Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

likita nashigowa yakarasa gurin kabir ya dubesa yace "alhamdulillah tabbas lafiya tasamu"

Dubansa yayi cike da mamaki yace "likita wai meke faruwane nifa bangane kuba"

Likita yai ajiyar zuciya sannna yace "kayi mahaukane a shekarun baya amm..."
Dasauri Mubarak yace "hauka kuma likita? garin yaya"

Nan likita ya labarta masa komai akan abinda yasani, akan haukarsa da kuma losing memory kansa dayayi harda aurensa da Rumaisa,

Hawaye Mubarak yakeyi yana fadan "innalillahi wa inna ilaihin raju un"

Duk jikinsa yayi sanyi, jinyadda labarinsa yakasance, ya tausawa kansa,

Likita yadube Mubarak yace " kai dan wane garine, kuma meye labarinka"

Mubarak yana kuka yatsayar da kukan yace "sunana Mubarak nidan kogi state ne, inada aure mata daya dakuma yaro daya mai suna Khalid, ni bansan meye faru daniba, sai yanzu dana farka daga mummunan bacci danayi"

Abba yayi saurin cewa "yanzu kai kanada aure"

Mubarak yace "tabbas inada aure harda yaro daya"

Abba yayi ajiyar zuciya yace "tabbas nayi babban kuskure, dana hada aurenka da 'yata Rumaisa"

Mubarak yadube abbq da mamaki yace "wacece kuka Rumaisa"...

https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr
[10/20, 10:53 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

107 and 108
Via *OHW*
_A love story_💝

Dakin kowa yayi shiru, faisal mamakin yake to meyasa baiji labari a gurin kowaba cewa yarima Mubarak yanada mata, hard yaro, kuma meyasa adnan ya gudu, kansa yake tambaya,

Jin kowa yayi shiru yasa Mubarak yayi yunkurin tashi yana fadan "yanzu gida zankoma, zanje naga mahaifiyata da matata"

Gaban Abba yafadi, sai yanzu yatuna da maganar da haj luba take fada masa, kar wata rana yaron nan yasamu lafiya yazo ya gujemu, yan idan yatafi wane hali 'yarsa rumaisa zata kasance, Abba yana hawaye yace " dan Allah karka tafi wlh idan katafi zan iya rasa 'yata, 'yata tafada sonka so marar misaltuwa, dan Allah kataima kamun ka aureta, karna rasata ita kadai nakeda"

Dakin kowa saida yaji tausayin abba,

Mubarak yadube abba yace "bazan iya auren kowace macce ba a yanzu, nidai dan Allah kubarni na naje gida"

Faisal yayi saurin cewa "tare zamu tafi, domin inason nasan gaskiya labarinka, kuma nizan maka jagora harzuwa gurin mahaifiyarka"

Mubarak yamike tsaye yana gyara tufafin dake jikinsa yace "yanzu zamu tafi, bazan iya kara awa daya a garin nanba"

Yayi yunkurin barin dakin abba ya rike masa riga, cike da muryar magiya yace "dan Allah kafin katafi, inason kaje kaga 'yata koda sau dayane domin nasan zatafi kowa farin cikin ganin kasamu lafiya"

Ransa baisoba, sai dai kuma abba yabashi tausayi, Mubarak yace "toh muje"

Daddy da faisal duk jikinsu yayi sanyi, sun zamo 'yan kallo,

Su duka suka fita suka shiga motar daddy, suka wuce gidan abba,
■■■■ ■■■■ ■■■■
A falo umma da haj luba ne zaune, sai rumaisa datake kwance a cinyar umma tana kuka, sai kuma kawayenta su biyu da sukayi jugum, falon yayi tsit, shanshekar kukan rumaisa kawai kakeji, suna jiran dawowar su abba,

Ji sukayi anturo kofar falon anshigo, dasauri suka maki ganin su abba sunshigo,

Haj luba tayi saurin kallon abba tace " ina fatandai komai lafiya" abba jiki a sanyaye yace " kuzauna zan muku bayani" tunda suka shigo, edon rumaisa yana kan Mubarak, taga yanayinsa ya chanza, kuma sannan ko kallonta baiba,

Bayan sun zazzauna abba yace "lamari ya lalace, domin abinda kowa yayiwa gudu yafaru, kabir yatuna da waye shi"

Umma, haj luba, rumaisa duk saida gabasu yafadi,
Cike da fargaba haj luba tace "abinda najima ina tsoro kenan yanzu gashi yafaru, to meya sanar daku"

Abba yace "yace mana sunansa Mubarak kuma shi dan sarkin kogi ne sannan kuma yace yanada mata harda yaro daya"

Ihu kad'an rumaisa tayi saida tasoma ganin jiri, zuciyarta ta harba da karfi, tafashe da kuka,

Haj luba ta tabe baki tace " ahaf ai saida nagaya muku, amma kukaki saurarona, kaidai burinka 'yarka tasamu lafiya, wlh usman kacika sonkai dayawa" tafada tana nuna abba,

Daddy yayi saurin cewa "hajiya ayi hakuri yanzu dai komai yafaru yariga ya wuce, maganar auren Rumaisa yanzu babu ta, da kyar ma muka samu yazo gidan nan domin yayi bankwana da ita, yamatsa akan cewa dole yanzu zai koma gida"

Kuka sosai rumaisa takeyi, ta dago kanta muryata na sharkewa ta dube majnoon dinta wanda yanzu yazamo cikakkan mutum kuma ayanzu zata rasashi tace "nice silar duk wannan, daya faru kaka, kidaina ganin laifin abbana, nataka SO a gefe mai tsini tayadda edanuna suka rufe akan cewa saina aure Kabir, ninasan dacewa wannan bakomai bane face KADDARA TACE, kuma.ban isa na guje mataba...." kuka ya hanata karasa maganar,

Sai a lokacin Mubarak yadubeta, tayi matukar bashi tausayi, shima hawayen yake yace "bazan iya auren ko wace 'ya macceba a yanzu, kiyi hkuri, koda ace an daura auren nan ne kafin nasamu lafiya to tabbas idan na warke zan tarwatsa auren, ki godewa Allah ba' a daura auren nanba"

Kuka sosai rumaisa takeyi, dasauri tatashi tanufi dakinta da gudu, kawayenta sukabi bayanta,

Mubarak ya dube abba yace "nagode da karamcin da kuka yimun, Allah yasaka muku da khairan"

Duk falon suka amsa da ameen,

Mubarak ya mike tsaye sannan yace " nizan wuce, sai Allah yasake sadamu da alkhairinsa" sannan yajuyo yadube faisal yace "muje koh"

Faisal ya mike cike da farinciki, jiyakeyi kamar, burinsa nadaf da ciki, na auren rumaisa,

Suka fita tare suduka, daddy yabasu motarshi, suka shiga, sannan sukayi sallama dasu

Rumaisa tana tsaye ta Window tana kallon lokacin da Mubarak yashiga motar, jiri taji yafara dibanta, edonta suka fara lunshewa, daidai lokacin da su Faisal suka fita daga harabar gidan, a daidai lokacin rumaisa ta zube kasa somammiya..

Kawayenta sukayo kanta suna jinjigata amma ina, bata mosti, dasauri leemart tafita taje takira abba, yana shigowa dakin yakira doctor,

Bayan sun yayyafa mata ruwa ta farka tana kuka,

Umma tana rike da ita tana hawaye, ta dube ta "yanzu shikenan umma an rabani da majnoon, wlh umma zan mutu, majnoon shine burina, dan umma kuce yadawo"

Hawaye umma takeyi, tace "kintaba ganin anmutu an dawo, to hakama Mubarak bazai taba dawowa garekiba, kedai kawai kiyita rokin Allah yabaki wanda yafishi"

Rumaisa takara fashewara da kuka tana fadan "babu shi umma babu wanda yafimun majnoon a cikin zuciyata,,, kutai makamun kuce yadawo,. Wlh zan mutu 😭.." nan dai taci gaba da sabbato sai kace wata zararriya,

Likita nazowa ya burma mata allurar bacci, sannan yasamu yaduba, sannan ya tabbatarwa su abba dacewa, jininta yana gaf da hayewa dan haka ayi gaggawar nema mata farin ciki, yana gama basu bayani sannan yafice yabar gidan,
□□□□ □□□□ □□□□
Su faisal kuwa sai tsala uban gudu sukeyi akan titi kamar zasu bar duniya , amma duk da haka shi Mubarak gani yake kamar ba gudu ne Faisal keyiba ,

Anan daf da kiran sallar la'asar suka karasa garin kogi,

faisal ya zarce sai gidan mai martaba,

Bayan sun karasa
Mubarak kallon gidan yake duk yaga gidan yasauya masa, a harabar gidan faisal yaja birki, babu kowa a gurin, duk suna wurin sallah,

Cike da kasaita da faduwar gaba, Mubarak yafito daga cikin motar, yana kallon harabar giadan ba kowa da saurin yake tafiya yanufi cikin gidan batare dawata ko wani yaganshiba, faisal yana bayansa

harya karasa falon da ummansa take ciki, yana bude kofar yaji gabnsa yafadi,

Kallo daya yamata saiga hawaye, cikin kuka bakinsa ya furta Umma!!!"

Saida kanta yasara a lokacin dataji muryasa, duk ila hirin jikinta yadau rawa, jitakeyi kamar almarane, bada gaske bane muryasa, a hankali kanta ke juyawa gurin dataji sautin muryar nafitowa,

Caraf edonta yafada kan Mubarak, a lokacin mubarak ya zuro da gudu ( kusa masa slow gurin karatun, yanayin gudun sa😫)

Kukan farin ciki take duk dacewa har yanzu bata gasgata lamarinaba, yunkurin tashi tayi sai kuma takasa hannu ta nuna masa bakinta na rawa tasoma furta mu..baa..rakkk" bata karasaba ta sulale kasa somammiya,

Da gudu yakaraso gurinta ya tallabo kanta yana kuka, yana kiran sunanta "ummaaaaaa....

https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr
[10/20, 10:53 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

109 and 110
Via *OHW*
_A love story_💝

Faisal dake tsaye a gefe abin tausayi yabasa sosai harda su hawaye,
Motsin mutane faisal yaji suna shirin shigowa gurin,

Dasauri yakarasa gurin, Mubarak cike da tsro yake cewa " mutanefa suna zuwa, kazo mubar gurinnann"

Ko kallonsa Mubarak baiba, kukansa kawai yaci gaba dayi,

Bodyguard ne su biyu suka shigo wurin, ganin mutane aciki, yasa sukayi saurin karasa cikin cike da zafin rai,

Faisal tuni jikinsa yadaurawa,
Mubarak ya juya musu baya, tayadda bazasuga fuskarsa saba, bayan sun karasa kusa da mubarak daya daga cikin bodyguard din yadaka masa tsawa " waye kai!!"
Mubarak yayi shiru, yaci gaba da kukansa, bodyguard din yakara daka masa tsawa yana kokarin kai masa duka,

Cikin zafin zuciya Mubarak ya juyo da karfi,
Sukayi edo hudu da bodyguard din saida yaja da baya saboda tsoro, cikin rawar murya bakinsa ke furta "prince Mubarak! !" Da gudu yajuya yafita waje, dayanma yabi bayansa suka fita,
□□□□ □□□□ □□□□
Daidai lokacin mai martaba yafito daga masallaci, yana kokarin saka takalmansa, bodyguard din suka karaso gurin suna hucin gajiya, da gudun da sukayi,

d'ayan yana nuna kofar shiga cikin gidan bakinsa na kokarin furta " prince Mubarak a dakin ummansa"

Gaban mai martaba yafadi, cike da razana yace " yarima Mubarak a ina"

Saida bodyguard din yasamu natsuwa sannan yace "dakin ummansa "

Mai martaba ya daukesa da wawan mari cikin zafin rai yace "kaba ganin wanda yamutu yadawo, d'ana Mubarak ya mutu, tsawon shekara biyu, shine yanzu zakacemun kaganshi"

Bodyguard din yana dafe da kumatunsa yace "wlh idan karya nake karka barni nakara nunfashi a duniya, prince Mubarak yana cikin gidan nan"

Jin rantsuwarsa yasa gaban mai martaba yakara faduwan, kasa saka takalmin yayi, saboda zumudi, yanufi cikin gidan, kamar zai hada da gudu wurin saurin tafiya,

Harya karasa bakin kofar falon, a daidai lokacin Mubarak yatashi yana kokarin fitowa , sukayi kicibus da mai martaba,
Saranda mai martaba yayi yana kallonsa, ayya kuwa wannan ba mafarki nakeyi bane, ko kumadai fatalwarsace,

Kafin zuciyarsa tagama saka2, Mubarak ya zo da gudu ya rungumesa yana kaka, har a lokacin mai martaba yakasa gazgata lamarin,

A hankali yake hade hannayensa, yana tabo jikin Mubarak, sai a lokacin mai martaba yaji tabbas mutum nea,

Wasu irin hawaye suka gangaro masa akan kumatu, na farin ciki, a hankali bakinsa ke furta "Mubarak"
Mubarak yafito daga daga jikin mai martaba yana kallonsa yace " eh nine baba, wlh nine" yakarasa maganar yana kuka,

Dariyar farin cikin mai martaba yayi yakara rungumo Mubarak jikinsa, sun jima a haka suna kukan farin ciki, kafin Mubarak yafito daga jikinsa, ya nuna masa ummansa yace " meya faru da ummata, meya sameta"

Sai a lokacin hankalin mai martaba yadawo kanta da sauri ya furta "subhanallah, meke faruwa ne" sannan ya juyo yadube bodyguard yace "maza kudau keta kutai dakinta, yanzu zan kira doctor"

Suna kakori karasawa gurinta, prince mubarak yadaka musu tsawa "karkowa yatabamun umma kumabarni nadauke abata nakaita daki, kumatsa daga gurin"

nan kaga kowa yaja da baya, prince Mubarak yakarasa gurinta, ya tallabota, yanufi hanyar dakinta,

Mai martaba yana kallonsa yana murmushi, girgiza kainsa yayi tabbas farin cikin gidan sa yadawo, hakan dayayi yakara tabbatar masa dacewa tabbas yaron sane,

Faisal duk jikinsa yayi sanyi, al'amarin sai mamaki yake bashi, taya za'a ce mubarak yamutu kuma yanzu daga ganin wannan sai ace kuma shine Mubarak, shidai haryanzu zuciyarsa takasa samun wannan amsar,

Mai martaba yabi bayansu bayan yagama waya da dr bukar,
□□□□ □□□□ □□□□
Prince Adnan da ummasa suna zaune a cikin daki sai faman kuka suke, nan sukaji gida yadau hayaniya, sai guda kakeji,

Prince adnan yakara rosa kuka ya dube ummansa yace "munshiga ukku umma, wlh yaya Mubarak ne yadawo bakiji yadda gidan nan yadau ihu ba, ni wlh bazan zauna na mutuba, na yafe komai na farin ciki, domin inason rayuwata, guduwa kawai zanyi"

Haj zaine ta watsa masa harara cikin bacin rai tace "toh shikenan kagudu, nisai kabarni a kasheni, komai nayi halan badanka nayib, wlh baka isa ka gudu kabarni ba"

Cikin gaggawa adnan yace "to kitashi mutafi, nifa bazan zauna a gidan nanba" yana gama maganar yamike tsaye yana kuka,

Haj zainab ta janyo mayafinta ta rufe jikinta, har fuskarta ta yadda wani bazai iya gane taba,

Sannan ta janyo dayan mayafi ta mikawa adnan tace " kaima ka rufe fuskarka" cike da tsoro yadauka ya nade fuskarsa sai kace buzu,

Sannan suka fita, tafiya sukeyi cikin sauri, kamar zasu tashi sama,

Dai kofar fita daga sashensu, sukaji ana kiran kaii, kaii, kutsaya a nan"

Tsoro da firgita suka kara ziyarar zukatansu,
cak suka tsaya guri daya, bodyguard din yakaraso gurinsu, fuskarsa a murtuke yace "suwaye ku" sukayi shiru, suka kasa furta komai, suna sauraronsa,

Jin sunyi shiru yasa yakara daka musu tsawa yace " magana nake muku suwaye ku"

Cikin bacin rai haj zainab ya yaye mayafinta, tana hararansa, da sauri ya durku kasa yana nonnoken kai " tuba nake sarauniya, Allah huci zuciyarki"

uffa batace dashiba takara mayar da mayafinta, sannan taja hannun adnan sukaci gaba da tafiya cikin sauri,

Mamaki yacika bodyguard, toh sukuwa wad'an nan ina zasu je, a murna cikin gida amma su kokari suke zasubar gidan,

Girgiza kai yayi yace "tabbas akawai abinda ke faruwa wanda yakamata mai martaba yasani, bari naje nasanar dashi" da sauri ya mike yanufi gurin mai martaba,

Koda yakarasa dakin, dr bukar yana kan umman Mubarak yana dubata, Mubarak yana zaune a kusa da ita, faisal kuwa yana tsaye bayan mai martaba,

Bodyguard din yakaraso kusa da mai martaba, cikin sanyin murya yace "my chief, labari nazo dashi"

Mai martaba yajuyo ya dube sa yace " banason jin kowane labari a yanzu, kajirani zuwa anjima"

Bodyguard din yace "my chief wannan labarin bana wasa bane, wani abin mamaki nagani"

Mai martaba yace " uhim ina jinka menene"

Bodyguard yace "hajiya zainab tare da yaronta prince adnan suna kan haryar barin gidan nan"

Cike da mamaki mai martaba yace " what! Da gaske kake wannan maganar"

"da gaske nake fada maka wannan maganar, domin yanzu nahadu dasu kuma harsun rufe fuskokinsu, ga dukkan alamu ba lafiya ba"

Cikin sauri mai martana yace "jeka zomin dasu, maza kaje ka danna kararrawar gidan nan kar a bar kowa yafita"

Dasauri bodyguard yafita yana fadan "angama my chief"

Yana fita yaje ya danna kararrawar, nan kaji gida yada sauti,

Babu tsaiko aka fara rufe kofofin gidan,

Haj zainab da adnan, daidai kofarsu, ta fita harabar gidan aka tsayar dasu...


https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr
[10/20, 10:54 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

111 and 112
Via *OHW*
_A love story_💝

Bude mayafinta tayi bodyguard dinda ke gurin gabaki dayansu suka durkusa akasa, cikin tsawa tace " kubudemun kofa nawuce"

D'ayan bodyguard din yace "angama ranki shidade"

Dasaurin yatashi yana kokarin
Bude mata kofar, saida ya wangale kofar baki daya, sannan tamayar da mayafinta, ta dora kafarta daya a waje daya acikin falon,

A daidai lokacin, bodyguard dinda mai martaba yacewa yazo dasu yakaraso gurin cikin gudun masifa, tun daga nesa yake cewa sauran bodyguard din da ke gurin "kutsayar dasu karku barsu sufita, umarnine daga mai martaba"

Ai kuwa kamar daga sama sukaji a chafkosu, haj zainab ta juyo cike da bacin rai, domin bataji abinda ake fadaba, tace "kankuwasan kowa kakama"

bodyguard din yace "nasani mana, matar mai martaba, amma kuma ai mai martaba ne yabada umarnin cewa kar' a barki kifita"

Gabanta yayi mummunan faduwa, cike da tsoro, take kallon mutanen gurin, ba musu tajuya ta koma ciki, jikinta na kyarma, aka sasu gaba ita da adnan, suka nufi gurin mai martaba,
□□□□ □□□□ □□□□
Yana tsaye akashigo dasu, yasa aka yaye masu lullubin da sukayi, adnan kuka yake sosai, haj zainab tarika kafar mai martaba tana kuka tace " dan Allah kayimun rai, ka gafarceni"

Cike da Mamaki mai martaba yace "mekikayimun ne, aini bakimun komaiba, tambaya daya kawai zan miki, ina zakije keda adnan"

Tana kuka tace "guduwa zamuyi saboda tsoron abinda zai samemu"
Cike da mamaki mai martaba yake kallonta ya maimaita kalmar "guduwa zakuyi, me kukayine"

Haj zainab tace " komai yafaru a gidan nan mune silar, sanadiyar wannan mulkin naka, naso ace d'ana adnan shine zai gajeka amma hakan bata kasanceba, shekaru biyu dasuka wuce, naje gurin boka nasa akayiwa Mubarak magana akan inason yahaukace ko kuwa ya akashesa, bokan yake cemun shibazai iya kisaba amma zaibamu maganin dazan sakawa Mubarak idan akayi amfani dashi zai haukace, inyaso da yadda zan iyayi acikin haukar nakashesa toh shikenan, haka na karbi maganin nadawo gidan, a ranar dana dawo gida nasamu labarin cewa Mubarak zaiyi tafiya zuwa abuja,
To ta wannan hanyar nasamu damar saka masa maganain a cikin motarsa,

Toshine bayan yatafi muka samu labarin cewa yayi hatsari a mota kuma motar ta kone kurmus, tana kuka takarasa maganar dacewa " wannan shine gaskiyar abinda yafaru akansa, tasanadiyar hakan ne yasa mahaifiyarsa takamu da wannan ciwon, kuma matarsa da yaronsa..." sai kuma tayi shiru tana kuka,

Edon mai martaba sukayi ja sosai, ransa yabace

Mubarak dake zaunr akusa da ummansa, yamike cike da bacin rai yana huci yace "ina kuka kaimun matata, da yarona, wlh idan kuka kashesu, kuma zan kasheku, kunkuwasan yadda nake sonsu,... suna inaneeee " yakarasa maganar yana kuka, ya durkusa kasa, sannan yakara dago edonsa yana hawaye yasauke murya abin tausayi yace "umman adnan dan Allah ina matata da yarona"

Umman adnan tayi shiru kuka kawai take, Mubarak yajuya gurin adnan yace "dan uwana adnan ina matata da yarona"

Cike da tashin hankali adnan yasoma magana, yana fadan "kaicona da wannan sonkai danayi, na cutawa rayuwar dan uwana akan mulki, a yanzu ina mai nadamar abinda zan fada masa"

Mubarak yayi saurin cewa "fadamun menene, meyasa faru dasu, adnan kafadamun ina matata da da d'ana"

Adnan yana sosai kuka yace "nina kashesu yaya mubarak, wlh nina kashesu da hannuna...."

Wani irin gunji Mubarak yayi yakara fashe da wani irn masifaffan kuka, edonsa sunyi ja sosai,

Faisal ma haka kuka yake, a zuci yake yafan tabbas har yanzu duniya akwai iblis,

Mai martaba, kasa furta komai yayi banda Hawaye babu abinda yake,

Sauran mutane dake cikin dakin wasu duk kuka suke wasu kuwa jikinsu yayi sanyi, ( nima dai komawa gefe nayi nashare hawayena sannan nadawo naci gaba da rubutu😭)

Mubarak duk ya fita hayyacinsa, harda sambatu yasomayi "sun mutu, gabaki dayansu sun mutu, matata yarona,..." yakara fashewa da kuka,

A daidak lokacin sukaji motsin gadon da umman Mubarak take kwance,
A hankali mai martaba yake kai edonsa a gurin, yaga farkawa take kokarinyi,

A hankali edonta suke kokarin budewa tana kallon dakin, mutanen dake cikin dakin tasoma kallo, har edonta yafada kan Mubarak dake durkushe yana kuka, habar bakinta narawa take furta " Mubarak"....

https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr
[10/20, 10:54 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

113 and 114
Via *OHW*
_A love story_💝

Da karfi Mubarak yad'ago kansa ya dubeta,

da sauri yakaraso gurinta ya rungumeta suka fashe da kuka, cikin kukan yake fadan "umma sun kashemun matata da yarona, taya akayi hakan tafaru, kina ina kikabarsu suka aika wannan mummunan kudurinsu akansu.." yakarasa maganar yana kuka sosai

Muryata na rawa tasoma magana "nasan komai Mubarak, komai akan edona akayi, KISAN GILLA sukayi musu"

Mubarak yafito daga jikin ummansa yace "umma mesukayi musu"

Umma tashare hawayenta sannan tace "babu abinda sukayi musu Mubarak, ranar dakayi tafiya zuwa abuja, a ranar suka kashesu, bayan tafiyarka, naje sashenka zanje na dauko khalid daga gurin mamansa domin nai musa wasa, ina karasa sashen, natarar da adnan menan kashe matarka, ina sauri nakarasa gurinsu, amma ina kafin nakarasa ya soka mata wuka a ciki, anan nayi saranda nakasa zuwa ko ina, akan edona bayan yagama da matar taka, ya dauko yaron shima yayakashi, tashin hankali nagani karara, ihu nasa haka yayi sanadiyar adnan ya biyoni da gudu, nima da niyar zai kasheni, da gudu nafita ina ihu, neman taimako, harna karasa shigowa sashena, ina shigowa anan kuma natarar da mutane ana kuka, koda na tambaya akancemun kaine ka mutu..." kuka ya kubuce mata ya hata karasa mganar,

Zuciyar Mubarak tayi zafi sosai, huci yasomayi duk hankalinsa yatshi mikewa tsaye yayi yana huci, yakarsa kusa da adnan ya shaki wuyansa, yana fadan "kaima saina kasheka irin kisan da kayiwa ahalina" ya shaki yuwansa, shakar dabazai iya furta komaiba,

Bodyguard sukayo kansa suna kokarin hanashi, basu karasa gurinba, mai martaba ya daga musu hannu, alamar karkowa ya hanashi, dole sukaja da baya,

A haka Mubarak yaci gaba shakar wuyan adnan cikin zafin rai, saida ya dauke nunfashi, tun yana shure har yazo yadaina, (Wannan shi ake kira da KISAN GILLA my next novel )

Saida yadaina motsi Sannan yasakesa, yana huci,

Rashin imani karara umman adnan tagani, a hankali take kai hannunta ta riko hannun adnan anan taji hannu yayi nauhi, tana sakin hannun kuma taga ya sulala kasa,

Wata irin kara tayi tana kuka tace " ya mutu, adnan karka mutu, dan Allah karka mutu kabarni, wayyyyyoo, takara saka ihu, ta dora kanta kan kirjij gawar adnan, tana kuka,

Mubarak yana gurfane agurin, duk ya fita hayyacinsa, zuciyarsa sai zogi take masa, har yanzu bai huce yakaicin rashin matar saba da yaronsa,

Kamar daga sama umma adnan tatsayar da kuka ta dago kanta ta dube Mubarak, edonta sunyi ja sosai, tayi ihu ta cafki wuyan Mubarak tana sunbatu "kaima saina kasheka kamar yadda kakesemun yarona" mugun shaka tamasa
Mubarak yakasa kwabar kansa,

Bodyguard sukayo kanta, da kyar suka iya babbare hannunta akan wuyansa,

Mubarak ya galabaita sosai, tana sakinsa ya sulale yafadi kasa somamme,

Ita kuwa ihu ta saka, tana kuka take fadan "sunkashe, wlh banyafe mukuba, mugaye azzalumai, maciya amana" tana cikin magana saikuma tasaka dariya,

Bodyguard suna rike da ita tasoma, kuce kuce tana ihu da karfi, tamkar zautanciya, sambatu kawai takeyi,

Mai martaba yana tsaye, tunda aka fara maganganun yakasa iya furta komai, tunanin yadda abin yakasance kawai yake,

Ihun umman adnan ne yadamesa, da karfi ya juyo, cike da hargowa yace " kufitarmun da ita daga cikin dakin nan, kukaita cen cikin dakin bayan gida kujefata a ciki kurufeta"

Haka kuwa akayi, suka fita da umman adnan aka kaita cen dakin bayan gida aka rufeta,

Suka dawo aka kwashi gawar

Please Login or Register in order to submit comment