Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

“CLASS MATE”
( ungulu da kan zabo )

ZAINUDDEEN JIBRIL
Tel: 08034840276
Email: [email protected]

GODIYA

Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, wanda iyawarsa ta zarce tunaanin kowa da komai, shi ne masanin sirri da ma abin da ke sarari, ikonsa ya wuce hasashen mutum bare dabbobi, shi ne kadai ke tafiyaar da lamura ba tareda karkata ba.

Salati ba adadi na yo gun Annabi Muhammadu (SAW) dan gata kuma sha lelen ubangiji, wanda binsa ya zamo wajibi kuma tilas akan duk mai kaunar ya sami dacewa da gidan tsira a gobe kiyama.

Na hada da iyalan gidansa da sahabbansa, tareda duk wadanda suka bi tafarkinsu ya zuwa ranar tonon asiri.

Ina mika godiyata zuwa ga mahaifiyata, da Allah ya sadata da gidan aljanna ya kuma kara daukakata ya yafe mata zunubanta ya lullubeta da rahama da jinkansa. Inason mamata sosai.

Masoyana, ina jinjina gare ku, da kokarin karatun kwamacala da nake gwaba muku, a hakan dai kuke daurewa kuke karantawa, Allah ya bar mu tare, ina yin ku irin sosai dinnan.

TSOKACI

Wannan labarin gajere ne kuma kirkirarre ne, na rubuta shi ne lura da wata barna da ke faruwa a cikin jama’a; in da za ka ga tsakanin mace da namiji kamar wasu mata da miji ko muharramai a yadda mu’amula ke gudana tsakaninsu, duk da sunan “class mate” wato abokin karatu a aji.

Labari ne na Sumayya tareda mai gidanta Ahidu, wadanda suke zaune lafiya da junaansu, suke gudanar da komai a gidan aurensu yadda ya dace, kafin tsautsayin “class mate” ya hau kan Sumayya, wanda ya yi sanadiyyar rusa duk wani farin ciki da suke ciki har ta yi danasanin kasancewa daya daga cikin wadanda suka yi boko.

Kamaar yadda na fada a sama, cewa labarin kirkirarre ne, sunaye da wurare da na yi amfani da su suma kirkira na yi, duk wanda ya ga sunansa ko halayyarsa ta dace da labrin ko jigon labarin, dace ne kawai.

Na yi wa dan gajeren labarin suna da “class mate”. Ina rokon ubangiji da ya datar da mu da alkhairi ya kuma sa abinda za mu rubuta ya fadakar ya kuma sa ya zama sanadiyyar tsirarmu a gobe kiyama.

*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_

Kamar kullum yau ma tun safe na ci kwalliya bayan da muka kammala break fast ni daHuubyna, tun ina cikin shower nake tuannin yadda yake kallona cikin shauki da nuna soyayya, hakan ta sa sai rero wakoki nake na Hausa hip-hop na Zainuddeen Zain ina cike da murna da bege hade da shaukin kauna, har nake ji, ba macen da ta kai ni dacen miji. Mijina ba ta yadda safiya za ta waye ba tareda ya gayamin zantuka masu ratsa zuciya ba, haka ko a cikin mutane ba ya gazawa wurin nunamani kauna, hakan ta sa nake bugun gaba da shi.

A jikina English wears ne, dan guntun skirt wanda ba zai wuce rabin cinyata ba, baki ne, wanda ya baiwa farar cinyata damar bayyana sosai, sai pink riga da ta matse ni sosai kamar dai yadda skirt din ya matse ni, sai rolling na gashin kaina da na yi kasancewar ba kitso a kaina, sosai ni kainaa ina jiyo kamshin gashin kaina wanda ya yi tsawo kuma ya ciko, duk ba wannan nake alfahari da shi ba, sai yadda Ahidu ke hadiyar yawu a duk lokacin da ya dora idanuwansa a surar jikina, ni kuwa sai tashi nake da gangan da sunan dauko wani abu a fridge ko daki, kawai domin na yi rangwada ta gabansa yadda zai ji dadi.

Sai fira muke yi kasancewar duk ranar weekend haka muke yi, ba ya zuwa ko’ina sai da maraice mu fita yawon zagayawa a kafa. Soyayya dai tsakanina da mijina har ta wuce kwatance.

Wata rana da ba zan taba mantawa da ita ba, mun tafi shopping mall domin mu yi sayayya, daga isarmu, na hango Sufy. Sufy class mate dina ne da muka yi kratu a jami’a ta JASU (Jarwo State University). Daga nesa muka fara jefawa juna zagi, “ke shegiya, ashe kina nan?” “shege mugun kwaro ina kuma aka shige?” daga isowarsa ya miko min hannu, ni kuwa abinka da sabo na mika masa muka tafa, ya rike hannuna cikin nashi, sai fira muke ta tuna baya, hannuna a cikin nashi yana wasa da shi, cen ya kalleni ya ce, “wallahi Sumy kinanan da kyawunki kalli fa yadda sai wani fresh kike karawa ga jiki duk ya ciko..” sai a lokacin na tuna fa tare muke da mijina Ahidu, kuma a kusa yake da ni, waigowa da zan yi, na ganshi sai mamakinmu yake, fuskarsa cike da alamar tambaya, gaba daya idanuwansa suka rikide suka koma ja, Ahidu da yake da haske sosai Fulani ne ga gemu mai tsawo da kasumba, amma haka fuskarsa ta dawo jawur, ya hadiye fuska kamar wanda aka turowa da sakon mutuwa. Na kalle shi, cikin rashin nadama na sake mayar da kallona zuwa ga Sufy, sai na ce “ga mijina” shi kuwa cikin rashin nadamar abinda ya aikata, kuma ya ki ya saki hannun nawu ya kalle shi ya ce “Ah! Yallabai kai ne ka kwashe muna most beautiful yarinya on campus?” ba tareda ya kalle fuskarsa ba, kawai ya dubi hannunsa da ke rike da nawu hannun, ya fara tafiya zuwa mota. Ganin haka nasan akwai matsala, cikin sauri na fizge hannuna cikin nasa, yana cewa “lafiya” na kasa ko na amsa masa, na fara sauri domin na tarar da mijina da ke kokarin bude kofar mota.

Sufy kuwa sai ya rike baki yana mamakin wannan abin, cen ya gyada kai ya wuce.

Ina masa magana, amma sam ya ki ya kulani nayi magiya na yi shagwaba na roke shi amma sam ya ki ya ko kalleni, tuki kuwa sai takar mota yake yi kamar wanda zai tashi sama, saura kiris mu buge wata mai tuyar awara kan titi.

Da misalin shida da sha bakwai na maraice muka karaso gida, ya fita ya bude gate din gida ya shiga ya yi parking, har yanzu dai ya ki ya ko kalle ni, ‘yan kayayyaki da muka siyo daga Shopping Mall dole ni na dauko su na saka cikin gida.

Shigowata ta yi daidai da shima zai fita, har yanzu fuskarsa a murtuke, har ma murtukewar yanzu ta dara ta farko. Na rike hannunsa, na ce “Hubby me ke faruwa ne?” ya janye hannunsa ba tareda ya kalleni ba ya fice abinsa cikin sauri.

Bayan na ajiye kaya, na shiga zullumi da tunanin me na yi wa wannan bawan Allah, iya sanina muna zaman lafiya, yau shekararmu daya da wata uku da aure, duk da ban haihu ba, ko kadan bai taba nunamin wani abu da rayuwata za ta iya baci a kansa ba, yana nunamin kulawa da soyayya, har ta kai ga ya shwagwaba ni, yau kuma ga shi yana kokarin jefa ni cikin yanayi da ban taba tsintar kaina a ciki ba. Nan wasu zafafan hawaye suka fara rigangayar sauka a lallausan kumatuna, tuni sautin kukan ya ci karfina har da shessheka, naci kuka har aka tada sallar magariba, na je na yi sallah, na dawo na dauko abincin da na girka muna kafin mu fita, na jera kan dining table, na shiga kamar yadda na saba na tsala wankana, da daukar kwalliya mai jan hankali, na dire kan TV ina kallon tashar Equity TV, ina jiran shigowar Hubbyna, amma shiru har aka fara sallahr isha, abinda ya bani mamaki sosai kenan, domin tsawon zamana da shi, duk inda yake, to bayan magariba yana gida, domin a lokacin muke cin abinci, idan muka kammala isha kuma, sai mu shiga fira har ila ma sha Allahu.

Daga ida sallah na dauko wayata coolpad, na danna lambarsa, amma har ta katse ba a dauka ba, a raina nace inaga aiki yake yi, na sake dawowa na dirshe a bakin TV naa ci gaba da kallo. Ban Ankara ba agogo ya buga kusan sha dayan dare, a lokacin har barci ya daukeni na farka, na sake janyo waya, na kira, kawai sai naji karar wayar a parlour, fitowa da zan yi, sai na ga Ahidu kwance kan three seater, waya cen kan teburi, sai kallon sealing yake yana karatun wasikar jaki. Nazo cikin rangwada na hau kujerar na dafa jikinsa da niyyar na sumbace shi, sai ya tashi zaune, fuska a murtuke.

Ganin haka na gurfana na saki kuka na ce “ka dubi girman Allah ka sanar da ni, laifin da na maka.” Ganin na shiga damuwa ya ce da ni “yanzu abinda kika aikata ya kyautu, kinsan dimbin zunubin da za ki kwasa kuwa, ace da aurenki, za ki bari wani kato ya rike hannunki a tsakiyar titi, wacce irin rayuwa ce wannan?” “haba Hubby, sai ka ce wanda bai waye ba? Dama kan wannan ne kake fushi? Wallahi har ka bani kunya, me ye a ciki? Class mate dina ne fa” ya sake kallona, a wanna karon cike da tsana, kamar ya sharamin mari, kawai ya rafka tsaki ya kwanta. Na yi rarrashinsa, amma kamar mai yi da gawa, dole na hakura, nima bansan lokacin da barci ya dauke ni ba, dole a parlour din na yi barci.

Tun ranar abubuwa suka fara rikicewa tsakanina da mijina, ga shi na kasa na nuna cewa kuskure ne na yi, bare na bada hakuri.

Wata rana ya kaini gun walima, dawowa da zai yi daukata, ya tarar da ni ina fira da Sufy, sai yi muke yi tareda kyakkyewa, har ina kaimasa duka shima yana kawomin, ganin haka ya kasa karasowa a kusa da mu, sai daga baya na hango motarsa, kafin na yi wa Sufy sallama, kawai ya buga motar ya wuce. Rikici ya dawo sabo tsakaninmu, a ranar bai shigo gida ba sai da misalin dayan dare. ya daina yimin magana gaba daya, ya daina cin abincina, kwwalliya idan na yi ko kallo ba ya yi bare ya yaba. Ni kuwa ganin haka na fara yi masa masifa, ina cewa, ai idan aure zai kara, bai dace ya dinga wulakanta ni ba, shi kuwa duk masifar da nake, ko kallo ban ishe shi ba.

A karo na uku ya sake ganinmu da Sufy, wannan karon har da rngumar juna kafin mu rabu. Ita ce ranar da ba zan taba mantawa da ita ba a rayuwata. Ina shigowa gida na hari daki domin nayi wanka, bayan na fito daga wanka, kan kayan kwalliyata naga takarda, a bayan takardar an rubuta, “zuwa gareki Sumayya” cike da mamaki na dauki takardar duk da nasan rubutun wa ye, na buda na fara karantawa. Ai na kasa karanta takardar gaba daya, numfashina ya fara kokarin kwacewa daga huhuna, hawaye kuwa kamar wanda aka baiwa gashi aka kwace, hankalina ya tashi na rude gaba daya gani daga ni sai towel a jiki. Sai maimaitawa nake yi, tun ina yi a zuciya har na fara yi a fili, “ya sake ni! Ya sake ni! Ya sake ni!” ina yi ina zabgar kuka.

Na yi bashi hakuri amma ina ya ki ya saurare ni, dole na hakura na kwashe kyana na koma gida, shiru ina jiran ya maidani, har na kammala idda.

Tun a lokacin na dauki alkawarin ba zan sake wannan fitsara ta class mate ba, nayi nadama sosai, ina kuma kira ga masu wannan halayyar da su duba irin hali da na shiga ta wannan sanadiyyar su yi wa kawunansu karatun ta nutsu.

*DR. ZAIN*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Book Chapters

Please Login or Register in order to submit comment