You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
kwaryan walima wacce za'agabatar da ita aranar bayan sallar la'asar.
4:00pm compound din gidan yasoma cika da 'yan uwa tare da abokan arziki.
Hud'u da rabi dai dai su Bahijja suka baiyan awurin, sanye suke cikin wani had'add'en material white, d'inkin riga da sket sai suka d'ora baqar abaya asamar kayan, faces dinnan tasu tasha makeup, duk da Bahijja batason irin wannan kyalliyar amma Adda Asma'u tadage sai anyima mata bayanda ta iya hakanan ta tsaya akayi mata, sai kuma gashi yayi matuqar mata kyau sosai.
Walima ta qayatar sosai, anci ansha an gyatse cikin walwala sai fatan Alkhairi akeyi musu.
Sun sami gifts awurin Bashir, Bilal, Mujaheed tare da wasu daga cikin 'yan uwa.
Ana kiran magrib ana yin addu'ar tashi a walimar don haka wasu duk cikin gidan suka shigo domin gabatar da sallah.
Bahijja ta fito wanka tana shafa lotion Sumy tashigo "Adda B kizo Abba nakiranmu yana parlour n shi "to jirani mutafi kawai.
Sun sami Abba tare dasu umma da kuma su Mujaheed da Adda Asma'u. Suka sami wuri suka zauna tare da gaishe da kowa daya bayan daya.
Abba ya umurci Mujaheed yayi addua tukunna, addua yaja mai tsayi sannan ya cike da fatiha aka shafa. Bahijja baki tasaki tana kallon Mujaheed ganin yadda yake feso addua kamar wani balarabe, har aka shafa adduar bata saniba, tana can wurin kallon Mujaheed, suna had'a ido ya harareta tare da motsa baki ahankaki yace "kallonfa? Ta fahimci miyace donka sai ta murgud'a mishi baki ita ahankali tace "shafa kaji, ido ya zare ya zaro yana nuna qirjinsa ma'ana ni ta gyad'a kai tana mishi kallon uku saura ya hade rai tare da kauda fuska itama kauda fuska tayi tana murmushi domin taji dad'I ganin tabata mishi rai.
Sumy dake kallon abinda ke faruwa ta sami cinyar Bahijja ta manna mata mintsili tayi fuska kamar ba ita tayiba. Qara Bahijja tasaki tare da miqewa tana kakkabe sket dinta tana fadan wayyo cinnaka ya cijeni washhh Allah azaba. Tsawa umma ta daka mata "ke!!! Natsu ko intashi insaba miki yanzu. Ta matsa jikin umma tana matsan kwalla, tace "umma wallahi da zafi ne, dibama kigani har ya tashi wurin tana qoqarin yaye sket din, hannunta umma ta make tana cewa "kifita idanuna fa, inbanda iskanci ina kika taba ganin cinnaka agidannan da xakice ya cijeki? To Allah inbaki shiga hankalinki ba zan mugun saba miki tam.
*Mrs j moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*
©Safiyya.
*17*
Takoma ta zauna tana share hawaye domin sosai taji zafin mintsilin, mumny ta jawota jikinta ta kwantar da kanta bisa cinyarta tana kallon Mujaheed wanda ke ta murmushi da alama yayi farin cikin ganin hawayenta, tura baki tayi tana share fuskanta. Abba yayi gyaran murya duk aka natsu yasoma magana "Alhamdulillah ala kulli halin, lallai yau muna cikin farin ciki a karo na biyu masu kama da juna, munyi ta farko kamar wannan sanda Mujaheed ya had'a haddarshi to gamu cikin ta biyu, muna fatan samuwar ta uku har ma data kasa irga.
Ya ja fasali sannan ya d'ora Bahijja da Sumayya kun sanyamu cikin farin ciki mara misaltuwa sakamakon haka bana daku za asauke farali ma'ana aikin hajji.
Allahu Akbar!! dakin ya dauka sai kuma akasoma yiwa Abba godiya su Sumayya da Bahijja baki har kunni anata murna zuwa can Abba yayi gyaran murya aka saurara.
