Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya janyo kafadunta

Ya kama mata magana a kunne cikin rada “Ke dawo ki mana dabgen kaji ,yanzu da na koreta kinga ai yayi mana auki”





Oum Aphnan
09065990265
*_🐹BAD BOYS🐹_*
By...
Oum Aphnan

008
___________________
_Bite & links republic_

Ya Sheikh kallon Ambassador Rashid yayi da suke zaune a gaban ƙatoton teburin cin abincin da aka shafe masu shi taf da su chicken wings da mahaukatan drinks masu shegun tsada ,an decorating table din sa fulawoyi masu daukan hankali sai sheƙi yake da walwali.

“Rashid kai abokina ne tun na yaranta ,har kawo yau muna tare ,amma haƙƙi na ne in maka nasiha , Almubazzarancin nan yayi yawa...Ta yaya zakayi mana ordern abun nan da bazamu iya cinye su ba mu biyu ? Sannan da nauyayen kudade kamar wannan? Kudi kwata miliyon ,akan me? Jarin wani ne fa”

“Ban gane ba Miqdad? Nifa ba a ƙasar nan nike rayuwa ba ,na saba rayuwa tsakanin tsibirin hong Kong da su Germany ,we spent alot wa 'yan mata ma ba cikinmu ba ,a America Gidan yin tausa ,in mun dawo daga aiki muna biyan kudi Naira dubu dari biyar to meye wannan? Aini arha yayi mun ,Alhaji meye amfanin samunka in baza kaci ba ,in fa ka mutu Salima kake tara mawa don har yanzu ka kasa bamu baby...”

Ya sheikh harzuka yayi ,ya fara keta kayan abincin uku yana jan kashi daya gabanshi sauran ya bar masa a wajen

“Ni zan biya kudin wannan sauran ka biya ,tunda asara dai ka ja mun...Ku kun saba da asararar da kudinku ma en mata to Ni Ko matata na koya mata tattali ,komai sai an ƙididdige ”

Zaro ido Ambassador Rashid yayi “Ahhhh (,kawai kuma sai ya fashe da dariya) bros kanaji ka barshi zan biya duka ,amma Plz naji point of error a maganar ka , fada mun gaskiya baka ƙuntata ma Saleemart?
Naji kana cewa ka koya mata tattali ,anya baka lalata fine cutie pie ba kuwa? Kasan dai yanda mu abokanka muka dinga santin Saleemart ,bro bari in Fada maka gaskiya da ace na kyalla ido akan salimart Kafin auren ku ,wlh sai na ƙwace maka ita”

Wani malolon kishi ne ya taso ma Sheikh abinda bai taɓa ji akan Salima ba tun bayan auren su sai yau ,nan take idonsa suka kada zuwa jaaaa.

“To Rashid ko zan saketa ne ko aureta kawai?”

“Hehehhee ,Meye yayi zafi miqdad,? Gsky nike fada maka,ynz ga tambaya yaushe rabon da ka fita da salimart outing irin yanda zakaga maza na fita da kyawawan matansu a gaban mota matsayin ƙawar su?”

“To ko shekaranjiya mun fita”

“Zuwa ina?”

“Munje kasuwa mana ,mun siyo kayan cefanen gida”

“Hmm just imagine,bafa cewa chilling kuka fita ba,irin kace babes Shirya muje musha ice cream din na ,come on ,kana fa da wayewan nan kudi kuma akwaisu ,kaji dalilin da yasa nace in baka so ka sallama abarmu mu shigo filin mu ririta Rose🌹”

Sheikh yanda kasan ƙaramin yaro haka ya zama ,abunka da bai taɓa samun wanda ya nuna masa zalama ido biyu ba ,kuma yasan halin Rashid ba karamin ɗan duniya bane ba ,ya kwallafa rai akan mace ko ba aure sai ya nemeta .
Jikinsa na bari ya daga waya ya fara kiran Salimart .

Dammm! Ƙirjin Salima ya buga ganin kiran ya Sheikh daidai ta rufo ƙofar falon ta dawo ,gode ma Allah ta shigayi a ranta da ta sallami Dr kafin nan.

“Assalamu Alaika ya zaujiy”(Mijina)

“Waalaikis Salam ya ustaziya ,kina jina”

“Eh ya sheikh”

“Yau Inason kici ado nan da sa'o'i biyu ina dawowa zamu fita shaƙatawa”

Ras gaban Sayyada ya ɓaci ,out of joy ta daka tsalle tace da gaske kake Habibiy?”

“Kwarai kuwa ustaziya zamuje musha Ice cream muci ɗan pizza ko ya kikace,ɗan flexing din nan dai kema ki fita gari ayi dake”

“Umuuuuh😘 Ina sonka mijina ” ta manna ma wayar kiss ta kashe da sauri ta yi cilli da wayar akan kujera ta haura sama da gudu zuwa sashen ta.

Ya Sheikh waigawa yayi ya kalli Rashid cikin Murmushi
“Mata wato sudai mata'ul hayat ne(Ƙyale_ƙyalen rayuwa) sudai a kashe kudi a ji daɗi,yanzu zo kaga farinciki da murna”

Rashid lumshe ido yayi yana kora drinks din hannunsa yana sanyaya maƙoshi
“I can perceive bros”


***
“Salima
Salimaaaaa
Wai kina Ina ne?”

Ya shigo gidan hannunsa rike da Car key .

A ruɗe tace “Na'am ya Sheikh Ahlan wa sahlan”(welcome)

Sannan ta fito daga ɗakin tana biyo stairs din da takalminta mai tsini yana ƙara cakas! Cakas! Cakas!

Ya Sheikh Binta da kallo yayi ,kawai sai yayi zumbur ya mike

Ta saka wani dandatsatsen less an mata ɗinkin bubu ya fita sosai ya zauna ɗas a jikinta ta murza daurin turban gingiringin ta sagalo mayafi a kafada hannunta daure da wrist watch da zobentana gwal daya hannun na azurfa sai ƙamshi take zubawa.

“Salima meye hakan kenan?” cak taja ta tsaya ba tare da ta gangaro ba ,sai bin jikinta da ya nuna da yatsa take da kallo,tana neman abinda yayi aibu a jikinta

“Salima wannan ba shine leshin da Anty uwani ta kawo maki tsaraba daga cotonou ba?”

“Eh shine mana ya sheikh” tafa hannu ya shigayi yana salati

“Hazbinallahu waniimal wakil ,yanzu Ke Salima ɗingurugum leshin nan kika bada aka tsiyata da wannan ɗinkin? Ji leɓatu kotaina suna reto a iska ,meye amfanin dinkin nan kenan? Kinsan tsadan leshin nan kuwa? Da aka tsiyata leshin da gown kwara ɗaya jal!!!”

Marairaice murya tayi a shagwaɓe tace
“Ni Ina son style din ne”

Dafe goshi yayi

“Ohwuuuuu,Salima meyasa bazaki zama irina ba, Leshin da za ayi kaya uku dashi anyi daya.....ya salam
Ya kamatane kisa tela ya maki dinkin yadi hudu doguwar riga,sai kuma ki siya wani yadin ko satin ne dai ayi maki combination dinki a maki ko riga da siket ,ba sun zama dinki biyu ba kenan?”

Langaɓe kai tayi ta ɗaura hannu a ƙarfen benen ta masa shiru

“Yanzu dai nawa aka maki ɗinkin nan?”

“kyauta kawata tayi mun”


“Ehennn kinji maganar nan,ta cuce ki! Ni dama nasan ɗan jikinki bazakici 6yards ba ,ta maki wayo kamar anci ƙyalle a ɗinkin ta kwashe sauran yadin....kiyi amfani da hankali salima🧏‍♂️” ya nuna gefen kansa kamar wani super professor

Caɓe fuska tayi duk ya sattar mata da gwuiwa

“Shikenan bari inje in sauya kayan ”

“Ke😳Tare nike da Ambassador ,sai kuma ki sake ɓata wani lokacin,kiyi amfani da hankali salima🧏‍♂️” ya sake nuna mata gefen kansa 😄

“To shknn muje ,za'a kiyaye gaba”







Oum Aphnan
09065990265
*_🐹BAD BOYS🐹_*
By...
Oum Aphnan

007
___________________
“Knock knock knock”

Daga can upstairs taji ana knocking a entrance door ɗin parlourn ta ,wannan ya sata fitowa da sauri tana faɗin “Ana zuwa”

Sanye take da bugujejen jallabiyar Ya Sheikh sai hulan wanka a kanta da falkata falkatan silipas ɗin da take sakawa a ɗaki.

Murza key ɗin ƙofar tayi ta buɗe ƙofar ,cak ta ja ta tsaya ganin very tall handsome man a tsaye , kyakyawar gaske cikin ƙananun kaya ,fuskarsa kewaye da ƙasumba ya ɗan ajiye tumbin kuɗi cif cif a riga

Yana ganin ta buɗe ya saki fara'a har jajayen leɓensa da suka haskaka brown ɗin fatarsa suka sake bayyana.

“Hajiya Barkanmu da rana” yanda yayi maganar a rarrabe ya bata dariya ta lura baida Hausa sosai

“Masa'al khair” Adnan Yana jin ta iya larabci yaji kamar ta taindimashi a Aljannah ,ji yayi kamar ya kamata ya rungume

“Masha'allh A adkhul?”(In shigo)

Yanda ya ruɗe sai kawai Sayyada ta tsinci kanta cikin jin nishadi ,daga gani wannan ɗan comedy ne ,kuma duk yanda akayi mutanen Sheikh ne na wasu ƙasashen

“Tafaddal”(Shigo) ta bashi hanya ya shiga ,itama ta rufo ƙofan ta biyo bayansa .
A tsakiyar falon yaja ya tsaya ,suka gaisa sosai

“....Ammm sunana Dr Adnan Ni Likitan ƙwaƙwalwa ne ina da Asibiti a ƙasar nan ,London Specialist ,nazo ziyarar aikine So nasa a siya mun gidan da innazo zan ringa sauka Inshallah ,shine aka bani wancan gidan da yike kallon nan Compound ɗin.”

A ɗan ɗarare Sayyidah tace “Sannu sir,Ashe maƙoci mukayi”


“Na'am,to shine fa tun safe na sauka da empty stomach ,bansan koina ba ,Inason inci abinci ,amma gaba-daya water system ɗin da wutan gidan na kasa connecting ,bansani ba ko ƙauyanci ne😆Ko tsarin naku na irin na ƙasar mu bane oho”

Dariya Salima ta fashe dashi
“Hummm ɗan gayu kamar ka ai saidai ace baku saba da ganin local one irin namu ba ,na en Nigeria...Nikam yanzu me kake so inyi maka”

“Yawwa don Allah to ki ɗan haɗa mun wai cofee ne insha atleast kafin in samu a gyara mun komai nawa”

Gaban sayyada fadi yayi dam ,a take idanuwarta suka zazzago
Ta fara sosa ƙeya “Ammm eh ,dama ehhhh ,wallahi bamu da kayan shayi ” ɗaga kai yayi yana ƙarewa falon kallo ,gida har gida kudi gasunan basu magana wai ba kayan tea” bai nuna mamakinsa ba sai ma wayancewa yayi irin na gogaggun maza da suka saba hulda da mutane .

“Nop karki damu ai ma taho da nawa kawai ruwan zafi nikeso ” ya mika mata ledan hannunsa ,Plz ki hado mun a ɗan mug.

Amsa tayi a kunyace ,ta wuce Katar Katar ,ɗuwaiwuka da nonuwa suna ta rawa a Jallabiya ,bin bayanta da kallo yayi ,inner side ɗin zuciyarsa tana harbawa da ƙarfi ,a zahiri yace “Wow Original kyau please”

Sai kuma yayi saurin minding business ɗinsa ta hanyar daukan remote Yana canja channel din TV.

Minti kaɗan sai gata ta dawo da ɗan mug din shayi a saman tray ɗinsa da ɗan cokale a gefen cup ɗin.
Ta saman kansa ta miƙo masa

“Gashi ” Hannu biyu yasa ya karɓa yana bin ƙirjinta da kallo
Haka yakai cup din baki ya kurɓa “Shukran”(Nagode) ...Amma ina naki?”

Zaro ido tayi ,a ranta tana cewa shi wanann ya faye shishigi Ni ya tashi ya fita kafin ya Sheikh ya dawo.

“Ya zanyi in Sha maka abunka ? Hazha haram,ga sauran kayanka nan” cikin mamaki ya ajiye cup din shayin a saman table yana kallonta .

“Kar kice mun kina da rowa?” girgiza masa kai tayi da sauri

“To Ni kayana na kowane ,in inacin abu Naga wani bayaci gaba-daya abun gundura na ma yake yi,don haka Matsawar bazaki hada naki ba to nima na fasa sha”

Sayyada da tun asali ƙamshin shayin yake damunta ,miƙewa tayi a sanyaye ta samo cup ta ɗiba Dan kaɗan zata mike yace “Wai ku haka kuke shan tea so watery _Ba kauri?_”

“A tattala Mana in ya kare fa kaya na tsada a nan?”

Zaro ido yayi
“Topah ,Add things johhhhrrr”

Lafiyayyen Tea sayyida ta haɗa tazo falon can nesa dashi ta zauna tana sha a ɗarare duk ta ƙosa ya tafi

“Kayi hakuri ba bread ”

“Nop banashan tea da bread ,akwai kaza? Ko soyayyene?”

Zaro ido tayi harda dafe ƙirji
“Kaza? A nan?(kawai sai ma ta fashe da dariya)

“Aah baƙo babu”

“Halan su mama da baba basa nan ne wai?”

“Nan fa gida na ne”

“Oh dama ƴan mata suna iya zama a gidansu su kadai ba aure?”

“Sir I'm married” tsuriii ya kafeta da ido yanason gano asalin gaskiyar

“Hummm Saboda kin ganni baƙo shine zaki mun kora da hali?”

“Aah wlh da gske”

“Wow amma fa mijinki ya iya zaɓe,wlh kin cika duk wasu quality da nike neman mace dasu ,da na sami irinki da tuni nayi aure"

Sai yanzu ta masa kallon ƙurilla ,tabbas ya haɗo kuma tana kallonsa ba abunda ya faɗo mata a rai sai aure. Ji take tamkar ta rungumesa ko zata samu sassauci,lokaci daya bugun nunfashinta ya daɗa hauhawa

“Ƙatotonka dakai ba mata abun kunya”

A shagwaɓe yayi magana gamida langaɓe kai kamar zaiyi kuka

“Hum ban samu taste Dina bane ,nikuma gaskiya bazan iya auren macen da take not active a gado ba,saboda gaskiya Ni maciyi ne,I'm sorry kuma kinsan duk foodie dole yana buƙatar ɗumin active woman a Koda yaushe...”

Sunkuyar da kai tayi cikin jin kunya.

“Sorry na baki kunya ko? Ni namijine ke namiji... magana ake na gender equality ,kinsan komai na sani daga halittan mu aka halicceku ,dole muna da sha'awar jinsin da bamu dashi ko ba haka ba ?”
Shiru ta sake yi Tana jin wasu feelings da ta manta when last ta jishi yana taso mata,Zuciyarta tayi rauni ,hawaye a take ya fara kwanciya a idonta ,babu abunda takeso sai taji ɗumin namiji a kan gadonta,amma ina abun ba da sauki bane ba ,kullum ya Sheikh yana cikin Alwala baya son ko da wasa hannun mace ya shafi jikinsa bare ta karya masa Alwala.

Zumbur tayi ta mike tasa bayan hannunta tana goge ƙwalla
,tana tuna hadisin Manzon Allah da yike cewa duk inda mace da namiji suka kasance na ukunsu shaidan ne.

“Mijina ya kusa dawowa zanje in masa girki”

Dariyar yake yayi “Ok Nagode da karamci,meye sunan ki to”

“Salimat” ta bashi amsa tana nufar ƙofa da sauri ta buɗe masa , Murmushi yayi amma shidai psychologist ne ,ya fahimci akwai abinda ke damun Salima ,kuma ya kudiri aniyar zai bibiyeta a hankali.

A sanyaye ya sakai ya fice saida ya kai saman varendar ɗin ta sanann ya ɗago mata hannu “Bye Nagode fa,kyakyawa"

Dammm! Ta rufo ƙofa ta koma ta maƙale bayanta a ƙofar kawai ta kurma ihu da ƙarfin tsiya kamar zararriya.






_Plz next update na masu Aurene ,kar a karanta mun in ke budurwace_



Oum Aphnan
09065990265
*_🐹BAD BOYS🐹_*
By...
Oum Aphnan

009
___________________
_Emirate_
Yau fa fada An tashi da baƙar labarin rashin Lafiyar mai martaba ,saidai a kwantar saidai a tayar ,an kwana dashi lafiya an tashi ba baki ,ba shiri Mai babbar ɗaki ta bada umurnin saita tafiya zuwa Cairo don binciken lafiyar mijinta don ga dukkan Alamu ya shiga _*Coma* and if care is not taking will definitely loose the king....what is the way out?_

A lokacin da ake kuciniyar fitar da sarki ƙasan kuma a lokacin duk wasu king makers suka kutso ɗakin da me martaba ke kwance rai ga hannun Allah ,don a cewarsu ciwonsa ta iya yiwuwa sharrin magautane.....But it will shock you ,all this drama Yarima baya gida baisan ana yi ba ,ya shiga cikin gari ran gadi.....wani wainar ake toyawa ?
Gadai Waziri,Fagaci,Ciroma da sauran manyan fada kewaye da gadon sarki a daidai Lokacin da Babban Malamin fada ke durƙushe a gaban Sarkin yaja carbi mai dubu da Alluna cike da ƙasa ,sai dukan ƙasa yake yana shafewa yana sake zanawa duk don gano me ke faruwa da Sarkin a wannan safiyar?

Mai babbar ɗaki da Autar sarki a furgice suma suka shigo ɗakin suka yi carko carko a tsaye .

An kwashe sa'oi biyu cikin wannan halin gidan yayi tsit bakajin ko tarin bil'adam

Babu zato sukaji Malamin fada ya doki ƙasa cikin tashin hankali ,wani zufa nan take ya shiga karyo masa kamar an watsa masa ruwan famfo.

Cak ya kakkaɓe rigarsa yana haɗa kayan wuridinsa cikin jakar fatansa ,zuruuuu kowa ya bisa da ido ,haka ya taƙarƙara ya mike yana dogara sandarsa yaje gaban kan sarki ya tsaya kana a sanyaye cikin mutuwar jiki yace “Sauya sabon Sarki shine samun lafiyar mai martaba !!!!”

Dararass gaban kowa na ɗakin ya fadi ,saboda indai malamin fada ya fadi magana to yanki takene haka zai faru ,kenan Lafiyar sarki ne zataci gadon mulkinsa

Kowa yayi jungum jungum cikin tunani ,kafin su ankara har malamin fada yakai bakin ƙofa zai fice daga ɗakin ,taran gabansa auta tayi cikin kuka ta kange bakin ƙofa

“Ya malamin fada to mu ya makoman abban mu? Yanzu zamu wuce dashi Cairo ganin likita”

“Cutar mai martaba ba na asibiti bane ba,idan har kuka bar dashi dakin nan tamkar kun fita da gawarsa ne,Kuma fitintinu su zasu biyo bayan hakan”

Ƙara auta ta saki gamida rugawa da gudu gadon da babanta ke kwance tayi ta daura kanta a ƙirjinsa ta kece da kuka .

Mai babban ɗaki kam ƙeƙam tayi cikin wani irin jarumta ,fuskarta nuetral ba yabo ba fallasa.

A dake ta kalli malamin fada sannan ta magantu “Sai a shirya gagarumin bikin naɗa yarona yarima sarkin faƙat!”

Ɗagowa yayi ya mata wani irin kallo mai kama da tausayawa ko tsorataswa .
“Bamu da damar ɗaura wani mahaluki akan kujerar mulki har sai masu tsaron kujerar sun bada umurnin wanda zai hau ,don haka ba naɗin sabon Sarki sai nan da sati guda .....daganan ne yarima zai tabbata magajin kujeran nan ko akasin hakan....”

Yana gama magana ya fice daga ɗakin yana dogara sandarsa dakyar ƙafafuwansa ba takalmi

****
Wani irin gudu motocin Yarima suke shararawa akan kwaltan garin duk inda talakawa suka hango layin motocinsa sauka da ababen hawansu suke ɗingurgum akan kwaltan har sai ya wuce.

Baba kadarko ,dattijo ne dan shekara 58 ya hudo ta ƙararramar hanya yina gungura tsohuwar kekensa da ya ɗebo kara daga Gona ,cikin gaggawa yake tafiya sakamakon yarinyarsa Ummulsulaim ta dawo daga makarantar kwana tun safe ba abinci a gidan ,shine ya fita yayo masu karare a samu ko taliya ƴar muji ne a ɗan silala mata.

Yina dab da karya kwana shiga layin gidansa da ake hange tun daga farkon layi ginin jar yanɓu an ma ƙofar Gidan labulen tsumma,ko arzikin kofa basu da shi.

sukuma daidai motocin su yarima suka keto fiyauuun fiyauuuun a tsiyace ,Raɓewa ya yi ta gefen hanya zai cusa kekensa a hankali .
Saidai Wani ƙara ne ya ziyarci kunnensa na bazata, yaji kuuuuuuu ! wanda ya sashi firgita ya ɗago a tsorace.


Kafin kace meye wannan motocin Yarima sunyi dafifi a kan baba ɗan tsoho ,firgita kam iya firgita yayi ,amma haka ya aro mazantaka ya saka a ransa .

“Bayin Allah lafiya?”

Basu tamkasa ba suka fara kiciniyar ɗaukar kekensa su saka a Boot ɗin motarsu .

Baba sa azama ya damƙi hannun Yakubu

“Ɗan nan tsahirta...karka karya mun wuyan keke ,meye hadinka da keke na?”

Banza yayi da shi sai ma yana ƙoƙarin fincikarsa haɗe da keken ,don haka baba yayi tagal tagal zai kifa ,wannan abu ba ƙaramar ƙona ransa yayi ba ,don haka cikin zafin nama yabi bayansa daidai zai saka keken a mota ya daddage ya tsinke guard ɗin yariman da mari .

Ji kake faffassss!

Kafin ya sauke hannu a kuncin Yakubu yaji wani lallausan hannu ya kece fuskarsa da mari Wanda yasa baba sakin fitsari a wanda ,idanuwarsa ɗif suka daina gani na wucin gadi ,kafin yana farfadowa yaga anyi gefen hanya dashi an yasar ,sannan kuma an dauke kekensa an cusa a mota.

Ɗaga ido yayi yana kallon mutanen da suke ƙoƙarin yi masa fin ƙarfi haka ,yana kuma son ganin wanda ya shafe fuskarsa da mari.
Bakowa bane face Yarima

“Allah ya ɗaiɗaita aniyarku ,yanda kuka tozarta Ni fanni ya tozarta kuruciyarki ,da duk abunda kuke takama dashi”

Cakkkk yarima yaja ya tsaya yana kallonsa
Tsirrr cikin bana ya tsirga ya mike da sauri ya taka zuwa hanyar ƙofar gidansa

“ku dakatar dashi ” he ordered

Bai wahalar da Shari'a ba yaja ya tsaya

“WAYE YA BAKA IZININ RAYUWA A MASARAUTA TA?”

Kallon mamaki Baba ya bishi dashi ,kawai sai ya sunkuyar dakai yana kallon kasa yana mamakin wannan Al'amari ,an wani banƙareshi kamar yayi sata.

“Ina takardan ka na shedan zama ɗan garin nan” waro ido yayi
“Topah ,jidali sabo!

Bai tamkasa ba ya yi masa shiru

Tsawa ya daka masa
“Kai talaka! Ka bani amsa ”
Girgiza masa kai yayi ma'ana baida shi .

“Kuma baka da takardan shedan zama ɗan garin nan har kake da gut ɗin zagina? Har kake da encin noma a ƙasa ta! Wannan kana zagin masarautana ne ”

“Ni ban taba noma a gonar kowa ba sai gonar da na gada iyaye da kakanni

Subhanahi yarima ya hassala iya hassala Don haka ya daka masa wani mugun tsawa

“Rufe mun baki ina magana kana magana.....Yaƙubbb” ya ƙwalla ma yaronsa kira da yafi ji dashi a kaf cikin yaranshi

“Ɗauko mun littafin ɗaukan rai!”

Da gudu yaƙub ya nufa wajen mota sai gashi ya dawo hannunsa ɗauke da wani rafkeken littafi Kamar album an saka farin ƙyalle a tsakiya .

Yana zuwa gaban yarima ya wangale masa tsakiyar littafin ,bindiga ce kwance akan farin ƙyallen cike taf da bullet .

Sa hannu yayi ya ɗauketa ya gyara mata zama tayi ɗan ƙara alamar alburushi ya shiga cikin mazauninsa kana ya saita goshin baba kadarko.


Ummusulaim da mamanta suna daga cikin gida suke juyo Hayaniya sama sama daga waje wannan yasa ummuh leƙowa , subhanahi wa zata gani ? Babanta ne an rirrikeshi an saitashi da bindiga za'a kashe banza .

Wani irin ƙara ta saki mai tada tsikar jiki ta fyalla da gudu ta rumfashe uban tana kururuwa.

Baba hansai da gudu ta nufi gaban yarima ta tumu akan ƙafafunsa tana majinjinu tana gyara leɓen zani ,tana roƙonsa yayi masu rai kar ya kashe mata miji shikenan gatansu

Yanda baba ke tima take burgima a kasa yasa ya sauke bindigar ƙasa yana kafe ummuh da ta sha gaban babanta ta masa rumfa tana faman tutturo ƙirji kenan harbin ya sameta kar ya sami abbanta.

Murmushin ƙeta yarima ya saki ,gamida taune leɓe.

“Na yafe ma mijinki” wani ihun murna baba hansai ta saki

“Ehoo mun gode Yarima mun gode....”

“...Amma har zuwa lokacin da zai mallaki takardar shedar zama ɗan garin nan ,zata kasance Tawa...” ya Kare magana yana nuna Ummulsulaim dake jikin babanta

Wani ƙara maman ta saki “Innalillahi ka taimake Ni kar ka rabani da ƴata ita kenan mana wallahi ƴar makaranta ce yau ɗin nan ta dawo....” bai saurare su ba ya juya zuwa motarsa aikuwa guards dinsa hudu sukayi ƙawanya suka cicciɓeta wannan ya rike hannu wannan ya rike kafa ,tana zille zille iyayenta na binsu da gudu ummusulaim tana kurma ihun kiran iyayenta tana ɗaga masu hannu amma haka suka je motan da yarima yake ciki suka bude ɗayan side ɗin suka wullata ciki.....


Ƙura ta tashi da karfi cikin minti kadan duk motocin suka watse aka bar su baba a yashe suna kurma ihu.


***
Ihu Ummulsulaim ta cigaba da kurmawa shikam gogan ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya yana karanta jarida tamkar ba kuka take ba waƙa take masa.

Zuwa wannan lokacin ba abunda ya ƙosa illah ya isa gida yayi wanka ya miƙe a ruwan cikinta ,don kallon farko ya hararo baiwan niima a ƙwarmin idonta .


“Ina fasa budurcin da kike taƙama dashi kuka ya ƙare ,as you know now you're belongs to me,ko ki lallaɓani ko in maki shigar fata fata ,in maki cin wulakanci....


Ɗif Sulaimiy ta ɗauke wuta ko tari ta kasayi ,ta fara tunanin yankata yake nufi zaiyi ya cinyeta ɗanye ko ƙaƙa?




Oum Aphnan
09065990265


Wannan shine zai kasance page na kusa da ƙarshe na pages ɗin kyauta ,daga page 10 na kyauta ya kare
Ki hanzarta biyan kudinki don ayi tafiyar dake ,BAD BOYS Ba Littafin Yara bane muje zuwa💃

Wacce ta shirya biya
Regular 500#
VIP 1000#
Special 2000#

Katin MTN ko ta nan bank din
7782217014
Mohammed Hassana
Fcmb bank
*_🐹BAD BOYS🐹_*
By...
Oum Aphnan

010
_LAST FREE PAGE_
Daga wannan page din na kyauta ya ƙare ki biya kuɗinki don karanta littafinki cikin salama🤗
Regular 500#
VIP 1000#
Special 2000#
Zaki biya ta katin MTN ta wannan Number
09065990265
ko kuma ta wannan Account Number
7782217014
Mohammed Hassana
Fcmb
Sai ki tura shaidar biyanki ta wannan Number
09065990265
___________________
Sayyada
It's late Evening gari ya fara duhu magriba ta ɗan gota ,Sayyida fitowa wajen compound dinta tayi da sauri ta saka shirmemen jilbab yasha squeezing hannunta rike da ledan bin na zubar da shara ,zata zuba a ƙatoton sanitary bin din da yake wajen gets din gidajen layin nasu .

Bismillah tayi a hankali a ranta kana ta buɗe bin din ta jefa discardable linning din ,ba zato taji ance “Hi”

Da sauri ta waiga bayanta ,Dr ne tsaye cikin shigar suit sai bulbula ƙamshi yake ,fuskarsa maƙale da eye glasses

Washe baki tayi “Aah ya ɗabib ,a'anta Huwa?” (Aah likita kaine haka?)

Murmushi yayi ya lanƙwashe hannayensa akan ƙirjinta ya ɗan yi tsayuwar samarin nan masu son janye zuciyar mace garesu

“Me kikeyi anan?”
“As You can see shara na zubar”
“Shara? Da Daren nan?” Murmushi tayi gamida gyada masa kai ,ita bata ma ji wani abu ba
“Ai nayi Bismillah kafin in zubar babu abunda zai sameni”
“Amma kamar naga mijinki ya dawo ai ko ,me yasa bazaki bashi ya zubar ba tunda bakida house help”

“Humm😁Ashema ka ganshi,to zan bashi next time ,ok?” ta ɗan yi magana in hurry tana son juyawa ciki

“Sissss ji mana” cak ta tsaya saidai wannan karon dukar da kai tayi saboda bata jin dadin kallon da yake mata ,infact kadaicinsu ma ya na sa mata jin wani yanayi na dabam ,wacce bata san ko menene ba

“I observed something...” A tsorace ta ɗago tana kallonsa ,cikin mugun tsarguwa

“Menene?”
“Salimart ,anya kinajin daɗin auren nan?,anya mijinki baya azaba maki?You look so unorganized ,ji hijabinki a yamutse kullum baki gayu despite the fact that ke ƴar gayu ce and well

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

1 Comments On BAD BOYS
avatar
fatima-muhammad-1-4

12 months ago

Reply

So sweet

Please Login or Register in order to submit comment