Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu ciki a jikinki ?

Dariyar yake tayi ta ce," A haba dai ciki kuma?ka manta wancan satin fa nayi wankan tsarki sai dai in a satinan cikin ya shiga, cikeda gamsuwa yace," okay hakane kam .....

Da kadan da kadan ta fara jin tashin zuciya , runtse idonta tayi tana son danbe aman amma ina yariga ya yunkuro mata , da gudu ta tashi ta nufi toilet...
bayanta Khalil ya bi shima , ya Shiga toilet din ya sameta tanata kaura amai kamar hanjin cikinta zai fita , bayan ta gama , ta kunna ruwa a famfo ta wanke bakinta , ta wanke fuskarta, tana numfarfashi , ga murdawa da cikinta keyi .....

A hankali take dafa bango tana kokarin fita,sannu yayi mata,ya taimakamata suka fito falo suka zauna ....

Kura mata ido Khalil yayi yace,"kai juwairriya daukko hijabinki muje Asibiti , ina tunanin akwai ciki a jikinki , wani mummunar faduwar gaba taji , muryar ta Na rawa tace,"amma Khalil ni fa banda komai , ka manta ma last week nagama period fa ...
kara kura mata ido yayi yace," duk da haka kitashi Mu tafi , batareda ta kara cewa komai ba , ta mike jiki a sanyaye ta daukko katon hijabin ta suka nufi asibiti......

Bayan sun Isa Asibitin gwajin farko aka gwadata aka tabbatar da cewa tana daukeda cikin watanni uku, cikin tsantsar tashin hankali juwairriya tace," ciki kuma?
wata tsawa Khalil ya daka mata yace," munafuka ai ni nasani narigada naga Alamar baiyyanar ciki a jikinki amma kin musamun to Allah ya toni asirinki , wallahi bazamu bar asibitinan ba sai an zubarda cikinan , ni har yanzu ban shirya haihuwa ba , in ba ma mahaifarki kwadayaiyya bace yaza ayi kidin ga saurin daukan ciki ,to tun wuri ki shirya yau dinan za,a zubar ba sai gobe ba ,kuma yanzunan ......

Cikin kuka juwairriya tace,"" ni wallahi bazan zubar da wanan cikin ba , akan me zan zubar , ni nagaji nagaji wallahi , sau nawa kana sa ni ina zubarwa , to a wannan karan bazan zubar ba domin likita ya tabbatarmun da cewa in na Kara zubarwa zai jamun Matsala , sabida haka ba zan zubarba bazan zubar ba tafada gamida tashi ta fita da mugun gudu , tana kuka .......

Bayan ta shima ya bi , ita ko da gudu ta tari abun hawa ya kaita gida , shima ya Shiga Mota ya bita a baya......

Tana Isa gida ta fada gado ta fashe da kuka ...
Shigo wa yayi a fusace cikin fada ya ce ni kika tsaya kina gaigayawa magana Ashe baki da mutumci baki da hankali lallali zaki gane kurenki , yafada yana kokarin curo belt din jikinshi ya fara zugamata , ihu tafarayi tana kuka tana neman taimako , cikin kuka take magana ,tace", Khalil me nayi maka , sakaiyyar da zakamun kenan , magana takeeyi amma ina baya ma cikin haiyya cinshi sai dukanta da yakeyi kamar yasamu jaka ....
sai da ya ta jigata , yafara mai da numfashi ya wurgar da belt din a jikinta yace," tashi tashi yanzu ki barmun gida na , *nasakeki saki uku* , sanan kije ki nemu uban dan cikinki amma ba ni ba na fada miki ......

Dagata yayi ya figota ya wurgata waje , ya daukko kudi ya Watsa mata yace," tashi kiwuce kije duk inda zaki bani ba ke ......

Tsabar tashin hankali ma juwairriya ta kasa kuka , kudin ta deba ta mike dakyar ta gyara hijabinta , ta tari a daidaita ....
Ganinta a jigace yasa mai Napep din tambayarta yace," lafiya? baiwar Allah , dakyar ta iya bashi amsa tace_" ka kaini Tasha kawai ....

kai tsaye Tasha ya kaita , bayan ya ajiyeta , ta lalaba ta sami motar Maiduguri , ta Shiga ta zauna a jigace ,bayan an gama Lodi aka kama hanyar tafiya .....

Bayan sun Isa garin mai duguri misalin karfe takwas na dare , dakyar da tambaya ta gane gidansu haidar ,Kasancewar tun tana karama rabonta da garin ....

Duk Wanda yaga juwairriya zaiyyi tunanin mahaukaciya, domin duk ta fita haiyyyacinta , ga yunwa da kishir ruwa dake damunta ga azaban ciwo da cikinta ke mata ga jiki duk tsami ga shatan duka a fuskarta ga zafi da dukan yake mata.....
Hakika juwairriya ta wahala ...

Misalin karfe tara ta Shiga gidansu haidar......✍✍

*Muje zuwa*

*COMMENTS & SHARE*


*BY MUM FU'AD*


πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*A SANADIN KUSKURE NA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

*MALLAKIN*πŸ‘‰ *ZAYNERB MUHAMMAD KABEER (MUM FU,AD)*

*SEARCH ME ON WATTPAD AT ZAYNERB MUHAMMAD KABEER*

*EMAIL ADREES AT ZAYNERBMUHAMMAD KABEER [email protected]*

*FACEBOOK ZAYNERBMUHAMMADKABEER*

*MARUBUCIYAR LITTAFIN*πŸ‘‡
*MAHAUKACIN KISHI*🌺🌺🌺🌺
*HATSABIBIYAR MACE*πŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈπŸ§›πŸΏβ€β™€οΈ
*AND NOW*πŸ‘‡
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’ *A SANADIN KUSKURENA*πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

_*INAYIMA DUKANIN DAUKACIN MUSULMAN DUNIYA BARKA DA SALLAH FATAN ANYI SALLAH LAFIYA ALLAH KUMA YA MAIMAITAMANA AMEEN*_.

*_banyarda a canzamum labari ta wani siga ba batareda da izinina ba_*.

*_Kamar yanda kukasani duk littattafaina true life ne ba kageggen labari bane, to wannan ma haka_*

*_HAR YANZU LITTAFIN HATSABIBIYAR MACE NANAN A NAIRA DARI BIYU KACAL , LITTAFIN DA YAKE KUNSHE DA DARUSSA IRI_IRI DA BAN DABAN HUMM KU DAI MAZA KU HANZARTA KU MALLAKI NAKU A NAIRA DARI BIYI KACAL , KUNUNAMUN KAUNA TA HANYAR SIYAN LITTAFINA A NAIRA DARI BIYU, SAI NA JIKU_*.

_*SADAUKARWA GA MY LOVELY MUM HAJIYA SAFIYYA MUHAMMAD*_
*_INA MATUKAR KAUNARKI HADE DA ALFAHARI MAMANA_*


*(A TRUE LIFE STORY)*

*_ASHA KARATU LAFIYA_*

*_____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PAGE 60*
*THE LAST PAGE*
πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š

Misalin karfe tara juwairriya ta nufi gidansu haidar dakyar da taimakon ,Allah , domin iya jigta juwairriya ta jigata duk ta fita a haiyyacinta matuka......

Da sallama ta Shiga gidan muryar ta kasa kasa ta na hakki .....

Tana shiga cikin gidan fadi Tim a kasa sai suma ....

Jin sallama yasa mahaifiyar haidar ta tashi ta leka taga ko waye....

Ganin mutum tayi a kasa a sume ...
cikeda tsoro ta karaso ta kai hannunta ta ja mata hijabin jikinta....

kasancewar akwai wutar Nepa yasa ta rafka salati tace," kai wannan ba zuwairra bace?tafada cikin tsantsar mamaki ....

Daki ta koma ta dauko torchlight , ta dawo ta haska fuskarta ..
wani faduwar gaba taji cikeda tsoro tace," nashiga uku wallahi zuwairah ce......

Cikin mamaki tace," kai anya kuwa? Anya itace abun fa da mamaki , amma me ya faru da ita haka?

Runtse ido tayi ta kai hannunta ta juyata , taga bata matso......

Cikeda dauriya ta dagata ta kaita daki ta kwantar da ita.......

Ido ta kura mata taga yanda tayi wani irin rama , cikin tsantsar mamaki take ta sake_sake iri_iri cikin ranta......

A Daren Ranar mahaifiyar haidar bata iya runtsawa ba , sai dai dan barci barawo......

Washe gari da safe misalin karfe takwas na safe haidar ya dawo gida , kasancewar a office ya kwana.....

Da salama ya shigo gidan , kai tsaye ya nufi dakin mahaifiyarshi ....

Zaune take a daki tayi ta gumi ,tana tunani, batareda da sanin cewa haidar ya shigo ba ....

Salama ya karayi , firgit tayi tace," wa alaika salam ,ai har kadawo , ehh yace yafada a takaice ....
kallanta yayi yace"Ummi lafiya kuwa me yasameki kika rafka tagumi haka?
Hmmm kai dai haidar bari kawai taso muje daki ka gane ma idonka tafada gamida mikewa ta nufi daki, shima ya bita abaya cikin mamaki yana me tunanin ko menen?

Kwance take, mahaifiyar haidar tayi mishi nuni da hannunta tace," haidar juwairriya ....

Cikin tsantsar mamaki yake kallanta yace," ummi yaushe tazo?

Take mahaifiyar haidar ta bashi labarin zuwanta har zuwa yanzu.....

Cikeda damuwa yace," Ummi to daukkota muyi asibiti da ita ,.....

Kai tsaye suka nufi asibiti da ita.....

Cikin mintuna Kadan aka kaita asibiti aka nufi emergency da ita aka fara bata taimakon gaggawa....

anyi sa'a numfashinta yafara daidaita tare da taimakon oxygen din da aka saka mata......

Cikin tantsan tashin hankali haidar yace," Ummi ko zamu kira Abban juwairriya Mu fada mishi halin da ake ciki ne?

Cikeda da gamsuwa ummin haidar tace,"eh hakan ma yayi ka kirashi din kawai sai a sanar da shi .....

Amma Ummi ko mijinta za'a kira ne?
A ganina kamar shima yakamata ya ji ko ?
haidar ya fada ?

A,a haidat kar a kira mjin nata ,mudai kira mahaifinta zaifi , kasani ma ko mijin nata ne yasa ta cikin wanan halin ma waya sani ne?
cikeda gamsuwa haidar yace," hakane kuma Ummi yafada gamida daukko waya yana shirin kiran mahaifin haidar ......

Zaune daddy yake shida mommy suna kallo su kadai....

Jin ringing din wayarshi yasashi saurin dauka , ganin sunan haidar akan screen din wayar yasa shi sakin murmishi yace," Allah sarki yaron Albarka kwana biyu bamu gaisa ba dama , yafada gamida daga wayar yakara a kunneshi .

Ina kwana daddy yafada cikin girmamawa "lafiya kalau haidar ya gida? ya mamanka ?lafiya kalau .....

shuru haidar yayi yace," daddy dama akan maganar juwairriya ne ...
bata rai ddady yayi jin an ambaci juwairriya sabanin daa da fuskarshi take daukeda murmishi .....

Cikin bacin rai daddy yace," amma haidar Kasan dai na kafa doka kar wani ya sake mun maganar juwairriya ko?

Cikin ladabi haidar yace," daddy kayi hakuri wallahi yanzu haka juwairriya bata inda take ba , bata San halin da take ciki ba tanan nan tare da Mu a nan Maiduguri.....

Cikin nuna Alamun ko in kula yace," banda abunka haidar ai bani zaka fadama ba mijinta yakamata ka fadama , ni yanzu Ai ba'a karkashina take ba so ba abun da ya shafeni , Allah ya bata lafiya ....
Kasancewar a speaker haidar yasa , wayan , yasa mahaifiyarshi tayi saurin karbar wayar tace," Haba kai kuwa Abban zuwairra meyasa kake hakane?kai kasan halin da yarinyar nan take ciki kuwa? yanzu haka a emergency take , batasan waye a kanta ba fa ,Allah ma ana mishi laifi ya yafemana bare mutum , sabida haka in har ka daukeni da muhimmanci kamar yandda kake fada , to Inda hakane ina rokonka da kazo ka duba halin da yarka take ciki kaji ..?

Jiki a sanyaye daddy ya kashe wayar batareda da yace komai ba ........

Tunda haidar ya kira daddy a waya Mommy take Jin maganar haidar kasancewar daddy yasa wayar a speaker , hakan yasa tafara kuka batareda ta iya cewa komai ba har zuwa yanzu da ya kashe wayar .......

Ganin tana kuka yasa jikin daddy ya karayin sanyi , yace," ke kuma miye haka kike kuka kamar yarinya karama.....

shuru tayi batareda da ta iya cewa komai ba saima kukanta da ya tsananta .....

Karasowa tayi gabanshi ta durkusa agabanshi ta tsuguna....
Cikin muryar kuka tace," Alhaji kamar yanda ba ni kadai na haifi juwairriya ba , haka kai ma ba kai kadai ka haife ta , kallanta daddy yayi cike da mamaki.......

Share hawayen fuskarta tayi taja dogon numfashi tace,"a wannan karan zanje naga juwairriya dan ta yuyu shine karo na karshe dazan ganta a rayuwata , domin jikina yana yana bani juwairriya bata cikin koshin lafiya kuma tana cikin matsanancin hali, zanje na ganta ko da kuwa hakan zai kawo karshen zamana ni da kai........

Jiki a sanyaye daddy yayi shuru yana nazari , kafin daga bisani yace," ki shirya zamu tafi tare yanzu yafada hade da mikewa ya nufi daki , ya dauki keyn motarshi ........

Itama daki ta Shiga ta saka hijabi ,cikin Sauri ta fito ,suka fita suka Shiga mota suka dauki hanya sai garin Maiduguri.........

A bangaren juwairriya kuwa sossai likitoci suke kokarinsun a kanta..........

Suna kan treating dinta , tafara bude ido a hankali , tana kallansu batareda da tace komai ba, kamar zautacciya .....

Wani 'kara ta sa jin wani azababben ciwon ciki da ya ziyarceta lokaci daya ....
runtse ido tayi , cikin kankanin lokaci numfashinta ya dauke.....
nan take tafara bleeding sossai jini yafara zuba ...

ganin haka yasa likitoci suka fara kokarin tsaida jinin gudun kar ta rasa cikin jikinta .......

Bleeding take sossai Inda likitoci suka gagara tsaida jinin , har guda_guda yafara Fita ...
cikin tashin hankali likitoci suka Kara kokari har Allah yasa jinin ya fara tsayawa ......

Amma anyi rashin sa'a cikin jikinta ya riga da ya lalace .....

Hakan yasa dole sai ancire sauran lalataccen cikin sanan anyi mata wankin ciki.......

Anyi nasara an cire lalataccen cikin ankuma yi mata wankin cikin ......

Hakika duk wanda yaga juwairriya sai ya tausayamata domin tajigata matuka tasha wahala, cikin lokaci kankanin ....
Tafita a haiyyacinta , tayi wani fari gawata rama da tayi , bakinta ya bushe yayi fari , kewayen idanuwanta sunyi baki ,kamar ba juwairriya ba......

Cikin ikon Allah likitoci suka daidaita komai , aka gama treating dinta suka nufi dakin hutu da ita gamida yi Mata Allurar barci ......

Bayan an fito da ita haidar da umminshi suka nufi gurin babban likitan da sauri, dan jin halin da juwarriya take ciki.....

Nan Likita yace ,"su bishi office...
bayan sunje office din ya zauna yayi musu bayanin duk abun da yafaru da juwairriya , ya kuma tabbatarmusu da cewar damuwa ce tayi mata yawa kuma jininta ya hau ga ciwon zuciya da take fama dashi ....

Jin haka yasa hankalin su ya tashi matuka....

Bayan haka likita ya kara tabbatar musu da cewar, mahaifarta ma daf take da lalacewa banda Allah yasa sunyi iya kokarinsu akai da yanzu bazata sake haihuwa ba sakamakon cikin da ta zuzzubar a baya, ga wannan ma da ya lalace .......

Sossai suka dinga mamakin yanda haka ya kasance ,haka suka bari su jira farka warta ta basu labari suji .......

Godiya sossai sukama likitan daga bisani suka fita .......


A bangaren Khalil kuwa ,hankalinshi a kwance yake batareda da damuwar halin da juwairriya zata Shiga ba .......

Bayan ya koreta hankalinshi a kwance, yafita sabgoginshi , yama manta da ita ....

Misalin karfe 8 na dare daddy da mommy suka Isa garin Maiduguri ....

Haidar ne ya kwatanta musu asibitin...
cikin kankanin lokaci suka karaso ......

Nan haidar yazo ya daukesu ya nuna musu dakin juwairriyan suka Shiga, cikin tsananin tashin hankali ......

Ganin juwairriya kwance da oxygen a hancinta yasa mommy jin wani mummunar faduwar gaba , tafara tafiya a hankali jiki a sanyaye , hade da wasu hawaye masu zafi ....
dakyar ta iya karasawa gurin juwairriyan, tana me mamakin ganinta a wanan halin......

Shima daddy dauriya sossai yayi ganin halin da yar tashi take ciki ya matukar daga mushi hankali ......

Dakyar mummy ta iya bude baki tayi magana cikin muryar kuka tace," Ummin haidar yanzu juwairriyace haka? garin ya ya? meyasameta ,ya akayi tazo nan???

Jiki a sanyaye ummin haidar tafara basu labarin yanda juwairriyan tazo har zuwa kawota asibitin da kuma bayanin da likita yayi musu akan abun dake damunta har izuwa yanzun da suka shigo .......

Tunda ummin haidar tafara bada labarin , wasu hawaye masu zafi suke fita a fuskar Mommyn juju ....
wani zafi ranta yakeyi mata , ga wani daci da bakinta ke mata ....
kuka ta fashe dashi tace," juwairriya! juwairriya ta !ciwon zuciya ? kai! kai !kai! takara fashewa da kuka mai cin rai da ban tausayi ........

Shikuwa daddy , banda rawa ba abun da jikinshi keyi, gamida runtse idonshi cikin ranshi yana me karanto innalillahi wa inna illaihir raj'un...
zuciyar na mishi zafi , hade da tausayin yar tashi cikin ranshi ....

Shuru kowa yayi , kowa da abun dayake sakawa a ranshi.....

Nan kowa yafara fadan Albarkacin bakinshi a kan halin da juwairriya take ciki, da haka har aka yanke shawarar jin ta bakinta da yanda hakan ta kasance in ta farka ........

Nan haidar ya fita ya nemoma mommy da daddy abincin da zasuci ....
Yakuma biya gida ya taho da duk abun da yasan za'a bukata na masu jinya , daga bisani yadawo asibitin........

Ko da ya basu abincin ma dukkansu kasa ci sukayi wai ba yanzu ba , domin damuwa bazata bari suci abinci ba in ba sun ga farfadowar juwairriya ba....

Misalin karfe goma sha biyu na dare juwairriya, hanun juwairriya yafara motsawa ...
Da Sauri ko wa ya matso gurinta yana kallanta ......

A hankali tafara bude idonta , ganin duhu yasa ta runtse idonta , tana jin wani irin jiri , kanta na juyamata....

bude idonta ta karayi , tafara ganin dusu_dudu cikin idonta ..
ga dakin Asibitin na juya mata, hannu tasa ta rike kanta .....

Sannu aka farayi mata ,mommy tace," juwairriya !!jin sunanta tayi kamar a mafarki, tana jin irin muryar momnynta ...
maida idonta tayi gefe taga mommy kusa da ita...
kura mata ido tayi tana kare mata kallo duk da cewa dusu_dusu take ganinta , amma hakan bazai hana ta gane mahaifiyarta ta ba ...
wani murmishi ta sakarwa mahaifiyanta, ta kawo hannuta daf da mahaifiyartata ....
da Saudi mommy ta kawo hannunta ta hada da na juwairriya guri daya ta damke tana kallan juwairriyan tace," Allah ya baki lafiya ...
shuru tayi sai binta da take da kallo , wani hawaye me zafi na bin gefen idonta .....

Shima daddy karasowa yayi daf da ita ya kalleta yace," juju! Idobta ta dago ta kalleshi gamida kura mishi ido ......
kokarin mikewa tafara , amma ta gagara.....
Da Sauri mahaifiyar haidar taje gurinta ta riketa ta komar da ita tace," A,a basai kin tashi ba ki kwanta kinji , da kallo ta bita batare da tace komai ba .......

Shuru tayi ta runtse idonta , kafin ta bude a Hankali gamida kara mai da kallanta zuwa ga Abbanta, wani murmishi ta sakarmishi shima ya sakarmata, ya mata nuni da ta kwantar da hankalinta tadan daga kai Alamar to .....

Shuru sukayi batare da kowa yace wani abu ba......

Cikin ransu murna sossai sukeyi ganin juwairriya ta farka.. ...

Nan haidar ya tuna musu da abincinsu .....

Dariya sukayi , suka dauka sukaci kadan , suma ,su haidar din da Mamanshi suka ci .....

Barci suka dan taba kadan ba sossai ba, ganin juwairriyan ta koma barci ne yasa suma suka dan runtsa , amma duk bayan mintuna sukan farka su dubata......

Haidsar kuwa yanda yaga dare haka yaga rana , domin bazai taba iya barci ba , idonshi kyar akan juwairriya tausayinta na kara kamashi ,yana jin wani sabuwar soyaiyyarta a ranshi.....

Da Asuba daddy da haidar suka tafi masallacin cikin Asibitin......

Suma su mommy sallan sukayi daga bisani suka tashi suka koma suka zauna, suna me kare ma yar tasu kallo hade da yimata Addu'ar samun lafiya ......

Misalin karfe 8 daddy ya kira suhail da Al_amin ya Sanar musu da halin da ake ciki , sossai hankalinsu ya tashi ...
sukace suna nan taho wa ....
dakatar dasu daddy yayi yace," su barshi ba Sai sunzo ba, suma baza su dade ba zasu dawo inshallahu ...
badan sunso ba haka suka hakura dan ba yanda zasuyi , Sai dan daddy ya umarcesu da hakan .......

Likita ne ya shigo dakin, ganin juwairriya ta farka ta bude ido ga numfashinta ya fara daidaita ba laifi ,hakan yasa ya cire mata oxygen din ...
Yakuma sake yi mata Allurai gamida batsa magunguna .....

Tea aka hada mata tasha kadan , kafin daga bisani Tasha magungunanta ta kara komawa barci ......

Suma tea suka dan sha, sukaci da bread.....

Bayan sun gama karyawa mommy tace," Ummin haidar ai da kinje gida kin huta kin yi wanka dan nasan kin gaji sossai ga kwanan zaune da kikayi na kwana biyu....
Dariya tayi tace," wallahi babu komai fa , zanje dai nayi wanka sai nadawo kema Sai kije kiyi ko?
To shijenan, badamuwa Mommyn Juju ta fada ....

Tashi ummin haidar tayi gamida tafiya gida .....

Shima haidar gida yaje yayi wanka daga bisani ya dawo asibitin ......

Bayan awa daya ummin haidar ta dawo Asibiti ....
itama Mommyn juwairriya ta tafi tayi wankan, daga bisani ta dawo asibitin ..

Misalin karfe sha biyu na rana juwairriya ta farka .....
wanan karan ba laifi jikinta yayi karfi sossai, ummin haidar tace," sannu juwairriya , muryar kasa_kasa tace,"aha nagode Ummi...
jin tayi magana yasasu yin Hamdallah sukace Masha Allah ah lallai jiki kam Alhamdulillah....

Ko a d'agaki ki ne ki dan jingina ?
Kad'a kai tayi Alamar ehh .....

Cikin hanzari mahaifiyar haidar ta tashi ta d'agata a hankali tasa filo ta bayanta ta jinginar da ita a bango......

Da kallo take bin kowa ta kura ma daddy ido tace," daddy ! da Sauri ya karaso gurinta yace," na'am juwairriya sannu ko Allah ya baki lafiya , Ameen tafada cikin sanyin murya .....

idanuwanta ne yafara ciccikowa tana shirin yin kuka tace," Daddy Ka yafemun?
Murmishi yayi yace," na yafe miki juwairriya kinji?
Hawayen da suka makale a fuskarta ne suka zubo tace," daddy nagode Allah saka da Alkhairi daddy nayi maka Alkawari bazan kara bijire maka ba bazan kara watsa maka kasa a ido ba , daddy kaga abun da kasance dani ko ?daddy ka yafemun ta fada gamida fashewa da matsanancin kuka ...
kiyi shuru kinji juju , mommy tafada cikeda tausayin yarta ta ......

Cikin lallabi daddy yace," juwairriya zaki iya fadamun ya ya akayi kikazo garin mai duguri? Kuma meyasameki ina mjjin naki?

Shuru tayi kafin hawaye suka fara zubowa a idonta..
kuka ta fashe dashi tace," daddy naga illar bijire maka danayi .....

Take tafara basu labarin zamanta da rayuwarta a gidan Khalil har izuwa wannan lokacin da ta farka ta ganta kwance a gadon Asibiti......

Tunda juwairriya tafara basu labarin rayuwarta mommy ke zubar da hawaye , jitake zuciyarta nayi mata zafi sossai , tana me matukar tausayin yar tata lallai juwairriya taga rayuwa.....

Jajawur idon daddy yayi ranshi yayi matukar baci , ji yake kamar yaje ya samu Khalil ya kasheshi koya ji saukin bacin ran dayake ciki , karfi da yaji Khalil ta mayar mishi da yarshi karamar bazawara , hakika ya ruguzamishi plan din da ya dade yana ginawa akan juwairriya , amma akwai Allah daddy ya fada cikin ranshi ....

Cikin matsanancin damuwa haidar yayi shuru yana me jin tsanar Khalil cikin ranshi.....

Sossai mahaifiyar haidar tayi Alawadai da halin khalil gamida tausayin juwairriyan ..

Numfasawa daddy yayi yace," juwairriya kingani ko? Kinga **SANADIN KUSKURENKI* a bun da ya haifar miki ko?

Juwairriya nasani bazan taba yi miki zabi maras kyau ba amma kika kekashe kasa kika ce sai wanan yaron yanzu ga abin da ya miki .....

Murya a sanyaye mommy tace"" Alhaji yanzu ba lokacin tuna wani Abu bane , a manta da baya , haka Allah ya kaddara ,mu gode ma Allah ma da bai kashemun yartawa ba .....

Cikin bacin rai daddy yace,," tabbas sai yayi dana sani a rayuwarshi na wulakantamun yata da yayi , bazan kyaleshi ba ......

Cikin bacin rai haidar yace," gaskiya daddy kam dole a hukuntashi , ya cutar da ita.......

Murmushi mommy tayi tace," Alhaji gaskiya daukan mataki ba namu bane , duniya ce mu rabu dashi inshallahu ,Allah zai hadashi da daidai shi , sannan bazamu kaishi kara ba ,ko ayi mishi wani Abu , wallahi ta ruwan sanyi ma Allah zaiyi mata sa kaiyya...

Mu barshi da Allah zai ga sakaiyya , badai ya saketa ba kuma saki har uku , shikenan ,kaga garama da Allah yasa auren aka rabu......

Shuru juwairriya tayi tana me tausayin kanta tana Kara jin tsanar Khalil cikin ranta ,soyaiyyar da take mishi ya koma zallar kiyaiyya , sai dai ta godema Allah dayasa iyayenta suka yafe mata ko ba komai yanzu hankalinta ya kwanta.....

*A guguje*

Satin juwairriya daya a asibiti aka sallamesu .....

Kwanan su daya a gidansu haidar daddy ya matsa su ka koma gida .....
Duk yanda mahaifiyar haidar taso hanasu ki yayi a cewarshi gara

Please Login or Register in order to submit comment