Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da takaici, kwata-kwata ya kasa cewa komai ko daga inda yake ma ya kasa motsi, da murmushi a fuskar Umar yace " sweet brother have a set, shine Abdul gaba d'aya ya zama mutum mutumi, "Ok" Umar yace, idan kai bazaka zo ba ni bari nazo, ya taso har gaban Abdul ido cikin ido yace " me ka ke san sani?".

Cikin kuka Abdul yace "why Umar, Umar why?, me yasa kai baka mutu ba?" Komawa yayi ya zauna ya hard'e kafafunsa yace " ya za'ayi na mutu bayan ni na kunna wutar, wata mahaukaciyar k'ara Abdul ya saki a zuciye ya nufi Umar, wata mahaukaciyar shak'a yayi masa ya hau dukansa tako ina yana sakar masa mahangurb'a, fito Umar yayi sai ga wasu k'attai sunkai 30 sun shigo ya kalle su yace " ku rik'e min shi, kafin ya rufe bakinsa sun canki Abdul sun dandanne shi, Abdul na wani irin kuka kamar ransa zai fita.


A hankali Umar ya tako gabansa yace "haba brother ai nafi kowa sanin halinka shi yasa nazo da shiri na, tun kafin ma kaji komai har ka fara haukan to kuma idan kaji sauran sai yaya kenan" ya fad'a yana wani irin kallo, komawa yayi ya zauna ya kalli k'attin yace " ku rik'e shi da kyau fa dan wllh idan ya kufce duk sai buzun mu".


Ya kalli Abdul yace " zanyi maka bayani dalla-dalla yadda zaka gane danna san yanzu kanka a kulle yake, da farko ni ne na kashe BABANKA, da sauri Abdul ya kalle shi, Umar yace" kasan me yasa? sannin bazai bashi amsa bane yasashi ci gaba da magana " duk maganar da ake zuwa a fad'a muku a kai na gaskiya babu k'arya sai ma abinda aka rage, bayan mun gama fashi muka fito daga gidan Alhaji Mati dake bayan layin mu, har ma mun kashe mai gadinsa, muna fitowa naci karo da Baba, muka had'a ido, na ganshi ya ganni, sanin matuk'ar yana raye bazai barni na auri Ramlat bane yasa ni dole na kashe Shi , bawai tsoran ya tona min asiri bane yasa ni na kashesa ba, nasan bazai tab'a tona min asiri ba, tsoron karna rasa Ramlat ne.


Bayan na gama da Baba, sai kai kuma ka b'ullo wai ba zaka bani auren ta ba, matuk'ar kana raye bazan auri Ramlat ba, hakan ne yasani yi muku talala, nayi muku basaja, kai Abdul tun ina Jss2 nake murd'e wuyan mutane akan biyan buk'ata ta, sau 5 ina attempting kashe ka kana excaping, duk wad'anda suke fitowa auren Ramlat nike kashe su, dukkan su ni na kashe su.


Ganin na kasa kashe ka, na kasa kashe wanda zai auri Ramlat ne, yasa ni dole kashe Mama da Ramlat, Auta, kasan kafin na kashe su me nayi musu, sai da Umar yayi murmushi sannan yace " *FYAD'E* a gaban Mama nayiwa Ramlat fyad'e, na cire mata *BUDURCI* ganin ban gama biyan buk'ata ta ta ba, kuma gashi Ramlat ta suma dole ta sani komawa kan *MAMA* ita nayi mata *FYAD'E* akan idon Ramlat nayi sex da mama, haka itama Mama akan idonta nayi sex da Ramlat.


Ya mik'e yana dariya, yace "Allah sarki Mama tana kuka tana rok'o na yana dariya yana gwada yadda Mama ke rok'onsa, had'i da kwaikwayon muryar Maman, bayan na gama ne, na zazzaga musu fetur, na cinna musu ashana, bayan duk na gama wannan sai kuma naga ai nayi babban kuskure idan na barka a raye hakan ne yasani zuwa na kai ka k'ara da sunan kai ne ka kashe su Mama, to kaji fa Abdul, in kana da wata tambayar kana iyayi.


"Hmmmmm Umar kayi kuskure wallahi kobanyi maka komai ba nasan Allah bazai tab'a kyale ka ba, da sannu zagaka abinda zai sameka, sai ka wulak'anta, ka tozarta, ta yadda mak'iyinka ma sai ya tausaya maka, tunda nake ban tab'a gani kona ji labarin wanda yaci amana yayi butulci irinka ba, sai yanzu nasan dalilin da yasa Allah ya barni a raye".


Wata mahaukaciyarr dariya Umar yayi yace "ko?".

Sosai Abdul ke kuka yana k'ara had'i da ihu kamar ransa zai fita, ya zama cikekken mahaukaci, idonsa yayi ja kamar garwashi, sai tirjewa yake yana son ya kwace daga rik'on da suka yi masa amma ina sarkin k'arfi yafi sarkin yawa, shiko Umar sai dariya yake, duk rashin imanin Sanata Sambo da kuma k'iyayyar da yake yiwa Abdul sai da ya tausaya masa, Umar ya kalli yaransa yace " ku kashe shi, sannan yasa kai ya fice.


Sosai suka hau dukan Abdul tako'ina, Sanata Sambo ne ya daka musu tsawa yace baku da hankali ne, dalla ku b'ace min da gani, dukkan su suka fita, da kanshi ya kama Abdul yana tayi masa faman sannu direct hospital ya wuce dashi, Haidar na biye dasu a baya, bayan an gama duba Abdul Dr ya sallame su, a waje Sanata Sambo ya tsaya ya kalli Abdul yace " gaskiya na tausaya maka, Umar ya tabbata cikakken butulu, amma bakomai, duk sanda kake da buk'atar taimako na akan koma meye ka neme ni, in Allah yaso zan taimaka maka, yasa hannu a zaro 300k ya bashi, k'in k'arb'ar kud'in Abdul yayi, Sanata Sambo ya zube masa kud'in a gabansa yayi tafiyar sa, sai da Haidar ya tabbatar Dadynsa ya tafi sannan ya fito daga inda ya lab'e.


Kud'in ya d'auka, sannan suka tafi, bayan sun isa bukka sun zauna suka d'auko camera suka kunna duk abinda ya faru ta d'auko tun daga shigar sa d'akin har inda Sanata ya fito zai kai shi hospital, sosai hankalin Yasmeen ya tashi, ta tsorata fiye da tunani sai da Abdul ya rarrasheta ya kwantar mata da hankali sannan ta samu nutsuwa.

Kallonsa Haidar yayi yace " ya za'ayi? Abdul yace " to ina ma dai na rasa k'wararar hujji mai zai hana mu gurfanar da shi a gaban kotu, shiru Abdul yayi sai kuma yace " a'a Haidar mu kyale shi kawai, " what!? tab wallahi kokai baza kayi ba ni sai nayi, ya mik'e fuuu ya fita cikin fushi , da kallo Abdul ya bishi har ya fita, Yasmeen tace" ka tashi ka bishi ka bashi hak'uri dan gaskiya koni kace a rabu da Umar ina iya yin fushi dakai, murmushi yayi ya mik'e yabi bayan Haidar a bakin ruwa ya same shi yana jefa dutse cikin ruwan, a hankali ya zauna kusa dashi yace " me kake so ayi" ba tare daya kalle shi, ba murmushi Haidar yayi yace "akai shi kotu".
" ok Abdul yace, gobe sai mu shigar da k'ara, yawwa Haidar yace had'i da rungume shi.


Washe gari da wuri suka shirya su kaje suka gabatar da k'ara, sai da aka sha bak'ar wahala sannan aka samo Umar kasancewar akwai k'wak'wk'warar hujja ba'a wahala wajen yanke masa hukunci ba, an yanke wa Umar hukuncin kisan kai ta hanya mai tsanani, kullum za'a rink'a yankar gab'a d'aya ta jikinsa har ya mutu, ido za'a fara kwak'ule masa, sannan sauran gab'ob'i, sosai Umar ke ihu yana kururuwa, saboda tsabar azabar da yake sha, an yanke masa hannaye, k'afafu, kunne, da ido.


Bayan wasu kwanaki aka sanar dasu Abdul cewa wasu 'yan iska sun k'ona Umar a gidan yarin wai ya dame su da wari.


Basu samu matsala ba wajen iyayen Yasmeen kai tsaye suka amince aka d'aura auren Yasmeen da Abdul, Sanata Sambo ne ya tsaya akayi bikin shiyayi komai, da taimakon Haidar da Sanata Sambo Abdul da Yasmeen suka tsallake suka bar Nigeria,suka d'aga zuwa Holland, Haidar ne yayi musu komai na tafiyar, sannan ya kawo 1 million ya basu.


Bayan shekara 2 sosai Haidar ya damu Abdul sannan yazo Nigeria, Yasmeen d'auke da kyakkyawan yaron ta mai sunnan Baban Abdul Muhammad suna kiransa da Nabil, shima Haidar yayi aure ya auri KAUSAR, Sanata Sambo shine ya zamewa Abdul uba, ya zama kamar mahaifinsa, duk duniya Abdul baida kamar Haidar da Sanata Sambo idan ka cire Yasmeen da Nabil.


Abdul ya d'ago kai ya kalli sauran jama'a yace " to kunji labari na, sosai jama'a ke kuka, musamman *6'S STARS* Al'amin ya kalli Abdul yace " to ranka ya dad'e ina HAIDAR & SANATA SAMBO suke yanzu? Kuma naji kace sunan matar Haidar KAUSAR?"


Da k'arfi k'irjin sa ya buga dammmm!! ya juya kalli Yasmeen da Fahad da Kausar.....................



*MOMYN ZARA*
[21/01, 04:12] ‪+234 701 517 2910‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_


~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA```




~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDU*


11


K'orafin ku ya karb'o masoya na, in sha zan ci gaba da posting a WhatsApp, amma sai na fara yi a wattpad.



Da k'arfi k'irjinsa ya buga dammmm! ya kalli Yasmeen, Fahad, Kaudar...


Sai ya maida kallon sa ga Al'amin, murmushi yayi yace " yana nan , " to yana ina? cewar Al'amin, a fusace Abdul yace " yana nan nace mak..... A'a a fad'a musu gaskiyar lamari cewar Fahad, "no Fahad inji Abdul, dafa kafard'ar Abdul Fahad yayi ya k'ura masa ido ya langwab'ar da kai yana yi masa alamar please, murmushi Abdul yayi yace " Ok.


Fahad ya d'ora da cewa " ni ne *HAIDAR* ya b'oye muku ne sakamon maganar fyad'en Aisha, shiyasa ya sakaya sunana, amma magana ta gaskiya nine HAIDAR, kuma ainihin sunana FAHAD ne ba HAIDAR ba, sannan bani kad'ai SANATA SAMBO ya haifa ba mu uku ya haifa, nine babba sai gani na, shine HAIDAR, amma bashi ne na cikin labarin Abdul ba, ni ne acikin labarin Abdul, sai k'anwa ta Zakiyyah, sai Momyn mu, sannan gaba d'ayan mu uwar mu d'aya uban mu d'aya.


" zaku ji sauran labarin dangina idan matata Kausar zata bada labarinta, sannan Sanata Sambo yana nan a raye, yanzu baya komai sai aikin Allah, yana amfani da dukiyar sa ne wajen yiwa musulci da musalmai hidima.


"Ya b'oye sauran yaran nasa ne, saboda yanayin siyasa, hakan ne yasa bai bayyanawa duniya k'anne na ba, sai bayan da komai ya zama dai-dai hankali ya kwanta sannan ya bayyanawa duniya su.


Bayan Fahad ya gama bayanin ne, ya kalli sauran jama'ar yace " zamu je muyi sallah idan mun dawo sai muci gaba, Khamal ne fara bada nasa labarin.


Duk suka mik'e suka shiga cikin *6'S STARS* Hotel, bayan sunci abinci sunyi sallah suka d'an huta sannan suka dawo, bayan komai ya dai-daita Fahad ya kalli Khamal yace " oya start , murmushi Khamal yayi ya suma.



*LABARIN KHAMAL*


Ainahin sunana Khamaludden Ahmad, haifaffaan garin Kaduna ne unguwar rimi, mu biyu iyaye na suka haife mu, ni da k'anina HAMZA, tun muna yara iyaye mun suka mutu, a hannun kakarmu muka taso ita ce komai namu, bamusan kowa namu ba sai ita, kakar mu wacce muke kira da Hajiya ta d'auki san duniya ta d'ora mana, kasancewar mahaifin mu ne kawai d'an data haifa a duniya gashi kuma ya rasu.


" ni kuma na d'auki san duniya na d'orawa Hamza, dan gani nake kamar shine gata na, kasancewar bamu da kowa, duk abinda Hamza ke so to nima ina sanshi, haka duk abinda baya so nima bana sanshi, haka duk abinda ya gani yana so hankali na baya kwanciya sai naga ya mallake shi, idan da abinda nafi tsana a rayuwa ta shine b'acin ran Hamza.


"Kamar yadda nake san Hamza haka shima abin yake a b'angaren sa, koma ince yafi so na, fiye da yadda nake sanshi, dan ko ciwo na kwanta to shima sai yayi rashin lafiya ba k'aramar shakuwa ce a tsakanin mu, daga ni harshi babu mai aboki, mu biyu ne kawai muke rayuwar mu, har Allah yasa muka shiga jami'a, ni ina level 4 Hamza yana level 2.


" tun ina yaro Allah ya d'ora min masifar san ball, hakan ya sani nacewa ball, dan haka na zama cikekken d'an ball, nayi zarra sosai, harta an fara fita outing garuwan mu na nan gida Nigeria dani.


" haka kuma a jami'a nake ta karatu na, sosai na dage nake karatuna, dayake Medicine nake karanta, dan duk class din mu nayi fice, babu kamata,



Khamal na zaune yana duba wasu handouts, kansa a k'asa yaji ance "sannu ko, bai d'ago kan sa ba, yace " yawwa, jin wata siriyar murya mai zak'i yayi tace " please aron biro zaka bani yanzu zan maido maka, kai ya d'ago had'e da cewa " ok.... a mak'ogwaro maganar ta tsaya masa kasancewar wata dalliyar yarinya daya gani, tuni Khamal ya tsunduma duniyar tunani, ka kafe ta da ido, sai magana take amma ina hankalin sa ya tafi baima san tana yi ba.


D'an guntun tsaki taja a ranta tace " maye, k'afarta ta saka da taka k'afarsa da k'arfi, aiko yayi firgigit yace " hmmm ga biron ya mik'a mata asuwakin dake hannunsa dariya tayi tace " biro nace ba asuwaki ba, aiko tuni dariyar ta ta k'ara tafiya da imanin Abdul.


Ganin bai ma san me take ba yasata yin tsaki da k'arfi ta juya zata tafi, tsakin ne ya maido da Khamal hankalin sa, da sauri ya mik'e yace " sorry gashi ya mik'a mata biro, in banda dole babu abinda zai sata karb'ar biron, warta tayi had'i da watsa mai uwar harara tayi gaba.


Hannu yasa ya shafo sumar kansa had'i da sakin murmushi, tun daga ranar Khamal ya kamu da mugun san yarinyar gashi bai k'ara ganin ta ba, ko karatu ya kasa dan daya kalli Handouts d'in furkarta yake gani, shi kad'ai zaka ga ya zauna yana sakin murmushi.


Shima Hamza tuni ya dad'e da kamuwa da mahaukacin son wata yarinya kamar yayi hauka, dan ko numfashi zai ja da yarinyar yake yi, sosai yake jinta a ransa, suna zaune a d'aki Hamza ya kalli Khamal yace " Yaya ina cikin damuwa fa, da sauri Khamal ya daina abinda yake ya maida hankalinsa ga Hamza yace " meye matsalarka bros?


Cikin yanayin tausayi Hamza yake kallon Yayan nasa yace " wallahi Yaya wata yarinya nake bala'in so amma kwata-kwata tak'i kulani, babu yadda banyi ba amma tak'i ji nake kamar nayi hauka, ya k'arashe maganar kwalla na zubo masa, da sauri Khamal yasa hannu yana goge masa hawayen dake zuba ya jawo shi jikinsa ya rungume yana shafa bayan sa, yace " karka damu bro in sha Allah zata so ka, sai ma tayi hauka a kanka, zan koya maka yadda zaka b'ollo mata, k'ara rungume Khamal yayi yace " nagode bros.


A hankali Khamal ya zame jikinsa daga nasa ya kalle shi ya kanne masa ido d'aya yace " bros nima fa na kamu, ido Hamza ya zaro waje yace " da gaske Yaya? Cikin murmushi Khamal yace " da gaske amma kusan matsalar mu d'aya, nan Khamal ya fad'awa Hamza komai, ya k'ara da cewa, tun daga ranar ban kuma ganin ta ba, da tausayawa Hamza yake duban Khamal yace " ayya Yaya karka damu kaji in sha Allah zaka ganta, kuma cikin sauk'i zaka shawo kanta, " Amin bros ngd kaji.


Cikin kwanciyar hankali Khamal yake tuk'in mashin d'insa (lifan) zuwa gida ga uban hadari ya had'o, ga iska na kad'awa a hankali aka fara yayyafi, kamar daga sama Khamal yaga hannun mace tana tsaida shi da farko k'in tsayawa yayi, sai kuma yayi tunanin akoyaushe ruwa yana iya sakkowa, a hankali ya juya baya, saboda iskar da akeyi ne yasata jan mayafi ta rufe fuskarta, bismillah yace mata, a hankali ta dafa kafad'arsa ta hau mashin d'in, wani irin yarrr yaji Khamal, kasancewar wannan ne karo na faro da mace ta tab'a tab'a shi, a hankali suke tafiya, cikin muryarta mai dad'i tace " nagode! K 'irjin khamal ne ya buga da k'arfi dajin muryar ta, sosai zuciyarsa taci gaba da bugawa.

Magana taci gaba dayi tace" kasan me? " a'a ya bata amsa, " da da farko danaga ka wuce sai naji babu dad'i dan harna fara hango yadda ruwan sama zaiyi min dukan tsiya, gashi bana san sanyi, murmushi Khamal yayi yace " dana dawo kuma fa? " ai sosai naji dad'i, kasan me? a'a Khamal ya kuma fad'a " ina bala'in san irin wannan yanayin sosai, sosai nasha duka a gidan mu saboda wankan ruwa, sosai taci gaba da zuba masa surutu kasancewarta mai shegen surutu har Khamal ya gaji da surutunta, suna cikin tafiya aka tsuge da ruwan sama aiko sosai ta shige and kinsa, ta saka hannuwanta ta rungumo shi ta baya, gaba d'aya Khamal ya fita hayyacinsa cikin k'arfin hali yake tuk'in mashin d'in, kwatance take masa amma sama-sama yake jinta, a bakin titi tace ya sauketa sai da maimaita masa yakai sau biyar sannan Khamal yaji, a hankali ta sake shi, yace " mai tasa baza ki bari na kai ki har k'ofar gida ba?


"Nan ma ya isa, bana san na b'ata lokaci ne, kaga kuma kaima kana son ka koma ka canja kaya, ta fad'a tana k'ok'arin saukowa aiko tana taka k'asa santsin ruwa ya kwashe ta tayi baya zata fad'i da sauri Khamal ya rik'o ta fad'a jikinta, mayafin data rufe fuskarta ya yayi Fuska ta ta fito, sosai Khamal ya shiga tashin hankali, zuciyarsa ta tsananta bugawa da k'arfi a hankali yace " kece?


" eh nice ta fad'a tana barin jikinsa, ta juya tana tafiya da sauri Khamal yace " ba godiya? " bayan wacce nayi maka wata kuma kake so? tana tafiya tana bashi amsa, yace kin manta baki fad'a min sunanki ba, tana kaiwa dai dai kwana tajiyo tayi mishi wani rikitaccen murmushi, ta wuce aiko suman zaune Khamal yayi dan yakai 10mts bai tafiya, yana kallon k'asa yaga ID card d'inta, a hankali ya d'auka yana dubawa sunanta ya gani FATEEHA ya gani a rubuce, murmushi yayi mai bayyana hak'ora.


D'akinsa ya wuce kai tsaye ya cire kaya ya fad'a bathroom yayi wanka, jallabiya ya zira, waje ya fito ya zauna kusa da Hajiya yana ta faman sakin murmushi, aikinta taci gaba dayi bata kalle shi ba tace " wacece?


Murmushi ya sake saki yace " kai Hajiya ya akayi kika gane? Dariya tayi ta maida kallanta kansa tace " haba khamalu yanzu har yanayinka ya canja na kasa ganewa, nafi kowa sanin waye kai Khamalu, dariya yayi yace " FATEEHA sunanta, mik'ewa tayi ta koma kusa dashi ta kama kumatunsa ta shafa kansa tace "ja'iri, kayi k'ok'ari ka kawo min ita kona samun sauk'in aiki.


Dariya yayi yace" kai Hajiya aiki zaki rink'a tulata mata, gaskiya ni dai a'a ya fad'a cikin shagwab'a, suna haka Hamza ya shigo, "yawwa bros k'arasu da labari fa! da sauri Hamza ya k'araso yace " ta samu kenan Yaya? " sosai ma, " da alama dai Yaya ka samu yarinyar nan, Khamal yace " ka canka daidai bros, nan ya kwashe komai ya fad'a masa, " gud Yaya you are so smart, dama nasan zaka iya.


Dariya Khamal yayi yace" ka daina fada min kai mana, kaga ni dai ya maganar ka da yarinyar nan? Dariya yayi yace" ina nan inayin yadda ka sani.


" yawwa bros, Allah yasa ka shawo kanta da sauri, Hajiya ta wuce su tana dariya tace " ja'iran yara, Hamza ya mik'e ya rungumo ta baya yace" Hajiya ke kinganta kuwa? fara sol kamar ke, data duguwa ga manyan ido da dogon hanci, duka ta kai mishi tace" ban guri marar kunya kawai, Khamal na gefe yana dariya.


Washe gari da wuri Khamal ya shirya ya fita zuwa gym yana tafiya ya hango ta tare da k'awarta, da sauri yayi parking ya bita yana kira, a hankali ta jiyo, murmushi yayi mata yace " barka dai?

Bata bashi amsa ba fuskarta babu yabo babu fallasa, tace " waye kai? Ido ya zaro ya nuna kansa yace " wai ni? tace " a'a ni, dariya yayi a ransa yace " kai mata akwai rainin hankali, " ok kai kanka baka san kanka ba kenan, ta fad'a tana ci gaba da tafiya, da sauri ya tari gabanta yace " sunana Khamal Ahmad, ina karantar medicine, sannan ni..... Hannu ta d'aga masa tace " fad'i , yace " me kenan? "abunda ke ranka mana, "oh Khamal yace, dama kin manta ID card dinki ne jiya ya fad'a yana mik'a mata card d'in, karb'a tayi ta wuce yace " haba Fateeha ba godiya kuma? " bayan wacce nayi maka wata kuma kake san nayi maka, "yaushe kika ce min kin gode? " baga shi nan ka fad'a yanzu ba, ta fad'a tana tafiya, dariya Khamal yayi, yana tunnin rainin hankalin Fateeha, harta shige gida,k'ofar gidan yabi da kallo yana murmushi, lek'o da kanta tayi ta sakar mishi murmushi, sosai murmushin ya tafiya da Khamal.


Ranar Monday around 5:30pm ya fito daga lectures a gajiye, direct ya wuce cafeteria, a zaune ya gansu su biyu ita da k'awarta ta jiya, murmushi yayi ya nufe su, k'awar ce ta fara ganinsa, a hankali ta rad'a mata ga mayenki nan, " what? Fateeha tace, kafin ta rufe bakinta ya k'araso inda suke, a hankali ya kalle ya da alamar tausayi yasa babban d'an yatsansa a baki, kallonsa tayi rai a b'ace zatayi magana da sauri ya tare ta yace " a'a pls karki ce komai ni zance yadda yayi maganar maganar dolo.


Kwaykwayon maganarta ya shiga yi yace " waye kai? sai yayi maganar normal yace " ni ne na jiyan nan dana kawo miki ID card, sai kuma ya kuma kwaykwayon maganar ta yace " oh! to lafiya? cikin maganar sa yace Alhamdulilla......a fusace ta mik'e cikin masifa tace " wai mai yasa ka takura min me!? haba ka dame ni, ido ya k'ura mata a ranta kuwa yace " masha Allah, ita komai kyau yake yi mata, yadda ya k'ura mata ido ya k'ara hasala ta, ta kalli k'awarta tace " Khadija zo mu tafi, da sauri ya sha gabanta, tsaki tayi, ta juya idonta had'i dafe kanta, amalar ta gaji, Khadija ta kalle ta tace " please ki saurare shi, kiji abinda zai fad'a miki, inba haka ba bazai daina bin mu ba, mu zama abin kallo.


Tsayawa Fateeha tayi ta kalle shi, tace " fad'i nutsuwarsa ya tattara ya maida hankalinsa jikinsa, with full confidence ya kalle ta yace " ina sanki, ido ta zaro waje tana kallansa, " eh Fateeha ina sanki, ina miki mugun so, ta yadda koyaya na motsa sai kin fad'o min, duk numfashin dazan ja dake nake yinsa Fateeha, ina sanki tsakani da Allah, i love you with all my heart, u are my first love please don't say no, yana fad'a ya juya yayi tafiyarsa, baki bud'e Fateeha tabi bayansa da kallo, cike da mamaki, hannunta Khadija ta kama suka tafi, a k'ofar gida aka sauke Fateeha, Khadija ta dafa kafad'arta tace " kiyi tunani k'awata karkiyi wasa da damarki, Khamal cikekken namiji ne da kowacce mace zata so ta mallake shi.


Cikin sanyin jiki Fateeha ta kalli Khadija tace" nagode sosai kawata da shawarar ki, tunda Fateeha ta koma gida ta kasa samun nutsuwa gaba d'aya tunanin maganganun Khamal da Khadija ya hana ta sakat, sosai yake fad'o mata arai, tana jin sa a ranta, sannu a hankali san sa ya rink'a shiga jin kinta, batare data yi aune be ya gama mamaye ko'ina nata, burinta kawai ta k'ara ganin sa.


Washe gari sun safe ta shirya kasancewar tana da lactures da safe, sai da kammala komai sannan ta fita, sai yamma sosai suka fito, a bus stop ta tsaya duk ta gaji Allah Allah take ta koma gida, ga rana na dukanta, duk bayan minti d'aya sai tayi tsaki, a gabanta yazo ya faka, had'i dayi mata sallama, a hankali ta d'ago kai ta kalle shi, sanye yake da light blue d'in shadda tasha simple aiki, ya saka

Please Login or Register in order to submit comment