Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hanya idan babu in sha Allah. Ai burina mu shiga labour room tare. Shakiyanci suka yi ta yiwa juna. Daga baya suka shiga kitchen da Zuhra tace kannen Hamza zasu zo. Hajara ta bude taga danwake...anya Zuhra kina da kai kuwa? Yan uwan miji zasu zo ki rasa abinda zaki basu sai danwake? Zuhra tace yayansu ne yace shi suka fi so. Plates suke hadawa da cups suka ji sallama a falo. Dama Zuhra da hijab dinta a hannu saboda kada suzo da maza. Kuskuren da mata da yawa keyi kenan. Yan uwan miji maza ko abokansa su zo sai mu fito babu lullubi ko hijab. Muji tsoron Allah mu kare mutumcinmu. Mota biyu suka yo duk a gidan nasu suka hadu suka taho tare. Zuhra fuskar nan dauke da fara'a sai kunyar su Mariya take yi. Suka gaisa da Nura yace zai tafi sai bayan sallar Juma'a zai dawo. Bajewa suka yi da 'ya'yansu ana ta hira da Zuhra. Ta sake musu sosai kada ma Adabiyya da Hamida suji labari. Ta tambayi yaran sunayensu suka fada mata. Karamin dan da Ummahani ke goyo kuwa Zuhra ta goya shi saboda ya hana mamansa sakewa. Tun yana kuka har yayi bacci. Da taimakon Hajara dasu Adabiyya ta hado musu abinci. Cikin tabarminta ta shimfida manya biyu. Jidda tace ai ki hada mana a tray kawai muci tare yafi kara zumunci. Zuhra na murmushi tace haka Ya Hamza ma yace. Su Ummahani suka hada ido suna dariya. Yaya yaji dadin aure....

Sakewa da jindadin da basu taba yi ba a gidan dan uwansu yau sunyi. Yabo da addua kam Zuhra tasha a wurinsu. Nura yafi kowa santi da ya dawo aka hada masa nasa abincin. Bayan sun gama kuma dukkansu sunsa hannu wurin gyara falon da wanke wanke. Tamkar 'yan uwana jini haka suke jin Zuhra. Sai da sukayi sallar la'asar suka fara haramar tafiya. Ana haka sai ga Hamza ya dawo daga wurin aiki. Shima yau ya gaji sosai. Kudi ya kusa kammaluwa zai sallami su Mr Peter ya rabo da kaya. Dadi yaji yadda ya tarar da kannensa sun cika gidan ana ta hira. Zuhra na tsakiyarsu da goyo kamar sun shekara tare. Suna ta gaishe shi da yi masa sannu da zuwa ita kuwa kanta na kasa. Duk kunyarsu take ji, tana kallo yace bari nayi wanka na sauko kafin ku tafi. Ummahani ce ta dan zungureta Anti Zuhra tashi mana Yaya ya dawo. Indai don wadannan ne, ta nuna Jidda da Mariya suna dariya...duk ki manta dasu kowacce ta iya rike miji in fada miki. Zuhra harda rufe fuskarta da hannuwanta. Hajara ce ta tasheta ta karfi. Zata hau saman Ummahani tace kawo dan nan kada yace zamu bankare masa kirjin amarya.

Ita fa ba saba binsa daki sannu da zuwa tayi ba. A falon ta dan tsaya sannan tayi sallama tare da cewa in shigo. Daga ciki Hamza yace yes come in. Kwance yake akan gado amma kafafun na kasa ko takalmi bai cire ba. A tsorace tayi saurin zuwa gaban gadon, cikin sanyin murya tace...Ya Hamza jikin ne? Harararta yayi sai yanzu kika ga damar zuwa. Zuhra tace ina? Zama yayi suna fuskantar juna tana durkushe a gefen gadon. Yanzu mijinki ya dawo ba sannu da zuwa bare ki karbi jakata. Tace yi hakuri, bai kula ba ya cigaba da cewa kuma na taho daki baki biyoni kin cire min kaya kinyi min wanka ba. Zuhra ta mike da sauri....eyyeeee Ya Hamza wanka? Ya kashe mata ido wanka fa. Don Allah kayi hakuri....sai kawai ta soma hawaye. Saurin tashi yayi ya janyota jikinsa. A cinyarsa ya zaunar da ita tayi saurin rufe ido. Wai meyesa Ya Hamza ke yi mata hakane yanzu. A hankali yake magana Cutie you scared me. Na kiraki yafi sau goma baki dauki wayar ba. Dafe kai tayi... ina jin hayaniya ce tasa banji ba amma kayi hakuri. Kokarin tashi take yi ya sake riketa sosai yana kallon wuyanta. Cutie me ya sameki a nan ya fada yana dan taba wurin...auchh Ya Hamza da zafi fa. Cikin shagwaba take magana tana kara narkewa jikinsa ba tare da ta sani ba. Sorry meye ya sameki? Murmushi tayi masa mai ne ya kona ni da har zanyi kuka saboda zafi sai na tuna ba karamin lada aka rubuta min ba. Na kone a kokarin karrama baki... ta washe baki tana murmushi. Hura wurin ya rinka yi yana mata sannu. Zuhra dai duk tsigar jikinta ke tashi ta dan wayance, 'yan gidanku suna da kirki duk ina sonsu. Zanyi kewarsu idan na tafi. Tashinta yayi shima ya mike...tam, zaki fara ko? Ni tashi muje na sallamesu sai na dawo nayi wankan.

Suna saukowa su Mariya suna ta dariya. Hamza yace zan hanaku zuwa gidan nan tunda gulma kuka zo yi. Cikin raha suka yi sallama duk suka tafi. Dubu biyu ya bawa Hajara ta shiga mota. Tayi masa godiya sosai. Suna shiga mota mai gyaran inji yazo ya fara aiki.

Zama Zuhra ta sake yi suka kafa sabuwar hira dasu Hamida sai ga Hamza ya leko yana kiranta. Tace bari ta sauko sai suyi shawarar abincin dare. A kofar dakinta ta ganshi ya bude tabi bayansa. A ina su Hamida zasu kwana? Zuhra tace ai tare zamu kwana a nan dakin kayansu na cikin kwaba. Sai da ya gama dariya sannan yace don Allah ki dena cewa kwaba sai a zata baki waye ba, wardrobe sunanta. Ta sha kunu sai kayi ta tsokanata ko? To Cutie kauyancinki ne yayi yawa. Yanzu dai har su Adabiyya su tafi a dakina zamu rinka kwana tare. Kinga kada suyi tunanin akwai matsala a tsakaninmu sannan zamu cigaba da lessons dinmu ko. Yana kare magana ya bude wata drawer inda yaga ta ajiye kayan bacci ya dauko mata wasu riga da wando. Rigar dai kamar bra ta sama sai ta bude kadan taga kasa. Wandon kuwa ko cinya bai gama rufewa ba. Zuhra na gani ta kwace kayan daga hannunsa a kunyace, ni gaskiya bazan saka wannan a gabanka ba. Yace to dauko wadda kike so....ta fara neman wata kenan yace amma ki kwana da shiri duk wadda kika saka ko kinyi bacci sai na cireta. Baki bude ya barta ya shiga toilet ya dauko brush dinta. Sannan ya dibi turaruka da body spray harda man shafawa. Ki karo wasu abubuwan idan kina bukata harda kayan da zaki saka da safe. Fita yayi ya barta a tsaye ta ma rasa abinda zata yi.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 53

Batul Mamman(Mrs)





Tunda suka yi maganar nan Zuhra take bata rai ko dakin nasa bata je ba . Ya ma za'ayi yace tasa wannan kayan duk ya gane mata jiki. Ta fasa kwana a dakin nasa ma a falon zata kwana a kan kujera. Sun gama girki sannan suka yi sallar Isha. Bayan sun idar tana daura dankwali Hamida tace Anti Zuhra meyasa bakya saka relaxer a kanki gashi kanki yana da yawa, irinsa yafi kyau. Adabiyya ta taba gashin don Allah ki fadawa Yaya gobe ya barmu muje salon din bayan layin nan. Baki ga yadda suka yi suna ba kuma duk musulmai ne matan wurin. Hamida tace ni da bikin Zayya munje har lalle suke yi mai kyau. Don Allah Anti Zuhranmu ki tambayar mana. Zuhra tayi murmushi nifa bana son Antin nan haka kawai bayan inajin duk kun girmeni. Nan aka fara fadar shekaru Adabiyya ta girmeta ita kuma ta girmi Hamida. Duk hirarsu Hamza yana tsaye a bakin kofa yana ji ya dawo daga masallaci. Zuhra ta sake tana ta hira amma tun bayan dawowarsa bai sami damar kebewa da ita ba. Abincinsa ma a falonsa na kasa ya gani. Gyaran murya yayi sannan ya shigo...kun hadu kun cika gida da hira ko sallama bakwa ji. Hakuri suka soma bashi Zuhra ta kawar da kai. Hakan baiyi masa dadi ba don ba na kunya bane, da gani fushi take yi. Tunanin dalilin fushin yake yi amma ya kasa ganewa. Kiranta yayi sannan ya shige falonsa. Kanensa na zaune bare ya tambayeta a nan.

Da ta shiga falon gani kawai tace ta dan durkusa a gefen kujera. Lallai ya tabo Cutie dole ya bata hakuri. Yi yayi kamar bai gane tana fushi ba yace tashi ki zubo mana abinci yunwa nake ji. Ni naci da su Hamida ta bashi amsa a takaice. Sai ya dan kashingida to shikenan ki barshi na fasa ci nima. Kallonsa tayi da mamaki a fuskarta ba yanzu kace kana jin yunwa ba. Ya kada kai tunda kinci ba tare da kin jirani ba shikenan, am not hungry anymore. Duk sai bata ji dadi ba. A hankali ta dan matsa kusa dashi, Ya Hamza nayi maka laifi ne? Yadda take maganar yasan kuka take shirin yi masa. Yace a'a naga kema kina ta bata rai shiyasa na dena jin yunwar. Sunkuyar da kanta tayi sai hawaye...hankalin Hamza ya tashi ya sauko kasan ya matso kusa da ita. Yanzu Cutie me nayi miki kike kuka....cikin kukan tace ba kaine kace sai na saka wannan kayan ba dazu, kuma da nayi fushi baka rarrasheni ka bani hakuri ba. Tasa hannu ta share hawayenta kuma shine yanzu kake fushi dani don Mala'iku su rubuta min zunubi. Zama yayi yana kallonta har ta gama bayanin sannan ya soma murmushi yi hakuri my cute baby ashe fushin duk laifina ne. Kiyi hakuri dazun ma wasa nake miki. A take ta washe baki kamar ba ita take kuka ba...da gaske ka yarda nasa rigar mutumci? Ya dafe kai wato wadancan ba na mutumci bane. To ki saka duk wanda kike so kinji. Yanzu dai bani abinci sai muyi shirin bacci. Tana tashi yayi ajiyar zuciya Zuhra akwai iya rigima. Ji yadda take masa kuka lokaci daya kuma ta dena kamar ba ita ba.

Bayan yaci abinci ta koma suka zauna kallo ita da su Adabiyya. Shiru shiru Hamza na jiranta a dakinsa taki hawowa har shadaya da rabi. Duk sai ya damu so yake kawai ya ganta. Gajiya yayi da jira ya sauko ya tashe su suje su kwanta dare yayi. Zuhra na ganin ya tafi tace akwai TV a dakina muje muga karshen film din. Adabiyya tace wane karshen film kuma ki tafi ki kwanta Anti Zuhra kada kisa Yaya ya kora mu gida da sassafe.
Suna shiga dakinta taga Hamida ta shiga wanka Adabiyya ta cire kaya ta daura tawul tana jiranta. A ranta Zuhra tace ashe kowa na wankan dare banda ni. 'Yan sauran kayan bukatarta ta dauka tayi musu sai da safe. Tana sallama falon nasa ta ganshi zaune ga laptop a gabansa ya zurfafa yana aiki, TV kuma a kunne ana news a BBC. Zama tayi a wata kujerar tace masa sannu da aiki. Hannu ya daga alamar amsawa ya cigaba da abinda yake yi. Remote ta dauka ta canja tashar zuwa film din da suke kallo kafin ya tashe su. Wurin minti shabiyar tana zaune, idonsa yana kan aikin gabansa yace Cutie tashi kije kiyi wanka. 'Yar shagwaba ta soma yi masa ka bari a gama don Allah. Dago kai yayi yana kallonta to babu komai bari na gama aikin gabana sai nayi miki. Bata jira ya kare zancen ba ta shige cikin dakinsa harda murda key. Girgiza kai yayi yana dariya. Tunda tare zasu kwana ai bashi da damuwa.

Sai da ta gama gyara jikinta tsaf ta tuna bata dauko wasu kayan baccin ba. Wadanda ya dauko ta gani akan gadon ta dauk tasa. Kayan sunyi mata kyau sosai ta saka hula sannan ta dauki hijab dinta mai hannu dogo har kasa ta dora a kai. A haka zata kwana a can gefen gadon idan yaki yarda ta koma falo. Tsoro take kada ya sake rungumarta irin na daren jiya ko ma yayi mata kiss irin yadda yayi da safe. Lips dinta ta dan shafa tana murmushi ashe kiss dinma ba kazanta bane. Ji tayi Ya Hamza ya kara shiga ranta sosai. Tunanin me kike yi haka harda murmushi Hamza ya fada yana rufe kofar dakin da mukulli. Hantar cikinta ce ta kada saboda tsoro murya a sarke tace bari na koma falo na kwana. Dan hararta yayi kina son muyi fada ne? Ta girgiza kai yace to sami wuri ki kwanta ni sallah zanyi. Kafin ya fito daga alwala ta shimfida abin sallah biyu a inda take tunanin nan ne gabas. Kallonta yayi tayi masa murmushi nima nayi alwala ai. Zuhra batasan komai tayi kara shiga ransa take yi ba. Dadi yaji mara misaltuwa da yaga ta tsaya akan abin sallah tana jira ya tayar. Da Izzy ce sai dai ta kwanta yayi ya idar da nafilarsa ko ta bijiro masa da bukatarta a lokacin. Sunyi kusan minti arbain da biyar suna sallah sannan ya idar yayi musu addua. Zuhra na ninke abin sallan tace Ya Hamza karatunka dadi wallahi. Yace nagode kinyi min addua kuwa? Yana kallo da hijab din ta kwanta tace sosai ma. Sai da ya kashe fitila suka kwanta kowa na nasa gefen Zuhra tace Ya Hamza ina son tambayarka amma kada kaji haushi na. Idan na bata maka rai kayi hakuri. In sha Allah raina bazai baci ba yi tambayarki. Sauke numfashi tayi da karfi...na kula tun satin da ya wuce wani lokacin sai ka zauna kayi ta tunani. Har ina tsoron ko duk saboda ni ne sai naga kuma kamar abin yafi karfin matsalar aurena da kayi ba'ason ranka ba. Idan bazaka iya fada min ba ma babu komai zan tayaka addua kullum. Amma kasan wani lokacin idan ka dan fadawa wani matsalarka sai kaji nauyinta ya ragu. Ko jibi idan su Khalifa suka dawo sai ka fadawa mamansu. Tunda ta fara magana yake kallon inda take kwance. Zuhra daban ce shine kawai abinda yake tunani. Har tana lura da damuwarsa duk yadda yake kokarin boyewa. Shiru yayi ya kasa magana saboda yadda ta tsaya masa a rai. A hankali ya fara yarda da cewa bazai iya rabuwa da Zuhra ba. Ji tayi yayi shiru tace Ya Hamza nayi maka laifi ko? Ka yafe min. Babana ne yace ana son mata da miji su rinka yiwa juna addua. Naga ko dai a yaya muka yi aure kai mijina ne yanzu shine nake son yi maka addua. Har yanzu bai yi magana ba sai ma haushin kansa da yake ji saboda yadda ya kuntata mata harda sa ranar saki. Hankalin Zuhra ya tashi da lalube take mika hannu saboda dakin yayi duhu sosai sai sautin AC, Ya Hamza kayi magana mana, Ya Ham....hannunta ne ya kai jikinsa ya janyota ya rungumeta sosai suka kwanta. Kanta akan kirjinsa da yake a bude bai balle maballan ba yaji saukar hawayenta. Saurin dagata yayi duk ta dukunkune jiki da hijab yace Cutie kukan me kike yi? Har da sheshsheka tace ba kaine kayi shiru ba na zata wani abu ne ya sameka. Hijab din jikinta yake kokarin cirewa tana rikewa a raunane yace Cutie kin damu dani ne haka. Da muryar shagwabarta tace kaifa Yayana ne yanzu wanda yake min kirki bana so muyi fada har mu rabu. Ta rike hijab din a jikinta don Allah kada ka cire min kunya nake ji. Kyaleta yayi ya rungumta a haka. A hankali ya bata labarin da babu wanda ya sani sai kalilan a kamfaninsa. Amma bai fada mata duk Izzatu ce take yin sanadiyar faruwarsu ba. Har mamakin kansa yake yadda ya iya budewa Zuhra kazamar yarinyar nan mara kunya cikinsa. Muryarta a kasa saboda labarinsa yasa ta kara yin kuka tace Ya Hamza ka godewa Allah da duk wata jarabawar rayuwa. Kaga ni bana sonka aka yi mana aure amma dana hakura na barwa Allah sai gashi ka zama mai kirki har ina sonka sosai a matsayinka na Yayana. Allah baya dorawa mumini abinda yafi karfinsa. Kuma yarda da qaddara yana karawa mutum imani da kusanci da Allah. Kada ka taba jin tsoron talauci Allah shine mai azurtawa. Zan rinka tayaka addua har Allah Ya kawo karshen komai. Hawaye ne suka cika masa ido ba na komai ba sai na karin imani da maganganun Zuhra suka saka masa. Abu daya ya kudurce a ransa zaiyi iya kokarinsa ya koya mata sonsa domin a halin yanzu baiga wanda ya isa ya rabashi da ita ba sai Allah. Idan abin nan da yake ji soyayya ce da bai taba tunanin zai yiwa wata ba bayan Izzatu to lallai ya amince har ransa yana son Zuhra. Ita kuwa duk da kunyar da take ji saboda yanayin kwanciyarsu ta hakura saboda yadda take jin tausayin Ya Hamza.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: [10/2, 9:57 AM] +234 803 220 0468: AL'ADUN WASU 54

Batul Mamman(Mrs)




A hankali ta dan bude idonta sai taga haske a cikin dakin. Bude idanun tayi gabadaya ta kalli agogo. Karfe bakwai harda minti tara. Subhanallah ta fada tana kokarin tashi daga kan gadon. Rabin jikin Hamza duk ya danne mata hijab tayi kokarin janyewa ta kasa. Tana son taba shi ta tashe shi amma haka kawai take jin wata irin kunyarsa. Baccinsa yake hankali kwance. Karewa fuskarsa kallo tayi tana ayyana irin kamaninnsa da dukkan kannensa. Duk Alhaji Nasiru suka biyo shiyasa kana ganinsu kaga 'yan gida daya. Sajensa yafi komai daukar hankalinta kuma yana karawa fuskarsa kyau da kwarjini. Ga wani tausayinsa da yake ratsata saboda labarin da ya bata da daddare. Shagala tayi da kallon mijinta tana tunanin yadda zata ji ranar da zasu rabu. Idonsa a rufe yace irin wannan kallo Cutie sai na zata irin son nan kike yi min, in ba ni ba sai rijiya. Saurin tashi tayi zata gudu saboda kunyar da taji ya kamata tana kallonsa hijab dinta ya shake mata wuya. Tashi yayi yana mata sannu. Kinga maganin masu kwana da miji da hijab kenan. Kan Zuhra dai yana kasa ta kasa kallonsa ya tashi ya shige toilet yayi alwala. Bayan ya fito itama tayi suka yi sallar asuba tare da salatul duha tunda gari ya waye.

Sai da suka gama azkar sannan yace mata yau kin janyo mun makara sallar asuba. Tashi tayi tana ninke abin sallah, babu ruwana ko yanzu ma ai na rigaka tashi. Gadon ta tafi zata gyara Hamza ya haye ya zauna a tsakiya yace ni bacci bai isheni ba kizo mu kwanta. Zuhra tace kitchen zani kaga muna da baki. Kinga zo kiyi kwanciyarki ya fada yana mika mata hannu. Indai wadannan yaran ne sai su kai shadaya suna bacci. Zuhra tace to maigadi fa. Tashi Hamza yayi ya zagaya ta bayanta, bata ankara ba taji ya dagata cak ya sauketa a taskiyar gadon. Tsoro taji ta kankame shi ya kwanto a jikinta yana kallon yadda ta runtse idanunta. Sonta yake ji yana shigarsa ko ta ina. Idan da wani ne ya fada masa zai so ta bazai taba yarda ba. Kamar mai rada yace Cutie ba'a son yiwa miji musu. Mu danyi bacci kadan sai ki tashi. A jikinsa ya kwantar da ita tasa hannuwanta duk biyu ta rufe fuska. Matsananciyar kunyarsa take ji fiye da ta da. Kanta na kirjinsa ya sake sassauta murya. In cire miki hijab din kisha iska? Maimakon ta bashi amsa kama jikinta tayi kam. Bai sake magana ba sai bayanta da yake shafawa a hankali.

Har bacci ya soma daukarsa ita kuwa ta zata shima idonsa biyu tace Ya Hamza akan maganar da mukayi jiya akwai shawarar da nake son baka amma don Allah idan hakan laifi ne kayi hakuri. Ina jinki yace cikin muryar bacci. Ta tashi zaune, kayi hakuri bansan ka soma bacci ba. Bude ido yayi yana kallonta, babu komai ina jinki. Komai nata kishiyar na Izzatu ne.

A nutse ta soma magana kamar ba ita ba. "Nasan duk wadanda suka san abinda ke faruwa da kai sun baka shawara kila ma irin wadda zan baka ko wadda tafi ta. Lokacin da tsautsayi ya ritsa da Baba a wurin aikinsu mun sha wahala. Sanda yake da duka hannuwansa munfi wadata da rufin asiri. Da aka yanke hannun yana jinya a gida ga kudin magani da sauran abubuwa na yau da gobe ya kasance an koro ni daga makaranta. Ba don Malam babansu Hajara ba abinci ma sai ya gagare mu wata rana duk da a haka Baba ya fishi rufin asiri. Wata rana Umma tace naje makota na sanar dasu zata fara wainar flawa. Ranar baka ga kukan da nayi ba." Hawayen ta soma Hamza ya sa yatsansa ya share mata. Ta cigaba da magana "bakincikina mun talauce har abin ya kaimu ga sayar da wainar flawa. Ina kuka na sanar da Umma bazani ba, ta soma fada nace so take kawayena suyi min dariya. Sai ta zaunar dani ta dena fada tace min. Zuhra aure ba abin wasa bane. Aljannar mace kuma tana karkashin kafar mijinta. Ma'ana samun aljannarta na tattare da yardar mijinta. Lokacin da babanki yake da lafiya ya wadata mu Alhamdulillah. Yanzu kuma lalura ta same shi 'yan uwa da abokan arziki duk sunyi mana kokari amma dole mu yiwa kanmu. Idan miji ya shiga matsala mace ana so tayi iya kokarinta da yin abinda bai sabawa shari'ah ba wurin kyautata rayuwarsu. Idan har bata da hali kuma sai ta taya shi da addua dare da rana har Allah Ya kawo musu sauki. Kada ki taba daukar maganar masu cewa idan mace ta taimaki mijinta wata rana zai saka mata da tsiya. Dama don Allah kika yi saboda haka ki nemi lada a wurinSa. Tun daga ranar na koyi tattali da adana abu saboda na ragewa Baba kashe kudi. Idan ya siyo min turare ko sabulu na rinka janjaninsa har kazanta ta dan kamani. Amma dai yanzu na dena ko " tayi maganar da murmushi sannan ta dago kanta suka hada ido da Hamza." Kasan me yasa na baka labarin nan?" Yace "sai kin fada". Zuhra ta gyara zama." Ni a shawarar da zan baka Ya Hamza kafin komai ya daidaita ka rage kashe kudi. Misali tunda nazo gidannan tun karfe shida na yamma ake kunna inji har tara na safe. Wani lokacin da rana ma sai an kunna duk yadda abubuwa suke tsada yanzu. Kuma na kula ranar alhamis a waje kake siyo abinci. Gashi yawancin safiya kullum za'a soyawa su Khalifa kwai kowa bibbiyu. Suci rabi su bar rabi ya shiga shara." Ta dan daga hannu " ba cewa nayi a takurasu ba amma a rage irin wannan. A koya musu yau su sami yadda suke so gobe su hakura saboda halin rayuwa. Injin ma a barshi sai kamar tara ko goma na dare a kunna. Da duk abubuwan da kasan basu da mahimmanci sai a barsu."

Tunda Zuhra ta fara magana Hamza yake kallonta. Kallo irin na tsabar soyayya da mutuntawa. Yarinya ce Zuhra sosai a kanshi da Izzatu amma duk yadda suke ganin shirmenta ta san abinda take yi. Matsalar gabansa bata dame shi ba kamar yadda yake son gina soyayyarsa a zuciyar amaryarsa.

Zuhra duk ta tsargu da kallon da yake mata tace Ya Hamza na shiga abinda bai kamata ba ko? Nasan duk aikin Maman Khalifa ne. Dama kawai nayi ne don nima na sami ladan da mata ke samu a gidan aure. Kaga bansan lokacin da zan sake aure ba idan muka rabu. Tayi masa murmushinta mai kyau...shiyasa nake son samun lada a iya zaman da zamuyi.

Kasa magana yayi sai mamakinta kawai. Dan taba shi tayi saboda yadda ya kasa dena kallonta. Ba tare da ya dauke idonsa daga kanta ba ya dorata kan cinyarsa tare da rungumeta sosai a jikinsa. Sannan yace nagode sosai Fatima, Allah Yayi miki albarka. Abinda na fada miki jiya babu wanda ya sani sai ke sai mutane kadan a office dinmu saboda haka ki rike min sirrina. Kuma na baki dama ki fada min duk abinda kika ga ya dace na gyara ni Hamza nayi miki alqawari zan gyara. So yake yace mata yana sonta amma baya son tsorata ta don yasan tana tsoron halin Izzy. A hankali zai bi da ita har sai yasa taji irin yadda yake ji game da ita a tasa zuciyar.

Ba jimawa ta fito daga

Please Login or Register in order to submit comment