"Abu nagaba kuma shine, shin zaku cigaba da karatu ne insakamakon ku yafito ko kuwa aure kuke so?
Tsit parlour n yayi na tswan wani lokaci zuwa can Bashir ya katse shirun da cewa "ita dai Sumayya zata fara karatu, inta kai kamar shekaranta ta biyu sai tayi aure tacigaba ad'akin mijinta. Abba yasaki murmushi "hakan yayi Allah yanuna mana lokacin "Amin mutanen parlour n suka amsa.
Abba yakai dubanshi kan Sumayya yace "dawa kukai Alqawarin auren ko sai lokacin yayi zaki fitar dashi? Ta sunne kai tana murmushi ta nuna Bashir da hannunta. Duk aka zubawa Bashir idanu, shi kam kansa ya sunkuyar yana murnushi. Abba cikin murna yace "to Alhamdulillah abu yayi dad'I, tunda kun had'a kanku muna murna da hakan Allah ya kaimu lokacin lafiya "Amin suka amsa.
Bahijja ta dimawa Sumayya dundu a baya sannan ta sa hannu dana qoqarin d'ago kanta data sunne a cinyoyinta tace "gulma wuya d'ago ki kalli kowa domin nan ba bare ciki da kike wani soke kai kamar bushiya. Buge hannunta tayi sannan ta dago tana hararanta "dallani kikyaleni, mutum yanajin kunya kinzo kina damunshi da surutu kamar akun kuturu. Dukka parlour n akasa dariya harda Abba.
"Nadawo gareki Bahijja, Abba yace hakan yana dubanta, zama ta gyara tare da gyad'a kanta.
"Ke waye gwaninna ki kuma kina da burin karatun ko a'a? Ta sunkuyar dakai tasoma magana ahankali "ni Abba ina son inyi karatu sosai inson samune sai na had'a degree sannan zanyi maganar aure kuma game da miji, na tsaida yaya Bilal. Daram!!! Gaban Mujaheed yabada sauti jikinsa yasoma rawa sam bai zaci zata kawo maganar Bilal ba sabida yasha jin tana fadin ita baza tayi aure yanzuba karatu zatayi, jin haka yasa bai gwada nuna mata shima yana cikiba, wai nufinshi sai ta kusa kammala karatun ta sai yafito mata amutum, duk da yasan tana tare da Bilal,wai atunaninsa Bilal shadow ne kawai.
*uhmm su mujaheed manya ooo*
Can yajiyo Abba nacewa "aina shi Bilal d'in yake? Mummy ce ta amsa "Alhaji yaron Sarki Ahmadu abokin malam nagarin su Lanti mariqiyarta.
shiru yayi zuwa can yace "oh yaronnan mai yawan zuwa ko? Yacigaba wanda nake yawan ganin su tare. "Eh shine Alhaji, to hakan yayi zan nemi iyayenshi inji.
Ya gyara zama ya dubi Mujaheed wanda duk ya had'a uban zufa kamar ba ac a parlour n.
"To kai fa, Miye labari game da wacce ka fitar? Kallo ya qure Bahijja dashi wanda yasa gabanta fad'uwa yana dukan 100~100 hhhhhhhh.
"Ehm ina saurarenka, muryan Abba yadawo dashi tunanin da yafad'a.
Da kyat yasaita kanshi cikin dakiya yace "labari na wurinta yanuna Bahijja da yatsa, tazabura ta matsa jikin Adda Asma'u tace "ni kada kasani a garejin haqora arasa mai taunani ehe, kadai memo mai adana bayanenka can amma baniba tam. Sosai taba da dariya a parlour n. Shiko gogan ko murmushi baiyi sai wani haderai yakeyi yana cin magani. "To ya isa nagano ba bayani agareka to inajiranka. cewar Abba, kai ya gyada yana sauke ajiyar zuciya, yasaci kallon Bahijja ta dalla mishi harara ta motsa baki ahankali "mugu kawai, murmushi yayi domin sarai yagano mitace masa.
