Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace Yes inaso, yafara hafsatu manga hafsi Hafsa, Hafsa tabata fuska wlh abba banason manga dinnan, Ahmed yace kedalla kiyi mana shiru ko gaisawa bamuyi ba kin hausa da shegen surutu,

Abba yace kabarta mana, aytafi wadanda sukayi halin ko in kula dani, Ahmed yadaka musu tsawa ku sha2 shan ina ne dazakuga ubanku ku tsaya kuna kallansa amina tace ina yini, abba afusace yace da ban yini ba zaki ganni shakiyiya kawai, yagalla wa uwarsa harara, abdallah yarusuna yace abba barka da zuwa , ya amsa ba yabo ba fallasa , hjy ta tabe baki tace yaya barka da wuni, abba yace barka De

Mahmud yashirya tsab tun da asuba yabi jirgi se sokoto, daga nan yashiga mota zuwa wajaki, yana kai bai tsaya wata2 ba yatare Dan achaba se dajin fulani, amma me yaga ya badai anrushe dajin ko tsuntsu babu balantana Dan Adam, oh gush yadafe kai bin dajin yake da ido yadda akafara foundation agurin da alama gidan mai za ayi babba , ina zan ganta wazan tanbaya?

Haka yabaro dajin rayuwar shi ajagule , kusan 4 ya isa gida wayarshi yajanyo yakira Ahmed yagaya masa cewa akwai matsala Ahmed yace Tamefa ? Mahmud yace yanzu daga dajin fulani nake na riske har antadasu, kai intakai cemaka har ankassafa gurin

Ahmed yace hava dai, yanzun miye abunyi, Ahmed yace shine dalilin kiranka nima bansan abunyi ba yace ni yadda naji ance za'a gina musu gidaje amma banyi zaton har antada suba kodai karya ce, Ahmed yace wannan kuma seka binciki newscaster kaga inada abunyi yanzu yakatse wayar, Mahmud baidamu da halin koinkula da Ahmed yamasa ba burinsa yaga halin dasu joda suke

WAYE AHMED?

Muje zuwa πŸŽ„ Dan jin wannan amsar
ASEEYAH BASHEER ALEEYU πŸ’•

πŸŽ„ FULANIN DAJI πŸŽ„
πŸŽ„ πŸŽ„ πŸŽ„ πŸŽ„ πŸŽ„
πŸŽ„ πŸŽ„ πŸŽ„ πŸŽ„
πŸŽ„ πŸŽ„ πŸŽ„
πŸŽ„ πŸŽ„
πŸŽ„
N@ B aleeyu πŸ’• page 1⃣9⃣
alhj usman shine mahaifin Ahmed da uwarsu margayiya Sarah wadda suke kira da ummah, alhj usman dane ga alhj zubairu wanda yayi tashen kudi azamaninsa yarasu yabarmusu dinbin dukiya lokacin dad na jamia inda yake karatun government, musa shine babbansu wanda suke kira da abba se dad alhj usman kenan se kanwarsu zainab wadda ke aure a kt yayanta ukku rufaida yasir se muniba, rufaida tagirma tana ss2 ayanzu,

Abba musa yanada yaya ukku anty aisha se anty nana se karaminsu jalal, dukansu sunyi aure acikin kd, jalal kuwa yana turkey gurin karatu inda yake karanta business

Awani bincike da Su dad sukace sudan anan yahadu da ummah, suka kulla soyy kafin yadawo yanemi izinin aurenta aikuwa atake akabashi saboda kirkinsa, yana zuwa gida yasanadda yayanshi musa aikuwa cike da murna, yasaka musu ranar zuwa ba adauki dogon lokaci ba akaje neman auren akasa auren wata shidda dai2 kare karatunshi kenan

Yana kammalawa koda yadawo har abba musa yahada lefe yagyra masa gidansa, alhj usman yayi matukar murna da hakan cikin sati ukku aka saka biki Anyi komai lfy amarya ta tare gidan mijinta dake unguwar maitama ,

Zamansu suke lami lfy ko gardama bata hadasu da mijinta, haka take bin abba musa tamkar mahaifinta da matarsa, batayi shekara daya ba tasami ciki, gidan kowa murna yake dasamun cikinta bayan shekara tajuye danta kyakkyawa tamkar Dan india

Aka sha biki sosai akasa masa muhammad shine suka maidashi Ahmed,
ummah batasake haihuwa ba , alhj imaran wato mahaifin hjy ya umurci dad daya aure yarsa tunda haihuwa ta tsayawa matarshi haka yadaure ya aure ta badan yasoba sedan kawai baya iya jayayya da shi amatsayin shi na aminin ubansa, Koda dad yazoma ummah da wannan zancen seyaga tayi murna sosai hakan yasa hankalinsa ya kwanta

Hjy ta shigo gidan cike da isa da gadara, Sam bata ganin girman ummah, haka zata yi ta yima ummah habaici dayake ummah bamai son fitina bace setayi banza da ita, amma sam ummah batadaukar raini, ga zuciya kamar me irinta fulanin usuli

Hjy tasamu ciki se murna take tana kananan zancen ummah kuwa batako bi takanta ba, ahaka har ta haifi danta na miji wato abdallah alokacin Ahmed nada 6yrs, seda abdallah yayi shekara hudu sannan tasake haihuwar amina daga nan itama haihuwar ta tsaya

Shekara daya da haihuwar amina ummah ta haifi Hafsa, har an cire ran samun haihuwar , Hafsa ta taso cikin so da kaunar yayanta Ahmed skull kadai kerabata dashi,
Ummah tarasu tabar Hafsa nada shekara biyar aduniya, baqaramun tabuwa dad yayi rashin ummah ba sedai yabarwa mai duka komai

Ahmed yataso tun yana yaro da shegen girman kan tsiya, ga miskilanci har na tsiya, uwa uba bamai hanashi kudurinsa abunda kedamun mahaifiyarsa kenan, yana kare skull yaje Pakistan karatu acan yakare duk karatunsa, haka Suka taso da Mahmud tamkar tagwaye sedai hali ba guda ba, Mahmud kadai ke iyawa da Ahmed se kuwa kanwarsa Hafsa

Mahmud yayi karatunshi a Mumbai acikin kasar india saboda haka lokacin2 suka ziyarci juna kasancewar babu nisa tsakanin Pakistan sa india kusan ma kasa yanki dayane, sunyi sa'ar fito da kwali mai kyau tareda aykinsu ahannu.......

πŸŽ„ FULANIN DAJI πŸŽ„
N@ B aleeyu πŸ’• page 2⃣0⃣
Koda Ahmed yadawo daga kara2 har Hafsa tafara college, hjy na matukar tsoron Ahmed tun ranarda mahaifiyarsa nada rai tagayamata magana Ahmed yadauko cup din glass ya watsa mata shi aka kuma yadinga dukanta da kujera, dkyar uwarshi ta rabashi da ita,

Uwa uba karatun dayayi na soldiers shine karin bakin ransa kullum fuskarsa a tamke idan dai kinga dariyar shi to yana tareda kanwar shi Hafsa, wadda a duk lokacin daya kalli kwayar idonta yakan tuna mahaifiyarsa, Ahmed nada shegiyar zuciya amma me daya sha eviron drink zai dawo normal ,

Yatsani ka masa laifi kabasa hakuri, yafi bukatar kabarshi da bacin ransa domin basa hakuri tamkar kada da laifi ne agurinshi , abdallah kuwa babu abunda yakoyo a indiaa illah shasahanci da shaye2 se biyar mata, hakama amina tana Dan tabawa ma'ana tafaye soyy zamani wato romantic love

Hafsa kuwa baruwanta daga islamiyya se skull dinsu bata saurareni, kowani saurayi, Dukda ana ne manta, Sedai ta mutu son Mahmud amma batabari yagane ba, Sedai batasan tuni Ahmed yakamo tashar taba yadai samata ido ne kawai

Mahmud yanada kama da Ahmed farinsu daya sedai Mahmud yafi haske, Ahmed kuwa yasurka da ja, karatun da sukayi a india, sundauki al adunsu da dama example barin suma, Sedai yayi retouching dinta amma baya cirewa sekuma ta dace da fuskar sa, dogo ne mai faffadan kirji, yanada dogon hanci da karamun lips wadanda suke pink sosai kamar ansaka musu lipstick,

Sam Ahmed baya saka manyan kaya zai iya shekara bai saka manyan kayaba , ko ranar Friday sedai yasaka jallabiya fara, akwai shi da son kamshi ka tsantsainin tsiya, akwai shi da kyama mutane, bai dauki mace abakin komai ba, baruwansa da sha anin mata,

Shi aduniya baida wanda ya tsana irin Wanda yace yana sonsa, ko agurin aykin suka je kowani mission. Tokuwa ko commissioner na tsoron Ahmed saboda saurin zuciyarsa, akwai lokacin da gardama ta hadasu da wani captain abun yafara yabawa Ahmed haushi yaki sakar masa, binidiga kawai yafidda ya halbesa a kafa, indai agurin ayki ne suke to kowa kafa2 yake dashi, in kuwa agida ne belt ke ayki amina tasha dukanshi har ta gode allah

Yau tin safe baffa yatashi da ciyon kafa, Gashi yana son fita kiyo amma ba hali tin yana daurewa har yafara nishi, gwaggo tace baffan joda lfyrka kuwa yau senaganka kamar ba kajin dadi ne , dakyar ya iya furta kafarshi, gwaggo duk ta gigice arude taje tasame hadi tagaya masa, Yace mata shi bashida kudin kai shi asibity, Gashi nan garin babu itace se daji balantana gwaggo tahada masa magani

Haka tacigaba da zama dashi har yafara kasawa domin kuwa baya iya tashi komai Itake yimasa, ga kafar har tafara doyi domin kuwa ruwa take fitarwa abun bakyan gani, gwaggo tayi fita a titi tana neman taimako amma dkyar tasamu wanda yabata dari biyu itama kuwa gurin cin abinci gari da sugar yakare

Joda kuwa duk tabi tarame bata cin komai sedai tasaka mahsifinta agaba tayi ta kuka, haka zata rungume gwaggo suyita kuka, joda da bakar zuciya, ta fita daga gidan ganin yanda aka wulakanta ubanta da zummar zatayi aiki kona Menene tasamu kudi, shago2 take bi tana lekawa , tana neman taimako amma babu wanda yataimaka mata sedai akorata

Har tajuya daga wani katon shago naka Yan cosmetic , Sega wani babban mutun ya Parker da katuwar mota, tana daga gefe labe tana share kwalla, seda yagama siyayyar sa, sannan yace yarinya meke damunki kike kuka, kara fashewa tayi dawani kukan , tace wai ku cikin gari bakuda imani ne bakuda tausayi zuciyarku bushash shiyace, Mutumin yace to wai me aka miki ne haka, toba baffana bane bashida lfy kafarshi naruwa tayi karuwa kamar hularka amma narasa mai taimakamun mukaihi gurin bokayen turai

Mutimin ya aza a dariya bokaye kuma, mai shagon yace alhj wannan fa, yar daji ce dubi kayanta ma da kwalliyar ta , joda tafusata shibai taimaka mataba amma yazo yana zaginta dukawa tayi akasa tadauko katon dutse tajefa masa aikuwa Sega glass din gurin yafashe ,

mai shagon yace babbar bura uba, wlh se an biyani kona kaiki station, mahaukaciyar banza, joda tace uwarka ce mahaukaciya😏 alhj kam yatsaya sororo yana kallanta, Yace yi hakuri manir zan biya kasan fulani da zuciya.........

πŸŽ„ FULANIN DAJI πŸŽ„
N@ B aleeyu πŸ’• page 2⃣1⃣
Alhj yabiya shi kudinsa kudin 30thnd yace wa joda kibiyoni amota na zamuje gidana inshirya semuzo adauki baffan naki amota, akashi asibity koh! Joda tayi shiru tana kallan motar tace ni zanjiraka anan yace a'a nibazan dawo nan ba, zan iya mantawa, takalli mai shago tace Dan allah bawon allah bakomai idan nabisa, munir yayi murmushi lallai wannan yarinyar akwai wautar fulani acikinta inba hakaba seda tagama masa rashin kunya sannan yanxu tazo tana tanbayar shi, Yace bakomai ay halinshi ne taimako

Cike da tsoro joda tabisa amotar, Shikuma se murmushin mugunta yake, seda Suka hau titin by pass sannan yadauko wata powder ya shaka mata, bata sake sanin inda kanta yakeba se bayan wasu awanni sannan ta farka ta ganta acikin wata motar tadaban bakowa aciki awani katon fili gurin mai kyau, ahankali ta buda inda taga ana budewa a shiga taji shi gam aikuwa tadinga bubbuga motar da karfin allah amma ina bamai jinta

Ahmed yashirya yadauki Hafsa sukaje dauko dad , Karfe hudu tabuga yakalli Hafsa yace dad ya iso, aikuwa Sega jirginsu ya sabka, aka gama duk wani shirye2 daza ayi, Ahmed yace 6ter sefa sunkai 30 mnt kafin Su fito, Hafsa tace abun haushi wlh bari indan sha ice cream, tafita ta siyo ice cream ta tsaya jikin wata mota tana sha gaf2 taji ana dukan motar jiyowar dazatayi taga joda kamar tayi hauka fuskarta duk taji ja

Ice cream din dake hannunta tayada ta sheka da gudu se gurin Ahmed tace bros c diz motor wata yarinya acike da alama satota akayi saboda daga ninta irin fulanin nan ne na daji fuskarta duk kwalliyar hauka ce, Ahmed yace a ina muje , Atare suka fito daga motar Tanuna masa, Ahmed yayi dannar ganbun har yagaji amma yaki budewa dole yayimata nuni da hannunsa datajanye yafasa glass din amma taki sunkai kusan minti goma amma taki janyewa Ahmed kuwa yafusata

Hafsa tace bros mezai hana kaballa kanbun yagalla mata harara , kafata karfece dazata bude wannan ganvun, Hafsa tace zaka iya bros ka gwada, mtsss yaja tsaki, hannunsa yasaka a aljihun wandonsa ya ciro bindina yasaita dai2 gurin key yaharba tuni ganbun ya bude yana fitar da hayaki , Hafsa ta karsa cikin motar taga yarinyar akwance tace bros tafa suma, Yace tomezan mata kuma ayanzu, Hafsa tace mutaimaka mata mana, Yace wannan kuma se inke zakiyi babu wani dalili dazaisa intava wannan najasar, Hafsa ta gyada kai, tace to kabani key din motar zan kaita hospital

Ahmed yace ar u mad, acikin mota na zaki saka mun wannan kazantar, Hafsa batasake cewa komai ba taciro wayarta takira driver tace masa maza2 yakawo mata motar a airport tana jira, Nan da nan kuwa Segashi yakawo mata, tasaka joda acikin motar tayima Ahmed sallama tawuce da ita hospital

Acan asibity kuwa joda seda tadau long time sannan ta farka tanata kankame jikinta, tana fadan daga zaka taimamun seka kawoni garin cire kai, Hafsa ta riketa tana fadan bashi bane kalleni, suna hada ido Hafsa taji wani shock itama kuwa joda dasauri kowannensu yajanye idonsa, joda tace Dan allah waye ke? Hafsa tace idan kinci abinci zan gayamiki joda tace ina wannan makashin yake?

Hafsa tace waye makashi kuma ? Joda tace wanda yake yawo da bunduga, Hafsa ta kyalkyale da dariya tace kintaba ganinsa ne, joda tace wlh kuwa Hafsa tace a ina, joda tace adajin mu anan tabata labarin fadawarta kogi ita kanta Hafsa ta tsorata amma tasan Ahmed zai iya wannan Hafsa tace yayana ne, kuwa soja ne shi isa yake yawo da bingida saboda tsaro da ceton jama'a yanzu ba gashi ya cece kiba, joda tace ehh kam

Hafsa tace meya kawoki cikin wannan motar kuma meyasa kike kuka satoki akayi ne, joda ta fashe da kuka mai ban tausayi, Hafsa tadafata tace kigayamun mana ahankali tagaya mata, Hafsa tace inbanda jahilci yadebeki yazakiga mutum yabiya miki dubu talatin lokacin guda batareda kinsan shiba kuma ki yarda dashi ai nakwarai sun karamta aduniya, kuma har in zai taimaka miki ai seya baki kudin alokacin tunda yana dasu amma seya jaki ke bakiyi wannan tunanin ba, joda tace kokadan cikin muryar kuka, hafasa tace yanzu inane unguwar ku inmaidaki, joda tace masallacin shehu ne, Hafsa tace ina ne masallacin shehu kuma?

Joda tace ai ance duk shine babba acikin garin nan, Hafsa tace wane gari kuma mukam nan bamuda masallacin shehu, joda tace asokoton nan akwai wanda baisan masallacin shehu ba, hafsa tazare ido sokoto kuma ke asokoton kike ne joda tace ehh mana hafasa tace tabdi waynzu kina abuja ne, joda tace inane abujan, Hafsa tace tsakanin ta da sokoto tafiyar awa tara ne amma inaga ajirgi kukazo, tuni joda takurma ihu tazube kan gado. ........

Muje zuwa πŸŽ„
ASEEYAH BASHEER ALEEYU πŸ’•

πŸŽ„FULANIN DAJI πŸŽ„
πŸŽ„ πŸŽ„ πŸŽ„ πŸŽ„ πŸŽ„
πŸŽ„ πŸŽ„ πŸŽ„ πŸŽ„
πŸŽ„ πŸŽ„ πŸŽ„
πŸŽ„ πŸŽ„
πŸŽ„
N@ B aleeyu πŸ’• page 2⃣2⃣
Hafsa tadago joda tace karki damu yar uwa ba abunda zai faru dake se alkhairi yanzu kibari zuwa gobe , se a maida ki garinku, joda tace wayyo allah nah wlh gwaggo zata dakeni kuma inason ganin baffana, Hafsa tace to zaki iya biyar jirgi muje, joda tace Menene jirgi, oh tsuntsu mai tashi zama, Hafsa tadanne dariya tace ehh shi, joda tabata rai kwarankwatsa bazan shiga wannan mugun abun ba na yahudawa, Hafsa dai da taga abun bana karewa bane taje tasamu doctor daya duba joda tace masa Dan allah Yayi mata allurar bacci

Haka kuwa akayi bayan Anyi mata allurar, Hafsa takira Ahmed takoro masa bayani haushin yarinyar yaci kashi yace yanzu akan wannan kucakar zakiyi missing din dad kije kaita gida why not da bazaki barta ba ay wannan ma dakikayi taimako ne,

Hafsa tace hava Bro yanzun fa idan babarta wlh zata iya Fadawa wani mugun hannun daban "plss give me one chance " Ahmed yace shikenan kiyi hankali dakanki kuma zanturo abbas yayimuku komai kina kaita gun iyayenta kijiyo kada kisa ba mun kinfi kowa sanin halina, Hafsa tace tnkuu bros insha allah bazanyi abunda badai dai ba,

Haka kuwa akayi abbas yayi musu komai cikin minti ashirin suka bar abuja se skt har suka isa joda bacci take mota Ahmed yatura a airport din skt, tadaukesu se unguwar masallacin shehu, jin atsaya kiyyy da mota ne yasa joda farkawa , tagwale ido tana kallan unguwar juyowar dazatayi ne taga Hafsa na mata murmushi, tace to yanzu gamu a unguwar ku seki nuna mana gidan, joda tace yanxu kwananmu nawa muna tafiya, Hafsa tace kodaya ko awaya biyu bamuyi ba yanzu dai kinuna mana gidan ahankali tanuna gunda almajirai ke daukar karatu, Hafsa tace tnk god muje koh

Ganin taron jama'a yasaka joda kaduwa , tace lfy kuwa dasauri tashiga cikin gidan carab idonta yafada kan gwaggo tana rungume da hannayenta hawaye nabin fuskar ta Fadawa tayi kanta tana gwaggo bari kuka mana jikin baffan ne koh insha allah zaiji sauki, gwaggo takara fashewa dakuka tareda kankame joda ajikinta, tace joda ina kika je tin safe baffanki yayita Kiran sunanki kafin yacika, joda batareda ta fahimci yacika ba, tace gwaggo yana ina in gaidasa, gwaggo tace joda zoki zauna wanda yafimu sonsa yakarbi abunshi, joda tace wai mekike son fadane haka, gwaggo tace wannan waye kuma Tanuna Hafsa

Hafsa takaraso tazauna, joda tace gwaggo itace wadda ta taimakamun dana fada hannun wani azzalumi nan tabawa gwaggo labarin komai, gwaggo tace hava joda muda muke baki agari yaushe zakije neman taimako bayan Bakisan kowa ba, hafsa tace ayi hakuri dai allah yaji kan shi da rahma, joda tafashe da kuka gwaggo baffana yarasu ne, gwaggo tace ya muka iya joda baffanki yatafi gidan gsky sedai muyi masa fatan dacewa

Hafsa ta tausaya musu sosai, gwaggo tace joda ki shirya mana kayanmu zamu bar garin nan, yau baffanki yace mufita daga gidannan kada Su hadi Su salwantar da rayuwar mu, Hafsa tace yanzu to idan kuka bar nan garin ina zakuje, gwaggo tace neman aiki ba ance kunan cikin gari kuna daukar mata aiki ba, hafsa tace haka ne amma kuyi hankali mutanen duniyar nan se a slow tadauko kudi sunkai 20k tabasu tace gasu kurage zafi nizan koma gwaggo akan murna kuka takara fashewa dashi, joda taraka Hafsa har mota tanata daga mata hannu sannan takoma ciki

Hafsa kuwa bata koma gida ba se kusan isha'i cike da gajiya ta isa gida, tana ta zumudin ganin dad dinta, Ahmed taci karo dashi a kofa yana fitowa yace mata sannu da wahala, dariya tayi hava bros yade wahala, nidai ina dad, Ahmed yace kinyi late yashiga bacci sedai gobe, ta tabe baki kai bros, Ahmed yayi wucewarshi yabarta atsaye

Tin 6 Ahmed yaje yatada Hafsata ta tashi tashiga kitchen tareda mai girkinsu akafara hada abinci kala2 zuwa 8 komai ready har gidan angyara takoma dakinta tayi wanka ta shirya , sannan tashiga dakin Ahmed tace bros zan gyara dakin, bai amsaba kuma batasa ran zai amsaba, toilet yashige itakuma tashiga gyaran dakin har tagama baifo ba seta dauko wani jarida tana dubawa kusan 15 mnt se gashi yafito daure da towel babba ya yaba wani sama Hafsa tashige toilet din ta wanke tass ta kunna turare ko ina sannan tafita

Ahmed yakira dad awaya yace dad kaimu ke jira a dining fah, dad yace ina zuwa, kowa ya hallara a parlour dad kadai ake jira, yafito cikin shigar alfarma, yajanyo kujera yazauna, Hafsa tace mrng dad ya hanya, lfy lau hafsatu , ina kika je jiya? tace dad idan mungama break zan gayama yanzu lokacin karyawa ne, dad yace wato kema kindauki akidar yayanki komai yanada lkcn shi kenan "

Murmushi tayi to dad ya kake son inyi ba kyau zance alokacin da ake cin abinci, Ahmed yace to yanzun ma mekike yi ne ? Hafsa ta dukadda kanta tacigaba da cin abunci,

Gwaggo sungama hada kayansu kaf sukayi wa hadi sallama , se tasha inda ake shiga mota, tsaye sukayi Dan basu San motar dazasu shiga ba, sudai sunji anata dadan kano2 katsina, kaduna, gwaggo taduba taga motar da ake cewa kaduna tafi mata dayawa Dan haka itama tashiga ciki , tarungume joda seda motar tacika kaf sannan suka daga

Ankai inda ake tsayawa saboda adan Ci abinci amma ina gwaggo tace bata cin komai joda kuwa najin yunwa amma tadaure tasha, ruwa kadai, matar dake gefensu na lure da yanayinsu aranta tace Tabbas akwai damuwa atattare dasu kamar ma basu yarda da kowa ba,

πŸŽ„FULANIN DAJI πŸŽ„
N@ B aleeyu πŸ’• page 2⃣3⃣
Matar tayago masa da malt tamikawa gwaggo tace yar uwa ungo bismillah, gwaggo cike da fargaba tace a'a mungode, matar tace hava keko ba a maida hannun alkhairi baya, dole gwaggo ta karba tabawa joda cikin sauri kuwa joda tacinye Su tass,

Matar tace boyar allah meyasa baki siyama yarki abinci ba bayan kinsan tanajin yunwa, gwaggo tace toya zamuyi tunda yn kudin mu ba yawa ne dasu ba, matar tace to yanzu ina zaku, gwaggo tace munfito neman na kanmu ne

Matar tace idan na fahimta aiki kike nema ko muhallin zama, gwaggo tace ehh, matar tace bakida matsala da wannan ni dinnan yara da manya nake daukowa a kauye na kaisu gurin aiki garuruwa za abaki muhalli mai kyau iyakacinki kiyi goge2 ko kuma wanke2 da sauransu inkuma kin iya girkin zamani shikenan, amma da alama se an gyara ku akwai dinbin kauyanci acikinku,

Gwaggo tace indai zamu Ci musha da muhalli to wlh komi nene zamuyi bama bukatar ko sisi indai muna da wadannan ababen, matar tace inafa dole in wata yayi abiyaku naku salary din, gwaggo tace ina ruwan riba goma

Haka dai suka cigaba da fira har Suka isa kaduna, matar takirga kudin gwaggo tacika mata tabiya ta tajata tace zo muje gidana ,haka kuwa akayi suka tare taxi se gidan matar gidane babba mai kyau, Filin gidan kadai yana wani gida ga mota kusan ukku acikin gidan , har parlour Suka je, matar tace kuzauna ina zuwa , wanka tayi tacanza sutura sannan tafito takawo musu ruwa da abinci dakyar suke cin abuncin saboda basu sababa , seda ta tabbatar sun koshi sannan tace subiyota ta nuna musu masaukinsu,

Katon daki takaisu ciki mai katuwar katifa tashiga nuna musu abubuwan yadda suke toilet tashiga dasu tana nuna musu yadda ake amfani da komai Gwaggo kam imani yakamata joda kuwa ta matso safiya tawaye taje toilet din wani dadi yakamata jin ta bisa kaifa mai shegen laushi, ga bargo suyi rufa, salloli sukayi sannan suka kira safiya

Karfe bakwai matar tashigo tasamesu har sun tashi sukayi mata ina kwana gwaggo nata dada godiya, matar tace bakomai ay yiwa kaine ni sunana hjy binta inada miji yana abuja gurin wani aiki dana guda salim yana America gurin karatu, gwaggo tace allah yabarku da mai gidanki yakara zaman lfy ameen, hjy binta tace joda kinyi brush kuwa, joda tayi shiru Menene brush kuma hjy binta tace zo kiga tajata se toilet tazuba mata colgate a brush sannan tabata tace kinga yadda zakiyi tanata nuna mata kafin tafito kam rigarta sharkaf da ruwa

Joda tace gwaggo kinsan abunnan danayiwa hakorana allah dadi ne dashi kamar minti yake, nikuma se tsotsewa nake, gwaggo tace to uwar kwadayi, hjy binta takawo musu tufafi joda kuwa nata duk kananan kaya ne, se dadi takeji ita ke nuna mata yadda ake sakawa da yadda ake cirewa

Ahankali take nuna musu abubuwan zamani, yanzu dai sundan rage tsoro da kyauyanci, tinda har TV suke kallo lfy lau, hjy binta kuwa batayi kasa a gwiya ba tacigaba da wayar musu dakai seda ta tabbatar yanzu basuda matsala da komai sannan tashiga nuna musu yadda gyaran gida da yadda ake tsara parlour sundau kusan wata tana nuna musu abubuwa asara kam tashata agun joda saboda joda akwai barna kamar mage haka take

Yanzu suna kan girki ne tinkan Su semo har zuwa abuncin zamani yanzu komai sun iya itada joda wata biyu kenan, hjy binta tace to gwaggo yanzu ko yaushe zaku iya barin gidannan saboda yanzu nasan kun kware akowani fanni sannan kuma ni kunga tafiya zanyi so kafin in wuce zan nemo muku

Please Login or Register in order to submit comment