Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

 *🍃KISHIN MATA🍃*
               🍃🍃🍃
         _mai dauke da salo na daban🤙..!_

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ*✍

   *NA*

         _*HAFNANCY LURF💕*_
           _*[Hafseesee]*_

   _*💫Dedicated to:-Anty Bahijjata & Grandma Zm Chubado*_

   
*#An_Intense_Jealousy_Story*
*#Love#fiction*
_•Copy cats are advised not to transform or reproduced this publication by all means including recording or any other electronic methods without the prior written permission of the writer°_

_#In this article, we will investigate what is going on in the minds of men who seek to marry more than one wife. What are their views on the matter? We also want to know what their wives think about their husbands’ looking to marry again_

    _*FREE PAGE…!*_

      _*💫BABI NA DAYA…☝*_

       _*★CENTRAL AREA GARKI,FCT ABUJA*_

______________★Awani tangamemen gida ne wanda ya amsa sunansa da gida,ginin zamani ne wanda aka ginashi on a low key,ma'ana anyishi ne very simple and attractive bbu wani tarkacen decorations da akewa irin mighty house dinnan,no wannan is juz too simple and beautiful,kana sada kanka cikin wannan gidan,from ur first view zaka tabbatarwa kanka da cewa wannan family house ne,sannan kuma acike yake fam da mata,yan'uwa ne da kuma abokan arziki duk anzo taya *'DCP SULEIMAN ALASSANA GIDADO'* murnar karin auren da yakeyi ayau wanda ya kasance ashirin da biyu ga watan nuwanba ah shekarar dubu biyu da goma sha bakwai,

Ko ina kabi zaka ga duk mata ne dake yau ne ake yinin bikin,ansha anko kai kace ko bikin farko ne,da yawan matan sunyi gungun,anyi group group ana tsegumin zancen auren,kowacce da gutsiri tsomar da takeyi akan *Jameelah* wacce ta kasance uwargida sarauniyar mata agdn DPC Suleiman Gidado,

Ramlah k'anwa ga DCP Suleiman wacce tafi kowa tsanar Jameelah tace da cousins dinta wa'enda suke kewaye da ita''Aini wlhy karku so kuga yadda nake cikin farin ciki da wannan auran da Hamma Gidad'o ya kara don atleast zai saka annamimiyar matar nan tasa nutsuwa da kuma yin ladab...''

Da sauri wata meh suna Baddo tace''Ramlah wai nifa ban san dalilin dayasa kika tsani anty Jameelah ba bayan matan tana da kirki sosae,ki duba fa wlhy idan kaje gidansu na rantse da Allah sai ta rasa inda zata sakaka dan murnar taga yan'uwan miji,kyautatawar da zata maka kuwa abun har baa magana,idan zaka tashi tafiya haka zata sallameka da sha tara ta arziki,sannan kuma ku rabu amutunce cikin raha da kuma fara'a,nidai gsky matar tamun don haka bana tsammanin Hafsah zatazo ta fita samun matsayi awajen dangin miji idan akayi duba da yadda Jameelar ta riga ta siye zuciyoyin dangin mijinta.....''

Ramlah data kai lomar abinci baki tayi saurin hadiyewa tare da kwasar Boddo da uban harara tace''Tadai siye zuciyoyinku amma banda nawa,sannan kuma ki bari ita Hafsan ta shigo mana kiga irin tata kalar kissar da kisisinar,ni na tabbata ma dole ta saukar da zamanin Jameelah aji kawai an bar yayinta,Allah i trust Hafsah bazata ta6a bani kunya ba.....'

Wata Hanifa tace''Don tana yayar babbar kawarki ko?'' ta furta tana harararta,ta6e baki Ramlah tayi kan tace''Abar batun wai tana yayar kawata yasa na fadi hakan,maganar gsky Hafsah karshe ce,she's juz a wife material 100yards,ga iya girki da kwalliya,iya karairaya murya,infact kar kuso kuga yadda take bamu labarin irin yadda zata tarairayi mijinta da danginsa idan tayi aure tou dalilin daya sanya na hadata da yayah kenan don shi yafi dacewa ya mallaketa,sannan kuma nasan zata share masa hawayen daya dad'e yana zubarwa ta rashin ya'ya wanda waccen juyar ta kasa share masa.....''

Dariya duk suka sanya su wajen biyar,Boddo ta cikon shiddan ce kawai bata yi ba illah takaicin Ramlar da take ji,tace''Ramlah wlhy kibi asannu don kema gidan wani zaki kuma idan dangin miji suka sanyaki agaba Allah bazaki ji dadin rayuwar aurenki ba,sannan kuma ita haihuwar ai naga ahannun Allah take,idan yaso ya azurtaka dashi,haka kuma in yaso yaki baka,don haka ki dena ganin laifin anty Jameelah don ita kanta bawai ason ranta take zaune ba haihuwa ba,and again ke baki tunanin ko matsalar daga wajen dan'uwanki take sai ita?ki duba fa duk sauran yan'uwanki ma bbu wanda ya haihu,kamawa daga Gidadon,mustapha har Surayya tou meyasa baki tunanin ko matsalolin daga wajensu yake?

Afusace tace''Wallahi ko rantsuwa nayi tou bazai ta6a kamani ba donni nasan duka yan'uwana lafiyarsu qalau don haka karki kuskura ki kakaba musu lalura if not zamu kwashi yar kallo anan wajen,mahassada kawai.....''

Dafe kirji Boddo tayi tace''lallai Ramlah ni kike fad'awa wannan bak'ar maganar?hassadar meh zan muku?okay na fahimceki,mungode da kasancewarmu talakawa acikin zuri'a,tunda dai har muna cikin qoshin lfy sannan kuma bamu rasa abunda zamu saka acikin bakin salati ba,alhamdulillah da wannan rufa asirin ta ubangiji,amma ki sani ke baki taka matsayin da har zan miki hassada ba tunda ba aljanna ce kika samu ba,sannan kuma idan matsalar ba daga wajensa take ba ai zamu gani idan Hafsan ta shigo......''

Fatima tace''Don Allah ku bari kar abun nan ya zamo muku fad'a kunga har hankalin jama'a ya soma dawowa garemu....

Da sauri Ramlah ta mike tana cin damara da gyalenta tace''Ai walhy karamar magana ta riga ta zama babba don bbu wanda zai hanani cin uban Baddo yau agidan nan,sai ta gayamun ko ni din sa'artace ko kuma ita Jameelar kanwar uwarta ce da take goyan bayanta....''

Hayaniya ta barke awajen,jama'a suka soma taruwa don tuni Ramlah takaiwa Boddo mari,ta rike kunci amma ta kasa mayarwa,cikin huci Ramlan tace''Don sarkin garinku sake maimaita abinda kikace idan kinsan baki tsorona kuma kin haifu dakyau,,shegiya sai iyayin bala'i wai ita kyakkyawa wacce tafi sauran matan zuri'ar nan kyau shiyasa tsoho ya sanya maki suna *'BADDO'* ,ai wlhy dama ina da cikinki akan wannan abun,shin wa kika fi kyau?in kin fisu tou ni Ramlah baki fini ba ehe....'' ta karashe maganarta cike da kishi,

Kuka Baddo ta fashe dashi tallafe da kuncinta dake azabar yi mata zogi,wasu suka rirrike Ramlah ayayin da wasu suka kama Baddo suna bata haquri,Anty Jameelah wacce zance har yakai kunneta itace ta fito ah rud'e,ta kutsa cikin jama'a tana zubda ruwan hawaye,sai kallo ya koma gareta ganin tana shirin magana,Ramlah ta rik'e kugu tana girgije girgije da kuma hararan anty Jameelah tamk'ar idanuwanta zasu fad'o waje,sosae Anty Jameelar ta lura da irin kallon da Ramlan ke watsa mata kuma tun ba yau ba tasan da cewa kanwar mijin nata ba kaunarta take ba,runtse ido tayi ayayin da sabbin hawaye suka tsiraro mata na takaicin abu biyu,wato auran da mijinta ya karo da kuma yadda wasu acikin danginsa suka bi suka tsaneta akan rashin haihuwa,haka ma sun tsangwami matar k'anin mijinta Azeema ammh sai dai ita basu saka mata ido ba kamar yadda ita aka saka mata,

Hada hannaye tayi tace''Don girman Allah na rokeku ku dena fad'a akaina,ni ban taka matsayin da zaku zauna kuna cece kuce akaina ba,da masu cewa bani da amfani sai faccala da dukiyar mijina,ni na rako mata ne zuwa duniya am fruitless,na rokeku pls stop bani na daurawa kaina rashin haihuwar ba,ayau da'ace mutum ne ke azurta kanshi da ya'ya tou wlhy da tuni na haifawa mijina ya'ya kan ya'ya don kawo karshen fitina da habaice habaicen dangin miji da nake fuskanta daga wajen wasunku da yawa......

Dakatawa tayi tana shesshek'a tare da sanya er yatsa ta dauke wasu hawayen da suka ziraro mata sannan ta cigaba''Ayau matar so zata shigo and i believe insha Allahu zata baku abinda kukeso wanda ni Jameelah na gagara baku shi for good 10years,ko kadan bana bakin ciki da wannan auran don ba'a kaina zata zauna ba amma pls you people should stop making me to feel dat am useless,sannan kuma Albishirunku nida kaina zanje dakko amaryata anjima don haka bni buqatar kowacce shegiya tamun habaici da jifana da kalamai na tuhuma don na rantse da Allah asannan ne zatasan ainihin kalar *JAMEELAH AHMAD SADDAM*

Tana gama furta hakan ta juya tabar wajen cike da dacin rai,kalilan mutane ne kawai ta birge ayayin da yawancinsu sun dauki hakan ne amatsayin nata salon *'KISHIN'*

   ________________★★★★

        _*BABBAN FALON GIDA*_

Babban falo ne wanda yake da girman gaske,anan ne ahalin _*TSOHO'*_  ke yada zango asha fira,ko ahadu aci abinci ko kuma aduk sanda family meeting ya taso,

  *'TSOHO'* kamar yadda ya'ya,surukai da kuma jikoki ke k'iransa,,haifaffen rugar Lugbe ne dake garin Abuja,fulanin usuli kuma wayayyen dan boko,kuma tsohon dan sanda wanda ya dad'e dayin ritaya,matan auransa biyu kuma kowanne ta zuba ya'ya ba laifi, *MAMA BARAKAH* itace uwargidansa kuma ya'yanta takwas, Alassana da Alseny (yan biyu),Haruna,maimuna,ladidi,karime,Munniru,sai Aissatou,

*MAMA DALANDA* Itace amarya mai ya'ya biyar,ita kuma duk ya'ya mata ne sai namiji daya kwal,Fatoumata,binta,Boddiya,Ma'u sannan autan gida Shagari,

Akwai zaman lfy sosai atsakanin wannan ahalin,tsoho be samu wani matsala da matayen nasa ba,,har suka koma ga Allah dukah yana mai alfahari dasu,bayan yayi ritaya shine ya'yansa maza suka daukeshi zuwa sabon gidan da suka tare da iyalinsu gabaki daya wanda shine wannan gidan da suke ciki ahalin yanxu,daga nan sai tsoho ya zamo shine mai jan ragamar rayuwar wannan ahalin nasa,akalla zai haura shekaru cassa'in aduniya ammh idan ka ganshi bazaka ta6a tunanin cewa yakai yawan wannan shekarun ba sbd yadda yake da kuzari da kuma karfinsa har yanxu,zuri'ar tsoho ba karama bace don idan na tsaya kirgo muku su kuna iya rudewa ammh zan iya ambatan kadan daga ciki,in yaso ahankali zaku zo kusan sauran,

Kamar yadda na fad'a gabaki daya ya'ya mazan tsoho su wajen hudu acikin wannan gidan suke tare da iyalinsu,Baba shagari ne kawai yake zaune da nasa iyalin ah garin Kano inda yake koyarwa awata makarantar secondary ta gwamnati,sauran yan'uwan nasa kuma wa'enda su Suke ciki daya kenan sun hada kaine suna kasuwanci dake su basu maida hankali wajen yin karatun boko ba,Baba Shagari ne kawai ya tsaya yayi shiyasa yake aikin gwamnati,,kuma wani ikon Allah sai kasuwancin ta karbesu dukah don alhamdulillah sun tara dukiyar da har jikokinsu zasu amfana dashi,Baba Alassana,baba Alseny,baba haruna,da baba munniru kenan,

Baba Alassana da kuma Alseny sune manyan 'ya'yan tsoho ammah ah ka'ida Alassana ne babba tunda shine ya riga fitowa duniya,

Kasancewar Alassana babban d'a agidan yasa tsoho yafi ji dashi aduk cikin ya'yansa,hakan yasa yafi kaunar duk ya'yan da suka fito daga tsatsonsa musamman takwaransa Suleiman,shiyasa yay masa lakani da _*GIDADO*_ wato _'LOVED ONE'_, ya dauki son duniya ya daurawa Gidado fiye da sauran jikokinsa wanda hakan ne ya haifar da kiyayyar da sauran iyaye ke masa ganin tsoho yafi fifitashi akan nasu ya'yan wato sauran jikokinsa,sai dai basu isa su fito da kiyayyar ah fili ba don atake anan tsoho zai musu wankin babban riga,

Kuma dadin dad'awa Gidado ya kasance farkon jika namiji agidan shiyasa tsoho ya dauki son duniya ya dora mishi,gashi kuma shine ya gajeshi ta hanyar zamowa dan sanda *'DCP SULEIMAN ALASSANA GIDADO'*

Uwargidan Alassana Mama Dije wacce akafi sani da Hajju ko barin wata bata ta6a yi ba,amarya mama Ummerherny itace kadai keda haihuwa,,ana kiranta da *Yumma* wato Mama kenan ayaren fulfude,ya'yanta sune ,,Gidado,Mustapha,Surayya sai auta Ramlah,

Baba Alseny matarsa daya shi kuma,mama Zaynabu,ita kuma da Haj.Karama ake kiranta,ya'yanta biyu,Aliyu da kuma Haneefah,sauran mazan kuma Baba munniru,baba haruna suma din matayensu biyu da kuma tarkacen ya'ya,Baba shagari shima dai irinta Baba Alseny ne don matarsa daya mama maryam,da kuma 'ya kwara daya tak itace *MUBEENAH* wacce tsoho yay mata lakani da *BADDO* Kasancewarta kyakkyawa mai zubin fulanin usuli don har ta dara sauran matan ah k'yau ma,

 
Duk ya'ya mazan tsoho su biyar din suna raye,acikin matan ne guda daya ta rasu wato goggo ma'u,goggo Boddiya da kuma goggo Binta ne kadai ke aure ah garin abuja,sauran kuwa kowacce da garin da Allah ya jefata,

  

   Acikin wannan kafcecen falon tsoho ne tare da ya'yansa da kuma manyan jikokinsa duk an zagayeshi sakamakon meeting din gaggawan daya hada bbu shiri sbd fadar da akayi tsakanin Ramlah kanwa ga Gidado da kuma Boddo d'iyar Baba Shagari,

Shekarun Gidado da Jameelah shekaru kusan goma da aure kenan ammh ko barin wata bata ta6a yi ba,aduniyar nan burin tsoho ayanxu be wuce yaga gudan jinin mafi soyuwar jikansa ba,duk da cewa Jameelah macece mai kyautatawa dangin miji ammh hakan be hanashi rufe idonsa ya matsawa Gidado kan ya karo aure ba,shi kansa Gidadon yana son yara don sosai ya'yan yan'uwansa suke bashi sha'awa ammh ko kadan baya da sha'awar yiwa Jameelah kishiya don aganinsa cin fuska ne,sai dai kuma ya ya iya da tsoho wanda idan ya kace ga yadda zaayi tofa kai baka isa kace a'ah ba,Ramlah qanwarsa ita da kanta ne ta hadashi da Hafsah yayar kawarta Nabeelah don dama can bata qaunar Jameelah,kai da yawan family din sun addabi Jameelah da rashin haihuwa,habaici kam tana shanshi daga wajen jahilai,kalilan ne kawai ke kaunarta,sosai take jin zafin wannan auran da mijinta ya kara ammh tasan ba laifinsa bane tursasashi akai ga mutanen da suka isa dashi,dake macece mai biyayya da kuma sanin yakamata sai bata daga masa hankali ba illa bashi kwarin gwiwar karo auran ko shima ya samu yaga gudan jininsa sannan ita kuma ta huta da fitinar danginsa,

Baddo da Ramlah ne durkushe gaban tsoho kamar ana zaman kotu,ayayin da wacce akayi taron domin cin zarafin da akayi mata tana zaune agefensu wato Anti Jameelah,fuskar tsoho ah murtuke tamau tamk'ar be ta6a dariya ba,kowa ya zuba idanu da kuma kasa kunnuwa yana jiran yaji abinda zai fito daga bakin uban mulki,

Gyaran muryarsa shine ya dad'a tattaro da hankulansu gareshi ya shiga kiran sunayen 'ya'yansa daya bayan daya''Alassana,Alseny,haruna,munniru,Shagari,Boddiya,maimuna,ladidi,karime,fatoumata,Aissatou,binta.....'' Ma'u ce kurum be kirayi sunanta ba tunda bata araye sannan kuma batayi aure ba ta koma ga mahaliccinta,

kowannensu ya amsa da na'am,Tsoho ya cigaba da magana cikin dacin rai''Inaso kowannenku ya zaunar da ya'yansa yay musu fada don abubuwan nasu ya soma kaini bango,bazan lamunci cin zarafi acikin wannan zuri'a ba,Alassana da Ummerherny ku gargadi y'arku dinnan Ramlah donna lura ita tafi kowa zakewa wajen cin zarafin Jameelah da Azeema kakaf zuri'ar nan,ita haihuwa nufin Allah ce,,ba wayan mutum ba ne ke bayarwa, iko ne na Allah,tou don menene zaku nemi ku tsangwami bayin Allah musamman ma Jameelah?bakwa ganin kyautatawar da take muku sai ci mata fuska kuke?ni harga Allah inaso ne dai kawai naga gudan jinin takwarana shiyasa kuka ga na matsa masa ammh badon naci mata fuska ba,ku kuwa yawancinku musamman ya'yanku sai habaici da kuma kalami marasa dadi kuke jifanta dasu,tou wlh gargadi nake muku da babban murya karna ji kuma karku sake nakara ganin wani yaciwa matar nan fuska in ba haka ba mutum zai gane kurensa ne,ke kuma Ramlah wlh ki kiyaye kanki dani tunda kince ke din fitsararriyar yarinyace tou kuwa bari zanyi maganinki,ke Baddo bani da matsala dake don haka kowa ya tashi ya bani wuri....''

Jikokin ne suka fara tashiwa jiki ah sanyaye suka bar falon ayayin da suketa cece kuce ahanya,ganin hakan yasa tsoho tsawatar musu atake akayi tsit don ba karamin tsoronsa suke ba,kai wasu lokutan ma idan suka bud'e masa filin rigima da tsohuwar bindigarsa yake watsar dasu😄,

Iyaye suka nemi gafarar ya'yan nasu awajen tsoho,yace''Nidai kuja musu kunne don wlh idan na tashi daukar mataki abun bazai muku kyau dukah ba,abar matan nan su wala agidajen mazajensu,ai haihuwar ba uban kowa zasuyiwa shi ba ehe,don haka karna ji kuma karna sake ganin wani nacin zarafinsu in ba haka ba sai mutum ya yabawa aya zak'inta....''

Duk suka amsa da ayi hakuri tsoho zaa kiyaye sannan sukayi gaba,wasu acikin ya'yan nasa irinsu Baba munniru da kuma wasu daga cikin matayensu suka kara jin tsanar Gidado da matarsa Jameelah,wai duk akansu ne tsoho ya had'a meeting din gaggawa har yake cin mutuncinsu agaban idon ya'yansu,lallai da sakel ya zama dole su dau mataki akai,,

Falo ya rage daga tsoho sai Jameelah sai Gidado wanda kansa yadau zafi don shi sam fitinar family dinnan nashi ya soma isarsa,gskiya gidan yawa beyi ba,tsoho ne ya umarcesu dasu tsaya yana da magana dasu,tsoho yay gyaran murya ya shiga tsokanar Jameelah''Tou wai bazaki dago ki kalli megidan naki bane ko kuwa so kike saina biya kudine kafin ah kallenin?'' murmushin yake ta sakar sannan ta dago tana dubansa,saukar da ajiyar zuciyar gidado ne ya maida kallonsu dukah gareshi,tsoho yace dashi''Kai takwara yaya dai?na takura rayuwarka da yawa ko?''

Ai kuwa kamar yasan abunda ke ransa kenan ammh kala bece masa ba,jin shirunsa yyi yawa yasa tsoho maida kallonsa kan Jameelah,da sauri ta mayar dakai kasa zuciyarta na bugawa,tsoho yace''Jameelah kiyi hakuri ki fahimceni,harga Allah bawai cin fuska nayi maki ba dana tursasa gidado karo aure ba illa yadda Allah ya jarabceni da son ganin gudan jininsa,,nasan akwai 'ya'ya da yawa daga sauran jikokaina ammh bansan meyasa nafi kwadaituwa da son ganin nasa gudan jinin ba,kiyi hakuri Jameelah ki karbi uzurina,,ammh ina mai tabbatar miki da cewa bbu wanda zai sake cin zarafinki ah zuri'ar nan harna tsaya ina kallonsa ban dauki mataki ba,sannan kuma kisa aranki cewa zamaninki nanan daram ah zuriar tsoho bbu wacce zatazo ta saukar da martabarki koda kuwa ta haifa ne sai in har kece kikayi sakacin da har zatayi nasarar sauke zamanin naki har abar yayinki........

        Cike da zafi Gidado yace''Tsoho meyasa ka kasa ganewa ne?sau nawa zance maka munje asibitoci yafi akirga akan rashin haihuwarmu ammh duk inda aka dubamu sai kaji ance lafiya lau muke dukah lokacin haihuwar ne kawai beyi ba,tou meh zaisa bazamuyi hakuri ba?ai Allah bai manta damu ba kuma nasan insha Allahu yana nan waiwayowa garemu ya share mana hawaye.....

Da sauri Jameelah ta mike ta fice tana cizgar kuka,fitarta cikin wannan halin ya sake daga hankalin gidado,da sauri ya mike zai mara mata baya,tsoho yay hanzarin dakatar dashi ta hanyar kiran ainihin sunansa da wani irin kakkausar murya _*''SULEIMAN…!''*_

Cak…! ya tsaya tare da waiwayowa dauke da tsantar mmki akan fuskarsa don da wuya tsoho ya ambaci ainihin sunansa,komawa yay ya zauna don yasan abinda yakeso kenan basai ya jira yace masa ya komo ya zaunan ba,

Tsoho yace with full seriouness''Suleiman kasa aranka cewa muddin itama wannan din ta shigo bata haihu dakai ba,,tou insha Allahu ni tsoho zansa ka jaraba auran gida gida,,don acikinku dukah hatta iyayenku bbu wanda ya ta6a shaawar yin auren dangi,,don haka ni dakaina zan za6o maka macen kirki acikin zuriar nan don ka aura,,watakila idan akayi 'yar gida gida sai kaga an dace....''

Kallon kwayar idonsa Gidad'o yake cike da mmkinsa don tabbas iya gaskiyarsa yake fad'a,be gama tsinkewa da lamarin ba kawai yaga tsoho ya fashe da kuka,da sauri Gidado ya isa gareshi zuciyarsa na kuna yake fadin''wai shin kaka ni kadai ne jikanka namiji acikin zuri'ar nan?gasu mansur,Gambari,Saikou,Yaro,Ibrahima Mustapha dadai sauransu,shin su din ba mutane bane sai nine zaka takurawa?ga kuma ya'yansu nan duk sun haihaifa inajin mustapha ne kawai muke jirgi daya dashi,tou meyasa bazaka takurashi ba sai ni?sannan kuma ai inajin ya'yan sauran sun isheka basai lallai dole mu mun haifa ba musamman ni daka fi takurawa,ni don Allah tsoho ka fita daga harkar rayuwata banison matsi da takura,kuma insha Allahu daga Hafsa dinnan bbu kari,,shin ina kke son nakai mata fiye da biyu ne?kai ne zaka ciyar mun dasu?ni wlh arayuwata bani da raayin ajje mace fiye da daya ammh gashi ka sani dole sannan kuma hakan be isheka ba tun baa kawo ta biyun ba kana sake bani umarnin karo wata idan har itama wannan din bata haihu ba,shin wannan wacce irin jarabace haka?ka sani koda kuwa zan aura mata sama da dubu ne idan har Allah yace bazan haihu dasu ba tou bbu wanda ya isa ya canza hakan.......''

Ji kake tatassss! an daukeshi da wani irin mahaukacin marin da har sai daya ga walkiya sun gifta idanunsa,azabar bata gama sakeshi ba yaji an kara mai wani,,muryar Baba munniru ne yaji ya daki dodon kunnensa,magana yake cikin tsananin fushi da kuma dacin rai''Uban namu ne ka tsaya kke jefawa magana haka tamkar wani sa'anka?ai idan tsoho bai haifeka ba ya haifi ubanka Alassana,,ko kuwa don kaga yafi kaunarka akan sauran jikokinsa ne shiyasa kke takashi yadda kaga dama...?ai ina ji ma adadinka ne don ya nuna damuwa akan rashin ganin gudan jininka ah doron kasa,,ammh dake kai din butulu ne......''

   Da sauri tsoho ya tari numfashinsa ta hanyar daka masa tsawa yace''Kai munniru banison iskancin banza,shin waya sako bakinka cikin zancen nan ne?ka tafi ka bamu wuri bbu ruwanka dani da jikana....'' kafin ya gama rufe baki yaga Gidado yasa kai ya fice zuciyarsa na azalzala,murmushin takaici ne ya su6ucewa Baba munniru yace''Tou dubi wanda kafi fifitashi akan kowa dubi yadda yake watsa maka kasa ah ido,,ko kadan baya darajaka da kuma ganin girmanka sai in an tursasashi dole,gaskia tsoho yakamata ace kayi karatun ta natsu,,lokaci yayi dayakamata ace ka fita daga rayuwar Gidado da kuma dena fifitashi akan sauran don hakan ba karamin haifar da kiyayya yayi atsakanin mutan zuri'ar nan ba,,kai ni kaina haushi nakeji yadda baka wani damuwa da nawa 'ya'yan sai tsatson Bobbo Alassana (Yaya Alassana),komi dansa Gidado Gidado haba yakamata ka kwatanta adalci mana yabba (Baba).....''

Shiru tsoho yayi don yama rasa ta cewa kuma baya jin zai iya rage son da yake ma Gidado don sauran su samu,ayau daace wani ne acikin jikokinsa yay masa wannan rashin ta idon tou da wlh daga shi har iyayensa sai sun fuskanci hukuncinsa,,ammh sbd qaunar da yakewa Gidado haka yana ji kuma yana gani yake takashi son ransa ya tafi kuma bazai dauki mataki akai ba kuma duk wanda yay yunkurin dauka sai kaga ya takama wannan din burki,,duk umarninsa da Gidado kebi tursasawar iyayensa ne in ba donsu ba bbu umarnin tsoho ko daya da zai cike.....

   ____________★★★★

 
Ciwon kan daya saukarwa Gidado akan rikicin Tsoho be gama sakeshi
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment