Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
⚜⚜⚜⚜⚜



*AMRATU*


*Written by*
*Khadija Muhammad*
*Ummusulymn*
*And*
*Fatima Aminu Ya'u*
*F.A.Ya'u*


*Bissimillah lahir-Rahmaneer-Raheem*









Da gudu ta shigo tafada kan mami dake zaune wash mum nagaji wallahi tai dariya kin gaji kuma kike san karya ni ko haba mami sai kace wata mai kibar axo agani Aliyu dake gefe yana cin abinci ya wurga mata harara kaga ni kadaina hararar mun diya wallahi mum kina shagwaba yarinyar nan da yawa ace yarinya tana SS3 bata dena hawa cinya ba tunda dai ba cinyarka ta hauba ai saika xuba ido.

Ke jeki ki daukon abincina kai yaya kai yaya ta fada tana xunbura baki aikifa nake ke nikike fadawa kina wani abu yakai hannu xai maketa tai saurin direwa daga kujerar mami dake shigowa tace kul karka sake ka daketa ta koma bayan mami tanai masa gwalo yakara kuluwa amman mami anman mai inajinku ace ka bi ka gallabi yarinya bakaga rubutu take ba baka ganin salame baka sata kenan mami ni ban isa in aiki kanwata ba kenan oho duk yadda kadauka.

Kanwis mai ake dafa mana ne nafaji kanshi ko ina mutumin naka ne ah kice yau da gara yafada yana dariya maxa gama kixo kiga abinda na kawo miki tai dariya that's my yaya sulaiman shima yandariya😀yace that's my little sister shiyasa nake sonki suna shirmensu mummy ta shugo tare da murmushi matsalata daku akwae hankali Suhailat ta turo baki"haba mamy wlh ke kk ja Yaya Aliyu yake mana son ransa"
Mummy ta"bige bakin ja'i'ra ba yayanki bane Amra ta fita kitchen a guje tana dariya.





Amra ta wayi garin ranar litini da xaxxabi sbd haka bataje makaranta ba tana qudundune a blanket,mamy ta shugo dakin tare da fadin Babyn mamy ya naji shuru baki fito parlour ba har munyi breakfast, kuma nagani baki da niyyar xuwa skul ta yamutsa fuska wallahi mami bana jin dadi ne subhanallahi ta fadi gami da saurin kai hannunta goshin ta yadda taji jikin rau daxafi yasa ta mike maxa wannan ciwon bana gida bane maxa mike Ali yakaiki asibiti ta xaro ido gami da mikewa nawarke umma kinwarke kamar ya bansanfa shiririta kintaba ganin inda mutun yaxauna da cuta tafice bari naje kar shima ya fita inda abinda Amra ta tsana bai wuce wata wurda ta hadata da yaya Ali ba dan bata debewa ta dadi.


Mami kinsanfa sauri nake kayi hakuri gadanga yanxu xata fito yakara duban agogonsa gami da xura hannu cikin aljihu ya ciro yan dubu dubu guda shida kibata kawai tahau taxi na makara ce maka akai bani da kudin bata ko kuwa motar hayace bansan ta hau inkuma ban isa insa kabane saika fada bahaka ne mami to maine yarinyarce yar rainin hankali kaga inbaxaka kaitaba ka iya tafiya yi hakuri ya fada atakaice gami da komawa mazauninsa mami ta mike tai sama inda dakin yar lelenta yake.


Haba Amra ashe ko tashi bakiyiba Alifa yanacan ke yake jira kinsan halinsa nifa mami nace miki na warke kinci gidanku nace maxa mike ta mike alangabe mami ta ruko hannunta sukayo waje kallo daya yai mata ya dauke kansa ganin yadda take wani shagwaggwabewa kamar wata jaririya yabashi haushi jiyake kamar yaje ya maketa ganin yadda mami duk tabi ta daga hankalinta.
Suna fitowa farfajiyar gidan ya galla mata harara dallah malama inxaki nutsu kinutsu bansan iskanci sanin yanxu ba mami ko dady masu tare mata yasa ta nutsu kai bakace Amra din da daxu tafiyama sai ana riketa tana wash wash da tafiya dakyar bace.



Haba yar gidan dady kidaure kisha maganin ta turo baki ni wallahi shiyasa banasan akaini asibiti yaya Habule dake gefe yace haba kanwis sha xan sai miki wannan abun naki wayon ta fada mami tace daurewa xakiyi ai daman shi magani badan dadi ake shansa ba kinga kar dadinki yadawo yaga kinrame baxaiji dadi ba sulaiman yashigo rike da waya ya mika mata ungo ta kara akunne hello dady ta fada cikin miryar shagwaba haba baby Amra yanxu yayanki yake fadan baki da lafiya ance allura kinki ga maganinma kinki sha indai kina so mushirya to kisha kinji ko ta hannun daman to dadi phone din yaushe xaka siyon kisha maganin indawo sai asiya to dady karka ji komi xan sha promise promise dad love u dad love u dear ta mikawa sulaiman wayar gami da watsa kwayoyin abaki ya Abdul ya mika mata ruwa a glass cup ta kurbi kadan gami da ya mitsa fuska gabaki daya suka saka tafi kaga yar gidan dadinta da maminta sauran nadare Ali da tun daxu ke xaune kujerar gefensu yanajin abinda suke baice tatafus ba inbanda wayarsa da yaketa dannawa mintina zuwa mintina yakan sakin murmushi alamar hirar tasu da kaltum tanai masa dadi sai yanxu yamike dalla malamai kun cikani da tafin banxa ai dakun kyaleta karta sha waxai ji badadi in cutar ta keantar dashi suna basu ce dashi uffannba ya gama banbaminsa ya bar fallon suka bishi da kallo kaji dashi inji sulaiman ashe mutin bai da aiki sai abota da fada Abdul yace ai matar yaya Ali ta banu da fada waya fadama ai iribsu rakumi da akalane suka saka dariya gaki daya mami tace maxa ku mike lokacin sallah yayi sukai waje yayin da Amra tai bayi....








Amra kinko yi sallah eh mami to maxa tashi ki karya time din shan maganinki ya kusa wayyo mami yanxufa sassafene wane safe gomafa ta wuce ni wallahi baccin nan be isheno ba kaji ja'irar yarinya yanxu da lpyr ki kalau aida kina sch ta ruko hannunta maxa ni fito kinga ansamu zazzabin ya tafi inkika ki shan maganin zai iya dawowa.



Dasauri ta mike zonan inazaki kuma baki gama cin a bincinba mami zuwa xan inkara tunawa yaya sulaiman sakona tai dariya se akace miki zama zai yaita jira harsaikin tashi ko to tun daxu ya fice oh my God na kwafsa kinga ba surutu zaki tsaya munba abinci zaki zauna kici ke nake jira zan shiga ciki.



Zaune take tana kallo taji ancillo mata leda adan tsorace ta dako yaya sulaiman tagani yana dariya matsora ciya kawai ta daka tsalle shiyasa nakesanka yaya baka mantuwa yai dariya ina zan mance da sakon yar kanwata ta bude kai amnan yaya nagode Allah ya saka saunawa zance ki dena godemun innai miki abu kai anman wannan yafi ma wanda nace maka kyau ta mike da gudu tai dakin mami tana kwala mata kira ke lpy kike kirana haka saikin kashen dodon kunne kingani yaya sulaiman ne ya kawon takarba tana dariya kai anman yayanki ya birgeki mami ki tayani godiya.



Kefa yar gata ce wallahi ji nake dama nice ke ko Allah maminki da dadinki nasanki yayyanki nasanki kowa ya kwaso alkairinsa naki ne tasa dariya Bilkisu ta kalleta kinsan Allah yayyanki ba birgeni musanman babban wanku yaya Ali ta turo baki tabdi mugun zakice ke nifa dabadan mami da dady ba ai kullun sai ya bugeni hakan ma sunai masa fada ya aka kaya aikedince wani xubin kinfiye abin haushi wallahi koni shagwabarki wataran sai a slow maryam tace kinji mu da bilki mutum bazai shana ba fada mata dai sis shiyasa nake sanki da yawa.



Kinsan mai ni wata alfarma zakimun ki taimaka ki danmun hanya yaya Ali yasoni hhhhh waima rufan asuri kar budurwarsa tajini yanada budurwa tanaso na wallahi nifa harba k'agu yai aure yabar mana gida ma huta ace dad yace anan zai zauna tab ai wallahi saina saka yace yabar gidan kinsan mgn ta yakeji shiyasa yaya Alin kekishi dani.





Mami wai yaushe dady zai dawo kya tambayeni keda kika san komi nasa kullun saiya cemun sai nanda sati ni haushina ma karmuyi candy bai gida haba aikema kinsan yanasane da ranar zai zo kodan gujema mitarki mami kema mai mita kike cemun tahawota da wasa nake yar gidan mami.



Ke ungo sauran kiyi
ta cikata da shirmen banxa kinji ko ta karba tabar gun dan sanin halinsa tana shiga daki tace aunty mukli yaushe xakixo daga can barin tace Amran mami kenan aina kusa zuwa na har abada anman kullum sai mami tace bakixo kin gaidata ba shikenan zanyi tunani shikenan ni zanxo intaho dake hooo amra sarkin rigima nidai zanzo to yaushe aisaidai ki ganni kawai to shikenan sunfi awa suna hira sannan sukai sallama ahankula take tafiya dan karta ganta harta shiga dakin ta aje masa wayar tana fitowa ta tsaya ta ajiyar zuciya alamar tasha saiji tai yace sai yanxu kika gama wayar tai saurin jiyowa tana rawar murya u a daman daman daman me kingama karar mun da kudi ce miki akai hako kudin nake yi hakuri yaya inbanyi mai kikeso nayi sai afkin kiyi barna ki bada hakuri bace mun dagani ni sunsun tabar gun hartakai kofa yace tsaya nashiga uku kije kitchen nakawo kifi mimun romonsa sauran kuma kisa asabe tayimun to yaya ta fice da sauri.




Ita tai komai na girkinki inka dauke dakan sakwara da asabe tayi hadadden farfesu tai masa da yaji kayan yaji sai lemon citta kasantuwar tasan yanasansa dining takai masa sannan tai dakinsa yaya angama ya fito falon dakin rike da waya ina yake yana dining haka nace miki acan zanci ayi hakuri tace gami da ficewa tana fitowa ta hango yaya sulaiman yana kokarin zubawa da gudu tai gun ta rike masa hannu rufan asiri na yaya Ali ne yasa dariya kincika tsoron yayan nan kaidai barshi danyafa dady da mami basa ban shine yaketa sani wahala ina mamin ta tafi gidan umma Balara haba koda naji nidai yanxu raina ya biya wallahi aikodai saidai kaje kasameshi yasanma wa rufan asiri tasa dariya ashe dik kanwar ja ce akwai a kitchen kaje ka xube au baxaki zubonba ni wallahi na gaji da yawa to kawo na tayaki kaimasa ya daukar mata saida sukaxo bakin kofa ya mika mata nagode tace tashiga sallama akasan makoshi ya amsa ta ajiye gashi yaya baice komaiba ta mike me kike nufi ni xanma xuba wayyo ta fada me kika ce bakomai tai saurin fade ta mika masa gashi ajiye nan ta ajiye tadan zauna adan kaikaice ya kalleta lafiya daman ko kana buk'atar wani abu no zaki iya tafiya Nagode dasauri tabar dakin karya tuna da wani abu











Sannu sis gaskiya na tausaya miki kaidai bari ni ba'abin inkai kararsa ba su kara tafiya ya hadan da duka ni wallahi dama kai mami ta fara haifa dana caba seka dunga zanenshi kodai cikin zamu koma ne tafara haifonin ta turo baki kajika yaya ana magana kana sako wasa yasa dariya.



Wallahi mami nai missing dinki yaushema na fitan balle kice kefa kike ta cewa intafi karnai dare Ali yashigo ah dole kice kinyi missing dina dodon naki yana gida kenan tai saurin tashi zaune daga kan cinyar mami ganin yadda Alin ke zabga mata harara kai narasa wane irin mutun ne baka da aiki sai harara barshi mami idon ya fado ai ke nikike fadawa haka sa'anki ne ni yi hakuri tace ta faki idon mami ta mai gwalo mami kina ganinta ko me kuma nagani sarkin mita Allah mami yarinyar nan ta raina ni saita dinga mun abinda taga dama innai mgn ace na fiye fada aikaidinne komai fada me yasa sulaiman bai cewa ta raina shi tun ana tsoronka har sai an dena ya kada kai kawai ya bar gun.




Tsaki yaja ni wallahi na gaji da jiran yarinyar nan kullum saita makarar dani banda abin Ali kwanan nan zata gama makarantar nan se ka dena kaita ina komai sulaiman ke mata kai makarantar ma kana mita ina yanxu waec suke ace saida aski yaxo gaban goshi zaka kosa kadaure ka karasa ladanka anman mami kina sane da bata makara a islamiyya bata makara dayake sulaiman ke kaita hakuri zakai da'ace zaka daure ka dena wannan fadan zakaga kun shirya tana makarane dan batasan kake kaita kinji ko mami kemafa dakanki kin fada baso na take ba rai dariya hoo Aliyu kaima kasan tana karama kai tafi so halinka ne bata so tana fitowa tace mami sena dawo to yar maminta Allah ya bada sa'a tace amin suka wuce.



Wai dagaske kike yayanki yanada budurwa bilki kenan inma baki yadda ba to wallahi kixo jibi nakesan zuwa gaida ta semuje bilki tace Allah sarki ni nafa tausayama kaina nikam nai miki murna da bake wannan dan xafin zai aurava ni murnata ma ya barmana gida uhum bazaki gane bane
Kawai anman dai zanje dan ganin wace me sa'arce.

A gidansu muklisa budurwar Ali an karbi Amra da kawarta hannu bibiyu da yake ba bakuwa bace tsaraba kuwa da zasu tawo ba'a magana ke nifa inbanda so sone Allah banga me ya Ali zaida wannan ba Amra ta hade rai banfa san cin fuska kema kinsan ta ko'ina aunty mukli tayi ga mutunci sankowa kin wanda ya rasa kedai kice kina kishi kawai haba yarinya kema kinsan na wuce kishi da wannan ohoo dai kyaji dashi.



Kinsan me mami sai kin fada aini shagali goma da ashirin gana bikin yaya gana candy ahlallai kice tarihi zaki kafa tai dariya ai wani abun sai ranar Allah dai yasa zamu gani amin Amratuna kaji mami bashi ne dan fariba ko kunya bakiji ba ungo nan ta watsa mata dakuwa yarinya sai zakulo zance tasa dariya aina girma candy zanyi ah lallai kin girma ni kike fadawa haka ko tai sama tana dariya.



Motar sa data hango yasa ta cewa na shi na salim dake gefe yai saurin kallon gefe mts yasaki karamin tsaki yasan yanxu wannan yayan nata zai katse musu jin dadi yadda ya hade rai yakara bata tsoro sannu da zuwa yaya yawwa ya fada me kike anan gurin ba komi ta fada to maza wuce gida tai ciki da sauri tana kuka kai kuma saunawa zan ce maka karna kara ganinka anan ba yanxu xanu aurar da ita ba to yaya ya fada yai gun motarsa.




Towo yar gidan mami keda wa mami ba yaya bane muna hira da salim yazo ya koroni shima ya koreshi to yo hakuri zaizo yasame ni. Yashigo yana huci mami sannu da gida bata amsa va tace Aliyu wai yaushe kakeson indena maka magana kan Amra takurar dakake mata tai yawa karka manta fa banazatai candy karka kara korar mata samari to mami zan kiyaye yai ciki yana huci gami da hararar amrar





Dad nai missing dinka da yawa yai dariya ai nima nayi missing diyar tawa dad kasan ka dawo adedai ko eh mn gobe be final pape dinmu ai nasani ban mance shiyasa nadawo yau ayi komai a idona har suka isa gida suna hira me dadi dan ita da mami kawai suka samu damar taroshi.




Agurin yaye su Amra tana daya daga cikin dalibai da suka sami kyautuk tuka na mai kokari tsafta da girmama malamai aikuwa dady da mami sai murna suke diyarsa ta zamo abar alfahari hotuna haka akai tayi kyautuktuka kam tasamesu daga gurin dangi da yayyenta suma kansu murna suke danma anbar nata taron sai ta hada da bikin yayanta anman hakan besa yan uwa sun zozzoba.


Yau za'a kai kayan lefen Ali kana ganinsa kaga ango yadda yaketa washe baki sai tsokanarsa ake kai banda abinka kafin azo daurin aure har kafara shinning irin na angwaye dayake bai cika magana sai dai kawai murmushin sati hudu akasa bikin dan haka kowanne bangare wato amarya d ango shiri kawai suke .



Yadda Amra ke zagewa kai kace itace amaryar komai ta bukata bata ake gyaran jiki takanas taje tai kyau sosai da biyu take wannan murnar bikin babban yaya sannan bikin su na farko gashi zai bar musu gida acewarta shanawa kuma ao ba kama hannun yaro.



Biki kam ya gabato dan yau ake Diner kaf kawayenta Amra ta gayyacesu dan itama yau take party dinta na candy biki ne irin na kasaita bikin girma da girma kudi kam an kashesu.



Yau take asabar yaushe ranar daurin aure Amra nacan na kwasar baccinta dan tace ita sai sha daya zata shirya ango yai kyau sosai yaci babbar riga milk komai milk kwarjininsa ya kara fitowa sosai .

Waliyin amarya yace eh kunji yadda akace waliyyin ango yace to gaskiya saidai ku tsaya ayi magana da ango abinda yace to to aishike nan bari akirashi awaya ga mamakin Ali wayar uncle dinsa ce ke kiransa aransa yace towo lpy asaninsa uncle yana gun daurin aure kaji waliyyan matarka sunce zaka bar yarsu zuwa Malaysia dan karo karatu shiyasa nace abari kar adaura inji ta bakinka Ali yace ina ni bamu taba batun dasuba kenan baka amin ce ba eh kawu nima dai hk nagani ti kunji yace be amince ba to falillahi hamdan sai afasa aure afasa kuma eh to kutsaya in tuntubi iyayan yaro ko zasi saka ya yadda nan ya fito yasamu baban Alin ya fada masa shi kuna yace bari suyi shawara fa matarsa ya fita daga baya ya shigo yake cemasa afasa daurawa da mukli anman aure babi fashi.


Abinda kunnuwansa suka jiyo masa yasa ya kara matsawa kusa bai yadda da abinda yaji ba kai Abdul wai me marokannan ke cewa cewa suke Alhamdulillahi an daura auren *Amratu* da angonta *Aliyu*
What dagaske kunnena dedai yajiyo nima dai jinake shirme suke muje mu jiyo suka kutsa cikin jama'a duk inda sikai maroka na biye dasu kaga ango gun amratu bai san sa'adda ya doka musu tsawa pls ku kyaleni haka kun isheni iyye yai cikin masallaci yana hango kawunsa yai gunsa kawu wai da wa aka dauran aure ya washe baki da Amratu mana what waje yai Abdul yabi bayansa yasamu waje ya rafka tagumi Abdul yace abinnan fa da daure kai ina wa ya taba auren kanwa inaji dai ba amra kanwarka suke nufiba shi gabaki daya baijin me yake cewa ba abinda yake tunawa sai Alhamdulillahi an daura auren Amra da .......


Alhamdulillah an daura auran Amra da Aliyu kalman da yake ta maimaitawa knan tabbas in abun da yaji gsky ne xaifi jin dadin inama ace mafarki yake Muhammad ne ya dafa shi haba Aliyu mene haka karka sa sauran jama'a su zaci wani abun yadago idonsa wanda yakada yai jawur pls muhd kafadan gaskiya bacci nake ko idona biyu kaga dan Allah ka tashi mu shiga jama'a yaufa ranar farin ciki ce agunka haba muhd taya zaka kira wannan ranar ta farinciki eh kai agunka ranar bakin ciki ce anman kowa yana kallon ta amatsayin ranarka ta farinciki be a man pls kadaure haka yai tabashi baki har yadan saki ransa suka shiga jama'a yake kawai yake dan shi kadai yasan abinda yakeji aransa.




Amra na kwance kamar kamar a mafarki taji wayanta na ringing xumbur ta tashi baccin me dadi da takeyi daddyne ya kirata yace ynxun nan yake son ganinta a falonsa saida gabanta ya bada dam a xuciyarta tana fadi meya faru Daddy kson ganina ynxun gashi ana biki ta bawa kanta amsa bb komai may be yanason ya sata abune tunda mummy mutane sunyi mata yawa da haka ta fito falon tunda tafito mutane ke rangada buda amarya ansha kamshi bata kawo komai aranta ba dan tunda aka fara bikin ma wasu kafi amarya suke kiranta tai bangaren dady.


Shi kadai ta tarar adakin kamar yadda ta zata ta russuna ta gaidashi ya amsa cikin sakin fuska badai sai yanxu autan tawa ta tashi ba tai dariya ai nai sallah ok daman magana nakesan muyu ta fahinta to dady ta samu guri ta zauna.


Amrah ya fada yanayin yadda ya anbaci sunan da iya saninta bai taba kiranta da shi ba yasa tai saurin dagowa na'am dady ni waye agurinki tace baba na ne ya kada kai yawwa daman alfarma na kiraki kimun tai saurin dagowa haba dady kadena cewa alfarma ka wuce ta aguna yafi kace umarni ashirye nake nabi duk abinda kace yai dan guntun murmushi irin nasu na manya kinsan yau ake daura auren yayanki ko ta daga kai yace yawwa adazu agun daurin auren andan samu matsala iyayen yarinyar sun bada sharadi mu kuma muka ga da cutarwa to hakan yasanya aka fasa auran tai saurin dagowa yace eh an fasa auren da muklisan hakan yasa muka yanke shawarar daura auranku keda Alin zunbur ta mike dady dan Allah karkace ba mafarki nakebe kafin yace wani abu tayi kasa yaraf inda yai dedai da shigowar mami batasan sa'adda ta watsar da ture dinba tai kanta tana jijjigata cikin kuka.



*Tuna Baya*

Alhaji muktar shine asalin sunan dady wanda yake haifaffen garin kano unguwar galadanci shine dana uku agidansu mahaifinsa wanda yake malamine ajami'ar bayero yayin da mahaifiyarsa take ma'aikaciyar jinya su su shida iyayaensu suka haifa yanayin yadda iyayensu suka tsara musu rayuwa yanayine mai ban sha'awa da birgewa ga kowa.

Lokacin da muktar ya kammala secondry dinsa ne ya wuce
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment