Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[15/07, 2:09 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*NAFISAT*

🌱🌱🌱🌱🌱🌱


NA_Nafisat Isma'il
*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

*EPISODE* (1)

'Yanmata ne su biyu da shekarunsu be gaxa 24years ba, suna xaune a tamfatsetsen Palo da yagaji da haduwa cikin luntsuma-luntsuman kujerun da aka qawata Palon dasu, sun hade Kansu sai latse-latsen waya suke, ihun da sukayi ne yasaka wata matashiyar yarinya da bata haura 19years ba tafito daga dakinta da gudu tana tambayansu lafiya? Bayan data xauna akan hannun kujeran dasuke, wacce ke riqe da wayan CE tamiqa mata cikin xumudi take fadin

Da Allah Ihsan duba kiga wadannan akwatunan sunyi matuqar kyau wlh, su nakeson sweety yamin gaskiya na FASA wadancan da nata6a nuna masa

Ta6e baki Ihsan tayi bayan tagama gani tamiqa mata wayan tana cewa

Ke dai aunty Nafeesa baki da aiki sai ganin abubuwa a social media kina cewa shi yaya xaimiki, duk da laifin Momy ma datake biye miki, ita kuma aunty Baseera tana xugaki shi kuma yaya yana biyewa shirmenki

Hararanta Nafeesa tayi tace

Wato shirme nakeyi ko Ihsan? To laifi ne Dan na xa6i abinda nakeso asakamin? Yanxu fa mun shigo xamanin wayewa ne ba gidadanci ba?

Ke dalla kyaleta 'yar baqin ciki CE wannan yarinyan, in kika biyeta zata maidake sakara CE, in baxata iya gani ba ta6ace anan wajen

Baseera take fadin hakan.. 'Dage kafada Ihsan tayi tana ta6e baki tamiqe takoma kan 3sitter dake nesa dasu kadan takwanta tare da mayarda earphone din dake rataye saman wuyanta cikin kunnuwanta tana latsa waya.. Wayan Nafeesa CE yasoma ringing, murmushi tayi bayan taduba me kiran tace

Kinga dan halak din yaqi ambato

Amsa call din tayi takanga akunni tana ci gaba da murmusawa lokacin datake fadin

Sweety yanxu nake tunaninka araina fa sai gashi kakira

Kyakykyawan murmushinsa me qara masa kyau da kwarjini yayi yana juyawa akan kujeran dayake, cike da nishadi yace

Allah ko Nafee na? But baki kiran ba har nariga ki?

Yafada yana lumshe fararen idanuwansa

Uhm yanxu nakeson fa kiranka, wayan ma na hannuna kakira

Tafada tana sakin murmushi qasa-qasa

I know! that's why naji ajikina, kina gida ne ko school?

Ina gida sweetyna, yaushe xaka dawo?

Maybe sai dare, xan raka Haidar duba kayanSa da'aka sauke mishi ne, kinason ganina ne?

Yaqare maganan yana kwantar da kanshi jikin kujeran.. Dariya tasaki me sauti tace

Akwai labari ne but sai kadawo

Okey kikulamin da kanki bye 👋

Aje wayan yayi saman table yana murmushi tare da kallon Haidar da yabuga tagumi yana  sauraronshi.. Gira daya yad'age 😉

Lafiya? Wannan kallon fa?

Ajiyan heart Haidar yasaki yacire tagumin dayayi yace

Ai Kaine kaxama abin kallo dole nakalle ka, mamaki wlh kake bani kamar ba kai bane kake cewa Momy ta liqa maka jaraba, but now kajone kunata xuba love har da saka rana

Ya son ranka? Kuma nan da one month asha biki ba

Al'ameen yafada yana miqewa tare da miiqa yana yarfe hannayensa

Kai 'Dansa ido tashi muje naraka ka, ka daiji abinda Nafee na tace "jirana takeyi

Tashi Haidar yayi yana dariyan shaqiyanci yace

Ai da katafi kiran nata, ba sai kanunan kana soyayya ba nasani, nima very soon xan shigo layi ai

Da ka kyautawa kanka kuwa

Cewar Al'ameen yana kad'a keeys dake cikin yatsunsa.. Fita sukayi daga office din suna xantawa..

***

RUGAN TARAU

Ruga CE dake jahar Kaduna cikin qaramar hukuman zaria.. Malam Lawali yana daya daga cikin dattawan garin kuma masani ne akan harkan magunguna na gargajiya, shiyasaka yayi fice cikin qauyen, ba ma iya nan ba har cikin birni ana xuwa amsan magani wajenshi, SBD indai kasha maganinsa to insha Allahu xaka samu sauqi sosai wasu ma sun rabu da ciwon kenan, matarsa daya inna Nafeesa da 'yarsa daya Nafeesa suna kiranta da Ummee kasancewar sunan Innanta taci, kafin haihuwar Ummee Inna Nafee tayi haihuwa dayawa 'ya'yan na mutuwa, daga an haifesu xasu mutu wasu ma tun daga ciki take 6arinsu, duk wani taimako da Baffa Lawali xai mata yayi but Abu yacitura, har saida tayi haihuwa takwas ana taran ne aka haifi Ummee, kuma tun daga haihuwarta Inna Nafee take ciwon ciki, kwanan Ummee biyar Inna Nafee tace ga garinkunan, mutuwan ya girgixa Baffa Lawali Sosai, mutuwan da suka daura akan Ummee sai gashi uwar Ummeen CE tamutu, shiyasa tataso cikin gata wajen Baffanta, yana matuqar sonta bayason ko quda yata6a ta, SBD ita CE ma yaqi aure har yanxu dan kawai kar matar uba tamuxguna mata

Ummee yarinya CE 'yar shekara 17 aduniya, fara CE Sol doguwa, tanada kaurin jiki da yalwan gashi, da kaganta kaga kyakykyawan bafulatana, tanada xanen uku-uku agefe da gefen fuskarta, macece mai tsananin kunya in nace muku kunya I mean sosai din nan, ga kawaici ga kirki tayi ne tako INA, tayi saukar al'qur'ani a makarantar allo, boko kuwa dama ba'a magananshi sbd ko primary babu aqauyen..

*

Tafiya take cikin sanyinta kanta dauke da tulu, jikinta sanye da kayan saqa na Fulani

Ummee.. Ummee..

qawarta Hajjo CE take ta kwada mata kiran batajiba, sai da har taxo kusa da ita tana sake kiranta kafin taji tadago madaidaitan idanuwanta takallota fuskarta cike da damuwa

Lafiya Ummee naketa kiranki amma bakijiba? Kamar ma ba'a duniyarmu kikeba, mike damunki?

Bud'e baki tayi cikin tsananin damuwa da yanuna a muryanta tace

Hajjo ni kaina banshan meke damuna ba, tun safe nake jina ahaka kuma gabana na fad'i kamar wani abu xai shameni, ga kuma ciwon Baffo dayau yayi tsanani har ba ya iya tashi, yanxu haka ma akwance nabarshi naxo d'ibo ruwa, bamu da ruwa ko d'igo aradu da ban fito na borshi shi kadai ba

Taqarike maganan cikin rawar murya idanuwanta taf da hawaye.. Cike da tausayinta Hajjo tadafata tace

Ayya shannu.. Ashe jikin Baffan ya kai haka? Dan Allah kidaina shoka damuwa aronki nashon ciwon Baffo ne yake shaki damuwa, kiyi haquri kinji qawata insha Allahu xaishamu lafiya dawuri, kigaisheshi kafin naxo nadubashi kinji ko?

Gyad'a kai Ummee tayi tana share hawayen da yafara sauka saman fuskanta tace

Ai banshon xaki d'ibo ruwan ba da na biyo miki, bari najiraki anan kitai kidibo shemu tai tare

A'a kitafi da Allah kinga kinbaro Baffo gida kar yajiki shiru, she naxo gaisheshi

Hajjo tafad'i haka tana tafiya

.

*Hmm in yamuku inason ganin comments.. Wanda keda qorafi ma yasanar dani qofa abude take.. Love ❤ u fans*
[15/07, 2:15 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*NAFISAT*

🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*3girls with the same name*




NA_Nafisat Isma'il
*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

*Allah kakawo mana qarshen wannan cuta ta corona virus. Ya Allah 👏👏 mun tuba* 😭


*EPISODE (2)*
*Ummee*

Baffo nadawo, in kawo maka furan kasha?

A'a Ummeeta baxan iya sha ba, kidai bani ruwa ne ishi nakeji.

To Baffona, xaka samu lafiya da wuri kaji?.

Tafadi hakan lokacin datake dago kansa tana kafa mishi qwaryan ruwan.. Sallama suka jiyo awaje

Baffo yace Ummeeta tahi kigani wa ke sallama.

To Baffo.

Ta'amsa tana miqewa tafice, koda tafita wani farin dattijo tagani jingine ajikin wata baqar mota, yana sanye da kaya na alfarma, xanen fuskanshi kawai xai tabbatar maka da kanuri ne.. Kanta asun kuye taqarisa wajensa taduqa har qasa tana gaisheshi, cike da fara'a ya'amsa mata yana tambayanta Baffan nata?.

Ayya Baffona ba lafiya, sai dai mushiga kasameshi ciki.

Tafadi hakan tana miqewa har lokacin kanta aduqe yake.. Dattijon cikin tausayawa yaimishi addu'a sannan yabita suka shiga ciki, har dakin takaisa sannan tafito tad'au tsintsiya tana share tsakar gidan da yacika taf da ganyen mangwaro, kasancewar gidan akwai bishiyoyin mangwaro har uku, har tagama wannan dattijon bai fito ba, sai tasami wuri kawai agindin bishiyan tai xamanta tana tunanin rayuwanta da Baffanta murmushi yalwace a kyakykyawan fuskanta.. Bayan wani lokaci dattijon nan yafito yayafito ta da hannu, dasauri taxo taduqa agabanshi.

Ummee Baffanki yace "kikira mishi Liman da Malam Mato".

Da "to Ta'amsa" ta tashi tafice, bata d'au lokaci ba tadawo tare dasu, har cikin bukkan suka shiga ita kuma takoma wajen xamanta tabuga uban tagumi tana jiran fitowansu xuciyanta cike da fargaba, ita kanta batasan iya mintocin data dauka awajen ba kafin sufito, dasauri tadago kanta tana binsu da kallo su ma kallonta sukeyi cike da tausayinta.. Malam Liman ne yace tashiga Baffanta na kiranta.

*

Baffona..

Takira sunanshi lokacin data gurfana gabanshi tana riqe da hannunshi, hawayen tausayinshi cike a idanuwanta ganin yanda yaketa numfarfashi cikin tsananin galabaita, murmushi yake mata idanuwansa akanta yace

"Ummeeta matso kusa dani inason nafadamiki wata magana".

Matsowa tayi sosai taganka kunninta wajen bakinsa, ta d'au lokaci ahaka hawaye nata kwaranya a fuskanta, jin shiru yadena magana yasata kallonshi taga idanuwansa aqafe ba ya motsi, riqo hannunsa tayi cikin kuka tana girgixashi

Baffona.. Baffona da Allah katashi Baffona, karka tafi kabarni Baffona.. Bafffooonaaaaa... Luuu tafada jikinsa asume.

*

Sai da aka kai Baffa makwancinsa sannan Ummee tafarfado, lokacin gidan cike yake da mata 'yan gaisuwa.. Fashewa tayi da kuka 😭 lokacin data tabbatar ba mafarki takeyi ba, Hajjo dake kusa da ita tana xubar da hawayen 😿tausayin qawarta, rarrashinta tasoma yi yayinda sauran Matan suke bata baki, xata baka tausayi yanda take kuka cikin rauni.

Hajjo tace "kiyi haquri da Allah Ummee Baffo ya tafi baxai dawo ba, addu'arki kawai yake buqata, kitashi mutai wajen Liman "yace inkin tahi mu'iskoshi qofar gidanshi".

Haka Hajjo ta taimaka mata suka fito tare da ratsawa cikin mutane, duk Wanda yaimata gaisuwa sai dai Hajjo ke amsawa Saboda kukan da takeyi, Lokacin da suka isa sun gurfana gabansa ga mutane cike da wurin "da duk kan alamu bayani yake musu, saida Liman yaima Baffa addu'a kafin yakira sunan Ummee.

"Nafeesa kiqara haquri da jarabawan da Allah yaimiki, nasan kinsan Baffonki yabada ke ga wannan Alhajin birnin".

Liman din yanuna farin dattijon dake xaune gefensu.

Kuma yanxu xai tafi dake, Malam Ja'e yasanshi har gidanshi, domin shi yahad'ashi  da Baffonki akan ciwon qafarshi kuma Baffon naki ya aminta dashi tunda har yabada ke gareshi, insha Allahu muma xamu biyo sahu muga inda kike abirnin, gonan Baffonki da shanunsa kuwa mun yanke shawaran xa'a saida, Alhajin birni xai aiko a amsan miki kudinki.. Kije gida yanxu kitattara kayanki xaku tafi, Allah miki albarka Allah yajiqan Malam Lawali.

Duk ka gurin suka amsa da amiin.. Kasa tashi tayi saboda tsananin kukan 😭 datakeyi, dakyar Hajjo tamiqar da ita suka tafi, koda suka koma gidan kasa had'a kayan tayi sai Hajjo ne take hada mata, tun da taxauna tatakure waje daya take kuka 😭 kamar ana yankan naman jikinta,. Maganganun Baffa kawai take tunowa.

Allah sarki Baffona.. Katafi ka barni ni kadai aduniyar nan na xama abar tausayi, Inno tatafi kaima katafi ba kowa tare dani, gashi yanxu ka qara rabani da mutanen danasani, ka miqani ga wani wanda bansan shiba, meyasaka Baffona? Meyasaka kayimin haka? Meyasaka bakabarni anan ba? Na tabbata ko Baffon Hajjo xai riqe ni, yanxu wani irin rayuwa xanyi ga mutanen da banshani ba? Banshan ya suke ba. Allah yajiqanka Baffoonaa..

*

Dakyar aka 6an6areta jikin Hajjo, tana kuka itama tanayi tashiga cikin mota suka tafi, tunda tashiga takwantar da kanta saman cinyanta tana wani irin kuka 😭😭 kamar numfashinta xai dauke, Alhajin be ce mata komai ba sai girgixa kansa da yakeyi cike da tausayinta, sai gab da isha'i suka isa cikin kaduna, direct anguwan sarki G.r.a inda tamfatsetsen gidansa yake yanufa.. Ummee batasan ankawo ba sai tsayuwan mota dataji da qaran bude  mota, sai kuma muryan Alhajin dataji yana cewa "tafito" iya gigita Ummee tayi lokacin dataga gidan dasuke, tsoro da fargaba suka d'arsu axuciyanta wanda yahaddasa mata kasa jin me Alhajin ke cewa, saida yariqo hannunta tukun tadawo duniyar data lulaqa, binshi kawai take kamar sokuwa jikinta duk ya saki har suka shiga babban palon gidan... Su Baseera na xaune suka jiyo sallaman Dadyn nasu.

"Sannu da xuwa Dady"

Suka had'a baki wajen fadi cike da farin cikin ganinshi.

Yawwa 'yan matan Dady, kunata hutawa ne?.

Yai maganan cikin fara'a

"Ee wlh Dady"

To ina kuka baro Momyn taku?.

Tashiga daki yanxu, inaga wanka takeyi ma.

Nafeesa tabashi amsa

Ok.. Ke Ihsan ga baquwa nan kikaita dakinki tayi sallah kibata abinci taci kafin nafito.

"To Dady".

Wucewa yayi dakinsa.. su kuma gaba daya suka kafoma Ummee idanuwa kamar xasu cinyeta, ita kam kanta aqasa sai dai tanajin yanda idanuwan nasu yake yawo ajikinta.

Ikon Allah.. wannan kuma daga INA Dady yatsintota?.

Nafeesa tafadi hakan lokacin data dauke kanta gefe tana yamutsa fuska.

Wa yaga bararoji

Cewar Baseera tana sakin dariyan raini.. qara duqar da kanta tayi tana jinta atakure, sai qara matse qullin kayanta takeyi xuciyanta cike da fargaba.. Jin anriqo hannunta yasata saurin d'agowa tana kallonta cike da rauninta, murmushi Ihsan tasakar mata.

Barka da xuwa baquwarmu, biyoni muje karki gaji da tsayuwa.

Kamar sakara haka tabita har cikin dakinta, amsan qullin kayan tayi ta'aje asaman gado sannan tashiga toilet tahada mata ruwan wanka a buckert da ruwan alwala tafito

Yawwa kishiga kiyi wanka gayinan na taramiki ruwan, ga ruwan alwala nan abuta.

Sumui-sumui tashige cikin toilet din, Ummee dai taxama kmr mara jini ajiki ko motsin kirki tagaxa, toilet din kawai takebi da kallo tana jinjina kyawu da tsaruwan wajen "wai shine makewayi, qarshe dai qin yin wankan tayi sai dai tadauro alwala tafito.. Ihsan na xaune gefen gado tana latse-latsen waya tadago tana kallonta

Kar dai ace har kinyi wankan? Amma meyasaka kika maida kayan jikinki? Ai akwai towel aciki da shi kika d'auro.. Ga rigan da naciro miki kisaka.

Ihsan tad'aga wata ash colour din doguwan riga tamiqa mata data Ciro mata cikin kayanta saboda duk ta duba qullin kayan nata bataga wani kayan kirki ba acewarta "shine taxa6o mata anata... Girgixa kai Ummee tayi cikin rawar murya tace

"Ah..a..a kibarshi na..nafison na jikina"

d'age kafad'a 🤷🏻‍♀ Ihsan tayi tamiqa mata hijab tanuna mata wajen sallah da yatsanta batare datace uffan ba taci gaba da latsa wayanta.. Saida tai magrib kafin tayi isha'i, bayan ta sallame Ihsan tamatso mata da abincin gabanta tace

"Bismillah ga abinci, kici ina xuwa".

Tatashi tafice.... Cikin natsuwa tabude abincin "jallof rice ne da naman kaji dana kasuwa ahad'e.. Ba wani burgeta yayiba dan tasaba cin irin wannan kasancewar Baffa na siyo mata duk ranan da yashiga cikin birni.

*"Sai yace Ummeeta yau abincin en burni nakeson kici, banason qi6ata hannunki da miyan kuka da qarnin nono"*

Duk sanda yafad'i haka kuwa dariya 😃 take mishi tace

*"Allah yabarni dakai Baffona, nashan wataran ma burnin xaka kaini"*.

Allah sarki Baffo gashi yanxu sanadinka naxo burni sai dai katafi ka barni.

Hawayen dasuka xubo mata tad'auke da yatsunta sannan tasaka hannu tasoma cin abincin, bata wani ci na kirki ba sabida damuwan dake cinkushe aranta.. An d'au lokaci kafin Ihsan tashigo takirawo ta suka fito palow....
[15/07, 2:17 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*NAFISAT*

🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*3girls with the same name*




NA_Nafisat Isma'il
*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

      *EPISODE (3)*
       *(Dady)*

Tun sanda Ummee tagaida Momy ta'amsa ayatsine jikinta yasake yin sanyi laqwas, da alamu dai bata kar6u gidan ga ba,.. Gyaran murya Dady yayi yasoma da cewa:

Hajiya Bilki ga baquwa ko ince 'ya, dan amana CE mahaifinta yabani, kuma xanso kitayani riqe wnn amanar, inbaki manta ba kwanakin baya INA xuwa rugan tarau amsan maganin qafa alhamdulillah har nasamu sauqi, hakan yasa nace xan koma in mishi godiya, to bai samuba sai da yau danaje Zaria nace to bari in wuce tunda qarisawa ne, to axancen dai danake miki malamin shine mahaifin yarinyan nan Ummee Nafeesa, lokacin da tayimin iso wajen mahaifinta na sameshi cikin matsanancin hali, ma'ana dai yana ahalin rashin lafiya, yana kuka yana fadin

"Allah sarki Ummeeta xan tafi in barki baki da kowa, nasan wnn ciwo nawa banatashi bane, naso na aurad dake kafin wannan rana taxomin amma hakan be yuwu ba, Ummeeta kiyi haquri naso naga auranki, naso naga auranki naso naga auranki"..

Wannan Kalmar yaketa maimaitawa yana kuka, wlh na tausayawa bawan Allan nan 'hakan yasa nayanke hukunci kuma naroqe shi da indai ya yarda dani ya amince da baxanci amanar saba, yabani 'yarsa ni kuma xan riqeta amana baxa tayi rayuwar maraichi ba insha Allah, wlh mutumin nan ya amince, ataqaice dai ban baro can ba sai da aka daura wa Al'ameen aure da Ummee

Wani irin xabura Momy tayi cikin kad'uwa tace

Alhaji wani Al'ameen?

Kinada wani Al'ameen din ne bayan d'an mu

Cewar Dady yana murmusawa... Nafeesa data fad'o qasa tai xaman 'yan bori tuni hawaye sun wanke fuskanta, muryanta na rawa tace

Dad..kana..kana nufin wnn CE matar Al'ameen dina? Ni..ni kuma fa Dady? Ko kamance nice xai aura?

Ban mance ba Nafeesa, kuma maganan tana nan insha Allah..

Taran numfashin shi Momy tayi da cewa

Ai ko wlh baxai ta6a yuwuwa ba Alhaji dole araba auran nan, ni xakama wulaqanci? Yo ba dole ubanta ya amince ba tunda yasan 'yarsa xata shigo daula..

Haba mana Bilki, baki ganin yara kike d'aga min murya?

Jin haka yasa Ihsan takama hannun Ummee suka koma daki, itama Baseera riqo Nafeesa dake faman shar6an kuka tayi sukabar palon

Yanxu menene aibun wnn abun danayi iyee Bilkisu? Ina taimako nayi? Kuma ke yakamata ki goyamin baya

Haba Alhaji wani irin taimako ne wnn xaka dau 'yar qauye ka aurawa d'anka, kuma bayan kasan akwai maganan Nafeesa, meyasaka in taimakon xakayi baka taho da itaba inyaso sai kahadata da wani, to gaskiya baxan lamunta ba dole araba auren nan wlh

Ran Dady a6ace yamiqe yana fadin

To baxa'a raba din ba haka naga daman yi, ai nasan da wasu na aurawa d'an nawa tunda nasan na isa dashi dole yaimin biyayya, bari kiji wlh indai har kikaga an raba auran nan to ki tabbatar baxai ta6a auran Nafeesa ba, xata xauna anan inyaso xa'a hada bikinsu sutare gaba daya

Yana fadin hka yabarta nan,. Cike da sanyin jiki itama tanufi dakinta xuciyanta na mata quna, ba haka dai rai yaso ba saidai ba yanda xatayi ne

*

Dady ne xaune cikin bedroom dinsa yana sanar da Al'ameen abinda ke faruwa

Ina fata  xakamin biyayya kuma xaka tayani riqe amanar dana kar6o?

Cikin sanyin murya Al'ameen yace

Insha Allahu Dady xan riqeta kmr ita CE xa6ina, kuma baxata ta6a kawo maka qarata akan nayi mata wani Abu mara kyau ba

Haka nakeso Allah yamaka albarka, za'a hada bikinta da Nafeesa inyaso sai su tare atare, tunda dama gidanka part biyu ne sai ka sakata anakan ko?

Eh Dady

OK to karka wahalar d kanka wajen mata kayan daki "ni ne xan mata komai kai sai kaji dana Nafeesa, tashi kaje Allah yadafa maka yamaka albarka

Da amiin ya'amsa sannan yamiqe yafita,. lokacin da yafito palow ba kowa sai Nafeesa, itama dan taga shiganshi ne taxauna xaman jiranshi, har yanxu kuka takeyi gaba daya ta furgice SBD tashin hankali, cike da sanyin jiki yaxauna kusa da ita

Me kikeyi har yanxu baki barci ba?

Kallonsa tayi da idanuwanta da sukai jawur tace

Kana tunanin xan iya barci adaren nan bayan bani da kwanciyar hankali? Kishiya fa Dady yaimin, meyasaka xaimin HaKa meyasa?

Tafad'a cikin tsananin kuka... Yatsanshi yadaura saman bakinta

Shiiii 🤫 ya iSA haka Nafeesa, menene na tada hankalinki bayan kinsan ke ce kadai yanxu a xuciyata, ko so kike nima kiga irin damuwan d nake ciki?

Girgixa kanta tayi hawaye na xubo mata

To kishare hawayenki tunda dai kinsan kece araina, be kamata kitada hankalinki akan wata 'yar qauye ba, biyayyan Dady ne xai xaunar d ita gidana banaso kina tadamin hankalinki akanta, yanxu muje kibani abinci yunwa nakeji inyaso sai kibani labarin magananmu ta daxu ko? Yawwa aN Nafee naa tashi muje

Batasan sanda tasaki yalwataccen murmushi ba "tamiqe suka nufi daining table

.

***

Asalin Alhaji Abubakar Khabeer Cindo da matarsa Hajiya Bilkisu Usman Cindo mutanen Maiduguri ne, familyn su babba ne sosai kuma suna yawan yin auren xumunci,.

Kasuwanci yakawo Alhaji Khabeer Cindo garin Kaduna acan yake da xama tare da matarsa Zainab da 'ya'yansu hud'u, Abubakar Hasna da Husna sai auta Hafsat, koda suka girma 'ya'yan nashi a can Maiduguri cikin dangi yaxa6a musu maxajen aure "yanxu haka acan suke xaune, shima Abubakar da yagama karatunshi can yaje yanemi 'yar qanin Babanshi ya aura suka tare agidanshi dake anguwan Sarki G.r.a cikin Kaduna.. Koda Bilkisu taxo da qanwarta Hannatu tataho xataci gaba da karatu anan

lokacin an haifi Al'ameen da shekara 4 Hannatu tasami miji d'an nan  Kadunan ta aura, bayan biki suka d'aga England kasancewar acan mijinta yake aiki.. Al'ameen nada 6years Momy Bilkisu tahaifi Baseera, alokacin ne kuma Hannatu itama tahaifi 'yarta Nafeesa

Lokacin da Hannatu da mijinta Aliyu sukaxo Nigeria sunbar Nafeesa wajen Momy akan xatai musu Hutu, da xasu koma ne sukai hatsari a hanyansu taxuwa airport kuma suka rasu, Momy kuma tace baxa'a rabata da Nafeesa ba, lokacin da tahaifi Ihsan kuma tace asaka mata suna Hannatu, ba musu Dady ya amince

Rayuwa taci gaba har girmansu da mutuwan su Alhaji Khabeer da Matarsa Zainab.. Yanxu haka  Baseera da Nafeesa suna final year a KASU (Kaduna State University) ita kuma Ihsan tana matakin farko ne, Al'ameen ya xama cikakken likita yana aiki a babban Hospital na gwamnati anan Kadunan

Tun tasowarsu Momy take tusa mishi Nafeesa kasancewar itama tana sonshi, tun baya ra'ayinta har dai yasoma kulata suka fara soyayya "gashi yanxu har xasuyi aure, ba wanda yafi Momy farin cikin wannan al'amari, domin tana matuqar son Nafeesa sosai that's why takeson Al'ameen ya aureta sai ayi tuwona maina 😋 💃

Al'ameen dai ingarmar namiji ne Wanda yahadu tako ina, fatarsa ja ne ba fari ba "yanada kyawu kasancewar gaba dayansu sunyi gadon kyau din, mutum ne mai sanyin hali baya da damuwa ko kadan, yanada kirki da tausayi kuma baya da hayaniya, rayuwansa dai very simply gunun sha'awa.

.

*Ina sonku masoyan littafin  NAFEESA*

Karku manta kuci gaba da haquri.. in kunji yunwa ku wanke hannu kuci gaba da haquri komi xaiyi qarshe..
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment