Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba ko?, domin kin san a dazun nan da ace ya gane ni ba mijinki bane yana iya daure mu da igiyar dake jikinmu wace sai mun tsufa a gidan yari ba wanda ya isa ya fitar da mu aman na jajirce na ce ke matata ce domin idan na bari ya tafi da ke na shiga ukuna"

Turawar da suke yana turowa ta fara sasautawa tana kallon yayarta da kuma kofar jin furucin bakinsa

Yayarta ta rage murya kasa kasa sosai ta ce" Kudinsa kika sato ne yau kuma SHUWWAR ? Waye shi mahaukaci kika janyo mana cikin gidan bayan kin san jiya na kori baba mai gadi?"

Kai ta girgiza itama ta rage murya sosai tana fadin" Ba mahaukaci bane, kudin kuma ba nasa bane na babansa ne, dan gidan mai shinkafa ne fa, na je gidan ne na masa barazana ya ban jakar kudin nan shine ya turon yaronsa ya kwace bayan inaga million goma sha uku ce a cikin jakar cen aunty"

Ido yayar tata ta zarro tana furta" Million nawa?"

Ta sake maimaita mata adadin kudin, hakan ya saka yayarta gannin a kan kudin nan ko trela ce tana iya tarba, kai a kan kudin nan ko karo ne da jirgi zata iya yi
Wata zuciya ta ciyota ta samu kanta da dakatar da Zahra'u dake sake dannewa kar ya shigo ta ja SHUWWAR ta mayar da ita bayanta da jakar suka bashi dama ya bude kofar suka bayana a gabansa sun yi cirko cirko da su

NAHIDT ta sake aro fuska irin ta rashin mutunci ta ce" Kai me kake so a nan ne? Nice nan uwarta idan wani abin ne bismillah ina sauraronka ka fara da ni!"

Wace ta kirayi kanta da maman SHUWWAR ya karewa kallo yana fadin" Mamanta kuma?"

Ta sake hade girar sama da ta kasa tana fadin" Eh da matsala ne a haka?"

Tsaki SHUWAR ta ja tana fadin" Dan Allah ki daina cewa mamana ce ke duba fa ki ga kalar gashin da kike da a saman kanki wa kike so ya yarda ? Ka ga yayata ce fada mata me na maka kake biye da ni !"

Murmushi ya sake yana kallon yadda suke shirin kaurewa da wani fada a tsakaninsu ya budi baki yana fadin" Kun ga, dan Allah ku yi hakuri ba maganar kudi ba ya kawo ni nan, haka kuma ba wani aiken babana da zan yi, abinda nake son sani, abinda ya fi daga min hankali a kan SHUWWAR , dan Allah SHUWWAR a shagon babanmu ake maganar budurwarsa harma aka jadadan an daura masa aure da wata mai sunna irin haka jiya, dan Allah, dan annabi shine nake so ki fadan cewa ba ke bace , domin idan kece na shiga uku na lalace"

Fauziya ce ta iya budar bakinta wajen fadin" Da aka yi me kuma?"

Kallon Fauziya ya yi yana fadin" Baiwar Allah Idan haka ne hakan na nufin wannan matar da kike gani matar ubana ce fa, kuma ni kuma na kamu da sonta bilhaki bilahilazi"

NAHIDT ta kalle shi da sauri sai kuma ta kalli SHUWAR da ta saki baki da hanci tana kallonsa itama

NAHIDT ta ce" Ka ga, ina ga mu shige ciki mana wannan maganar ai ba ta a yita a waje bace ka ji? Bismillah"

SHUWWAR ta ce" wani irin ya shigo daga ciki kuma kamar kina son amsar maganarsa a bayane bayan ni ba bariki nake aikatawa ba kema sheda ce? Ka ga bawan Allah eh nice aka dauran aure da babanka jiyan nan"

Da sauri NAHIDT ta ce" Eh kuma ya sake ki ba tare da ya kwonta auren ba ko dan an ce ni yar bariki ce, ko akoy abinda ya shiga tsakaninki da mai shinkafa ne bani da labari?"

Kai SHUWWAR ta dafe jikinta ya fara mugun yin sanyi ta ce" Aunty, ko dai so kike ki nunan mu je ciki da shi ta yadda zamu tatse shi kudinsa kamar yadda kike gagawar kawowa tunaninki? Kar ki ce min bayan halin rayuwar da muke ciki kin manta cewar D'a baya auren matar ubansa koda kasa ta binni idonsa? Da ace ba'a dauran aure da mai shinkafa bane ake iya duban wani abu makamancin haka, aman aunty so kike mu fara shiga hurumin ubangijinmu kuma?"

"Kin ga SHUWWAR kar ki sakani a uku bayan wanda nake ciki mana, ni bana nufin aure ya shiga tsakaninki da shi dan Allah aman kuma ya shigo cikinma ai ba laifi bane ko?" NAHIDT ta fada tana kallonta da tsatsareta da manyan idannuwanta

SHUWWAR ta girgiza kanta tana juyawa wajen ABDUL Mutalab da ya kai duke a wajen ya kurawa waje daya ido a sanyaye ta ce" Ka yi hakuri , ban san sunnanka bama, ka ga du iskancina bana son taka dokar ubangijna,, domin na yarda da mutuwa kuma na yarda da tsayuwa a gaban Allah gobe kiyama, shi yasa nake kiyayewa, nake matukar kiyayewa dan da tarin laifukana idan na sake bayana da irin wannan wanda nake tunanin cetonsama zan iya rasawa watau annabi Muhammad sallalahu alaihi wa salam"

Ta sake sauke ajiyar Zuciya tana fadin" ka ga sakina ya yi a cikin motarsa bayan ya gama zazagin yayata da sunnan karuwa, shi yasa na tarda shi gidansa nima, idan dan wannan ne ka barshi ya rama abinsa, aman ni babu wani abu da zai iya shiga tsakanina da d'a namijin da ba muharamina ba da ya wuce aure, AURE nake so na yi, so nake na yi aure mai daraja na raya sunnar ma'aiki, ina so idan na mutu mijina ya salaci gawata, ina so na haihu na samu ahali irin na kowa, ina so na zauna a kasata duk rintsi na kula da y'ayana na basu tarbiya, ina so na rayu da su har karshen rayuwata, kai a ganninka idan na fara biye biyen y'ayan mazan da suka sakeni na nemi Allah ya zuba ruwan sanyi a saman ALKALAMIN KADARRATA kuwa?, Zaman lafia nake nema, bana neman idasa lalacewa"

Daga haka SHUWWAR ta yi shigewarta ciki da jakar kudinta a hannunta ta bar yayarta da binta da kallo baki a sake tamkar tashar anguwa uku sannan ta maido dubanta kansa da sauri jin wata murya garjejiya ya bude yana fashewa da kuka

Ido suka zarro daga ita har Fauziyar sunna kallonsa yana zaune dangalgal yana fadin" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, leke leken abanmu sai da ya kaishi ya leko wannan yarinyar kuma ya aureta dan wulakanci sannan ya saketa? Gashi Allah zai kama shi a kaina bayan ni kadai Allah ya bashi d'a namiji na kamu da son abinda yake haramun a gareni koda ya bar duniya? Innalilahi wa inna ilaihi raj'une yanzu yanzu fa na ganta a gidanmu idona ya rufe a kanta ashe haramun dita ce Ita din? Aunty kun tabata Shuwwar ta haramta a gareni kuwa? babu irin sabanin bakin nan da malamai kan yi a kan wasu fatawowin ? Kun tabata harshensu ya zo daya a kan wannan lamarin? Ba abinda ya shiga tsakaninsu fa"

Kallon junna suka sake yi a karro na ba adadi suka kuma kallonsa, gannin tsakaninsa da Allah kukansa yake ya saka aunty cike da tausayawa ta ce" Ka ga, ka daina kukan nan hakanan, ka tashi ka shigo ka zauna har a ga yaya garin idan kana iya fita sai ka tafi gida, kar ka damu Allah zai daidaita zamu tambayi malaman mu ji ka ji?"

Kai ya ringa gyadawa aman bai shiga ba ya sheda mata yana iya yawo shi dan takardarsa ta likita da kuma wada aka basu yanzun a hannunsa take

Sunna tsaye sai da ya fita sannan suka kalli junna Fauziya na fadin" Yaya zaki ce masa ya dawo bayan kin san wannan abun haramun ne kuma kin san ta san haramun ne ko daureta muka yi muka kaita zata kunto kanta ta dawo ta same mu, balema ta yaya hakan zai iya faruwa?"

NAHIDT ta shiga takawa dan ta he ta sanyo motar gida sannan au rufe tana fadin" Ke baki ga zai sume mana ba a nan? Ni ba dan hakan zai gyaru ba na ce zamu tambayi malamai kuma ma ai ilimi fadi gareshi, ko waye kai ba zaka ce ka san komai ba a kan lamarin, idan fa akoy wata aya da ta halata hakan? Bayan wannan kawai dan dai gani na yi idan ya sume mana ina zamu iya shiga da shi ne a haka"

Ita dai tana biye da ita ta bude mata gidan da kyau ta sanyo motar ta rufe suka rurufe ko'ina suka nufin falon

Sunna shiga Fauziya ta sake ja ta tsaya ta ce" Kin ga, kin sha saka kila wa kala a kan maganarki ki dawo kanta, koda hakan halak ne ki ajiye maganar dan gidan mai shinkafa, kin ga mutun ne mai iyali, y'ayansa yawa ne da su a duniya, koda auren muka je wasu suka daura masu mun siyar mata walahar rayuwa, ba zasu taba karbarta ba koda bayan ran mahaifinsu, maganin kar a yi karma a fara , ki ajiye kwadayin hakan gefe mu fuskanci reality da sauki a garemu baki dayanmu"

NAHIDT ta ce" to uwata, na ce to uwata Fauziya,, na kula du kun daukeni a wata dakikiya ko wata kura, na ce maku na bar maganar ko?"

Fauziya ta tabe baki ta yi gaba a ranta tana ayana' da ace ban san ko ke wacece a kan maganar son farantawa IBTISAM bane da sai ki fadi haka, ke burinki wani wanda zai sota a haukace kamar wannan saurayin, wanda koda ya ji menene sana'armu ba zai gujeta ba ki aura masa ita, bayan idan har muka yi haukan kaita gidansu yaron nan soyayar sai ta dawo ta zama kiyayar da kare ba zai iya sinsinawa ba, baganin kar a yi kar a fara'

__________________________________

Aikin da suka wuni yi, suka kuma raba dare a kai ya saka shi magana yana lumshe ido tamkar wanda ya yi marisa
Wayar dake kange a kunnensa ya sake saurarawa yana jin muryar mahaifiyarsa dake magana cikin hawaye wanda hakan ne ya saka shi ajiye komai ya masu alamu ya shiga ciki

A hankali ya kai zaune bakin gadonsa muryarsa a shake dan ya wuni yana ihu da bakinsa ya ce" Kuka kike yi?"

Shiru ta yi tana hadiye kukan dake tukota hakan ya saka shi fadin" Mamah, kin san irin ilar kukanki a kaina fa, saboda Allah dan kawai na saki mace sai ki yi kuka?"

Yanzun kasa rike kukan ta yi tana fadin" Kawai ne? Sakin macen na ce kawai ne? Ana cewa kai ta haka hau ya shigeka auri saki shin gaskiya ne? Yaya kake so rayuwa da mace wace zata zamto ta amsa dukan komai a kan daidai bayan ita din da kanta an hakiceta ne da kashin hakarkarinka dake tankwashe? MUHAY daga kara siga a tea?"

A hankali ya ringa murza hannunsa ya ce" Ba iya shine damuwar ba "

Mamansa ta ce" Mecece damuwar?"

A hankali ya ce" Nikakiyar kwalba ce ta zuba mij a tea ba siga bane ya yi yawa"

Sai da mahaifiyarsa ta mije tsaye a zabure tana fitar da idannuwanta ta ce" Ka ga, kar ka fadi haka dan zama da ita ya fice maka a rai, ka riga ka yi mata saki uku ba dawo da ita zan yi ba, fada ne nake maka dan ka gyara halinka dan bana so gobe ka sake sakin wata kai tsaye daga ta yi dan laifi, domin na gaji da irgen matan da ake yi maka MUHAY"

A hankali ya furta " Toh ba zan sake ba"

Ido ta kikiftaa tana kaiwa wajen madubin dakintaa ta ce" Wani irin toh, ba toh ba zaka ce min, ka fada min sone take ta kashe min kai, ka fada min yadda abin ya faru, yaya aka yi ka sani? Me ka yi mata? Wani ne ya aikota? Tun yaushe ta fara zuba maka kwalba a tea? Yaya aka yi ka gane kwalba ce ta zuba maka a tea? Shine suka zo suka nemi da na yi maka magana ita da mamanta? Ka fada min ni kuma sai na yi shara'a da su domin ba zan taba yarda da wannan ba"

Idannuwansa da ya rintse gam dan da karfi maman nasa ke magana ga dukan alamu kai kawo take yi ranta ya yi kololuwar bacin nan tana jero tambayoyin da ya rantse da Allah a yanzu dai da ya wuni bakinsa na haikar magana idan ya ce amsoshinsu zai bata sai an kwontar da shi a gadon asibiti koda baya so ya saku kansa da bude bakinsa da kyar ya ce" Mama kar ki shiga cikin gwagwarmayata da magautana, ni na tabata idan ba *ALKALAMIN KADARRATA* ne ya zo da zanen sai sun cin min ba sai dai su yi su gaji, abinda ba zan iya dauka ba shine a fara hakonki, inda kike din nan hankalina a kwonce yake, so plz ki huta mamanah"

Kasa furta komai ta yi a tsayen da take domin ya kashe kiran ne

Tana kokarin maida masa da wani kiran mesage ya shigo kamar haka" Dan Allah ki yafe min , kukan nan da kika yi kuma ki saka min albarka ki share hawayenki, zan zo gobe tare da Shugaaban kasa.......mamah i love you"

Daga haka ya kashe wayar yana saje mayar da idannuwansa ya rintse ya kwontar da kansa a baya yana jin kansa na sake sarra masa, gaba daya duniya ita daya ke masa irin haka abinta a lokacin da ta ga dama abinta, yanzun babar rigimar da yake tunanin mai kwontar masa da tarzomar hakan sai Allah SHine maganar kaurowarsa garin nan da aiki har na tsayin shekara biyar, yaya zata yarda da wannan kudiri nasa? Anya zata amince masa kuwa?........









I don't know oh LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN MUHAY😍





Shin yaya wannan salon? Yana shiga cikin zuciyarku kuwa?

Maza garzayo ki samu naki a kan farashi mai sauki yar uwa NAIRA DARI UKU NE KACAL TA ASUSUN BANKINA, KU TUNTUMBENI TA NUMBER WAYANA KAMAR HAKA +22793811618 "na'💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥


*The Hero writer*


*SAJIDA*


_Bismillahir rahamanir rahim_


PAGE:. 6️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*






*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*


*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*



*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*



*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*





Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.


*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618


Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰


Taro ne aka gabatar mai sunna taro wanda sai da yama ta yi aka ba al'uma damar fitowa ta kafofin sada labarai

A cikin wa'inda suka dauki wanka suka fito cikin gari harda SHUWWAR da yan uwanta
Kowace ta nufi hanyarta da irin kudirin dake cikin zuciyarta a lokacin da mutane suka fara watsewa a wajen taron

A hankali SHUWWAR ta gama yarda da abinda zuciyarta ta saka mata kafin ta juyo ta sauke dubanta a saman kwaltar tana karewa dukan motocin dake wucewa kallo

Cen ta hangi alamu na mota mai motsi na karasowa hanyar da take tsaye hakan ya sakata Sauke ajiyar zuciya a hankali ta saka kafarta ta shiga tsalakawa zuciyarta na dokawa tana tsale cike da tsoron kasadar da zata yi da tunanin Allah ya sa ta yi dace a kudurinta

Ido ta rintse sakamakon horn din da aka dana mata mai kukan gaske sannan aka danno kai kanta da tunanin ai zata kauce tunda shigarta ta farar abaya batai kama da mahaukaciya ce ita ba bale kuma yannayin fuskarta bai nuna makauniya bace ita bale a yi tunanin bata gani ba haka kuma bata ji ba Horn din da ake yi mata

Sai dai direban ya makaro a lokacin da ya kunnace mata wuri ne ya iya take birkin gaba daya hakan ya saka motar bada wani karra kuuuuuuuuuuuuuuuuu sannan ta daki kafafuwanta a da gasken gaske kafin take tsayawa inda Shuwwar ta yi tangal tangal ta saka ihu tana sakin jakarta da sabuwar takardar shedar yar kasa ce ita da ta saje domin wancen din ta nemeta ta rasa kadai a ciki ta fadi kasa sannan ta bita ta zube tana dauke numfashi a mugun tsorace domin bata taba tunanin wannan matukin motar zai iya sakin kansa har ya zo ya bigeta ba, koma waye wannan an yi dan airs walahi

Haya haya haya, kafin ka ce meye wannan, nan da nan wajen neman dinkewa yake yi da al'uma, hakan ya sa sojoji biyun da suka zo da gagawa bada damar yan uwansu su karaso su talafa masu dan a tsagaita cinkushewar hanyar domin Sir bai jima da keta hazo ba, a awa dayan da zai yi kuma a sararin samaniya bata cika bale ace ya sauka garin da zai je, karma ace har ya saukan ba zai iya dawowa da wuri wuri ba balema dawowar tasa ba wani abu ne mai wahala ba idan ya ji ana bukatar ya dawo din zai dawo ne yanzu yanzu ba tare da bata lokaci ba, gashi wanda yake cikin motarma baba ne na polisawa tare da masu bashi tsaro zai nufi gida ne hakan ya faru

Alamu take hange, kuma take ji a kunnayanta masu nuni da kamar wannan motar da ta kadeta ta soja ce

A lokacin da hannu ya kawo dan juyar da ita domin ana yi mata magana ne kan tana farke kuwa? Ta yi shiru, ta yi bakam tana saurare har sai da ta ga alamun hannu zai taba jikinta ta dago da sauri tana dan ja baya hadi da kurawa kakin jikinsa bakake irin na police ido lokaci daya tana fadin" Ka ga kar ka taba ni, ina wanda ya kade ni ne?"

Datijon da ya zubawa kyakyawar halitar ido ya yi dan murmushi yana fadin" Motocina ne suka samu hadari da ke yan mata, ina fatan baki raunata ba? Bismillah kawo hannunki na taimaka maki ki tashi"

Wani shegen takaici mai zafin gaske ne ya taso mata a cen kasan zuciyarta, yanzun du irin wannan wahalar da kasadar da ta yi da rayuwarta dama da mai kaki zasu hade ? Gaba daya sai ta ji hakan da ta yi bashi da anfani, wannan police din kuwa take ji a kasan zuciyarta da idan ta zage shi zata wanye lafia da ta aikata ta ji sanyi a kasan zuciyar tata

Da baya da baya ta sake ja tana girgiza kanta hadi da fadin" Ba sai ka kama ni ba zan iya tashi "

Tana fada ne tana son kama motarsa ta mike da kyar tana sauke mawuyaciyar ajiyar zuciya ta juya tana faman fadin" Ba sai kun rike ni ba ban ji rauni ba, aa ba sai kun rike ni ba ban ji ciwo ba....." A haka har ta samu ta ratsa mutanen ta wuce tana jin takaicin mai kaki a zuciyarta, ta tsani soja, soja bai yi mata ba sam, tana da dalilai na tsanar soja a rayuwa, soja yana da baban kamasho a cikin zanen kadarta!


Da kyar ta samu ta yi wata kwana ta zauna jikin garu tana janyo kafafuwanta jikinta hadi da sauke nanauyar ajiyar zuciya a bayane ta ja tsaki tana bude hannunta zata fara yin magana ta ji wata murya mai laushi an yi mata salama lokaci daya mai muryar kuma ya rage tsayinsa yana kallon kafarta da ta janye abin rigarta sama kadan har zuwa idon sawun kafar tata
A hankali ya ce" Bai dace ki zauna a nan yar kyakyawa ba bayan motar soja ce ta kade ki? Na so ki ba sojan cen wahala ki saka shi daukan ki da kai ki asibiti , ki langwabe ki saka shi daukan ki a hannunsa ba a cikin kujerar tuki ba, shima mu saka shi yin gumi kamar yadda yake son gannin ya wahalar da mu a duniya......ko kina son ce min bakya sha'awar ganninsa yana tafe yana share gumi a gaban goshinsa?"

Tunda ya dukan bata dago ta dube shi ba sai yanzu da ya gama karewa soja wulakanci
Da murmushin da ya subuce mata ta dube shi tana shirin yin wata maganar ya yi gagawar fadin" Wauh, masha Allah, ur splendid yar budurwa , kin ga I'm Sudais ke fa?, Na san sunnanki ba zai wuce Zahra'u ba domin kin hasken idannuna tunda na kyalo ki a wajen nan a zaune"

Kanta ta dan cire a kansa a kasan zuciyata tana ayana' Ba dai surutu ba shi wannan'
A bayane kuma sai ta furta" Am SHUWWAR "

" SHUWWAR, unik, magnifique, SHUWWAR, ko zaki taimaka min na samu na kaiki likita ya duba min kafarkin nan da kika dingiso da ita daga cen har zuwa nan?"

Watau ba zaku gane ba, a duniyar SHUWWAR tana matukar kaunar ta ga ana caring dinta, idan ta ga mutun ya bayana a gareta da wannan espri din, gaba daya tafia yake yi da imaninta, 'shin idanma ba maza ba akoy abinda ya kai ku bi maganar Allah ne a kan matayenku? Ku kula da mu, domin mu din halita ne masu rauni mana.....ama da yake kawunanku na daidai da jikinku sai kunna daga mana kai' ta samu kanta da ayanawa sannan ta wani shagwabe fuska irin an samu abinda ake so din nan ta mula kai a hankali ta ce" Ba zan iya tashi ba, kuma gashi bana kama hannun namijin da ba muharamina ba"

Murmushi ya sake yi yana karra kallon yarinyar a kasan zuciyarsa yana ayana' Tabas wannan ta yi, abana da yake faman na fitar da mace gata Allah ya bani sai hankalinsa ya kwonta, ka ji malan bama zata iya bari na tabata ba, a gaban idannuwana kuma ta ki police din cen ya tabata, wannan ita zata kasance uwar y'ayana, ta zamto a kilace a fadata, na juya abina son raina domin da ganni wannan irinsu ne basu da ummm basu da ummm, ni dama burina na zamto sarki a cikin gidana , idan mu ba sarakai bane a duniya ai dole mu mulki mace ko

1 Comments On ALKALAMIN KADDARATA
avatar
deejah-danjumah

1 year ago

Reply

thanks

Please Login or Register in order to submit comment