Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

RANA DA WATA
Littafi na daya 1
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
PART:- A

Masu karatu ayimin afuwa don kuwa farkon fallen littafin ya yage amma ga abunda ya kunsa
.
Acan cikin wani kauyene wata mata mai suna shafhila sai faman naku da ta ke tayi yayin da sararin samaniya kuwa sai amsawa yake, ba'a bata lokaci ba matar ta haifo yaranta guda biyu
.
Babu abun da zai baka mamaki da wayannan yara face sam basa kaunar junansu, don kuwa koda yaran suka fara girma sai ya kasance suna matukar GABA da juna tamkar RANA DA WATA ,
A kowani lokaci kuwa babu abunda suke yi face fada da junansu wanda wannan abu yana matukar damun mahaifiyarsu shafhila
Shekaru suna ta ja har takai sun girma sun mallaki hankulansu amma basu daina wannan gaba da fada ce fadace ba
Macen mai suna zuhaisa zuciyarta bakine sam babu ko digon tausayi ko imani a tattare da ita
Shi kuwa namjin mai suna huzainu babu abun da ya tsana face zalunci , kuma shi kadai ne acikin wannan gari wanda yake hana Zuhaisa ai kata zaluncinta don kuwa aduk lokacin da zata aikata zalunci sai ya bayyana, sannan su cigaba da bakin yaki tamkar ba ciki daya suka fito ba
.
Hakan shi yasa mahaifiyarsu ta nufi wajen boka wani shahararren boka mai suna sharanu koda isarta wajensa har ta budi baki zatace wani abu sai boka shuranu ya dakatar da ita sannan yace" yake wannan tsohuwa kiyi sani cewa nasan abun da ke tafe dake ,"koda jin haka sai shafhila tace
Shin boka yaya za'ai su hada kansu su daina wannan gaba da fadace fadace

Koda jin bukatar shafhila sai boka sharanu ya tuntsire da dariya
Al'amarin da yai matukar firgita shafhila kenan
Lokaci guda boka sharanu ya murtuke fuska ya dubeta yace "yake wannan uwar jarumai ki sani cewa har abada yayanki ba zasu taba kaunar juna ba , kuma ba zasu taba zama ba a waje daya domin tamkar RANA DA WATA suke .
.
Sai aranar da dayansu ya kashe daya sannan nadama da takaici zasu zo masa.
Ki sani cewa kin haifi yayanki ne a ranar da aka samu kisfewar rana.
Ita macen kin haifeta ne a dai dai lokacin da rana zata kisfe , don haka ta zamo mai bakar zuciya da bakin rai . Saboda rana aba ce mai zafi,
.
Shi kuwa namijin kin haifeshi ne a dai dai lokacin da wata ya kisfe, shi yasa ya zamo mai tausayi da sanyin rai (kaman ni kenan, kar dai ku shagala Alkalamin shuraih 99% ne]
.
Wadannan yaya naki zasu daukaka a duniya irin wacce babu kamarta a wannan zamani.
.
Macen zata zamo gagarumar matsafiyar sarauniya .shi kuwa namijin zai zamo gawurtaccen sarki ma'abocin wani bakon Addini,
.
Zasu yi ta yakar junan har izuwa lokaci mai tsawo, yayansu ma sai sun gaji wannan gaba kuma a karshe sai dayansu ya kashe daya"
.
Koda jin wannan labari sai tsohuwa shafhila ta dafe kai tana mai fashewa da matsanancin kuka na bakin ciki tamkar ba zata daina ba .
.
Da kyar boka sharanu ya lallasheta tayi shiru snnan ta dube shi tace da shi.
"Yakai wannan boka mai daraja , yanzu wace hanya zan bi na sauya wannan al'amari ya zamana cewa wadannan yaya nawa sun hada kansu sun daina gaba?"
.koda jin wannan tambaya sai boka shuranu ya sake tuntsirewa da dariya a karo nabiyu , daga san ya takarkare ya kwarara uban ihu mai firgitarwa , har yana birgima a kas,
.
Al'amarin daya firgita tsohuwa shafhila kenan har ta ja da baya .
Ta takure jikinta ajikin bangon dakin kamar zata saki fitsari saboda tsananin tsoro daga can kuma sai taga boka shuranu yayi doguwar ajiyar zuciya a lokacin daya jike sharkaf da gumi sannan ya dubeta yace "yake wannan tsohuwa, kiyi sani cewa babu wani abu da zai iya canza wannan al'amari face ki sallama rayuwarki don inganta tasu.
Kuma yin hakan ma ba abu bane mai sauki ba domin dole kije har can kogon darul yazmin dake can karshen birnin sin ki yanka jijiyar hannunki na hagu a cikin kokon dodonniya HUJUMU-MAJNUN har sai kokon ya cika ta zo ta shanye jinin duka , nan take rana zata kisfe .
.
Idan da rana ne abin ya faru. Haka kuwa wata zai kisfe, idan a lokacin da abin ya faru dare ne ki sani cewa a tarihin kogon darul yazmin tun daga wanzuwarsa kawo izuwa yanzu, babu wani bil'adama ko aljani daya taba shiga cikinsa ya fito a raye sai dai a mace aciki har ya rube, ya zama kwarangwal.
.
Duk abin da mutum yake nema na duniya in dai ya shiga cikin darul yazmin sai ya sameshi walau dukiya ko maganin wata cuta data gagara . Matsalar dai itace koda mutum ya sami biyan bukatarsa bai isa ya iya fitowa ba araye daga cikin kogon saboda hujranul-majnun ce take gadin duk abin daya ke cikinsa
(Lallai dole nayi shiri na ttunkari kogonnan saboda wata bukata tawa ehm shuraih 99%)
.
Dodonniya hujranul majnun ta kasance gabjejiyar dodonniya mai tsawon gaske gami da kauri da fadi. Idan ta tsaya a gaban mutane komai yawansu sai su ga kamar a gaban tsauni suke.
Ta kasance basadaukiya mai tsananin karfin damtse domin komai girman dutse da kwarinsa
.
Idan ta dokeshi da hannunta sai yayi bindiga ya tarwatse, kuma tana iya kwakule duwatsu da kaifin faratan hannayenta ko ta yanka karafa da su ta sarrafa karafunan wajen kera abubuwa da yawa kamar kofunan zinare,gadaje,kujeru,da saurran kawa irinsu lu'u lu'u jauhar da sauransu wanda Aljanu suke zuwa su siya a wajenta
.
Masana da masu bincike sun tabbatar da cewar a duk fadin duniya babu wani makeri wanda yafi dodonniya hujranul-majnun iya kira da sanin karfe kuma babu wani boka wanda yafita karfin sihiri, babu wani sadauki wanda ya fita karfin damtse gami da zafin nama.
.
Kaifi da tsini basa tasiri a jikinta
.
Dukiyar data tara kuwa a kaf duniya babu wani Attajiri daya tara kamarta komai karfin arzikinsa da karfin mulkinsa.
Dodonniya hujranul-majnun tana iya tarwatsa runudunar mayaka ita kadai komai yawansu, sai dai su tsere su gudu su barta
.
A halin yanzu dodonniya hujranul-majnun tana da shekaru dari da talatin da uku a duniya.
.
Yake wannan tsohuwa isan har zaki iya siyar da rayuwarki kije har can dajin inda kogon darul-yamzin yake a karshen birnin sin to sai kiyi shiri ki zo nan akwai fataken da zan hada ki dasu su kai ki har birnin sin daga can kuma akwai aljanu wadanda za'a hada dasu su kai ki har bakin kogon darul-yamzin
.
Ammafa ki sani cewar wannan tafiya zata daukeki a kallah shekara shida, kafin ki isa birnin sin kuma zaku ketare ta cikin mugayen dazuzzuka masu dauke da mugayen aljannu, dodonni da mugayen dabbobin daji wadanda zasu iya zama sanadin ajalinku , sai mai cikakken rabo da matukar sa'ane zai iya kaiwa har can a raye kuma cikin koashin lafiya
.
Toh ana zan dakata sai kuma gobe in Allah ya kaimu da rai da lafiya
Daga shuraih Usman
Inkiya 99%
Sai kunjini da part BRANA DA WATA
Littafi na daya 1
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
Part B

Shuraih 99% nake cewa daku Lokcin da boka sharanu yazo nan a zancensa sai tsohuwa shafhila tayi doguwar ajiyar zuciya , sannan ta dubeshi a cikin nutsuwa tace " yakai wannan boka mai yawan daraja ka dubeni ka gani , nifa na tsufa banida wani buri da yai mini saura a wannan duniya face ganin cewar bayana tayi kyau. Ina mai tabbatar maka cewa raina da duk abinda na mallaka ba'a bakin komai suke ba, muddin wadannan yayan nawa zau hada kansu su zauna lafiya a matsayin yan uwan juna na jini ba abokan gaba ba .
.
Yanzu zan koma gida naje na sayar da duk abunda na mallaka domin nayi guzurin wannan tafiya .
.
Abinda na ke so naji daga gareka kawai shine yaushene abokan tafiyar tawa zasu hallara anan mu gamu mu dunguma gaba daya mu tafi birnin sin(abokan tafiyarmu zakice don kuwa har dani acikin wanga tafiya ehm shuraih 99%)
.
Yayinda tsohuwa shafhila ta zo nan a zancenta sao boka sharanu ya kura mata idanu cikin natsuwa da mamaki, sannan yace " na rantse da darajar iyayena da kakannina da kuma darajar tsafina ke ce mutum ta farko data taba cin alwashin zuwa kogon darul yamzin ba tare data girgiza ba, hakika yake wannan tsohuwa shafhila , ina ji ajikina cewa zaki samu nasarar zuwa wannan kogon koda kuwa wannan bukata taki zata zamo ajali a gareki.
.
Saboda haka maza ki gaggauta kammala shirin tafiya nan da kwanaki uku"
.
Lokacin da boka shuranu ya zo nan azancensa , sai ya taba hannayensa a take ya bace a gurin , Tsohuwa shafhila ta daina ganinsa.
.
Kar dai ku shagala kuna tare da Shuraih 99% ne
.
Yayin da tsohuwa shafhila ta samu kwanaki uku. Daidai lokacin data karasa duk wani shiri nata tsaf .
.
Sai shafhila ta gabata a gaban boka sharanu zuciyarta ta kekashe a yanzu bata da wani buri a rayuwarta face taga yayanta huazainu da zuhaisa sun hada kansu wuri daya sun daina tsananin gaba da kiyayya da junansu .
.
Lokacin da boka sharanu ya dube ta sai ya tuntsire da dariya kamar bazai daina ba. Al'amarin daya dada karfafawa shafhila guiwar zage damtse kenan akan wannan tafiya kuma a
.
Lokacin ne fataken da zau tafi tare suka karaso. Daga cikinsu akwai manyan attajirai da jarumai masu tsananin kafiya da dakakkiyar zuciya. Yawan fataken duk su dari uku ne.
.
Boka sharanu ya dubi tsohuwa shafhila sannan ya mika mata fatar barewa yace da ita "ki rike wannan a duk lokacin da kike bukatar sanin wani abu a yayin wannan tafiya taku ki shimfida wannan fatar barewan sannan ki kirayi sunana sau uku fuskata zata bayyana a kai ki fada mini matsalarki"
.
Sa'adda boka sharanu yazo nan a zancesa sai tsohuwa shafhila tayi godiya a gareshi , sannan ta shige cikin a yarin fataken nan ba tare da bata lokaci ba suka kama tafiya cikin azama a wannan gagarumar tafiya tasu mai cike da hadarurruka.
.
Kwanci tashi har suka shafe kwanaki goma suna tafiya ba tare da sun sami wata matsala ba.
.
Dukkana fataken nan sun cika da tsananin mamaki akan tsohuwa shafhila domin tafi kowa doki da tsananin kuzari a wannan tafiya, sai ya zamana a yanzu tsohuwa shafhila ce ke jagorancin tafiyar duk da cewa akwai manyan sadaukai da jarumai a ciki.
.
Lokacin da suka sake shafe kwanaki uku a wannan lokacin sun zo wani daji mai tsananin duhuwa da dogayen itatuwa masu tsayin gaske . Daga cikin ayarin fataken akwai wani sadaiki mai suna sabitul-agadawur ibni ihwas.
.
Ya dubi tsohuwa shafhiila yace da ita .
"Hakika yake wannan tsohuwa ki sani cewa a yanzu munzo dajin mutane ma'abota cin naman mutane.
.
Ki sani a wannan daji duk girmansa babu ko dabba daya dake rayuwa a cikinsa.
Saboda tsananin shawagi irin na wadannan mutane shi yasa ko tsuntsaye basu kusanto wannan daji .
.
A tarihi ba'a taba samun wani ayarin fataken da suka taba ratsa wannan daji suka fita lafiya ba , face wasu da yawa daga cikinsu sun halaka
.
Sannan suna da yawa ,kuma suna da tsananin kafiya da naci, ance saboda maitarsu idan suka asa mutanen da zasu halaka su cinye, sai babbansu yasa ayi kuri'a duk wanda tsautsayi ya afkama to a wannnan ana sune kalacinsu.
.
koda sadauki sabitul-agadawur ya zo nan azancensa , sai ya dubi sauran abokan tafiyarsa ya kara da cewa "saboda haka ya zama wajibi mu yi taka tsantsan wasun mu su rika lua da bayanmu wasu kuma su rinka lura da gefen dama da gefen hauninmu"
.
Daga nan babu wanda ya kaa cewa komai suka ci gaba da ratsa dogayen itatuwan dake a wannan daji
.
Anan zan dakata , Kar dai ku manta kuna tare da
Shuraih Usman
Inkiya 99%RANA DA WATA
Littafi na daya 1
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
PART:- C

*********
Al'amarin huzainu da zuhaisa kuwa arana da suka fahimci mahaifiyarsu bata na duk kuwa da cewa basu san inda ta tafi ba ha tsawon wata guda cur , sai zuhaisa ta hada kayanta tsaf tayi shigar kayan yaki, tayi tsalle ta dare akan ingarman dokinta a dai-dai wannan lokacin huzainu ya karaso a gurin
.
Zuhaisa ta dubeshi da tsana cikin tsananin kiyayya, sannan ta zare takobi tareda nuna shi da tsinin takobin tace "na fahimci mahaifiyamu tayi wata tafiya daba dta son mu san inda ta tafi, kama yadda kasani a duk fadin duniya babu wani mahaluki dana tsana da tsananin kiyayya sama da kai.
.
Kamar yadda na daukarwa kaina alkawarin da karfin damtsena sai na sanya takobi na datse jijiyar wuyanka, da iyakance numfashinka [ its shuraih 99%] a doron kasa .
.
Hakika bani da wani buri daya wuce na ga na shafe babin rayuwarka. Don haka na yanke shawarar barin mahaifata a yanzu , zanje na dada yin shiri da mummunan tanadi a akanka
.
Inasi ka sani daga ranar da muka sake haduwa da kai ,to ka sani a wannan ranar ne mala'ikan mutuwa zai gabata zuwa gareka, na rantse da iyayena ba zaka kubucewa kaifin takobina ba face na halaka ka"
.
Koda huzainu yaji wannan batu sai ya tuntsire da dariya, ya dade yana yi tamkar bazai daina ba, al'amarin daya harzuka zuhaisa kenan ranta ya baci jijiyoyin jikinta suka motsa sai kawai ta diro daga kan dokinta ta nufi huzainu da bakar zuciya tana gurnani kai kace zaki ne yayin da zaluncinsa ya motsa masa a lokacin daya ga wata karamar dabba
.[shuraih Usman nake inkiya 99]
Zuhaisa tana kusanto huzainu sai ta kawo masa wani gawurtaccen sara a saitin dokin wuyansa da niyyar ta sare masa kai cikin tsananin zafin nama, kwarewa da jarumta huzainu ya goce takobin ta wuce ta saman kansa ta kara kawo masa wani mummunan sara a anan ma ya kauce
.
Da huzainu yaga da gaske fa zuhaima take sai shima ya zare nashi takobin nan ne fa suka fara wani azababben yaki, suka kasance cikin kai ma juna sara da suka suna masu zafin nama, juria da jarumta
.
Sai da suka shafe sa'a uku babu wanda ya samu nasarar yiwa daya koda sara daya ne har sai da takubbansu suka dakushe saboda tsananin kai sara ga junansu
.
Sannan suka zubar da makaman nasu suka kacame da kokawa da naushe-naushe.
.
Babu jimawa kowannensu ya hada gumi woho ho mai karfi sai Allah ya isa nan fa tsagwaron karfin damtse ya soma amfani sai gashi su duka biyun kwanjin jikinsu ya dada kumbura , jijiyoyin suka tashi sukayi burdinburdum.
.
Can gabannin faduwar rana kowannensu kamar an yi masa umarni sai suka turje suna masu kallon juna kamar zakaru [shuraih Usman nake inkiya 99]
.
Zuhaisa ta nuna huzainu da dan yatsa ta ce da shi " kamar yadda na fada da farko ka saurari haduwarmu anan gaba kadan. Ka sanni bana afuwa , kuma bana mance gaba komai kankantarta"
.
Lokacin data zo nan a zancenta sai tayi tsalle ta dare akan dokinta taci gana da tafiya . Huzainu yai tsaye yana kallonta kawai ba tare da yace da ita ci kanki ba.
.
A haka har ta bace masa ya daina ganinta
.
Da farko Zuhaisa tayi niyyar shiga duniya domin ta dada samun horo da jarumtaka fiye da huzainu yadda da zarar ta sake haduwa da shi tayi masa kwab daya ta gama da shi
.
Sai kuma ta sauya ra'ayinta akan ta fara neman ilimin bokanci wanda tana ganin ta wannan hanyar ne yafi sauki, kafin ta hallaka shi ta kashe shi.
.
Sannu a hankali har zuwa zuhaisa ta bar nahiyar kasarsu ta danna kai cikin daji
.
Lokacin da zuhaisa ta shafe wata daya tana tafiya ba tare da ta hadu da wani abu na cutarwa ba , sai ta zo inda hanya ta kasu gida uku nan take sai ta karkata linzamin dokinta ta dauki hanyar da ta nufi arewa.
.[shuraih Usman nake inkiya 99]
Bata dade tana tafiyaba sai kuwa taci karo da wadansu mahaya dawai har su hudu dauke da makamansu
.
Daya daga cikinsu wanda yafi sauran zafin zuciya da karfin hali ya dakawa zuhaisa tsawa yana mai cewa da ita "yake wannan kyakkyawar yarinya ma'abociyar kyawun fuska, maza ko gaggauta miko kanki zuwa garemu da dukkanin abinda kike dauke da shi, ko kuwa fushinmu ya sauka a kanki ba zamu lura tsananin kyawun fuska da cikar zatinki ba"
.......Wai lallai wannan ya tsokano tsuliyar dodo
Mai shirin kuka an jefeshi da kashin a waki
.
Anan zan tsaya sai Gobe
Kar ku manta dai kuna tare ne da Shuraih Usman
Inkiya 99%RANA DA WATA
Littafi na daya 1
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
Part D

.
Sa'adda wannan sadauki yazo na a zancensa sai zuhaisa tace da shin cikin zafin zuciya " kada kayi zato ko tsammanin kasancewata mace kuma ni kadai ki hudun nan zaku iya razana ni.
.
Yakai wannan karamin sadauki ma'abocin shisshigi da kokarin haikewa ajalinsa, kayi sani cewa a yadda kuke din nan izan za'a ninka ku sau goma ba zaku sa naji dar a zuciyata ba.
.
Ina mai ja maka kunne akan wadannan munanan kalamai daka ambata zuwa gareni.
.
Maza ka tuba ko ka samawa kanka afuwa da sassauci akan fushin da zai afko zuwa gare ka kai da mutanenka"
.
Yayin da wannan sadauki yaji wannan batu, sai ya dada harzuka fiye da farko.
.ni dinne dai Shuraih 99%
Nan take ya dakawa daya daga cikin yaransa tsawa akan ya saro masa kan zuhaisa .
.
Koda ganin haka sai ran zuhaisa ya baci ita a ganinta ya za'ayi kamarta za'a turowa wani karamin sadauki tare da umartarsa daya saro kanta
.
Ai kuwa sai ta zare takobi tun ma kafin sadaukin ya karaso zuwa gareta ta tareshi a kai masa wani gawurtaccen sara ta halaka shi, sannan karkata linzamin dokinta ta afkawa ragowar da sara da suka cikin tsananin bacin rai da jarumta ,
.
Anan take wani sabon azababben yaki ya kacame a tsakanin su cikin kankanin lokaci zuhaisa ta zabtarewa biyu hannayensu wadanda ke dauke da makamansu. Sannan ta juya ga babbansu tana kai masa sara ba kakkautawa.
.
Acikin dakika sittin ta galabaitar da shi, kawai ya zubar da makamansa ya mika wuya ga zuhaisa
.
Ita kuwa ganin haka sai tayi kururuwa ta daki kirji da hannun hagu sannan tasa takobi ta sare masa kunnen daya.
.
Take ya fado daga kan dokinsa ,jini yai tsartuwa a inda ta cire masa kunnen. Zuhaisa ta diro daga kan dokinta ta cakume shi ta kuma tuntsirewa da dariya a karo nabiyu sannan da shi "wannan zamo misali a gareka da sauran masu hali irin naka . Maza ka sanar dani izan nabar nan ina zan dosa?"
.ni dinne dai Shuraih 99%
Koda sadaukinnan yaji wannan tambaya ta zuhaisa saiya amsa mata da cewa
"Yake wannan matashiyar basadaukiya kiyi sani cewa zai fi miki abu mai sauki da ki koma inda ki ka fito domin kuwa hadarin da zaki tarar akan hanyar nan yafi gaban tunaninki.
.
Ko mu din nan da kike gani nan ,idan muka yi fashi bama kusantar hanyar nan.
.
Kiyi sani cewa akwai wani hatsabibin boka kuma takadari mai suna AHAKAMUL-BAINUN yana da tsananin karfin tsafi, yana da hatsarin gaske kasnacewar manyan jarumai da hatsabiban bokaye komai yawansu sai ya gagare su ya addabesu a karshe kuma ya hallaka su gaba daya .
Yake wannan basadaukiya ina mai shawartarki da ki juya da baya , ki canja hanya domin yafi maki sauki "
.
Koda zuhaisa taji wannan bayani na wannnan dan fashi sai tace da shi " kada ka damu, tunda ka sanar dani komai to lallai sai na shiga dajin nan ,koda kuwa zamuyi arangama da fito-na-fito dashi wannan hatsabibin bokan nan"
.ni dinne dai Shuraih 99%
Batare da bata wani dogon lokaci ba ,zuhaisa ta dare akan dokinta ta zabureshi sannan ta kutsa kai a cikin daji ba tare da fargaba ko shayin komai ba .
.
Ai kuwa zuhaisa ba tayi nisa ba sai hango wani katon dutse agabanta , ajikin dutsen akwai wani kogo mai zurfi wannan ya tabbatar mata da cewa wannan boka yana a cikin wannan kogon dutsen ne .
.
Zuhaisa ta sauka daga kan dokinta kai tsaye ta danna kana cikin kogon dutse ba tare da fargabar komai ba .
.
Kogon dutse ne mai tsananin girma da fadin gaske babu komai a ciki face kasusuwa na sassan jikin mutane sai kuma kayayyakin irin na bokanci a ko'ina , yayinda zuhaisa ta gama nazari a cikin kogon dutsen sai ta fara tafiya acikinsa tana lura tare da sauraren wani motsi dake dada karuwa sannu sannu
.
Daga bisani ma sai kofar shigowa kogon ta shafe kuma asannan ne wani bakin duhu ya mamaye kogon .bayan kaman dakika sittin kuwa sai aka fara girgiiza kogon, sautin kukan yara kana na. Yana amsa kuwa a cikin kogon.
.
Zuhaisa tayi alkafura tana juyi a sama ta dira a wani guri can daban, sakamakon jin sautin tahowar wani a gareta . Wato wani katon dutse ne ya mirgino yana niyyar taushe ta.
.
koda zuhaisa taga matsawar tayi wasa zata iya rasa rayuwarta a cikin wannan kogon dutse, sai ta bude baki ta fara magana cikin madaukakyira murya ,tace" hakika wannan al'amari naka yakai wannan ma'aboci bokanci, yana nuni da cewa ka tsorata da al'amarina , saboda ka ki bayyanarr da kanka gareni , ka labe kana kokarin cutar da ni. Ka sani baya daga dabi'un manyan mutane madaukaka suyi yaudara ga dukkan Al'amurransu"
.
Koda jin wannan batu sai ya harzuka boka ahakamul-bainun, hankalinsa ya dugunzuma ,kasnacewar tun da yake zaune a cikin wannan daji babu wani mutum da ya taba kwatanta fada masa wata magana ,mai daci da muni irin wannan saboda sanin matsayinsa da daukakarsa a duniyar tsafi.
.ni dinne dai Shuraih 99%
Nan take sai yayi kururuwa da karfin muryarsa , gaba daya kogon ya amsa kuwwarsa,sai kawai ya bayyanna gareta .kuma a wannan lokacin ne duhun ya yaye, haske ya maye gurbinsa.
Koda boka ahakamul-bainun ya dubi zuhaisa cikin tsananin bacin rai ya daka mata tsawa
.
"Hakika
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment