ke hawa
manyan motoci masu tsada da yanda take fita
gari ko d'an gwamna Albarka, ko kad'an dadynta
bekawoma ransa kome akan hakan ba, dan
atunaninsa kud'i sane ilham ke amfani dasu,
besan ilham ta dad'e da barin amfani da
'kud'insaba sai wanda 'kungiyar aji dad'i ke basu.
Momy kuwa har yau har gobe tana son
tsawatama ilham amma takasa, addu'a kullum
take Allah yayimata maganin abin, kuma ya
ku6utar da ilham daga sharrin shaid'an.
**********************
_BAYAN AHEKARA UKKU_
Yau 'kungiya tayi taro na musamman wanda ba'a
ta6ayin irinsaba, su ilham ne duddur'kushe gaban
Abigael wacce ke zaune kan wata katafariyar
kujerar tsafi, sanye take da ba'ka'ken kaya sai
wani jan kyalle data d'aure 'kugunta dashi.
Yayinda duk matan dake gurin suke d'aure da
wani yadi me sil6i me zanen jikin maciji, iyakar
d'aurin be wuce gwiwarsuba, sunyi d'aurin gaba
dashi an d'aure daga baya.
Mazan kuma sanye suke da gajerun wanduna
kalar ja.
Sun nutsu suna sauraren bayanin da Abigael
kemasu na yanda 'kungiya zatasamu cigaba.
Bayan ta gama ne taro na shirin tashi tace
"sannan bayani na 'karshe 'kungiya na bu'katar
jinin mahaifin ilham,.......
Wani mummunan fad'uwar gaba ilham taji cikin
tsananin firgici ta d'ago da dara-daran idanunta
takai dubanta ga Abigael tana fad'in "no
impossible bazan ta6a bayar da jinin dadyna ga
'wannan 'kungiyarba, kunsan kuwa yanda yake
nunamin so.....ta fashe da wani mahaukacin
kuka, dan gabanta yan 'kungiyar ke sadaukar da
iyayensu ko 'yan'uwansu dan suji dad'i kuma da
ita ake cin moriyar abun, yau kuma abun yafad'o
kanta anya tanada hujjar hana jinin dadynta,
"Nooooo...... Tafad'a da 'karfi, hakan yayi dai-dai
da dawowar ruhinta jikinta,
Momy tagani tsaye kanta tana tofa mata addu'o'i
duk illahirin jikinta yajike da gumi kamar wacce
aka watsama ruwa.
Love u all
Zee Elkaseem

YARINYAR BABA
[07:38 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR* *BABA* _*Written & Edited*_ _*By
Zee Mmn Khady*_ *```Just a short story```*
*Page* 141-150 washe gari da misalin 'karfe tara
na safe, Zaune suke kan dining suna breakfast
Kowa naci hankalinsa kwance Amma banda
ilham wacce taketa juya spoon d'in cikin cup d'in
tea ba abunda ke zuciyarta sai tunanin yanda
zata ku6utar da daddy daga hannun shugabar
'kungiyarsu Abigael. Duk abinda ilham keyi daddy
na kula da halin datake ciki Saboda haka shima
duk sai yaji yashiga damuwa lokaci guda Ya
maida dubansa ga ilham yace _*"YARINYAR
BABA*_ meke damunki? Da sauri takai dubanta
ga daddy sannan tasaki fuskarta ta 'ka'karo wani
busashshen murmushi Wanda zamu iya kira da
ya'ke Wanda yafi kuka ciwo tace "Ba kome, cikin
damuwa daddy Yakama hannunta ya had'e
danashi cikin sigar rarrashi yake magana "Haba
ilham ashe akwai wata damuwa dazata sameki ki
6oyemin. Ilham ta wasance tace wallahi daddy
ba kome, kawai hakanan naji jikina ba dad'i
amma yanzu ma naji kome ya wuce. Duk abinnan
Momy na zaune tana kallonsu, bata sanyamasu
bakiba, illah wani irin 6acin rai dake addabar
zuciyarta Ganin yanda daddy kullum yake 'kara
shagwa6a ilham Gashi itakuma yanzu bata iya
hana kome. Cikin jin dad'i dady yace "yauwa
ilham d'ita kinsan banison 6acin ranki ko kad'an,
wani murmushi ilham tasaki wanda bekai cikiba.
Dady yace "yanzu dai ki shirya mufita shan ice
cream, ko kin washe dan banison kina shiga
damuwa, 'Kila idan muka fita muka d'an zaga
gari kin warware. Su Hassan da hussaina dake
zaune sunajin duk yanda daddy ke rarrashin ilham
kamar wata 'karamar yarinya, Wanda kosu
beyima haka, suda suke 'kannenta wacce tabasu
kusan 9 Year's, sukace "daddy muma muna
zuwa.... Kafin su ida fad'a ya tari numfashinsu
tare da d'aga masu hannu yace "kubari anjima
driver ya kaiku banison 6ata lokaci.... Sunajin
haka suka nufi d'akinsu suna turo baki dan sun
dad'e da sanin yanda daddy ke nuna banbanci
tsakaninsu da 'yar'uwarsu. Bayan sun wuce ne
daddy ya kalli ilham yace bari inshiga toilet inyi
wanka, Kema kije ki shirya, bejira jin amsar
dazatabashiba yanufi toilet d'in Ilham tayi saurin
binshi takamo hannunshi idanunta na zubar da
hawaye tace dan Allah daddy kada kayi
wankannan...... Dady yace dan me? Ilham tarasa
amsar dazata bashi sai hawaye dake zuba daga
idonta. Ganin batada niyyar yimashi magana yasa
ya zare hannunshi daga nata tare da saka
'kafarshi toilet d'in. Love u all Zee Elkaseem

YARINYAR BABA
[07:45 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR* *BABA* _*Written & Edited*_ _*By
Zee Mmn Khady*_ *```Just a short story```*
*Page* 131-140 lham lafiya mike damunki,
tundaga d'akina nake jiyo ihunki kina fad'in
impossible, meye baze yiyuba? Cikin tsananin
rud'ewa jikinta na 'kyarma tace "ba kome kawai
nayi wani mafarkine wanda ya tsoratani, Cike da
damuwa momy tace ilham dole kiri'ka muyagun
mafarkai ilham baki damu da addininkiba, baki
damu da sallah ba barantana addu'a Nidai sai dai
ince Allah kyauta. Haka momy tabar d'akin ilham
zuciyarta cike da tunani barkatai, al'amarin ilham
yana matu'kar tsoratata, gashi ko kad'an bata iya
tsawatar mata. A ranar haka ilham ta wuni
sukuku ba 'karfi jikinta ko kad'an tana tunanin
yanda zata tseratar da daddynta daga sharrin
Abigael, Bakin iya tunani tayi amma batasamu
wata mafitaba. Washe gari kuka ilham tayini
tanayi ta kulle kanta cikin d'aki, dan jiya 'kungiya
ta tabbatar mata da kada ta kuskura tawuce
kwana biyu bata bada jinin daddyntaba. Haka
tayi kuka tagode Allah batare da wani yasaniba,
har kanta yafara ciwo. _*BAYAN KWANA BIYU*_
Yaune kungiya ta ibarma ilham kada ta wuce
bata kawo jinin mahaifintaba, _*Misalin 'karfe
3:00am na dare*_ Taron 'kungiyane kamar yanda
suka saba, saidai yau tsai-tsaye suke yayinda
Abigael ke zaune kan katafariyar kujerarta, ilham
kuma tana dur'kushe gabanta tana sharar
hawaye, Cikin tsananin 6acin rai Abigael ta kalli
ilham tafara magana tare da mi'kewa tsaye tana
nunata da sandar dake hannunta "Kisani ilham
baki isa kisha jinin iyayen wasu ba kuma kiyi
arzi'ki da kud'in kiji dad'in rayuwa kekuma kice
baza'aji dad'i da jinin iyayenkiba. Tunda kika
shigo cikin 'kungiyarnan yau tsawon shekara
bakwai bamu nemi wani kwa'kkwaran Abu daga
garekiba sai yau, saboda haka dole kibi umarni
ko kinso, ko kin 'ki. Sannan kisani guri na'kara
kure mana kinaso ki kawo mana cikas, tokisani
gobe da daddynki yashiga toilet da niyyar yin
wanka baze fito da raiba, dole ne musha jininsa
yanda akasha jinin iyayen Kowa cikin wannan
'kungiya. Abigael nagama fad'in haka taro
yatashi, ilham na dur'kushe inda take takasa ko
motsin 'kirki sai wasu hawaye masu yaji ke zuba
daga idanunta. 'Dago kan dazatayine taga wayam
ba Kowa gurin ba Alamr mutane sun zauna,
hakan ya tabbatar mata duk sun tafi, Wata uwar
'kara tayi sannan tafd'i gurin tana birgima, Jitayi
andafata Hakeem tagani, cike da tausayawa yake
rarrashinta, har a zuciyarshi yakejin ilham besan
6acin ranta amma yazasuyi dokar 'kungiyace dole
tabi, haka Kowa yayi. Sai gab da dallar asuba
sannan ilham da Hakeem sukabar gurin. Love u
all Zee Elkaseem

Yarinyar Baba
[05:48 AM, 02-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR*
*BABA*
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```*
*Page* 151-160
saka 'kafar daddy keda wuya cikin toilet d'in ya
dorata akan wani jan abu me kama da bawon
ayaba, wanda keda tsananin tsantsi sai kuma ya
had'u da santsin tiles d'in dake toilet d'in 'kafarsa
tayi gaba yayinda yakasa d'aga ta bayan, kawai
sai jinsa yayi 'kasa tare da sakin wata
razananniyar 'kara
Da gudu Momy tayo kansa tana salati, amma
kafin ta 'karaso inda yake har rai yayi halinsa.
Wata irin razananniyar 'kara ilham tasaki lokacin
da aka tabbatar mata da mutuwar daddynta,
tashiga rera wani irin kuka na fitar hayyaci,
Koke koke akayi sosai 'yan'uwan daddy Dana
momy duk sunzo akayima daddy sutura aka
kaishi makwancinsa.
*su daddy an kwanta dama, oh,oh duniya kenan*
**********************
Yau kwanan daddy bakwai da rasuwa ilham
bataje meeting d'in 'kungiyaba, saboda haka
'kungiya tayi matsanancin fushi da ita,
Yau da misalin 'karfe biyu da rabi na dare duk
'yan 'kungiyar sun halarta hada ilham, gurin yayi
tsit Kowa yana jiran jin irin hukuncin da Abigael
zatayima ilham dan ba wanda besan yanda
Abigael take jiran zuwan ilham ba,
Saboda tsarin 'kungiyarsu ba'a fashin zuwa
meeting saboda hakan ba 'karamin cibaya yake
kawomasuba rashin zuwan d'aya daga cikinsu.
Cikin bala'i da matsanancin 6acin rai Abigael ke
magana "ilham kina nema kikawo mamu na'kasu
cikin wannan 'kungiyar tamu, a tarihin wannan
'kungiya yau tsawon shekaru goma sha biyu
kenan da kafuwarta amma babu wanda yata6ayin
fashin kwana biyu be halarci taroba, amma ke
yau tsawon kwana bakwai bakizoba, sabida haka
yanzu zamuyimaki hukunci dai-dai da laifinki.
Sannan ta kalli sauran 'yan 'kungiyar tace kunsan
duk wanda yayi fashin kwana d'aya bulala goma
ce, saboda haka zamu had'a goma sau bakwai
zamuyima ilham hukunci kamar yanda akema
kowane d'an 'kungiya.
Hakeem najin haka hankalinsa yayi matu'kar
tashi dan yasan da'kyar idan akayima ilham
bulala saba'in ta rayu saboda yasan azabar
bulalar ana bugunka kamar ana zubama wuta
ajiki.
Saboda haka cikin tsananin tausayin ilham yafito
ya dur'kusa gaban Abigael sannan ya had'e
hannuwansa alamar Neman alfarma yace "ina
neman alfarma daga gareki shugaba da a
rangwantama ilham sakamakon jikinta baze iya
d'aukar bulalar 'kungiya d'ai-d'ai har saba'in ba.
Hakeem yanada 'kima a idon Abigael baze iya
naman wani Abu tahanshiba, saboda haka aka
sassautama ilham zuwa bulala hamsin.
Ilham na dur'kushe gaban Abigael,
Abigael ta nunata da hannu take wata igiya ta
d'ad'd'aureta ta yanda ko motsin kirki bata
iyawa, sannan tanunata da sandar tsafinta
bulalace taji tanata sauka ajikinta me tsananin
azaba batare dataga Wanda ke dukantaba.
Haka akayimata bulala hamsin tanata ihu, bayan
an gama ne, Abigael tace "sannan kuma
hukuncin na 'karshe agareki muna bu'katar jinin
momynki daga yau zuwa gobe, bamu buk'katar
6ata lokaci.....
Love u all
Zee Elkaseem

YARUNYAR BABA
[05:50 AM, 02-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR*
*BABA*
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```*
*Page* 161-170
washe gari haka ilham ta tashi cikin tsananin
tashin hankali, dan yanzu tariga tasan Momy
kad'ai taragemata idan taba 'kyngiya jininta wane
hali zasu shiga itada 'kannenta,
Wani irin kuka tafashe dashi, kukan yinsa take
kamar na fitar rai har batasan shigowar momy
d'akin ba.
Momy takai kimanin minti goma tsaye tanama
ilham magana amma ilham batasan da
zuwantaba, saboda haka zama tayi gefen gadon
tare da dafa ilham d'in tace "ilham meke
damunki,? Meyasa kike kuka haka,?
Wani irin rud'u ilham tashiga dan batasan da
zuwan momy d'akinba.
Saboda haka batada amsar dazataba momy
kawai sai tafad'a jikin Momy tacigaba da wani
irin kuka me tsuma zuciya,
Momy kuwa ganin ilham na kuka batasan lokacin
da itama wasu zafafan hawaye suka zubo daga
idanuntaba, tashiga rarrashin ilham dan a
tunaninta ilham tana kukan rashin mahaifinta
ne.....
Haka sukayita kuka bame rarrashinsu, ilham dai
tana kukan yanda Abigael takeson takawo jinin
momy, itakuma momy tana kukan tausayin 'yarta
dan tasan irin sha'kuwar dasukayi da mahaifinta.
Ranar haka ilham tawuni baci ba sha, duk tabi
tafita hayyacinta, momy tayi rarrashin harta gaji,
tasamata ido.
_*3:00am*_ na dare, duk yan 'kungiya sun
halarta, yayinda ilham take dur'kushe gaban
Abigael tanata kuka tana ro'konta akan
tabarmata momynta kada takasheta, wata irin
mahaukciyar dariya Abigael ta 6a66ake da ita,
sannan ta d'ad'd'aure kamar bata ta6a koda
fara'aba tace ilham kina wasa da 'karfin tsafin
wannan 'kumgiyar amma yanzu zakiga abin
mamaki.
Momy na kwance kan katafaren gadonta tana
bacci marar dad'i, duk tahad'a uban gumi
sakamakon mafarkin datakeyi meban tsoro daban
mamaki.....
Abigael dake zaune kan katafariyar kujerar
tsafinta tayi nuna wani iccen bedi dake nesa
kad'an da gurin dasuke, saiga momy ta bayyana
d'ad'd'aure jikin iccen anyimata mugun d'auri
yanda ko motsin kirki bata iyawa.
Abigael tayi nuni da momy tare da cewa ilham
kalli can,
Cikin sanyin jiki ilham takai dabanta ga inda
Abigael ta nunamata
Wani irin matsancin tashin hanakali tashiga
sakamakon ganin momynta daure jikin iccen bedi
gakuma wani 'katon mutum ya tunkareta da wata
shar6e6eyar wu'ka da niyyar soka mata ita aciki.
Ilham naganin haka batasaan lokacin datafasa
wata uwar 'karaba tanufi gurin da gudun tsiya
wanda ita kanta batasan tanadashiba, yayinda
shima wanda ze kashe Momyn ya zura a guje
yanufi momy da wu'ka tsirara a hannunsa.
Amma kafin yakai ga momy ilham ta isa ta shige
gaban momyn takareta, shikuma idanunshi sun
rufe besan lokacin daya caka wukar da niyyar
cakata a cikin momy, amma sai ya cakata a
cikin ilham
Lokacin tasaki wata mahaukaciyar 'kara wacce
duk illahirin dajin saida ya amsa, tafad'i nan ba
alamar numfashi tattare da ita.
Lokacin momy tafarka daga mawuyacin baccin
datake duk tahad'a uban gumi kamar an
she'kamata ruwa,
Lokacin kuma mugun mafarkin datayi da ilham
yashiga dawomata a kwalwa.
Cikin tsananin firgici tatashi ba abunda bakinta
keyi sai addu'oi tanufi d'akin ilham dan ganin
halin datake ciki.
Love u all
Zee Elkaseem

YARINYAR BABA
[05:52 AM, 02-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR*
*BABA*
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```*
*Page* 171-180
Da hanzari momy ta Isa d'akin cikin tashin
hankali dan ganin ilham kwance 'kasa tayi wata
irin kwanciya wacce daganin wanda yayita kasan
be cikin lafiyarsa koma ace babu rai tattare
dashi,
Ilham......ilham....ilham...momy tashiga jijjigata
tana kiran sunanta, amma ba Alamar numfashi
tattare da ita, cikin tsananin tashin hankali momy
takira Ameeno me aikin ilham takama mata ilham
suka kaita mota driver yaja suka nufi asibiti.
Suna zuwa aka nufi emergency da ita wani
likitane ya tabbatar masu da mutuwar ilham.
Nan momy ta aza hannu aka tafashe da wani irin
matsanancin kuka me ban tausayi, haka aka
d'auko gawar ilham aka koma da ita gida,
Bayan sunkoma ne momy tashiga kiran
'yan'uwanta dana daddyn ilham tana sanar dasu,
cikin 'kan'kanin lokaci gidan yacika da jama'a
haka akayima ilham sutura aka kaita kushewa.
_*Oh ilham anshafe babinta tazama labari,*_
_*Ya Allah ka tsare mana 'ya'yanmu a duk inda
suke, Allah karesu daga duk wani sharri na
duniya Allah kabamu ikon tarbiyantar dasu
tarbiya tagari*_.
A gurin 'kungiya kuwa tun lokacin da 'yan
'kungiya sukaga yanda akyima ilham kisan
wula'kanci duk sai hankalinsu yatashi dan basu
ta6a manta ranar da aka kafa 'kungiya saida
Abigael ta tabbatar masu babu cuta ba cutarwa
ga 'yan 'kungiya, amma gashi yau an kashe
'yar'kungiyar kenan suma watarana za'a iya
kashesu.
Aiko nan suka shiga magan-ganu 'kasa-'kasa
take suka yanke shawara tsakaninsu, aiko kamar
had'a baki sukayo kan abigel suna fad'in bazamu
ta6a yarda da kisan 'yar'uwarmuba, suka rufar
mata da duka, kafin ta farga sunyimata laga-laga,
saida suka tabbatar dabata numfashi sannan
suka barta, amma meze faru suduka suka kasa
matsawa daga inda suke, yayinda wani ba'kin
haya'ki ya turni'ke gurin suduka suka shiga wani
irin mawuyacin hali wanda ko nufashi basu iya
maidawa.......
Hakeem kuwa yana gefe ba abinda yake sai
zubar da hawayen ba'kin cikin kisan da'akayima
ilham d'insa.
Yana kallon yanda 'yan kungiyar keta wahala
cikin wannan ba'kin haya'kin me tsananin yaji.
Love u all
Zee Elkaseem

YARINYAR BABA
[05:52 AM, 02-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR*
*BABA*
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```*
*Page* 181-200
haka sukacigaba da sha'kar azababben hayaki
me d'aci da yaji cikin 'kan'kanin lokaci
numfashinsu yafara d'aukewa, kafin kace me
wasu dayawa daga ciki sun rasa rayuwarsu,
Haka Abigael tacigaba da sarrafa tsafinta saida
ta tabbatar da duk 'yan 'kungiyar sun mutu bame
sauran numfashi sannan ta 6a66ake da wata
mahaukaciyar dariya.
A hankali Hakeem ya bud'e idanunshi wad'anda
ko gani baya iyayi sosai, yacigaba da jan ciki
yana matsawa daga inda yake, har ya isa inda
wukar da aka kashe ilham take yade yasa hannu
ya d'auko.
Abigael kuwa tajuya bayanta, tanata zuba wata
uwar mahaukaciyar dariya, dan ganin tayi nasarar
kashe mutanen dasukayi niyyar kasheta, har
Hakeem yazo gaf da ita batasan yazoba saboda
tsananin sautin dariyar datake gagga6awa, dan
yanzu burinta idan kome ya lafa zata sake
sabbin yan kungi.
Hakeem kuwa iya 'karfinsa ya da6ama Abigael
wannan wu'kar gefen cikinta, wata
matsananciyar 'kara tasaki tare da d'aga sandar
tsafinta ta bugama hakeem a ka, shima wata
uwar 'kara yasaki lokaci guda sukayi mutuwar
kasko.
_*Wannan shine 'karshen 'kungiyar aji dad'in
rayuwa tare da 'yan 'kungiyar baki d'aya*_.
Bayan kwana bakwai da rasuwar ilham, momy ta
aiki Ameeno me aikin ilham kasuwa tasiyo mata
cefane, kan hanyarta ta dawowa gida taga an
dadda6e wani me siyar da jarida anata siye
matsawa tayi itama dan ganema idonta, ganin
hotunan su ilham 6aro-6aro cikin shigar yan
mafiya yasa hankalinta yayi masifar tashi, kud'i
tami'ka itama ta siyo sannan ta wuto gida.
Bayan taba Hajiya cefanen tawuce d'akinsu can
ta iske jummai me aiki dame aikin 'yan biyu, bata
tsaya wata-wataba ta tattara yanata-yanata tace
tom sai anjimanku ni aikina daga yau yakare
gidannan, su jummai suka tambayeta dalili bata
tsaya wani dogon bayaniba tami'ka masu jarida
tafice ko bankwana batayima momyba tabar
gidan.
Su inna jummai ma koda suka fahimci abinda
jaridar ta kunsa tattara yanasu-yanasu sukayi
sukabar gidan tare da bawa momy jaridar.
Koda momy ta karanta tayi kukan ba'kin ciki,
'karshe kuma tagodema Allah dayasa ilham ta
mutu kafin ta kashesu, amma dukda haka
tanamata addu'ar neman gafara gurin ubangiji
itada mahaifinta.
_*Alhmdulillahi Anan nakawo 'karshen wannan
takaitaccen littafin nawa, ina fatan masu karatu
sun ilmantu kuma sun nishand'antu sun kuma
d'auki darussan dake ciki*_
Litatafan marubuciyar.
1)Siyasa ko soyayya
2)Duniya juyi
3)Halin girma
4)Gidan Asali
5)Autar Hajiya
6)Alhini
7Yarinyar baba.
*ZANEN ZUCIYA*
*Coming* *Soon*
```Kyakkyawar gaisuwa ga group members
*Ciwon ya mace* *Zee Mmn khady fans nd
novel*```
*Sai kunjini a sabon littafina bye*
Love u all
Zee Elkaseem


By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)

WHATSAPP NO:
07039625239


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment