Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan ne sarki hinzur ya dubi sarkin yaki zabbagu
yace da shi
"Ya kai sarkin yaki birnin tehran shin ta ina wayannan
runduna suka bi har suka shigo cikin wannan fadan"
.
Sarkin yaki yace " ranka shi dade ina kwance bisa
shimfidata naji sautin busa toh a sannan ne nasan an
kawo mana harine ,"
Wani badakare dake gefe yazo ya durkusa agaban
sarki hinzur yace"ya shugabana muna cikin aikinmu
na bada tsaro , kwatsam sai gani mukayi sun bayyana
rike da makamai a hannuwansu"
.
Koda sarki yaji haka sai ya bada umarnin a kwashe
gawarwakinsu a tafi a kona, nan ya wuce zuwa
turakarsa ,
Washe gari kuwa afada sarki hinzur ya nuna tamkar
bai damu da al'amarin daya faru jiya da dare ba
.
Amma a boye ya saka wani bokansa mai suna
KAMSUSULJANI yayi masa bincike
.
Kwanaki suka ringa ja harzuwa watanni biyu acikin
watanni biyunnan abubuwa da yawa sun faru ciki
kuwa har da aurena da sarki hinzur,
Al'amarin ya kasance ne wata rana sarki hinzur na
zazzagaya gari yana duba yanda talakawansa suke
kamar yadda ya saba aduk karshen shekara
.
Ni kuma alokacin banfi shekaru goma sha tara ba ,
nazo kasuwa zan siya kallabi, kawai sai ganin
cincirindon jama-a nayi a waje guda dana tambaya
kome ke faruwa sai aka sanar dani cewa sarki hinzur
ya kawo ziyara , kawai sai na tsinci kaina ina mai
karissawa. Wajen,
Don nasha jin labarinsa da kuma irin yabonsa da
jama'a keyi, amma ban taba ganinsa ba
.
Ashe dai kyaututtuka yake rabawa wa jama'a ,
Dogon layi akayi a yayin da shi kuma sarki hinzur
yake gaban wata rumfa dankarere ,agabansa wani
makeken teburine akan teburin kuwa kyaututtukane
kala kala ,
Banyi kasa a guiwa ba nima nabi layi , har layi yazo
kaina ,
Kaina na sunkuye ina dago kaina nai arba da
kyakkyawar fuskarsa ma'abociyar murmushi , nan
take naji zuciyata ta buga,
Maimakon sarki hinzur ya miko mani kyautar dake
hannunsa sai ya kura mini ido kaman yana nzarin
wani abu a tattare dani ,koda naga haka sai na
sunkuyar da kaina kasa,
Ina sunkuyar da kaina kas ne idanuwa suka ci karo da
abin da ya tayarmin da hankali
Bakomai bane illa wata zabgegiyar macijiya baka
kirin, jelar macijiyar da sauran jikinta yana kasan
teburin a yayin da kan macijiyar ya leko ta saman
teburin daidai saitin hannun sarki hinzur,
Nan take macijiyar ta fiddo da harshenta , ai koda
naga haka sai nayi wuf cikin zafin nama na bangaje
hannun sarki hinzur ,da hannuna kafin na kauce da
hannuna sai wannan macijiyar ta dankara mani cizo a
hannu, nana na kwala ihu daga nan ban san meya
faru gareni ba.
.
$ai farkawa nayi na ganni acikin wata kimtsastsiyar
turaka bisa wata luntsumemiyan katifa na alfarma
wannan turaka ta isa daular duniya don kayan dake
cikinta yayi hannun jarin wani attajirin.
.na mike zaune
Kofan dakinne ya bude sannan wata kuyanga ta shigo
, koda wannan kuyanga taga na farka sai ta washe
baki sannan tamin sannu na amsa mata cikin boye
murya ,
Fitan kuyangan keda wuya sai naji takun sahun
mutun yana nufo dakin , ya bude kofa ya shigo ya
kariso har inda nake zaune bisa katifa ,
Bakowa bane face sarki hinzur , yai mani sannu da
jiki sannan ya fice,
Ficewarsa keda wuya
Sai wasu kuyangi suka shigo nan suka tasar dani sannan suka shiga bayi sukai mani wanka bayan mun fito daga bayine suka zaunar dani bisa wata kujera,
.
Anan sukai mani kwalliya sannan suka sanya mani wani tufafi na yadin alharini. Sannan suka ce dani naje sarki naso yayi magana dani.
.
Acikin wata turaka na sameshi kai alokacin in ka ganni kace sarauniyar duniyace , doguwar rigace sanye a jikina rigar an yimata ado da duwatsun lu'u lu'u sannan na yafa wata mayafi wadda akayi mata cin baki da zubar jadi, wannan mayafi ya rufe mani ilahirin fuskata
.
Bayan na zaune a daya daga cikin kujerun dake cikin turakar sai na yaye mayafin dana rufe. Fuskata da shi , koda sarki hinzur yai arba da fuskata sai ya mike tsaye yana mai cewa " tsarki ya tabbata ga wanda ya kagi wannan kyakkyawan halittar"
.
Koda naji sai na sun kuyar da kaina kasa cikin jin kunya
Sarki hinzur yacigaba da cewa " ya ke wannan sarauniyar kyawawan duniya kiyisani a lokacin dana dora idanuwana akanki tunanina,hankalina,dakuma natsuwata duk sun guje daga gareni,
Banki nayi shekaru ina kallon wannan kyakkyawan fuskar taki ba,
Kiyi sani yake wannan kyakkyawa wannan sarki yazo da kogon barar sa gareki da jin cewa zaki amshi tayin soyayyarsa"
.
Koda naji yayi shiru sai na dago kai na dubeshi nace
"Yakai wannan sarki ma'aboci a dalci, kayisani cewa babu wata ya mace da zatayi arba da kai sonka bai shigeta ba,
Kasani tun alokacin dana fara ganin ka naji ina matukar kaunarka,"nayi shiru cikin kunya
Anan dai mukai ta hira cikin nishadi
In ka ganmu sai ka rantse munfi shekaru muna tare
.
Aranar sarki bai fita fada ba
Bayan kwana uku aka daura aurena da sarki hinzur sai da aka kwashe kwanaki goma ana ta shagulgulan bikinmu
Abun babu kama hannun yaro
.******* **
Al'amarin waziri humaiz kuwa tun dayaga shirin daya shirya na halaka dan'uwansa baiyi tasiri ba sai ya shiga kulle-kulle ya kulla wannan ya kwance wannan har dai daga karshe wata dabara ta fado masa.
****** **
Al'amarin boka kamsusulajani kuwa bayan yayi bincike a hallaran tsafinsa sai ya gano cewa waziri humaiz ne keson kashe sarki hinzur
Sai yaki fada ma sarki gaskiyan Al'amarin
.
****** **
Sarki hinzur kuwa yayi tacin amarcinsa ya kasance baya zuwa fada sosai kuma kullum cikin farinciki yake
Wata rana a fada ana cikin fadanci sai ga wani badakare yazo gaban sarki ya tsuguna yace
"Ranka shidade wani bakone akofa yace wai daga birnin KuFA yake kuma yazo ya isar da sakone,
Nan sarki yace abarshi ya kariso
Koda zuwan wannan manzo sai ya zube kasa ya kwashi gaisuwa wajen sarki sannan ya fidda wata takarda ya mika ma wani badakare,
Take maga takarda ya karbi takardan yafara karantawa kamar haka
.
Sako daga sarki hurshad bin harush mai mulkin birnin kufa zuwa ga aminina sarki hinzur bin humas, dafatan kuna cikin koshin lafiya kai da al'ummarka kayi sani cewa ban rubuta wannan wasikar don komai ba face don na sanar da kai cewa, matata kuma abar begena ta haifa mani santalelen yaro ayanzu haka dai na zama baba, sannan ina gaiyatarka walimar radin suna , dagamai mulkin birnin kufa sarki hurshad bin harush,
.
Koda magatakarda ya idda karatunsa sai sarki ya dubi dan sakon cikin murmushi yace "kagayawa aminina ina nan tafe nan da kwanaki biyar
.
Marubuci:- Shuraih Usman
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%

Namijin gaske 1
Part 1E
(c) shuraih Usman
@shuraih 99%
NAMIJIN GASKE
Littafina daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Tel. 08133209890
Part E
.
Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa
wannan labari ta
ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan
za'a kiyaye
Copyright
Shuraih Usman
.
Koda magatakarda ya idda karatunsa sai sarki ya dubi dan sakon cikin murmushi yace "kagayawa aminina ina nan tafe nan da kwanaki biyar
.
A washe garin ranar ne sarki hinzur ya shirya nima ya sanar dani, na shirya muka tasamma birnin kufa dagani sai sarki hinzur da kuma dakaru goma kacal,
.
A tarihin sarki hinzur baya tafiya da dakaru masu tsaron lafiyashi, don wani sa'in ma shi kadanshi yake shiri ya tafi rangadi,
Koda yan fashi, ko wasu muggan dabbobi sun tareshi kuwa, take yake tarwatsa su duk yawansu,
Muna tafe bisa dawakai nida mahaifinka a cikin wata daji mai dogayen itatuwa .
Kwatsam ba zato ba tsammani sai gani nayi sarki hinzur ya dakata,
Nima sai na dakata na dubeshi nace
"Yakai mijina kuma abin kaunata shin ina dalilin tsayuwarka acikin wannan dokar daji mai mugun yanayi" murmushi kawai yayi sannan ya bingiro kasa, yafado daga kan dokinsa,
Toh anan ne naga abin daya tayar mani da hankali, acaccake a bayansa kibau ne har guda biyar,
Koda ganin haka sai na sauko bisa dokina , sannan na karisa wajen dayake kwance bakinsa sai aman jini yake,
Na tallafo kansa ina mai fashewa da kuka, su ko dakarun da muka fito da su suna zazzaune bisa dawakansu.
Nan na daka musu tsawa kan cewa su fara binciken wanda yayi wa sarki haka.
Wani daga cikinsu ya bushe da dariya sai da yayi mai isarsa sannan ya dubemu yace
"Kusani yaku wayannan sarakan yau kam kun gamu da ajalinku"
Sarki hinzur najin haka sai yayi wuf ya mike yayi tsayuwa irin ta manyan sadaukai tamkar babu abinda ya sameshi, sannan ya zaro takobinsa yace da wayannan dakarun
"Ai NAMIJIN GASKE baya faduwa kasa banza, shin kuna tsammanin wayannan kibau din da kuka harbeni da su zasu illata nine hakika kunyi babbar kuskure domin kuwa jinake tamkar Allurai kuka sossaka mini"
Yana gama fadin hakan ya falfala da azababben gudu don ya isa wajen da suke, ai koda ya rage baifi saura taku biyu ba tsakaninsa da su sai ya daka tsalle sama , ya sanya kafafuwansa ya doki dakaru biyu dake kan doki , take suka fado kasa daga kan dawakansu.
Cikin zafin nama ya sanya takobinsa ya guntule kawunansu.
.
Koda sauran dakarun suka ga haka sai suka ruga aguje don su tsira da rayuwarsu, duk sun kasance suna kan doki shi kuwa sarki hinzur bisa kafafuwansa ya falfala aguje don ya cimmusu,
Nan dai aka kasa tsere tsakanin dakarun da kuma sarki hinzur
Cikin kankanin lokaci ya cimmusu, nan take ya daka tsalle sama a samanne tun kafin ya sauko kasa ya sanya takobinsa ya shaftare makwogaron dakaru uku nan suka fadi matattu.
.
Koda ganin haka sai sauran dakarun suka zage damtse sai gudu suke a yayin da shi kuma sarki hinzur ke biye da su abaya, koda sarki hinzur yafara jin gajiya , sai ya yar da takobinsa sannan ya kwala ihu wanda ta haddasa karamar girgizar kasa,
Take tsuntsaye suka ringa canja sheka,
Take dawakan da dakarun suke kai suka firgita ainun da wannan ihu, nan suka tsaya cak suka ki gaba sannan suka ki baya, a haka sarki hinzur ya kariso ,
Koda zuwansa sai dunkula hannu yaiwa doki daya naushi take dokin ta fadi akas sumammiya
Cikin zafin nama ya cafe wuyan badakaren daya ke kai sannan ya murde
.
Cikin kankanin lokaci duk ya karkashe wayannan dakaru
,
Koda yagama kashe su sai yazo inda nake a durkushe ina kuka
Ya mika mani hannu don na mike tsaye
Kawai sai gani nayi kibau ta hudo ta gadon bayansa ta fasa kirjinsa cikin azama na mike na tallafeshi ina mai kiran sunansa cikin karaji,
.
Ya lumshe idanuwa sannan yace " yake abar kaunata hakika naji bakin cikin rabuwar da zamuyi na umarceki daki gudu don ki tsira da rayuwanki"
Cikin sheshshekan kuka nace mai"yakai miijina alfaharin qalbina,kayisani babu abinda zaisa na rabu dakai a kowanni hali ka tsinci kanka aciki duk rintsi duk wuya ina tare da kai ,
Ko mutuwace ta zo daukarka toh sai dai ta dauke mu gaba daya "
Ina gama fadin hakanne sai muka ji an bushe da dariya a bayanmu, koda muka juya sai mukayi arba da waziri humaiz shi da dan fashi kallabu sai kyakyata dariya suke,
.
Nan take hawayen bakin ciki ya zubowa sarki hinzur ya dubeni yace
"Na rokeki da ki gudu don ki tsira da rayuwarki..." Maganar tasa ta katse a daidai lokacin da wata kibau ta cake sa acinya
Nan take ya fadi kasa yana mai aman jini,
Yasake cewa " ki gudu ki tafi ki barni"
Ba don son raina ba haka na falfala da gudu nayi cikin dokar daji, koda kallabu yaga na ruga sai shima ya biyoni,
Koda ya zo wucewa ta gefen sarki hinzur sai sarki hinzur ya gabza mai wata naushi a yayan marenansa, take kallabu ya durkusa sannan ya kama wajen da hannayensa bisa jin wata muguwar zogi,
Damar da sarki hinzur ya samu kenan cikin zafin nama ya zare takobin kallabu a kugunsa,
Sannan ya fille mai kai take dungulmin kan tayi tsalle ta fado a gaban waziri humaiz,
.
A lokacin waziri humaiz na rike da kibau a hannunsa , cikin har zuka ya yarda kibau din gefe,
Sannan ya zaro takobinsa ya fuskanci sarki hinzur,
Nan fa suka rugunzume da azababben yake, nan fa waziri humaiz ya wanzu yana kai ma sarki hinzur sara da suka, shi kuma sarki hinzur ya wanzu yana mai karewa, sannan kuma yana maida martani, sai da aka shafe kimanin sa'a biyu ana wannan gwagwarmayar toh a sannan ne waziri humaiz ya tuna cewa ya riga daya illata sarki hinzur koda gama aiyana hakan aransa sai ya yarda takobinsa sannan ya yage rigan dake jikinsa,
Lallai shima waziri humaiz ba karamin kato bane don kuwa jikinsa a mummurde suke,
Faruwan keda wuya shima sarki hinzur ya yar da takobinsa ya tsaya atsaye toh sai a wannan lokaci ne sarki hinzur yafara ganin jiri a sakamakon jininsa dake zuba,
Nan suka afka ma junansu, wannan karon salon fadan ya canja don cikin dakiku kadan suka hada ma junansu jini da majina,
,
Sarki hinzur ya gaji likis amma saboda tsabar juriya da naci hade da cin rai
Tabbas badun sarki hinzur ya kasance NAMIJIN GASKE ba toh da tuni waziri humaiz ya gama da shi.
Koda suka ga tsagwaron karfin su yazo daya sai kowa yaja baya ya tsaya, nan sukai cirko cirko suna kallon juna,
Cikin matukar fushi sarki hinzur yace"shin yakai dan uwana kayi sani daka zo ka sanar dani cewa kana son mulkina toh tuni na baka, amma tun da ka biyo ta wannan hanyar ne lallai ina tabbatar maka sai na hallaka ka ayau dinnan"
.
Koda waziri humaiz yaji haka sai ya bushe da mahaukaciyar dariya sai da yayi mai isarsa sannan ya dubi sarki hinzur yace mai
"Ni ba dan'uwanka bane kada ka sake ka sake kirana da dan'uwanka'kayi sani tun muna kanana mahaifinmu yake nuna matukar kauna agareka,
Kulawar dayake baka sam ni baya bani, sannan maimakon ni danake Babba na gaji karagar mulkinsa amma sai ya nadaka a matsayin sarki alhalin kaine a kasa dani, tun daga wannan lokaci na fara kulla tarko ina ta kaima ka hare hare amma kana ketarewa, toh yau gashi ka fada a cikin babban tarkona wadda ina tabbatarma ayau dinnan zan halaka, ka sannan inbi matarka ita ma na hallakata"
Koda gama fadin hakan sai sarki hinzur ya kauma waziri humaiz wata naushi adaidai makogaro da nufin ya fasa mai makogoro cikin zafin nama humaiz ya goce sannan ya fidda wata yar karamar wuka a kugunsa cikin shammace ya soka ma sarki hinzur wukan a cikinsa, nan take sarki hinzur ya kwala kara wacce ta amsa a gaba daya ilahirin dajin
Nan take sarki hinzur ya fadi matacce
.
Koda waziri humaiz yaga ya samu nasarar kashe sarki hinzur sai ya nausa cikin daji nemana, nikuma alokacin ina saman wata bishiya na rakube sai kuka nake tayi
.
Yadda agaban idanuwana aka kashe mani masoyi,
.
Bayan tafiyarshine na sauko daga kan wannan bishiyar sannan na nausa daji
.
Alokacin ina dauke da cikin ka wata takwas haka na kariso wannan waje a matukar galabaice.
Na hada sanduna,itacuna na sana'anta wannan dan karamin bukkar haka na cigaba da rayuwa acikin wannan jejin har sa'ar dana haifeka
.
Babu abinda nake ci face yayan itatuwa ,da kuma tsuntsaye sune abincina a haka na raineka ka girma."
.
Koda hamasiya tazo nan a labarinta sai taa dubi muhaisin tace mai"toh dana kaji labarin mahaifinka sarki hinzur bin humas na birnin tehran wanda ayanzu ya zama tarihi"
Koda hamasiya ta kawo nan azancenta sai taga fuskar muhaisin ta jike sharkaf da hawaye nan ya mike tsaye sannan ya rungume mahaifiyarsa yana mai fashewa da matsanancin kuka na bakin ciki.
.

Marubuci:- Shuraih Usman
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%
Namijin gaske 1
Part 1F
(c) Shuraih Usman
@shuraih 99%
NAMIJIN GASKE
Littafina daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Tel. 08133209890
Part F
.
Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa
wannan labari ta
ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan
za'a kiyaye
Copyright
Shuraih Usman
.
Acan birnin tehran kuwa tun lokacin da sarki hinzur ya mutu, sai aka rada waziri humaiz, a matsayin sarki.
.
Nan fa waziri humaiz ya dawo izuwa sarki humaiz,
Nan ya fiddo da asalin siffarsa ta mulkin zalunci,
Mutanen birnin tehran sun koka sosai akan wannan mulki nasa,
Ya kara yawan haraji, bisa na da, kuma bai dauke wa kowa ba, yaro,jinjiri,babba,tsoho, dole su biya,
Laifi kadan talaka zaiyi yanzu zaisa ayanke masa hukuncin kisa
Su ko attajirai na matukar jin dadin mulkin nasa ,
Rabon da a shimfida irin wannan mulkin zaluncin tun zamanin wani gawurtacce kuma sadaukin Azzalumin sarki mai suna Lu'umanu
(A duba kundin tsatsuba)
.
Wata rana sarki humaiz na barci sai yayi mafarkin wai ga sarki hinzur ya dawo izuwa birnin tehran
Yana zuwa ya nufi gidan sarauta
Da zuwansa gidan ya shiga dakaru suka taso masa amma koda sukayi arba da tsohon sarkinsu
Sai suka zubda makamansu,
Nan sarki hinzur ya dakumo wuyan sarki Humaiz,
Bayan ya hada masa jini da majina ya luguigita shi,
Sai ya sanya masa igiya a kafa sannan ya daure igiyar a jikin doki, nan ya hau kan dokin sannan ya zabureshi,
Wannan dokin yai ta tsala gudu, bai tsaya ako inaba sai da ya kariso tsakiyan gari,
Koda mutane sukai arba da sarki hinzur sai suka kamu da matukar farinciki ,
Nan take sarki hinzur ya dubi jama'an garin yace da su"Ya ku al'umman birnin tehran shin kuna son wannan sarki naku kuna jin dadin mulkinsa ,koko a'a na kashe shi"
.
Gaba daya jama'an garin sai cewa suke akashe shi, la'ananne,azzalumi,akashe shi kawai
Nan take sarki hinzur ya sauko daga kan dokin daya ke kai sannan ya amshi takobi a hannun wani badakare, ya daga sama da nufin ya fille ma sarki humaiz kai.
Humaiz na bada hakuri amma ina
Nan take sarki hinzur ya sauke mai takobin....
.
A daidai wannan lokaci ne sarki humaiz ya farka a firgice, wata kyakkyawar mace dake kwance agefensa ta mike , cikin kissa tace
"Ya masoyina shin meke damunka ,da har ka farka haka a firgice"
.
Murmushi yayi yace"Wani mugun mafarki nayi "
Yana gama fadin hakan sai ya sauko bisa kan luntsumemiyar katifan da suke kwance akai,
.
Cikin kankanin lokaci ya sanya kayansa, sannan yayi tafi da hannu,
Gama tafinsa keda wuya sai ga wasu dakaru su biyu sun shigo cikin turakar, dakarun suka russuna a gabansa nan ya umarcesu dasu tafi su kira masa boka kamsusulajani,
Nan suka fice.
.
Cikin kankanin lokaci sai ga boka kamsusulajani ya bayyana acikin turakar ,
Yace "ya shugabana shin me nene dalilin daya sanya kace ayi kirana,"
Sarki humaiz yace" yakai boka kamsusulajani kayi sani yau nayi mugun mafarki wanda ya tsorata ni ainun,dalilin kiranka kuwa so nake ka fassara mani wannan mafarki tawa,
.
Take ya kwashe labarin abinda yagani acikin mafarkinsa ya sanar da shi,
Koda boka kamsusulajani yaji haka sai yace ya shugabana, ina bukatan lokaci don nayi bincike bisa halwar tsafina "
Sarki humaiz yace" na baka daga yau zuwa gobe da safe lallai ina son jin fassarar wannan mafarki,"
Koda gama fadin haka sai boka kamsusulajani ya bace bat.
Washe gari a fada ana fadanci ayayin da kowa ya lura da hankalin sarki humaiz ya dugunzuma ainun,sabanin da dazakaga sai annashwa yake yana keta dariya .
Kwatsam sai gani akayi boka kamsusulajani ya bayyana tsulum acikin fadan,
Wasu fadawa har sun tattara rigunansu da niyyar su ruga amma koda suka ga boka kamsusulajani ne sai hankalinsu ya kwanta
.
Nan ya kwashi gaisuwa a wajen sarki
Srki humaiz ya sallami kowa a fadan fada ta rage su su biyu,
Sarki humaiz yace "gareka boka kamsusulajani shin me ka ganpo abinciken dakayi,"
Nan take boka kamsusulajani yafara bayani kamar haka" hakika mafarkinka sai ya tabbata..."
Sarki humaiz ya daka masa tsawa yace"ashe kai wani sakarai ne ban sani ba tayaya mutumin dana kasheshi da hannuna zai dawo ya kasheni, ko ka taba ganin anmutu an dawo ne"
Boka yai murmushi yace "eh ba'ataba mutuwa an dawo ba , amma kasani alokacin daka kashe sarki hinzur ai baka kashe matarsa hamasiya ba,babban kuskuren daka aikata kenan,
Kayisani koda hamasiya ta tsira daga hannunku, tana dauke da ciki wata takwas, kuma ta haife wannan da nata yanzu haka ya girma ya zama gawurtaccen jarumi, kuma gagarabadau, lallai ina sanar da kai cewa yana nan zuwa birnin ka nan da yan wasu lokuta kuma ya kasheka sannan ya amshe mulkin mulkin mahaifinsa .
Koda sarki humaiz yaji haka sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ,nan ya dubi boka kamsusulajani yace dashi"toh shin yanzu ina mafita,
.
Boka kamsusuljani yace" mafita dayace "
Cikin kaguwa sarki humaiz yace "yakai dirkan birnin tehran gaggauta sanar dani mafitar da ka samo mana"
.
Boka yace "bakomai bane wannan mafita face ka mallaki Wata KAMBUN TSAFI wacce aka killace ta a tsibirin bahar jallus"
.
Boka kamsusulajani ya dubi sarki Humaiz bin Humas yafara bashi labari kamar haka
.
Kimanin Shekaru aru aru da suka shude A Cikin wannan birnin Na Tehran anyi wani gawurtaccen Azzalumin sarki mai suna LU'UMANU na birnin Tehran a duba KUNDIN TSATSUBA
.
Shi wannan sarki mai suna Lu'umanu yana da wata kambu na tsafi wacce take daure a hannun hagunsa,
Da wannan kambune yayi amfani inda yai ta shimfida mulkin zalunci ,
Har lokacin da wani ma'abocin bakon Addini ya hallakashi
.
Yanzu kambun tsafin na ajiye a tsakiyar tsibirin bahar jallus,
Muddin ka mallaki wannan kambu toh duk duniya babu wani jarumin da bazaka taka ba,
Sai ka zama guguwar Annoba mai shafe birane,
Akwai wasu Manya manyan sarakunan aljanu na duniya baki daya guda goma sha bakwai da ke ma wannan kambu bauta,
Muddin ka mallaki wannan kambun toh duk zasu da wo karkashin ikonka,
.
Ita wannan kambu tana tattare da alkaluman sihirin tsafi guda dubu
Kasani muddin ka mallaki wannan kambu toh tamkar ka mallaki wayan can sihirin tsafin ne,
,
A baya jarumai, sadaukai, da Mazan kwarai, duk sun rasa rayukansu bisa mallakar wannan kambu ta tsafi,
.
Kayisani yakai wannan sarki
Kafin ka isa tsibirin bahar jallus kuwa sai ka bita cikin wasu mugayen dazuka guda biyu,
.
Dajin farko ana kiransa da suna Burkum
Babu komai acikin wannan daji face dandazon yan fashi wayanda adadinsu yafi milyan
Su wayannan yanfashi sun kasance mugayene sam basu da imani ko kadan don ko bera sukai arba da ita toh take suke gutsutstsure namanta su rabata ga junansu yadda kowa sai ya samu
.
Komai suka samu raba daidai suke da ita yadda kowa zai samu duk kankantashi kuwa,
.
Atarihin wannan daji babu wani mahaluki walau mutum ko aljan wanda ya taba ratsawa ta cikin wannan daji a raye,
Kai muddin mutum ya shiga wannan daji toh tamkar ya shiga lahira ne don kuwa baza a sake jin duriyarsa ba
.
,
Daji na gaba kuwa ana kiransa Da suna Darul marid babu komai acikin wannan daji face wasu irin zabga zabgan maridai wayanda adadinsu yakai dubu
.
Su wayannan maridai kaifi ko tsini baya tasiri ajikinsu face zagwaron karfin damtse, don sun kasance suna masu baiwa jikinsu horo ta hanyar shan wani tsumi wanda muddin suka sha toh ko kwana zakayi kana saransu ,
Ba za su san kanayi ba
.
A tarihin duniya baki daya
ba'ataba samun wanda ya ratsa ta cikin wayannan dazuka guda biyu sannan ya fito a raye ba walau mutum ko aljan,
.
Shi kuwa tsibirin bahar jallus, duk yafisu masifa da bala'I
Don kuwa wasu irin Aljanu ne a wajen
Su wayannan aljanun suna da katon kai kaman randa sannan sai sililin kafafuwa wanda ke barazanar karyewa a ko wani lokaci,
,
Aljanun gaba daya jikkunansu launin ja ne,
Da sun hadu da mutum ko aljan nan take zasu zuke jinin jikinsa, ta hanyar taba sassan jikinsa
.
Su wayannan aljanu suke tsaron wannan Kambu ta tsafi
.
Lallai tafiya neman wannan kambun tsafi bakaramin masifa da bala'I bane
Don kuwa NAMIJIN GASKE ne kadai zai iya tunkarar wayannan masifu batare da yaji tsoro ko shakka acikin zuciyarsa ba
."
Koda boka kamsusuljani yazo nan azancensa sai yaga sarki humaiz ya bushe da dariya al'amarin daya bashi mamaki kenan
Sarki humaiz ya dubi boka kamsusuljani cikin yarda da kai yace
"Lallai ko zan rasa rayuwata sai na mallaki wannan kambun tsafin kuma ina sanar dakai cewa ka shirya don kuwa da kai za'ayi wannan tafiyan
.
SHIN SARKI HUMAIZ ZAI SAMU NASARAR MALLAKAR KAMBUN TSAFI KUWA
.
WANI IRIN MASIFU DA BALA'IEU ZAI HADA DASU
.
SHIN BOKA KAMSUSULLAJANI ZAI AMINTA YAYI WANNAN TAFIYA MAI MUGUN HADARIN KUWA
.
INA LABARIN JARUMI MUHAISIN DA MAHAiFIYARSA
.
SHIN ZAI SHIRYA YAZO BIRNIN TEHRAN DAUKAN FANSA
.
WANI KARAN BATTA ZA'AI TSAKANINSA DA SARKI, HUMAIZ,
.
Domin jin wayannan amsoshin sai ku tsumaye ni a littafi na biyu
.
NAMIJIN GASKE
Littafina daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Tel. 08133209890
.
Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa
wannan labari ta
ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan
za'a kiyaye
Copyright
Shuraih Usman
.
SHEKARAR RUBUTAWA:- 2017
Addreshi:- tshon/kasuwa gidan malam Usman ,nasarawa state Keffi
.
Akwatin waya:- 0908626148,08133209890
.
Kagaggen labari daga shuraih Usman
SADAUKARWANE GA
M.malam Usman
M.hajiya Maryam
Mujahid hamza(mijin biza) best friend forever
Sis.Zainab Usman
Bro.abdulaziz Usman
Sis.Amina Usman
BAN MANTA DA KUBA
Dahiru Usman Diffusion(D.U.D)
Anas aliyu katuka (bin malik)
Suleiman ishaq(Big army)
Abdullahi Isa (B.O.C)
Dafatan kuna cikin koshin lafiya
Alhamdulillah


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment