Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kamata. Kasa mika mata ta yi don gani ta ke in ta ba su za su kara dawowa hannu rabbana su ce jaririn ma ya cika. Kaunar da ta ke yi wa Habiba daga Allah ne saboda kyawawan halayenta. Daddy ne ya kwakulo jaririn daga hannunta ya ba su suka juya wani daki na musamman da ake kira (day-old). Shi kuma ya kama hannunta ya ja ta har kan kujerun reception din ya rungumo ta yana lallashi.
“Kullu nafsin za’ikatul maut Maryama, cool yourself...” Ya fada yana bubbuga bayanta, sai ta fashe da kuka.
Abdul’azeez ya ce, “Daddy Habiba ta rasu?”
Ya daga masa kai.
“To wannan Baby din fa? Haifarsa ta yi?”
Ya kara daga masa kai. Bai san sanda shi ma ya fashe da kuka ba.
Haka Daddy ya zama dan lallashi, ya lallashi uwar ya lallashi dan. Daga karshe su duka biyun ya hada ya rungume. A haka aka turo gawar Habiba ta gabansu aka saka a ambulance duk suka mike suka bi bayan motar a tasu motar zuwa gida.
Tun a mota Ambasada ke waya da abokan aikinsa na Embassy Of Nigeria da makotansa yana fada musu akwai janaza a gidansa, don haka kafin su isa har mutane sun fara cika get dinsa. Hajiya Maryam da matar makocinsu Hajiya Sugrah su suka wanke Habiba suka shirya ta, mutane sama da hamsin duk ‘yan Nigeria ne suka sallace ta suka yi mata rakiya zuwa gidanta na gaskiya. RAI ba a bakin komai ba! Duk haka za mu tafi daya bayan daya. Ya Allah ka sa mu cika da kyau da imani (hawaye).
Sai dare mutane suka daina shigowa, ya rage daga Hajiya Maryam sai yaranta. Sun hadu su biyar har ita sun yi jigum-jigum a babban falo. Da gani cikinsu duka babu wanda gushewar Habiba ba ta doka ba. Musamman Abdulazeez. Hatta Halim da yake karami ya yi sanyi ya daina walwala, ya fi kowa sabawa da Habiba, ya fi kowa hawa bayanta ta goya shi. Sai ta yi awanni biyu da shi goye a bayanta tana ayyukanta ba tare da ta gaji ba. Suna yi suna hira tana biyewa shirmensa babu kosawa. Tun safe bai ganta ba, ya kuma ga sanda aka fita da ita kwance kan wani gado ya tambayi Mammah ina za a kai Habiba sai ta sa mishi kuka, tun daga nan bai kara tambaya ba, sai dai kuzarinsa ya zube, ya yi shiru a kwance saman kujera kamar yadda ya ga kowa ya yi shirun.
A lokacin Hajiya ta tuna da babyn da suka baro a asibiti. Zumbur ta mike ta tadda Daddy a (bedroom) dinsa. Yana zaune a bakin tankareren gadonsa yana waya, shi fa da alama mutuwar nan ba ta doke shi ba, harkokin gabansa yake yi tunda ya tsaya ya yi wa gawar Habiba gata, ya yi duk abin da musulunci ya umarce shi tuni ya koma sabgoginsa.Dukkansu tun karin kumallon safe ba abin da ya kara shiga bakinsu, amma tana kallonsa ya je kicin ya dafa shayi da kansa ya aika direba ya sayo masa Dajaj (KFC) ya shige daki ba ta kara jin duriyarsa ba.
Da sallama ta shiga dakin, bai fasa wayar da yake yi ba. Ya daga ido ya dube ta, ta zauna gefensa tana kallon yadda ya ci kaza ya bar kasusuwa haushinsa ya kama ta, wato ba ya taya su makokin da suke ciki balle ya je ya lallashe su ita da ‘yan samarin ‘ya’yanta.
Ya sanya hannunsa cikin tafukanta ya matse da karfi, a lokaci guda yana ci gaba da wayarsa inda ta fahimci da kawunsa Sanata Abdulkarim yake yi. Kawun da ya zame masa kamar aboki sabida shekarunsu daya kuma tare sukayi karatu tun daga sakandire har jami’a. Sai da ya kammala ya ba ta (attention) dinsa.
A sanyaye ta ce, “Zan koma asibiti ne in ji halin da Baby ke ciki”.
Sosai ya kalle ta, yini guda duk ta zuge, ta fige. Yana mamakin wannan kauna ta ‘yan aiki da Allah ya dora wa maidakinsa.
“A dawo lafiya, Allah ya jikanta, Ya ba ku hakuri”.
Ta ce, “Amin”. Tare da mikewa za ta fita.
“Maryama!” Ambassada ya ambata cikin sanyin murya.
Ta dakata ba tare da ta juyo ba. Ya miqe ya tako zuwa jikin kofar, har inda ta ke tsaye rike da (handle) din kofar. Hannayensa ya kai ya zagayo da su cikinta, wato ya rungume ta ta baya. Ya dora kansa saman kafadunta.
“Yau ko sumba daya ban samu daga Maryam dina ba. I’m sure kina son Habiba. Ko kanwarki ce ta ciki daya sai haka! My condolence dear, Allah ya yi mata rahma”.
Sosai hawaye suke sauka a kan kumatunta. Ta juyo ta rungume shi ta sumbaci goshinsa,
“Na gode Daddy”.
Ta sake shi da sauri ta fita.
Bayan fitarta Ambassador zancen zuci ya shiga yi, “Allah ya sa kada ta ce ita za ta riqe abin da mai aikinta ta bari. Abin da ba zai taba yiwuwa ba ne, ko ‘ya’yan ‘yan uwansa ba ya dauka riko balle ‘yar mai aiki, duk wani taimako zai yi maka, amma ban da dauko ka ya tsoma cikin iyalinsa. Yana da kakkarfan ra’ayi a kan ‘single nuclear family life’, ta yadda ko bako ne ya zo zai kwana daya ba ya sakewa cikin iyalinsa har sai bakon nan ya tafi. Ji yake kamar a kansa yake zaune.
Ya girgiza kai, ya ci gaba da kiraye-kirayen wayoyinsa.
Hajiya Maryam a gaban tebirin likita Unaisa, “Jaririyar mace ce, an haife ta da cutar pneumonia, numfashinta ba ya fita yadda ya kamata. Da alama uwarta na yawan ta’ammali da ruwa, da shan ruwan sanyi ko? Za mu rike ta cikin kwalba (incubator) har sai ta cika watanni tara”.
Hajiya Maryam ta ce, “An gode Doctor, Allah ya raya ta. Zan iya ganinta?”
“Sosai kuwa. Zo mu je, don yanzu za a cire (oxygen cylinder) din a sanya ta a kwalba. In ta cika watanni tara sai ki zo ki tafi da ita”.
Hajiya Maryam ta tsura wa jaririyar ido, ta dade ba ta ga kyakkyawar halitta ta fulanin usul irin wannan ba. Komai nata na Habiba ne. A very cute baby. Ta kai bakinta ta sumbaci goshinta, kumatunta da bakinta wata irin kauna ta UWA ga DA na ratsa zuciyarta daga Ubangiji subhana. Allah bai taba nufarta da haihuwar diya mace ba, abin da kullum ta ke wa addu’a, amma tun daga kan Halim haihuwar ma ta dakata mata ko batan wata ba ta kara yi ba. Ba ta jin ko dangin Habiba da uban yarinyar nan za ta yarda su raba ta da wannan jaririya da ta sanya wani irin sanyi a idanu da zuciyarta.
Da kyar Dr. Unaisa ta karbe jaririyar ta shiga wani daki na musamman da ita. Direba ya dauko Hajiya Maryam suka dawo gida.
Bayan kwana bakwai da rasuwar Habiba, Hajiya Maryam tana zaune a falo ta kira Hajiya Halima aminiyarta. Wato wadda ta samo mata Habiba. Bayan sun gaisa da tambayar lafiyar iyali, Hajiya Maryam ta ce, “Halima, ko kin san asalin inda Habiba ta fito? Ina nufin garinsu na ainihi, miji da iyayenta?”
Hajiya Halima ta ce, “Tabdijam! Wallahi ba ni da sani a kan ko daya. Ni ma wata mai aikin Rabi’a ce (kanwarta) mai suna Asabe ta kawo min ita, kuma ta ce haduwa suka yi a motar haya sabo ya shiga tsakaninsu, duk da lokacin Habiban ba ta cikin hayyacinta ta ganta kamar wata mai iskoki. Saida ta kwana uku a wurinta tana yi mata addu’a sannan ta warware. Ta ce tana son ta samar mata gidan aiki ta fito neman aikatau ne. Asaben ta ce, ita ma aikatau ta ke a Abuja, su wuce can za ta samo mata. Suka zauna tare a gidan Rabi’a na tsayin watanni biyu tana bincika mata gidan aiki, shi ne da na ce ina so ta kawo min ita, washegari kuma na ba ki da na lura kin fi ni bukatarta. Ita kanta Asaben yanzu sun dade da rabuwa da Rabi’a ta koma kasar su Ghana. Ba mu yi wani zama mai tsawo ba da har zan binciki wani abu nata”.
Hajiya Maryam ta nisa, “Halima Allah ya yi wa Habiba rasuwa”.
Hajiya Halima ta ce, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un...”
Mama ta katse wayar, ba ta so Hajiya Halima ta sa ta kukan da ta samu ya tsaya mata tun kwana uku da rasuwar Habiba.
Kullum cikin kirga kwanaki ta ke na ranar da za ta amso jaririyarta. Haka duk sati tana tafe ganin baby a cikin kwalba daga nesa cikin rakiyar Dr. Unaisa. Tana gaya wa Halim kwanan nan za ta kawo masa kanwa, ya samu abokiyar wasa da zuwa makaranta.
Hutun Abdul’azeez na wata uku ne, don haka Daddy bai barshi ya zauna a gida ba ya komai ba har watanni uku, ya dauke shi ya sanya a Tahfiz inda yake daukar haddar Alqur’ani mai tsarki daga islamiyyar wasu Larabawan Madinah da sauran littattafan addini shi da sauran ‘yan uwansa a ranakun karshen sati, wato Alhamis da Juma’ah, in sun tafi tun safe sai karfe shidda na yamma, don haka Hajiya Maryam ba ta cikin matsalar rashin mai aiki sosai a dan tsukin, kafin kowannensu ya tafi tahfiz ta raba musu aikin cikin gida da za su yi a tsakaninsu don ita sam bata son harka da Takari. Abdul’azeez shara, Isma’eel wanke-wanke, Usman (mopping), Halim kara bata wuri, sauran ayyukan gidan na waje maza masu aiki ke yi, kamar wanki da guga, gyaran furanni da ba su ruwa.

Rayuwar gidan Ambassador Hamza Atiku abar sha’awa ce abar koyi. Ba su da abin da ya fi tarbiyyar ‘ya’yansu da nema musu ilimi muhimmanci a gare su. Yaransu nitsattsu masu hankali da sanin yakamata. Uwar da uban kuma soyayya da shakuwa mai karfi ce a tare da su, ta yadda in ka lura za ka fahimci ba soyayyar aure ce kadai a tsakaninsu ba, akwai ta jini mai gudana a cikin jiki da jijiyoyi. Kaunar da suke yi wa yaran ba ta hanawa su ba su ingantacciyar tarbiyya, su kwabe su in sun yi ba daidai ba cikin nasiha da jansu a jiki. Sai dai fa kaunar Abdul’azeez daban ta ke da ta kowa a zuciyar Ambasada.
Idan da abin da Abdul’azeez ya tsana shi ne a yi masa tsawa, ya fi son ko ya yi ba daidai ba ka fada masa a hankali shi ya sa ya fi son Daddy, ya fi sakin jiki da shi tunda Mammah tana yin tsawa. Rannan ya yi laifin yin kwallo (ball) da Magenta (qiddah) inji larabawa, sabida ta sa masa baki a abinci, Mammah ta yi tsawa. Yatsunsa biyu ya sa ya toshe kunnuwansa ya rufe ido jikinsa yana bari da karkarwa, cikin karkarwar jiki data murya ya ce.
