Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

al’amuran cinikayya ke gudana.
Tafe take a bisa ingarman doki cikin ƙayatattun tufafi ta rufe fuskarta da rawani idanuwanta kaɗai ake gani, waɗansu irin gabza-gabza samudawan dakaru ne ke take mata baya, hannayen su ɗauke da miyagun makamai sai muzurai suke yi tamkar za su ci babu, kallo ɗaya za ka yi masu ka fahimci cewa murmushi bai taɓa wanzuwa a kan fuskokinsu ba.
Duk wajen da Sarauniya Abidat da dakarun suka durfafa a kasuwar sai dai ka ga yara da manya na zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa cikin ladabi, kuma suna darewa suna buɗa masu hanya tamkar sun hango mutuwarsu, ko ciniki ake yi da zarar su Abidat sun durfafo wajen sai ka ga masu siye da sayarwa sun zubar da kayayyakin dake hannayensu, sun faɗi ƙasa sun kwashi gaisuwa.


Haka dai Sarauniya Abidat da tawagarta suka ci gaba da tafiya suna ratsa layuka da unguwannin kasuwa.
Ana cikin wannan tafiya ne Sarauniya Abidat ta hango wani dattijo yana gyara waɗansu kayan marmari a cikin kwandon kaba, har ya zaman tazarar dake tsakaninsu bata huce taku shida ba amma dattijon bai daina aikin da yake ba ya zo ya kwashi gaisuwa.


Koda ganin hakan sai Abidat ta fusata ainun zuciyarta ta kama tafarfasa tamkar za ta kone bisa ganin yadda dattijon ya nuna rashin ladabi a gareta.
Cikin matukar fushi Abidat ta kama linzamin dokinta ta sauko ta yiwa dakarun ta inkiya da wutsiyar ido.
Tamkar dakarun sun san abin da take nufi sai kawai suka je suka cakumo wannan dattijo suka gurfanar da shi a gaban ta
Kawai sai Abidat ta zaro wata ‘yar siririyar wuka a damtse ta yanke kunnen dattijon na dama, saboda tsananin raɗadi da zogin da dattijon ya ji bai san sa’adda ya kurma wawan ihu ba a lokacin da jini kezuba daga wajen, cikin alamun rashin imani Sarauniya Abidat ta sake yanke masa dayan kunnen na ɓarin hagu jini ya yi tsartuwa gami da feshi.
Haka ta ci gaba da yankewa dattijon ƙananan gaɓoɓin da ke jikinshi. Haƙiƙa Sarauniya Abidat ta cika AZZALUMA ta gaban kwatance, domin komai rashin imanin mutum idan ya ga yadda dattijon ke ihu da koke-koken neman agaji dole ne ya tausaya masa ainun.


Da yawa daga ckin jama’ar da abin ke wakana a kan idanuwansu ba su san sa’adda ƙwalla ta cika muasu idanu ba suka fara zubar da hawayen tausayi.
Koda Sarauniya Abidat ta ga cewar ta yanke duk wata gaɓa da ke jikin dattijon sai kawai ta takarkare ta bushe da dariyar mugunta.
A dai-dai wannan lokaci ne numfashin dattijon ya sarƙe jikinshi ya sandare ya faɗi ƙasa, alamar dake nuna rai ya yi halinshi.
Kawai sai aka jiyo ihu da kururuwa a tsakiyar jama’a, koda Sarauniya ta duba sai ta ga ashe matar wannan dattijon ce ta rugo izuwa wajen, tana mai rusa kuka, hannayenta riƙe da jariri ɗan shekaru biyu da haihuwa.
Kafin matar dattijo Safwan ta iso wajen, Sarauniya Abidat ta zaro wani dogon mashi a jikin badakaren ta jefawa matar, mashin ya tafi cikin matsanancin gudu a cikin iska ya soke a ƙirji, ya fasa ta gadon bayanta jini ya kwaranya gami da tsartuwa, take ta sulale ƙasa tana shure-shuren mutuwa, kafin wani lokaci idanuwanta sun ƙafe, komai na jikinta ya daina motsi, alamar ta baƙunci barzahu, amma wani abu da ya ɗaurewa Sarauniya Abidat da sauran jama’a kai shi ne, duk da kasancewar matar dattijo Safwan ta sheƙa barzahu babu rai a tare da ita, amma hannunta riƙe yake da jaririnta gam! Kuma fuskarta cike da annuri.
Cikin matuƙar mamaki Sarauniya Abidat ta nuna jaririn da ɗan yatsan ta na hagu, take jaririn ya baro hannun mahaifiyarshi ya sauka a hannayenta biyu yana mai tsala kuka, koda ta ƙura wa jaririn idanu sai ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi, al’amarin da ya yi matukar ba ta mamaki, kenan ta ce a cikin ranta, “Me ya sanya da na haɗa idanu da wannan jariri zuciyata ta buga da ƙarfi alhalin hakan bai taɓa faruwa a gare ni ba?”
Amsar tambayar da ta kasa bawa kanta kenan kawai sai ta miƙawa wani badakare jaririn, sannan ta kama linzamin dokinta ta hau, ta zabure shi ta shige gaba dakarun ta suka mara mata baya, yayin da aka isa gidan Sarauta sai Saruaniya Abidat ta bayar da renon jaririn ga wata baiwarta mai suna Sunaifa, daga wannan rana Sarauniya Abidat ta kasance dare da rana face bincike bisa halarar tsafinta domin ta gano sirrin da ke tattare da jaririn dattijo Safwan.
Sa’adda ya rage saura kamar taku huɗu tsakanin su Sarki Urwat da karagar mulki sai suka zube ƙasa bisa gwiwoyinsu suka kwashi gaisuwa ga Sarauniya Abidat, cikin matuƙar taƙama da BAKAR IZZA Abidat ta karɓi gaisuwar.
Shiru ne ya mamaye fadar na ɗan wani lokaci sai daga bisani ne Sarki Urwat ya dago da kanshi sama ya buɗi baki cikin ladabi ya ce “Ya shugabata gani na amsa kiran ki kuma tare da abin da ki ka buƙata domin FANSAR RAYUKAN jama’ata.”
Koda jin wannan batu daga bakin Sarki Urwat sai Sarauniya Abidat ta miƙe tsaye tsam! Daga kan karagarta ta tako
matattakalar fadar ta sauko ƙasa, sannan ta taka da kafafuwanta har izuwa inda Sarki Urwat da jama’arshi ke duƙe ta shiga kewaya su tana mai bushewa da dariyar mugunta a lokaci guda kuma sai ta turɓune fuska tamkar an aiko mata da SAKON MUTUWA ta dubi sarki Urwat ta ce “ya kai Urwat ka bi dukkanin wani umarni da muka baka sai dai a halin yanzu ina so ka umarci mutanen ka su fice daga birnin Nurul-Kusuf su nemi wajen da za su zauna.”
Koda jin wannan batu daga bakin sarauniya Abidat sai idanun sarki Urwat suka zazzaro, cikin alamun matuƙar kaɗuwa da firgici ya dubi sarauniya Abidat cikin biyayya ya ce.
“Haba ya sarauniyar duniya ta ya ya zan cewa al’ummata su fice daga birnin Nurul-Kusuf bayan cewa tun iyaye da kakanni suke zaune sannan fiye da rabin harajin da na kawo miki sune suka haɗa rabinshi ina neman alfarma a wajen ki da ki janye wannan ƙudiri na ki.”

Da jin wannan batu sai sarauniya Abidat ta bushe da dariyar mugunta a karo na biyu daga bisani ta haɗe rai ta ce, “Tabbas duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, kuma rashin sani ya fi dare duhu” ya kai Urwat ka yi sani cewa, tun da nake a rayuwata kai ne mutum na farko da na taɓa faɗar magana ya ce ba haka ba, yanzu zan gindaya maka sharuɗɗa guda biyu dole ne ka zaɓi ɗaya daga ciki. Na farko shi ne ko dai kai da jama’arka ku fice daga birnin Nurul-Kusuf ko kuma ku bayar da ZARATAN MAYAKAN KU mutum hamsin.”
Sa’adda Sarki Urwat ya ji waɗannan sharudɗa daga bakin Abidat sai ya sake marairaicewa, yana mai yiwa yi mata magiya a kan ta janye waɗannan sharudɗa na ta.
Al’amarin da ya jefa tausayi a zukatan jama’ar kenan kuma zukatansu suka kama tafarfasa tamkar za su kone, bisa ganin yadda Urwat ke ƙasƙantar da kanshi a gaban wacce bata huce ‘yar cikin shi ba.
Su kansu sauran jama’ar fadar sai da suka kamu da matukar tausayin shi.
Ya yin da Abidat ta fahimci cewa Sarki Urwat ba shi da niyyar amincewa da ɗaya daga cikin sharuɗɗan da ta gindaya mashi sai kawai ta yi wuf ta zare wata sharɓeɓiyar takobi a gadon bayanta ta datse masa wuya, take kanshi ya yi fitar burgu gangar jikin ya faɗi ƙasa rikica! JINI ya yi tsartuwa haɗe da feshi tamkar an buɗe kan famfo.
Kafin ɗaya daga cikin jama’ar marigayi sarki Urwat ya yi wani yunƙuri sarauniya Abidat ta afka masu da azababben yaƙi cikin abin da bai gaza daƙiƙa talatin ba gaba ɗaya ta sare kawunansu ta zubar da gawarwakinsu a ƙasa ɗayan su bai tsira da rayuwarshi ba, nan fa jini ya dinga malala tamkar an ɓalle ƙorama. Sannan aka ga Abidat ta runtse idanunwanta ta karanto waɗansu ɗalasiman tsafi, tana gama rufe bakinta sai aka ga wani baƙin hayaƙi ya ratso daga cikin karkashin ƙasa ya tashi izuwa saman fadar ya ɓace ɓat! Kawai sai ta sake bushewa da dariyar mugunta tamkar ba za ta daina ba.

Mu haɗu a babi na hudu domin cigaban wannan ƙayataccen littafi
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Karshen Zalunci book 1 end
Littafan yaki
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071
BABI NA HUƊU

A can birnin Nurul-Kusuf kuwa, shugaba Hushaib na zaune a fada bisa karagar mulki a matsayin halifan Sarki Urwat ana gudanar da sha’anin mulki cikin walwala. Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai aka ga sararin samaniya ta yi duhu dunɗum! tamkar hadari ya gangamo, nan take gari ya kaure da guje-guje haɗe da iface-ifacen jama’a.
Har shugaba Hushaib ya buɗi baki da nufin ya ce wani abu sai aka hango sarkin yaƙi ya shigo fadar hankalinshi a matuƙar tashe, tun kafin ya iso inda karagar mulki take shugaba Hushaib ya je ya tare shi ya dube shi cikin alamun tsananin damuwa ya ce, “Ya dirkar birnin Nurul-Kusuf shin mene ne ke faruwa?”


Koda jin wannan tambaya sai sarkin yaƙi Ikram ya dube shi cikin tashin hankali ya ce, “ya shugabana ka yi sani cewa tabbas yau ce rana ta farko da zamu fita yaƙi iya tsawon kafuwar wannan birni namu domin kuwa waɗansu irin halittu ne suka sauka a wannan birni namu, ni kaina tunda nake ban taɓa ganin irinsu ba ko a labari.
Koda jin wannan batu daga bakin sarkin yaƙi Ikram sai shugaba Hushab ya dube shi cikin kaɗuwa ya ce, “Haƙiƙa na ji a jikina cewa shugaba Urwat da tawagarshi na cikin halin tsaka mai wuya kuma waɗannan halittu da suka bayyana a garemu ba sa rasa nasaba da abin da ya faru da su a can birnin Sin ɗin saboda haka sai ka yi umarni a yi maza a je a buga kugen yaƙi domin a tari abokan gaba…”


Kafin shugaba Hushaib ya gama rufe bakinshi sarkin yaƙi ya juya, ya fice daga fadar da sauri.

***
A can fadar sarauniya Abidat kuwa sai da tayi dariya ta ishe ta sannan ta yi umarnin a kwashe gawarwakin sarki Urwat da jama’arshi kuma aka goge jinin da ya zuba a fadar, sannan ta koma kan karagarta ta mulki ta hakimce.
Kawai sai ta zura hannunta a cikin aljihunta na hagu ta ɗauko madubin tsafinta wanda duka tsawonshi bai wuce girman faɗin tafin hannunta ba ta shafeshi da hannun hagu tana mai karanto waɗansu ɗalasiman tsafi, tana gama rufe bakinta sai ga taswirar abin da ke gudana a birnin Nurul-Kusuf ya bayyana a kan madubin.


Sa’adda sarauniya Abidat ta ga yadda waɗannan miyagun halittu da ta tura ke hallaka jama’ar marigayi Urwat ba ji ba gani tamkar suna kashe kiyasai, hatta dabbobin garin ba sa
ƙyalewa ballanatana ƙananan yara.
Koda ganin wannan al’amari sai farin ciki ya cika zuciyarta haka dai ta ci gaba da kallon yadda artabun ke gudana har kawo izuwa lokacin da halittun suka kammala kashe duk wata halitta da ke birnin kasancewar su ma su shugaba Hushaib ba karamar ɓarna suka yi masu ba.
Jim kaɗan sai taswirar birnin ya ci gaba da canja launi har ya nuno taswirar wata mata tana gudu a bisa doki, a cikin daji waɗannan halittu na biye da ita a baya suna so su cimmata amma sun gaza.
Ba wata ba ce wannan mata ba face Suhaimat matar marigayi sarki Urwat, Suhaimat na cikin gudun ne ta iso wani waje mai tattare da kwazazzabai al’amarin da ya sanya gudun dokinta, ya ragu kenan, kuma ya bawa ɗaya daga cikin halittun dama ya samu nasarar mako ta daga kan dokinta.
Kash! Hakika rashin sani ya fi dare duhu, ashe inda dokin Suhaimat ya durfafa wani ƙaton rami ne wanda a ƙarƙashin shi akwai ruwa, koda wannan halitta ta make Suhaimat daga kan dokin sai ta ci gaba da mirginawa a ƙasa ya yin da ta isa daf da ramin ta ga inda za ta afka sai kawai ta taƙarƙare ta kwarara wawan ihu take numfashinta ya ɗauke.


Sa’adda taswirar ta zo dai-dai nan akan madubin tsafin sarauniya Abidat sai ta bushe da dariyar farin ciki, ta mayar da madubin izuwa cikin aljihunta sannan ta sake miƙewa tsaye tsam! Daga kan karagar mulkin ta ta durfafi wata ƙofa da za ta sada ta da gidan sarautar dakaru na take mata baya.
Nan take sauran jama’a suka miƙe daga wajen zamansu suka fice daga fadar suna masu faɗar albarkacin bakunansu bisa wannan tsantsar zalunci da Abidat ta yiwa Sarki Urwat da talakawansuhi, wasu har suna
rokon abin bautarsu da ya a kawo KARSHEN ZALUNCIn Sarauniya Abidat.
Lokacin da Suhaimat matar
Margayi Sarki Urwat ta faɗa izuwa cikin wannan rami mai zurfi cikin halin suma sai igiyar ruwa ta ci gaba da tafiya da ita, sai da gari ya waye sannan igiyar ruwan ta kawo gaɓar tekun, kusa da wani daji ma’abocin tarin bishiyu da duwatsu da ƙoramu, kuma ya tara kayayyakin ni’ima, waɗansu irin kyawawan tsuntsaye na shawagi a sama suna fitar da sauti mai daɗin sauraro.


Ya yin da hasken rana ya fito sosai sai Suhaimat ta farka daga dogon suman da ta yi tana mai jan dogon gwauron numfashi, kuma ta buɗe idanuwanta ta miƙe zaune koda ta ga a inda take hawayen baƙin ciki suka zubo daga idanuwanta.


A sannan ne ta ji yunwa da kishirwa sun addabeta kuma raunikan da ke jikinta
suna yi mata raɗaɗi da zugi, don haka sai ta miƙe tsaye da ƙyar ta shiga izuwa dajin domin ta samu abin da za ta yi kalaci.
Daga wannan rana Suhaimat ta kasance a cikin dajin ba ta da abokan ɗebe mata kewa face tsuntsaye, a duk sa’adda ta tuna maigidanta marigayi Sarki Urwat da jama’ar birnin su sai ta fashe da kukan baƙin ciki.
Amma da zarar ta tuna cewa tana ɗauke da juna biyu sai ta cika da matuƙar farin ciki domin ta san cewa za ta haifi abin da zai dawo mata da farin cikinta kuma ya kawo KARSHEN ZALUNCIn Sarauniya Abidat Sa’adda Suhaimat ta fahimci cewa juna biyunta ya cika wata tara. A koda yaushe naƙuda za ta iya kamata ta haife abin da ke cikinta, sai ta yanke shawarar ta ci gaba da tafiya domin ta samu wani birni a gaba da za ta haife abinda take ɗauke da shi.
Sai da ta shafe tsawon kwanaki huɗu tana tafiya a ranar kwana na biyar ne lokacin da rana ta take ta yi tsananin zafi Suhaimat ta iso wani kasaitaccen birni tun da ta shiga birnin ta kama kalle-kalle da dube-dube tamkar ɗan ƙauye ya shigo birni a iya tsawon rayuwarta bata taɓa ganin birnin da ya ƙawatu kamarshi ba, tana mai tambayar kanta a cikin ranta tana cewa shin wannan wane birni ne na shigo? Kuma a wace nahiyar nake.

Amsar tambayoyin da ta kasa bawa kanta kenan, kawai ta ci gaba da tafiya a cikin birnin, tana cikin tafiya ne ta zo giftawa ta cikin kasuwa sai ta ji waɗansu dattawa guda biyu suna hira a tsakanin su a inda ɗayan ya dubi ɗan uwanshi ya ce, “Shin wai kuwa ka ji labarin abin da ya faru da Sarki Urwat na birnin Nurul-Kusuf da jama’ashi na kisan wulakancin da Sarauniya Abidat ta yi masu.”
Ɗayan ya ce, “Kwarai kuwa na samu labari kuma na jinjina al’amarin matuƙa, fatana shi ne a samu wani GWARZON ƘARNI da zai kawo maka KARSHEN ZALUNCIN wannan sarauniya tamu.”
Sa’adda Suhaimat ta ji abin da dattawan ke tattaunawa a kai sai zuciyarta ta kama tafarfasa tamkar za ta ƙone ta ji ta tsani sarauniya Abidat fiye da komai a rayuwarta.
Kuma a sannanne ta fahimci wannan birni da ta shigo shi ne birnin Sin tana tana cikin wannan hali wani tunani ya faɗo mata, tunanin kuwa shi ne ya zama wajibi ki fice daga wannan birnin matsawar kina bukatar ki haife abin da ke cikinki, domin da dazarar Abidat ta ganki ba za ta bar ki a raye ba.
Koda Suhaimat ta zo nan a tunaninta sai kawai ta ci gaba da tafiya da sauri domin ta fice daga birnin baki ɗaya.
Wannan shi ne dalilin da ya sanya dakaru Sarauniya Abidat ke farautar wannan mata wato Suhaimat matar marigayi Sarki Urwat na birnin Nurul-Kusuf.

SHIN SUHAIMAT DA JARIRIYARTA NA TSIRA DAGA SHARRIN DAKARUN SARAUNIYA ABIDAT!
WACE IRIN ƊAUKAKA
JARIRIYAR SUHAIMAT ZA TA SAMU A DUNIYA?
SHIN INA LABARIN ƊAN DATTIJO SAFWAN WANDA
SARAUNIYA ABIDAT TA BAYAR DA RENONSHI GA BAIWA SUNAILA?
WANE IRIN AZABABBEN YAƘI ZA A YI TSAKANIN DAKARUN SARAUNIYA ABIDAT DA WANNAN ZAKANYA?

Mu hadu a KARSHEN ZALUNCI 2 na biyu domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment