Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta dawo, duba da yanzu ga shi har an kusa kiran sallar la'asar, kuma tana ta kiran wayarta sai dai ta gama ringing d'inta ta katse ba tare da ta d'aga ba, hakanne yasa hankalinta ya kuma dugun zuma ko zama ta kasa yi addu'arta kawai shine Allah yasa suna lafiya, ganin abun ba na k'are bane ta kira wayar Miq ta sanar masa, ba sai hankalinsa ya fi na Inna mugun tashi ba, a birkice ya taho gida, Samaila da ya saka ya dinga binsu a baya da mota ya kirawo ya tambayesa garin ya akai ya dawo ba tare da su sun dawo ba, ya gaya masa abinda ya faru ai bai bari ya gama rufe bakinsa ba ya kikkifa masa wasu mahaukatan maruka had'e da fad'in duk abinda ya same su ka kuka da kanka don ba za ta yi maka kyau ba, phart d'insa ya nufa, sai ga shi ya fito da wani zagayayyen abu mota ya shiga ya jata da kansa da gudun gaske yayin da suka rufa masa baya had'e da sakin jiniya.

"Kaiii Na Lami kamar jiniya nake jiyowa fa.”
"Eh itace ya kamata fa muyi ta kanmu. ”
Ai kanma ya gama rufe bakinsa Na Lami ya ja motar da gudun gaske, su na barin gurin motar Miq na dira, mamaki ne ya kamani ganin ta wannan zagayayyen abin yake ganin hanya, wai ashe ya mak'alawa Reesah zobe a hannunta, zoben da shi ya san me ya taka a kansa, to wannan zoben da ya saka mata shine dalilin da yasa wannan abun ke nuna masa hanyar da suke, hanyar ya mik'a sai kuma yaga motar Munassan a pake a gefe, fita ya yi ya dudduba baiga kowa ciki ba, wani daga cikin yaran nasa ya saka ya d'au motar tata ya kaita can gida, kana koma motar yaci gaba da tafiya har sai da yazo bakin kangon da suke ciki sai zagayayyen abun ya hau k'ara d'in², tsayawa ya yi cak, yaransa da ke bayansa suma suka tsaya ba tare da sun kashe jiniyarsu ba.


Sai yau na tabbatar da in ka shiga tashin hankali kanka yana kullewa, sai a yanzu tunanin waya ya fad'omin, me yasa ban kira Inna ba a kawo mana d'auki? Gashi kuma yanzu na baro wayar a mota bare na kira ta, wani kuka ne yazo mini mai d'aci, kaina har wani juyawa yake saboda ruwan dake sauka a kansa, ruwan da ya tsagaita zai kuma dawowa mai k'arfin gaske, jikina ban da rawa babu a binda yake, na riga na saddak'ar sai na kwanta mugun ciwo, sanadiyar wannan ruwan da ke sauka a kaina don gara ruwan ya yi mini illa da na fita wani abun ya sameni ya sami Reesah gara ya tsaya iya kaina, wani ikon Ubangiji kuma har lokacin Reesah ba ta farka da ga baccin ba, ana haka na jiyo k'arar motoci da jiniya, jin mota ta tsaya a dai² gurin da muke sai da zuciyata ta yi wani irin harbawa, gaba d'aya na kuma firgicewa, shikuwa Miq fitowa ya yi ya shiga dube² d'aya daga cikin yaransa ya fito da lema zai kara masa ya dakatar da shi da hannu, duk da ya san matsalar da zai fuskanta idan har ruwan ya tab'a sa, amman a ganinsa mai sauk'i ce idan har yaga ruhinsa ga baki d'aya, saboda wani b'ari na zuciyarsa yana gaya masa kamar zoben ne kawai aka yadar a nan, kamar ance ya lek'a kangon ya lek'a.
Doguwar riga ce a jikina ta swiss less, kaina ba d'an kwali sai parking d'in kaina da na yi a tsakiya, gaba d'ayana na jik'e sharkaf, tsayawa ya yi yana kallona zuciyarsa na dokawa na ban mamaki, bugun da tawa zuciyar take yi ji nake tafi tasa bugu, alamun tafiya kawai nake ji amma ban san waye ba duk da hancina ya jiyo k'anshin turaransa amma na k'aryata hakan, kawai na gama saddak'arwa an riga an yanka kawunanmu an gama.
"Munas....”
Ji ya yi sunan ya kakare a mak'o shinsa juyowa na yi don na gas gata zatona, ji na yi zuciyata ta sanya ya na nemi dukkanin wani tsoro da fargaba na rasa, Reesah da ke kwance na d'auko na mik'o masa ita, bai karb'e ta ba sai kallona da yaci gaba da yi cike da tausayawa, musamman da yaga hijabina na cire na nannad'eta da shi, sannan na kareta kar ruwa ya tab'ata yayin da ni ruwan ya yi mini jagab, kar b'arta ya yi don ganin ruwa na neman jik'ata, mota yaje ya kaita tare da ce mini kar na fito sai gashi ya dawo da wata jibgegiyar riga a hannun ta kakinsa ce ma, da kuma hijabina da na nannad'e Reesah da shi, hannu ya mik'o mini ba musu na mik'a masa nawa hannun don ina buk'atar taimakon da gasken gaske, rigar ya saka mini yana mai shigar da idonsa cikin nawa, yana gani yadda ya wani kod'e saboda kuka, hijabin ya saka mini ya rik'oni a jikinsa muka fito don bazan iya tsaiwar da kaina ba.

Gidansa da ke k'ofar guga ya nufa da mu, amma ya kira Inna ya sanar mata an ganmu don ta samu ta kwantar da hankalinta, tun kafin mu isa nake kar karwar sanyi wani wahalallan zazzab'i na son rufeni, ko da mukaje shine ya d'aukoni don babu wani k'arfi da ya rage mini a jikina, Faisal da yazo yanzu shima ya kawo mana kaya shine ya d'auko Reesah ya biyo bayanmu da ita a lokacin ruwan ya gama daukewa gaba d'aya, a kan gado Faisal ya kwantar da Reesah ya ajiye mana ledar kayan, shima Miq ficewa ya yi ya barmu, da k'yar na iya raba kaina da jik'ak'k'un kayan, wani d'an littafi ne ya fad'o daga aljihun rigar da Miq ya saka mini, d'aukarsa na yi na ajiye a gefena, doguwar riga ce 'yar kanti, ita na saka na kwanta a gefen Reesah ina mamakin wannan bacci nata, ta dad'e rabon da ta yi bacci irin wannan, haka kawai sai naji wani b'ari na zuciyata na son sanin mai littafin nan ya k'unsa, hakanne yasa na janyo shi na bud'e a pagin farko sai naga an saka;
_Sunana Miqdad Muhammad Mahmud_
Mur mushi na yi don dama ina son sanin mai rayuwarsa ta k'unsa, kuma kuma ma's u karatu na san kuna son kuji labarin Miq dalla² ta yadda zaku cigaba da fuskantar labarin cikin sauk'i, sai dai ku sani muna da sauran tafiya a gaba...


Idan kun jini Asabar, lahadi, litinin shiru ku mini uzuri hidimar biki ce, idan kuma na samu lokaci zaku iya ganin post d'ina.


ALK'ALUMAN NAGARTATTU
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[7:23PM/26/3/2020]


Folow me on wattpad @Rashuna.

_Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_
__________________
*TWENTY SIX*
Nocking ya yi mini, gyara kwanciyata na yi gami da cewa.
"Shigo. ”
Shigowa ya yi d'auke da Reesah a hannunsa yana janye da akwatinmu.
'Wai yana nufin mun dawo gidan nan ne ko kuwa?
Na tsinci zuciyata da tambayar haka, ban kai ga bawa kaina amsa ba naji yana.
''Ki sauya mata kaya.”
Wa ta kan wanka sukayi don shima ga shinan ya sauya kaya sai zuba k'amshi yake mai saka zuciya nutsuwa.
Sai da yaje bakin k'ofa kana yace.
"A da kata da zuwan makarantarta tukunna. ”
Ya na fad'in haka ya fice, akwatin kayan na bud'e na saka mata kayan bacci kawai tun da a lokacin gari har ya fara duhu, wankan nima na yi nai shirin bacci tun da ina cikin hutun sallah, kwanciya na yi na bar Reesah ta na ta 'yan wasan ninta, don bacci ba yanzu wannan bacci da ta sha haka, littafin na janyo cike da zumud'in cigaba da karantawa na d'ora daga in da na tsaya.


_Sai da na kammala karatuna na secondary Daddy ya yi aure, bayan ya samu wacce ke matuk'ar k'aunarsa shi a ganinsa, amman kuwa ba shi take so ba dukiyarsa take hank'oro, saboda talakawa ne su fitik, mijinta ya rasu ya barta da 'yarta d'aya tilo, itama haifaffiyar katsina ce sun matuk'ar gwanance a sihiri da tsafi, tsafin nasu ne ya kama Daddy har yasa ya aureta ta taho tare da 'yarta, zallar soyayya da k'auna ta ke nuna mini wacce ko kwatan kwacinta ban samu a gurin Inno ba, a gaban Daddy da bayan idonsa haka take nuna mini soyayya wacce ko kad'an ba zanyi tunanin soyayyar k'arya bace, ashe ita ta shigo cikin duniyarmu ne don ta wargaza mana ita gaba d'aya daga bisani ta turamu inda babu mu ba dawowa cikinta, k'alu bale d'aya ta fara fuskanta shine na rashin samun cikin da ta yi, babu yawan da ba ta yi ba don samun haihuwa Amma Allah ya hanata, hakanne yasa ta fara hasashen had'amu aure da 'yarta Sumayya._
_Bayan kammala karatuna na secondary makarantar sojoji da ke london Daddy ya kaini, a can na yi karatuna har na kammala tare da samun nasarori masu tarin yawa, bayan dawowata gida na fara laluben in da mahaifiyata take tun da ita ba ta neme ni ba, ashe ma tana cikin garin katsinan a unfuwar shinkafi, bayan rabuwarsu da Daddy da shekara biyu ta yi wani auran, ba laifi shima mijin da ta aura da kud'insa, sai dai ko farcen Daddy bai kama ba ko kad'an, 'yan biyu duk maza Allah ya azurta su da su Mudansir da Mahboub, sai kuma Allah ya jarabceta da mugun soyayyarsu yadda ba ta zato, shekarunsu goma a duniya Allah ya yiwa mahaifinsu rasuwa, mutuwar ta girgiza duniyar Inno sosai da sosai, bayan mutuwar kuma sai ta koma kan kasuwan cinta, taci gaba da bawa 'yan biyunta soyayya da mugun gata, gatan da babu kwab'a ko nuna ba dai-dai ba a cikinsa, hakanne yasa suka ta so a mugun sangarce komai suka yi dai -dai ne gurin Innonsu, bayyanar Miq cikin duniyarsu sun yi matuk'ar farin ciki, bare ma da suka ga ya zama young miloniar, Inno ta yi farin ciki duk da har lokacin ba ta jin soyayyarsa kamar yadda take jin su Mudan, hakanne yasa ta fara asircesa yadda za ta juya dukiyarsa fiye da yadda yake zato._
_Da tsafinsu zuciyata ta kamu da matsanan ciyar soyayyar Sumayya wacce ba na had'ata da komai, Daddy ya yi matuk'ar farin ciki, hakanne yasa nan da nan aka sha bikin Sumayya da Miq ba b'ata lokaci wanda Inno sam ba taso hakan ba itama har sai da suka tsafaceta tukunna, shekararsu biyu da aure babu haihuwa ba labarinta, ga shi Daddy yana matuk'ar son ganin jikansa, shikuwa Miq soyayyar Sumayyansa ce kawai a ruhinsa, tashin hankali babu wanda Mom ba ta yi ba na rashin haihuwar Sumayya, babu inda ba su karad'a ba don ganin ta samu ciki amman shiru kake ji, tsoron Sumayya d'aya kada Miq yace zai mata kishiya ta na matuk'ar k'aunar abinta, kuma ta na bashi kulawa yadda ya kama ta, baza ta tab'a lamuncewa ganinsa tare da wata halitta ta da ban ba ita ba, idan har Miq ya mata kishiya duniyarta ta ragargaje gaba d'aya, ana cikin haka Fareesah ta shigo cikin duniyarsu._
_Fareesah 'yar abokin Daddy ce, a bayan layin su Miq suke, Allah ya yiwa mahaifiyarta rasuwa, kwata² ba tayi sa'ar matar uba ba, ta azabtar da ita fiye da zaton masu karatu, b'angare d'aya da zance ta yi mata gata shine da ta koya mata girki, shine kawai gatan da ta mata, ganin irin matsin rayuwar da take ciki, don ko mahaifin nata ba ta jin dad'insa ta zigasa ya bayar da ita sadaka shine Daddy yace ya nemawa d'ansa auranta, ai ji ta yi kamar ta had'iyi zuciya ta mutu, ita da ta so rayuwarta ta k'are a wahala sai ga shi Allah ya tsamota lokaci guda..._



AlK'ALUMAN NAGARTATTU
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[10:59PM26/3/2020]


Folow me on wattpad @Rashuna.

_Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_
__________________
*TWENTY FIVE*
Alamun tafiya na jiyo da sauri na b'oye littafin, Miq ne ya shigo tare da wata mata a bayansa, zama matar ta yi kusa da ni, shikuwa Miq ficewarsa ya yi bayan ya ajiye ledar da ke hannunsa, tsintar bakina na yi da gaisheta, murmushi ta yi mini kana tace.
"Wani yanayi kike ji a jikinki?”
Sai a lokacin na fuskanci likita ce.
"Kaina ke d'an mini ciwo, sai wani sanyi da nake ji yana shiga ta, kunnuwana sunyi mini dumm gaba d'aya, hancina ma ina jinsa a d'an toshe.”
"Ok, bara na rubuta miki magun guna, amma zan miki allura saboda kariyar zazzab'in da yake son kama ki.”
Magun gunan ta rubuta ta fita, a falo ta same shi, takardar magun gunan ta bashi, shikuma ya kira Faisal ya bashi ya siyo magun gunan.
Bayan fitarta komawa na yi na kwanta ba tare da na sake bud'e littafin ba, can jimawa sai gata ta
sake dawowa, tambayata ta yi naci abinci nace mata a'a, janyo ledar da Miq ya ajiye ta yi tana.
"Ina to abincin ya ajiye miki. ”
Ilai kuwa abincin ne a d'an soson take a way, bani ta yi na ci, haka na dinga kai lomar abincin da k'yar saboda ta matsa mini, kafin na ture shi nace ya isheni, tunanina ma yanzu shine idan Reesah ta farka tea za ta nema kuma ban san ya zanyi ba, ga shi ina buk'atar wayata da takardar da na anso, kuma shi wannan hamshak'in baice mini komai ba, a mota ma da nace masa motata da na ajiye ban ganta ba kawai ce mini ya yi an kaita gida, ga shi yanzu ina buk'atarta kuma yazo ya zubemu a nan, ko meye dalilinsa oho,kuma ko ya tambayi abinda ya faru da mu, muryar matar ce ta dawo da ni daga duniyar tunanin da na tafi.
"Ta so to na miki allurar.”
Juya mata bayana na yi ta mini allurar lailaya mini ta yi sannan tace na cigaba da lailayawa, ta bani magun gunan na sha, sannu na mata, ita kuma ta mini Allah k'ara sauk'i ta fita, kwanciya na yi ina jin bacci na son fisgata ga shi kuma yamma ne ban son yin bacci kuma babu abinda zai d'ebe mini kewa, Reesah ce ta farka cike da rigimar shayi za ta sha, rasa yadda zanyi da ita na yi na rik'o hannunta muka fito falon gidan, ba kowa a falon, wata k'ofa na gani da take kallo k'ofar d'akin da muke ciki, hannuna na rawa na murd'a handle d'in k'ofar tun kafin na kai ga shiga ciki na ji an saki wani siririn tsaki mai d'an sauti, kansa ne ke masa matuk'ar ciwo hakanne yasa yazo ya kwanta, bayan ya kashe wayoyinsa baki d'aya saboda bai son takura da damuwa, k'arar bud'e k'ofar da yaji ne yasa ya saki tsakin ba tare da ya juyo ba, ji na yi Reesah ta zare hannunta daga nawa ta nufi kan gadon da gudu, kan gadon ta hau ta na lek'a fuskarsa, murmushi ta saki tace.
"Papa”
A hankula ya bud'e lumsassun idanuwansa yana jin zuciyarsa na sanyi, janyota jikinsa ya yi yana mik'ewa zaune tare da ita, idanuwansa ne suka sauka a kaina, kallon mamaki ya tsaya yana mini, ni kuwa tun d'azu na k'asa had'a kalmomin da zanyi amfani da su gurin fad'in buk'atar da nazo da ita, dago kaina na yi da zummar gaya mishi Reesah ce za ta sha tea, idanuwana ne suka samu masauki cikin nasa, wani irin abu ne naji ya tsirga mini ta tsakiyar marata yana tsirgawa ta cikin jinina, rintse idanuna na yi har lokacin bai janye idanuwansa daga kaina ba yana jiran jin abinda ya kaho ni, bakina na rawa nace.
"Reesah ce za ta sha tea. ”
Ina gama fad'i ban jira cewarsa ba na bar d'akin.
Wayarsa ya kunna ya kira Faisal ya kawo masa kayan tea, don babu komai a gidan, ya kuma biya ya anso mana kayanmu.
Ruwan zafi ya jona a kettle Reesah na ta zuba masa surutu har ruwan ya tafasa sai kuma ga Faisal d'in ya zo, cup ya d'auka ya had'a mata shayin, zuba mata idanu ya yi yana kallonta yana jin wata soyayyarta na ratsa masa zuciya, a hankula yaji ciwon kan da ke damunsa ya na raguwa.
Ina shiga d'aki kwanciya na yi, ganin zaman shirun ya isheni yasa na janyo littafin nan na bud'e shi na soma karantawa.


_Mahaifina haifaffan garin katsina ne, shi kad'ai ne gurin iyayansa kuma dukkaninsu sun rasu sun bar masa tarin dukiya mai yawa bayan sun gina masa rayuwa har sai da ya zama babban soja wanda ake ji da shi saboda k'warewar aikinsa na tsakani da Allah, Mahaifiyata mai suna Ruk'ayya muna kiranta da Inno itama 'yar katsina ce sunyi aure da mahaifina auren so da k'auna, tare da ita yake yawon duk inda aiki ya kama shi zuwa, to ita irin wayayyun matan nanne ga mugun asiri duk ta bi ta mallakesa komai sai da izininta yake yi, da ta samu cikina kuwa babu abinda ba ta sha ba don ya zube amma ko gezau cikin bai yiba Allah ya riga ya rubuta sai nazo cikin wannan duniyar mai cike da harzik'in rayuwa, bayan haihuwata ba na samun wata gamsas shiyar kulawa daga gareta a gurin mahaifina kawai nake samun kulawa da soyayya had'e da riritawa hakanne yasa na taso da soyayyarsa mai girma a zuciyata, kuma kaman ninmu da shi sak kamar an tsaga kara, tun ina yaro ya kwad'aita zuciyata da son zama soja kamar shi hakanne yasa nima na girma da burin zama babban soja tamkar mahaifina_
_Laifi kad'an zan yiwa Inno za ta rufeni da duka, kwata² ba ta k'aunata ko kad'an wani duka da ta mini ta farfasa mini jikina Daddy ya k'asa jurewa hakan ya yi mata matsiyacin duka itama ya farfasa mata jikinta, fad'a sukai ga garumi wanda ya janyo musu tashin hankali mai girma har sai da ta kai ga yai mata saki d'aya ba tare da yaso hakan ba, saboda yana matuk'ar sonta, gashi kuma ta bashi farin cikin duniyarsa Miq, haka ta tsallake ta bar duniyarmu babu hanyar da Daddy bai bi ba don ya dawo da ita amma fir ta k'i, daga k'arshe dai sai katsina ya dawo da ni gurin Inna mai musu hidimar gida sanda suna katsina, don a yanzu ba shi da wani shirin yin aure, a gurin Inna naci gaba da karatuna cikin kulawa da soyayya._

Alamun tafiya na jiyo na yi saurin b'oye littafin na koma na kwanta.


ALK'ALUMAN NAGARTATTU.
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[7:37PM/31/3/2020]


Folow me on wattpad @Rashuna.

_Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_
__________________
*TWENTY EIGHT*
_Wani dattijon mutumi na gani a durk'ushe a k'ofar gidan, dafa sa na yi hakan yasa ya d'ago kansa ya kalleni, idanuwansa sun yi matuk'ar jaa na ban mamaki, rik'o hannuna ya yi yace._
" _Bawan Allah ka taimake ni ka ceto rayuwar marainiya, ta na cikin gidan nan ka taimakeni dan Allah._”
_Ba tare da nace masa komai ba na koma mota wani k'arfe na dauko, duka d'aya naiwa k'ofar ta bud'e, na tusa kai ciki mutumin ya biyo bayana tare da sauran mutanen da ke waje, d'akin da nake jiyo ihun naiwa wani irin duka da k'afata ya wangale, wata budurwa na gani, an rabata da komai na jikinta, rintse idanuwana na yi ina kiran sunan Allah a zuciyata, yayin da mutanen suka rufe mutumin da ke neman haike mata da duka, shikwa dattijon nan kallonta yake da jikinta duk ya fashe saboda duka, rik'e saitin zuciyarsa ya yi ya na jin rad'ad'in tausayinta, wani bargo ya d'auko ya lullub'eta da shi, kuka ta fashe da shi ta na jin dama mutuwa tazo ta risketa za ta fi buk'atar hakan sama da komai akan irin wannan rayuwar da take cikin duniya._
Juyawa na yi da nufin mik'a mutumin a hannun hukuma rik'o hannuna ya yi gami da cewa._
" _Zan had'aka da abu mai girma domin ni wannan amanar da aka barmin ta fi K'arfina, Khadija ba ta da kowa da ya rage mata a duniyar nan sama dani, kuma amana ce a gareni, mahaifanta sun rasu sanadiyar had'arin jirgi, tun daga sannan rayuwarta ta shiga tangard'a, 'yan uwan mahaifinta suke neman ganin bayanta don su samu damar cinye dukiyarta, na tabbata yanzu ma su suka turo a wulak'anta_ _rayuwarta bayan sun samu goyan baya a gurin mai d'akina sun siyeta da abin duniya, ina mai rok'onka da kayi nesa da ita daga garin nan, ina kuma son ka aureta dan Allah ba don ni ba._
_Guiwoyinsa biyu ya saka a k'asa ya rik'e k'afata gam yaci gaba._
" _Allah ne ya aikoka cikin Duniyarmu don ka tsame Khadija daga k'angin rayuwa, duk da ban sanka ba amma zuciyata ta na gaya mini kai alkhairi ne a rayuwar Khadija, ka taimakeni ka kuma taimaki tsufana da maraicin Khadija, ka aureta don ka_ _tsameta daga cikin wannan rayuwar, don idan ka tafi ka barmu ban san da mai zasu zo mana nan gaba ba._”
_Tari ne ya sark'e sa, ya fara wata iriyar shak'uwa gigicewa Khadija ta yi ta ruk'unk'umesa ta na kira sunansa gami da cewa._
" _Kar ka tafi ka barni Baba idan ka barni ban san ya rayuwata za ta k'are ba, kai kad'ai nake ganin soyayyata cikin idanuwanka bacin kai bani da kowa a duniyar_....
_Maganar ta ce ta tsaya cak, sakamakon ganin numfashinsa ya daina kaiwa da komowa, wani marayan kuka ta saki mai saurin narkar da zuciya, tun da nake a duniya ban tab'a jin tausayin wani mahaluk'i sama da Khadija ba, fita na yi ba tare da na waigo na kalleta ba, mutanen har sun fashe sakamakon mutumin ya samu ya arce sai sauran munafukai masu jiran a kashe komai a gabansu, mota na shiga, wata zuciyar ta na ce mini na tafi wata kuma ta na ce mini kar na tafi na bar rayuwar Khadija, idan na tafi na barta bazan tab'a samun nutsuwar zuciyata ba saboda magan ganun dattijon ne ke yawo a kwanyata._
_Hakanne yasa na koma cikin gidan, a lokacin mutane har sun fara taruwa da alama mutuwar tasa ta fasu, a yadda na bar Khadija a haka na sameta, sai dai ta saka kaya a jikinta, hannunta kawai na kamo na fito da ita don idan na tsaya magana banjin za ta saurareni, wata mata ce ta biyo bayanmu ta na tambayar inda zan kaita, ban tsaya sauraranta ba na saka Khadijan a mota na shiga na jata da gudun gaske, ina jin ta ta na ihun kiran b'arawo._
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[7:4PM/29/3/2020]


Folow me on wattpad @Rashuna.

_Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_
__________________
*TWENTY SEVEN*
_An d'aura Aurena da Fareesah ba tare da saninmu ni da Sumayya da Mom ba, bayan kammala d'aurin auran Daddy ya d'aukota ya nufo gidana da ita, had'amu ya yi a falo gaba d'ayanmu ya ga batar da ita garemu ta lallami da nasihohi, yace kuma amana ce a garemu idan muka cutar da ita Allah zai saka mata, duk da zuciyar Sumayya ci take kamar wuta haka ta daure ba tare da ta nuna b'acin ranta ba wanda hakan ya k'ara mata girma a zuciyata na kuma ji na tsani yarinyar tun kan naga fuskarta amma zan yi biyayya ga mahaifina zan kuma rik'eta amana kamar yadda yace, Mom ma da taji zancen ta ji ba d'ad'i sosai, hankalinta ya yi mugun tashi amma haka ta danne ba tare da ta nunawa Daddy ba, sai ma tausayin Fareesan da ta nuna tana ji, hankalin Daddy kasa kwanciya ya yi, gani yake kamar rayuwar Fareesah za ta kuma shiga matsi, hakanne yasa yace Inna ta daho kusa da mu ko don ta dinga kula da Fareesan._
_Sam ba na shiga sabgarta, babu ruwana da ita, kullum k'ok'arin Sumayya na ganin ta dai daita tsakaninmu ne ni kuma ina bijirewa, yayin da

Please Login or Register in order to submit comment