You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
data kawo mata ita".
Duk basuso haka ba, amma babu yadda zasuyi, shiko Bakura jin haka, yasa ya fara nazarin abinda zaiyi".
Washe gari, Amina ta kitchen tana aiki, kiran hjy ne yasa ta saki aikin da takeyi, tana zuwa gun hjyn, hjy tace jeki ki kwaso kayanki, yau zakibar gidan nan, domin medaki zanki inda kika fito".
A sanyaye Amina taje ta kwaso kayanta,shi kuwa Bakura tunda yaji magana tafiya, ya haďa baki da driver, yace anjima zasu fita da hjy, dan Allah yanaso idan lokacin fitan yayi yace bayajin dadi".
Koda hjy tazo akan yaje ya kaita unguwa driver yace bayajin dadi, keyadda Bakura ya uzarcesa".
Dole yasa hjy tace Bakura yazo ya kaisu, unguwar".
Bakura yayi haka ne,sabida yanaso yasan inda hjy zata kai Amina, domin ko lokacin da aka kawota, baya nigerin, lokacin yana waje yana karatu, dawowa kawai yayi yaga Amina a gidan".
Bakura yana driver, hjy ce ke nuna masa hanya, sabida duk yawon da yakeyi, bai taba zuwa ta nan area ba".
Suna isa, duk suka sauka, shiko Bakura sai faman karewa area kallo yakeyi, hjy tana meda Amina gun wacce ta kawota aikin gunta, sukai sallama ta fito ta shige mota, suka juya zuwa gida, abuja".
Bayan komar hjy gida da kwana uku, saiga Bakura yazo suleja, gun Amina, wannan karo har cikin gida ya shiga, bayan yayi sallama kanta ta leko, gani Bakura ne, da mamaki kande tace ya shigo, har ďaki tayi masa iso, bayan su gaisa, ya kalli Amina dake zaune gefe daya, murmushi kawai yayi mata".
Kanďe dake zaune, tana mamaki zuwan Bakura gunta, Bakura yace, hjy gunki nazo, niman wata alfarma, amma bansan yaya zaki dauki al'amarin ba".
Nan ya zauna ya warware wa kanďe komai dake tsakaninsa da Amina, buďe bakin kanďe tace, dama biri yayi kama da mutum, sabida gaba daya naga canji a gun Amina, nasan ba karami kaya take ja ba, lalla yaro kace kaima kana waya network".
bakura yace, yanzu abinda nakeso, shine auramin Amina zakiyi, amma banaso kowa ya sani, hatta iyayena, kada ki damu, idan maganar kuďi ne, konawa ne zai iya kashewa dan gani na mallaki Amina".
Jin maganar kudi yasa kanďe washe baki, nan dai suka shirya, batare da tayi tunanin abinda zaije ya dawo ba".
Washe gari da zuwa Bakura suleja, hjy ta bijiro da maganar zata aiki Bakura england gun babansa, da farko yaso yaki amincewa da tafiyar, amma da yayi wani tunani baki kawai ya washe, yana tambayar yaushe nene zai tafi".
Hjy tace nest week, hakan yayi dai-dai da lokacin yariga ya mallaki Amina a matsayin matarsa".
Washe gari Bakura ya koma suleja, kuďi ba dan kaďin ba, Bakura yabawa kanďe, ita kuwa Amina daukarta yayi yaje yayi mata paspot, su jima a wani guesthouse suna hira, sai aroud four sannan ya koma abuja".
Hjy dasu Am'abuwa suna can suna nema wa, Bakura visa, shima Bakura yananan yana nema wa Amina tasa visa ďin,".
Ranar juma'a bayan saukowa daga masallaci, aka daura auren Amina da muhammed, wato Bakura kenan".
Ranar asabar kuwa, daya daga cikin abokansa Bakura ya tura, suleja yaje ya dauko masa Amina, yace dashi kai tsaye airpot zai wuce da ita, kuma dan Allah yanaso yayi mata komai, har izuwa lokacin shiga jirginsu, kuma dan Allah bayaso tayi nisa dashi, kuma inaso ta kasance a gabata, ko kuma bayana, idan muzo layin shiga jirgi".
Wani irin shiga Amina tayi, cikin bskin jallabiya, haďe da nikabi, daga hannunta har zuwa kafarta duk ssnye suke da safa".
Har su Bakura da Amina suka shiga jirgi, su hjy da Am'abuwa basu gane ba, cikin sa'a kamar suka samu gun zama daya".
Saida jirgi ya tashi sannan Bakura yasa hannu ya buďe wa Amina fuska, da take rufe da nikab".
Wani irin murmushi ya sakar mata, haďe da rungumarta, yana faďin amaryata, itako Amina daga daya hankalinta baya gunsa, domin daga daya hanji cikinta han wani kugi yakeyi sabida tsoro, sabida tunda Amina take a rayuwarta bata taba zato zuwa koda filin jirgi ba, balle shiga cikin jirgi".
A lokacin ne, Amina ta tuno da mahaifiyarta, wani irin kuka Amina tasa, haďe da kiran ummata, kuka sosao Amina keyi, gani haka yasa bakura rungumarta a jikinsa sosai yana bata magana".
__________
Tun bayan kammala karatu Bakura da yaje a kasar Germany ya dawo gida nigerian, hjy khursum ta buďe ws Bakura katafaren kanti anan cikin garin abuja a area 11, kantine daya haďa komai-da komai,kama kayan su turaren ďaki na jiki, na gyaran amare da dai sauransu".
Hjy khursum ba'a nan ta tsaya ba, domin har sari take badawa, gari gari, sannan kuma tana sikawa dasu kaashen ketare, Bakura yana kai mata, dalilin da yasa kenan, yanzu haka baya kaunar aikin gwamnati, duk da kasancewarsa business admi ya karanta,amma yanzu business ďinsa yafi masa aikin gwamnati".
Bayan dawowar Bakura ne daga waja, aka kawo Amina aiki a gidan su, da farko kam babu wanda ya kaisa tsanar Amina, kasancewarsa yar'kauye,amma data fara kilewa tana wanda da sabulai masu kyau da tsada, ga kuma cima ba daya ba, hakan yasa Amina ta canza, kyawuta ya kara fita, sosai, dan ma ba kwalliya takeyi ba".
Tun daga lokacin Bakura ya fara raya abu a zuciyarsa, a duk lokacin da zasu haďu da Amina saiyaji zuciyarsa yana raya masa abu iri-iri".
Wata rana, ranar Bakura ya tashi babu lafiya, babu yadda su hjy basuyi dashi ba, akan yafito yazo cikin yaci abinci, amma bakura yace bazai iya ba".
Hjy dake zaune, tacewa Amina ta dauki abincin Bakura takai masa side ďinsa, da sallama Amina ta shiga ďakin, dai-dai lokacin Bakura amai ya yunkuro masa, tana shiga,gani halin da bakura ke ciki yasa Amina ije kular dake hannunta, hannu tasa ta dagosa daga duken da yake, ruwa ta dauka ta fara zuba masa a fuska, sannan Bakura ya numfasa daga nishin da yakeyi, a lokacin ne bakura ya lura da yadda wiyar rigan Amina duk a bude yake, karaf idanusa sukai arba da nonuwar Amina, nan take yaji wani irin, ita kuwa Amina bata lura da haka ba, ci gaba kawai tayi da abinda takeyi".
Amina batabar ďakin ba, har saida ta gyara ko'ina, sannan tabar ďakin, koda Amina ta koma cikin gida, dasu hjy suka tambayi dalilin daďewarta, a side ďin Bakura, nan ta kwashe ta faďi masu".
Tun daga lokacin Bakura yake fako, duk lokacin da su hjy basu gida, yake lallabar Amina ya biya bukatarsa, amma duk irin abinda Bakura keyi bai taba sex nata ba, sai shafa da sauransu, sannan kuma yace kada ta sako wani yasan abinda ke faruwa a tsakaninsu, idan tabari wani ya sani, musamman ma hjy, shi babu ruwansa, kuma Allah yasa tafi kowa sani halin hjy".
Da lilin da yasa kenan koda wasa Amina bata bata gaya wa kowa ba, tun Bakura nayi tana kuka, har tazo ta daina, wani lokaci ma, ita da kanta ke nimar hanyar da zasu haďu, dan dai yayi mata irin abinda yasa yi mata, abu kamar wasa Bakura yaji babu wacce yakeso a rayuwarsa irin Amina, dalilin kenan daya sa mata suna *ZYNAH* wato *BEAUTY* duk lokacin da suka keďe da ita, da sunar yake kiranta".
__________
Tun bayan tafiyar Amina sadiya ta shiga matsanancin hali na damuwa, har ciwon zuciya saida sadiya tayi, daga karke, ta fauwala wa Allah komai, ta koma addu'a da rokon Allah, duk inda Amina take Allah ya tsareta ya kuma kareta, daga dukkani masu shirri, ya kuma haneta yin zinar da ake nufita dashi".
Babu mamaki, addu'ar sadiya ce tayi tasiri akan Amina da bakura, duk tsawon lokacin da suka ďiba suna wannan aiki, Allah bai basu ikon sex a tsakanisu ba".
Romacing kam, iya romacing sunayi, amma banda sex ".
Ban garen zainab kuwa, rakiya ta samu sa'ar zidda cikin da tayi, batare da wani ya sani ba,amma sati biyu, zainab taji sauki sosai ta gare, suka koma bakin aiki, duk da sadiya ta san komai amma babu wanda ta taba gaya mawa, sabida tasan koda ta fada ba lalla bane a amanice, karkanta ma za'a iya cewa bakin ciki ne, hakan yasa taja bikinta tayi shiru a ce warta akwai ranar kin dillanci"
_*wannan kenan*_
_*Germany*_
*mmn uswan ce📚✍*
🍀🍀🍀🍀
_*ZYNAH!!!*_
🍀🍀🍀🍀
*WRITTEN ✍ BY MMN USWAN*
_______________
©©©©©©
_*follow me on*_
_*wattpad:Hauwa s zaria*_
_*Facebook group*_
_*Mmn Uswan*_
➿➿➿➿➿➿
_*BISLLAHI RAHAMANI RAHIM*_
_*In the name of Allah, The Beneficent, the Merciful*_
🅿1⃣5⃣-2⃣0⃣
Bakin hjy har rawa yakeyi, domin ta kasa kiran sunan bakura, sai faman cewa takeyi, babbbbkura!!!" Kanka daya kuwa? Kodai gamo kayi?"
Shiruuu yayi, bai tanka mata ba".
Da kaukausar murya tace, karyane wlhy, domin wannan maganar da kakeyi, kwata-kwata hankali ba zai dauka ba, sake fisho zynah tayi tana kokarin igijeta waje".
Da karfi zynah ta rike bakura, idanuta kafe a kansa".
Ita ko hjy sai faman cewa takeyi, dan ubanki sai kin bar gidan nan, idan ma wani asiri kikayi masa to wlhy daga yau takare, domin"...
Kafin ta hurta abinda ke bakinta, hannu bakura yasa ya jawo zynah zuwa ciki, yana faďin kiyi hakuri hjy, nine nayi maki laifi,amma ba Amina ba, idan hukuci zakiyi ni yafi dacewa da ki hukuta amma ba ita ba".
Sokoko hjy ta tsaya baki buďe, gaba daya kanta ya daure, ta kasa gane sama take ko kasa take, domin jin takeyi kamar mafarki takeyi, ido kawai tabi su dashi".
Suma kansu yayyun nasa, mamakine ya hanasu magana, domin suma gani suke duk a cikin bacc suke kallon wani dimaďin".
Kan cushion bakura ya kaita ta zauna, s lokacin ne hjy ta dawo daga tunanin da takeyi, wani irin ihu tasa, tsalle tayi tai kansu, kafin hjy tayo kansu da sauri bakura ya rufe Amina, hakan yasa hjy bata samu kamar damko Amina sai bakura, nan ta hau dukansa kamar Allah ya aikota gareshi".
Duk irin dukan da hjy kewa bakura, bai damu ba, shidai kokarin kare Amina yakeyi, su Am'abuwa da Yah-na da suke tsaye, gani yadda hjy ke dukan dan uwarsu, gaba daya sukayo kan hjy suna kuka suna kokarin jawota daga jikinsa".
Gani hjy taki hakuri yasa Yah-na ta h'au Amina da duka, tana dukanta haďe da zagi, gani haka da sauri bakura yayo kan Yah-na, shima yana kokarin kai mata duka".
Da sauri Am'abuwa ta shiga tsakiyarsu, ba tare da bakura ya ankara ba, saukar mari yaji kass kass kass har sau uku, a lokacin ne hjy ta yanke jiki ta faďi akan cushion tana maida numfashi".
Shi kuma kamo hannu zynah yayi zuwa side ďin shi, sabida kuka, saida zynah ta kasa magana, suna shiga ďakin saida bakura ya rufe kodar da key sannan ya rungumo zynah yana kallashinta haďe da bata hakuri".
Cikin kuka zynah tace ita tafiya zatayi, nan ma hankalin bakura ya kara tashi, hakuri kawai yake bata, haďe da faďi mata daďaďan maganganu masu kwantar da hankali, har ta hakura, da maganar tafiyar".
Tunda suka bar part ďin hjy basu dawo ba, shirun da hjy taji, yasa ta kwashi kayan zynah ta watsa mata a waje, bakura da zynah sukai thre hour a ďaki basu fito ba,suna ďaki kwance, yunwa yasa bakura buďe kofa zuwa part ďin hjy, yana cikin tafi yaga kayan zynah a zube a kasa, dukawa yayi ya kwashe yakai ďakinsa".
Bayan ya ije kayan ne, ya dawo, falo ya gansu suna cikin abinci, ko kallonsa hjy bayi ba, duk da baiji dadi hakan ba, amma ya matse, ya juyo gun Am'abuwa yace sis ina tawa a abinci?"
Yana kitchen kawai tace masa, daga sannan bata sake magana ba, mikewa bakura yayi ya nufi kitchen,buďe bakin hjy tace ina zaka?"
Kitchen zani daukar abinci na"
Kada ka shiga min kitchen, idan har kashiga wlhy saika gamu da bacin raina,"" harr bakura ya buďe baki zaiyi magana, wani irin tsawa hjy ta daka masa da bacemin da gani, tun kafin na taso maka".
Jiki a sanyaye bakura ya fita, Am'abuwa dake zaune bataji dadin abinda hjy tayi wa ďan uwanta ba, Yah-na ko cewa tayi, ai wlhy hjy kinma masa kaďan da baki tsine masa ba, shegen yaro kawai, kamar bakura shine har zai aikata wannan irin aikin".
Cikin harshen barbanci taci gaba da cewa, ki bari kawai, besan dawa yakeyi ba, kuma wlhy idan har nacika barebari sai shegiyar yarinyar ga tabar gidan nan, shi kuma ni dashi ne a gidan nan, tunda har ya'iya irin wannan aiki, ni kuma saina nuna masa kuskurensa, kuma daga yau na haramta masa cin abincin gidan nan".
Sai kuwa hjy, wlhy bama abinci ba, duk wani abu da kikasan kinayi masa, wlhy duk ki daina, har sai ya koreta sannan kuma yazo ya duka gwiwa bibiyu ya rokeki gafara".
Aini wlhy hjy a yadda nasanki da zafi, ban taba zaton iya hukuncin da zaki yanke wa bakura kenan ba".
Himm kawai hjy tace, daga sannan bata sake cewa komai ba, sai faman cizon yatsa da dakeyi".
Am'abuwa dake zaune idan ba kallonsu ba babu abinda takeyi".
Bakura yana fita daga part ďin hjy, ďakinsa ya koma yaje ya dauki key ďin mota, restaurant yaje ya siyo masu abinci ya dawo, a lokacin da yake dawowa ne, hjy taji motsi mota, da sauri ta mike ta nufo waje, gani bakura ne a motar, tsayawa tayi har yayi parking, hannu kawai ta mika masa alama ya bata key ďin motar".
Ba tare da musu ba ya mika mata, sannan kuma tace ya bata key ďin shagunarsa, ďaki ya koma ya kwaso key's ďin yazo ya bata".
Bakura na shiga ďaki yaga kular abinci, zynah take sheda masa, Am'abuwa ce ta kawo masu, bakura yaji daďin haka sosai, na nuna kulawarta a garesa".
Tun daga lokacin da hjy ta amshi key's ďin shago be wani damu bakura sosai ba, coz duk abinda ya tambayi daddynsa yana turo masa shi, abinci kuma duk lokacin da Am'abuwa tayi girki tana sa masa, ba tare da hjy da Yah-na tasani ba".
Amma ita kanta bataji daďin abinda yayi ba, da kuma abinda yayi wa hjy, nan tace yabari idan ta huce yaje ya roketa gafara" Bakura yace, in sha Allahu".
Sati bakura daya, koda gaida hjy yayi bata amsawa, cikin side ďin ma gaba daya ta hanasa shiga, dole yasa yakoma rayuwa daga shi sai zynah".
_*wannan shi ake kira ga koshi ga kwanan yunwa, duk daďi abu idan babu kwanciyar hankali, ba daďin sa zakaji ba*_
Gani ba zai iya zama mahaifiyarsa tana fushi dashi ba, zuwa yayi A.Y.A, gidan hjy *Ashe* ya zayyana mata komai, ďan babu abinda ya boye bata".
Hjy Ashe tayi mamakin bakura daya iya aikata haka, sai dai a wani ban gaare kuma, taji daďi sosai dayayi tunani zuwa sanar da ita, faďa tayi masa sosai haďe da faďi masa bai kyauta ba".
Duk fadar da tayi masa bakura bai musu ba, domin ya amsa laifinsa, godiya sosai yayi mata sannan sukayi sallama tace zatazo gidan ta sami hjy".
Bakura yaki sanar wa daddy sane, ba dan sabida komai ba, duk mutumin da baya tare da iyalansa, idan za'a kirasa a sanar dashi abinda ke a gida, hankalinsa sai yafi naku ku da kuke gidan tashin. Da lilin da yasa bakura bai sanar wa daddy ba kenan".
Washe gari saiga hjy Ashe tazo, hjy khursum da murnanta ta tari hjy Ashe, kai tsaye bedroom suka nufa, waya ta dauka ta kira bakura, tace yazo ya sameta a ďakin hjy".
Mikewa yayi haďe da daukar jallabiyarsa yasa, ina zuwa kawai yace wa zynah dake kwance".
Kai tsaye ďakin hjy ya nufa, da sallama ya shiga, hjy Ashe ce ta amsa masa, har kasa ya duka gwiwa bibiyu ya gaida ta, bayan su gaisa hjy Ashe tace bakura ya memeta abinda yazo ya faďi mata".
Nan bakura yasake faďin irin abinda yazo ya faďi mata"
Sannan hjy Ashe ta juya kallonta zuwa ga hjy Khursum tace kinji ko,yanzu tunda ya amsa laifinsa kiyi hakuri ki yafe masa".
Shiruu hjy Khursum tayi tana kallonsu, ba tare da tace uffan ba, har zuwa tsawon minti goma zuwa ashirin, sannan tace yanzu sabida Allah abinda yaronga yayi ya kyauta kenan?".
Ya rana wacce zaiyi wa ciki sai er'aiki? to a daďin me? Nan ta fashe da kuka tana faďin Allah ya gani kuma shima sheda ne, daga ni har mahaifinka bamu bata yin zina ba, shine kai zakaje ka aikata haka ko? To wlhy bari kaji, bazan taba amsar er'shege a matsayin jikata ba".
Bakura yanaso ya sanar dasu kamar ba shege bane, amma kuma yana tsoron yadda hjy zata dauki maganar, hakan ma yaya aka kare, balle taji maganar aure" Can dai wata zuciya tace, Muhammed fito ka faďi gaskiya, kawai zaifi maka,domin boye-boye bazata amfana maka komai ba, balle ma a irin wannan lokaci".
Cikin rawar baki yace bafa shege bane, aure mukayi"""...
Bakin hjy Khursum har yana rawa, tace auuauuauure fa kace?"
Shiru bakura yayi, kansa na kasa".
Ba tare da sun ankara ba, daga bakura har Hjy Ashe tsalle hjy Khursum tayi sai kan bakura hannu tasa ta shakosa, itama hjy Ashe da sauri t tayi kansu tana kokarin cire wa hjy Khursum hannu a wiyar bakura, babu yadda hjy Ashe batayi da hjy Khursum akan ta sakar wa bakura wiya amma taki, sai faman cewa takeyi bari na kashesa na huta da gani abin takaici da bakin ciki".
Kururuwan sune yasa su Yah-na da Am'abuwa suka gashi ďakin a guje, gani abinda ke faruwa ne, yasa su fashewa da kuka, suna kokarin cire wa hjy hannu a wiyar bakura".
Da'kar suka cire mata hannu a wiyar bakura, duk a lokacin tana zaune a kanta, gani haka yasa ta koma mutsilinsa,duk inda tasamu mutsila kawai takeyi, tanayi tana babatu".
D'akar suka samu ta sauka, tana sauka bakura ya tashi zaune, gyara rigan dake jikinsa yayi ya koma a duka a gefe, hjy Ashe tace su Yah-na su fita su basu gu".
Nan bakura yaci gaba da bawa hjy Khursum hakuri, ta yafe masa, hada baki sukai suna bata hakuri, har ta hakura amma da sharaďi".
Ashe tace, shawaďin me?"
Saidai ya rabu da Amina, idan kuma yace ba zai rabu da ita ba, ita kuma a maysayinta ta mahaifiyarsa bazata yafe masa ba".
Babu irin hakirin da hjy Ashe bata bawa hjy Khursum ba, amma taki hakuri, daga kaeshe dai cewa tayi bakura ya basu gun, bakura yana fita hjy Ashe ta gyara zama sannan tace Khursum".
Itama juyowa tayi suna kallo juna, tace keki godewa Allah da har Allah yabashi hankalin da tunanin yin haka, ni nawa yaronfa? So nawa nake kama *Malah* da yaran aikina, idan baki sani ba to yau zan sanar dake, duk yaron da zan dauka aiki, wlhy ba sabida Allah nake sallamarsu ba, malah ke addabansu".
Daga karke iya abu dana dauka a karshen nan, tana bacc cikin dare malah ya fada mata, Allah ya taimakeni bai riga ya shigeta ba nazo".
Ki duba dagani har alhj bbnsu wani irin gatane, bamu nunawa yaran nan ba, kinfi kowa nasanin irin en'matan dake garin nan, amma dan jarabar duniya su rasa wanda zasuyi irin wannan har kan dasu sai yaran aikin?"
Himm Ashe kenan, ni abinda yafi bani mamaki da yaran nan kwata-kwata guda nawa suke, to yanzu fa ji abinda bakura ya ďibi, ni abinda ma yafi bani takaici, ace er'aiki".
Er'aiki ba mutum bace?"
Haba Ashe, kamar ni ace er'aikin gidantace kuma ta koma sirikata?"
Nidai koma menene, inaso bakura yaci arzikina ki yafe masa, kuma ki bashi key's ďin shago dana motarsa, duk da dai babu daďi, amma inda haka malah yayi ai daya fi, akan kullum ya rika faďa wa yaran jama'a, ke banda ma Allah yasa ba gida daya muke da kishiyoyina ba, kema kisan sai fata ya gagareni, sabida gori".
Himm Ashe kenan, keta kishita kike, yanzu sabida Allah idan kawayena sukaji wannan labari mai zance dasu? er'aikifa?"
Idan er'aiki menene to, kada ki mance rayuwar nan, ba kamar gida ba, kowa harkan gabansa yakeyi, idan ma su sani menene? Kice daga gida maiduguri aka auro ta".
Nan dai hjy Ashe tata tausar hjy Khursum har ta hakura ta bada key's ďin shago dana mota da kuma sharaďin Amina zatabar gida, sannan ta tafi".
Bakura godiya yayiwa Ashe sosai, washe gari tare suka fita da zynah, gidan kanďe ya kawota, yana bayan kwana biyu zaizo ya dauketa, ita kanta zynah ďin yace kada ta faďi wa kanďe abinda ake ciki".
Tun daga ranar da zynah tabar gida hjy ta shirya da bakura, komai yayi kai tsaye kamar yadda ya saba dah!".
Bayan kwana biyu yasa aka nima masa gidan haya a cikin sulejan, wata unguwa da ake kira *A.P.C* quarters, ba wasu kaya ya zuba ba, sabida yasan na ďan zaman nata na ďan lokaci ne".
Katifa kawai sukasa sai abinda baza'a rasa ba, bayan kwana biyu da tare warsu, yasa kanďe ta samo masa er'aiki, sabida tarinka taya zynah hira, itama zynah ďin waya ya bata, yace duk abinda takeso ya kirasa, yaso bata babba waya,coda chat ne, sai suyi, matsala daya ce, ba karatu tayi ba,dole yasa ya barta da karami".
Yanzu kam hankali bakura yaďan kwanta, ba kamar dah ba,mafi yawanci lokaci koda ya sallami hjy da sunar zaije shago ba nan yake zuwa ba, gum zynah yake zuwa, susha soyayyar su, balle dama bakura irin mazan nanne masu yawan bukata".
Ko kuma kuruciya ne, kesa shi haka oho" Domin a yadda yakejin kansa yanzu babu wanda ya kaisa jin dadi duniya".
Ďan yasa yanzu yake sheke ayarsa da zynah, gashi zynah tada abu daya, koda kwana zaiyi a kanta bata magana, domin itama abinda takeso ne".
Hjy tayi gudun garane ta faďi ma sago, domin yanzu irin da sukeyi, sai Allah, amma kuma, inda a cikin gida suke dole su rage wani abu, ďan ma har yanzu zynah bata gama kilewa ba, wani abin bakura ke koya mata, gani harda rashin boko ke cutarta, yasa bakura duk lokacin daya tare da ita, yana kokarin koya mata A.B.C.D, bayan ta iya, sannan ya fara koya mata two letter world three letter, da shike mai kwakwalwace, har ta iya, yanzu kam ta fara iya rubuta sunanta da nashi".
Wani lokaci kuma idan anzo karatun, mancewa akeyi da shi a kama soyayya".
Kullum na barawo, rana daya ta me kaya, abinda sa ido irin ta hjy, bayan bakura ya sallameta akan zaije kasuwa, yana zuwa bayan yaran shago su buďe shagon, tunda bakura yabar kasuwa, kai tsaye suleja ya nufo, gun zynah, be koma akan lokaci ba, domin duk lokacin daya tsicci kansa tare da zynah, mancr komai yakeyi".
Bayan azahar hjy ta shirya zuwa kasuwa, tun a bakin kofa ta fara zargin bakura baya shago, bata gasganta ba saida ta shiga ciki, ganita yasa duk yaran shagon suka mike, sukazo suka gaisheta a ladabce,bayan su gaisa ne, hjy take tambayar ina bakura?"
Magana ďin shago yace, tun safe daya shigo, ya sake fita bai dawo ba har yanzu, take hjy ta juya harshe tana faďin wlhy idan har ysnzu suna tare da shegiyar yarinyar nan ne, saina bata masa rai".
Yau da gobe ya wuci wasan yaro, ashe yaron shagon yaji abinda hjy ke faďi ".
Hjy na juyawa yace, yau ne kawai ya fara haka ko yau ne kawai?"
Daya tuno irin alkhairin da bakura keyi bamu yasa shi rufa masa asiri, yace yau ne kawai hjy".
Ba tare data tanka masa wayar ta ta ciro daga cikin jaka ta fara kiransa, bakura yana gani kiran hjy yaji gabansa ya faďi, hjy tayi kira har sau uku amma bakura bai daga wayar ba".
Lokacin da bakura yaga kiran hjy, lokacin yana kan network yana sending messages ne ya hanasa daga wayar".
Tsaki kawai hjy tayi, haďe da juyawa, cikin bacin rai tabar gurin".
Yana sauka yaje yayi wanka, yau be daďe ba kamar