Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na soma jin zazzaɓi ya soma kama Ni, komai ina yi ne cikin ƙarfin hali sabida yanda ciwon yake ɗan ci na kaɗan-kaɗan, sai kuma ciwon ciki da ta sako Ni gaba, a ranan da cikina ya soma ciwo kamar zan yi hauka, kuka na dinga yi na cika gidan da ihu na

Har sai da Yaya Ahmadi ya shigo sashin namu yana cewa, "wai ke Madina lafiya kike wannan ihun? Ina mutanen gidan? Kuna ciki ashe dan uwarku take ihun nan ku kayi shiru?" Ya ƙare maganar da faɗan hakan; bayan ya buɗe labulen dakin ya ga su Fa'iza da Fatimah zaune sun tasa Ni a gaba, ina kuka na jiƙa fuskata sharkaf da ruwan hawaye

Duk sai suka ruɗe suna cewa, "mun ce ta sha magani ta ƙi sha ne, kuma yanzu Inna Lami ta shiga sasan Baba Sama'ila ta amso mata na ciwon cikin."

Shigowa dakin yayi yana kallona sosai, tare da cewa, "me ke miki ciwo ne Madina?"

"Cikinta ne wai, da zazzaɓi." Nafisa ta ba shi amsa jikinta na rawa don sun san halin su babu wasa yayyin nasu, musamman ma shi da Yaya Shamsu, akwai saurin hannu

"Ku ɗaga ta ta sha maganin."

Da sauri suka ɗaga Ni suka kafa min kofin da aka jiƙa magani a ciki. Babu musu na soma sha duk da ɗaci da baurin da ke ciki; saboda tsoron ganin Yaya Ahmadi a kaina don na san idan ban sha ba ubana zai ci,
Ganin na sha sai ya juya ya fice,
Ni kuma na kwanta ina ci gaba da kukana a hankali riƙe da ciki na

Inna Lami da Inna Habiba suka shigo ɗakin a tare

"Wai cikin ne har yanzu?" In ji Inna Habiba da ke kallonmu

"Wlh kuwa. Nima na je samo mata magani ne wajen Zainabu ta haɗa ta sha ko zata samu sauƙi, idan kuma bai yi ba a je a kira Jummai mai magani ko Malam Bala Na-Allah. Ɗago ki sha."

"To Allah ya sawwaka." Inna Habiba tace hakan tana fice wa

Ni kuma aka bani maganin na sake sha sannan na kwanta. Duk na takure waje ɗaya ina ta hawaye. Sai can kamar ya lafa ashe wahalan na gaba, wani irin ciwo da ya turniƙe Ni lokaci ɗaya numfashina ya soma sama da ƙasa, haka nake kuka ina kiran sunan Ummana kamar zan mutu

Duk sasan an yi cirko-cirko sabida yanda na gama ruɗa su da ihuna. Har sai da Baffa tare da YaYa Nasiru suka shigo sasan suna tambayar lafiya? Aka faɗa musu halin da nake ciki

Baffa yace, "a aika a kira Jummai ta zo ta duba Ni."

Da gudu A'isha ta je ta kira ta. Babu jimawa sai ga su sun dawo tare, ta shiga ta soma duba Ni,
A lokacin har jini ya soma zubo min daga wando na, ban san mene ne yake zuba ba amma ina jin danshin sa

Jummai ta gane Al'ada ne ya zo min, shiyasa ta duba magani ta bani sannan tace, "ai al'ada ne ya zo mata, kuma da alamu ya zo mata da gardama domin ciwon al'ada ba ya denawa har sai an kai mutum ɗakin Mijinshi, Allah yasa ma abun ya zo da sauƙi an yi auren, amma ga wannan maganin a riƙa jiƙa mata tana sha zata rage jin raɗaɗin ciwon, Allah ya sawwaka."

"Amin AMin." Duk suka amsa mutanen sasan

Sannan Baffa ya bata kuɗin maganin nata bayan ta faɗa mishi. Ya dubi Inna Lami yace, "don Allah a kula da ita yanda yakamata, Allah ya bata lafiya, Ni bari in je sai in Yi ma Baban sasa bayanin halin da ake ciki."

A cikin mintuna ashirin har ciwon ya lafa min wani wahalallen barci ya ɗauke Ni. Lokacin da na tashi gaba ɗaya jikina ya jiƙe da jini, duk kunya ya kama Ni tunda ina jin abun da aka ce ya same Ni, Ni wato nawa bai zo a cikin sirri ba sai da mutanen gida suka sani, ashe wancan ba jinin Al'ada bane, mai sosan yana gaba


Nafisa na zaune gefe na tana kallona, tun lokacin da ta ga na motsa hankalinta ya dawo gare Ni, sai ta soma min sannu tare da cewa, "Inna tace idan kin tashi akwai ruwan zafi a coolern ta na kichen ki ɗiba kiyi wanka, sannu gaskiya na tausaya miki domin naki ya zo da wahala, mu kuwa kinga duk cikin mu babu mai ciwo sai dai mu ga ya zo, kinga Ni na wata uku fa na taɓa yi, sai in yi wata biyu ma ban sake yi ba, shiyasa nake murna wlh don Ni na tsani jinin nan inga yana zuba, sai duk hankalina ya tashi, ke ma yanzu kin shiga sahun mu kin zama babba." Ta ƙare maganar kuma tana dariyan shaƙiyanci; kasancewar ta da son wasa da raha

Ni dai ban ce mata komai ba illa ƙoƙarin tashi zaune da nayi, sai nayi shiru ina tunanin yanda zan tashi in fita a wannan halin

"Ko in sake miki ruwan wankan ne in kai miki?"

Gyaɗa mata kai nayi batare da na kalle ta ba, domin wlh kunyan haɗa idona da kowa nake ji

Haka ta sake min ta dawo ta faɗa min, "ruwan yana bayi in je in yi."

Dole na na tashi ba don ina so ba, sai kare jikina nake yi ina harharɗe ƙafafu na gaza fita

Nafisa tana ganin yanda jinin yayi min sai ta zaro ido tare da cewa, "Kai! Haka jinin yayi miki? Kinga yanda ya ɓata miki jiki kuwa?"

Kamar in nutse a ƙasa haka nake ji, har hawaye ne suka soma taruwa a kwarmin idanuna saboda maganar da Nafisa take min

Ita kuwa bata lura ba sai ƙara kururuta yawan jinin take yi tana mamakin yawan shi, "wai kuwa kinga yanda ya ɓata miki jiki? Kai ji be ma wurin da kika tashi, ko dai ciwo kika ji?" Ta ƙare maganar tana kallo na, sai ta ga yadda nake hawaye kashirɓan ƙiris nake jira in fashe da kuka, nan kuma hankalinta ya tashi ta soma tambayana abun da ke faruwa? ganin na kasa magana jikina sai rawa yake yi sai ta fita da sauri ta je ta sanar da Innarta

Sai ga su sun dawo da Inna Lami, itama ganin yanda jinin ya zuba ta tausaya min, ta kalle Ni tace, "to mene ne na kukan ko har yanzu kina jin ciwon ne?"

Girgiza mata kaina nayi ina kai dukka hannayena saman fuskata; tare da share ruwan hawayen da ke ɗiga min

"To wuce ki je kiyi wankan, Allah ya kyauta gaba, ke kuma Nafisa fito da katifan ki wanke mata."

"To Inna." Nafisan ta amsa mata tana yin abun da tace

Ni kuma tuni na fice daga ɗakin na wuce makewayi. Daga bayin ina jin Inna Lami tana sanar da su Inna Asabe halin da nake ciki, sai Allah ya kyauta suke min

Inda har Inna Habibah take cewa, "ai sauƙin ta ma an yi mata aure za a huta, ko matsalolin ciwon cikin ma zai ragu."

Wankan nayi tsab sai na ɗaura ɗankwalin kayan nawa a ƙuguna; tunda skirt ɗina ya ɓaci, a haka na fito jikina a buɗe illa daga ƙuguna zuwa cinyana dana rufe, kuma ban damu ba tunda na saba yin hakan kasancewar ganin bani da komai da zan iya ɓoyewa, kunyata kawai yanda na fara Al'adan nan kowa ya sani, har ba na son haɗa idanu da mutanen sasan

Inna Lami ta taimaka min ta nuna min duk yanda zan yi, har ƙunzugu ita tayi min da tsumma na saka da wando, gaba ɗaya a ranan ji na nake yi a wani irin baƙon yanayi, sam na kasa sakin jiki na saboda jin yanda ƙasana yake a takure; sakamakon saka tsumma da kuma jinin da nake fitar wa, a haka na wuni sukuku babu wata walwala a tattare da Ni, duk da dama Ni ba Mutum bace mai yawan magana sai idan ina tare da Yaya Haula ko Ummana, da su kaɗai nake iya sakin jikina; a wajen mutane kamar farar Kura haka nake; ga miskilancin tsiya

Kwana na biyu ina wannan halin, har Yaya Haula ta zo ta gaishe Ni duk da jikina da sauƙi amma jefi-jefi ina fama da ciwon ciki

A rana na uku ne na samu sauƙi jinin ya ɗauke gaba ɗaya, shiyasa nayi wanka kamar yanda aka koya mana a islamiyya

A kuma ranan ne sai ga Alh. badamasi ya zo gaishe Ni; kasancewar Baffa ya sanar mishi halin da nake ciki. A falon Baffan ya jira Ni kamar yanda ya saba zuwa

Bai jima ba nima na shigo falon ina sanye da riga da zani na atamfa baƙa da kalan yellow a jiki wanda aka yi kwalliya, duk da kayan sun koɗe amma sun amshi farar fatana sun yi min kyau, har ɗaurin ɗankwali Fatimah tayi min ga sabon gyale na Nafisa da na saba saka wa duk idan zan je, nayi kyau fuskata da hoda da tozali sai man baki

Shi kansa alamu ya nuna ya ji daɗin gani na a haka, nan da nan ya washe bakinsa yace, "in matso kusa dashi."

Babu musu na isa inda yake amma na kasa zama, sai ya kama hannuna ya zaunar da Ni a saman cinyansa kamar yanda yake min, ya kalle Ni da murmushi bayan ya ɗago fuskata yace, "kin yi kyau Matata, yau har da kwalliya kika yi min?"

Ban san sanda nayi murmushi ba har ƙasan gemu na yana lotsawa, wanda sosai yake ƙara min kyau idan nayi murmushi ko nayi dariya ya fito, sai na sunkuyar da kaina ina wasa da hannuna

"Na ji daɗin ganin ki a haka, dama Baffanki ne yace min kina fama da rashin lafiya shiyasa na zo duba ki." Sai yayi wani murmushi har da sauti yana ƙara cewa, "Ashe Amaryan tawa ta girma ne?".
  
[23/06, 6:56 AM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
    *RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

         *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._










______________ *EPISODE 8*
 _____Saurin rufe idanuna nayi sabida kunyar abun da ya faɗa

Shi kuma sai yayi dariya, alamun hakan bai dame shi ba, ya sake cewa, "Oh ƴar Amaryata ta girma yanzu, bani da wata matsala tunda ko yanzu aka bar Ni dake za ki iya dani, ko kin fi son nayi ma Baffanki magana ya bani ke mu tare a gidana?"

Saurin girgiza masa kaina nayi bayan dana buɗe idanuna, ba wai don na fahimci mai yake nufi ba

Murmushi yayi yace, "har yanzu kina nan ba ki yarda dani ba ko? Na ce ki ɗauke Ni kamar Babanki amma kin kasa sakin jikin ki dani, ko kina tunanin zan yi miki wani abu ne idan kika koma gidana?"

Shiru nayi masa ina sake sunkuyar da kaina

Sai ya ɗaura hannunsa a saman ƙirjina yana shafawa, ina jin sanda ya saki numfashi tare da kawo bakinsa kusa da kunne na yace, "to faɗa min, kin gama jinin da kike yi ne?"

Ban san sanda na runtse idanuna na ƙanƙame shi ba tsaban kunya kamar in nitse

Shima hannu yasa dukka biyun ya kama Ni sosai yana raɗa min, "ƴan Matana kin cika jin kunya wlh, naga ranan da za ki saba dani, shiyasa na ƙosa a kawo ki gidana ko don mu riƙa yin wasa ko? Kina son mu riƙa wasa tare?"
Jin nayi shiru ina ta ƙara ɓoye fuskata a jikinsa, sai yace, "kin cika jin kunyana, ki rage kinji? Ko ba kya son in riƙa siyo miki ƴar tsana a birni ne? Da wannan chocolate ɗin da na siyo miki?"

"Ina so."

"Yauwa ko ke fa, to ɗago kanki ki dena jin kunyana."

Ɗagowa nayi kamar yanda ya buƙata. Sai yace, "gobe zan tafi birni, ban manta da alƙawarin ki na kaya ba, zan siyo miki in na dawo, ki riƙa min irin wannan kwalliyan kinji zan ji dad'i."

Kaina na gyaɗa mishi ina jin farin ciki a raina

Shima sai yayi murmushi yace, "yauwa ƴar gatan Babanta, to yi min addu'ar tsari idan na tafi in samo kuɗi masu yawa kinji ko?"

Murmushi nayi na ɗaura hannuna a saman fuskata, a hankali na furta, "Allah ya ba ka abun da ka je nema."

"Amin Amin Amaryata, na ji daɗin addu'ar ki, ina sonki sosai, za ki ji dad'i idan kika zo gidana, komai zan riƙa miki in kina min biyayya." Ya ƙare maganar yana ci gaba da shafa Ni

Ba tare da Ni na damu da abun da yake min ba, sabida ko kaɗan ban kawo komai a abinda yake min ba, Ni dai ina farin ciki sabida abubuwan da yayi min alƙawarin zai siyo min. Sai da ya sallame Ni sannan na tashi na tafi

Yau ma sun yi tunanin zan shigo da wani abun ne, shiyasa Inna Asabe ta kasa ta tsare tana gani na sai ta taho wuri na tana tambayana, "ko ya bani wani abun ne?"

Nace mata, "a'a."

Sai ta ja tsaki ta wuce abun ta tana surutai kamar ta aike Ni

Haka su ma su Nafisa suna ganin na shigo daki suka soma tambaya na,
"Allah yasa dai ya kawo miki wannan abun mai shegen daɗin tsiya? Ke kam kin more wlh Madina."

Zama nayi a gefen katifana ina yaye gyalen jikina, tare da furta, "bai bani komai ba yau."

Dukkan su fuskokin su ta nuna rashin jin daɗin su,
Amma sai suka share suka ci gaba da hiran su, don dama hiran wata ƙawarsu suke yi na cikin anguwa, Hansai,
Dayake jiya Luba ta je gidan su; shine take basu labarin abun da ta gani a gidan, tana tsegunta musu yanda ta ga tana yi da wanda aka yi musu baiko, gidan babu kowa Allah ya faɗo da Luba ta biya ta gidan da Innarta ta aike ta, shine fa ta gansu suna iskanci,
Ita kuma yanzu take shafa wa su Nafisa labari,
Har wani rage murya take yi don kar su Inna Lami su ji

Ni kuwa jin abun da take faɗa, shiyasa nima na kasa kunne ina sauraro duk da ban gama fahimtar maganar sosai ba, tunda ba dani aka somo ba

Inna Amarya ce ta leƙo tana cewa, "wai ku uwar mai kuke yi a ɗaka baza ku fito ku sha iska ba?
Munafurcin mai kuke yi?"

"Wlh Inna babu komai." A cewar Luba tana watsa hannaye,
Yayinda su ma dukkan su suka basar suna ɓashe baki kamar ba abun da suke yi,
Har Binta tana ƙarawa da faɗin, "Inna Amarya labaran duniya muke yi shiyasa kika ji mu mun nitse ciki."

"Ku dai ku ka sani, ke Madina taso ki ɗebo min ruwa a rijiya in tace ƙullun nan."
Tayi maganar tana sakin labulen tare da wuce wa

Nima kuma sai na amsa mata ina mike wa tsaye, tare da ajiye gyalen Nafisa a jakar kayanta, na fice da sauri,
Dama hakan ke faruwa dani kodayaushe, ba sa son su ga na huta ko misƙala-zarratan, Ni kaɗai ce baiwa a gidan, kuma dayake ba na ƙyuya sannan bani da son jiki, tuni na ɗauki bokitin na nufi hanyar rijiya da ke cikin gidan a can wani makewayi ta bayan sasan Baba Iro,
Can na nufa na saka ƙatuwar gugan da ke ɗaure a rijiyan, cikin ƙanƙanin lokaci na cika farin bokitin, na ɗauro shi a kaina na kawo mata

"Yauwa, kinga yanzu sai in tace har in gama in leƙa gidan Abashe, tunda na ji an ce Matarsa ba lafiya."

"Wai da gaske ne ashe? Ɗazu Yusuf yake sanar min ina ce ƙarya ne tunda na ji maganar bata shigo cikin gidan ba."
A cewar Inna Habibah da ta fito daga ban-ɗaki tana riƙe da buta, ta samu wuri ta zauna a saman dutse kusa da kichen

Ita kuma Inna Amarya take bata tabbacin, "da gaske ne wlh, ɗazu Baraka ta shigo take faɗa min, wai jikin ma ya matsa mata kuwa. Madina ɗauki sake min ruwan a wannan Bawon ki ƙaro min sahu ɗaya."

"To." Na amsa mata ina juye wa kamar yanda ta bani umarni, na ɗauki bokitin na koma rijiyar, har na je na dawo suna maganar rashin lafiyar ne,
Inda Inna lami ma ta fito daga ɗaki rike da ɗankwali a hannu tana tsulma musu baki, fuskar nan nata ta tasa da alamun daga barci ta tashi,
Tana gani na tace, "zubo min ruwa a buta Madina, nima in yi sallan nan sai mu leƙa su.
Ina su Nafisa? Kuna ina; baza ku fito kuyi sallah bane kuna jin har an kira lokaci zai ƙure?"

"Gamu nan Inna."
A cewar Nafisan ita da Fatimah da suka amsa a tare

Su kuma suka ci gaba da hiran su har na kawo ma Inna Lami ruwan, sannan na juya na ɗauki butan nima na shiga bayi,
Zuƙuna wa nayi ina fitsari amma wani irin zafi ne yake tsarga min, hannu na tara a fitsarin nawa na ji zafi kamar an tafasa, abun ya bani mamaki amma ban kawo komai a raina ba, illa tunanin meyasa fitsari na yake zafi yanzu kamar an saka a wuta? Ga kuma wurin yana min zugi har da ƙaiƙayi, hannu na sa na dinga sosa wa kamar zan ƙwantale fatar jikina, azaban ya ishe Ni hakan yasa na saka hannu biyu ina gurzan jikina sabida azaban ƙaiƙayi, kamar zan yi kuka haka na dage ina ta abu ɗaya,
Har sai da na ji muryan su Nafisa suna maganar, "na bar su a tsaye zasu zaga na ƙi fitowa."
Dole nayi tsarki na mayar da wandona na fito daga bayin,
A nan bakin kofan na tsaya zan soma alwalan

Fa'iza tace, "idan kin gama ki bani butan."

Dayake Nafisa da Luba sun samu nasu butan, shiyasa ina fitowa Nafisa ta fara shiga bayin, daga baya Luba ta shiga bayan ta fito

Ni kuma ina gama wa na wuce daki nayi sallan nawa; sannan na fito ina amsa kiran Inna Asabe da take min,
Aiki ta sanya Ni na tsinke ganyen alayyahu wanda zamu yi miyan dare

Da ɗai-ɗaya suke fito wa duk wanda ya idar da sallan,
Kowa ya kama aikin da ke gabansa tunda har biyar tayi,
Su Luba kuwa kai tsaye sashin su suka wuce su da Nafisa, suka koma can suka ci gaba da hiran su,
Babu wanda ya damu dasu a cikin su Inna Lami bare ya sanya su aikin, sai dai Ni Jaka, in da sabo ma na saba wlh,
Ina gama wa aka sanya ni share tsakar gidan,
Haka na ɗauki tsintsiya na ƙalƙale ko'ina, tun daga ɗakunan su har filin sasan, na fice da sharan zuwa haraban tsakar gida, a can na tara ina kwashe wa sai ga su Baffa sun shigo shi da Baba Iro

"Ah! Wa nake gani haka kamar Madina? Shara da Magriba?"

Sannu da zuwa nayi musu ba tare da na amsa maganar nasa ba, illa ma sunkuyar da kai da nayi cikin ladabi

Suka amsa min, inda Baba Iro shi tuni ya wuce sashin sa tunda akwai kaya a hannunsa

Shi kuma Baffa ya tsaya yana min tsiyan yin shara a wannan lokacin, yace, "in riƙa yi da wuri ban da irin wannan lokacin."

Na amsa mishi da, "to."

"To maza ki kwashe ki tashi a wurin."
Ya ƙara furta wa yana yin gaba zuwa nashi sasan

Kafin ma in bar wurin haka Matasan gidan suma sai shigowa suke yi, kowa ya dawo daga aikin sa, duk wanda zai wuce sai nayi mishi sannu da zuwa,
Ina kwashe wa na zuba a kwandon sharan da ke hanyar ƙofan gida

Yaya Shamsu ne ya shigo a lokacin, firjan-jan tamkar wanda aka koro shi duk yayi biɗi-biɗi da alamu daga gona yake tunda yana rike da fatanya,
Har zai wuce ya ji siririyan muryata ina mishi sannu da zuwa, sai ya dawo da baya yana faɗin, "wace ce nan?"

Da sauri na amsa mishi, "Ni ce Madina."

"Yauwa, shiga sashin mu ki ce wa Innar mu idan akwai ruwan zafi a zuba min yanzu, ki ɗauko ki kawo min kofar daki na."

Amsa mishi nayi ina wuce wa, sai da na ajiye tsintsiyan hannuna sannan na wuce kai tsaye ɓarayin Baffa, a can na haɗu da su Nafisa suna alwala,
Shigowar Baffa ne ya kaɗa su yace, "su yi alwala suyi sallah ana kira."
Kai tsaye dakin Inna Uwa na wuce, uwar gidan Baffa, har ɗakin na shiga, ganin tana sallah shiyasa na fito muka ci karo da Baffa shima yayo alwalan yana sauri zai wuce masallaci, tunda a lokacin an kira,
Yace, "Madina me kike yi a nan ba ki ɗauki buta kin yi alwalan ba ke ma?"

"Yaya Shamsu ne ya aiko Ni wurin Inna, shine zan sanar mata."

"To ɗauki buta ki yi alwalan kafin ta idar da sallan, nima na shiga na ga tana sallah."
Yana ida maganar ya wuce da saurin sa ya fita sashin yana gyaran murya

Nima sai na wuce nayo alwalan,
A lokacin Inna Uwa ta idar da sallan har ta fito tana tambayana, "me Shamsun yace?"
Shine na faɗa mata saƙon sa

"To ai bai gama zafi ba, bari ki jira sai in sake mishi kikai mishi."

"To Inna."
Alwalan na ƙarisa, na koma kusa da su Fa'iza da ke tsakar sasan sun baza tabarma suna sallah a wurin, nima na tayar da kabbara, ina idar wa ban jira nayi addu'a ba tunda na ji Inna Uwa tana kwaɗa min kira, shiyasa na tashi da sauri na wuce kichen ɗin su

"Ɗauka ga shi nan na zuba mishi, kar kuma ya ji shiru."

Ɗaukar bokitin nayi ɗakyar na nufi sashin Samarin gidan, a bakin kofan sa na ajiye masa ina kwaɗa sallama, da alamun basu dawo daga masallaci ba shi yasa nima na wuce abuna na koma sashin mu.
***

_____Sai ƙarfe tara muka haɗu muka ci abincin dare kamar yanda muka saba, kowa ya baje a tsakar gidan ana ta raha da hira,
Dukka Iyalan Baban sasa ne sai mu ƴan Matan da muke kwana a sashin,
Masu saurin barci tuni sun soma hamma, wasu har sun kwanta a wurin,
Nima har dani tunda ban da jimirin zaman hira, tun ina jin su Binta sama-sama suna magana da shewa, har dai na ji ɗib na dena jiyo su, tuni wani nannauyan barci ya kwashe Ni

Sai can sama-sama na ji ana tashi na in koma daki,
Haka na miƙe na koma dakin mu na kwanta na ci gaba da barcina, sai asuba na farka nayi sallah,
Daga nan kuma ban sake samun damar koma wa ba sai aiki kamar yadda na saba

Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya tun ina ƙirga kwanakin dawowar Alh. Basamasi har na cire ran ganin sa, tunda ga shi kusan sati biyu babu labarin sa,
Sai da muka yi wata ɗaya curr sannan ya zo gidan, dama da abun a raina na kayan da yace zai kawo min, shiyasa tunda aka zo kira na yana jira na, shiyasa na dinga murna, a raina ina addu'ar, "Allah yasa har da kayan dad'i ya kawo min."

Ilai kuwa, leda shaƙe ya zo dashi na tsaraban da yayi min, bai manta alkwari ba har kayan saka wa sai da ya zo min dasu guda biyar, dogayen ruguna ne ƴan kanti dai-dai jikina, guda uku sai riga da skirt guda biyu, dukka sababbi a ledan su, sai takalma guda biyu da gyale guda biyu, sai kuma ledan sweets da chocolates bakitin ɗaya

A sanda ya nuna min kayan; wani irin dad'i ne ya rufe Ni, tuni na washe baki na bi ina ɗaɗɗaga kayan, cikin yarinta irin nawa nake ce mishi, "wannan duk nawa ne wai?"

"Kwarai kuwa Amaryata, wannan duk naki ne, na siyo miki ki min kwalliya da su."

Baki na washe ina kallonsa, cikin farin ciki da ɗoki nace, "wlh ba a taɓa siyo min irin wannan kayan ba, ko na sallana waɗannan sun fi kyau."

Dariya yayi cike da nishaɗi, yace, "in taso in zauna a kan cinyansa."

Da kaina na ɗare saman cinyan nasa, bayan na ɗauki sweet ɗaya na buɗe na saka a baki ina jin wani irin daɗi na ratsa Ni

Shima kuma nan ya ƙanƙame Ni a jikinsa yana labarta min, "in har zan riƙa yin abun da yake so, komai zai siyo min, idan ma sallah ta zo wanda ya fi wannan kyau zai kawo min."

Ai nan na dinga jin daɗi, a raina kuwa har Allah - Allah nake yi Yaya Haula ta zo in bata labari ta ga kayan

Dayake shima Alhajin sauri yake yi, yau bai jima ba ya sauke Ni a jikinsa yace min, "zai wuce, amma zan gansa aka-akai yanzu tunda yana gari."

Murmushi nayi masa nace, "na gode Baba."

"Babu komai Amaryata, duk abin da kike so kawai

Please Login or Register in order to submit comment