Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[12/6, 9:38 AM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹


*By*
*fatima* *Batula*

*Dedicated*
*to* *my* *shadow*

wattpad@fatimaumarmoddibo

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

...............................................................

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

..................................................................

Page 1
.

.....Cikin yanga da ƙasaita take saukowa daga matakalar benan gidan, idan ta ɗaga kafa daya kafin ta ƙara ɗaga ɗayar ta sai ta ɗau saƙonni,duk wanan abun cikin kayan makaranta take yi,sikit ne ɗan ƙarami iya gwuwarta nevy blue sai rigarta fara mai ratsi-ratsin blue ba hijjab a jikin ta sai hular da ke kanta.

Wata kyakykyawar dattijowar matar da ke zaune a cikin tanƙameman falon ta hango yadda take saukowa daga benan murmushi tayi sanan ta ce "ƴar aljanna!! ke kullum sai kinyi latti,kinsan ƙarfe nawa ne yanzu kuwa?
cikin tausasawa take mata maganar.

It kuwa wacce aka kira da ƴar aljanna ko a jikinta banda ma ƙara rage saurin da tayi.

Wanan dattijowar bata ƙara ce mata komai ba, binta da kallo da tayi ko kaɗan bata nuna alamun ɓacin rai ko wani abu makamancin haka a fuskarta ba banda ma wani lafiffayan murmushi da take yi .

Ƙamar ta ƙarye dan tsabar yanga,ta iso falon,kan jikin dattijowar ta faɗa ,kanta matar ta taɓa,cikin so na nuna damuwa ta ce "Ƴar aljanna ko ba zaki makarantar ba ne? idan ba zaki ba muje ki cire kayan sai ki gayamin inda kike son zuwa mu je"

Kamar mai tsoron magana ta buɗe bakinta cikin shagaɓa ta ce "Zani *Hajiya* bana son wahala ne gashi wanan ƴar iskar malamar ce maiyar turanci zata fara shiga ajin ,ta kai ƙarshen maganar haɗe da ramutse fuska tana kallon Hajiyar.

"Kam to kina jina,duk abinda aka miki ki kira ni,zasu ga wanda ya tsaya miki,ni da su ne shege ka fasa ɗan halar sai yanka"

Washe ƙaramin bakinta tayi ,tana jin daɗi da alfahari,rungume hajjiyar tayi "Ina sonki hajiyata"

Tana faɗa ta tashi tabar falon cikin jin daɗi.

"Nima ina sonki ƴar aljanna sai kin dawo"

Tun kafin hajiya ta gama maganar ta bar falon.

Ɗaidai waata ƙatowar makaranta wacce kallo daya zaka mata ka fahimce makarantar bata ƴaƴen yara ba ce,ta tsaro da navy blue da farin fanti,yanayin makarantar idan ka gani ka ce ba'a j9 ba ne dan yadda suka tsarata,ƙatowar motar ta tsaya.

horn ɗaya direban yayi aka buɗe ya kunna kai,saida ya isa inda ake faking ɗin motoci sannan ya tsaya,bata wani tsaya ɓata lokaci ba ta fito.

J S S 3
Aka rubuta a saman ajin,kai tsaye ta kutsa kai ba tsoro ba tantamar komai,kanta a ƙasa.

"Hy how dare u enter me class without any excuse"

Saida nayi da ƙyar sanan naji abinda take faɗi,dan yadda take turanci kamar ba ƴar 9j ba,ko wacce tai karatu a kasar turai.

Ko ƙadan bata ji tsoro ba ta ɗago kai ido biyu suka yi,da wacce tai maganar

Tsaye take a gaban Allon,kyakykyawa ce ajin farko kallo daya zaka mata ka fahimce yadda tsarin halitar jikinta yake,ƴar gajerace ba cancan ba,sirirya ce ga dogon hanci kyakykyawa,bata da wani girman jiki amma kana kallon fuskarta zata san cewa wanan ba yarinya ba ce,dan ta kwana biyu.

Tun a kallo na farko na gane ƴar iyaye ce,dan yadda take yamutsa fuska kamar tana kallon ɗanyen kashi.

Ido cikin ido suke kallon juna,bata ɗauke idanta ba ta fara tafiya.

"Keee wacce irin dabbace mara hankali da wayau kuma jahila"
Cikin ɓacin rai da kausassaiyar murya ta faɗa.

Wani irin mugun kallo ta bita da shi mai cike da tsana ,amma sai naga ta sake wani ɗan karamin murmushin keta ta ce "Au sari kinsan bana jin turanci balle irin naki me kama da yaren chaina"

Tana rufe baƙi yan class ɗin suka fashe da dariya wanda daman tunda ta shigo hankalin su ya dawo gareta dan sun san sai anyi drama...

Fita tayi daga cikin ajin ranta a ɓace,ita kuwa ko a jikin ta daman hakan take so ,tana jin zafin maganganun da Aunty ke gaya mata,shiyasa ta ke son ganin ɓacin ranta.

" *Sabreen* *Muhammad* *mai* *taƙama*"
Da ƙarfi ya kira sunan cikin faɗa.

"Kina ina?yana maganar yana kallon ƴan class ɗin.

Gaba daya ajin yayi shiru kamar ba halitta a ciki dan ko numfashi a hankali suke yi dan tsabar tsoron wanda ya shigo ajin.

Cikin nuna ko a jiki na ta tashi daga gurin da take zaune ,hankali kwance ta nufi inda suke,kallon Aunty ta fara yi wacce tare suka shigo class ɗin da shi.

Saida ta matsu kusa da shi sosai sannan ta tsaya ,ta kuma zuba mishi manyan idanuwanta wanda ba alamar tsoro a tare da su.

"Me kika cewa Malama *Haulat* *Hashim* *Kabir* ?eyeeh ba dake nake ba,kin kafe ni da ido"

Saida ta kalle malama Haulat ɗin sanan ta dawo da kallonta gare shi "Ce mata na yi ni bana jin turancin ƴan chaina,tamin na ƴan nigeria"

Shi kanshi bai san lokacin da dariya ta suɓuce mishi ba,dan duk makarantar kowa yasan iyayenta gurin turanci amma ba wanda ya taɓa mata magana sai Sabreen.

Ganin shi ma ya fara dariya abin ya ɓata mata matuƙa ga yan ajin suna dariya,a fusace tabar class ɗin,tsanar sabreen kuma da niyyar ɗaukar fansa.

Ganin ta fita yasa shi ma yai sauri yabar ajin.

wani annuri ya baiya na a fuskar sabreen dan jin daɗin yadda ta ga ranta a ɓace,komawa tayi ta zauna amma duk ji take yi bata rama hulaƙancin da malama haulat ɗin ke mata.

Zaune take ita kaɗai a staff room tana tunanin wani irin abu zata ma Sabreen ta huce,murmushi naga tayi wanda ya ƙara baiyana kyawun ramammiyar fuskarta,wato abinda zata ma Sabreen tayi shi yasa ta yin murmushi.

Ƙarfe ukku daidai aka buga ƙararrawar tashi,koya hankalin shi ya koma gidan, gaba ɗaya malamai da ɗalibai sun fito kuwa ya nufi hanyar gurin ajiyar motoci.

Har aka gama zuwa ɗaukan dalibai Sabreen tana zaune ita kadai ,ranta ya ɓace sai huci take yi,tana turo baki,tashi tayi zata fita bakin get.

Da mugun gudu motar malama Haulat ta zo wuce wa,ta gabanta kamar zata ɗauke ta,da sauri a ruɗe sabreen ta matsa har saida ta faɗi kasa,wani irin ƙululon takaici ya kamata,da zafin nama ta tashi ta nufu motar.

Tana ganin ta nufota ,ta fito daga motar tana wani yamutsa fuska kamar wacce tai arba da kashi

" U are very no what u are,okkk i forget u are illiterate ,baki da gwagwalwa ne ko a garin mahaukata aka daukoki da kina ganin mota ba zaki iya kaushewa ba"

Tunda ta fara magana Sabreen ki binta da idanuwa wadanda sukai jajiir dan tsabar takaici.

Ita kuwa malama Haulat ganin ta cinma burinta yasa ta wuce ta barta anan tsaye, ta kuma ja motar da karfi har saida ta watsa mata kura.

Wani lafiyayyan hawaye ya fara bin fuskar Sabreen wanda ita kanta bata san da zuwan su ba, sai jin su tayi a fili ta ce tana huce kamar wacce tai faɗa da zaki "Hmm baki san waye Sabreen Muhammad mai taƙama ƴar Aljanna ba ne,bana yafiya kuma bana biyar bashi zan rama ramuwar gaiyya"

Tana faɗa ta sa hannuwanta ta fara goge hawaye tana faɗin "Hm kika sa ƴar aljanna hawaye zai kin biyasu"

"To yah zanyi idan na gayawa hajiya ,A'a ba zan gayawa hajiya ba,ni da kai na zan ji da ita "

Ita fitowa bakin get ɗin direban ta ya zo ,bata ce mishi komai ba ta buɗe motar ta shiga.

"ƴar aljanna kiyi hakuri wallahi faci tayar motar tayi,jikin shi har rawa yake yi dan tsoron karta gayawa Hajiya"

Banza tayi da kamar bata san da wani a cikin motar ba.

Sai magiya yake mata akan karta gayawa hajiya.

"To naji amma zai kamin abu ɗaya ta faɗa tana kallon shi

"to zanyi ƴar aljanna koma meye zanyi"

Murmushin mugunta tayi da jin daɗi ,harda sauke ajiyar zuci.

Daidai wani katafaren gidan direban yayi horn aka buɗe mishi,giɗan ya haɗu iya haɗuwa abin sai wanda ya gani,dan tsayawa kwatanta muku sai ya ɗauke ni lokaci mai tsawo.

Tana jin ƙarar motar su,ta fito da sauri har bakin motar ta fito tana wace baki ,ita da buɗe mata kofar hade da faɗin "Ƴar aljanna kin dawo tun ɗazun naji shiru ina ta jira hankali na ya tashi ina fatan dai kina lafiya"

Murmushi tayi sannan ta rungumeta "Kina lafiya hajiyata yau bamu fito da wuri ba ne,wanan ƴar iskar malamar ce ta tsayar da mu"

"Cikin nuna damuwa ta janye jikin ta tace"Wai ko sai na tura anje gurinta ne aja mata kunne,ko na fitar da ke daga makarantar gaba ɗaya ma"

"A'a Hajiya ki barta kinji "

"to ni bansan duk wani mahalukin da zai ɓata miki rai,zan iya yin komai akan farincikin ki"

Daidai da isar su cikin katon falon wanda shi ma ya ƙyyatu har tsoro yaban dan tsabar kyaun shi,ga wani asirtaccen kamshi wanda ya haɗe da AC ɗakin.

Murmushi tayi cikin shagwaba ta ce "Nima na sani hajiyata,amma tunda na ce ki barta kawai ki barta zanyi maganin ta ,zan gwada mata ni ɗin ƴar gata ce"

"Hajiya bari na hau zama nayi wanka sai nayi sallah na huta"

"Yawwa ƴar aljjanna na manta ban gaya miki ba,ɗan india ya dawo an jima sai ki je ku gaisa"

Yamutsa fuska tayi yin sunan wanda ya dawo din"Wanan dan iyayin wanda aka je ɗauko mu tare"

"Eh shi fa"

"Tabbb gaskiya ni ba zani ba saida shi ya zo "ta faɗa tana hada rai

"to shikenan ba zai kin ɓata rai ba,zan sa ya zo da kanshi,kinji hankalinki ya kwanta"

ta washe baki "eh hajiyata,ta haye sama ,a ranta tana faɗin yadda zata ganshi dan tun sanin farkon da ta mishi kafin yaje india dan iyayi da kinibibi ne,to bari yanzu da yaje india....

Kasa kwanciyar tayi, tunanin abinda zata yi ma malama Haulat ta shiga yi, wani guntun murmushi tayi dan ta gano abinda zata mata , gajiya da zama ita kaɗai tayi ta sauƙo falo.

Ba Kowa a falon ,har zata ɗakin Hajiya sai kuma ta fasa ta dawo ta zauna.

"Banza dabba daƙiƙiya mara hankali"
Runtse idanuwanta tayi tuno zafafan maganganun da malama haulat ke gaya mata.

Bata san lokacin da hawaye suka ƙankaro mata ba,sai jin su tayi ,ƙasa share su tayi dan takaici a fili ta ce "Wallahi sai kin biya,baki san waye ƴar aljanna ba,bana yafiya kuma ba zan yafe miki.

Wani irin hamshakin ƙamshi hancin ta ya ji,wanda saida ta lumshe ido tai wata irin ajiyar zuciya ,ɗago da manyan idanuwanta tayi dan ganin wanda ƙamshin ke tashi a jikin shi.

Waw masha allah ,allah yayi halitta wanda duk wanda yai arba da ita saiya ɗan tsorata dan tsabar kyau,kyakykyawa ne first class ga kwarji ni irin na jaruman maza ga izza,abin kamar a novel,fari ne sul mai yalwar gashin kai da na ido da na gira,ga dugon hanci kamar na indiyawa,duk da fuskarshi a murtuke take amma saida kyawun shi ya fito

Tsaye yake a kofar falon hannuwan shi gaba ɗayan su ya rungume su a ƙirjin shi,fuskar nan a murtike sai yatsinata yake yi ,kamar wanda ya shigo bola.

Tun kallon farko da Sabreen ta mishi ta gane shi,ganin yadda yake yatsina fuska yasa ta kau da kai ,ta ƙara gyara zaman ta rimot ta ɗauka ta chanja tasha ta kuma ƙara bulum,ta gafen ido take kallon shi yakai saƙonni a tsaye a gurin kafin ya fara tawo wa,wani ƙululon takaici ya kamata,Sabreen ta tsana mutum mai iyayi da kilibibi.

Dan guntun tsaki ta ja,ta cigaba da kallon tivi abinta.
Har tsakiyar falon ya iso,kallon ta yayi yana mamaki hali irin ta,wanda zai kira da rashin tarbiyya,bai ce mata komai ba ya samu guri ya zauna yana wani yatsina fuska haɗe da hura ɗan karamin hancin ta,yana kuma taɓe ƙaramin bakin shi,ni dai kuwa kallon shi kawai nake yi ina murmushi dan abin ya mishi kyau.

Ganin bata da niyyar mishi magana gashi yana sauri yasa ya kalle ta a hankali cikin wata irin murya wacce zamu kira da ƴan kilibibi ya ce "Sabreen plss go call hajiya for me"

Da sauri ya juyo tana kallon shi bata san lokacin da wata irin muguwar dariya ta kubuce mata ba,"Bala'i yau ga wanda yafi malam haulat bala'i to ikon allah "
A zuciyarta tayi maganar ta kuma ƙasa daina dariyar.

Wani irin kallo ya bita da shi yana yamutsa fuska haɗe da taɓe baki,cikin wani irin ƙaƙale ya ƙara ce mata "What Rong with you"

Haba ai sai ta ƙara fashewa da wata muguwar dariya harda hawaye dariya dariya kamar ba zata daina ba,idan zata daina sai ta ƙara tunowa ta ƙara kwacewa da dariya.

"Ƴar aljanna dariyar me kike yi haka ,lafiya?

Hajiya ta faɗa lokacin da ta shigo falon gurinta ta ƙarasa,ɗagowan da tayi ta ganshi ,ta washe baki ta ce "Ƴan india ne a gidan yaushe ka shigo"

Saida ya yamutsa fuska kamar wanda ke jin wari ko wanda yake kallon kashi ya ce "Ɗazun ne"

Haba ai wata irin dariya ta ƙara fashewa da ita har saida ta faɗo daga kan kujerar dan tsabar dariya.

"Waiyo ni Sabreen hausar ma ba za'a barta ba"

A zuciyar ta faɗa,ita kuwa Hajia ruɗewa tayi dan ganin irin dariyar da Sabreen ke yi.

"Waiyo Allah na bani ƴar aljnna"

*Naufal* hajia ta kira shi, ka taimaka ka kira likita"

"u mean doctor"

Ba Sabreen ba ni kaina saida na dara dan yadda ya ƙira doctor ɗin,mugun ɗan ƙaƙale ne,dan abin dashi ya wuce iyawa ya koma kaƙale,kamar yadda ake fitar da harafin larabci haka yake fitar da kowanne harafi harda ƙari ma.

Kuka hajia ta fara "Waiyo na shiga ukku ni yau"

Ganin hajia na ƙara ruɗewa yasa ta fara kukarin tsaida dariyar amma ta kasa,saida ƙyar da sassauta dariyar ta kalli hajia ta ce "Waiyo hajia ta ba komai lafiya ta lau dariya ne Kawai"

Shi kuwa Naufal yana gefe yana kallon su dan bai gane shi take yiwa dariya ba,dan shi a nashi ganin baiyi abin dariya ba,kallon mahaukaciya yake mata.

"Jajia bari na tafi ana jira na"

yadda ya ke kiran sunan hajiyar ma abin a dara ne,dan mugun ɗan ƙakale ne na ƙarshe.

Kasa ɗaurewa Sabreen tayi haba ai sai ta cigaba da dariyar.

"To mutun india ka gaida hajiyar ku ,zamu shigo da daddare mu amshi tsarabar mu"

"Okkk hajia sai kun zo"

Kamar wanda ba bahaushe ba haka yake hausar.

Yana gama faɗa yabar falon yana tafiya cikin ƙasaita da izza tafiyar ma abin kallo ce,da ana karatun iya tafiya da sai na ce ,yayi digiri gurin iyawa.

Da ƙyar sabreen ta iya tsaida dariyar ta"Hajia ta wai ke ba ki ji abinda da nake yiwa dariya ba"

"Yo ina zan ji ni tsoro ma kika ban"

"Wancam ɗan indian ne yaban dariya ji yadda yake magana kamar shi ya kawo magana duniya u mean doctor"

ta maimaita abinda ya faɗa ta irin yadda yayi maganar.

Dariya ita ma hajiyar tayi ta ce "kin san daga india yake shiyasa"

"Su ƴan indian haka su ke,ƙilibibi ne na bala'i,kai bari n Je nayi wanka dan jikina duk ya mutu .

"Ba dole ba irin wanan mahaukaciyar dariya ai dole jiki ya mutu"

hajiar na gama maganar ta haye sama tana dariya da mamaki dan bata taɓa tunanin za'a samu wanda yafi malama haulat iyayi da ƙilibibi ba...

~~~~~~~~~~~~~

Zaune take a tankameman falon wanda yasha fentin pink da fari haka zalika komai na cikin falon kujeru da flowers da sauran kayan alatun rayuwa.

Fuskar nan tata dauke take da annuri wanda nake ganin kamar haka halitta yake wato smile face akan 2 sitter take zaune,ita ma karya kyakykyawace ga murmushi, babba mace ce mai halin girma.

A gafe guda kuwa Wata kyakykyawar yarinyace ko na ce budurwa wacce shekarun ta ba sufi goma sha takwas ba, tun kallo na farko na gane suna da alaka da matar nan dan irin Yadda suke gama.

Cikin siririyar murya ta kalli matar ta ce "Momy nifa na ƙagara naga tsarabar da yaya Naufal ya kawo min,wai ina ma yaje ne daga zuwan shi"

Murmushi tayi wanda ya ƙara baiyana zatin fuskarta ta ce "ke kuwa *farrah* kina da gajin hakuri kuma kin san halin Naufal baya son damuwa idan kika nuna mishi kin zaƙu ya hanaki,ya je gurin Hajia ya gaida ta"

Taɓa fuska tayi ,bata ƙara cewa komai ba,da juya ta fuskanci tivi.

"Assalamu alaikum ya faɗa a hankali ita kanta sallamar kamar da turanci yayi na ce da Sabreen nan hhh da tasha dariya.

A tare suka amsa mishi kowanne su fuska ɗauke da Annuri ,Farrah ce ta fara magana "Yaya ka dawo"

cikin yatsine ya ɗaga mata kai bai ce komai ba.

Ita kanta farrah bata son hali irin na shi ga rashin kula mutum ga sharewa ga yatsine.

"Naufal ya hajiar"

"Tana lafiya tana gaida ke wai anjima zata shigo"

Yana faɗa ya tashi cikin yauƙi yabar falon.

"Allah momy yaya ya ƙara Chanjawa daa da ɗan sauki ,amma yanzu tunda ya dawo abin ya ƙaru"

Murmushi momyn tayi dan nasan gaskiya farrah ta gaya mata.

~~~~~~~~~~~~~

Cikin shigar doguwar jira ƙirar dubai ta ke baƙa ce rigar ta matuƙar amsar jikin ta kamar dan ita aka yi rigar,rolling tayi da ɗan ƙaramin gyalen waw,masha allah *Sabreen* kyakykyawa ba wani haske gare ta ba,amma akwai kyau kamar me,ɗan karamin bakin ta wanda yake kamar an zana shi,shi ke ƙara fidda kyawun ta,hancinta dogo ne amma ba siriri ba ne tana da cikar fuska ga fararen haƙora da ido gata da yalwar gashin gira da na ido ,ga iya murmushi hmmm abin dai sai wanda ya gani dan kamar a novel lolx to meye wanan..

🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀yehh yanzu zan fara.

ga me bukatar shiga grp ɗin 08155184562

comment
shire
✅ote me on wattpad@fatimaumarmoddibo

~Bhartoolerty~
[12/6, 9:38 AM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: _ 🇵σѕт 🇧у 🇬яσυρ 🇴 🇫 🇭уρє 🇭αυѕα 🇳σνєℓѕ 🇧σσк 🇼нαтѕαρρ 08064400100_ 📚📚
[12/9, 1:05 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: 🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹


*By*
*fatima* *Batula*

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

Page 2

.......................................
Cikin yanga ta ƙara su falon tana murmushi ta ƙagara gobe tayi,dan taje makaranta ta rama abunda Malama Haulat tayi mata.

"Kai masha Allah ƴar Aljanna kinga yadda kike da kyau kuwa "
Hajiya ta faɗa tana kallon Sabreen ɗin.

Washe baki tayi ta ce"Hajiya ta ai ke na biyo shiyasa nayi kyau"

Ƙarasawa gurin Hajiyar tayi fuskan nan tata ɗauke da annuri, kan jikinta Hajiyar ta kwanta.

"To tashi muje tunda kin shirya"

Murmushi tayi tuno Gidan su Naufal zasu je,wanda ba wani tazara a tsakanin su dan a layi ɗaya suke.

"To muje ta faɗa haɗe da tashi ta fita gurin direba ta nufa ,yana ganinta ya taso a ruɗe.

"Kai kaji dai abinda na gaya maka,wallah inda aka samu matsala kasan abinda zan ma ba zai na gayama ba,da zaran ka ga kira na goben sai ka shirya,kasan yadda zaka yi da mai gadin makarantar ka kul....

"Ya dai lafiya ko wani abun ya miki ne" faɗar Hajia.

"A'a ba abinda ya min ,muje ko"

Buɗe musu motar yayi suka shiga,ba wani lokaci suka ɗauka ba dan daman duk a layi ɗaya ne.

Baban Gida ne mai ɗan karan kyau amma bai kai na su.

Hajiyar Gidan da farrah suna zaune a falo suka isa cikin falon.

Ba wanda Sabreen take jin kunya a rayuwarta sama da iyayen Naufal musamman hajiyar shi.

Har kasa da duƙa a gaban ta ce "Ina wuni momy ya gida"

Fuska ɗauke da annuri ta kalle ta ce mata" Lafiya lau Sabreen ya makarantar baki son zuwa gidan nan bansan abinda aka miki ba"

Ita murmushin tay ta ce "Ba komai momy zan dunga zuwa"

"Yawwa ko kefa ƴar gatan hajia"

Dukkan su suka yi murmushi,momy ta gaida hajia cikin martabawa da mutuntawa.
Inda farrah take nan Sabreen da zauna suna shiri da ita sosai ɗan farrah bata da iyayi da nuna iyawa da alfahari da gadara shiyasa suke shiru sosai da ita.

Hajia ta kalli Momy ta ce "Wai ina mutan india ne,ya zo ya bamu tsarabar mu "

"Sun fita tare da Alhaji amma yanzu zasu dawo tunda yasan da zuwan ku"

"To allah ya kawo su "

"allah yasa kar nayi dariya" sabreen ke faɗi a zuciyar ta.

Basu wani jimaba sai ga sunan ,Alhaji babban mutum ne kallo ɗaya zaka mishi ka fahimce hakan ga Annurin fuskar ko da yaushe kamar yana murmushi haka fuskarshi take irin ta hajia.

Da sallam suka iso falon,Shi Naufal ba wanda yaji tashi sallamar dan bala'i irin nashi.

Kan kujerar da Hajia ke zaune a nan Alhaji ya Zauna fuskan nan tashi ɗauke da murmushi
"Sabreen zo nan Alhajin ya kirata.

Cikin jin kunya ta taso kasa da tsugunna,yasa hannu ta ɗago ta ya zaunar da ita kan cinyar shi.

Wani gululun takaici ya kama Naufal "Duk kun lalata yarinya da gata sai abinda ta ke so ake yi ba dole ta lalace da dinga yiwa mutane fitsara ba,kamar wanan katowar yarinyar zaka zaunar da ita kan jikin ka "

Duk a zuciyar shi yake wanan bambamin yana wani yatsina fuska kamar wanda ke kallon ɗanyan kashi.

"Sabreen ya gida ya makaranta?

"Lafiya lau dady"

"Masha allah Sabreen ki dage kinji,yanzu tunda ga yayan ku ya dawo kafin ya fara Aiki zai ɗinga zuwa har gida yana miki lesson"

Dumm Dumm gaban shi yai mugun faduwa,"shi xai ɗinga yiwa ƴar rainin wayun nan lesson kuma sanan shi zai bita har gida bama ita zata zo ba" a zuciya yake wanan tunanin dan baya gardama da dadyn shi.

"Aiki ja wanan ba zai
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment