Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

y’ar dab’as... wata dariya ce ta kufcewa Hamda, ganin duk suffofin da ta zayyana
Haka zubinta da fasalinta yake, sam bata da tsaho ko kad’an...



Hajiya Didi tamu....
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE


YA ABIN YAKE ?

LIttafin Nazeefah Nashe.

08033748387


Follow me on ArewaBooks
@nazeefah
https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e



✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽


ELEGANT ONLINE WRITERS

(Haɗin kai shine takenmu.)

Page 5
Ina macen datake fama da ciwon mara in mijin yana saduwa dake kirinka jin xafi to kixo kimallaki female care

Ina masu fama da basir constfree tea yana magnin basir yana gyara fata tayi kyau

Royal jelly ya gyara mace yafito mata da shafe dinta kama daga breast hips duwawo

Fat bunner yana rage kitse ina wanda kitse ya mata yawa a jiki kigarxayo kimallaki naki 09131164861

Gamai bukatan yin register xai iyayi yasaya afarashin company

Company ght zakiyi registered akan 4500 kikawo mutun biyu suyi siyaya company zatabaki 36000 inbaki shiryaba karkimin mgn ngd








****************************
_Mu d’in ba wasu masu wadata
bane sai dai muna cikin ni’imar ubangiji, don bamu rasa ci ba, bamu rasa sha ba, Kakanku a tsaye yake sosai akan iyalinsa ta yarda duk abinka baka isa ka hango gazawarsa ba, ya tsaya sosai musamman ga karatun iyayenku, burinsa a kullum bai wuce yaga sun samu nagartaccen ilimi ba, na boko da na muhammadiyya, Musamman Babanki Umar. Sanda ya gama secondary School Allah ya taimake shi har jami’a yaje can zaria inda yayi karatunsa a ‘bangaren Zane-Zane kasancewarsa mai hazaƙa wata rana kawai yazo min da labari mai dad’i wai Gwamnati ta d’au nauyin karatunsu ‘kasar waje can ‘bangaren larabawa ‘kasar Jordan zasu je su yi babban degree a can. Mun yi murna sosai sai dai Kakanku ya ce bai isa ba, ba zai tafi ba sai da aurensa, amma mahaifinku ya turje ya kuma kawo uzurin gwamnati tace ba zata d’au masu mata ba saboda ba zasu d’au nauyin mutum sannan su d’au nauyin iyalinsa ba, har da ce mana sunce sai dai ya hak’ura Haka dai dole muka k’yaleshi ya tafi ashe tafiyar zata zame mana jangwamgwam domin dai a can ya had’u da alak’ak’an uwarki ya aura.



Tafiyarsa da wata uku yayi mana aike akan ya samu mata zai yi aure a can. Ai kuwa na rufe idona na ce bai isaba, hakan ya tashi hankalinsa sai gashi ya dawo k’asar ba shiri lokacin watansa shidda da tafiya. Da Allah da annabi da saka malamai suyi mana wa’azi muka amince da yayi auren amma da sharad’in ni da kakanku zamu je muga tushe da asalin yarinyar. Bai wani damu ba ya ce mana ya yarda. Nan muka fara cuku-cukun tafiya kakanku ya siyar da gonarsa d’aya muka tafi har da k’aninsa da suke ciki d’aya wanda kuke kira Baffa Mamman.


Mun samu tarba Ta mutunci daga iyayenta,babu aibu sam a tattare da su dattawa ne sosai, don shi kansa Umarun a gidansu yake zaune kuma yana d’an aiki a kamfanin mahaifinsu mutumin kirki shima daga Nigeria yaje karatu sai ya had’u da uwarta mutuniyar Jordan d’in ta nuna bu’katar aurensa shikkenan zamansa ya koma can don haka da yaga Umar bahaushe ne ya ja shi a jikinsa,
ya shiga farin ciki, ko da yarinyarsa ta nuna tana sonsa take ya amince ya bashi aurenta.

Hankalina ya kwanta da naga ubanta bahaushe ne, kuma har kwatancen gidan su yayi mana a garin Niger (Minna) cikin unguwar limawa nan ce mahaifar Kakanku na wajen uwa, ta daina muku fankamar wai asalinta balarabiya ce, asalin uwarta dai.Kakanku ya ce zai bincika ya gani, ai Niger ba bak’on waje bane a wajensa.

Ba mu dawo ba sai da aka d’aura auren, amma jikina ya yi sanyi da na lura da uwar Sakina ce take kula da al’amuran gidan shi uban nasu ba shi da ta cewa sai abinda Ta d’aurashi a kai, kuma yarinyar da naji suna kira Sakna ni ce nan na mayar mata da sunanta Sakina har yanzu a garinsu Sakna ake kiranta, kaf halayen uwarta ne a tare da ita bata ganin mutane da gashi. Gaisuwa kanta sai taga dama take min gashi iyayen suna ji da ita tamkar masifa ko don itace babba.

Satinmu biyu muka baro garin daga nan umara muka wuce, na kuwa dad’e a d’akin Allah ina kaiwa Rabbil Izzati kukana akan aurennan na ubanki don sam zuciyata ba wai ta gama yarda da auren d’ari bisa d’ari bane, na yarda ne dai don Malam yafi ‘karfina.


Dawowarmu Nigeria muka dinga zuba idon ganinsu sai dai kamar mun shuka dusa ba amo ba labarinsu.

Hankalina ya tashi matuk’a da gaske ga gari ba kusa ba kuma lokacin wayar hannu bata zo ba iyakaci ta landline ce shima ba waje mai nisa ake kira ba.


Ganin tashin hankalin nawa ya yawaita hakan yasa Malam ya shiga addu’a da a lokacin ake kiranta addu’ar kiranye. A lokacin har aka yi bikin k’anwarsa amma bai dawo ba. Na haifi autata lauratu shima bai dawo ba.



Kwatsam wata rana muna zaune da hantsi sai ga sallamarsu ina d’aga Kai suna shigowa da hakimar uwarku tana wani cin magani tana yatsina kamar ta shigo gidan da ake tsubire himulin kashi, ba mu bi ta kanta ba muka shiga murnar ganin Umaru da duk yayi ‘kiba ya zame min babban mutum kuma duk da a lokacin ko shekaru talatin bai rufa ba. Na shige rumfa ina musu lale marhabin ku shigo mana. D’aki na tsaf yake duk da dai ba kujeru amma malale yake da sabuwar leda sabuwa dal don mun fara shirin azimi daga gefe kuwa fanka ce Ta tsaye sai dadduma da tum-tum irin na gidan sarauta.


kuma bana mantawa a lokacin k’amshin turaren tsinke yake da na kukkunna a duk wata kusurwa da take d’akin, ya kuma sha Fenti da farar k’asa kamar yarda malam yake k’o’kari duk shekara a watan sallahr tsofi yake shafe gidan da farar k’asa.

Duk da wannan abin amma Sakina yamutsa fuska kawai take, ta d’ofana d’uwawunta akan tum-tum d’in da yake gefe sai sannan Umar ya kalleta ya ce “Ki gaisheta mana.” Fuskarta kamar ta zunduma ihu cikin gwarin hausarta da ko fita bata yi a lokacin ta ce “Ina kwana?” Ina murmushi na ce mata “Lafiya k’alau Sakina.” Ji nayi tana masa magana da turanci ban dai fahimci abinda tace masa ba amma tabbas naji ta ce Sakna da Sakina a cikin zancen nata. Sai naga yayi murmushi ya ce “Didi sunanta ba Sakina ba Sakna sunanta.”

Na kuwa daddage na jefe shi da umbola na ce nak’i nace Saknan ka gaya mata ba zance ba Sakina zance Au nan k’arata Ta kawo don rashin Ta ido? gaisuwar ma ina ce sai da kace ta gaisheni, kai Umaru!ni dai ka tak’aitan da ba ka auro mai jin hausa ba balle ta fahimci masifar da nake mata ja’ira fuska kamar jan k’osai.” Kallona kawai take tana ta’be baki ni kuwa na mik’e ina kallon Ummaru da yake ta guntse dariyarsa nace “Sai ka kawo mana bak’uwa ba sanarwa yanzu mai kakeso mu bata? Ga d’akin naku ma ba a gyare yake ba.” Na k’walawa Ali kira yana zuwa nace “Gadanga sai ka tattara kayanka ka dawo d’akin nan na tsakargida sai a gyara musu can d’in tunda d’aki ne da rumfa har da makewayi a ciki.” Ali cikin farin ciki ya shiga aiki ma’kota kuwa tuni aka fara shigowa ganin Amaryar Ummaru ana mamakin yarda ya auro balarabiya sai da nayi musu jan ido sannan suka fice na saka sakata a Zauren gidan ina sake tsinewa k’auyanci banda haka meye na dandazon zuwa ganinta abinda gobe zan saka ta zaga gida-gida su gaisa dasu.


Abincin da muka yi na rana shinkafa da miya da salak na juye musu kaf na bawa gadanga ya siyo kifi sukunbiya na saka musu, har da dafaffen k’wai wai duk don na karramata. Na zuba musu zo’bo mai sanyi har da fura da yake ina siyarwa k’aton firiza ne dani a tsakrgida, nake sararwa da mutane zo’bo da fura mai sanyi kuma cinikin ya kar’beni sosai.

Reras na jere musu langunan abincin har da cokula na sababbi gal dasu.

Umaru yayi saurin jan tray d’in abincin ya fara k’o’karin zuba musu, gani nayi tayi wuf Ta ri’ke hannunsa tana girgiza masa kai sai kuma naji tana ambaton hotel da nuna masa lokaci ta hanyar kallon agogo. Sai naga ya mayar da abincin ya rufe yana sakar min murmushi ya ce “Didi ai wucewa ma masauki za muyi mun riga mun kama d’aki a hotel.” Ban san sanda bakina ya zunduma masa zagi ba nace “Ba Otel ba Otalo kai har kayi kud’in da ba zaka iya ajiye iyalinka anan ba? to wallahi baka isa ba nan d’in da take ‘kyama anan zata zauna ba gidan uwar da zata je, ina kallo da ma tun d’azu kallon rainin da take wa gidannan to ka gaya mata nan kwana nan yini don uwarta ba inda zata je ga d’aki can na saka gadanga yana gyara muku, kuma ko dawowa kayi gaba d’aya ga ‘bangarenka can malam yasa ana gina maka anan d’in zaka zauna. Ni za’a kawowa fi’ili da zancen banza.” Ina kallo tana tambayar me nake cewa naji ya ja ajiyar zuciya yana mayar mata da harshen da tafi wayo a kansa kawai sai naga yarinya ta saka kuka ta mi’ke tana d’aukar jakarta tayi hanyar waje da sauri Umaru ya bita dai-dai lokacin da malam yayi sallama ya shigo.. kamar zata bangaje Malam, Umar d’in yayi sauri ya rik’ota ai kuwa munyi kallo don fad’awa jikinsa tayi tana kuka sosai kamar yarinya cikin kukan babu abinda nake ji sai furucin Back da kuma Jordan sai kuwa wata kalma da take yawan maimaita Ta wai now now. Malam ya saka salati tare da furta “Umaru saukar yaushe naji kuma amaryar taka tana ita Jordan zata koma? Ku muje ciki naji me yake faruwa a tsanake.” Umaru ya ja hannunta ko kunyarmu bai ji ba ya saka ta a gefen hammatarsa yana goge mata k’wallar idonta. Sosai takaici ya kumeni nama kasa magana zuwa lokacin da suka shigo Malam ya sake tambayata na bashi labarin kaf abinda ya faru. Take shima na ga fuskarsa ta sauya da yanayin ‘bacin rai amma da yake namiji ne sai bai nuna ba kalmar Ashsha kawai yake fad’i sai kuma ya girgiza kansa ya kalli Umaru ya ce “Kai kuma don sakarci sai ka biyewa matarka ka ‘batawa uwarka rai? Meye da gidannan d’in da ba zaku sauka ba? ka gwammace Ku kama Hotel ina ce kaima a gidan ka rayu?” Kasa cewa komai yayi ganin ran mu ya ‘baci ina kallo yana ta fama da hakimar tasa kan ta ha’kura amma taja ta turje akan sai ta tafi abincin da na kawo musu ma ko ci ba suyi ba. Bama ta kalleshi ba ran Malam a ‘bace ya ce masa su wuce su tafi sa dinga lek’omu kafin su tafi. Abin mamaki Umaru kuwa ko ja da lamarin baiyi ba yaja matarsa suka wuce ba abinda ya dameshi balle ya gane Malam gatse yayi masa.


Bayan fitarsu Mun dad’e muna ta’ajibin abin, mamaki kuwa kamar ya kashe mu haka yasa Malam yanke shawarar aura masa yarinyar mak’ocinmu Sadiya, Yarinyar da kowa ya shaida da nagartar halayenta ga son ibada kamar me. Ubanta Aminin Malam ne. Murna na shiga yi da shawarar Malam na karb’eta d'ari bisa d’ari muka kuma ce ba za mu sanar dashi ba sai dai yaji an aura masa aure da ita dole kuma ya amsheta matsayin mata.


Malam bai bari sai kashegari ba a daren ranar yaje wa da Talle amininsa zancen, Talle yayi farin ciki sosai don babu wanda zai k’i had’a zuri’a da Malam sai marar rabo, take suka saka lokacin aure Sati biyu masu zuwa. Malam ya cigaba da ginin da yakewa Umaru a gefe guda a gidanmu. D’aki biyu ne da babbar rumfa sai makewayi ‘d’aya da yake dangar rumfar daga can gefe.


Kashegari Umaru shi kad’ai ya zo don hakimar ta ce ba zata
Biyoshi ba, ban ko tambayeshi ba shi yake rattabo min bayani, na ta’be baki na ce ta sha zamanta ai ni ba na nemanta, don na gane k’yank’yamun mu take kuma tayi Ta banza don kwanannan zata gane kurenta.”


Bai wani da’de sosai ba ya tafi.



Da ku’dina da na Malam har da na gadanga da Y’ar uwarsu da tayi aure muka ha’da aka yi lefen kishiyar Uwarki Sadiya.


Da yazo yaga ana had’a lefen bai kawo komai a ransa ba ranar ma bai dad’e ba kuma nan ma bata biyoshi ba sai wasu dogayen riguna na k’asar da Ta aiko min dasu da na k’annensa ni kuwa duk na tattara na zuba a lefen Sadiya....



To fa!
Ko me Ummaru zai ce idan ya
Samu labarin aurensa da Sadiya? Shi da yake da tsaleliyar Balarabiya
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE


YA ABIN YAKE ?

LIttafin Nazeefah Nashe.

08033748387




Follow me on wattpad

Nazeefah381



ELEGANT ONLINE WRITERS

(Haɗin kai shine takenmu.)






Ya Abin Yake? Daban yake da sauran.


✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽

6


Duk tunaninsa lefen Gadanga ake haɗawa, shi yasa bai damu ya tambayeni ba.



Sai ana gobe ɗaurin aure kamar an jefo su sai ga su sun zo da yamma. Fuskata babu wani alamun damuwa na tareta da murnata da komai, na malala mata tabarma a rumfa, ta kuwa zauna ranar kamar abin arziki har tana gaisheni cikin gwarancin hausarta. Lauratu da ta dawo daga islamiyya ganin ta yasa ta faɗawa jikinta a guje sai naga ta tureta a fusace tana kaɗe jikinta, mamaki ya hanani cewa komai sai janye Lauratu da ta fara kuka nayi. Lokacin bata wuce shekara goma ba, cikin lallashi nace mata yi haƙuri daɗin abin burinmu daf yake da cika.”

Sai naga ya kalleni da alamar neman ƙarin bayani, ni kuwa na galla masa harara. Muna zaune Malam ya dawo fuskarsa fal ɗauke da murmushi da katinan aure a hannunsa. Shi kansa Malam ɗin ba fara'a ba girmamawa ta shiga gaisheshi, shi kuwa ya amsa ba tare da komai a ransa ba. Ya miƙe ya shige turakarsa yana faɗin “Idan ka tashi tafiya ka sameni.”

Ƙasa yayi da kansa kafin ya ce "Malam ai tafiya zamuyi jirgin dare yau zamu bi." Daga ni har Malam ba wanda bai firgita da jin zancen ba muka ji tamkar saukar aradu a ka. Ni dai har razana nayi.

Malam ya dawo da baya yana masa kallon tuhuma kafin ya ce “Da kazo mai kace min? Ca nake cewa kayi wata guda zaku yi?” Ya ɗaga kai kawai, idanunsa sun nuna yana cikin wani yanayi na ƙaƙa ni kayi. Malam ransa a ɓace ya ce "To menene dalilin canjin zancen?” Daburcewa yayi sosai kafin ya ce “Kawai dai zafin garin ta ce ya isheta.” “Shine kai kuma kabi abinda tace wajen ruguza shirinka kuka ɗaura aniyar tafiya yau?"

Na faɗa raina a ɓace da tunanin sun canja min ainahin Ummaruna wannan ba nawa bane wani ne can daban. Zufa ya goge kafin ya ce “Duk ba haka bane,jarrabawa zata je ta zana.” Malam Yaja ajiyar numfashi a kufule ya ce “Jarrabawo ba jarrabawa ba, ta bakin uwarka ne duk an canja maka halaye, to albishirinka ungo nan.”
Ya faɗa yana manna masa katin auren a tafin hannun da ya miƙo "Ɗaurin aurenka gobe da Sadiya, sai ka sanar mata idan taga zata tafi sai tayi gaba ita kaɗai." Sam bamu san zufa bace take karyo masa, sai da na kai idona kansa sannan na ankare. Na kuwa saka salati ganin yarda ya durƙushe a gaban Malam yana faɗin "Kayi min rai wallahi ba zan iya haɗa Sakna da kowacce mace ba."

A zafafe Malam ya ce idan an ɗaura ka saketa, amma ka tabbatar in dai ni na haifeka to babu shakka aure ya ɗauru." Yasa kai ya fice Lauratu da take gefe sai dariya take zuciyarta fal farin ciki, duk da umbolar da nake mata bata fasa ba. A zuciye Ummaru ya jawota zai fara jibga. Na kuwa saka
Hannu na janyeta ina cewa kada ma ka fara, don wallahi ba zan ɗauka ba. Ina kallo tana tambayarsa daga yanayin fuskarta na gane tambayarsa take masifar mai muke? Sai naga ya saki murmushin dole ya girgiza mata Kai.


A daddafe ta bari suka cika awa guda cur, naga ta miƙe hannunta ɗauke da Jakarta ta kalleni a banzace naji ta ce "Good bayi." tana ɗaga min hannu shima ya mara mata baya bayan ya ajiye min wata leda yasa kai ya fice da sauri.

Shikkenan daga ranar bamu sake ganinsa ba, amma haka Malam yasa aka d’aura auren kuma Sadiya ta tare a shiyyarsu da aka gina mata ita da Umarun da
Ya wuce ya koma Ƙasarsu ko salaam babu.


Bai kuma dawo k’asar ba sai bayan shekara Guda, Ba ni kad’ai ba wannan karan hatta Malam sai da ya nuna masa ‘bacin ransa.

Don muna zaune a tsakargida wannan karan ma muka ji sallamarsu. Nayi turus ina kallonsu, Allah yaso ranar juma’a ce dama Sadiya ta saba duk sati a juma’ar take kitso idan kuma k’unshinta ya goge ta sake mayar da wani. Ranar ma haka ta kasance tsaf da ita tayi adonta cikin atamfa Diamond ta kada d’auri had’e da zubo himulin gashinta da ko balarabiyar ba zata nuna mata komai ba a gashi ko dirin jiki sai dai ta nuna mata hasken fata da santsin Gashi. Sadiya na da sirrin kyau da baya bayyana sai idan ta haske idanunka da murmushi anan zaka hangi zallar madarar kyau,
Sai dai bak’ace kamar yarda kika sani kuma bak’innata sam bai dameta ba balle tayi shafe-shafe kullum cewa take haka Allah yaso ya ganni.

Tayi karatu sosai duk da karatun nata yafi k’arfi ana addini na bokon kam ka’dan ta samu a k’aramar sakandire ta tsaya.

Murmushin dai ta haske shi da shi da ya sakashi ya tsaya cak yana kallonta da alama addu’ar da muka duk’ufa yi ni da sadiya taci don kullum addu’armu Allah yasa ha’duwar farko ubangiji ya jefa k’auna mai girman dutsen dala a
Zuciyarsa, ba ta kowa ba sai ta Sadiya baiwar Allah da Sam
Duniya da abinda yake cikinta ba su dameta ba.


Da fara’a ta na mik’e ina aukin fa’dar Ta’al Ta’al Ta’al! Wata irin dariya naji Sakina ta shek’e da ita har da dafa ciki. Raina a b’ace nake kallonta ganin kamar ta mayar dani mahaukaciya, Lauratu tayi kanta a zafafe tana fad’in Uwarki kike wa dariya?” “Uwar ki wannan nake wa.” Ta fad’a cikin gwarin hausarta ina kallon Ummaru ya dafe kai cikin takaici ya “Zagi fa kika yi!” Sai naga ta bud’e hannu tana girgiza kai, shi ma kansa a k’asa ya ce “Didi ba zaginki tayi ba, ba mamaki jin kina yarensu ne abin ya burgeta kika ga tana dariya.” Na girgiza kai ina faɗin Yo ko da naji. Ku zauna” Sai naga wannan karan ta saki jikinta ta zauna har da d’an murmushinta tana kallon Laurat da ko kallonta ba tayi ba da alama bata manta abinda tayi mata wancan zuwan da ta zo ba. Hannu ta miƙawa Lauratu amma Laurat tayi shigewarta d’aki bata fito ba. Shi kuwa Gogan idanunsa akan Sadiya, sai da na gaji da kallon da yake jifanta da shi baka ganeta bane? Sai naga matarsa tayi saurin kallon Sadiya da alama wannan karan ta fara
Jin yaren Hausa don haka don kar nayi ɓaranɓarama nace masa ta fata jin yaran Hausa ne? Ya girgiza kai ya ce "Ta fara ji Didi kawai dai ba sosai ta iya mayarwa ba" nace "Hakan yayi kyau, kada kace mịn baka gane Sadiya ba?” Girgiza kai yayi “Wallahi Inna ban Wanye da ita ba.” raina a bace nace Ai kuwa naga alama to tashi muje waje zan yi magana da Kai.” Ya kuwa bini muka shiga madafa. Idanuna cikin nashi na rik’e kunne nace “Ka jini da kyau Sadiya ‘yar gidan Baba mak’oci CE, ba zaka santa ba tunda ba anan tayi wayo ba daga yaye yar uwarta ta tafi da ita can Zariya sai da ta girma baka ma k’asar aka dawo da ita, itace matar da muka aura maka kashegarin ranar da ka gujemu.” Ji nayi kawai yana jan Innalillahi kamar na watsa masa wuta a jiki. Cikin wata iriyar murya ya ce “Yanzu Didi sai da aka yi aurennan?” Tab’e baki nayi ina kallonsa nace “Aure kam an yi shi yau shekarata uku kenan da aurenta akan ka, baka kuma isa ka saketa ba wallahi ka saketa sai na d’aga maka Nono, ko Bayan raina ban amince ka saki Sadiya ba. Ga can shiyyarku an gama d’aki biyu ne da parlour sai bayan gida a rumfa ta d’au d’aki ciki d’aya Sadiya dama an Zuba mata kayan a d’ayan ita kuma ta d’au d’ayan kuyi maleji kafin ku tattara ku koma.” Hawaye sosai ya zubo masa takaici yasa na fice daga madafar Na shige Rumfa.


Idanuna a kanta tana ta faman yatsina tana kurb’ar zob’on da na kawo musu, nace “Kinyi ta banza ke Sadiya zo kije ga shi can ki kai musu abincin su k’arata a can yasan yarda zaiyi ya sanar da ita ke a matsayin kishiyarta, na san dai yau akwai dambarwar tsiya, da kinji taga-taga ki gudo suje can su k’arata ai tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka. Sadiya murmushi tayi tana yafa mayafinta idanunta akan matar tana fatan bata ji abinda na fad’a ba. Tsaki nayi nace “Duk iya hausarta ai bata isa ta kamo nan a Hausaba.”



*********************************

Kai ranar mun ga abinda ake kira tashin hankali, ashe hausawa duk haukan da suke idan an musu kishiya na su Lami ne akan na Balarabiya Sakina, k’iri-k’iri ta fito daga ita sai d’an tofi da vest tana cilli da duk abinda ta samu a tsakar gidan tana sai ta tafi, idan kuma ya k’i barinta ta tafi sai ta kasheshi ta kashe Sadiya sannan ta kashe kanta. Duk ta jijjiwa kanta ciwo da kyar ya turata a d’aki ya gark’ame da d’an mukulli yana sakin ajiyar zuciya, murya a raunane ya ce “Didi kinga abinda na gaya miki ko? Su k’asar su wallahi basu san kishiya ba, kuma duk abinda ta fad’a zata iya aikata shi ba burga bace irin ta Malama Bahaushiya, don Allah a raba aurennan.” Na ce “Wallahi ba za’a raba ba sai dai ita ka saketa ta tattara ta koma k’asarsu don ni yanzu ba zan ma amince ka bita ba, balle su kashe min kai a can.”


Da kyar da sid’in goshi Malam ya rarrasheta, yayi da guntun larabcin sa ya haɗa da guntun turancinsa sai ga shi tayi luf wallahi ta yarda ta amince zata zauna zuwa lokacin da zasu tafi. Tunda ta tabbata idan sun tafi da kyar zata barshi ya dawo nan kusa.


Ni kuwa gefe guda, na dinga tsuma Sadiya da kayan magunguna kala-kala da na tanada saboda irin wannan ranar, har gyaran jiki nake mata a b’oye. Sai gashi kafin suyi shirin komawa Sadiya ta fara kwarara amai a bakin rariya da alama dai ta k’unso. Itama Sakina sai gashi ta fara nata laulayin. Hakan yasa ta uzzira masa sai sun koma can inda suka fi wayo.


Ya lallab’a Malam aka siyar da wata Babbar gonar Malam d’in, ya bashi kud’in da niyyar zai je can ya kafa bisiness d’insa. Wannan kud’in shine silar arzikinsa.


Basu tafi da Sadiya ba amma yayi mata alk’awarin ba zai kai shekara ba zai dawo da zarar ta haihu. Don kam ya karb’i Sadiya hannu bibbiyu ya tabbatar da zancen da nake gaya masa na kasancewarta yarinya mai hak’uri mai kuma ibada.


Duk wani abin buk’ata na haihuwa sai da ya dire mata shi. Tun farkon cikin matarsa ta k’wallafawa ranta haihuwar namiji don kullum sai ta fad’a idan muna hira cikin gwarancin Hausarta zata ce “Insha Allah Sadiya na mata zata haifa ni kuma na maza.” Dariya muke mata Sadiya ta ce Allah dai ya kawo mai albarka.



Ita ta fara haihuwa ta haifi Mace, suna yin arba’in da kwana biyu suka zo Nigeria Sadiya ta dinga murna da ganin y’ar nan ita da Lauratu, yarinya jajir kamar Balarabiya Ta d’auko uwarta Sak.


Zuwansu da kwana goma Sadiya ta zankad’o namiji sak mahaifinsa tun a ranar Sakina ta fara bak’in ciki kuma ta kasa dannewa har sai da ya fito fili. D’an shirin da aka fara yi da ita duk ta watsar, ta janye

Please Login or Register in order to submit comment