Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY


1


Writting by Maryam S Indabawa
MANS



Bismillahir Rahmanir Rahim
Da sunan Allah mai girma da Rahma.


Na fara da sunan Allah mai Rahma mai jinkai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin Muhammad (SAW).


Allahumma salli ala Sayyidina Muhammadil al fatihi lima uglika wal khayimi lima sabaka nasiril hakki bil hakki wal hadi ila siradikal mustakim wa'ala alihi hakka qadrihi wal mikdarihil azim.













Wannan littafin naki ne yar uwa, rabin rai, NUSAIBA SULEIMAN INDAVAWA, Allah kara mana kaunar junan mu, Allah daurar da zumuncin mu AMEEN,

Allah baki miji nagari, Allah inganta rayuwar ke da little MEEN, HAUWA'U USMAN (YASMEEN) Ina kaunar ku ina alfahari da ku kannena,

Allah ya faranta muku a duk inda kuke Allah baku zuri'a ta gari AMEEN! Da dukkanin musulman duniya baki daya.










zaune suke shi da abokan sa a babban tsakar gidan, akan carpet suna cin abinci, mikewa yayai ya shiga cikin dakin sa, adai dai lokacin wata kyakyawar budurwa wace bazata wuce shekara 15 ta shigo gidan da sallamar ta gannin da Mutane a tsakar gidan yasa ta cire takalman ta, ta ajiye a soro dan girmamawa.

Karaso war ta ciki kenan shi kuma ya fito daga daki, da gannin ta ya rufe ta da fada.

"Ke baza ki girma ba har yanzu ji yawo ba takalmi,"

Ya fada yana nuna kafar ta, durkusawa tayi tace.

"Yana soro fa takalmin ganin da Mutane yasa na ajiye a can,"

"Karya kike ni wuce ki bani waje."


Daki ta shige inda Yayar ta take, tana matsar kwalla dan tana jin zafin yadda yake mu'amala dasu, amman in 'yar sa ce 'yar shekara 4 yai ta mata dariya amman su sam basa gannin fara'ar sa ko meyasa ohoo?


Antyn ta dake zaune kan kujera tana ta danne dannen wayar ta dan aikin ta kenan kullun.

Tana zaune tana fama da wannan abun, Mahaifiyar su wacce suke kira da UMMU ta kwada mata kira,

"KHADIJA!"

"Na'am,"

Ta amsa da sauri ta fice, ta durkusa tace

"Gani UMMU"

"Ungo maza je ki siyo Ruwa."

Karba tayi ta mike tayi waje dan daman da hijab din ta ajikin ta,

Aiken ta kai wa UMMU, sannan ta fada mata za taje gidan UMMA dan za suyi gwajin rawar gada, da za ayi bikin yar kannin mahiafin su,

Suna cikin yin Gwajin taji yo ana kwada mata Kira.

"KHADIJA! KHADIJA!"

"Na'am"


Ta amsa da karfi, dan katanga daya ce ana iya jiyo wa in an kirata,
Gida tayo tana addu'ar Allah yasa ba kuma wani abu tayi ba.

Ta shigo gidan da Sallama, tin a soro ta fara jiyo mitar sa,

"Ke dama ke kike kara daure mata gindi, ta fita taje tana ta rawa ai da Mahaifin su na da rai da bazai bar ta ba,"

"Haba dan Allah ai bikin yar Kannin. ABBUN su akeyi,"

"Kina ina ke zonan ki shige ciki."


Daki ta wuce inda ta samu Antyn ta na aikin da ta saba, wato danne dannen wayar ta. kallan ta KHADIJA tayi taga duk ranta a bace yake, dan Anty in Akwai abin da ta tsana bai wuce fada ba ki hayaniya.

Mikewa tayi ta shige dakin baccin su tayo Alwala tace,

"KHADIJA sallah"

Da sauri ta mike itama tayo alwalar, tare sukai Sallah Magariba.

Bayam sun idar da Sallah ne, sai ga Yaya Maimuna ta shigo yar gidan Umma ce.

"Ina UMMU"


Ta tambaya, KHADIJA ce ta mike taje ta kira ta.
"UMMU ina yini,"

"Lpy Maimuna,"

"UMMU daman KHADIJA ce zamu raka Maman Hidaya gida,"


"To shkn kar kudade,"

Suka fice KHADIJA na matsar qwalla dan har yanzu tana takaicin abinda ya faru.

HAFSAT wato Anty tana daki kwance kan gadon ta, tana ta danne dannen ta,

tin da suka fita basu dawo ba sai 10 dare, Yaya Maimuna ita ta rako ta har gida, KHADIJA ce tasaka sakata tayo ciki.

UMMU tace "sai yanxu kika dawo ko, bakya jin magana ko?"

Murya sa suka jiyo yana fadin

"ai gashi nan, yarinya bata jin magana....,"

KHADIJA dai daki tayo ta barshi yana ta mitar sa.

A daki ta iske Antyn ta HAFSA tana rike da wayar ta a hannu, fuskar nan ba walwala, ba tai dai magana ba amman ta tsani wannan mitar da yake wa Mahaifiyar su.

Abin ci suka ci sannan suka zauna kallo, daga baya kuma suka mike suka kwanta....





MUJE ZUWA



MS INDABAWA

08062882472
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY

2




Writting by Maryam S Indabawa
MANS



Wannan shafin naki Sis Rashidat Abdullahi Kardam (Rash Kardam).

Anty Rash ina alfahari dake, Allah ya kara miki daukaka, Allah yasa ki gama lpy, Allah ya shige akan duk al'amuran ki. Allah yasaki a gidan Aljannah.
AMEEN







Tin asuba HAFSAT ta tashi, sannan ta tashi kanwar ta KHADIJA, alwala suka yo sannan, sukai sallah.


UMMU ce ta shigo dan gannin sun tashi duk da dai tasan sun tashin, gaishe ta sukai ta fice.

HAFSAT falo tayi ta kunna karatun Al-qurani, ta mike ta shige dakin baccin su sannan ta gyara gadon ta ta share dakin,
Ban daki ta shiga ta wanke shi tas, sannan falon su ta share tayi mopping, duk da suna da ma aikata amman ita bata son ana gyara.mata dakin su.

Kitchen ta wuce taje ta daura ruwan tea sannan ta daura farfeson naman kai, dan tasan UMMUN su na son sa, firar dankali ta fara, ta gama ta soya ta gyare kitchen din, can bangaren ma aikatan gidan tayi, dan ganin me suke yi.

Baba Lami ta tarar tana soya musu doya da kwai, durkusawa tayi ta gaidata, Baba lami ta amsa cikin fara'a dan tana son HAFSAT duk da bata sakin fuska amman tana da girmama na gaba da ita.

Juya wa tayi ta shige cikin gida, ban daki ta shiga tayo wanka, ta fito mai ta shafa kawai sai powder sai man leba amman tayi kyau sosai, sabida ita din kyakyawa ce, doguwar riga ta dauko ta saka ta fito falon su bakin shayi kadai ta sha,

Sannan ta dau wayar ta ta kira UMMU, UMMU ce ta dauka, tace.

"UMMU zanje Makaranta,"

"To da kudi a hannun ki,"

"Eh,"

Kawai tace

"To a dawo lpy"

Wayar ta kashe, sannan ta fice, State Liberty ta nufa, ID Card ta nuna sannan ta shige, tin 11 taje wajen bata fito ba sai karfe 2 shima dan zatayi Sallah ne.

Sai da ta fito ta dauko wayar ta missed call ta gani guda 22, guda 2 na kanwar ta KHADIJA ne, guda 10 na HAUWA ne sai sauran 10 na FAIZA ne, tsaki tayi dan tasan yau sun zuba ido su ganta amman bata je ba, ita abinda yasa ta fito gaba daya ma dan MIJIN UMMUN tane, dan in yana gida ya fiya hayaniya, ita kuma ba abinda ta tsana kamar hayaniya.

Yau bata yi niyyar zuwa ko ina ba amman sbd da shi ta fito yin karatu kawai.

Sallah tayi sannan ta kira KHADIJA,

"Sis kina ina ne, su Hauwa sun kira wai baki je makaranta ba,"

"Eh naje karatu ne,"

"Ok adawo lpy, a tahon da ice cream nima,"

"Toh"

Kadai tace ta kashe wayar. HAUWA ta kira, HAUWA tace "Sisi ina kika shiga ne yau, duk ba dadi baki shigo makaranta ba, kin tafi ma buyar ta ki ne,"

"Eh," kadai tace, Hauwa tace,

"Dan Allah fada mana ma buyar nan,"

"Naki!, in anyi Sallah la'asar zan shiga shoprite mu hadu acan."

"Ok tace sai mun hadun,"

"Ina FAIZA,"

"Ta shiga Sallah ne,"

"Ok."
Ta katse kiran, Sai baya minti 10 ta daga waya ta kira FAIXA. FAIZA tace "Sisi yau buyar manan ce ta zo kenan, wa ya bata wa miki rai ya shafa mana har mu aka gudar mana."

"FAIZA kin fiya sa ido, ki tambayi HAUWA nace anjima mu hadu,"

Ta kashe wayar. A ranta tana cewa lallai su FAIZA sun karance ta dan kuwa ran nata ne a bace,

dayake in dai an bata wa HAFSAT rai to ranar bata son haduwa da kowa dan kar ta huce akan sa, to gudun hakan yake sata buyar wa kowa, yanzu haka mitar ABBI ce wato MIJIN UMMUN SU, shi ya bata mata rai sosai, dan a duniya tafi tsanar sa akan kowa.

Dakin karatun ta koma ba ita ta fito ba sai la'asar, Sallah tayi sannan ta zauna cikin garden din, sai 5 ta mike tayo waje.

In dai ABBI MIJIN UMMUN SU na nan bata son zaman gidan dan bata son ranta ya baci, kuma bata son ta batawa UMMUN su rai dan in ranta ya baci zata iya batawa kowa rai.

Napep ta tsara tace shoprite, ta shige sai da ta kusa sannan ta kira HAUWA tace,

"kina ina ne,"

"Gamu nan pls ki tsaya a bakin gate mu dauke ki,"

"Ok,"

Lokacin da taje har sun je ma, mai Napepe ta mikawa 1k tayi gaba, yace canjin fa Hjy, hannu ta daga masa kawai tai gaba, shi kam sai godiya yake mata.

HAUWA ce ta fito da sauri ta rumgume ta tace,
"Munyi kewar ki sisi,"

"Nima haka,"

Jan ta tayi suka shige cikin motar a wajen parking space suka tsaya su fito, tace,
"ya makarantar ne yau,"

FAIZA ce tace
"Ba dadi yau sisi bata nan,"

"Ke dai fadi gaskiya,"

"Allah sisi fada mata"
ta fada tana me son HAUWA ta kara mata bayani,

HAUWA tace "gaskiya ne,"

"Na ji, ni muje yunwa nake ji,"

FAIZA ce ta karbo musu abinci,

HAFSAT tace
"ni bazan ci bafa,"

A tare suka hada baki suka ce
"Saboda me sisi"

"Lemo kawai zan sha,"

"Haba dan Allah, kar fa Ulcer ta kama ki, ke bakya son cin Abinci, bayan kuma yunwa kike ji" Cewar FAIZA


HAUWA ce ta kamo hannun ta tace
"dan Allah sisi kici, keda kike jin yunwa,"

Kai kadai ta gyada musu ta dan tsakura ta barshi, sai lemo da take sha, tana zaune jiran su.

Sai da suka gama suka fice, suka je dan siyawa musu Ice cream, ta siyawa su HAUWA da FAIZA sai nasu da ta siyo musu da chocolates ta KHAIRAT.

FAIZA suka sauke a nan Zoo Road bayan gidan Buhari, sannan muka wuce nida HAUWA a bakin gate suka dire ni sannan suka wuce tana dagan hannu.....




MUJE ZUWA


MS INDABAWA
08062882472


08062882472
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY
3



Writting by Maryam S Indabawa
MANS



Wannan shafin naki ne yar uwata, Kawata HAUWA KAMILU ZIMIT, Allah ya biya miki dukkan bukatun ki na Alheri Ameen
Ina kaunar ki, ina alfahari dake a matsayin ki na kawata.







Da sallama ta shiga gidan, Baba Lami tasama a harabar gidan, tana gannin ta ta washe baki, tace
" 'Yar nan kin dawo,"

"Eh," tace sannan ta dan kursa ta gaidata tana tambayar ta ya gidan, "lpy, ya Makarantar" ta tambaye ta, "Alhamdulillah," ta amsa ta shige gidan.

A tsakar gida ta sami, UMMUN su karasawa tayi da sauri gun ta, ta duga tace "UMMU barka da gida,"
"Yauwah HAFSAT, ya Karatun dan nasan yau karatu kika je, dan su HAUWA sun kira wai baki daga ba."

"Eh wallahi," tace tana mike wa, muryar ta da KHAIRAT ta ji yasa ta fito a guje tana "Yoyo Taty,"

"Oyoyo baby nah, ya gidan,"

Dariya KHAIRAT keyi tace "lpy,"

Dire ta tayi, sannan ta mika mata leda, karba tayi tana lekawa, robar ice cream ta ganni sai chocolates dayawa, tsalle tayi tace "Nagode Taty,"

Murmushi na sakar mata na shige dakin mu, ita kuma da gudu tayi wajen UMMU tana nuna mata, Murmushi UMMU tayi tace "Iyye yar gidan Antyn ta,"

Daki tayi da gudu dan nunawa ABBIN ta.

HAFSAT na shiga daki, firiji ta nufa ta saka kayan dake hannun ta sannan ta shige dakin baccin su, toilet ta fada ta sakarwa kanta ruwa, ta cuda jikin ta sosai, Alwala ta dauro, sannan ta fito ta saka duguwar riga mara nauyi mai shimi, turare Aseel ta fesa sannan tayo falo rike da hijab, zaman ta kenan HAUWA ta kira ta, daga wa tayi da sallama, Hauwa tace "kin shiga gida lpy, yasu UMMU da KHADY da KHAIRAT,"

"Duk lpy, yasu Ummi,"

"Suna lpy, sai anjima toh,"

"Aha,"

Tana kashewa sai ga kiran FAIZA, Murmushi tayi ta daga, da karadi ta yi sallama, HAFSAT ta amsa cikin nutsuwa,
FAIZA tace "Sisi ya kuka je gida,"

"Lpy, kefa,"

"Nima lpy, yasu UMMU,"

"Kowa lpy,"

"To shkn sai anjima ki gaida min KHADY da KHAIRAT,"

"To ki gaida min Momy."

Ta kashe wayar tayi, sannan ta lalubo number kanwar tata KHADIJA,

KHADIJA ta dauka da sallama sannan tace "Sis munje gidan Anty Umma ne, kin dawo ne,"

"Eh, kuma kada ku kai dare kisa ai tai mana hayaniya a gida,"

"Kar ki damu yanzu zan dawo,"

kishingida tayi tana me kara jin soyayyar kawayen nata. Wanda suke kula da ita sai kace yar uwar su ta jini, ko yar cikin su.

Tana kwance ta jiyo kiran Sallah Magariba, zaune ta tashi, sannan ta mike tasa hijab din ta dan yin Sallah, sai da ta iddar sannan ta nufi kitchen din su, Madara ta diba a cikin kofi mai yawa, sannan ta fito, a daki ta zauna ta zuba ruwa kadan sannan ta diga zuma a ciki, ta zauna tana sha tana kallo, sai da akayi isha'i sannan ta mike tayo alwala tazo tayi sallah, UMMU ce ta shigo tace, "HAFSAT kinci Abinci ne," "A'ah UMMU na koshi,"

UMMU ta dube ta tace "HAFSAT ban son rashin cin abincin nan naki fa, kinsan kina da Ulcer amman bakya kiyayewa ko?"

"UMMU naci abinci, ki tambayi su HAUWA ma,"
"Shikenan tinda kince kin ci,"

Ta mike ta fice tana cewa "kina dai kula,"

Sai karfe 9 KHADIJA ta dawo a hankali ta shigo dan kar ABBI yaji shigowar ta, rike da system ta sameni ina yin game, gefe na ta zauna tace "washh, na gaji,"
kallon ta HAFSAT tayi ta gefen ido, kawai. KHADIJA tace "Anty ya karatun,"
"Lpy, sarkin yawo."
"Lah Anty gidan Anty Umman,"
"Eh nan din fa,"
"To yi hkri Sis, ina abun nawa,"
"Duba firiji,"
Firij ta nufa ta bude, robar ice cream ta dauka ta nufi Antyn ta ta, tana godiya.

UMMU ce can ta shigo tace "Sai yanzu ko!"
KHADIJA tace "UMMU na jima fa,"
"Allah shirya min ke KHADIJA,"

Daki HAFSAT ta mike ta shige tayi kwanciyar ta,


Muryar ABBI ta jiyo yana "ai in baki wasa ba, sai yaran nan sun saki hawan jini, yara basa ji sai kace me,"

Tsaki nayi na mike na wuce toilet na rufe kofar, sai da na tabbatar ya gama fadan sannan na fito nai kwanciyya tah.


Muje Zuwa...


MS INDABAWA

08062882472
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY

4



Writting by MARYAM S INDABAWA

MANS






Wannan shafin naki ne, Zahra'u Muhammad Mahmud (Surbajo).
Allah kara basira, Allah kare ki daga sharrin mahasaada, Allah ya biya miki bukatun ki, Allah yasa kifi haka Ameen.





Yau ma tin asuba ban koma bacci ba, sai da na gama yi mana abinci sannan na shige nayi wanka, Mai na shafa sai powder da man leba da nasa ka, humra na dauka na murje jiki na da ita, sannan na fesa body spray na emergency, doguwar riga nasa mai A shape ta atamfa kalar yallow da ja, na daura dankwalin,

bangaren su Baba Lami naje, na tarar tana musu koko da kosai, har kasa na durkusa na gaida ta amsa cikin fara'a.

Gefe na koma na zauna, kosan ta mikon tana cewa "gafa mutumin naki,"
Murmushi nayi nace "na gani fa."
Mikon tayi a cikin filet, na amsa ina godiya, nace "kin tafasa ruwan zafi ne,"
"Eh, gashi can a fulas,"
Ta mike da nufin dauko min nace ta barshi, sai da naje na hado na zambada uban sugari sannan na dawo na zauna, sai da na dumama ciki na sannan na ci kosan, guda 4 naci na mika mata nace "na koshi,"
Kallo na tayi tace "haba dai HAFSAT har kin Koshi, ki daure ki karaa,"
dan dole ta kara guda 2.

Na mike na nufi bangaren mu, KHAIRAT na hadu da ita tace "Taty kin tashi,"
"Eh My Baby,"
"Ina kwana," "lpy," na amsa mata. Nayi ciki,

UMMU ce ta shigo dakin mu, na durkusa na gaidata, ta shige cikin daki tana cewa "har yanzu bata tashi ba ko," "Eh," na amsa mata.
Ita ta taso KHADIJA tayi wanka sannan suka yi break dinsu, karfe 12 na kara fesa turare na dan shafa hoda, sannan na dauki jaka ta da mayafi nayo waje, a tsakar gida na sami UMMU nace, "UMMU ni zan shiga dan Agundi sai na dawo,"
"To a dawo lpy,"

Napeep ne ya kai ni har kofar gidan Anty Gwagwo na sauka na shige gidan, a falo na sameta na gaidata sannan muka dan taba hira tana tambaya ta mutan gidan, daga nan gidan Umma nayi acan nayi Sallah azahar sannan na na mike da niyar tafiya, ai kam ta rike ni da surutu, ni kam duk so nake na wuce gida amman ta na ta zuba, da kyar na fito nayi gida, duk kai na na ciwo sbd surutun da Umma ta cikani dashi, a kan layin Anty Bilki nasa me Napep ya sauke ni, kwankwasa nayi tazo ta bude min, na shiga nace "ina yini,"
"Lpy lou, yau kece a gidan namu,"
Murmushi kawai nayi na wuce dakin ta na zauna, wayata na zaro naga Missed call din su Hauwa da Faiza,

Faiza na fara kira muka gaisa, ta dan jani da hira mukai sallama, Number Hauwa na kira ita ma hirar take ja na da ita dai, daga karshe na biye mata dan lbrin Nuran ta take bani.

Bayan mun gama na mike na shige kitchen na bude firij na dauko lemo mai sanyi na zauna ina sha.

Kitchen Anty Bilki ta shiga ta daura mana indomie dan daga makaranta ita ma take, suna hada project din su, a filet ta zubo mana, indomie da kwai tare muka ci, sosai naci ba laifi, muna gama wa na debe kayan naje nai wanke kwani kan, zama nayi muna dan hira, har akai Magariba, anan nayi Sallah sannan na kira Ummu na shaida mata ina gidan Anty Bilki.

Ni na daura mata abincin dare, Muna zaune Yaya Muktar ya dawo, da tsarabar gyada da Masara ya shigo ai kam na dauki masara dan ina son masara dafafiya, hira muke yi har akai isha'i kowa yaje yayi.

Sai karfe 9:30 nace zan tafi, Anty Bilki wai sai na ci abinci, nace na koshi, to wai sai na kwana da kyar dai na samu na taho gida.

Ina shiga gida na ajiye mayafi na sannan na shiga bandaki na watsa ruwa a jiki, kayan bacci nasaka nayo Falo inda Khadija take, tace "Anty munyi kewar ki fa yau," nace "nima haka,"

Hayaniyar tasa na jiyo, nayi tsaki, Khadja tace "kai Ummu na fama, ace mutum bazai yi magana a hankali ba sai da fada nace "abin na damuna,"

Kitchen na nufa, na dauko robar nono na dibo madara a kofi, a falo na zauna na hada nonon da madara na sha shi, sannan na mike akan kujera na jawo system dina, ina sa wani indian film,

Wayata ce tayi kara na dauka Hauwa ce tace "in hau Whatsapp akwai magana,"
Nan da nan na hau ashe ba wata magana bace kawai chatting take so muyi a wani group din mu 3stars ni da ita sai Faiza.muka dan taba chat da su Hauwa, nayi musu sai da safe. sai ga Ummu ta shigo, tace "kin dawo" nace "eh, ya gidan" hira ta zauna muka danyi daga bisa ni kowa ya mike yayi makwancin sa.

Sai da nayi alwala nayo brush sannan na haye gadon na, wayata na jawo! Sai da na dan yi game din Tom Run Gold, wanda sai karfe 11 na kashe wayata, addu'ar bacci nayi, sannan na lumshe ido na sai bacci.




muje zuwa


MS INDABAWA


08062882472
MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY
5



Writting by MARYAM S INDABAWA
MANS

Dis page is for u FAIZA YAHUZA, Besty kuma Sis dita.
Love you soo soo much. Allah barmu tare Allah biya miki dukkan bukatun ki Ameen






Yau tin asuba ta tashi, bayan tayi sallah ne, ta wuce falon su karatun Al kur'ani ta saka, sai wajen 6:30 tayi kitchen din su,

Ruwan tea ta daura, feraye dankalin ta soya shi sama-sama ta kwashe shi, kwai ta fasa ta zuba attaruhu da albasa da kayan dandano, soyayen dankalin da dinga diba tana soya shi a cikin ruwan kwan ta. Sai da ta kammala, sannan ta daura farfeson kifi, kitchen tini ya dau kamshi, bayan ta gama ta gyare shi tsaf sannan ta wuce dakin su ta gyara.

Wanka ta shiga ta fito daure da towel tana sane jikin ta, gaban mudubi ta nufa ta zauna, Cocoa butter ta dauko ta murza a jikin ta sannan ta dauko powder ta blackup ta safa, kwalli ta dauka ta sanya a dara daran idanun ta, tana sawa su ka qara girma da ban sha'awa, man lebe ta dauko ta shafa a pink lips dinta.

mikewa tayi ta nufi durowar ta wacce take cike kayan a ciki, tsayawa tayi kallon su daga karshe ta dauko wata bakar doguwar riga wacce gaban ke da adon ja, a kan gado ta ajiye su sannan ta dauko body spray ta fesa ta dauko humra ta murje jikin ta, bra ta saka snn ta saka pant sai wani 3 quarter wando tasaka ves. Rigar ta zura ta dauko jan mayafi tayafa sannan ta dau wani jan sandal mai kyau ta saka shi.


Bangaren su Baba Lami ta isa, a kitchen ta isketa tana musu abincin kara, Kubra kuma na ta share share, har kasa ta duqa ta gaida Baba Lami, Baba lami ta amsa cikin sakin fuska, tana tambayar ta ta tashi lpy, da Lpy kawai ta amsa mata ta juya tayi cikin gida,


Bakin tea ta hada ta sha sannan ta mike akan kujera, yau tun da ta tashi take jin kamar ciwon ta nason tashi, dan kwana 2 tana fama da bacin ran MIJIN UMMUN tah, addu'a ta dinga yi Allah ya lafa mata abinda ke damun ta.


Motsin Khairat ta jiyo ta yk dakin su, da Sallama ta shiga Hafsat ta amsa mata, da gudu ta fada kan Antyn ta, sanye take da dark blie din wando saj sky blue din riga iya gwiwa, sai dan hijab iya wuyan ta, kafar ta sanye da sandal da farar safa kayan a wanke agoge sai kamshi take zubawa, ta dube Hafsat tace, "Taty yau ke
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment