Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

🌹 SHEIKH IMAM🌹


By

YAR LELEN ROYAL STAR.


Page......1


Yammacin Juma'a ya kasance yammaci Mai cike da ni'ima da albarka Mai tarin yawa, ga samaniya ta hada wani irin hadari, Wanda ya saukar da daddar iska mai haɗe da kamshin kasa, da wani Yana yi na musamman Mai saukar da nishadi a cikin zuciya....


Wasu kyawawan motoci ne kirar Audi A6 e-tron, suka tsaya a gefen titi, kusa da wasu mutane masu gajiyayyen karfi da nakasassu, bude motoci aka shiga yi ana fitowa, wasu samari ne da a qalla zasu iya yin shekara Ashirin da biyar² , kyawawan ne sosai masu duhun launin fata. Motar da take tsiyarsu aka bude, a kalla an dauki fiye da minti ukku da bude motar amma wanda yake ciki bai samu zarafin fitowa ba.


Daya daga cikin samari ne ya Dan leqa kansa, magana yay da na cikin motar kafin ya koma gefe ya tsaya, ba afi 1 minutes da komawarsa gefe ba na cikin motar ya zuro wasu kyawawan fararen kafafu masu dauke da wani half cover Mai masifar kyau da yay dai² da karamar kafar da a kallo daya ba zaka tab'a yarda ta namiji bace, saboda yarda take samun kula daga mamallakinta, kyakyawar fatarsa na karewa kallo ta gurin da wandonsa bai karasa rufewa ba, Wanda kallo daya zakawa kafafun kasan mai su kwankwadi Sunnah ya k'oshi, saboda yarda yanayin wandon yake , bak'ar gargasa ce ta like farar fatarsa, wanda kallo daya ba sai ka Kara ba kasan mamallakin jikin yana da baiwar gashi irin mai zaro² din nan bak'i sid'ik gwanin sha'awa.


Ya dan jima da zaro k'afafunsa kafin ya fito da gangar jikinsa, sanye yake cikin dakakkiyar shadda light blue , mai maiko sai shek'i take, an masa dinkin babbar riga da yar ciki, kansa sanye da hula tangaram mai kyawun gaske wadda ta kasance dark blue da yarfin light blue,
Cikin natsuwa ya juyo gurin mutanen da suke gurin, maa sha Allah, kyakyawa ne aji na musamman, ya kasance kyakyawan da ba zai fadu ba sai dai kawai a fasaltasa, fari ne sosai Wanda farinsa har wani tsabi² yake, yana da kyawawan idanu manya da suka kasance light blue masu matukar kama da na mage, Yana da wadatacciyar gashin gira Mai yawan gaske da ta kasance bak'a, yana da dogon hanci Mai dauke da madaidaitan kofofi masu kyau da tsari, sai bakinsa Dan karami da shi, yana da saje sai kuma gemu Mai yawan gaske, wanda da ka kalla kasan ana matukar ji da shi, don sai wani shining yake gashi gazar², sumar kansa bak'a ce sosai, ta saukar masa har kusan kafada , kallo daya zaka masa k'asan cewar shi din half-caste ne saboda tsananin kyansa, uwa uba kwarjini da wani irin cikar sati da yake da shi, ga kuma wanka ga kamshin turaren Viktor &Rolf Flowerbomb Haute couture , Mai sanyi da sanya natsuwa da yake fitarwa .


Cikin hausarsa da bata gama dai²tuwa ba suka fara gaisawa da mutane, mutane sai matsowa suke suna mika masa hannu , kowa so yake ya mika masa hannu ya tab'asa domin k'afa tarihi, ba tare da kyama ki wulakancin ba yake mikawa duk Wanda ya mika masa hannu, hannu su gaisa, bayan gama gaisuwa, ya fara rarraba musu abubuwan da yake bin gajiyayyu da marasa karfi yana rarraba musu, duk yawan mutanen gurin sai da suka bawa kowa kafin suka koma mota suka ci gaba da tafiya.


Kai tsaye LNC Estate suka nufa, tafiya suke cikin Estate din, suna wuce kyawawan gidaje masu kyawun gaske, sun jima suna tafiya cikin estate din, shi kuma idanunsa na kan window motar yana kallon tsarin gurin .


Basu tsaya ba sai da suka kawo gurin wani babban gida mai kyau da tsari, wanda za'a iya cewa kusan duk cikin estate din babu gidan ya da kai sa kyau , tsari da haduwa, horn suka danna, a take Mai gadin da tun tsayawarsu gurin da yaji numfashin motocin ya taho da gudu domin bude musu get din gidan , a hankali kyawawan motocin Yan yayi suka sulala cikin damfareren gidan, wanda yake dauke da get ukku, sai wata tsararriyar kofa da ta kasance ta hudu, wadda daga ita ne idan kai yar tafiya kadan zaka karaso asalin cikin gidan inda zaka tarar da kofar shiga parlour .


Bayan sun gama dai²ta parking a get na ukku, gaba dayansu suka sauka a motar, bude masa a ka yi, kamar d'azun ya share wasu mintuna a cikin motar kafin ya fito, cikin wata iriyar natsuwa ta musamman, a hankali yake tafiya kamar baya son taka kasa, ba wai yanga bane ko iyayi nature nasa ne a haka, komai yana yinsa ne cikin natsuwa da kamala, bai cika son gaggawar domin gaggawa aikin shaidan ce hakan yasa yake komai cikin natsuwa.


Duk a kofar parlourn suka rabu da Yaran da suke tare sai su biyu ne suka shiga cikin parlourn shi da wani kyakyawan sai dai bai ko kama kafarsa a kyau ba, shi ma din banyan kaya ne a jikinsa, sai dai ba kalar shigar da yay ba don wannan riga ce dinki boda da kuma wando, bai sa hula ba sai gashinsa mai tulin a bude.


Cikin karya harshen da iya sarrafasa ya furta "Assalamualaikum", cikin natsuwa matar da take zaune a parlourn ta d'ago da manyan idanunta, cikin murmushi ta mayar masa martanin neman amincin da yay mata, kyakyawa ce matar kallo daya zaka mata ka fahimci cikakkiyar Balarabiya ce gaba da baya, cikin natsuwa da kuma harshen larabci ta fara masa magana, cikin natsuwa shi ma ya mayar mata.


Bai tsaya anan ba kai tsaye ya haye saman bene, a hankali ya tura kofar parlourn, duhu dakin baka iya ko ganin tafin hannunka, shiga yay ciki tare da mayar da kofar ya rufe, ba tare da ya damu da duhun dakin ba, ya ci gaba da tafiya.


Sai da ya kai chan gurin wata kofa kafin haske ya mamaye gaba days cikin d'akin, kayataccen parlour ne Mai masifar kyau , babu wani hayaniya cikin parlourn amma ya yi kyau sosai, daga kujeru sai TV plasma sai TV stand , sai babban carpet din da aka malale gaba daya parlourn da shi, wasu Manyan tuntu ne na alfarma aka jefar a k'asan carpet din kwara hudu ko wacce kusurwa daya, gefe kuma dining room ne mai girma da aka k'awatasa da wani baza mai dauke da wasu kyawawan kasanan dutsuna masu k'yalli gaske, wanda suke matukar kama da duwatsun masu daraja(gold) wanda in baka san su na zaka iya tunanin ko su ne.


Babban table ne mai dauke da kujeru shidda, an k'awatasa da manyan wormers ga kuma wasu flowers masu kyau da suke gefe, fridge ne a gefe sai kuma wani hadadden show glass da aka jera cups , plates da kuma spoons , gefe daya chan Kuma washing hands babies ne, babu dai wata hayaniya sosai a gurin amma babu karya komai ya yi, kuma arziki ya koka....


GORUBA ROAD..

Wata mota ce kirar Audi TT kalar red mai kyawun gaske ce ta shigo cikin layin, tun kafin motar ta karaso kusa da kai zaka fara Jin tashin kid'a, cikin wak'ar turanci, sosai suka kure volume din motar, gashi kuma suna wani irin gudu irin na ganganci , fit! Haka suke wuwwuce mutane, har suka shiga chan wani layi da yake bayan Khalamu-wadeed inda jerin gwanon gidajen masu kudi suke, Anguwa ce da ta amsa sunanta a duk fadin cikin katsina kasantuwar duk wani jigaggen Mai kudi da yake cikin garin, in dai baya G.R.A to fa tabbas yana Goruba road, Hakan yasa ake ji da anguwar ake kuma kwantancenta.


Gaban wani gida Mai azababben kyau da tsari suka saki wani razanannen horn, cikin gigita da firgici Mai gadin ya taho da gudu tare da wangale get din gidan mai girman gaske, ba laifi gidan katon gaske ne, Mai Kuma kyau da tsari don tun daga waje zaka fara hangen tsaruwar gidan don wasu Manyan flowers ne masu kyan gaske aka jera a wajen , har ka shiga cikin gidan .


Parking Akai a fadedan parking lot din da yake cikin gidan, an dau lokaci kafin a bubbude k'ofofin motar, wasu kyawawan kafafu ne aka ziro , Yan mata biyu ne suka fara fitowa a motar, daya daga gaba dayar kuma baya, sai kuma kofar driver da ki tab'ata ba ayi ba.

Kyawawan Yan mata ne sosai, fararen ne sai dai sun kara da mai, suna da kyawun fuska ba laifi , sanye suke cikin wasu kananun kaya riga da wando da suka kama jikinsu sosai, kafafunsu sanye da heels shoes.


Kofar driver aka bude sai Kuma gaba daya kallona ya koma gurin, Tubaraqallah shine kalmar da ta fara darsuwa a zuciyata, kuma ita ce kalmar farko da bakina ya furta.


Kyakyawar doguwar budurwar ce fara tas kamar baturiya, tana da kyan fuska fiye da tunani, tana da zagayayyar fuska mai dauke da idanu dai² misali Wanda suke lik'e da sunglasses, hancinta ma dogo ne sosai, bakinta dan cif da cif, shigarta na karewa kallo , Riga ce baka a jikinta wadda bata gama rufe mata cibiyarta ba, a jikin rigar an yi rubuta YOU WISH da manyan harrufa da kuma jar kala, kasan cibiyarta da kadan kuma waist chain for women gold body belly chain ne, sai wani dan karamin jeans wanda bai karasa saukar mata kasa ba daga kasansa an tsatsargasa, kafarta ta dama kuma sanye take da classic anklet bracele leg chain jewelry ne.
Kafarta sanye da short boots-black , hannunta na sanye da Agogo dayan hannun kuma rike da kirar Diamond forever handbag, kan nan ya ci u an attachment, ba tayi kwalliya ba amma tayi kyau na fitar kwatance.


A hankali ta fara tafiya tana dan karkad'a key din motarta , rufa mata baya sauran Yan matan suka yi, tafiya su kai kadan kafin su iso gurin kofar parlourn, budewa su kai suka shiga, ban tsammaci zasu sallama ba don gaba days Yana yinsu bai yi kama da na 'ya'yan musalmai ba, duba da yarda shigarsu mu'amullansu yake .


Daga ciki aka Amsa musu, cikin gajiyawa tun daga gurin kofar parlourn ta fara wurgi da abubuwan hannunta, lokacin da zata karaso daga ita sai suturar da take jikinta, cikin gajiya ta fada kan kujera tare da lumshe idanunta cike da gajiya.


"Evening Mom", duk su biyun suka fada Banda wadda ta kasance cikin ta ukkunsu, cikin fara'a ta amsa musu,housemaid dinsu ta fara kira, da sauri ta k'araso , zubewa tai a gabansu , duk fada mata abun da zata kawo musu su ka yi, ban da ta ita da ta kishingida, cikin turanci ta tambayeta mai za'a kawo mata, amma in dutse da yake guri daya ya motsa ko yay magana to ita ma ta aikata daya daga cikinsu, sai da ta tambayeta sau ukku kafin matar da suka tarar a gurin tace "hi Blessing, make her a cup of coffee", jiki na matukar rawa ta tashi I zuwa wata kofa da take chan nesa kasan , cikin abun da ba zai wuce ten minutes ba ta dawo da katon tray a hannunta, wanda yake dauke cups .


Bawa kowa nasa ta yi, jiki a sanyaye ta durkusa gabanta cikin Dan rawar jiki tace "Maa. ga coffee", shiru tayi da ita bata ce komai ba, kara maimaitawa ta yi, sai da ta fada sau ukku kafin ta ware manyan idanunta da kwayar cikinsu ta dada baki sosai sannan ta kara girma sosai(co.......



Hope tsarin da tafiyar zai yi dai² da tsari da Kuma yanayin yarda kuke so ya kasance ?. duk da a karshen last book nawa ban fada muku ko wani book zan sa a gaba ba amma nasan in sha Allah wannan din ba zai kasa muku yarda kuke so, Allah ya bamu ikon rubuta dai², y karemu da fad'ar sharrin da ba daidai ba, ya bamu ikon tunatarwa da fadarkarwa har ma da nishadantarwa...



YOUR YAR GABAN GOSHI😂


YAR LELEN ROYAL STAR......🌹 SHEIKH IMAM🌹


By

YAR LELEN ROYAL STAR.


Page....2

(Cocaine sign) , cikin b'acin ran da bata san daga inda yake ba, ta dauki cup din coffee da zafinsa da komai ta juye mata tsab a jikinta, yar kara ta saki, da sauri ta shiga kakkab'e Yar b'ingilar rigar da take jikinta , cikin fada wanda bai hana zazzakar muryata fitowa rangadau ba tace "Did I tell you I need something?" Ta fada tana ware mata idanu masu firgita wanda bai tab'a ganin irinsu ba, jikinta na rawa sosai ga kuma zafin coffee da yake ratsa illahirin fatar kirjinta wanda har cikin kwakwalwar kanta take jin zafin , cikin rawar baki tace "So.. sorry Maa", ta fada cikin kankar da kai, tare da tattare glass cup din da ya tarwatse, cikin rashin jin dadi Mum tace "haba mai yasa ke baki san darajar na gaba da ke ba ? mai yasa kike Abu kamar wadda ta samu tab'i a kwakwalwarta ?....", Tun da ta fara magana ta zuba mata idanu, ganin za'a iya kai wa inda bata son a kai ne yasa ta daka mata tsawa "Shut up Maa.you know better than anyone, I don't want anyone in my life. therefore leave me alone please, " ta fada tana mikewa daga gurin da take a zaune ta haura sama, duk gaba daya bin bayanta su ka yi da kallo, babu wanda ya kara furta uffan, matar kuwa wani kakkaurar numfashi da ya fito tun daga k'asan zuciyarta ta fesar cike da d'aci da bakin cikin maganar da Yarinyar ta fada mata.


Sauran ma tashi suka yi suka rufa mata baya, a saman ma akwai yar tafiya kafin a k'araso wani kofa , bude kofar suka yi , wani babban parlour ne ya bayyana, parlourn y hadu sosai , gaba daya kayan cikinsa red and black ne, hatta da wallpaper din jikin bangon red and black , parlour ya yi kyau sosai, gashi ba wata hayaniya a cikinsa, kujeru ne saiti biyu irin mai zungureriyar nan, sai kyakyawa kuma lallausan Chinese carpet mai kyau, gefe daya kuma kayan kallo ne da tarin speakers, chan gefe kuma dining ne karami Mai daukar kujeru hudu jal.


Bata zauna a parlour ba kai tsaye sai ta shige cikin bedroom wanda shima gaba daya komai black and red ne, Italian bed ne babba sosai da wardrobe wanda ta kusa cinye bango daya, side drower sai kuma mirror .


Gefe kuma wani kofa ne da ban, na ga ta bude ban yi k'asa a guiwa ba na bita ciki, tab na furta lokacin da na gama karewa band'akin din kallo, ya hadu sosai gashi katon gaske, komai na ciki kuma latests one ne, katon bathtub ne a gefe daga gefensa wani karamin loka me mai murfin , sai Kuma toilet da yake chan gefensa da ban, sai sink shima gefensa da ban, sai wata babbar kanta da aka buga inda anan aka jera wasu expensive body lotion, heir cream, turarukan wanka masu tsadar gaske,Wata kofa ta tura ta shiga, wannan Kuma gurin da kaya suke ne gasunan mak'ale a hanger , kala², yawancinsu Kuma duk kananan kaya ne, bangaren da aka Ajiye towels ta nufa, wani black ta dauka, karami da babba...Cikin natsuwa ya fito Yana sanye da Jallabiya fara kar an Dan yi mata aikin surfani a jikinta, kansa sanye da hirami da maka-wuya, masu kyau da tsada, kafarsa sanye da wani leather slippers da suka kama kafarsa, hannunsa daya na cikin aljihun jallabiyar jikinsa, dayan hannun kuma na dauke da tamfarsetsiyar wayarsa yar yayi da ba kowa yake rike kalarta ba saboda tsadarta bugu da kari ma ba tayi ko wata biyu da fitowa ba, kirar iphone 15 pro max, sai wani walali da daukar idanu take.



A hankali yake tafiya cikin natsuwar da ta zame masa jiki, sai baza kamshin turaren Viktor &Rolf Flowerbomb Haute couture Mai sanyi da tausasa zuciyar Mai shak'a, a parlour ya tarar da matar d'azun ita da wannan dai da suka shigo tare, Rolex watch din da take msnne da tsintsiyar hannunsa ya kalla , cikin sanyayyiyar muryarsa Mai sanyi da taushi yace "Lokacin Sallah ya yi", yana fada ya nufi barin cikin parlourn, da sauri Matashin da yake zaune ya biyo bayansa, a babban masallacin da yake kofar gidan suka tsaya, anan Dan saurayin ya tsaya yin al'wala shi Kuma da yake da al'walarsa shiga ciki yay.



Cikin sanyayyar muryarsa mai amsa amo wadda Kai tsaye daga bakinsa take shigewa kunnuwan gaba daya jama'ar yankin ta hanyar loudspeaker da take a jikin masallacin, fara kiran Sallar Magrib cikin tausasawa da wata kalar murya mai dadin gaske.
Dandanan mutane suka fara ansa kiransa na zuwa bautawa Allah daya, kafin kace Mai gaba days masallacin an hadu sosai babu masaka tsinke.
Cikin muryarsa Mai dadi ya fara raira karatun Al-qur'ani Mai girma wanda duk wanda ya ji , in dai kana da imani a zuciyarka dole zuciyarka tai taushi sannan kaji wani abu na musamman Mai kama da shauk'in Jin dadin karatun yana tsirga cikinta, haka aka gabatar da Sallar Magrib cikin shauk'i da natsuwa.



Bayan an idar da yake ranar juma'ar bama juma'ar ba kusan ko wanne lokaci ana gabatar da wa'azi Amma an fi gabatarwa ranar juma'a, kuma mutane ma sun fi samun damar halarta a wannan ranar.
Haka guri ya hadu da mutane, sakamakon da yawa sun San shu zai gabatar da karatu shi yasa duk aka hallara har ma wanda basu samu damar gabatar da sallarsu anan ba sai da suka garzayo domin samun kwankwadar madarar ilimi daga hamshakin Malamin Addini, da duk duniya ake marari da son gani ki jinsa.


Gyara zamansa yay a gaban daruruwan mutanen da suke kallonsa cike da yakini da kuma girmamawa, cikin natsuwa Dan agajin da yake gefensa ya matsa tare da gyara masa abun maganar da yake jikin rigarsa , gyaran muryar yay cikin muryarsa mai dadi , yay musu sallama, Amsa masa suka yi cikin sauri da zakwadi, k'ara gyara zamansa ya yi, kafin yace "yau za muyi magana ne akan", shiru ya dan yi kad'an , yana kuma kallon fuskokin kamar mai nazartar fuskokin, cikin natsuwa yace "Imani.!".
"da farko ma mene Imani ?", Shiru ya dan yi ba kuma don yana bukatar wani ya Amsa masa tambayar ba, domin lalubo maganar da take kwance lame² cikin zuciyarsa wadda bai fiye yawaita yin ta ba.




"Imani:Furuci ne da harshe tare da kuduri a zuciya had'e da aiki da gab'b'ai, yana k'aruwa sannan yana kuma raguwa." Shiru yay hannunsa na dan tab'a gemunsa mai kyau da yake ta zuba k'yalli.
kamar irin wanda bai san mai zai ce din nan ba, "Allah Makaukaki yana cewa 'ba wasu ba ne muminai face wad'anda da zarar an kira Allah sai zukatansu su razana, idan kuma aka karanta musu ayoyinsa sai su kara musu imani, kuma ga Allah kad'ai suke dogaro. Su ne wad'anda da suke tsaida sallah, kuma suke ciyarwa daga abin da muka azurta su da shi. Wad'anan su ne muminai na gaskiya, suna da darajoji a wajen Ubangijinsu tare da gafara da arziki mai yawa'. A duba suratul Anfal chapter 2-4.
Allah Madaukaki ya ce,'Duk wanda ya kafirce wa Allah da Mala’ikunsa da Littattafansa da Ranar lahira to hak'ik'a ya bata bata mai nisa. Suratul Nisa’i chapter 136'.
Saboda haka akwai Imani da harshe,kamar zikiri, addu’a, umarni da kyakkyawan aiki, hana mummunan aiki, karatun Alkur’ani da makamantansu", shiru yay na dan lokaci mai nisa yana sauke numfashi, don ji yake harshensa yana masa nauyi sakamakon shi ba mutum bane da ya saba sannan kuma yake jurar magana mai nisa, ga hausarsa ba wani fita take sosai ba hakan ne ya tilasta mata hada Engausa.


"Akwai kuma Imani da zuci,kamar k'udurcewa zuciyarka kad'aita Allah a cikin rububiyarsa ,wato mulki da halitta da cancantar bauta masa, sanan kuma da kad'aitasa a sunayensa da siffofinsa, da kudurce wajabcin bautar Allah shi kadai ba tare da an had'a sa da wani abin bauta ba, da sauran abubuwan da suke da alaka da zuciya kamar niyyoyi da manufofin ayyukan bayinsa haka nan ayyukan da malamai ke kiransu 'ayyukan zuci' suna shiga cikin imanin da a ke yi da zuciya. Misalinsu shi ne son Allah, tsoronsa, komawar zuciya gare Shi da dogaro da Shi, da makamantansu.
Daga cikin abubuwan da sunan imani
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment