Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

RIJIYA GABA DUBU
Littafi Na Hudu (4)
Part A
Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke Magana

Kyan Alkawari cikawa Saboda haka zamu cigabaa kamar yadda mukace

Marubucin yaci gaba da cewa....

Su kuwa waɗanda suka zabi jarumi zambaru a matsayin jaruminsu na caca sai suka fara tsalle gami da murna, domin sun san cewa kakarsu ta yanke saka dan sun gama zamowa manyan attajirai. Yayinda wadanda suka zabi jarumi Imhal kuwa a matsayin jarumin gasarsu sai suka fara kuka sannan suka kamu da tsananin bakin ciki saboda sun san cewa karayar arziki ta zo masu.

Lokacin da Zambaru ya tunkaro Imhal rike da wannan lafceciyar takobin tasa, kuma ga Imhal in kwance a kasa ya kasa miƙewa saboda karyewar da kafarsa ta yi, sai hankalin Gimbiya Shumaira ya dugunzuma ta ji kamar ta dafe kanta ta kwala uban ihu, kafin ta ankara tuni hawaye sun fara sartu a bisa kumatunta, tana daga idanu da sarki Taryan sau taga yana yi mata murmushi sannan yayi mata rada da cewa ki kwantar da hankalinki yake yata ai kada mage ba yankawa bane, wannan yaro Imhal dan baiwa ne baza a ci shi da yaƙi faraddaya ba sai rai ya baci.
A bangaren Sarki Gurzalu da Gimbiya Lumairat kuwa sun tabbatar da cewa karshen Imhal yazo domin dai gani kuru-kuru a zahiri an fi karfinsa, sannan fadan ya nuna cewa bashi da sauran kataɓus, haka ma sauran yan kallo da dukkanin attajirai da suka sanya kudin cacarsu akanshi jikinsu yayi sanyi, Wannan karon kuɗin da suka sanya a kanshi ya ninka na farko, saboda ganin yadda ya lashe gasarsa akan sadauki Darwaz jarumin da babu kamarsa a duk faɗin birnin Misra. Zambaru na karasowa daf da Imhal ai kawai ya kawo masa wawan sara a wuya da nufin ya tsinke masa kai, cikin bakin zafin nama Imhal ya kauce wa saran, saboda karfin saran da kuma nauyinta sai da takobin tasa ta nutse a cikin kasa kamar haka akayi aka sakata, kafin Zambaru ya zaro takobin tasa tuni Imhal yasa kafarsa mai lafiyar ya doki tsakiyar fuskarsa, saboda tsananin karfin dukan sai da Zambaru yayi taga-taga kamar zai fadi amman ya turje, duk kuwa da tsananin girmansa gami da karfinsa, take hancinsa gami da bakinsa suka fashe suka kama yoyon jini.
Al'amarin da ya baiwa yan kallo mamaki kenan, sai kawai akaga Imhal ya yunkura ya mike tsaye yana dingishi sakamakon karayar dake a kafarsa, daga cikin an kallo ne aka cillo wa jarumi Imhal wani dogon icce, cikin sauri Imhal ya cafe shi ba tare da ya ga wanda ya jefo masa ba. Nan take ya karya icce gida hudu ya daure karyayyar kafar ta shi. A daidai wannan lokaci ne kuma Zambaru ya miƙe daga durkuson da yayi yana mai shafa fuskarsa, koda yaga ya shafo jini a hannunsa sai ya fusata ainun ya takarkare ya kwarara uban ihu irin wanda yayi a karon farko, su kuwa jama'ar dake cikin wannan fili sai suka kaure da shewa gami da yiwa jarumi Imhal tafi bisa ganin irin jarumtakar da ya yi da kuma juriya, ya kasance ga shi dai ya karye amman ya ɗora kansa kuma ya ci gaba da gumurzu. Duk da cewar shi kansa Jarumi Imhal ya karaya amman sai da yaji dadi kwarin gwiwa da jama'a suke bashi, da kuma yadda yan kallo keta masa jinjina.
Bayan Zambaru ya gama miƙewa tsaye gami da yin wannan kururuwar mai firgita kowa sai kawai ya daga takobins sama ya riketa da hannu biyu ya tsaya cak! A inda yake ya kura wa Imhal idanu.
Koda ganin haka sai shima Imhal ya daga tasa takobin sama ya riketa da hannu biyu kamar yadda Zambaru ya yi suka ci gaba da kallon kallo, a wannan lokaci makada suka fara kada gangunansu filin ya sake hargitsewa da hayaninyar kida gami da surutan jama'a, tsawon kusan dakika dari uku da ashirin maroka da makada sunata zuga wadannan Jaruman gasar, daga can sai Zambaru ya rugo da mugun gudu, cikin tsananin mugun nufi izuwa kan Imhal, yana gudu kasa na rawa, nan take filin wajen ya hau girgiza shi kuwa jarumi Imhal ko motsawa bai yi ba daga inda yake ba, kawai sai ya cigaba da kurawa Zambaru idanu yana jiran isowarsa tunda shi bashi da ikon yin gudun amman ya tsaida hankalinsa sosai akan Zambaru yana jiran yaga ta inda zai kawo masa hari, kowa a wannan filin gasa hankalinsa a tashe yake domin babu wanda yake da tabbacin cewa ga wanda zai samu nasara.
Koda Zambaru ya iso daf da Imhal sai suka kacame da sabon azababben fada tamkar yanzu ma suka fara, ya zamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta, amman fa karfin saran Zambaru ya ninka na jarumi Imhal a jahiri kowa ya tantance.
Duk sa'ad da ya kawo wa Imhal sara da wannan labceciyar takobi tasa koda Imhal ya kare saran nasa sai dai aga yana durkushewa kasa saboda nauyin saran. Amman saboda naci gami da kwarewa haka yake dagowa da sauri ya ci gaba da artabu yana mai mayar da martani.
Sai da suka shafe kusan rabin sa'a a haka dayansu bai samu nasarar koda kwarzanar jikin ɗaya ba.
Ko da ganin irin tsantsar jarumtakar da Imhal ke nunawa gami da juriya da naci har sai da "yan adawarsa ma suka ji ya burgesu ba su san sa'adda suka rinka yi amsa tafi gami da jinjina ba. Kai hatta attajiran da suka zuba dubunnan kudadensu a gasar akan Zambaru sai da suka koma goyon bayan Imhal basu sani ba, suna masu kiran sunansa.
Lokacin da Sadauki Zambaru yaga gaba daya yan kallo sun daina yi masa jinjina, zuga gami da tafi kowa ya koma kaunar Imhal sai ransa ya baci ainun zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone, cikin shammata ya gabza wa Imhal wani wawan naushi a fuska, saboda karfin naushin sai da imhal yayi katantanwa sau uku a wuri daya a lokacin ne kuma hakorinsa na sama yayi fitar burgu gami da gudan jini, sai kawai aka ga ya sulale kasa a matukar galabaice cikin mugun yanayi mai kama da birkicewar hankali.
Shi kuwa sadauki Zambaru sai ya kurma uban ihu na murnar samun nasara, sannan yaci gaba da dukan Imhal hannu da kafa, cikin kankanin lokaci kuwa ya galabaitar da shi ainun fuskar Imhal ta kumbura tayi suntum har ya zama cewa baya gani sosai da idanunsa sai dishi-dishi kuma tun yana yunkurin mikewa tsaye har sai da ya kasa ya baje kasa wanwar yana mai fidda numfashi sama-sama.
Tuni a wannan lokacin Gimbiya Shumaira ta sunkuyar da kanta kasa tana sharbar kuka domin ta fidda ran cewa Imhal zai iya tsira da rayuwarsa, kai hatta ita knta Gimbiya Lamirat wacce ta tsani Jarumi Imhal kamar yadda ta tsani mutuwarta sai da taji ta kamu da matukar tausayinsa.
Lokacin da Sadauki Zambaru yaga ya samu wannan gagarumar nasara ne sai ya ci gaba da kurma uban ihu yana yi wa kansa kirari, kawai sai yazo ya durkusa a gaban jarumi Imhal ya kamo gashin kansa yana mai dago da kansa sama da nufin ya dora kaifin takobinsa a bisa wuyansa da nufin yayi masa yankar rago a gaba kowa, tabbas kowa dake wannan fili ya fahimci manufar zambaru, kuma bakin ciki ya turnuke jama'a bisa ganin cewa za a yiwa wannan gawurtaccen jarumi kisan wulakanci a banza.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai akaga jarumi Imhal ya gabza wa Zambaru naushi a bisa makoshinsa, saboda karfin naushin sai da Zambaru ya yi sama sannan ya fado kasa a matular galabaice yana kakarin mutuwa.
Kafin ya mike zaune tuni Imhal ya rarumi takobinsa ya daka tsale daga inda yake zaune yayi sama kamar tsuntsu, bai dira a ko ina ba sai a kan ruwan cikin zambaru, kawai sai ya soka wa Zambaru takobi a cikin bakinsa take takobin ta faso keyarsa ta lume a cikin kasa, jini ya dinga malala ta cikin takobin tamkar idaniyar ruwace ta balle.
Imhal ya mike tsaye da kyar daga kan gawar Zambaru yana layi sai kawai akaga ya sulale kasa sumamme, nan fa filin gasar ya kaure da shewa, masu murna da tsalle na yi, masu rawa na yi. A guje likitoci suka suka karasa kan Jarumi Imhal, dakaru na kewaye da su dan tabbatar da tsaro, nan fa suka shiga yi masa magani domin ceto rayuwarsa.
Gawar sadauki Zambaru kuwa sai da karti majiya karfi mutum talatin suka taru sannan suka iya dauketa.
Cikin tsananin tashin hankali Sarki Gurzalu ya shiga cikin masaukinsa ya kama zarya kuma yana kai kawo zuciyarsa cikin kunci kamar ya dafe kai ya fashe da kuka bisa ganin yadda al'amura suka chakude masa, abu na farko da yafi dagula masa lissafi shine rashin sanin barawon da ya sace masa kambun sihirinsa, abu na biyu kuma shine ganin yadda lokacin karawarsu da Jarumi Imhal ya ke kara karatowa, tunda saura wasa uku kacal su hadu a filin gasar, ga shi kuma tsananin sa'ar Imhal din daya samu akan sadauki Imhal ta bashi mamaki, domin gaba daya filin babu wanda ya taba tunanin cewa Imhal zai tsira da rayuwarsa har ya lashe wannan gasa, amman sai ga shi yayi wa zambaru kisan farat daya.
Sarki Gurzalu na cikin wannan hali ne na kaikawo a cikin kuryar daki, sai ga Gimbiya Lamirat ta shigo cikin dakin, koda ta shigo taga sarki cikin wannan hali sai hankalinta ya tashi, ta karaso gareshi ta kama hannayensa ta rike ta jashi izuwa kan wata doguwar kujera suka zauna tare sannan ta dubeshi ta ce "Ya kai Abbana na san abinda ke damunka, amman ina so ka kwantar da hankalinka, ka yi sani cewa jarumi Imhal ba zai tsallake karo na uku a wannan gasa ba."
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Sarki Gurzalu ya dubeta ya ce "Mene ne hujjarki na fadar hakan, shin kin san jarumin da zasu fafata da shi ne, kuma kina da tabbacin cewa shi jarumin sai ya samu nasara akan Imhal din?"
Koda jin wannan tambaya sai Gimbiya Lamirat ta yi murmishi ta ce Kwarai kuwa nasan jarumin, kuma ina da yakinin cewa a halin yanzu ko kai bana zaton zaka iya samun nasara akan sa."
Koda jin haka sai sarki Gurzalu ya cika da tsananin mamaki, sannan kuma ya bushe da dariya ya ce Haba yake yata, hakika na fuskanci cewa har yanzu kina wasa da al'amarina, bakisan cewa na wuce duk yadda kike zato ba, ai duk da cewa bana tare da gurun tsafina babu wani jarumi da zai iya rabani da wannan kambun na jarumta a duk fadin wannan duniya, sai dai ko muyi ragas ni da shi. Yau dai saura kwana uku rak bokayen garin nan su gano mani barawon kambuna, kuma ban san ranar da zanyi karo da Jarumi Imhal ba, tunda dai ga shi ya sake samun karaya a kafarsa, kuma dole ne yayi jinya ta yan kwanaki.
Koda jin wannan batu sai Lamirat ta dan yi guntun murmushi ta ce "Ai al'amarin Jarumi Imhal yana da matukar shammata gami da ban tsoro, domin wannan karaya tasa zata iya warkewa a kowanne lokaci, ka duba fa yadda wannan lafcecen rauni na kirjinsa ya warke a cikin kwanaki uku kacal, alhali muna zaton cewa sai ya shafe sama da kwana bakwai yana jinya."
Sa'adda da Gimbiya Lamirat ta zo nan a zancenta sai Sarki yayi ajiyar zuciya gami da dan guntun murmushi Ya ce babu komai lokaci zai warware mana komai.
Yana gama fadin haka sai kawai ya shige cikin kewaye ya bar Gimbiya Lamirat zaune tana mamaki da tunanin abinda mahaifinta ya taka da har yake irin wannan lafazi.
Acan wani ɓangare na gidan sarauttar kuwa Gimbiya Shumaira ce tare da Gimbiya Muzaira zaune a cikin lambun sarki Taryan suna cin yayan itatuwa suna firarsu cike da nishadi amman duk hadiman gidan dake kai kawo basa iya jin abinda suke tattaunawa a tsakaninsu albarkacin wannan gurun sihirin dake daure a kugun Muzaira wato gurun Sarki Gurzalu, a cikin hirar tasu ce Muzaira ta dubi Shumaira cikin alamun damuwa ta ce Ya ke kawata wai shin mene ne yake damun kine, alhalin gashi danki jarumi Imhal yana samun nasara ko yaushe a cikn wannan gasa ta kambun jarumtaka, kuma ga shi kin samu nasarar raba Sarki Gurzalu da babban abin dogoronsa wato kambun sihirin da yake amfani da shi wajen cika dukkanin burikan rayuwarsa.
Lokacin da Muzaira ta ji wannan tambaya sai ta kawo gwauron numfashi ta ajiye fuskarta tana mai nuna damuwa da takaici ta ce Ya ke wannan yar sarki ki yi sani cewa har yanzu bani da kwanciyar hankali, duk da cewar na raba sarki Gurzalu da wannan gurun nasa na tsafi saboda shi mutum ne mai basira da hangen nesa, duk yadda zai yi yaga bayan makiyansa sai yayi, inba don bashi da ikon komawa birninsa ba a cikin wannan lokaci da tuni ya gano duk abinda nake ciki.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Shumaira ta dubi Muzaira ta ce Ya za'a yi ya gano abinda kika shirya alhalin kina tare da abin dogaronnasa.
Muzairat ta ce ai yana shiga cikin dakin halwar tsafin nasa ba zai yi sama da sa'a daya ba zai gano komai, yanzu babban abinda ke tayar mani da hankali shine ban dan irin tuggun da sarki Gurzalu zai shirya ba a ranar da zai fafata da Imhal ba, nasan dole ne ya dauki mataki gami da mugun shiri akan hakan tunda baya tare da kambun sihirinsa.
Kodajin wannan batu sai Muzira ta ce amman kin dada tayar mana da hankali saboda na fiskanci cewar rayuwar Imhal na cikin mugun hadari, ni ina ganin cewa dole ne ki taima wa Imhal wajen tsare lafiyarsa da rayuwarsa a ko yaushe kuma a duk inda yake.
Koda jin wannan batu sai Muzaira ta yi murmushi ta ce ai mahaifinki yana matukar kokari akan haka, ni nawa babban taimako sai a filin gasa, ni yanzu matsalata guda daya ce jal kuma ba komai bane face batun tsoho Imzanu wanda na baro a cikin gidana shi kadai, sa'adda da na barshi yana matsananciyar rashin lafiya duk da cewa nayi masa magani kafin na taho nan, kuma babu abinda zai nema ya rasa a gidan koda kuwa zai shafe shekara a gidan, hakika zaman kadaicinsa na damuna a gidan.
Koda Shumairat ta ji wannan batu sai ta yi ajiyar zuciya cikin alamun karayar zuciya ta dubi Muzaira ta ce Kwantar da hankalinki yake Ummul Imhal, ni ina ji a jikina cewa har a gama wannan gasa zaki koma gida ki iske wannan tsoho wanda ya raini Imhal, alfarma daya nake nema a wajenki ina son a daren yau ki shigar da ni har dakin da aka kulle imhal domin in ban ganshi a halin da ake ciki ba nasan cewa ko barci ba zan iya yi ba.
Kodajin haka dai Muzaira ta yi murmushi ta ce kada ki damu ai wannan mai sauki ne, kuma wannan karon ma sai ya ganki ido da ido kuma kunyi magana domin akwai sakon da nake son na baki ki, ki isar masa, gama fadar hakan keda wuya sai Muzaira ta kwanta, kafin cikar dakika arba'in bacci mai nauyi ya dauketa har ta fara munshari.

Zamu dakata anan saikuma Allah ya kaimu zamu cigaba
AA Misau ke magana
whatsap group

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30QRIJIYA GABA DUBU
Littafi Na Hudu (4)
Part B
Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke Magana

Barkanmu Da wannan lokaci inayima kowa fatan alkhairi

Marubucin yaci gaba da cewa

kafin cikar dakika arba'in bacci mai nauyi ya dauketa har ta fara munshari.

Al'amarin Gimbiya Lamirat kuwa bayan tq rabu da mahaifinta sarki Gurzalu, sai ta tafi izuwa can wani bangare da ban na gidan sarautar sarki Taryan nda aka kewaye wani babban fili wanda aka kawata shi da shimfidu na alfarma gami da ujeru iri iri ga tsuntsaye nan kalakala birjit a cikin keji masu dan karan kyau da ban sha'awa, musamman arki Taryan yasa aka kawata wannan waje domin ya zame masa wajen shan iska, rangadi da kuma debe masa kewa musamman a lokutan da ransa ya baci. Kai tsaye Gimbiya Lamirat ta cike cikin wannan lambu can kurya taje ta zauna a bisa wata karamar kujera ta yi zugum. Nan fa ta fda cikin kogin tunani, babu qbind ya fara fado mata a rai irin abinda mahaifinta ke yi mata, sannan ta tuno da duk irin maganganun da yayi mata qkan irin abinda zai faru idan har Jarumi Imhal ya samu nasara akan sa a wannan gasa da za a yi. Kod tazo nan a tunaninta sai kawai taji ta tsani Jarumi Imhal a cikin zuciyarta fiye da ko yaushe a rayuwarta don haka sai ta ayyana a ranta cewa lallai ta ko wane hali sai ta tabbatar ta samu nasarar hallaka Imhal a wannan gasa da zasu yi kodan ta baiwa mahaifinta mamaki tunda shi bai san cewa ita ce jaruma ta uku ba, wacce zata fafata da imhal akan kambun jarumta ba. Koda Gimbiya Lamirat ta zo nan a tunaninta sai ta mike tsaye zumbut tana mai zare takobinta gami d kaiwa iska sara da suka, wato tana kara bauwa kanta horon yaki. Duk hafimin d yazo figtawa ta wajen da zarar ya hangota sai kawai kaga ya tsya yana kallonta cikin matukar mamaki, domin babu wanda zai taba tunanin cewar akwai wata ya mace irin irin wannan horon yakin a duniya.
Kafin a jima tuni waje ya cika makil da barori, bayi, hadimai da kuma dakarun gidan sarautar sai faman yi mata jinjina gami da tafi suke yi. Sai da Lamirat ta shafe sa'a guda cur tana tsalle tsalle gami da kaiwa iska naushi hannu da kafa da kuma sarq da suka tamkar jikinta bana jini da tsoka bane, sannan ta tsaya cak a lokacin da ta lura cewar ta tara yan kallo masu yawa, cikin sauri ta mayar da takobin tata cikin kubenta, kuma ta ruga izuwa cikin gidan sarautar tabar yan kallo tsaye sunafadar albrkacin bakinsu.
Sai da dare ya raba a wannan lokacin ne aka fara wata irin iska mai sanyin gaske wacce tasa dakarun dake jiran gidan sarautar suka ringa lullube jikinsu da barguna wasu kuma da fatun dabbobin daji, a sannan ne Shumairat da Muzairat suka nufi dakin da aka kulle Jarumi Imhal.
Da isarsu bakin kofar dakin sai suka iske jarumi Imhal kwance a cikin dakin yanata faman sharar bacci, ga kafarsa guda a daure cikin itace wacce ya samu karaya a filin gasar. A wannan lokaci kafar tasa ta dan kumbura sakamakon cewar shine da kansa ya gyara karayar ba likita ba.
Koda ganinsa a cikin wannan hali sai tausayinsa ya turnuke Shumairat da Muzaira har hawaye ya zubo wa Muzaira ya budi baki tace yanzu wannan shine halin da dana yake ciki ammqn ace bazan iya fitar da shi ba? Hakika inba dan ina da buei na daukar fansa akan sarki Gurzalu ba, da yqnzu take zan dauke Imhal na gudu da shi izuwa cqn wani dajinmai nisa inda daga baya sai muyi shirin dawowa domin karbar karagar birninmu tunda dama mune da gadonta tun asali.
Koda tazo nan q zabcenta sai kawai ta dafa karafunan dake jikin kofar dake da Imhal ke ciki da hannunyenta biyu tare da fashewa da matsanancin kuka.
Cikin hanzari Shumaira ta kamota tare da rungumeta a jikinta ta shiga rarrqshinta gami da bata baki har saida ta daina kukan.
A sannan ne ta nutsu ta kalli Shumaira ta ce yqnzu sai ki shiga cikin dakin ki tashe shi daga bacci, kuyi dukkan maganar da zaku yi sannan ki tabbatar kin bayyana masa soyayyarki a gareshi, kuma ki kada ki manta ki sanar da shi sakon nawa ni kuma zan jiraki anan hr sai kin kammala sannqn ki fito mu tafi.
Cikin mamaki Shumaira ta dubi Muzaira ta ce to yanxu ta yaya zan iya shiga cikin wannan daki alhalin kofar tana kulle da makulli.
Muzaira tayi murmushi sannan ta ce Hakika kin manta cewa ina tare da gurun sihirin sarki Gurzalu, ai kawai kiyi dukkqn abinda na umarce ki
Kafin Muzaira ta rufe bakinta tuni Shumaira ta kunnakai ta tsakankanin wadannan karafan, bisa ga mamaki sai kawai gani tayi ta wuce ta tsakaninsu kamar adda haske ke ratsa duhu ta bayyana a gaban jarumi imhal, kawiq sai ta tsugunna daf da shi ta dan daki kafadarshi sau biyu.
Imhal yayi mika domin a zatonsa gari ne ma ya waye ake tashinsa kamar yadda aka saba, koda ya bude idanunsa sai kawai yayi arba da Gimbiya Shumaira duke a gabansa. Sai ya mike tsaye zumbur cikin firgici da dimauta ya ja da baya da sauri yana mai takure jikinsa a jikin bango domin a zatonsa aljana ce ta kawo masa ziyarar bazato, musamman ma daya dubi gabas da yamma, kudu da arewa yaga kofa a rufe take kuma babu bango da aka fasa. Cikin yana yin tsoro Imhal ya dubi Shumaira ya ce da ita Ya ke wannan yar sarki shin ta yaya har kika iya shigowa wannan daki alhalin ga kofa a rufe kuma mene ne dalilin zuwanki wajena, idan kuma ke ljana ce ba mutum ba kika zo da niyyar cutar da ni, to ki sani cewa ba zaki samu nasara akai na ba.
Koda jin wannan bati sai Gimbiya humaira ta bushe da dariya, al'amari daya kara razana Imhal kenan, ya dubi dakarun dake tsaron dakin da yake ciki, yaga ko kadan mahankalinsu baya kansu kuma da alamu basa ganin Shumaira domin sam basa jin dariyarta.
Lokaci
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment