Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

buk'ata saboda haka ni ban yarda da wannan maganar taki ba."

Sai ta kasa ce masa komai domin duk abinda zata fad'a masa ba zai yarda ba, bahaushe ya ce." Mai d'aki shi ya san inda yake masa yoyo, gaskiya ne tunda ta taso babu wani namiji da ya taba cewa yana sonta.

Hannu tasa ta goge hawayen fuskarta, ta kalleshi har yanzu fuskarsa bata sassauta ba."

"Zan tafi Baba." tafad'a tana k'okarin tashi. ya ce."Ki bari sai yamma idan an kammala soya naman ki tafi da naki."

Ya sosa mata in da yake mata 'kai'kayi cikin fargaba ta ce."Baba ina ka samu kudi ka yanka SAH! har da Rago?"

Ya kalleta yana sake tamke fuskarsa." Ke ni kikewa wannan tambayar don ubanki."
Ya fada yana zazzare mata ido!

A sanyaye! ta ce." Kayi hakuri." Hanyar fita ya nuna mata da hannu cikin tsawa! yace." Tashi ki fita ki bani guri."

Da sauri ta tashi ta fita gabanta na wani irin fad'uwa! akwai dalilin da yasa ta tambaye shi saboda sanin halinsa mugun dan rigima ne zai iya zuwa yaci bashin mutane duk domin yazo yayi bajinta da burga! da neman suna a cikin unguwa babban burinsa ace masa ya isa shi mai kudi ne.

Hasashenta ya tabbata domin kuwa bayan fitar ta, ya zurfafa cikin tunanin hanyar da zai bi gurin ganin ya biya mahaucin da ya kar'bi SAH! da Ragon a gurinsa.

Yayi nazari ya hanga ya hango a yanzu dai bashi da dubu dari uku da hamsin din da zai biya mutumin idan ba gidan da yake ciki a zaune zai daga ya siyar ba.

Dama yasa ran samun wasu kud'i ne sai kuma asara ta same shi, domin hak'ansa bai cimma ruwa ba, a gurin sana'ar tasu shine ya tashi fanko fayau!(ziro) hatta da motarsa bata tsira ba sai da aka 'kwamushe haka ya dawo gida a motar haya.

Kwabo yanzu babu a cikin asusunsa sai 'yan canjin dake hannunsa, gabadaya tunaninsa ya ta'allaka gurin ganin hanyar da zai biya mahaucin kud'insa.

Talatu ta shiga d'akin tana gyara d'aurin zanin jikinta da yayi muguwar daud'a sai karni take fuskarta na maiko.

'Kerere ta tsaya a kansa da fadin." Babu icce ya 'kare ga kuma uban 'kashi can da za'a soya yanzu dai abunda ake bukata icce da man gyada."

A sakarce ya kalleta yaji wani mugun takaici ya turnuke shi, ta tsaya masa aka kerere! ba ta san halin da yake ciki ba, girgiza kansa yayi yace." Je ki zan fito yanzu na bada kudin."

Ta juya ta fita bagazan-bagazan!

Ya fito tsakar gidan yana nazarinsu. babu Shahida a cikinsu ta tafi, wato da yace ta tsaya ta tafi da nata rabon shine ta kama hanya ta tafi, shikkenan ai tayi wa kanta, waje ya fita minti biyar ya dawo gidan tare da zaratan samari biyu, a yanzu dai bashi da kudin icce ballantana wani man gyada, saboda haka ya yanke shawarar bada sadakar naman da niyya biyu.

Ganin abinda yake shirin faruwa yasa ta fito afujajan! baki na rawa tace." A'a ya haka kuma?"

Bai saurareta ba ya cigaba da loda zallar tsoka da k'ashi cikin buhu yana fad'in gidajan da za'a kai musu.

Talatu kamar ta dora hannu ka ta kurma ihu! jikinta sai rawa yake tana fadin." Ya haka ina za'a kai kuma?"

Ya ce." Na bayar sadaka dama haka Allah ya ce ayi saboda haka wannan na cikin kaskon ya ishe ku."

Idonta ya ciko da ruwan hawaye ta dinga zabga masa harara! wannan ai wulakanci ne! duka na cikin kaskon bai fi ya cika bokin fenti ba.

Su Hadiza ma jikinsu ne duk ya mutu saboda ganin yankan k'aunar da mahaifin nasu ya yi musu.

Kaf ya kwashe naman ya bayar, ya bar musu kadan hatta da kawunan dabbobin da gandar dake shanye a buhu bai bari ba sai da ya bayar, dalili baya bukatar ta sake zuwar masa da wata bu'kata ta siyan icce ko man gyad'a da makamantansu.
[4/19, 10:26 AM] Bintu: Talatu tare da su Hadiza kamar su mutu saboda takaicin da Hujaj ya k'unsha musu, babu shakka ya cutar da su, domin naman da ya bar musu bai taka kara ya karya ba, da 'kyar zai kai sati d'aya, gashi sun ci burin ajiyar nama saboda bayan sallah idan kwad'ayi ya tashi su fito dashi su gyara abinsu, Talatu dai kasa hakuri tayi ta shige d'aki tana matsar hawayen ba'kin ciki, tunanin hanyar da zata k'untata masa take.

'Bangaran sa kuwa har ya manta abunda ya aikata domin wanka ya yi ya shirya cikin sabon yadi mai tsada anyi aikin kufta a wuyan rigar da hannuwa, ya dora hula zannar bukar a kansa ya fito yana kamshin tsadaddan turaransa.

Yaran ya samu sunyi jugum-jugum! kamar anyi mutuwa.

Ya kallesu na minti biyu kafin ya girgiza kansa ya kama hanyar fita ba tare da yayi musu magana ba, Jamila ce kawai ta iya yi masa a dawo lafiya Hadiza da Walida kuwa harara suka bi shi da ita yana fita Hadiza taja tsaki ta mike tsaye tana 'kunk'uni! d'aki ta shiga, Jamila ta bita da kallon mamaki! ita kuwa Amina bakin kasko ta nufa ta juya naman dake kan wuta kafin ta tsamo 'katuwar tsoka tasa a bakinta tana taunawa tare da hure zafin dake barazanar 'kona mata dadashi.

***
Jiki a sabule ta koma gida. Abin duniya ya yi mata katutu! matsalar Baban-Baba ita tafi damunta, sai kuma matsalar mahaifinta, sharad'in daya gindaya mata na fito da mijin aure cikin wata uku yayi mata tsauri! ba ta da madogara sai Allah domin kuwa babu wani namiji da ya nuna yana sonta ballanatana har su kai ga maganar aure.



Sallah ta wuce da sati biyu da yawa daga cikin wad'anda su ka yi layya sun cinye naman su, har sun fara sayan na miya, ita kanta Baba Asabe da ta yanka RAGO a yanzu bata da nama sai diddiga da kakide domin ba tayi son zuciya ba tayi sadaka da naman kamar yanda Ubangiji ya umarta Saliha ma tuntuni ta cinye nata, Shahida ce kawai mai nama a gidan ta kime shi a cikin kakide ta boye a karkashin gado ita bata ci ba, ba kuma ta bawa wani yaci ba yana ajiye.

Tana zaune a tsakar rumfa tana taimakawa Baban da d'aurin gishiri taji motsi a cikin uwar daki.

Haka kawai jikinta ya bata wani abu, da sauri ta ajiye gishirin dake hannunta ta shiga dakin wanda yayi dai-dai da lokacin da Saliha ta janyo kwanon naman da ta 'boye a k'arkashin gado.

Suka had'a ido Saliha ta diriri ce! sai ta wayance da fadin." Ke ni ba naman ki zan ci ba ina neman warin takalmi na ne."

Tsaki taja ta dauke kwanon naman da fadin." Saliha ko kinfi kud'a maita wannan naman yafi 'karfin ki wallahi domin wanda na ajiye wa ya fiki daraja a guri na."

Saliha ta fusata! "Ni ce mayya."

Tace." Me yasa to zaki zo kina min binkice naman nan an raba an baki naki kin cinye, sai kuma ki dinga bibiyar nawa."

Tace." Don Uwarki sharri za ki yi mini naman banza naman wof.......! Shigowar Baban ya katse maganar ta ce." Menene wai ? tun daga soro nake jin hayaniyarku."

Cikin yanayin maganar ta ta ce." Nama na zata satar min shine don na ganta take borin kunya."

Cike da mamaki tace." A ina ki ka samu nama ke kuma.?"

Ta ce." Wanda ki ka bani ne na b'oye abina."

Ta ce." Meye amfanin boye wa sai ya lalace yanzu lokacin zafi ne gwara ki fito dashi ki cinye ni bana san neman fitina."

Kai tsaye tace ." Baban-Baba na ajiye wa."

Gabad'aya suka zuba mata ido.

Baban ta sake maimaita maganar." Ki ka ce Baban-Baba ki ka ajiye wa?"

Ta gyad'a kai alamun "E."

Ba ta iya cewa komai ba kawai ta kama hanya ta fita daga dakin da tunanin wani abu a ranta, lallai dole ne idan Kawu Musu yazo ta sheda masa abinda ke faruwa domin ta fara zargin wani a cikin ranta.



ABUJA
Tun daga bakin Estate din zaka gane lallai mazauna gurin manya mutane ne, gida hudu ne kacal sai tarin sucurites wanda suke kai kawo a gurin, can gefe kuma wasu lafiyayyun karnunaka ne biyu a kwance da alama suna rama bashin baccin da su ka ci.

Gida d'aya a cikin hud'un yafi tsaruwa da burgewa yanayin ginin zai baka sha'awa sosai babu shirman kyale-kyale irin na almubazzaranci.

Daga saman babban gate din da ya katange gidan anyi ado da suna Annabi Muhammad SAW da gold an rufe da wani irin glass mai mutukar daukar ido daga ciki wasu irin fitilu ne da suke bada haske kala-kala sai dare abin yake sake k'ayatuwa da jan hankali.


Ginin tsakiya ne wanda yake dauke da bangare uku sai filin ball dake can gefe da parking spece a in da dace, sai kuma gurin hutawa wanda akayi masa ado da wasu irin kujeru masu kyau da daukar hankali.

Suna tsaye sanye da bak'aken kaya a bakin k'ofar suna dakon fitowarsa, Adamu ne da Sule Escort dinshi.


Yana zaune a gabanta kafafunshi a tankwashe kamar karamin yaro da alama Umarninta yake jira."

Hajiya Saude ce kakarsa wacce ta haifi mahaifinsa ita kad'ai ce ta rage masa a duniya ita kuma yake gani yayi farin ciki duk mai son yaga walwalarsa ya mutunta ta, mai san ganin dariyarsa ya daraja ta.


"Hajiya lokaci na tafiya." Ya fad'a yana duba tsadaddan agogon dake d'aure a hannunsa.

Ta kalleshi babu fara'a a fuskarta ta ce." Alhaji Habu." ita kad'ai ce take kiransa da wannan suna HABU tun yana yaro, Asalin sunansa Abubakar-Assadiq mahaifinsa ne kadai ke kiransa da Saddiku sai kuma abokan karatunsa, amma da yawa daga cikin 'yan uwan mamansa kuwa suna kiransa da 'DANGASKE wanda mahaifiyarsa ta sanya masa dalilin yaci sunan mahaifinta da kuma alkunya irin ta dan fari, wannan dalilin yasa 'yan uwanta suka 'boye sunan domin daraja sunan mahaifinsu, sunansa ya 'bace gabadaya a famliy idan zaka kwana kana kiran ainihin sunansa babu wanda zai gane wanda kake nufi mutukar baka kira DANGASKE! ba.

Ta cigaba da cewa." Na ce wai kai ina zaka kai kudi ne? kullum baka gajiya, kai ne can kai ne nan, a duniyar nan babu 'kasar da baka taka ba, wannan kud'i dai haka zaka tafi ka bar su, ka na ji kana gani Shukura ta zama magajiya tun da ita kadai ka ajiye gemai-gemai da kai da gemu da furfura kana zaune babu aure." Sai ta fashe da kukan b'akin ciki ta cigaba da cewa." Ya jama'a ba zasu zarge ka ba, Habu nima na fara zarginka kana neman matan banza a waje."

Ya sunkuyar da kansa yana sauraran kukanta dake mutukar tafarfasa masa zuciya! zubar hawayenta yana nufin abubuwa da yawa a tare dashi, dole ya rarrasheta domin duk irin bayanin da zai mata ba zata yarda ba bahaushe yace (mai daki shi ya san in da yake masa yoyo) duk ta san gwagwarmayar da ya sha a baya, ya tabbatar da cewar ba za tayi masa uzuri ba tunda kullum fadi take ai matan ba duka suka taru su ka zama daya ba."

"Ki kwantar da hankalinki Insha Allahu zanyi aure very soon."

Hanci ta ja kamar wata k'aramar yarinya murya na rawa tace." Alhaji Habu ni na fi so ka dawo da Fatima Uwar Shukura domin matar fari itace rufin asiri."

Lokaci guda fuskarsa ta sauya! idonsa yayi jah! kansa ya girgiza da fadin." Hajia kada ki sake min maganar Fatimah idan kina so mu shirya.''

Ta kalle shi ganin yanda kwayar idonsa ta sauya yasa taji tsoro kada ciwonsa ya tashi dama can Fatiman ce SILA ta ce." To yanzu ka samu wacce zaka aura din kuma 'yar wane gari ce? domin wannan karon ba na so ka auro 'yar wata k'asar."

A cunkushe ya ce." Ina dubawa tukkuna tunda na ce miki na kusa aure to kisa al'amarin a cikin ranki kuma ki taya ni da addua."

A sanyaye ta ce ." Allah ya tabbatar da alkairi.'' Ya amsa da "Ameen hankalinsa na kan agogon dake daure a hannunsa.


Tsaye ya mike wanda yayi dai-dai fa fitowar Shukura daga dakinta.

"Daddy yau fa duka kwananmu biyar da dawowa ba zaka zauna ka huta a gida ba."

Hannunta ya ri'ke da fadin.'' Shukura ku kwantar da Hankalinku ba nisa zanyi ba KANO na nufa insha Allah zan duba ma'aikatu na (company's) domin ganin abinda yake gudana."

Ita da Hajiyan suka sauke ajiyar zuciya domin duk a tunaninsu sun d'auka zai bar 'kasar ne kamar yanda ya saba tafiye-tafiye.


Cikin nutsuwa yake musabaha da jama'a bayan idar da sallar asubahi a massalacin dake jikin gidansa wanda ke unguwar giginyu, cikin kamala ya fito daga massalacin da cazbaha a hannunsa yana sanye da farar jallabiya mai k'aramin hannu kansa sanye da hula mai raga-raga irin ta larabawa kamar ko da yaushe ya nad'e kansa da farin rawani.
Can tsallake ya hangi wasu matasan samari a tsaye, jikinsa ya bashi cewar shi suke jira ya fito daga massalacin, aikuwa dai gabanshi suka zube suna gaishe shi, ya saki fuskarsa tare da basu umarnin tashi.

Bayan sun gaisa sai kuma su kayi shuru suna sunkuyar da kai dukkaninsu da alamun magana a bakinsu.

Gyaran murya yayi cikin kamala da dattako yace." Ko meye yake tafe daku kada kuyi shakkar fada min ina sauraranku."

Na farkon yace." Alhaji Taimako nake nema a gurin ka, kayi min suttura kamar yanda Allah yayi maka, tabbas nazo gurin da za'a share min hawaye na." Da rawar murya yake maganar.

Ya dafa kafadarsa da fadin." Menene bukatarka? fadi kanka tsaye."

Yaji kwarin gwiwa a tare dashi yace." Mata ta ce ta haihu yau kwana bakwai kenan bani da abin hakika da goro da Alawa hankali na ya tashi sosai Alhaji domin maula ba hali na bane, kawai don bani da yanda zanyi ne kasancewar gwamnati ta yanke min albashi na, babu laifin tsaye bare na zaune wannan dalilin yasa wahala tayi min yawa yara na biyar gashi karamin ma'aikaci ne albashin duka dubu talatin da biyar nake dauka amma yanzu tsayin wata shida kenan da gwamnati ta zabge rabin albashin ya koma dubu goma sha bakwai, to wannan dalilin yasa duk wani karamin ma'aikaci yake cikin tashin hankali."

Ya dinga girgiza kansa yana jin wani irin zafi a zuciyarsa. ido ya tsurawa mutumin yana tunanin wani al'amari daya faru a cikin shekarun da suka gabata lokacin ma da duniya take kwance kenan Malam me za'ayi da mulkin Najeria.

Numfashi ya sauke kafin yace." Kada ka damu komai yana da sanadi kuma kowane bawa akwai hanyar abincinsa saboda haka ni zan taimaka maka daidai gwargwado Allah ya rufa mana asiri."

Gabadaya suka amsa da "Ameen."


Ya kallesu kafin yace."Abokansa ne ko kuma tafiyar kowa daban?"

Hada baki sukayi gurin bashi amsa da cewa." Abokansa ne."

Sai yayi murmushi wanda yake fitar da zahirin kyawunsa ya umarce su da su bi bayanshi zuwa gida.


Dubu dari cash ya bashi da fadin." Ya je yayi hidimar haihuwa, ya kuma yi masa addua sosai.

Shi da abokansa suka rasa bakin godiya.

To ganin gari ya soma haske yasa a gaggauce ya shige cikin gidan ya bar su a bakin gate tare da masu gadi sai godiya suke na irin alkairin da akayi musu.

****
Yau haka kawai ta tashi da kwad'ayin cin wainar gero, kuma mai soya wainar a can bakin titin Jakara take.
Ta fito tsakar gidan ta same su, a zaune suna karyawa da kunu da kosai jawur dashi, sam bai bata sha'awa ba, wainar geron dai take 'kulafuci.

Ta kalleta da fadin." Baba bani naira d'ari zan sayi waina yau kwadayinta nake ji."

Ba tace komai ba ta zuge zif din lalitar dake daure a jikinta ta dauko 'yan hamsin biyu ta mika mata.

Kar'ba tayi da sauri tasa hijab d'inta ta fita tana adduar Allah yasa ta samu kada taje ta tarar ta 'kare tunda yanzun tara ta wuce ana zancan goma.


Wani mugun farin ciki ne ya ziyarce ta sakamakon tozali da ta yi dashi a kwance a k'asan mota akan wani tattararan buhu wanda yayi datti da kasa da k'azanta har da kashin awakai."

Mantawa tayi da abunda ta fito siya, ta tsallaka titin kai tsaye gurinsa ta durfafa fuskarta cike da annuri.

Yana daga kwancen ya hangota sai yayi saurin rufe idonsa kamar mai bacci.

Tana isa idonta ne ya sauka kan kafafunsa, gabanta ya fadi! ta tsurawa kafafun ido tana mamakin abinda ta gani. wata lafiyayyar kafa ce kamar bata taka k'asa, jikinta yayi sanyi lokacin da take kallon fuskarsa da hannuwansa kamar sansanin kanikawa saboda tsabar baki da maik'o sai ka rantse da Allah cewa 'kafafun ba'a jikinsa suke ba.

Tsoro yasa ta d'an ja baya amma ba ta daina kallonsa ba, kuma ba tayi masa magana ba.

Ya bud'e idonsa tare da k'okarin tashi zaune, fuskarsa a murtuke yake kallonta.

Bakinta na rawa ta kirayi sunansa.
Uffan bai ce mata ya dauki wata tsohuwar buta dake k'asan motar yasa bakin kazantacciyar butar da ko arzikin murfi babu a bakinsa ya gumtsi ruwan ciki ya fesar dashi har sai da ya same ta a kafafu.

Ya sake kafa bakinsa a bakin butar yana kokarin shan ruwan dake ciki.

Cikin rauni da tausayi tace." Kada kasha wannan ruwan bashi da kyau zai maka illah.''

Ko kallonta bai yi ba ya kafa baki ya sha ya ajiye butar a gurin da take.

Tsigar jikinta gabadaya ta tashi, sam bata san kallon butar saboda yanda take da 'kyankyami


Komawa yayi ya kwanta ya rufe idonsa yana takure jikinsa, taji wasu zafafan hawaye suna kokarin kwace mata, wallahi da tana da yanda za tayi akansa da tuni ta samar masa nutsuwa da makwanci mai kyau.

Can gurin mai siyar da wainar geron ta nufa. A ka ci sa'a wainar bata k'are ba. to koda ta sayi wainar a maimakon ta nufi gida kai tsaye gurinsa ta koma domin ba ta tsammanin za ta iya sanya wani abu a cikinta mutukar ba tabbatar da cewa shi din yaci wani abu ba.

daf dashi ta tsuguna da ledar wainar a hannunta, cikin yanayin tsoro ta kirayi sunansa, ya bude ido yana kallonta, ta ce." Ga waina za ka ci ko.? ya bi hannunta da kallo lokacin da take mi'ka masa ledar wainar.

Ta fara k'ok'arin kwance ledar tana fadin." Ga ta nan da zafi ka ci bari na je gida na kawo maka kunu ka had'a."

Kallonta kawai yake bai sa hannu ya kar'bi wainar ba.

Ta marairaice fuska kamar za tayi kuka ta ce." Don Allah ka ci wallahi tausayi kake ba ni.''

Tsigar jikinsa ce ta tashi jin abinda tace. Ya tsira mata idanuwansa yana jin wani irin tausayinta, ya lura da yarinyar ta na sonshi sosai kuma duk abinda ta fad'a gaskiya ne.

Hannu yasa ya 'karbi wainar a takaice ya ce." Na gode."

A hankali ya yi maganar shi yasa ba ji ba, amma ta fahimci godiya yake mata.

Ta mi'ke da fadin." Bari na je na dawo."

Bai ce mata komai ba, ta tsallaka titin ya bita da kallo yana ayyana abubuwa da yawa a kanta.


Cikin farin ciki ta shiga gidan, lokacin har sun fara aikace-akaice abincin siyarwa Baban tana yanka kabewa ita kuma Saliha na gyara alayyahu.

Da farin ciki a tare da ita tace." Baba akwai kunun ko?"

Ta ce." Eh saura naki a kadai gashi can a jug."

Tace." Baba yau dai na ga Baban -Baba a bakin titi wallahi dadi ya rufe ni.'

Ta harareta da fadin." Matsalarki ce wannan Shahida ni abinda nakeso ki zo ki daka min gyadar miya domin yanzu zan hura wuta na dora miya."

Tace." Shikkenan yanzu zan zo nayi."

Ba ta sake magana ba, kawai sai gani su kayi ta shiga daki minti biyu ta fito da kwano a hannunta, ta dauki jug din kunun ta kama hanya ta fita.

Saliha tace." Wallahi Baba idan ta dawo da kwanukan kada kiyi amfani dasu domin ba kowa za ta kai wa ba sai wannan mahaukacin.'

Tace." Saliha ya zanyi da Shahida, na yi magana cibi ya zama 'kari, na zuba mata ido kawai amma ya zama dole idan mahaifinki yazo mu tattauna dashi domin ina wani tunani a kan yarinyar."


Tana 'yar dariya ta ce." Wallahi lafiyarta lau tsabar iskanci ne wai ita mai tausayi watarana sai taje ya buga mata dutse idan haukan nasa ya motsa."

Ta girgiza kai da fadin." Allah ya rufa asiri.


"Wannan naman sallah ne na kawo maka, wannan kuma kunu ne in sha Allahu da rana ma zan kawo maka abinci."

Ya kalleta kafin ya kalli abubuwan da ke gabansa, hannu yasa ya bud'e kwanon naman babu abinda yayi suyar tayi kyau sosai sai k'amshi yake.

Rufe wa yayi kafin ya bude jug din kunun shima da zafinsa sai kamshin lemon tsami yake, sosai kunun ya bashi sha'awa, amma bai nuna a fuskarsa ba.


Sunkuyar da kansa yayi ba tare da yace mata komai ba.

A sanyaye ta ce." Sannu ko baka da lafiya ne?"

Ya d'aga mata kai alamun ."Eh." gabad'aya jikinta ya mutu kamar za tayi kuka ta ce." Zazzabi ko ciwon kai.?

Ganin tana shirin fashewa da kuka yasa ya sassauta fuskarsa ya ce." Babu ko d'aya jikina ne yake ciwo."

Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Sannu Allah ya sawwa'ke amma ka daina kwanciya cikin lema dubi abin shimfidar ka a jike ga 'kazanta da kashin awakai dole lalura ta kama ka."

Shuru yayi bai ce komai ba.

Tace." Ka sha kunun sai na tafi na siyo maka magan........Ya buga mata tsawa! a burkice yace."Ke! tashi ki bani guri bana so kin dame ni da surutu."

Ta tsorota ta mi'ke tsaye tana kallonsa, gabad'aya idanunsa sun jirkice! ya d'auki robar ruwan paro ya jefa mata, wanda ya janyo hankalin yara gurin.

Aikuwa suka fara ihu! "Baban-baba mahaukaci! Baban Baba mai annakiya." wasu suka fara tsintar duwatsu suna jifansa tare da tofa masa yawu, sai su ruga a guje suna dariya.

'Karkashin motar ya shige ya takure jikinsa guri daya yana makyarkyata!

Ita kuwa zuciyarta a 'kuntacce ta bar gurin wani k'atoton abu ya tokare mata a wuya tana shiga gidan kai tsaye daki ta nufa ta kwanta saman gado tare da fashewa da wani irin kuka!
Kuka taci ta koshi ta fito idanunta jawur! babu wanda ya tambaye ta abinda ya sa ta kuka aikin gabansu kawai suke, murya a dashe tace."Baba ina gyadar take.?

Da hannu ta nuna mata. ta cigaba da aikin gabanta zuciyarta cike da kunci da takaicin halin da yarinyar take 'kokarin jefa kanta.


****
"Wai ana sallama da maigidan." muryar wani yaro kenan, yayin da aka aiko shi ya yi sallama da Hujaj.

Jamila ce ta fito da fadin." Ba ya nan.'' yaron ya juya ya fita, minti biyu ya dawo da fadin." Wai idan ya dawo a fada masa cewa Saminu abbatuwa yana nemansa."

Ta ce." To za'a fada masa.


Da ya dawo gidan Talatu ta sheda masa cewa wani yazo nemansa mai suna Saminu Abbatuwa, ko gezau bai yi ba ballanatana ya razana, cin bashi dai ba akansa aka fara ba, kuma sai yana dashi zai biya.

Hankalinsa a kwance ya cire babbar rigar jikinsa ya rataye, ya kashingida yana tunanin yanda za'ayi kudi su shigo masa, kwana biyu kamar wanda a kayi wa baki gurin sana'ar tasu haka yake dawowa babu ko sisi a aljihunsa, hakan kuma baya ha na shi gobe ya koma da wata kadarar tasa domin samun nasara tare da nin ka abinda ya bayar.
[4/19, 10:26 AM] Bintu: Bacci ne ya fara fizgarsa kamar a mafarki ya ji muryata a kunnansa, ya bude ido yana kallonta tana tsaye 'kerere a kansa. cikin 'bacin rai ya ce." Wai ke Talatu yaushe zakiyi hankali ne.? ta'be baki tayi ta nannago 'bakar magana ta ya'ba masa domin har yanzu da ragowar haushi da takaicin abinda yayi mu su, haka kawai ya kwashe nama ya bayar, sun tashi a tutar babu.

Babu ladabi a maganarta ta ce." sai ranar da akayi hankali ni ma zanyi." Ya tsira mata ido yana kallo.

Ta ce." Tun shekaran jiya wannan mutumin yake zuwa sallama da akai, ya ishi mutane nace yau dai tunda kana gidan sai ka tashi kaje domin kaji abunda yake tafe dashi."

Yana kokarin tashi zaune ya ce."Ki aika Jamila ta fada masa cewa bana nan."

"Wane irin na aika Jamila bayan

1 Comments On BA MAHAUKACI BANE Book 1
avatar
arfat-aliyu

1 year ago

Reply

Masha allh

Please Login or Register in order to submit comment