Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

“Na sani haka dai sai dai nawa yayi kuka,amma wallahi ba zan wahalar da kaina akan wata banza ba, ya d’an kalli mummy yace “Kamar awa za’a bayar Mummy?”
A kaikaice ta ce “Ai da yake ba wata mahashuriyar k’arya za mu yi ba, tunda dai sun fi mu wadatar arziki, don haka sai mu tsaya a matsayinmu saboda haka ina ganin miliyan takwas ma ta Isa.”
Da sauri Hisham ya d’ago kai cikin zare ido ya ce, “Million takwas Mummy? Gaskiya ba zan iya ba, akwai wahalwalu da yawa a gabana, ai na yi ma k’arya sai kace wata y’ar Gold”.

Da sauri Alhaji Hamza ya dakatar da shi ta hanyar d’aga masa hannu ya ce “Ya isheka, mutumin banza kawai, zaka ce wani sai kace y’ar gold, ai k’anwar y’ar gold d’in ce, tunda ubanta ya raini y’arsa da Naira,Ai dama za ka ce haka mana tunda yanzu idonka ya rufe kana son y’ar talakawa,toh bud’e kunnenka da kyau ka jini,ba gidan kananan mutane xaa kai lefen ba, don haka dole ka ba da kud’in ka aka nema, za kace baka da miliyan takwas, to ka ba da miliyan biyar, ni na cika ukun.”
Don dole Hisham ya amsa ya mik’e ya bar wajen zuciyar sa na tuk’uk’in bak’in ciki, wanann shi ake kira k’ara wa mai k’arfi _ k’arfi. Allah na tuba ya raya a ransa. Da na ba da wad’annan mak’udan kud’ad’en a kan wata banzar bidia ba gwara na tara miskinai na raba musu jari ba? Balle ga Abban Sauda da yake cikin yanayin Mai buk’atar a tausaya masa matuk’a,amman babu abinda danginsa suka saka a gabansu sai son zuciya da son a sani, babu mai yin Abu fisabillahi.

Don dole ya turawa mahaifinsa kud’in, bayan ya isheshi da waya ko ba don haka ba yana so ya sake lallab’ar su, su amince masa auren Saudat, zuciyarsa ce ta bashi shawara akan ya je ya samu Inna falmata da zancen, ya san mahaifinsa yana sauraron maganarta,kasancewar tana da abin hannunta.
Inna falmata tana ganin sa ta saki fara’a, tana fad’in “Maraba da angon gobe"
Zuciyar sa ce ta karaya don ya san da k’yar zai samu nasara a gurinta, amman bari ya gwada ya gani.
A kan kujera ya zauna yana fuskantar ta. Bayan ya Mik’a gaisuwa ta kalle shi ta ce “Ya aka yi Hisham? Ko kazo mu tattauna zancen bikin ne? Don d’azu Abbanka ya yimin waya yake sanar da ni na fara shirin tafiya dubai hado laifanka, kai fa naji dad’in wanann zancen ai Hisham ka yi dace da gidan arziki, gidan wadata wanda kowa yanzu burinsa kenan a ce ya auri yar gidan wane, duk cikin y’an uwa ma babu wanda yayi dacen da kayi tabbas ka yi auren nasara kai gaba d’aya rayuwarka ma a cikin nasara take masha Allah......


Zumuncin Zamani (New update)

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.


Typing: fadima Sabi’u Dankaka

(Allah ya baki abinda kike nema duniya da lahira.)


Zuciyar Hisham ta sake k’ullewa da tarin bak’in cikin maganganun Inna falmata. ya ilahi, ayi mutane sam babu Allah a ransu? Dubi dai yanzu duk wadatar da Allah ya bata ammn hangen abun wani take yi, ya kuwa za a yi imani ya ratsa mutum, shi yasa kullum mutane ba sa godewa Allah in dai za ka hango na samanka, yanzu falmata nawa ta fi wadatar amman hangen na wani take.
Ganin Hisham ya yi tsit, hakan ya sa Inna falmata ta gyara zamanta tana kallonsa, tace “Hisham kayi shiru?”
D’ago kai ya yi yace “Bakomai Inna dama wata magana ce ta kawo ni.”
Inna falmata tace “to ina jin ka,ga me da me?”
Hisham ya saki ajiyar zuciya ya ce da man mun yi magana da Abba akan mata biyu nake son na aura.to sam Abba ya k’i ya amince min, kuma na riga na yi alk’awari a gidan su yarinayr, ba nason na zama k’aramin mutum.”
Inna falmata ta gyara zama kafin ta ce "Gaskiya babu dad’i, tunda da dai har ka yi magana a gidansu, ita kuma yarinyar wane ne babanta?”

Hisham ya d’an zunkud’a kafin ya ce "To kin ga Inna abinda nake gaya wa Abba kenan, sam ya kasa fahimta, bafa wata ba ce yarinayr, Saudat ce y’ar gidan Abba Mustafa”

Da sauri Inna ta zaro ido ta ce " “ ‘yar gidan mustapha? Lallai ubanka ya k’i amince maka, wa zai so ya had’a jininsa da Jinin tsiya? Kai ma dai ka zama sakarai, bar ganin ana maka murna ka taso da nasibi wallahi idan ka had’a jini da jinin Mustafa tsaf za su tsiyataka, don tsiya a jininsu ta ke. Kuma tilas Babanka ya hanaka ana murna ka rab’i arziki, kana rab’o wa kanka tsiya?”
Hisham mikewa kawai ya yi ba tare da ya sake cewa kanzil ba illa, “Sai anjima”

Falmata ta watsa masa wani kallo, sannan ta ce mu jima da yawa,banda abin ma yaran zamani ina tsiya ina y’ay’an Mustafa da talauci ya yi wa katutu?
Hisham ko da ya shiga mota sunkuyar da kansa ya yi a kan sitiyarin Yana mamakin mutane masu k’in jinin Y’an uwansu saboda talauci. Direct gidan wani abokinsa ya wuce wanda ake kira nejeeb ya yi sa’a kuwa ya same shi a gidan.
Cikin farin ciki najeeb ya tare shi. Bayan son gaisa Hisham ya Sanar dashi halin da yake ciki, najeeb tsit ya yi yana son gano wa abokin nasa mafita, duk da shi yana ganin wautar abokin nasa na zab’ar d’iyar talakawa, akan y’ar sanata, a sanatocin ma babanta shine senate president, tabbas abokin nasa yana shirin tafka babban kuskure, sai dai hausawaa sun ce daidan wani karkataccen Wani, tunanin hakan yasa ya dubi abokin nasa ya ce “ina ganin fareeda zaka samu ka sanar da ita halin da kake ciki, kasan mata da tausayi musamman idan suna sonka,sai ka ga ta tausaya maka har ta lallaba iyayenka su amince da batun.”

A take Hisham ya amince da batun abokin nasa. bayan sunyi sallama ya karkata akalar motarsa, zuwa gidan su Fareeda da yake nassarawa G.R.A Kano
Yana danna lambar wayarta bugu d’aya ta d’auka cikin tattausan kalami ya ce, “Ran gimbiya ya dad’e ga ni a k’ofar gidanku”
Mamaki ya kama fareeda don ta dad’e ba ta ji kalamii irin wannan daga gareshi ba. Sai dai ta danne mamakin nata ta hanyar sauya mayafi ta fice harabar gidan.




A cikin motar ta same shi bayan sun gaisa ta ce "ya aka yi? Na ga kana ta doka murmushi?”Hisham ya d’an lumshe ido ya ce, “Ina kallo tsananin kyan da uwargidata tayine."
Fareeda ta saki murmushi jin dad’i ta ce “Uwargida kuma amarya ba, ka san ina da tsananin kishi, don haka daga ni babu K’ari”
Dam!! Dam!! K’irjin Hisham ya buga, don kuwa bai hango dacewa a wajen ba, cikin k’arfin hali ya daure ya ce “a haba ai yanzu mata kansu ya waye, sun daina wannan tsananin kishi........

“Ban dani Hisham, don kuwa zafin kishina ya wuce duk yadda kake zato.” fareeda ta fad’a a hassale “Don kuwa wallahi da mace ta yi kishi dani zata gwammace ta fad’a rijiya ko ta rungumi transformers......


Jin abinda tace yasa Hisham zare ido had’e da cewa, “kin san abin da kike cewa kuwa Fareeda? amman dai ina so furuncin ki yazama gangan. don kuwa rana d’aya zan aure ku ku biyu.”
Fareeda ta yi murmushi, lokaci d’aya kuma ta sha mur had’e da fad’in, “Bari Hisham a rayuwa ta ina son kowanne irin wasa amman ban da na kishiya.”
Hisham ma ya gintse fuskarsa, kafin ya ce. “Da gaske nake fareeda, babu batun wasa rana d’aya zan aure ku ke da saudat......

"Dakata Hisham!! Wallahi indai har da gaske kake na hak’ura da aurenka ko kai ne autan maza....... Daga haka ta bud’e k’ofar mota ko waiwayonsa ba ta yi ba.
Zuciyarsa ta yi zafi, ya rintse idonsa yana fadin,"Oh God " menene mafita kuma?”

Fareeda tana shiga gida ta sakawa mahaifiyar ta kuka, hakan ya rud’a mamin tata, ta shiga tambayar ta dalilin kukanta.
Fareeda ta rattabo mata bayani.
Zuciyar mahaifiyarta ta tunzira , ta ce “share hawayan ki, shi d’in banza. ai wallahi ya yi kad’an ya wulak’anta ki yanzu zan Yi waya gidansu na ji dalilin wananan tozarcin. naji.shin ,da saninsu ko babu?”
Wayarta ta D’auka ta danna lambar mahaifiyar Hisham, bugu d’aya Hajiya laraba ta d’auka.


Hajiya sa,a cikin kausshiyar murya ta ce “laraba Sak’on da ku ka turo Hisham da shi ya isar mana, sai dai ina so ki sani ban zauna da kishiya ba, d’iyarta baza ta yi kishi ba, don haka idan Hisham autan maza ne fareeda ta bar auren sa.......
Laraba ta zaro ido tace "Hajiya sa’a wallahi saurare ni don Allah, sam ba mu muka turo Hisham ba,kiyi hak’uri zan samu mahaifinsa da maganar."
Sam Hajiya sa’a ba ta saurare ta ba illa D’uf data yi ta kashe wayar, cikin jin zafin Hajiya laraba
Ita kuwa Hajiya laraba tana ajiye wayar tagumi ta zuba tana tunanin irin asarar da Hisham ya ke Shirin janyo musu, amman kuwa tabbas zai zo ya same ta,ba ta yi kasa a gwiwa ba ta kira mahaifinasa ta sanar dashi abunda yake faruwa
Tsam mahaifinasa ya yi da ransa yace," barni da dan banxan yaro,zan dawo daga kadunan gobe _ gobe kuma sai na yi abinda saii ya gwammace bai ce yana son d’iyar Mustafa mai k’ashin tsiya ba daga haka ya Kashe wayar cikin matuk’ar zafin rai Ita ma hajiya laraban zurfin tunani ta afka tare da hasasho irin hukuncin da za ta yi wa zuriyar Mustafa ma’kurar basu k’yale Hisham ba. Ta zabga tsaki,ta rasa har yaushe ta yi sake da Hisham ya fara zuwa gidan Mustafa.

Ko da ya dawo da daddre sai da ya isa sashen sashen mahaifiyarsa don cin abincin dare, wani banzan kallo ta watso masa tare da shigewa D’akinta . Hakan ya tabbatar masa ta samu labarin abinda ya aikata a gidan su Fareeda, sai dai shi ko a jikinsa Allah yasa ma a fasa auren, sam ba shi da damuwa.


Kashegari Alhaji Hamza ya dawo ko zama bai yi ba ya danna kiran wayar Hisham, cikin sakin fuska ya amsa wayar tawa, Alhaji Hamza yace, “ka zo ina son ganin ka yanzu.”
Daman yana cikin gidan,don haka babu bata lokaci yaxo, abban nasa da walwala fal a fuskarsa ya tare shi yana fadin angon mata biyu Hisham ya sunkuyar da kansa don yana zaton abban nasa gatse yake masa, ga mamakinsa sai yaji abban nasa yace,tashi muje gidan mustapha a tare na ji ba a yi wa yarinyar miji ba.

Cikin matuk’ar mamaki Hajiya laraba ta kalle shi had’e da cewa, “Alhaji daure masa gindi zaka yi? Ya d’an d’aga mata hannu, “Ba ruwanki mustapha jininane, kuma ba zan k’i jinina ba saboda wani, muje Hisham."
Hisham kuwa dadi ne ya lullube shi ya ayyana a ransa Allah kenan,Al_hakimu dubi dai yardda cikin hikimarsa ya shirya mahaifinasa a rana daya lokacin daya wa ke da wannan ikon banda Allah.

A kofar gidan Abba mustapha Hisham yayi parking din motarsa cikin zakwadi da tsananin murna ya fito ya zira kansa cikin zauren gidan Abba mustapha,da fara’a fal a fuskarsa ya shigaa gidan sauda da take gefe tana yanka alaiyahu tayi saurin d’agawa ta haska shi da wadatattun idanunta cikin sakin murmushi.shima murmushi ya sakar mata, sananan ya ce" Abba na nan kuwa sauda?”

Ta d’aga kai cikin karassahin murya, yana nan yau gaba d’aya bai fita ba, saboda baya jin dad’i, Hisham ya ce Ashsha Allah ya sauwake, ga shi da abbana muke ya xo ne a kan maganar auren mu umman tana ciki? Sauda ta d’aga kai tace "tana ciki bara nayi mata magana”
Kafin ta shigaa cikin d’akin Umma ta fito da fara’arta ta ce "Hisham ashe kai ne a tafe.”
Durkusawa yayi ya gaishe ta, sannan ya sake gyran zamansa had’e da cewa “ashe abba bai ji dad’i ba?” Umma ta gyad’a kai tace. “Wallahi jikin nasa yau ya tashi babu dad’i, kasan abinka da mai ciwon hawan jini yau da lafiya gobe babu.”
Hisham yace "haka ne daman Abbane yake son ganinsa yazo ne akan maganar mu da Sauda.
Umma ta gyad’a kai tace “To Allah yasa lafiya da fatan dai ba wata matsalar ba ce ta faru?” Hisham ya girgiza kai had’e da cewa "babu komai In sha Allah sai alheri. Ya xo ne su tattauna maganar auren.”
Cikin farin ciki umma ta ce kai Masha Allahu bara nayi masa magana.

Daidai lokacin yayyen sauda suka shigo gaba d’ayansu,suka mimmik’a wa Hisham hannu. Abba ko da ba ya jin dad’i haka ya k’ok’arta ya fito, bayan Umma ta isar da sak’on ana son ganinsa
Cikin walwala ya fito yana duban dan Dan uwansa Alhaji Hamza, cikin sakakkiyar fuska yace, Hisham maza kace ya shigo mana, ya zaa bar shi a tsaye?”
Hisham ya juya shima cike da walwala.
Abba mustapha ya saka umma ta Malala tabarma a tsakar gidan, ya zauna ya jingina da bango don kam matuka da gaske ba ya jin dadin jikinsa.
Fuskar alhji hamza a hade ya shiga gidan yana karewa gidan kallo, da alamar raini k’arara a fuskarsa gaba d’aya jikinsu ya yi sanyi,amman hakan bai hana Abba mustapha yi masa tarbar mutunci ba, ya mik’a masa hannu had’e da yi masa iso kan tabarmar.

Alhaji Hamza bai ko dube shi ba, ya sake tamke fuska a karo na biyu, ya saki murmushin da kai tsaye za a iya kiransa na rainin hankali, ya kai dubansa kan Hisham, “Allah wadaran naka ya lalace, yanzu Hisham duk tarin baiwar nasibin da Allah ya yi maka na katarin samun arxiki a nan kake so ka ce min kana neman aure? to me na sama ya ci balle ya bai wa na k’asa ya juya kan Mustafa yace, Ina so ka ji ni da kyau Mustafa babu Hisham babu y’arka, ban ga yarda had’in zai had’u ba, abin da hausawa suke cewa HAD’iN GAMBIZA kun ga yaro ya taso da arzikinsa kun bi kun makale masa saboda ku kassara shi. Wallahi d’ana yafi k’arfin ku me Hisham zai yi da jinin tsiya.idan ma kwad’ayin abin hannusa kuke bud’e kunnunwanka da kyau Hisham kaji daga yau ficikarka ta k’ara shigowa gidan nan Allah ya isa ban yafe ba,duk wahalar dana yi maka tun kana cikin Uwarka.” Hisham dake gefe ya rintse idanunsa sai ga kwalla na tsiyaya.


Shi kuwa Abba mustapha murmushi ya saki, ya ce “duk me ya yi zafi haka? ina ganin idan har an yi abin a hankali, komai zai zo da sauki, Hisham dai d’an kane babu wanda zai yi maka iko dashi kana da ikon saka shi ka kuma hana shi da alfarmar annabi saudat dai ko ta rasa mijin aure ba zata aure shi ba sai dai ina so ka ja masa kunne shi ma babu shi babu ita.....
Hisham ya girgiza kai yana duban mahaifinasa ya ce “Abba bai dace ba abinda ka yi, sam bai dace ba wallahi.”
Wani kallo ya bi shi da shi kafin ya girgiza kai “ko d’aya ban yi mamakin furucinka ba nasan ba haka aka barka ba, sai dai ina so ka sani, ko dame mustapha yake takama wallahi na fi shi, mu zuba ni da shi shege ka fasa. Hisham ya sake bud’e baki ya ce Abba....

Ya Harare shi “ mutumin banza nuna min matsayitan mutane sun fi ni a wajen ka. Wallahi idan ba ka yi da gaske ba sai na tsine maka akan wad’annan matsiyatan tashi ka fice mu tafi, kuma ka kaddara ka yi wa gidan nan kallon karshe,don ko da wasa ka tako kafarka zuwa gidan nan wallahi ba zan yafe maka ba.”
Cikin tashin hankali Hisham ya mik’e ya fice yana bin bayansa Yana sake jaddada, “Matsiyata kawai”
Suna fita umman sauda ta bi bayansu ta shige d’akin mijinta. Sauda kuwa hawaye kawai take. mahamud ya dube ta yana girgixa kai a zuciyar sa yana ayyana tabbas talauci bai yi ba . A hankali ya ce saudat ki yi shiru, Abu d’aya za kiyi ki cire soyayyar Hisham daga ranki . ki bawa mahaifinsa kunya shi ne ki ka cika ‘ya’


Zumuncin zamani

Na
Nazeefah Sabo Nashe.


(Typing: Fadimatu sabi’u d’ankaka jazakillahu bil jannah.)


Not edited a karanta da hak’uri Ba ni da lafiya.


*****************


Saeed ko girgixa kai ya yi ya zabga tsaki kafin ya ce “ba ma tilas ta hak’ura da auren sa ba, ai ko shi ne autan maxa ba xata aure shi ba.”

Umman su kuwa tana d’aki ta zabga uban tagumi Abba mustapha ya girgiza kai “yanxu fisabillah umman sauda ba za ki yi shiru da hawayen nan ba? Kada kii manta, ita fa rayuwar nan yanzu haka take sai kana dashi sannan kake xama mutum idan kuwa ba ka da shi kare ma yafi ka daraja Shi yasa yanxu mutane idonsu ya afu da Neman kud’i ko ta wace hanya wanda nake rok’an Allah ya kare ni daga fad’awa sharrin zuciya. Ina son don Allah ki jajirce ki zama mace jaruma kada wanann abun ya dame ki...

Girgixa kai umma ta yi tace "Abban sauda dubi fa irin cin mutunci da mutumin nan ya yi mana ya ilahi me mutane suke son su mayar da zumunci ne?”
Abba ya girgiza kai ya ce “babu komai, kansa ya yi wa. Ina rok’on Allah Kuma ya ganar da shi gaskiya” daga haka ya janyo carbinsa ya ci gaba da laziminsa hakan ya tabbatar wa da umma da ba ya son magana a lokacin

Jikin umma a salu’be ta mike ta bar d’akin zuciyar ta cikin zafi da matuk’ar K’una
Shi kuwa Hisham tunda ya yi parking ya dire mahaifinsa a sukwane ya ja motar ya bata wuta, bai zame ko ina ba sai wani park, flat ya kwanta a kan ciyayi, zuciyar sa naci gaba da yi masa wani tukukin bak’in ciki idan ya tuno kalaman da mahaifin nasa ya yi amfani da su wajen cin mutuncin bayin Allah nan me suka yi masa? Kawai dalilin talauci sai mutum ya zama abin gudu abin wulak’antawa da tozartawa?


Ya rintse ido kafin ya ciro waya ya kira wayar saudat sai dai haka tayi ta ringing ba a d’auka ba shi kenan ya sani saudat ta rabu da soyyarsa, bai ga laifinta b kuma ko wacece ce ma kuma xa ta aikata, ya ayyana hakan a ransa tabbas idan har bai auri sauda ba shi kenan farin cikin sa ya k’are a rayuwa, ya zai yine? Kuma a ina zai samu mafita?

Alhaji hamza kuwa ko da ya shiga gidansa dariya ya shiga kyakyatawa tamkar wani zararre, matarsa balaraba ta dube shi kafin ta ce "lafiya Alhaji?
Ya yi tsaki had’e da cewa “ni da wad’annan matsiyatan mutanan ne su sun zata da gaske neman aure na je har da wani malala min tabarma. Ni kuwa na zage su tass na ci musu mutunci”

Hajiya laraba ta saki murmushi ta ce "ai ni na zata da gaske kake ina nan ina ta tsuma ina jiran ka dawo naji dalilinka na aikata haka.”
Alhji hamza ya ce “ni mahaukacin ina ne zan yarda d’ana ya jajaibo min tsiyar dangi ke ko a mafarki aka ce miki zan yarda za ki amince? Wai ni na yarda Hisham ya auro min dangin tsiya.”
Hajiya laraba tace “ai shi na gani,abin ya yi matuk’ar d’aure min kai, da naji kai ne ka amince
Alhaji ya girgiza kai “yanzu abin da zaa yi, tashi zakiyi kije ki bawa mahaifiyar yarinyar hak’uri,ki sanar da su maganar banza yake, ki dai san yadda kika yi kika shawo Kansu.”
Hajiya ta ce “yanxu kuwa, ai ba a bori da sanyi jiki”

Alhaji hamza ya ce. “A to, kin dai sani da bazarsa muke taka rawa, idan Hisham ya k’i auren y’arsa na tabbata duk wasu kwangiloli da suke shigo min dainawa zai yi, yadda yake ji da yar nan tasa tamkar gold”

Haj laraba cewa ta yi, “to ba dole ya ji da ita ba ita kad’ai ce fa tamkar ajali”

Alhaji hamza ya girgiza kai kafin ya ciji baki ya ce “don haka ki sake jawa yaronki kunne a game da yarinyar nan don wallahi matuk’ar ya k’i bin umarnina sai dai ya sake wani uba amman ba ni hamza ba” ya fad’a Yana nuna kansa..
Hajiya laraba kuwa cewa ta “In sha Allahu ma ba zai k’etare umarinka ba, ai Hisham tun Yana yaro ba dai muka saka masa doka ya k’etare”
Ya sake girgiza kai had’e da cewa “Ah to, na dai fad’a miki, bin umarnina shine kwanciyar hankalinsa a gidana,sab’anin haka kuwa ke ma kin san sauran” daga haka ya mik’e ya shige d’aki hajiya laraba kuwa mi’kewa ta yi ta nufi gidan su fareeda don ta ba mahaifiyar ta hakuri...


Fareeda na zaune ita da maminta, daidai lokacin hajiya laraba tayi sallama cikin kwantar da murya saboda ta san gidan da ta zo daman haka lamarin yake kafi wani wani ya fika.
Maman fareeda a wulak’ance ta amsa sallamar saboda ita sam ba ta san dalilin da da yasa mijinta son auren ba, sam a nata tunanin ba su da dukiyar da har za a yi rububin had’a zuria da su,to ka ji fa, wannan fa shi ake kira gaba da gabanta!! Aljani ya taka wuta ita a son ta a nemi wani hamshakin mai kud’i a bashi auren d’iyarta ko ma d’an shugaban k’asa,amma ba wannan ba wanda mahaifinsa yake samu daga taskar mijinta.

A shagube ta amsa gaisuwar daga haka ta ja bakinta ta tsuke. Ita kuwa fareeda ko kallonta bata yi ba, ta mik’e ta shige d’aki.
Hajiya laraba ta sake rusunar da kai ta ce "hajiya daman hak’uri nazo na baki tabbas na san Hisham ya b’ata muku amma a yi hak’uri yaran yanzu ne ka haife su ba ka haifi halinsu ba"

Da saurii hajiyar ta dakatar da ita,fuskarta a had’e sosai ta ce, “wasu yaran ba, wad’anda ba su da tarbiyyah to ki sanar da shi in dai fareeda y’ata ce to daga yau na haramta masa aurenta, kuma za ki san na isa da 'yata dama duk alhaji ya jawo,idan ban da haka ai wannan had’in sam bai yi min ba. to me na sama ya ci balle ya ba na k’asa? Ai babban goro sai magogin k’arfe,don haka ni na yi farin ciki da abinnan ya faru, ya je can ya k’arata .Allah raka Taki gona yo ma banda iskancin wane ne Hisham da har zai wulak’anta min ' yah, to an fasa ya je ya auri ko wace ce amma y’ata ba kalar kishiya ba ce." Daga haka ta shige d’aki
Hajiya laraba na sake ba ta hak’uri amma ko waiwayen ta bata yi ba haka nan jikinta a sanyaye ta mik’e ta bar gidan zuciyar ta cike da tunanin tsagwaran rashin kirkin mamin fareeda
Ko da ta koma gida alhaji hamza yana nan yana tsimayin ta. fuskarta babu walwala ta shiga gaya masa yarda suka yi da mamin fareeda
Alhaji hamza ya girgiza kai ya ce “mata kenan rabu da ita shi honourable d’in zan samu na san zai fahimce ni”
Hajiya laraba ta ce ai kam matar nan tasa bata da mutunci wallahi ko kad’an” alhaji hamza ya girgiza kai ya ce "duk ba kowa ne ya jawo wannan matsalar ba sai Hisham"


Tun da safe da ta mike take ta share- share a gidan, zuciyarta sai matuk’ar suya take mata, ga shi umman tata ta tafi asbiti kasancewar ba ta jin dad’i kanta ya matsa mata da ciwo.

sai karfe goma ta gama share_sharen sananan ta shiga wanka,da sauri take komai kasancewar karfe 11 safe take da (lecture).
Bayan ta kimtsa tsaf duk da ba wata shahararriyar kwalliya take ba, yanxu ma riga da zani ne na wata koriyar atamfarta ta kamfanin NOUVA , ta yafa wadataccen mayafinta mai kaurin gaske, sannan ta shiga d’akin mahaifinta yana zaune yana lazimi har k’asa ta durk’usa ta sanar dashi zata tafi makaranta.
Addu’a ya yi mata sosai, sannan ya ce "Àllàh ya bada sa’a sai an dawo saudat.”
Jikin ta a sanyaye tafito daga gidan don ko ficika ba ta da shi na shiga mota. Don suna da test ne yau kam da babu abinda zai sata zuwa makaranta.to wa yake ta karatu ana ta abin da zaa saka a ciki?gaba dayan su yau azumin suka tashi da shi saboda babu wadataccen abincin da za a iya

Please Login or Register in order to submit comment