“Mammah please... tell me what you want to me to do, but please don’t shout.......”. Sai ga hawaye sun shimfido a guje.
Jikin Mammah ya yi sanyi, daga ranar ba ta kara daga masa murya ba sai lallashi da nasiha, don Abdul’azeez ko dukansa aka yi ba ya hawaye. Amma in kayi masa tsawa zai yi abinda yafi kuka.
Hutunsa ya kare ranar wata lahadi, suka kai shi airport ya daga Abuja, gidan karamin Kakansa Sanata Abdulkarim ya sauka. Washegari ya koma makaranta.
Ya yi daidai da ranar da Mammah ta karbo baby daga asibiti, bayan likitoci sun tabbatar da koshin lafiyarta. Dr. Unaisa zaunar da Hajiya Maryam ta yi, ta yi mata lacca ta lokaci mai tsawo kan yadda ake kula da mai lalurar nimoniya, da shawarwari kan abincinta. Ta bada shawarar madarar da za a dinga ba ta (SMA) tana buqatar dumi (heat) a kowanne lokaci, kasancewa cikin kaya masu kauri a lokacin zafi, kasancewa cikin kayan sanyi sosai a lokacin sanyi. Ta kasance jikin uwa a kodayaushe don samun dumin jikin uwa, kasancewa a daki mai dumi da shan madara mai dumi sosai. Wannan zai taimaka ta murmure sosai cikin watanni kalilan.
Hajiya Maryam ta yi wa Dr. Unaisa godiya sosai, ta karbi lambar wayarta ita ma ta karbi tata. Duka ‘bill’ din da asibitin ya caje su ta file din iyalin Ambasada aka biya.
Karfe shidda daidai na yamma Salah direba ya yi (parking) a cikin (gate) din gidan Ambasadan Najeriya a kasar Saudiyyah Professor Dr. Hamza Atiku Dakata, Hajiya Maryam ta fito rungume tsam da kyakkyawar bakwainin jaririyarta cikin farin shawul mai tsananin taushi. Salah ya biyo ta da jakar ‘shopping’ din kayan jarirai da abubuwan bukatar su da ta yo a kasuwar (Baaba Sheriff), ta karasa cikin falon bayan ta ture kofar gilashin (sliding door) da ta raba harabar gidan da tangamemen falon wanda ya ji kayan alatu da ababen more rayuwa iri-iri.
Daddy ne zaune a kan kilishi cikin ‘ya’yansa uku yana duba littattafansu na makaranta, don ganin halin da kwakwalwar kowannensu ke ciki. Halim yana kan cinyarsa da nashi (drawing book) din, a yadda ya fahimta Isma’el shi ne mai matsala, yana da rauni kwarai a kan darasin lissafi (mathematics). Nasiha yake masa sosai cikin hikima kan ya maida hankali ya iya lissafi domin shi ne kashin bayan ilimin boko. Mammah ta yi sallama suka mike da gudu suka yi kanta. Fadi ta ke,
“Ku yi a sannu kada ku kada kanwarku, kun ga ba ta da lafiya”.
A sannu Daddy ya daga ido ya dube su, ya soma dan yamutse fuska, suka hada ido da matar tasa. Ta fahimci ya canza fuska, gwiwoyinta suka yi sanyi, amma a haka ta karasa gare shi ta zauna dab da shi ta miqa masa jaririyar, kamar ba zai karba ba ko me ya tuna kuma ya karba, ganin Usman ya danne Isma’el duk a kokarinsu na kowanne so yake a bashi jaririyar ya dauka, sai ya karba don ya raba fadan, amma ba cikin dadin rai ba.
Sama-sama ya kalli ‘yar sai kuma ya mika mata, ya tambaye ta,
“To yanzu ya za ki yi da ita? Bana jin gidan marayu na Saudi-Arabia za su amshe ta, tunda mu ba ‘yan kasa ba ne”.
Mammah cikin mamakin sauyin da ta gani a tare da Daddy farad daya, ta ce da shi cikin kwantaccen sauti.
“Wai da so nake ka yi min izini in sha magani in samu ruwan nono in shayar da ita”.
Girgiza kai ya shiga yi,
“Wasa ne wannan, ki shayar da dan da ba nawa ba?”
Kamar za ta fashe da kuka ta ce, “Daddy........”
Ya dakatar da ita, “Please don’t argue with me Maryama. Ki maida ita wajen dangin mahaifiyarta, ba zan iya riqon dan da ba nawa ba balle in kasa yin adalci tsakaninsa da ‘ya’yana Allah ya tuhume ni, musamman rikon maraya. Na yi miki alkawarin zan dauki nauyin iliminta har zuwa digiri na kololuwa idan tana so a ko’ina ta ke cikin duniya. Amma ba zan hada ta da ‘ya’yana in rike ba”.
Hajiya maryam ta fashe da kuka, “Don Allah Daddy kada ka yi min haka... ina sonta, ina son uwarta ina son diya mace... Allah bai ba ni ba... don Allah Daddy ka yi min alfarma ka barni in rike ta koda wannan itace alfarma ta karshe da zaka yimin a rayuwa”.
Ta daga hannuwanta biyu gare shi tana kuka tana roko.
Dukkan yaran ma kuka suka sa suna rokonsa har Halim,
“Daddy ka bar mana don Allah, muna so, kada a kai ta wani waje ta mutu kamar yadda Mamanta ta mutu, do us a favour”. Inji Usman.
Suka kama babyn duka suka kankame, ita kuma da ta ji matsa ta canyara kuka da muryarta kamar gyare don zaki. Su biyar din duka kuka da hawaye share-share.
Sakin baki Ambasada ya yi yana kallonsu, kafin ya ce “Na shiga ukuna. Ku dakata, mu yi magana ta maslaha”. Ya fada yana daga hannu irin na saranda. Duk suka dakata suna share hawaye suna hadiyar zucci.
“Zan bi ra’ayinku tunda kun rinjaye ni, amma da sharadin ban yarda Mammah ta yi (breast-feeding) dinta ba, a nemi ‘alternative”.
Sai duk suka juya suna kallon Mammah don jin ta bakinta. Kowannensu fuskarsa na nuna “Mammah ki yarda da hakan”.
Hajiya Maryam ta sa habar zaninta ta goge fuska da majina, “Daddy ba ta da lafiya ne, tana da pneumonia, tana bukatar ruwan nono da dumin jikin uwa, in ban shayar da ita ba bani da kulawar da zan ba ta fiye da hakan”.
Mikewa ya yi yana dakile fuska. Ya kakkabe rigarsa ya nufi matattakalar da za ta sada shi da dakinsa. Yana tafe yana fadin, “Shawara ta rage ga mai shiga rijiya, na ba ku daga yau zuwa gobe ku yi shawara, har madara zan dauki nauyin saye sadaqah fisabilillahi. Amma in ba haka ba gobe zan sa a buga mata fasfo ku kai ta inda ku ka dauko uwarta”. Ya yi wucewarsa ya shige daki ya rufo kofa.
Usman ya matso sosai jikin mammanshi, idonsa a kan babyn da ta zuba fararen yatsunta cikin baki tana tsotso alamun yunwa.
“Mammah ki yarda don Allah mana? Tunda mun samu ya bar mana?”
Isma’el ya ce, “Mammah don Allah ki yarda ta sha madaran, rayuwa da ciwo duka na Allah ne, idan mai tsawon rai ce sai ki ga Allah ya raya mana ita. Take heart Mammah...”. Ya fada tare da kai hannu santar kirjinta yana shafawa alamun ta yi hakuri ta bi abin da Babansu ke so.
Hajiya Maryam ta tsura wa ‘ya’yan nata ido, yara masu hankali da tunani tun a qananan shekaru irin nasu. Har sun fi ta tawakkali da hangen nesa. Da gaske Allah shi ne mai rayawa ba nonon uwa ba. Ta rungumo su gefe da gefenta, jaririyar na bisa cinyarta, ta sumbaci kowannensu a goshinsa,
“Na amince. Gobe zan gaya wa Daddy. Yanzu zan fara ba ta madara kun ji ana kiran sallah, maza kowa ya je ya yi alwala yanzu Daddy zai sauko ku wuce masallaci”.
Duk suka mike cike da murna har da tsalle suka nufi toilet don dauro alwalar. Ita kuma ta dauki ledar shopping dinta da babyn ta nufi dakinta.
A take ta tafasa ruwan zafi ta hada madarar ta soma ba ta. Wata irin kauna tana mamaye zuciyarta na ‘yar da ba ta san daga ina uwarta ta ke ba balle ubanta. Sai dai kaso 90% na zuciyarta ya amince yarinyar nan ba shegiya ba ce, da ubanta. Habiba ba ta yi kama da mutanen banza ba, sannan ba yarinya ba ce balle a ce shege ta yi ta gudu. Ta fi amincewa da cewa wani nau’i ne na kaddarar rayuwa ya rabo ta da gidan mijinta da iyaye da ‘yan uwanta.
Ba ta yi gigin zuwa turakar Daddy a yau ba kwata-kwata, shi ma bai neme ta ba. Duk abubuwan da ta saba yi masa kafin su kwanta da kansa ya yi, zuciyarsa fal haushin Maryam, tunda daga samun ‘ya har ta fara watsar da shi, da ma a ce ita ta haifa da sauki ba zai damu ba. Ya yi tsaki yana shan ‘gahwah’ (coffee) ya fi sau shurin masaki. A haka ya kwana cikin bacin rai, ita kuma tana can tana ceton rayuwar ‘yar marainiyar Allah. Ta kashe A.C ta kunna (room heater), ta ciro kayan sanyi masu kyau cikin sayayyar da ta yi ta sunke ta a ciki, da pampers. Ta cika mata ciki da madarar da Dr. Unaisa ta yi umarni. Nan da nan ta hau baccinta cikin kwanciyar hankali. A lokacin ne ta tuno da Daddy, ta yi ajiyar zuciya ta yi shirin bacci ta manna jaririyar a jikinta, ta rufe su ruf cikin lallausar bargo, suka yi bacci abinsu.
Tun asuba kukan baby ya tashe ta, ta tashi zaune ta dauke ta ta yi toilet da ita. Wanka ta yi mata da ruwa mai dumi sosai, ta nado ta cikin shawul. Shafe ta ta yi da man zaitun ta canza mata (diaper), ta shirya ta cikin (overall) farare tas! Da hula mai kauri. Sannan ta hado madararta ta shiga ba ta. Ta kura mata ido ba ta ko kiftawa. Habiba ta ke tunawa da karamcinta, da yanzu ta fara jiyo sukurniyarta tana shara da goge-goge kafin ta fada kicin ta hada mata kayan girki kafin ta sauko. Hawaye suka ciko a idonta, me ya sa Habiba ta yaudare ta? Me ya sa ta boye mata asalinta da cikin da ta ke dauke da shi? Rayuwar yarinyar a gaba ta ke kokawa idan Allah ya raya ta ta fahimci ita din ba uwarta ce mahaifiya ba, ba a san kowa nata ba, ba a san daga inda ta fito ba. Ta ajiye ajiyar zuciya mai nauyi, ta share hawayen idanunta. A hankali ta sanya babyn cikin gadon da ta hada yanzu, sai bacci ta ke sadidan cikin koshin lafiya.
Wanka ta yi, ta ci gayunta kamar yadda ta saba, kai ba za ka ce ta yi shekaru talatin da biyarba. Ta san sirrin gyara na diya mace kala-kala. Ta lakanci ado da kwalisa tun tana budurwa, haka yanzu da shekaru suka fara turawa ba abin da ya canza Maryam Dakata. Farar mace mai farar aniya, uwar gidan Professor kuma Ambassador Hamza Atiku Sakata.
Kicin ta fada ta soma hada wa iyalinta abin kari. Sosai ta yi latti, domin har gari ya waye. Sanin Daddyn a sama-sama yake da ita ta ce bari ta yi masa abincin da ya fi so, don ta dan faranta ransa. Kunun gyada ta hada ya ji madara yadda ya kamata. Ta hau suyar sinasir din da ta kwaba tun daren jiya. A gurguje ta ke yin komai, miyar ta ji ganyen alayyahu sosai da tsokar kaji. Sun dahu sun yi lugub. Yaran kuma (quaker oat) ta dama musu, ta soya musu ‘pancake’ ta shirya wa kowanne a sundukin abincinsa. Da hanzari ta shirya wa Daddy tebur jin baby ta fara kuka. Su Isma’el suka fito daga dakinsu cikin shirin makaranta kowanne goye da dirkekiyar (school bag) dinsa.
“Mammah sabahul khair”. Duk suka fadi a tare bayan sun shigo kichin din cikin russunawa.
Kansu ta shafa daya bayan daya tana murmushi, “Sabahul khair, ‘yan albarka, kun tashi lafiya?”.
Isma’el ya ce, “Karasa aikinki Mammah, I will help you with the baby”.
Ta yi murmushi ta daga masa kanta.
“Madararta na nan a kan (side drawer) ba ta ina zuwa”.
Da hanzarinshi ya juya zuwa dakin nata.
Tun a kan Halim Isma’el ya iya raino, shi ke taimaka mata da rainon Halim har ya yi wayau. Yanzun ma baby ya ciro daga gadonta ya aza a kafadunshi yana rirriga ta har ta yi shiru. Ya zauna gefen gadon Mammah ya ba ta ruwan zam-zam ta sha sosai, sannan ya sanya mata madarar a baki. A ranshi yana cewa, duk da dai an ce ba a gane kamannin jariri, amma wannan da ganinta Habibah ce sak!
Mammah turakar Daddy ta nufa da saurinta, suka ci karo a matattakalar bene ya yo shirin office tsaf, rike da (briefcase) dinsa. Ta karba suka sauko tare, sai faman dauke mata kai yake yi. Ta yi murmushi a ranta ta ce, “Insha Allahu watarana sai ka yi alfahari da ‘yar da ba ka son rikewa din”.
Su Isma’el ya kwala wa kira yana kokarin ficewa daga falon ba tare da ya dubi (dining) din ba. Ba ta yi fushi ba, ta ce, “Daddy break fast fa?”
“I’m ok”. Ya fada yana duba agogo.
Ta ji ba dadi yadda mata ke ji in sun takarkare sun zabga wa maigida girki ya ki ci.
Usman da Halim suka wuce tare da shi, Isma’el ya fito dauke da baby ya mika wa Mammah, sannan ya dau jakarsa da kwandon abincinsa ya bi bayansu da gudu. Ta yi ajiyar zuciya ta goya baby jikinta a sanyaye. Da gaske Hamzanta ya canza daga halin da ta sanshi da shi. Ta san shi mutum ne mai tausayi da taimakon na kasa da shi, ba ta san me wannan yarinyar ta tare masa cikin gidan nan ba, da alama za ta fuskanci barazana mai yawa a rayuwar aurenta a kan rikon yarinyar daga mijinta, abin kaunarta. Ta kuma shirya karbar kowanne kalubale in har zai bari su rayu tare. Ba za ta kai ta Nigeria ba, inda ko sun je babu inda za ta kai ta a karba in ba gidan marayu ba.
Ta shirya yin jihadin rikon ‘yar Habibah ko da Daddy zai kara aure ya kora ta Nigeria a dalilin haka. Ta watsar da tunanin ta shiga harkokinta. Islamiyyar ma ta daina zuwa sai ‘yarta ta isa bari a makarantar rainon yara (creche). Amma dole ta nemi ‘yar aiki don ayyukan gidan sun fi karfinta. Karshen

1 Comments On AUREN KWANGILA
avatar
saratu-7-7

1 year ago

Reply

Auren kwangila complete pls

Please Login or Register in order to submit comment