Bashir ne yarufe zaman da addua aka shafa.
Fruits da aka yanka aka umurci kowa yad'ebi yadda yakeso, Sumayya ta cika wani faranti mai fad'I tafice zuwa kaima su hindu.
Sun baje sunata shan abinsu sannan suna hira cikin nushad'I, Bahijja ta koma gefe ta zauna shiru, cikin tsokana Sumayya tace "uhmm uhmmm!! Ku karkad'e kunnuwarku kusaurari labaran duniya. "Munajinki suka kace atare, sai da tayiwa Bahijja gwalo afakai ce sanna tace "aha yau wata yarinya ta fada tarkon son mazaje biyu, daya mai wuyar raqumi daya kuma tubar kallah masha Allah, to aganinku waza ta zaba cikinsu? Munirat ce ta amsa "a'a ga tubarkallah me zatayi da mai siffan ragumi.
aiko Sumayya tasa dariya har da ruqe ciki, suma dariyan sukeyi,
tsaki Bahijja taja tana hararan Sumayya "iska na wahalar damai kayan kara, tace sai kuma tafice zuwa part din mummy.
Tana shan kwana Mujaheed na fitowa parlour n zata koma da baya cikin zafin nama ya fizgota ta bude baki yaza fasa ihu ya rufe bakin da hannunshi, yajata zuwa d'akin Sumayya sabida yasan mummy bata cikin parlour n.
*masoya inaji daku aduk inda kuke sosai, wannan shafin nakune, Allah yabarmu tare Amin*
*mrs j moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdun *(bebeelo)*
©Safiyya.
*18*
Bai saketaba sai a tsakiyar dakin. Hararansa tayi cikin tsoro taja baya tace "miye haka malam? Bai amsaba ya soma matsota fuska ahad'e ganin haka yasa tanemi gudu tashige toilet tako daya yayi ya damqota ya had'ata da jikin bango ya matse tasaki ihu, ya d'aga qafarsa ya take qafarta ya murza da qarfi ta qamqameshi tare da cukuikuye mishi gaban riga, cikin jin azaba tace " wayyo mummy yajimin ciwo,
kallonta yayi yana murmushi ya dan jabaya yana qarewa qirjinta kallo, sanye take cikin t-shirt mai gajeran hannu ta matseta kadan sabida robace rigan.
Warware qaramin gyalenta data daura tayi ta yafa akanta zuwa qirjinta, lura datayi da ya tsurama boobs d'inta idanu.
Harara ya aunamata tare da jan tsaki, ta sunkuyar da kanta qasa tana qunquni, d'ago kanta yayi da hannunsa ta runtse idanunta, ya tsurawa sumar giran ido sai kuma yasauke idonsa bisa bakinta, d'an qarami mai kyau da alama zaiyi test yayin kiss; ya ayyna haka aransa sai kuma yamatsa sosai jikinta,
don tanajin saukan numfashinsa, da sauri ta bud'e idonta tare da zarosu waje, cike da tsoro ta bude baki zatayi magana yayi saurin ta hannunsa a bisa lebbanta yana mata wani kallo mai wuyar fassaruwa. Ido ta zura mishi tana ganin ikon Allah.
Bude hannayenshi yayi, yamata bake bake tare da yimata rumfa da faffadan qirjinsa. Daf da kunninta ya furta "mikike cewa d'azun kafin asoma taro?
Shiru tayi, tana gwama numfashi, ya cija kunninta da d'an qarfi tasa qara tare da liliya wurin "ko bakyaji nane ina tambayarki? Yace mata, Cikin daburcewa tace "to ni minace maka? Murmushi yasaki mai sauti yace "au kimanta kenan? Tana zare idanu kamar kyankyaso a gora, tace "eh, tunamin to.
Yana kallon idonta ya dora hannunsa akan boobs dinta da sauri ta buge masa hannun tare da turashi baya
"banson wuqanci jaheed tace dashi fuska ahad'e, hararanta yayi sannan yace "au bashi dama kikeso inshafaba, da dazun kikacemin inshafa inji, to wai dazanji ne ko ya nuna ko da sauranshi. Idanu waje tace "yau naboni!! Dama haka kake yaya Mujaheed bansaniba?
"Minayi kuma? Daga na aikata abinda kikeso sai kimin fassara don gulma.
Juya mishi baya tayi don haushi yabi hips dinta da kallo ga mazaunarta masha Allah duk sun ciko, ya batarai "to juyo haka nan nagama kallonan nasu, nagani sun soma cika sai abar shafa musu mai din hakannan.
Juyowa tayi tana dan bubbuga qafafu cikin shagwaba tace "wallahi Jaheed zan hadaka da mummy tayimin iyaka da kai, kuma kabudemin qofa in fita. "In anqifa? Yace tare da tsaceta da ido, tatura baki "inma ihu, "oya yima maza kiyi. Tayi shiru tana kallonsa shima ita yake kallo. "Uhmm nidai kayi haquri ka budemin tafad'a cikin sanyi, yayi mata banza "don Allah yaya Mujaheed ka budemin qofa kada anemeni, takuma fad'a, tsayuwa ya gyara yace "zan bude miki amma sai kin koma kincewa Abba ni kika tsayar amatsayin abokin rayuwarki ma'ana ni zaki aura inkin gama karatunki.
Baki bud'e take kallonsa saikuma tasa dariya ta nuna shi da yatsa "ni da kai ne zamu zamo abu 1 tafd'ijan!! Zako ayi k'wan wuta, kut!! in aureka fa kace, lallai mufarki kakeyi kuwa.
Taja numfashi tare da watsa mishi kallon banza sanna tace "to bara kaji wallahi Allah kai bakamin ba, baka cikin irin mazan da nake muradi, kai ba type d'ina ne, kaji da wai ni Bahijja kayan Bilal ne kuma shine abokin rayuwata na har abada da yar dan Allah, don haka sai kaja jiki kanemo type d'inka amma banda ni! kayan saraki ehe. Tasa aya tana murguda mishi baki cike da tsiwa.
Kallonta kawai yakeyi yana murmushi, dama voice dinta kawai yakesonji yayin da take fad'a, asannu yake fita ba wani hayaniya duk da kuwa ita tadage sai masifa takeyi aganinta.
Bud'e qofar yayi yafice abinshi cike da nushad'i.
Bayansa tabi da kallo tana mamaki bai dokeba ganin tayi masa rashin kunya saima ya fice yana murmushi kamar gonar auduga.
Siririn tsaki taja ta fad'a bisa bed tana dafe kanta dake sara mata.
*my b3 low, ayi haquri da wannan, qila zuwa dare in d'ora akai*
*mrs j moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*
©Safiyya.
*19*
Kwanarsu Hindu biyar sukayi haramar tafiya gida.
Umma tabawa ko wacce kayan kyalliya masu kyau da tsada ita kuwa mummy kayan gyaran jiki tabasu dangin su humra da kulacca da dai sauransu, suna ta godiya. Abba yayi musu kyautan kud'i sannan yabada riga da wanda tare da babbar riga na shadda mai kyau da tsada da hula da takalmi yace akaiwa malam.
Misalin 11:15am Bilal ya iso, shi zai maidasu kamar yadda ya kawosu.
Suna tsaye jikin motar suna magana ahankali yadda bamaiji sai su. "Princess yanaga ranki abace, ko da matsala ne? Bilal yace da ita yana leqen idanunta data sunkuyar dashi qasa. Bata amsa shiba illah ta matsa tasoma tafiya yabi bayanta cikin sanyin jiki, d'annesa dasu tayi sannn ta tsaya ta juyo tana kallon motar, idanun Munirat na kansu wacce ke zaune gaban motar su kuma suna Nana suna site d'in baya.
Ta d'auke kanta tare da had'e giran sama dana qasa. Cikin lallami Bilal ya kama hannunta yayi qasa da murya "sweetie don Allah minayi miki wai?
Kallon hannunta da ya riqe tayi dasauri ya saki hannun yana wani marairai cewa "queen bakyaso inyi driving mai kyau ko? Ta girgiza kai, "to in hakane fadamin damuwarki inji, sai da ta kalli sashin Munirat wanda idanun ta nakansu har lokacin, sannan tace "mike tsakaninka da Munirat? Tambayar tazo mishi abazata sabida haka sai duk ya daburce bakinshi na rawa yace "wani abu akace miki akanta? Ido ta kafeshi da shi ganin duk ya daburce sai tasamu kanta da fad'uwar gaba. Shin kodai maganar Sumy zaitabba ne, tafada haka aranta. Shiru sukayi suna kallon kallo zuwa can tace "tunda kaqi amsamin tambayata to kayi maza ka maidata site din baya, maryam tadawo gaba domin ban amince da zamanta gefen kaba, kallonta kawai yakeyi yarasa gane inda ta dosa.
Tsayuwa ya gyara yace "sweetie ban fahinci inda zancen ki yayi ba "ta tura baki tare da hararan motar tace "to bara nayi maka gwari gwari, cewa nayi Munirat ta fita a gabar motar ka takoma baya sai maryam tadawo gaban, kafahimta yanzu ko? Kai ya gyada yana share zufar da ya tsatsafo mishi agoshi.
"Queen kiyimin alfarma ta zauna a inda take, next time sai in kiyaye tunda ba kyaso. Zatayi magana ya rigata "don Allah don Annabin rahama ASW kada kimisamun.
kauda kai tayi sannan tace "to nabari amma sai kafadamin mike tsakaninku.
"bakomi Allah queen sai 'yan uwantaka najini "uhmm naji amma bangamsu "don Allah kiyarda dani ni nakine ke daya har abada, bawata agabanki, haba my princess hasken ruhin Muhammad Bilal, yaqarasa yana soka yatsarshi a dimple d'inta hannunsa ta buge tana murmushi, jinjina yayi mata yace "sai kayan saraki ita daya kwallin kwal tasa 'yar dariya tana jinjiga kai.
Suka jero zuwa wurin motar suna zancensu cike da nushad'i.
Bayan ya daura belt ya dubeta "haskena kada kiyi barci yau kwana hira zamuyi, "tam habibi ta amsa masa tana duban Munirat ta gefen ido, fuskan nan nata kamar anyi gobara.
Ta zagayo gefenta ta dafa kafad'anta "my neerat agaidamin da mama sosai, nagode sai nazo muku bangajiya, gyada kai tayi batare da tayi magana ba.
Suka had'a ido da maryam ta yimata jinjina da hannu, murmushi tayi tare cewa "Nana sai nazo bikinki "kai Adda Bahijja nisai kinyi zanyi tana hararanta ta amsa "ni sai nayi degree har da degir gir yarinya, sabida haka kisawa kanki onga ki shiga daga ciki abinki.
Dariya sukasa dukkansu har da Bilal.
Tana tsaye har suka fice get sannan ta juyo tayi ciki.
Lokacin aikin hajji yayi, suka tafi tare dasu umma, suna can result dinsu yafito. Suna dawowa bajimawa Bashir yayi musu registration sabida sakamakon nasu yayi kyau sosai.
Sumayya mass com zatayi, Bahijja kuma computer science.
Soyayarsu da Bilal sai qara bungasa takeyi sai dai tana zargin yana boyewa mata wani abu amma tazuba mishi ido tagani ko zai fadamata
Tsaye take tana daura agogo a tsintsiyar hannunta, ta tsinkayi qamshin turarensa mai dadin shaqa, ta amsa sallamar da yayi tabi gefenshi zata wuri ya riqe mata gefen gyale wani kallo ta watsa mishi ta fizge gyalenta yayi gaggawan janyo kafadunta ya riqe gam tare da matsasu ta runtse ido ta bud'e tana hararansa murmushi yayi sannan yace "haka aka ce miki ana tarban masoyi? Ta zare ido tana waige waige sarai yagano dubawa take ko wani yajiyo zancenshi.
Ganin bakowa a parlour n yasa ta tureshi tace "Allah yakyauta inzamo masoyiyanka, nafadama ni din kayan sarakine, don haka sai gani sai hange daga nesa, duk kuwa maitanka sai kabarni ehe, kwalelen mai qaton ciki.
Cizon lebbansa yayi tare da shafa tumbinsa "'ya'yanki ne a ciki ai 'yanmata, tsirtar da yamu tayi tace "wa!?
can gasu gada dai wai zomo yaji kid'an farauta, tasa kai tafice tana gyara ruqon handout dinta.
yabi bayanta da kallo, ahankali ya furta "insha Allah sai na mallaki komi naki yarinya, ya qarasa dinning domin yin break.
*Ayya khadeeja candy sannu, Allah qara lafiya yasa kaffara ne.*
*uhmm uhmmm dafatan ba ehmmmm kikesoba, in shine kitaho niya ina da magani hhhhh*😜
*mrs j moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*
©Safiyya.
*20*
Wurin wata qaramar motar fara sol sai daukan ido takeyi ta nufa ta bude tayi bismillah sannan ta zauna ta juya back site ta zube handouts dinta kusa da laptop da ke ajiye.
Horn ta danna zuwa can ta qara latsawa taqi cire hannunta awurin don haka horn din yayi tafita baqau qautawa zuwacan sai ga Sumy tafito gyale ahannu tana goge bakin ta da tissue, har ta iso Bahijja bata saki horn dinba, saida Sumy ta zauna gefenta sannan ta saki, hararan Sumy tayi "tace kin kyau ai tunda kin dimaitani da qara bata tanka taba sai da tayi reverse tana shirin fita get tace "ai Allah daga yau kingama batamin lokaci da shiririntanki kamar mai naqudar d'iya mace duka ta taska mata acinya tana dariya "ke fa 'yar buhu ce mai naqudar mace ce tafiye shiririta ko mi? "A'a dalla can bashirita nake nufiba dad'ewa, kinsan ance naqudar mace wai yafi dadewa da wuya "injiwa? "Ke bansani ba 'yar jaridan banza kawai "aiko sai kinfadamin yau "innaqi fa? "Kici na jaki sai dayi dariya sannan tace to bissimillah, wuyanta takawoma shaqa cikin wasa, ido ta zare tace "ke bari wasanan haka kada tsautsayi ya afku tana dariya ta kwanta baya tace "Allah yatse afkuwan komi sai Alkhairi "Amin.
Suna zaune qasar bishiya suna hira bayan fitowarsu lecture.
"Adda B wai ya kukayi da sarakinki akan kiranshi da kikayi Munirat ta dauka, lumshe ido tayi sanan ta amsa "yakasamin gamsheshshiyar bayani sai kame kame keyimin sabida haka tun jiya nakashe 4n dinta, nasan yanzu yanta nemana, quri Sumy tayi mata da idanu, tacigaba "amma nayanke shawara zan tambayi Maryam inji mike faruwa sabida tun wuri insan matakin daxan dauka akai "uhm to Allah yasa kiji Alkhairi "Amin ta amsa.
"Amma dazakijj shawarata da kinyi qoqarin cire son Bilal aranki ki kama dahir wanda kika tabbatar da baki da 'yan hamayya ciki. "A qufule ta dagamata hannu "ya isheki haka nan Sumy, riqe shawarnki bata samu karbuwaba anan.
"Wallahi Adda B komi zakiyi sai nafada miki gaskiya indai akan Bilal ne, haba ace mutum kamar 1 don siranta, amma kina nacinsa alhalin ga d'an dama dama, son kowa qin wanda yarasa, amma kin kau da kai a gareshi, taja numfashi sai kuma tacigaba haba don Allah kisanja tunani gaskiya kam, domin ba kudace da junaba sam wallah.
Tagumi tayi tana sauraronta har tasa aya "kingama campaign din? "Bawani campaign sai gaskiya kuma daga qinta sai bata "bakinki yabiki Sumy bazanga bataba ataraiyata da yaya Bilal, sai dai naga Akhairi insha Allah, kuma kisani konarashi bazan auri yaya Mujaheed ba sabida bana son.... saikuma tayi shiru kana kallon Sumy. "Cigaba man da zancenki Adda B, ko kunya kikaji?"to kibar jin kunya. Sumy take fadin haka tana kallon Bahijja.
kauda fuska Bahijja tayi ranta abace.
Sumy ta miqe "bari insamo abu mai sanyi a shop dincan, tayi gaba abinta batare datajira amsawar Bahijjaba, amma da alama ranta yabashi itama.
Ta ajiye mata kwankwanin deaw mai sanyi sosa, ta zauna a inda ta tashi dazun tare da bude nata deaw din tasoma tsotsa ahankali. Bahijja tayi tsam daranta sai kuma ta matso jikin Sumy "Sis Sumy kiyi haquri, rai nane yabaci wallahi amma inason yaya Mujaheed sai dai ba irinta ta aureba. Murmushi Sumy tayi "Allah nafahimceki Adda B kada kidamu.
Rungumeta tayi "nagode sis dakika da fahimta ta da kikayi, Allabar zumunci "Amin Adda B abin dadin saraki, duka ta kai mata "baki da kunya Sumy "yo ai kece malamata, murmushi tayi bata qara cewa komiba.
*mrs j moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(bebeelo)*
©Safiyya.
*21*
Zaune take akusa da parking space awani dan baranda da aka zuba kujeru, tsakiyarsu wani table ne mai d'an fad'i. kujeran dake fuskantar get ta zauna yadda zata iya hango duk wanda zai fita da wanda zai shigo.
Tana ta latsa laptop tare da bin karatun QUR'ANI wanda sheikh Abdulrahman sudex ke ja cikin suratul Namli, dake fitowa daga acikin wayarta.
Sumy ta iso ta zauna gefenta, ta kwanto jikinta bisa kafadanta.
Kallaonta tayi cikin kulawa tace "Sis baki da lafiya ne? "Eh, marata ke mintsilina kuma banjin kuzari ajikina sam"ayya sannu, shiyasa naji jikinki da zafi, ta amsa "yawwa tana leqa abinda takeyi a laptop.
"Waye junaid kuma Adda B? Tana cigaba da typing ta amsa "abokin yaya Bashir ne "miye hadinki dashi? Sumy tasake tsilla mata tambaya tare da zuba mata idanu, daka tawa tayi da abinda takeyi ta tsare Sumy da idanu itama, sun dauka wasu 'yan daqiqu suna kallon juna sanna Bahijja ta kauda fuskanta tace "mikike nufi da min wannan tambayar?
Dariya sumy tayi "kedai amsamin tambayata sannan taki tasami shiga.
Ta gyada kai "babu komi illah friend dinane a Facebook, to shine yaganni a online yake tambayata yaya Bashir yana gida yazo yasameshi? Nace ya fita, daganan ya tambayeni karatu da dai sauransu.
"Ok nazaci shima yana cikin layine, "koba layiba tace tana hararanta, tacigaba "dayake kinmai dani kaza uwar son maza ai dole kowani jajibe jajibe kice ni.
"Kai Adda B, to maida wuqar ni ba haka nake nufiba, inadai taya saraki gadin kayansa ne. "Kyaji dashi dai 'yar rainin hankali, inma zakifito amutum kifadi gaskiya kifito, baruwana da gulma,
ko yaushe kika soma yi da sarakin dazakice wai kina tsaron kayansa ne.
"Allah Adda B yanzu bana adawa dashi sabida nagano gaskiyan zuciyarki, na sanar da yaya Mujaheed da yayi haquri dake, Allah zai bashi wata.
Tana kallonta a yatsine tace "to miyace da yaji haka? "Sirrine yarinya, baza kijiba. "Surro mata dallanku ma kwal kwala kawai, dariya Sumy tayi sosai, cikin dariyan ta amsa "eh dai munji, kuma zakiyi mamakin matar da zai zabo cikin tarin