Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mun mutu muna da yak'inin ba mu barki a hannu mara inganci ba, Faruoq zai kula da ke fiye da kulawar da zaiwa kansa bazai tab'a CIN AMANARMU ba.‘’

‘’Amman kunfi son Yaa Faruoq a kaina Abba?‘’
‘’Dukkaninku muna sonku, shi soyayyar da muke masa mai had'e da tausayi da tausayawa ce.‘’
A dai-dai nan Faruoq ya shigo d'akin, idanun nan nasa sunyi jahur na ban mamaki, kallo d'aya Abba yayi masa ya sunkuyar da kansa, bashi da wata tambaya tun da ga amsar nan ya karanceta cikin idanuwansa da suka birkice, wani mugun tausayi da k'arin k'aunarsa yaji ya shigesa, shi kuwa Faruoq kallon Abba yake yana jin wata sabuwar soyayya mai silki da zallar k'aunarsa na kuma huda k'ofofin zuciyarsa suna shiga, ga wani girma da kimarsa da ke kuma shigarsa, da me zai biya wa'yanna bayin Allahn? Bashi da shi har k'arshen numfashi sai da zai rik'e musu 'yarsu tamkar zinare, bazai tab'a barinta tai kuka da idanunta ba zai kuma kiyaye b'acin ranta, zai rik'eta rik'o mai inganci, bai san so ba bai san ya yake ba, bai tab'a d'and'anasa ba amman zai k'ok'arin d'and'anasa a kanta ya kuma kulle zuciyarsa ga kowa don Fadila aka halicce shi don kuma ita kad'ai zai rayu har k'arshen numfashi wannan alk'awari ne ya d'aukarwa kansa.

(To masu karatu ga Farouq dai ya d'au alk'awari, shin zai cika wannan alk'awarin? Ya manta mutum bashi da damar tsara rayuwarsa, rayuwa gaba d'aya tana hannun wanda ya haliccemu ne haka zalika zuciya baka da ikon sarrafata indai akan abinda take so ne, ku muje zuwa dai.)

‘’Abba bani da bakin godiya gareku, bani kuma da abinda zan biyaku, Allah ne kad'ai ya san da me zai biyaku, ina rok'on kaci gaba da amsa sunanka na mahaifina domin bazan tab'a iya kankare hakan daga zuciyata ba, na gwada sau shurin masaki na gaza d'aukar hakan cikin kwanya da zuciyata.‘’
Rungumeshi Abba yayi kafin yace.
‘’Har bayan mutuwata kai d'anane Faruoq, sunanka bazai tab'a canjawa ba, ko da mahaifanka sun bayyana, domin ina ji a jikina zasu bayyana lokacine bai yi ba, kai d'in d'an BABBAN GIDA ne Faruoq k'addara ce kawai ta kawoka nan.‘’
Umma ji tayi jikinta yayi sanyi, duk makaman da ta d'iba da duk ta watsar da su ta amshi Faruoq a matsayin jikanta shi ma ya amsheta a matsayin kakarsa bai duba abinda ya faru a baya ba yayi mata uzuri domin hakan yana cikin k'addararsa zai san kansa bai zo a cikin masu asali ba haka zanen k'addararsa yake yana kuma godiya ga Ubangiji da ya bashi tsarkakan ahali cikin duniya.


Ansha bikin Fadila da Faruoq cikin amincin Ubangiji, Abba yana mai godiya ga Allah da ya nuna masa wannan rana, ko da mutuwa ta riskeshi a yanzu zai kwanta a kabarinsa cike da kwanciyar hankali domin bai bar tilon 'yarsa a hannun da zata wulak'anta ba.
Watansu tara cif Fadila ta haifi d'anta namiji wanda yaci sunan Abba suna kiransa da Aseef, shekara d'aya tsira ta kuma haihuwar namiji wanda yaci sunan Shugaban Faruoq d'in a gurin aiki I.G Mustapha, saboda k'auna da soyayyar da shugaban nasa yake mishi (Duk wani mataki da faruoq din ya taka a gurin aiki to da taimakon IG Mustapha ne, wanda gaskiya da rik'on amana da k'warewar aikinsa ne suka siya mishi soyayya gurin shugaban nasa har yake jinsa tamkar d'an da ya haifa. )suna kiransa da Abrar, kaf wanda ke zaune k'ark'ashin inuwa d'aya sa IG Mustapha sai da yazo barka kuma kowa da abin arzik'insa a hannu, Hajja ce kawai ba ta samu zuwa ba saboda rashin lafiyar da take fama da ita sai aka kai mata shi har gida, gaba d'aya ahalin IG sun d'ora soyayyarsu akan Abrar har ma Aseef d'in basu bari a baya ba, ji sukeyi tamkar jininsu ne ya haifesu, wanda hakan ya haifar da k'arfaffan zumunci tsakaninsu.
Sai da Abrar ya shekara biyu sannan ta kuma haihuwar mace wacce taci sunan Oummi suna kiranta da Aydha, yanzu shekararta d'aya da haihuwa amman tana tafiyarta, shekarar Fadila yanzu a duniya ashirin cif-cif Faruoq yana da talatin da shida, har zuwa yanzu soyayyar da Faruoq yake mata ba ta canja zani ba, ita kuwa ba ta da wani buri da ya wuce taga zallar soyayya da k'aunarta cikin k'wayar idon mijinta, ta riga ta,mutu, mutuwa sosai cikin zallar k'aunar mijinta tana tsoron wata ta kutso cikin rayuwarsu musamman yanzu da Faruoq din ya kuma gogewa kwarjini da cikar haibarsa suka kuma bayyana, kud'i sun zauna masa sosai don tun daga kan Abba zuwa kansu ba wanda baije hajji da umara ba duk k'ark'ashin dukiyar Faruoq d'in, a haka ma wai don ya tsayar da zuciyarsa akan halal insa bai tab'a amsar cin hanci da rashawa ba don sam baiga amfanin haram ba face azaba da zaka d'and'ana gurin Ubangiji.
Sam ba a son ranta ya tafi Dalhi gudanar da aikin da ya tafi yi can ba, haka kawai sam taji ba ta aminta da tafiyarsa ba amman bata da dama da ikon hanashi, aiki ne da Shugabansa ya tura shi saboda ya aminta da shi, sai dai ita tana jin kamar acan ne zuciyarsa zata bud'e wanda ba ta fatan hakan za taso su k'arashe rayuwarsu a hakan, Faruoq yana da girma da kima kuma ubane, Yaya,d'an uwa, miji, masoyi a gareta wanda ita matsayin da take hanga cikin idanuwansa baza su wuce, k'anwa, mata, sai kuma girma da kimarta su kad'ai tasan matsayin da take da su a gareshi, shekararsu hud'u da aure bai taba furta mata kalmar ina sonki ba ko kalamai na shauki da soyayya, wanda zasu fito ta aminta daga k'asan zuciyarsa suka fito, idan tayi k'orafi yakan ce.
‘’Ita soyayya ka aikatar da ita a zahirance yafi ka zauna kana wa'yanna shirmen.‘’
Tana buk'atar jin wannan sautin tana kuma mararinsa, shin yaushene za ta samu?



‘’ Fadeela, wani irin zurfaffan tunani kikeyi hakane?‘’
Muryar Oummi ce had'e da jijjigata suka dawo da ita daga dogon tunananin da ta tafi, baza ta iya cewa ga tsawon awoyi nawa ta d'iba tana wannan tunanin ba, wanda ya makantar da ita ya kuma kurmantar da ita, don Aydha ce a hannun Oummi tana ta kuka, Oummin na ta k'wala mata kira ba ta san ana yi ba, sai da ta kai ga jijjigata sannan ta farga, karb'ar Aydha tayi cikin sanyin jiki ta fara jijjigata kafin tayi shiru ta fara shayar da ita har kuma lokacin Oummi na tsaye a kanta tana karantarta had'e da damuwar da ke kan fuskarta kafin ta kira sunanta.
‘’ Fadila‘’
‘'Na'am Oummi’' Ta amsa a sanyaye.
‘’Ina so ki lalubo hankali da tunaninki a duk inda suka tafi, shi namiji da kike ganinsa mijin mace hud'u ne, kuma bashi da wani dama da iko na tsara dukkan rayuwarsa yadda zata kasance sai yadda Ubangiji ya yardar masa, zakiga mutum yana da burin k'ara aure amman idan Ubangiji bai yardar masa ba da guda d'ayan nan zai koma ga mahaliccinsa wani kuma yana da burin kuma Allah sai ya nufesa da k'arawa, wani kuma sam bashi da buri ko sha'awar k'ara aure amman idan hakan yana cikin k'addararsa bai isa ya gujewa hakan ba, don haka ina shawartarki da ki dawo hankalinki ki mik'awa Allah lamuranki, duk yadda yaso yayi rayuwarku ba ku isa ku canja hakan ba, don haka zaifi ki sanyawa zuciyarki salama, musamman ke da ba lafiyar zuciya ce da ke ba, ki rok'i Ubangiji Allah yasa babu kishiya cikin k'addararki, in kuma akwai Allah ya baki ta kirki wacce ba za tazo ta ruguza muku rayuwa ba hakan yafi da ki zauna kina k'untatawa zuciyarki.‘’ Tana kawowa nan ta juya ta fice, ta barta ta samu sararin yin tunani akan shawararta, ta kwa yi donkwa wani sanyi taji sosai zuciyarta tana yi, tana kuma yarda da amanna da shawarwarin da Oummi ta bata.
....









KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai.
Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan littafi mai suna KATANGA zai zamo bakandamiya da zarar ya ratsa duniyar marubuta, akwai abin amfani a ciki, yi k'ok'ari ka mallaki naka kar ka tsaya jiran na aro, domin kwa akwai hanyar da zamu bi mu gyara zaman auranmu a gidajenmu cikin tarbiya da koyarwar islama, ba nan kad'ai ya tsaya ba akwai hanyar da mace za ta tsaftace jikinta cikin koyarwar islama ba tare da ta sanya abinda zai cuceta ba, akwai d'umbin abin amfani a ciki mudai had'e a cikin KATANGA an jima ba'ayi kamarsa ba maza neme shi akan farashi mai sauk'i naira 500 kacal.
09037093702


#N.W.A
#Comment
#Share
[7/19, 1:09 PM] Rabi: BEBE'ARTH


CIN AMANA


®️NAGARTA WRI.. ASOCIATION


Wattpad@Rashuna


11

Zaune yake cikin mota yana zaman jiranta ta fito, K'arfe bakwai tace masa yazo saboda akwai shari'ar da zasu gudanar k'arfe tara na safe to tana son shiga kafin lokacin ya cika saboda akwai abubuwan da za ta k'arasa.
Suit ne a jikinta bak'ak'e, sai shek'i suke da walwali sun matukar amsarta sun zauna a jikinta sun fito mata da k'uruciyarta da zallar kyahunta, d'an k'aramin farin hijabin da ta saka shine ya bam-bamta ta da 'yan k'asar bacin haka rantsuwa zakai kace ba asalin Bahaushiya bace wanda ita kanta yaune taga damar saka hijabin kuma shima Faruoq ne yayi mata magana wanda har ya kusa kaisu ga yin fad'a amman haka kawai kuma sai taji tana son bin umarninsa bacin haka tafi son ta saka bandana wacce za ta rufe mata rabin gashinta a haka za ta fita duk inda taga dama duk kuma inda take so saboda aladar k'asar ta riga tabi jikinta,kasancewar anan ta tashi ta bud'i idanuwanta amman duk da haka ba ta yin shigar nuna tsuraici shima kuma taimakon Mama Ma'u ne saboda idan ta Dad da Mom ne ko da daga ita sai pb ne za ta fita babu me hanata bare ya tsawatar mata, da ba dan Mama ma'u ba ma haka za ta tashi ba ta san musulma ce ita ko kafira ba.
Kamar ko yaushe tana tunkarar motar zuciyarta na bugawa da sauri da sauri har Easha ta rigata isa jikin motar ta bud'e gidan baya ta shiga, ta kusa isa gab da motar Sameer yasha gabanta yana k'ureta da mayun idanuwansa, ko d'aga kai ta kallesa ba tayi ba saboda ta riga ta san waye zai mata hakan, kuma k'amshin turarensa ya sanar da ita, kaucewa ta fara k'ok'arin yi ya kuma tare hanya kafin yace.
‘’Kwana biyu me ya hanaki zuwa cluve, kuma in na kira wauanki ba kya ansawa, in nazo ki hanani ganinki?‘’
‘’Saboda duk bana ra'ayi.‘’
Ta bashi amsa kanta tsaye, wani shu'umin murmushi ya saki me sauti kafin yace.
‘’Lokacinki ne yarinya, kiyimin duk abinda kikaga dama nima lokacina ya kusa farawa daga ranar da kika zama mallakina, kuma ina miki albishirin Mom na dawowa za'a tsayar da ranar biki, cire wannan kidahumin abun duk ya ragewa Baby face inki kyau.‘’
Yakai k'arshen maganar yana kawo hannu zai fusge hijabin tayi saurin ja baya tana doka masa harara kafin tace.
‘’Sameer na gaya maka ka fita hanyata, ina da abu me muhimmanci ka zauna kana b'ata mini lokaci.‘’
‘’Hanya da ni da ke Fanan ai ta gama had'ewa babu zancen na fita daga ciki, idan sauri kike ki shige muje na kaiki a motata.‘’
Kai ta d'aga ta kalli Faruoq yayi mata nuni da ido alamun taje, girgiza mishi kai tayi k'walla na son zubowa daga idonta, da harshen hausa wanda ya san Sameer d'in ba ji yake ba yace.
‘’Ki bishi kuje, babu abinda zai faru insha Allah, zamu sameku a can.‘’
Wani wawan tsaki sameer ya saki kana yace.
‘’Sai wannan kidahumin drivern ya baki umarni zaki bini?‘’

‘’Ya fiye mini kai ai, saboda shi bai tab'a k'ok'arin keta mini haddi kamar yadda kake k'ok'arin yimin ba.‘’
Wani tsakin ya kuma ja had'e da zubar da miyau.
‘’Amman kin cuceni da kikace wancan jakin abin ya fini, dubi fa kansa da bak'ar fuskarsa ga wani uban tsagu a fuska, amman wallahi kin cuceni Fanan.‘’
Murmushi ta saki ganin ta saka ransa ya b'aci, Sameer kyakkyawa ne na bugawa a jarida, wacce duk wacce mace idan ta sameshi tayi damkatakar a fannin kyau amman babu kyahun zuciya, ko kusa baza ki hada kyahunsa da na Faruoq ba duk da shima Faruoq d'in tsagun fuskarsa ne suka bata kyahun nasa sai sal-sal in kansa da bak'in fuskarsa sai dai kuma idanuwansa masu mugun kyau ne wanda in har ya d'ora idonsa kanta sai taji wani bak'on yanayi yana shigarta idan kwa tsoautsayi yasa idonsu ya had'u guri guda sai taji kamar wani dafine me girma ke fitowa daga idonsa yana shiga cikin nata idanuwan.
Inda yayi parking in motarsa ta nufa ba tare da tace masa komai ba, shikwa sai da ya zabgawa Faruoq wata muguwar harara kamar shi ya masa laifin, kafin yabi bayan Fanan in.
Suna fita Faruoq ya mara musu baya suna tafe suna hira da Easha wacce yacewa ta dawo gidan gaba, sam ban san wata hira suke ba na kasa jiyo muku, sai da ya fara ajiyeta a schl in da ta fara zuwa, shekara uku za tayi tana zuwa kafin ta zana takardar gama secondar, duk abinda ya danganci tun daga Nursery zuwa Secondary a cikin shekaru ukun nan za ta iya komai indai ta mayar da hankali akai sosai.


Sameer yana ajiyeta ya juya akan zaije ya dawo kafin su fito daga shari'ar, shikwa Faruoq fitowa yayi daga motar ya hau samanta ya zauna yana bin duk mutanen da ke zirga-zirga a gurin cike da nazari.
Bayan shud'ewar awoyi biyar zuwa shida ta fito daga cikin kotun murmushi d'auke akan fuskarta saboda nasarar da take jiyo k'amshin samunta, duk da yanzun ma alk'alin ya kuma d'aga k'arar zuwa sati biyu masu zuwa, taga alamun shima siyeshi ake k'ok'arin yi amman Allah ya fishi da ikon Ubangiji sune zasui nasara akansu, sam ba ta ji k'walla mata kiran da Faruoq yake ba akan ta kauce sakamakon bulet in da aka harbo yayo saitinta da gudu ya k'araso gabanta yana k'ok'arin janyeta bulet in ya sauka a kafad'arsa, yayin da police in gurin suka ankara suka sakarwa wanda yayo harbin harsashi shi kuma ya fara k'ok'arin tserewa.











09037093702


#N.W.A
#Comment
#Share
[7/20, 8:22 AM] Rabi: 12
Rintse idanuwansa yayi yana jin yadda bulet in ke shigewa jikinsa, kan kice meye rigarsa duk ta b'aci da jini, Fanan kuwa duk ta gigice sai faman sannu take masa.
Itace taja motar suka nufi hospital gaba d'ayanta a firgice take Allah ne kawai ya kaisu lafiya yaso ma ya karb'i tuk'in ta hana shi, a ranta kuwa sai mamakin dauriyarsa da k'arfin halinsa take, da itace bulet ya ratsa ta jikinta ta tabbata sai dai a d'auketa a sume, gashi shi kuma har fad'i yake a bashi yayi driving.
A gurin cire bulet inma nan taga ikon Allah, don k'in fita tayi akayi a gabanta, rintse idanuwansa kawai yayi ba tare da yace uffan ba ko kuma razana ba, ta tabbata da itace indai idonta biyu za'a cire mata to sai an samo majiya k'arfi sun rik'eta 'yan asibitin kuwa sai dai dukkaninsu su toshe kunnuwansu don wallahi sai ta cika asibitin da ihunta da karaginta, can k'asan zuciyarta taji ta watso mata tambayar.
Anya kuwa wannan karanne bulet ya fara ratsa jikinsa kuwa?
Gaskiya dai banjin hakan, wata zuciyar ta bata wannan amsar.
Kallo aya tayi mishi ba ta kara marmarin sake kallonsa ba, saboda babu riga a jikinsa kuma k'irarsa tayi mugun firgitata wani irin mirdaddan jiki ne da shi, wanda da alamu akwai suffar k'arfi a tattare da shi, rik'o aya yayiwa mutum to tabbas sai yaji iji a jikinsa. Mamakin yadda taga fatarsa tana wani irin glowing sam ba ta nuna yana cikin yanayi na wahala ba har da zaizo yana aikin driving inta da alamu dai Dad bai mishi wani cikakken kallo ba kafin ya daukeshi aiki ba,don tabbas ta fara zargin ba aiki ne ya kawo Faruoq cikin rayuwarsu ba akwai abinda yazo koma menene dai tayi alkawarin sanya mishi idanu har sai ta binciko.

Rigar tasa dai ya mayar saboda shi kansa ba zai so fita a haka ba, dad'in ves kenan da ya sakata s ciki bashi da wata damuwa, hannu d'aya na rigar ya yage sai ta zamana me hannu aya saboda ciwon nasa ya samu sakewa ga kuma bandejin da aka nad'e kafad'ar tasa da shi.
A wani pharmacy ta tsaya ta siyo magungunan da aka rubuta mishi sannan ta kalleshi tace.
‘’A wani anguwa kake naje na ajiyeka?‘’
‘’Kar ki damu madam zan hau nape ko taxi ya ajiyeni, muje dai gida inga kin shiga gida lafiya hankalina zaifi kwanciya.‘’

‘’Bana son taurin kai kana buk'atar hutu yanzu, ya kamata na saukeka gida ka kwanta ka huta.‘’
"Ta ya kike tunanin zan bari ki kaini ki kuma juyo ke kad'ai, in baki sani ba ya kamata kisan rayuwarki ake buk'ata ko ta wani hali, don haka ya zama dole ki daina fita ke kad'ai sai tare da masu tsaronki don kiyayewar lafiyarki, duk da na san bakya buk'atar takura cikin rayuwarki kinfi son rayuwar 'yanci wannan dalilin ne yasa kika k'i amsar masu tsaron lafiyarki to yanzu lokaci yayi da zaki amshesu."

"Har yanzu banjin zan iya rayuwa duk inda zanje sai da mutane a zagaye da ni, don haka har yau ban shirya amsarsu ba, duk wata kariya da zasu bani baza ta wuce wacce wanda ya halicce ni yake bani ba, ka gaya mini unguwar da zan ajiyeka, bana son doguwar magana.‘’

"Saukeni anan.‘’ kawai ya fad'a da kakkausar murya, ba tace uffan ba ta gangara gefen titi a hankula tayi parking yana k'ok'arin fita tace.
"Na baka wutun wata guda, idan kaga baza ka iya cigaba da aikin ba kuma to sai kayi zamanka ba sai ka dawo ba saboda kar wani tsautsayin ya kuma samunka, nima duk da banji dad'in hakan ba na so ni harbin ya sama ba kai ba, don haka na gode da wannan kariyarma da na samu."

"Idan kikai wasa da rayuwarki kanki kika cuta ba Faruoq ba." Yana fad'in hakan ya b'alle murfin motar ya fita, yana fitowa taxi tazo wucewa ta gabansa yayi saurin tsayar da ita ya fad'a ciki saboda ganin bai akko mutum ko aya ba sai da ya shiga ya zauna kana ya gayawa mai taxin inda zai ajiyeshi, Fanan ba tayi wani tunani ba kawai ta bi bayan wannan me taxin sunyi nisa da tafiya tana ankare da duk inda me taxin yake ba tai aune ba ta nemi inda suka shiga ta rasa, babu yadda ta iya haka ta juya ta nufi gida a mugun gajiye saboda kwana biyu ba tayi tuk'i ba shiyasa take jin muguwar gajiya da mutuear jiki gaba aya.
Kate ta saka ta had'a mata ruwan wanka mai d'an zafi ta shige ciki, tana mugun son zama cikin ruwan wanka irin hakan take hasasho musu ita da mijin da zata aura su shiga cikin ruwan wanka su dade suna wasansu na masoya a ciki, amman kuma ba ta hasasho hakan da Sameer ta rasa me yasa sam ba ta jinsa a ranta da cewar wai shine mijin da iyayanta suka zab'ata, duk wata hanya da zata rusa auranta da Sameer ta duba ta laluba ba ta hango ta ba amman kuma har yau tak'i yardarwa da ranta shine mijinta.
Har sai da ruwan ya huce kana ta bud'e gurin da zai fita kafin ta sakarwa kanta shower bayan ta sanya hular da za ta bawa gashinta kariya don kar ya jige, don ita sam ta tsani taji gashinta a jik'e drayer ma wahala yake bata don ko wankan tsarki tayi kate ce take busar mata da shi yanzu kuwa da suke tare da Easha ita keyi mata,don ta karbi kusan rabin ragamar aikin da kate in take mata, duk da wani abin Fanan in tana hanata tana nuna mata ita ba aiki ta d'auketa ba,wankin kai kuwa dama ba tayi a gida sai dai taje saloon.

Bayan fitowarta daga wankan zama tayi akan stool in mudubin tana bin kanta da kallo, ita kanta da kanta fatarta tana mugun burgeta saboda yadda take da wani shek'i da santsi,wanda santsinta baya barin ruwa ya zauna a jikinta, idan ba tab'ata kayi kaji danshi ba to ko tace wanka tayi k'aryata hakan zakai saboda babu ko d'igon ruwa a jiki kuma ba bushewa tayi ba tsabar santsin fatarta ne, mayukanta desighners masu mugun tsada da kyau ta d'auko ta fara shafe jikinta da shi, ko wani loko da sako na jikinta sai da ta bi ta shafe shi kafin ta fesa body spray a jikinta kafin ta nufi gurin da kayanta suke, wata doguwar riga ta d'auko ta saka iya kacinta guiwarta kuma siririn hannu gareta, rigar ta amsheta kuma ta mata kyau sosai kana ta fito dining area kawai ta nufa don 'yan hanjinta har nannad'ewa yake saboda yunwa ko kyakkyawan kari ba ta tsaya tayi ba saboda shariar nan da ta saka a gaba, dama tunkan ta shiga wankan ta gayawa kate ta sama mata sassauk'an abinda za ta sanyawa cikinta ta ajiye mata shi kan dining in ta fito za taci.

Bayan ta gama cin abincin ta barwa kate sallahun in hud'u yayi ta samu wani yaje ya auko Easha daga makaranta, za ta shiga ta kwanta don haka ba ta buk'atar ganin kowa, ta fad'i hakanne don ta san dole Sameer zaizo nemanta, cikin duvet mai matukar dumi ta shige ta rufe idanuwanta tana son baccin da ba ta samu tayi jiya ba ya sureta kafin lokacin sallar azahar ya k'arasa, a hankali baccin ya fara d'aukarta kafin ya d'auketa gaba d'aya.






#N.W.A
#Comment
#Share
[7/20, 8:22 AM] Rabi: BEBE'ARTH


CIN AMANA


®️NAGARTA WRI.. ASOCIATION


Wattpad@Rashuna



13
Tashi tayi yau da son zuwa beach ta kwana biyu ba taje ba kuma tana samun nishad'i a gurin in taje, kuma dama yau hutu take don ko gun aiki baza taje ba,da yamma in taje beach daga can sai ta huce club shima an kwana biyu ba'a lek'a ba, wuni tayi akan gado sai sallah ke tada ta, tana yin sallar la'asar kuwa ta fesa wanka ta fice, sun had'u da Easha da aka d'aukkota a makaranta a gate taso ta jirata ta shiryo su fita tare tak'i ba don komai ba sai don zata club kuma ba ta son zuwa gurin da Eashan.
Easha tana shiga ciki wayar Faruoq ta dinga kira amma ba'a d'aga ba, tana so ta sanar masa ne Fanan ta fita ita kadai gashi kuma bai daga ba, a bangaran Faruoq d'in kuwa bacci yake yi kuma wayar tashi a silent take, da zazzzafan zazzab'i ya kwana wanda hakan yasa bai samu wani isashen bacci ba sai yanzun shiyasa baccin nasa yayi nauyi.
A kasalance ya farka duk da yanzu jikin nasa da sauki zazzabin ya sauka, wayarsa ya fara dubawa wanda ya tarar da tarin miss call in Fadila, sai kuma na IG guda biyu, wanka yake buk'ata a yanzun, don in yace duk zaiyi waya da su to bashi da karfin yin hakan, kuma yasan zai shafe awoyi suna kan layi, kamar ance ya duba k'aramar wayarsa da yake fita da ita anan ya tarar da misa call daga landline in gidansu Fanan, haka kawai jikinsa ya bashi akwai abinda ke faruwa don haka kawai ya danna gurin

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment