You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
shi makarantar isalamic yake, amman nisan da yake dashi ya hana hakan, sai dai yanxun yana tunanin zai hadasu da ummeetah ne yakai su, yayi dan murmushin a a hankali yake furta kalman,,
Humaira, ya dan noke fuska yana hangota cikin kyakyawan dresing dinta, ya rasa me yasa ita ko wani shiga tayi kyau yake mat........., wayarsa ne ya katse mai tunani dake ringing, ije bisa seat din dake gefenshi, DR. khamis shine abin da ya gani a rubuce, da murmushi ya daga wayar yana fadin,,
yah mutumin?shima daga can bangaren yake fadin,,
mutumin kai dai bari, yanxun naje gidan ka nayi tsintuwar wata fulani girl, babyn ta yifa......, karan cijewan mota ne ya katse maganar nashi, yana faman fadin,,
mutumin ya dai lafia?, daker ya saisaita kan steery yana tattaro dukkan natsuwarsa, tuni annurin dake fuskanshi ya dauke yana fadin,,
lafia, kace mene?ajiyar zuciya DR. khamis yayi da cigaba da fadin,,
watar yer fulani na gani a gidan ka, ko sistern kace?ya dan kakalo murmushi da fadin,,
ummm, meya faru?daga can bangaren DR. khamis ke fadin,,
kai mutumin ina fada maka da magana a bakina sosai, jinjina kai yayi da fadin,,
haba mutumin, mijin wata ga engagement dake kanka, yayi dan tsaki da fadin,,
kabar wannan maganar, nie mijin mace hudu nefa, musamman da yarinyan ta shiga rain.........,,
kaga yanxun ina driving ne, ka bari koma menene na dawo zamu tattauna, ya karisa maganar yana cijewa, sosai abin ke masa zafi, shi yasa ya katseshi, haka sukai sallama kowa ya ije wayar, murmushin takaici kawai yakeyi da faman jera tsaki.
Ranshi be kuma baci ba, sai daya koma gidan, ganinta cikin wannan suturar, daker ya iya amsa sannu da zuwan da take mishi, ya wuce daki rai bace da faman ayyana,,
yanxun a haka khamis yaxo ya gan......, bai karisa ba yaja tsaki yana ije briefcase dinshi da kuma ayyana,,
toh kai ina ruwanka, ka wani damu, ko ka sanja ra'ayin da kayi niyya ne, ka dai san zaman da yer yarinyan can bashi cikin tsarinka, sannan meye laifin khamis donya nuna yana sonta, nagartaccen mutum kamarsa, kayi tunani bashi da wani mugun hali,,
hakane kuma, ya fada da son kauda zancan a zuciyarsa, yana son cire duk wani damuwa.
sai dai me, harya futo don yin lunch, abin na damunsa, ya lumshe ido komai yakeyi ransa bace, ya rasa gane kanshi,,
sanda yakai spoon daya bakinsa, daci yaji abincin na masa, yayi tsaki yana ije spoon din, kalaman DR khamis kawai yake tunawa, wani dogon tsaki yaja yana bude idanunsa, dai dai sanda ta futo daga kitchen din, idanun suka hada, tayi saurin kauda nata, ganin a irin yanayin daya dowo gidan yau, tana shirin rabawa ta wuce, taji muryansa na fadin,,
ke zonan kiban ruwa, jiki a sanyaye ta iso wajen, glass cup taja tana daukan jug cikin natsuwa, ta dan rankwafa tana zuba mai ruwan, yayin da kirjinta ke cigaba da dukan uku uku,,
idanu ya samu kanshi da zuba mata, yana kishingida jikin dinning chair din, hannayensa rungume a kirji, sanye take da black dankwalin data daura bisa ka, yayin data sakalo da ko wani both side, suka sauko ta saman kagafadarta, kitson kalaban data ziraro dasu ta gabane suke ta faman lilo, bakin nan yaji wet lips sai kyalli yake, yaja wani tsaki da kuma raya,,
amma yarinyan nan ta cuceni data futan ma khamis a haka, wani tsakin ya kuma jaa, yana kauda kansa gafe, dai dai sanda ta kammala zuba mishi ruwan tana dan mika mai gabanshi, cak ya rike hannunta, a razane ta dago, be ko kalleta ba yake fadin,,
zauna nan muyi magana, ba musu ta zauna kujeran dake kusa da nashi, gabanta na luguden fadi, ya cika mata hannun, so serious yake fadin,,
ummeetah ina daukanki mai hankali, a haka kika futan ma wani kato, har da zama kuna hira, da auren nawa......, cak ya tsaya da maganan a tare kirjinsu yace wani rassss, ya dan kauda kai da raya,,
sadeeq me kake shirin a'ikatawa, itakam zaro ido tayi, tana marairaicewa da fadin,,
kato kuma?da sauri ya dago idanu da mamakin amsar data bashi, duk tunaninsa maganarsa na karshen ya kamata tafi bama hankali, ta cigaba da fadin,,
wayyo Baffah, wannan bakon naka ko?Allah ka tambayeshi, da hijjab dina na futa, kuma bakin kofa ne, nie ba muyi hira ba, wani ajiyar zuciya ya sauke da raya,,
thank god da bata jiba, gefe daya kuma yana jin dadi, daya kasance ta rufe jikinta, amman saiya kuma daurewa da fadin,,
toh in ba kuyi hira ba, ya akayi yasan ke fulani girl ce? dan shiru tayi kafun tace,,
oh, kasan rapper nah ya kalla, ya tambayeni, shine nie kuma na bashi amsa da eh, amman inna yie laifi, na bata maka rai, don Allah kayi hakuri, sai yanxun yaji wani dan sassauci kuncin dake zuciyarsa, ya dan basar da fadin,,
nie nace kinmun laifi ne?cikin ladabi tace,,
a'ah, kawai dai duk d'a nagari ba zaiso yaga iyayanshi sunyi fushi dashi ba, kunyace ta dan kamashi, yanda ya zake yana nuna zallar kishinsa, harda son yin katobara, toh me yake damunsa ne wai? wannan shine tambaryar dayai ma kanshi, ya dan hada rai yana cigab da cin abincinsa, tsam ta mike zata bar wajen, yace,,
zauna, waya baki damar tafiya, ba musu ta koma ta zauna, ya cigaba da cin abincinsa hankali kwance, sai daya kammala ya sha ruwa, tare dayin hamdala, ta gefen ido yake kallonta, kanta a kasa tana wasa da yen yatsunta, kafun ya fuskanceta sosai, a sanyaye ya kira sunanta ta dago kai, yana cigaba da fadin,,
kin gane, bana so kina hulda da mutanan da baki sansu bane, musamman nan da kie sabuwa a wajen, kinga baki gama sani mutanan wajen ba, shi yasa nake son ki rika lura da kyau, da fatan kin fahimta, kanta ta daga sama da fadin,,
eh, in sha Allahu zan kiyaye, dan murmushi yayi da fadin,,
good, ta cigaba da fadin,,
amma Baffah a'ishi uncle khamis yana da fara'arsa sosai, ta karisa maganar da murmushinta daure fuska yayi yana kallonta da wani kallan tunani, kawai saiya samu kanshi da kushe yana fadin,,
excuse maa, waya fada miki daga fara'ar mutum ake gane halayyansa, jiki a sanyaye take fadin,,
oh, amma nie sai naga kamar yana da kirk........., tsit tayi da bakinta, dalilin kallon daya jefo mota, yana kuma wani hada fuska, dai dai sanda taji horn din motar matarsa, alamu yau an dawo da wuri, tsam ta mike cikin natsuwa, tana kokarin barin wajen, murmushi ya saki, dama wannan hirar nata ya isheshi, idanunsa a kanta yake fadin,,
yadai kika mike, kie zauna ki cigaba da bayanin naki mana, ko juyowa bata yiba ta wuce bedroom dinta, da wani murmushin ya bita da ido harta shige, ya lura tana da gudun abin tashin hankali, shiru kuma yayi da wani tunani, besan me yasa ta waske ma subutul kalam din da yayi ba, sai yake tunanin kaman taji abin daya fada,,
amma me yasa ba tace komai ba?ya tambayi kanshi cikin wani irin cool voice, dai dai sanda matarsa ta shigo falon a yakice, alama duk ta gaji, jaka a hannu sai wasu takardu a dayan hannun, ta kariso da annuri a fuskanta.
comment
share
vote
*matatace 2019*
Na meemartjj
[14/08, 14:29] Dala Grp: 🕯🕯🕯
*MATATACE*
🕯🕯🕯
story&written by
Haleematu💕meemartjj💕
wattpad@Meemartjj
*Dedicated to swt sisters*
_Aunty Jamee, aunty Ummeetah and my Fa'ixation._
page 35~36
_________ kujeran da ummeetah ta mike ta koma ta zauna da fadin,,
Hi sweetheart, idanu kawai ya zuba mata, ya lura zuwanta kasan nan ya taimaka wajen lalata abubbuwa da yawa, kafun yayi murmushi yana jera mata cikakken sallama, daga gira sama tayi da fadin,,
hmm umm, sannunka da a'iki, nie ina zan iya jero wadannan kalaman, ta karisa maganan tana bude warmers din abinci, yayin da yake fadin,,
angel shifa a'ikin lada baya kadan, idanu ta zuba mai yana cigaba da fadin,,
yess, bcos ko wani kalma kika fada lada goma ake baki, sai kie lissafa kie gani, keda kika fada kin samu lada 30, nie kuma dana amsa miki nima na samu ladan, zakuda kafada tayi da fadin,,
hmmm, yhu won't understand, swthrt na gaji da yawa yau dinnan, yace,,
naga alama, kina kokari a'i, dan dariya tayi da mika mishi wata takarda tana fadin,,
ka gani, promotion sheet dina ne,,
wow, ya fada da amsar takardan yana kallo, kafun ya cigaba da fadin,,
Allah ya sanya alkhairi, a'ikin cancanci hakan, lura da yanda kika bashi muhimmaci fiye da komai, ta lura tsokanarta yake da wayau, don haka ta basar da maganan tana fadin,,
kaga swthrt nie yunwa nakeji ko zan samu abinci, da ido y a nuna mata kayan abinci dake wajen, ta wani bata fuska tana fadin,,
no, nie kai zaja bani, sai da yayi murmushi, kafun ya zuba mata wani sabo, a baki ya rika bata, harta kammala cinyewa, sannan ya zuba ruwa a cup shima ya bata, takai hannu zata zari tissue paper na goge baki dake wajen, da sauri ya rike hannunta, sakar mai tayi ya dauka yana fadin,,
kie bari in karisa ladana, banda blushing ba abin da takeyi, kawai sai ta samu kanta da zuba mai ido, a zuciya tana raya,,
tabbas tana tsananin son mijinta, wanda bata san iya kan shiba, cikin natsuwa mai cike da soyayya ya kammala goge mata baki da fadin,,
ouk now say Alhamdulillah,,
Alhamdulillah, ta fada tana wani farr da ido, kafun ta mike tana fadin,,
bari kuma naje na dan watsa ruwa, harta juya yayi saurin fadin,,
yawwa, angel plss ina so kiyi mana list din duk wani abu da muke da bukata, na ramadan da yake zuwa, kinga sai mu shiga super market muyo siyyaiyan ko?a yastine ta juyo tana fadin,,
ummm, gaskiya abubbuwa sun mun yawa, but why not kasa yarinyan can ummeetah tayi list din komai da komai, nasan zata iya, inya soma ko tare sai kuje don siyyaiyan yafi maka sauki, daga haka ta juya tabar wajen,,
shiru kawai yayi, yana tuna gidan DR. khamis jiya daya shiga, matarsa na zaune rike da joter da pen tana lissafa kayayyakin girki, yayin dashi ke zaune bisa hannun kujeran da take zaune, tana nunnuna mishi da mishi bayani, tare da maganan su kasa kasa, haka ya shiga gidan ya samesu, sai yaji sun burgeshi, yai dan tsaki yana kawar da zancan, tare da mikewa shima ya shiga ciki.
*NAIJA, KD*
£££
A falon mahaifyar yake zaune yana faman ciccika, shifa tunda ummeetah tabar kasan ya matsa shima zai koma abroad, inda ya futo ya cigaba da karatunshi, rigima kullum yake ma mahaifyar tasu, ita kuma tana lallaba Abban sune ya yarda tukuna,,
yanxun haka zaune take tana waya yana faman tsula rashin mutuncinsa, ta dago ta kallesa da fadin,,
muheet kaga don Allah ka bari inji me ake cemun a waya, waya fah nake ko baka ganine, daga haka ta danja tsaki tana cigaba da fadin,,
eh daughter ina jinki, daga can bangaren suhymah take fadin,,
aunty don Allah karki bar munat ta auri Abdullah, saboda muna good time da sakeena, baxan jie dadi ba ace yer uwata itace kishiyarta, tunda ba masoyan ta rasa ba, ta zaba daya ciki, ko abokin daddynmu dake sonta, Alh Ribado, ta hakura dashi tunda in kudinnanne ma ya tara, ajiyar zuciya mummy ta saki da fadin,,
hmm daughter gaskiyanki, inaji haka kawai za ayi, dama ina son ranan dazan nuna mata nie na haifeta ba haj. indo ba, to tabbas anxo wajan, da sauri tace,,
yawwa my aunty, Allah ba kiji yanda naji ba da sadeeq yake waya da Abdullah, kai namiji bashi da rukan amana, duk soyayyar da sakeena take ma Abdullah, yace haka zai mata, plss&plss aunty do this for me, itama munat din zan kirata muyi maganan, tace,,
ba matsala, dole zan tursasa mata, hope dai lamura nan wajanki suna tafiya yanda ya kamata?, yer dariya tayi da fadin,,
my aunty karki damu, komai na tafiya normal, na kara dora shi akan wani network dinma, ta numfasa da fadin,,
good haka ake so, ki cigaba dayi yanda ya kamata, daga nan suka cigaba da yen kulle kullensu, kafun suyi sallama suna ije wayar, muheet yasa ihu da fadin,
mummy ina magana kina wayaaaa, nifa na ce miki na gaji da zaman kasan nan, sai data toshe kunnuwanta tana fadin,,
muheet zaka fasa mun kunnine, nace ka bari inma Abbanku magana mana, inka kwantar da hankalinka komai zai tafi yanda muke so, turo baki yayi dai dai sanda munat ta shigo da kaya niki niki, tare da kaninta muneeb yana binta da wasu a baya, bisa kujera ta zauna tana blushing da kallon mummyn nasu, dake yatsina fuska tana fadin,,
wannan fa?da murnanta take fadin,,
Abdullah ne ya kawo mana kaya nida su sisters, daga nan ta shiga kwalla musu kira, ko wacce ta futo kai na rawa ana murna ana daga kayan, jefi jefi take kallon mummyn dake bin kayan da harara, kafun tace,,
shi kayan axumin da naga ana saukesu sashin haj. ido fa?a sanyaye tace,,
shine ya a'ika dasu can kawai, amman za'a kawo nan, tsaki taja da tabe baki tana fadin,,
dole mana ya a'ika dasu can, tunda kin nuna mishi itace ta haifeki ba niba, shiru kawai munat tayi don ta lura akwai wata a kasa.
***
sanye da wata amy green din yadi ya futo, mai santsi da kyalli, dikin kananun kaftain, karamin riga mai gajeran hannu, sai kamshinsa na yau da kullum yake, wanna karon tunda aka fara azumi yake wani tashen kiba, jin dadi ya zauna a jikinsa sosai, yayin da ummeetah ke kashesu da kalolin dadadan abincinta,,
madam ma anyi wata uwar kiba, bare yanxun kuma da aka samu ciki, nan aka kuma narkewa, azumin ma ijewa tayi, lokacin daya koma kaman wani mai a'ikacinta, lallami da tarairaya ba wanda bata gani, duk da ba wani laulayi na azo a gani takeyi ba, yanda ummeetah ta lura gaba dayansu suna matukar son cikin nan, musamman shi da taga yana faman rawan kai, kaman basu taba haihuwa ba,,
a haka sallah ke gabatosu, yau kusan saura five days, ya futo yana son su futa wani siyyaiya ne, amman madam dai, ba abin da bata iya complain akai ba, yauma tana can daki ta kudundune cikin blanket, wai babynshi ke damunta, suje kawai shida Irfan, in yaso ummeetah taje ta ruko musu kaya,,
da dan tsaki yake zama bisa kujeran dake falon, yana harde kafa daya kan daya, ya ciro wayansa yana daddannawa, lokaci lokaci kuma yana kallon sashin dakin ummeetah don yana son su futa da wuri ne,,
can sai gasu sun futo Irfan a guje, ita kuma tana rike da wani dan cute kumb dinshi, cikin saitin na gyaran kanshine, saman kujeran ya dade yana faman tsalla akai yana dariya, ta kariso da fadin,,
Irfan zo mana in kammala shiryaka, kokarin sake guduwa yakeyi ta cafkoshi, yana dariya itama tana yie, ta zube gwiwowinta bisa kasan kujeran, tana jawo shi kasa, kallonsa take da fara taje mai yer sumar dake kanshi mai laushi irin na babanshi, da wani big smile take fadin,,
baka so na gyara maka yayie kuyau, in maka irin na uncle........., kumb dinne ya fadi kasa ta duka dauka, cak ya tsaya da danna wayar da yakeyi, yana son yajie wa za tace, ta cigaba da taje mai tana dan dariya da fadin,,
yawwa, bara na maka shi mai kyau, irin na uncle khamis, kana so k......, bata karisa ba ta tsaya da maganar ta cak, tana zaro ido waje, sakamakon jin wayar dake hannunsa a kasa fasssss, ya fadi,,
tswssssssss, shine dogon tsokin daya ja, ya dan runtse ido, wani abu mai zafi ke waiwayi a zuciyarsa,da dayan hannunsa yake murza zoben azurfan dake dayan hannun, can kuma ya bude ido, yana numfasawa da kirjinsa dake buga sautin lub dub, ya duka ya dakko wayar, yama kasa kallo, don yasan tabbas baxai rasa fashewa ba, lumshe idanu kawai yayi da kishingida bayansa jikin kujera,,
khamis khamis khamis, tunda suka hadu, bata da wani magana sai nashi, shima nashi bangaren duk ya isheshi da zancen fulani girl, lallai ya kamata ya sa musu birki, jie yayi ta kamo wani dogon zancen, da faman kiran sunan abokin nasa, kuma makwabcinsa, ya sashi jan wata doguwar tsakin yana bude idonsa a kansu, wannan yasa duk suka juyo suna kalonshi,,
come on, malama inkin kammala yawan surutun kije ki shirya zamu futa ne, ya karisa maganan cikin sanyi, da murnanta ta mike ta nufi daki, don tunda taxo so daya aka taba futa da ita, randa su kaje siyyaiyan kayan axumi wani super market, sai kuwa yau, ko bakomai taba ido abinci, Irfan ya kariso da gudu yana fadin,,
daddy nima zanje, sosai ya daurashi a jikinsa yana fadin,,
ouk my boy, tare da zuba ma gashin Irfan din idanu, sak kuwa shigen na khamis dinne ta mishi, da yike shima fulani ne, yai dan tsaki ga mamakinsa, sai ya samu kanshi da bin sumar dan nashi da harara, kafun yasa hannu yana mummutsuke gyaran kan yaron dake fadin,,
daddy zaka bata mun abina, murmushin yake yayie da fadin,,
a'ah, zan gyara maka ne, sai da yaga wacan ya bace sannan ya sauke ajiyar zuciya, ta futo sanye da black arebain jallabiya, mai bubu shape, wanda yaji adon duwatsu golden, baima taba ganinta dashi ba, yayi mata kyau gashi ta kuma cika, duk da abayace, bai hana kerarran dirin jikinta futowa ba, ta yafo wani golden viel dayin mopular, kamar zai magana kuma saiya fasa, suka wuce suka futa.
Haka suka tafi, yayin da ummeetah ke gidan gaba, Irfan na baya yana nuna mata wasu wajajen dake cikin birinin worshin town din, wakan yusuf islam, i look i look, ke tashi so cool a cikin motar, sabanin wacan tafiyar da aka cika musu motar da wani english song, na wata yer nigeria, yanda ta lura yana son jin wake wake, ita dai ta cigaba da kalle kallenta, har suka isa wani katon shopping mall,,
ta rude sosai da irin kayan dake wajen, Irfan aka shiga zaba ma sutura, har mamaki takeyi yanda yake dibar ma yaron kaya kamar hauka, shiko sai murna yakeyi, da baban ya zaba mishi kaya, idan ya gani sai yace be mishi ba, idan ummeetah tace kuma sai yace nata yake so,,
abin ya koma gasa, kowa nasan ya zaba mishi wanda zaice yafi mishi kyau, yayin daya zabi kayan da ummeetah ta daukan mai fiye dana babanshi, sai hararansu yake da murmushi, kafun ya shiga dibar ma matarshi,,
ke baki son daukan komai ne?ya fada bayan ya kare ma matarsa nata siyyaiyan, cikin sanyi tace,,
a'ah, nagode nie ina da kaya nah, wata uwar harara ya zabga mata da fadin,,
oh muma sai akace miki suturar muka rasa, yasa muka xo siya ko?, inace kece mai shirya mana kayan cikin wardrobe, sosai maganan ya mata zafi, nan da nan ta hada fuska muryanta har yana dan rawa da fadin,,
a'ah, Baffah kayi hakuri, amman nagode, bana da ra'ayin daukan komai ne, jikin sane yayi sanyi, idanunta harsun tara kwall,,
oh my god, ka bata mata rai fa, ya ayyana hakan, da shiga cikin wani damuwa, Irfan ya kalla da fadin,,
Irfan tunda auntyn ka ta zaba maka kaya, kaima ya kamata ka zaba mata ko?kai ya daga da fadin,,
yess daddy, hannunta yaja yana nuna mata wasu wajen da tsawanshi baxai kaiba, ita dai dauka kawai takeyi, yayin da shima ya zaba mata kaya masu kyau, ko wanne ya kwaso mata sai taga dai dai da ra'ayin tane, sunyi siyyaiya sosai, lokacin da suka zaga ko wani bangare, haka suka kammala siyayyansu cikin farin ciki, su kaje ya biya duka kudin kayan, tare dayo kayan ledoji.
dai dai entrance din wajen su kayi karo da DR. khamis da yaranshi biyu sun shigo wajen, da gudunsu suka kariso suna rungume uncle sadeeq, ya daddaga su sama yana saukesu da musu wasa, kafun ya karisa wajen abokin nashi daya tsaya cak yana kare ma ummeetah kallo, dan kafadarsa ya bubbuga da fadin,,
hello, kallonsa ya dawo dashi gareshi, yana wani murmushin yake, kasancewan ya kare mishi ita baya ganinta yanxun, sai kuma ya dan rankwafar da kanshi, ya lekata ya dago ya kalli sadeeq, sai da yayi haka sau uku, kafun ya dan nunata da dan yatsa yana kallonshi da fadin,,
wait, wacan a'i fulani girl dina ce right?shiru sadeeq yayi mishi, da zufan dake neman rufeshi, a zuciya yake raya,,
barawo basai ka sata ba, kafun yayi wata magana, khamis ya wuce gunta kai tsaye yana faman blushing,,
ya salam, ya fada yana dafe kanshi, kafun ya juya yabi bayanshi, kyarere ya tsaya yana kallonsu, dukansu da annurin fuska suke magana cikin yaren fulanci, dama yasanta don son danginta, duk randa tasan shi fulani ne, ba sauki kuma, sai hararanta yake amman bata san yana yi bama, dai dai nan matarsa data tsaya kulle mota ta kariso wajen, da sadeeq suka hada ido suna gaisawa da tambayar,,
a'ah mutumiyar bata biyo kuba, da dan murmushin yake, yake fadin,,
a'iko bata jin dadine, shiyasa bamu shigo tare ba, ya karisa maganan yana dan tabo kafadar khamis daya bada hankali wajen ummeetah, ita kuma matarsa na kallonsa da wani tuhuma, shikam sai janye kafadarsa yake, tace,,
Allah sarki, my regard to her plss,,
in sha Allah, ya fada yana cire hannunsa a kafadar khamis, ta kalli yaranta da fadin,,
misha, Easha muje ko?sai lokacin ya dago da nuna alamar ashe kin shigo, sukai sallama dasu sadeeq tana fadin,,
bari muma mu shiga muyi namu siyyaiyan, yayin da gogan yaxo dai dai kunnin sadeeq yana rada mishi magana, kerere kawai sadeeq yayi da mamakinsa, sai murmushima ya kubuce masa, da raya,,
kai khamis da abin dariya kake, ga kuma hadama, kana da wata girl friend kana so, ga kuma wannan itama duk kana s........., tsaki ya samu kanshi da saki, shikam dariya yakeyi da fadin,,
Allah ina fada maka da magana fa mutumin, da wannan suka rabu da juna, yabi ummeetah da kallo data raka uncle khamis din da ido, rayuwanta tana son taga yen uwanta fulani,,
harara ya zabga mata da suka hada ido, a mota kuwa takura mata yayi, kan saita fada mishi abin da suka tattauna da fillanci, dole ta sanar dashi, sunanta kawai ya tambaya, shine shi kuma yace iri dayane da sunan first born dinshi,
ajiyar zuciya ya saki dajin dan dama dama, baya fatan wani alaka ta shiga tsakanin su, yana son yin tunani akan lamarin aurensu, kafun yayi kwafa da kallonta yana fadin,,
ina son wannan ya zama na karshe da zaku hadu, ku sanja language a gaba na, a yishi a harshen da kowa zai gane, idan za kuyi yaren ku, to ku tsaya sai bana wajen, hope kin fahimta da kyau? yana maganan ne cikin wani bacin rai, kai ta daga sama alamar gamsuwa, ya maida hankalinshi sosai bisa titi, yana jan wata doguwar tsaki, da cigaba da driving.
Haka suka isa gida kowa rai bace, ummeetah rike ledoji biyu zata shiga ciki, yayin da shima ya kwaso wasu, harta kai nata ledan kayan daki, ta futo zata nufi dakin Irfan ta futo sabe da gyale a kafada, sai makullin mota a hannu, ja tayi ta tsaya tana tokare ma ummeetah hanyar wucewa, da daura hannu daya bisa kugu, wani kallon tsana take bin yarinyan dashi, dai dai sanda shima ya shigo da kaya a hannu, ya ijesu bisa cushion yana kallon ikon Allah, cikin tsawa take fadin,,
keee uban me ya hadaki da mijin shaakirah, zaro ido tayi waje tana kifkiftawa, da kallon site din da yake, kafun ta maida kan suhymah dake faman zabga mata harara, shi ya rigata magana da cewa,,
madam kaman yaya?a'i ita bata san wata shaakirah ba, ki mata bayani dai da kyau zata fie ganewa, yatsina fuska tayi da fadin,,
hakane bara na kira miki sunan hrtcooler din naki, maybe kya fahimta, meye alakarki da DR khamis mijin neighbour dita?, hawaye ne suka wanke ma ummeetah ido, ta gefen ido yake kallonta, kafun ya nisa, sai yanxun ya gane kwanan zancan,,
kai mata da kishi suke, ya raya yana zama bisa hannun kujera, cikin sanyi yake fadin,,
suhymah ban gane ba, wani irin DR khamis, wani abinne ya faru?ganin haka yasa ta zake wajen fadin,,
ehmana, yanxun ta kirani kunje shopping dinnan maybe kai kana can kana fama da siyyaiya, ita tana can zata janye mata hankalin miji, kasan halin khamis wani jarababbe yake jinshi, banda haka me zaiyi da wannan, usuli mai kyau babu, yana tunanin parent dinshi zasu yarda ya aure house girl ne, yana yaron vice president, shi kanshi daga sanda ya gane yer a'iki......,,
ya isa haka, ya fada yana dakatar da ita, yayin da zuciyarsa ke cigaba da kuna, dukkansu baya son ya ransu ya baci, musamman inya kalli cikin ido ita oganniya, gashi
Book Chapters
Chapter 16
Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43