Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Karshen Zalunci book 2
Littafin yaki
Rubuta labari
Mansur Usman Sufi
08137237071
Babi na ɗaya

Sa’adda aka ci gaba da kallon-kallon tsakanin dakarun ke biye da Suhaimat matar marigayi sarki Urwat da wannan zakanya.
Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa talatin a na wannan kallo-kallo daga can sai dakarun suka zare makamansu suka zaburi dawakan su izuwa inda zakanyar take suna aihu da kururuwa mai firgitarwa.


Koda ganin hakan sai zakanyar ta sake dako wawan tsalle a karo na biyu ta dira a tsakiyar dakarun, tana gurnani mai ban tsoro.
Nan take aka ruguntsume da azababben yaƙi mai matuƙar muni da ban tsoro gami da ban al’ajabi.

Wohoho! Tabbas mai ƙarfi sai Allan ya isa ana fara wannan artabu ne wani abin al’ajabi ya fara gudana, domin halitta guda ɗaya jal ta addabi mutum dubu biyu ta zame masu alaƙaƙai sun rasa yadda za su yi da ita.
A duk sa’adda dakarun suka kaiwa zakanyar hari sai ka ga ta wurƙita haɗe da zamewa ta zillewa saran kafin badakaren ya sake ɗaga takobinshi, zakanyar ta dako tsalle sama ta sanya farantata ta tsire mashi idanu ruwan cikin ya tsiyaye take ya sulale ƙasa daga kan dokinshi yana mai kurma wawan ihu a wasu lokutan idan ta bangaji badakare a kirjinta take badakare da dokinshi za su make ‘yan uwansa dakaru fiye da goma sun zube a ƙasa matattu, kai wasu lokutan ma idan ta daki badakare a wuya sai ka ji ya karye ya yi ƙara ruƙus!! Ƙas! Ya faɗi matacce ko shurawa bai yi ba.


Haƙiƙa waɗannan dakaru suna ganin tashin hankalin da ba su taɓa ganin irin shi ba, domin kafin cikar rabin sa’a zakanyar ta kashe fiye da rabin su.
Babban abin da ya dugunzuma hankalin dakarun kuma ya fusata su shine. Gashi dai ƙiri-ƙiri suna saran zakanyar da makaman su amma sun kasa koda kwarzanar jikinta, nan fa dakarun suka fusata ainun suka zage damtse suna kaiwa zakanyar miyagun hare- hare.
Nan fa karafniyar ƙarafa da ihun mazaje, haniniyar dawakai haɗe da gurnanin zakanyar ya cika dajin baki ɗaya. Ƙura ta turnuƙe sararin samaniya saboda yadda dawakai ke yin turmutsutsu, kofatunsu na kartar kasa.

Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce idan wuya ta kai wuya sai ka ga ZARATAN MAYAƘA suna neman cika wandunansu da iska domin TSIRA DA RAYUKAnsu.


Hakanne kuwa ya faru ga sauran ‘yan tsirarun dakarun domin koda suka ga cewa a kowanne lokaci za su iya baƙuntar barzahu sai suka cika wandunansu da iska da nufin tserewa.
Amma sai zakanyar ta dinga ƙure masu gudu tana turmushe su suna faɗuwa ƙasa matattu, kafin wani lokaci ta zubar da gawarwakinsu a ƙasa.
Koda samun wannan nasara sai zakanyar ta yi girgiza sannan durfafi inda Suhaimat ke kwance tare da jaririyar ta, koda ta ga halin da Suhaimat ke ciki sai ta ruga izuwa bakin wata ƙorama ta guntso ruwa a baki sannan ta dawo inda take ta fesa mata ruwan a kan fuskarta.
Faruwar hakan ke da wuya sai Suhaimat ta ja dogon gwauron numfashi gami da ajiyar zuciya, idanuwanta suka buɗe tarwai, kuma ta miƙe zaune ya yin da ta yi arba da wannan zakanya sai ta razana ta ja da baya tana mai ɗaukar jaririyarta ta ƙanƙame ta a kirji.
Koda ganin halin da Suhaimat ta shiga sai zakanyar ta juya ta ruga izuwa cikin wannan kogon dutse da ke cikin dajin.
Cikin matuƙar farin ciki Suhaimat ta miƙe tsaye ta matsa izuwa inda wannan ƙorama take ta yiwa jaririyarta wanka itama ta tsaftace ƙazantar dake jikinta, sannan ta dawo izuwa ƙarƙashin wata bishiya, ta zauna ta shiga shayar da jaririyarta tare da shafa gashin kanta zuciyarta cike da matuƙar farin ciki.
Kuma ta shiga tambayar kanta a cikin ranta tana cewa shin wane ne ya kashe waɗancan dakaru, ko kuwa wannan zakanyar ce?.
Amsar tambayoyin da ta kasa bawa kanta kenan, a cikin wannan hali ne zakanyar ta dawo izuwa gare ta, bakinta riƙe da waɗansu ƙunshin ciyayi ta ajiye a gaban ta a wannan karon bisa mamaki sai Suhaimat ta ji ko kaɗan ba ta tsora ta da ganin zakanyar ba.
Ba tare da fargabar komai ba Suhaimat ta ɗauki ta shiga warware ƙunshin, ai kuwa sai ta ga ashe nau’ikan kayan marmari ne a ciki, dangin su ayaba da inibi kawai ta shiga ci har sai da ta ƙoshi sannan ta fasa kwakwa ta shanye ruwanta zakanyar na tsaye a gefen ta tamkar mai jiran umarni,
a sannan ne ta lura cewa a jikin zakanyar akwai alamun jini take ta fahimci cewa ita ce ta hallaka waɗannan dakaru domin ta ceci rayuwarta da jaririyarta.

Mu haɗu a babi na biyu
Ƙasaitaccen littafin yaki mai cike abubuwan al'ajabi da darasin rayuwa
Karshen Zalunci book 2
BABI NA BIYU
Rubuta labari
Mansur Usman Sufi
08137237071
Dukkanin abin da ya wakana tsakanin Suhaimat, zakanya da dakarun sarauniya Abidat.
Abidat ta gani a cikin madubin tsafin ta tun daga farko har ƙarshe. Koda ganin wannan al’amari sai takaici da baƙin ciki suka turnuƙe ta ta ji tamkar ta kurma wawan ihu.
Ba komai ne ya sanya ta wannan baƙin ciki ba, sai domin ta tabbatar da cewa a halin yanzu Suhaimat da jaririyarta sun tsira daga sharrinta.
Babban abin da ya dugunzuma hankalin ta kuma ya jefata cikin damuwa ainun shi ne wani al’amari da ta gani a cikin madubin tsafin ta.
Ta gano cewar wannan jaririya da Suhaimat ta haifa ita ce za ta kawo KARSHEN ZALUNCIn ta daga doron ƙasa. Asalin dajin da Suhaimat ta haihu a ciki ya kasance mallakin wannan zakanya mai tattare da abubuwan al’ajabi ana kiranta da suna Juraima.
Binciken bokaye da MATSAFAN DUNIYA ya tabbatar da cewa dajin Baitul-Shazwas na ɗauke da wata takobi ta musamman mallakin sarkin bokayen aljanu na duniya Sababul-Ukub, babu wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai mallaki takobin face ya zamewa duniya ANNOBA DARI.
MANYAN SARAKAI haɗe da matsafa
da JARUMAN DUNIYA sun rasa rayukansu bisa muradin mallakar takobin, domin zakanya Juraima ba ta barin duk wanda ya raɓi dajin a raye. Bisa dole bokayen suka janye ƙudurinsu na shiga dajin Baitul Shazwas domin mallakar takobin Saiful-Imfal.
Abinda binciken ya ƙara tabbatar masu shi ne babu wani mahaluki da zai mallaki takobin Saiful Imfal da zakanya Juraima face wata jariya da za a haifa a dajin na Baitul Shazwas, sai dai ba a bayyana masu ga nahiyar da za a haifi jaririyar ba.
kuma zakanya juraima na ɗauke rabin sirrikan tsafin sarkin bokaye a jikinta, takobin Saiful-imfal na ɗauke da sauran.
Tsakanin Sarauniya Abidat da zakanya Juraima akwai gaba mai tsanani tun iyaye da kakanni, domin mahaifinta da kakanta sun rasa rayukansu ne ta hanyar mallakar
takobin Saiful Imfal, kuma lokacin da mahaifinta yana raye ya gargaɗe ta a kan kar ta kuskura ta ce za ta shiga dajin Baitul-Shazwas domin ɗaukar fansa.

Nan fa Sarauniya Abidat ta ƙara cika da matuƙar baƙin ciki tana mai tambayar kanta a cikin ranta tana cewa.
“Hakika na tafka babban kuskure da har na bari Suhaimat ta shiga dajin Baitul-Shazwas yanzu gashi ta haife abin da ke cikinta yanzu shi kenan ba ni da ikon hallaka Suhaimat da jaririyarta har sai ranar da ta fito daga dajin Baitul Shazwas.”


Daga wannan rana Sarauniya Abidat ta kasance dare da rana bata aiki face gudanar da bincike a halarar tsafinta, domin ta gano lokacin da Suhaimat za ta fito daga dajin Baitul Shazwas.
Bayan Suhaimat ta kammala kintsa cikinta da waɗannan kayan marmari sai Zakanya Juraima ta juya, ta nufi kofar wannan kogon dutse tana mai yiwa Suhaimat nuni da ta biyo bayanta.
Ba tare da gardamar komai ba Suhaimat ta miƙe tsaye ta bi bayanta tana rungume da


jaririyarta a kirji, da shigarsu cikin kogon dutsen sai ke da wuya sai Suhaimat ta ga kogon ya gauraye da wani irin haske na ban al’ajabi, sannan yana cike da dukkanin kayan more rayuwa da ɗan adam zai bukata, kai wani abin ma Suhaimat ba ta taɓa gani ko jin sunan shi ba.
Al’amarin da ya yi matuƙar ɗaure mata kai kenan kuma ya ba ta mamaki ta kama kalle-kalle da dube-dube.
Ba tare da ta jira wani umarni daga Zakanya Juraima ba sai kawai ta je ta kwantar da jaririyarta bisa wata shimfiɗa ta lulluɓe ta da mayafi sannan itama ta kwanta domin ta rintsa amma sai hakan ya gagara, ba komai ne ya haddasa hakan ba, sai domin raunukan da ke jikinta na yi mata zugi da raɗaɗi kuma inda wannan badakare ya harɓe ta da kibiya yana yi mata ciwo.


Sai da zakanya Juraima ta kawo mata wani ganyen bishiya ta murza ta sanya a raunukan, sannan ta kwanta barci ya ɗauke ta.
Wannan shi ne abin da ya faru da Suhaimat matar marigayi sarki Urwat na birnin Nurul-Kusuf a lokacin da ta tsira daga sharrin sarauniya Abidat ta birnin Sin.

Al’amarin baiwa Sunaila kuwa tun sa’adda sarauniya Abidat ta bata renon jaririn dattijon Safwan, sai ya zamana cewa dare da rana tana bawa jaririn kulawa, kuma suka shaƙu da juna ainun ya yi wayo sai Sunaila ta sanya masa suna Himlas, ma’ana ma’abocin hikima da abubuwan al’ajabi, domin tun yana da shekaru huɗu ta fahimci cewa yana tattare da kaifin basira da jarumtaka.
Sannu-sannu ba ta hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba sai gashi Himlas ya girma ya zama cikakken saurayi.


Nan fa ya zamana cewa ya zama zarra a tsakanin sauran ‘yan uwanshi bayi, a wasu
lokutan idan suna ba wa juna horon yaƙi suka yi masa rubdugu amma sai ka ga ya tarwatsa su ta karfin tsiya.
Wata rana Himlas ya dawo daga farauta yana zaune tare da baiwa Sunaila a cikin ɗaki sai ya lura cewa tana cikin damuwa.


Don haka sai ya dube ta ya ce “Ya Ummina shin mene ne dalilin wannan damuwa ta ki?”
Koda jin wannan tambaya sai baiwa Sunaila ta yi murmushi a gare shi, mai tattare da takaici sannan ta sanya hannayen ta biyu ta dafa kafaɗunshi ta dube shi cikin alamun tsananin damuwa ta ce.

“Ya ɗana abin alfaharina ki yi sani cewa ba komai ne ya sanya ni a cikin wannan damuwa ba sai domin na san cewa duk daren daɗewa ɓoyayyen sirrin da na daɗe ina ɓoye maka zai fito fili ƙarara.”
Koda jin wannan batu sai idanun Himlas suka zazzaro cikin tsoro ya kama sa cikin alamun rashin fahimta ya dubi Sunaila ya ce. “Ya Ummina ban fahimci abin da kike nufi ba, shin wane sirri ne ki ke son bayyana mani.”
Sunaila tayi ajiyar zuciya sannan ta kawo gwauron numfashi, ta ajiye kana ta yi gyaran murya ta ce, “ya ɗana ka yi sani cewa a yau ne zan bayyana maka sirrin da na daɗe ina ɓoye maka, ya farin ciki na ka yi sani cewa kamar yadda kake tsammani cewa ni ce mahaifiyarka to ba ni ce na haife ka ba.” Nan take Sunaila ta kwahse labarin kaf abin da ya faru tsakanin dattijo Safwan da Sarauniya Abidat da irin mugun kisan gillar da ta yiwa mahaifinsa tun daga farko har ƙarshe ta zayyanewa bawa Himlas.
Sa’adda baiwa Sunaila ta zo dai-dai nan a labarinta sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya shima Himlas bai san sa’adda ya fashe da kukan ba, yana mai rungume ta yana mai cewa “ba zan taɓa canja ki ba har abada ke ce Ummina.”
Inda ace mutum yana wannan waje lokacin da wannan al’amari ke faruwa dole ne ya kamu da tsananin tausayin Sunaila da bawa Himlas.
Sai da suka ɗauki wani lokaci a cikin wannan hali sannan daga bisani Sunaila ta janye jikinta daga na Himlas ta dube shi a lokacin da hawaye ke ci gaba da kwaranya daga idanunta ta ce.
“Ya ɗana ka yi sani cewa ba komai ne ya sanya na ɓoye maka wannan sirri ba sai domin ba na so ace na rasaka a rayuwata, a halin yanzu kai kaɗai ne ka rage mini ba ni da kowa.”
Da jin wannan batu sai hawaye suka sake zubowa daga idanun Himlas ya ji ya tsani Sarauniya Abidat fiye da komai rayuwar shi.
Sunaila ta sanya hannunta ta share hawayen da ke fuskarta, sannan ta ci gaba da cewa, “Duk abinda za ka yi ina roƙon ka kada ka ce za ka ɗauki fansa a kan sarauniya Abidat a halin yanzu domin ba za ka taɓa samun nasara ba, jikina ya ba ni cewa akwai wani ma’abocin ɗaukaka da zai zo ya cire mu daga cikin wannan KANGIN BAUTA kuma ya taimake ka ka kawo KARSHEN ZALUNCI na sarauniya Abidat.”
Sa’adda Sunaifa ta sake zuwa dai-dai nan a zancen ta sai Himlas ya sanya hannunsa ya share mata hawayen da ke fuskarta yana mai cewa, “Ki daina kuka ya ummina duk abin da ki ka ce shi za a yi domin farin cikin ki shi ne nawa.”
Koda Himlas ya zo nan a zancen shi sai Sunaila ta sake fashewa da kukan farin ciki tana mai sake rungume shi tana cewa, “Ina alfahari da kai ya ɗana kai ne cikar burin rayuwata na tabbata cewa kai ne za ka kawo KARSHEN ZALUNCIn sarauniya Abidat daga doron kasa.”
Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin baiwa Sunaila da Bawa Himlas dan dattijo Safwan, wanda Sarauniya Abidat ta bayar da renonsa a hannun Baiwa Sunaila bayan ka yiwa mahaifinsa kisan gilla.

Mu haɗu a babi na uku domin jin cigaban wannan ƙayataccen littafi
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
MANSUR USMAN SUFI
08137237071
Karshen zalunci book 2
Babi na uku
Rubuta labari
MANSUR USMAN SUFI
08137237071
A can dajin Baitul-Shazwas kuwa, Suhaimat da jaririyarta na cikin ƙoshin lafiya walwala da jin daɗi.
Sannu-sannu ba ta hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba sai kwanci tashi sai ga shi jaririyar Suhaimat ta cika shekara sha biyar da haihuwa, da ranar haihuwar ta zagayo ne aka raɗawa jaririya suna Sulairat bintu Urwat.
Kyan ɗa ya gaji ubanshi, kamar yadda marigayi sarki Urwat ya kasance GWARZON MAYAƘI ma’abocin hikima, haka Sulairat ta kasance.
Wasu lokutan idan Sulairat da zakanya Juraima na bawa junansu horon yaƙi sai ka ga Sulairat ɗin ta samu nasara akan Juraima. kasancewa Sulairat ba ta da abokan ɗebe kewa sai zakanya Juraima sai suka shaƙu ainun kwanciyar barci ce kaɗai ke raba su ko farauta Sulairat za ta je bisa gadon bayan Juraima take hawa su tafi tare.
Idan a kazo batun kyawu kuwa Sulairat ta gaji mahaifiyarta Suhaimat har ta ɗarata ne sa ba kusa ba, kasancewar a koda yaushe ba su da wani abin kalaci da ya wuce naman tsuntsaye da nau’ikan kayan marmari sai ya zamana cewa fatar jikinta ta yi lub-lub ta yi kyau da sheki tamkar a tsaga ta jini ya fito.
Wata rana da hantsi bayan Sulairat da mahaifiyar ta sun yi kalaci suna zaune a cikin wannan kogon dutse sai Sulairat ta dubi mahaifiyarta ta yi gyaran murya sannan ta ce.
“Ya Ummina shin ina Abbana yake, ya tafi ya bar mu a cikin wannan daji, ko kuwa mu kaɗai ne bil’adama a wannan duniya?”
Koda jin wannan tambayoyi sai Suhaimat ta yi murmushi mai taushi a gare ta, sannan ta dubeta ta ce, “Ke kuwa me ya sa ki ka yi mini waɗannan tambayoyi, bayan cewa kina tare da ni ina yi miki duk wani abu da ki ke buƙata na rayuwa.”

Sulairat ta ce “ya ummina ke kuwa mene ne ya sa duk sa’adda na yi maki waɗannan tambayoyi ba kya amsa su, tabbas akwai wani al’amari da kike ɓoye mini wanda ba kya so na sani.”
Koda ji wannan batu sai zuciyar Suhaimat ta buga da ƙarfi kuma hankalinta ya dugunzuma ainun ta ce a cikin ranta, tabbas rashin bayyana wa Sulairat gaskiyar lamari na iya sanyawa mutuncina ya ragu a idanunta, sannan kuma idan har na sanar da ita dole ne ta ce za ta je ta ɗauki fansa.


Wani ɓangaren a zuciyarta kuma na cewa da ita ai babu wata mafita face ki sanar da Sulairat gaskiyar lamari, domin ai duk daren daɗewa dole ne ta sani.
Koda Suhaimat ta zo daidai nan a tunaninta sai ta dubi Sulairat ta ce “Ya ‘yata ki yi sani cewa a yau ne zan ba ki amsar tambayoyin da ki ka daɗe kina yi mani, na cewa ina abbanki yake.”
Nan take Suhaimat ta shiga bawa Sulairat labarin mahaifinta sarki Urwat da irin kisan gillar da Abidat ta yi mashi tare da jama’ar birnin su, har kawo izuwa lokacin da zakanya Juraima ta ceci rayuwar su daga sharrin dakarun Abidat daga farko har ƙarshe ta zayyanewa Sulairat.


Sa’adda Suhaimat ta zo dai-dai nan a labarin ta sai ta fashe da kukan baƙin ciki tana mai rungume ‘yarta su duka biyun suna zubar da hawaye tamkar ba za su daina ba.
Sai daga bisani ne Suhaimat ta janye jikinta daga na Sulairat har ta buɗe baki da nufin ta ce wani abu sai suka ji alamun motsi a bayansu, koda suka waiga sai suka ga ashe zakanya Juraima ce a tsaye idanunta sharkaf da hawaye.
Al’amarin da ya yi matuƙar bawa Sulairat da mahaifiyar ta mamaki kenan, abinda ba su sani ba shi ne dukkanin hirar da ta gudana tsakaninsu zakanya Juraima ta ji, saboda haka tsananin tausayinsu ne itama ya sanya ta zubar da wannan hawaye.
Suhaimat ta ci gaba da cewa, “Ba komai ne ya sanya na ɓoye miki wannan sirri ba, sai domin sanin cewa za ki iya yunƙurin ɗaukar fansa a kan sarauniya Abidat a halin yanzu.


“Ina so ki kwantar da hankalinki ki sani cewa lokaci zai zo da za ki shiga har cikin birnin Sin ki ɗauki fansa a kan Sarauniya Abidat ki kawo KARSHEN ZALUNCIn da take shimfiɗawa al’umma.”
Da jin wannan ƙarin wajabi sai Sulairat ta ji ta daɗa ƙaunar mahaifiyarta fiye da ko yaushe.
Sannan ta sake duban mahaifiyarta ta ce “Ya Ummina idan ba za ki damu ba ina neman wata alfarma a wajenki.”


Cike da matuƙar mamaki Suhaimat ta dube ta ta ce “faɗi alfarmar da kike nema a waje na ni kuwa zan yi miki ita.”
Sulairat ta numfasa sannan ta gyaɗa kai ta ce, “alfarmar da nake nema a wajen ki ita ce ki amince na shiga birnin Sin domin kawai na ga yadda sauran bil’adama irinmu ke rayuwa.”
Koda jin wannan alfarma sai Suhaimat ta dubi ‘yarta cikin alamun tsananin damuwa ta ce, “Haba ya ‘yata yanzu ta ya zan bar ki ki ziyarci birnin Sin bayan cewa a koda yaushe Sarauniya Abidat na farautar rayuwarki.”
Ya yin da Sulairat ta zo nan a zancen ta, sai ta hango zakanya Juraima na yiwa Sulairat nuni da ta zo inda take.
Ba tare da gardamar komai ba Sulairat ta miƙe tsaye ta taka da kafafuwanta har zuwa inda zakanya Juraima ke tsaye, da zuwanta sai Juraima ta yi mata nuni da ta tona wani waje a kogon da ke saitin kafarta.
Cikin hanzari Sulairat ta tsugunna ƙasa ta sanya hannayenta biyu tana ƙwakule kasar wajen ta yi rami da girmanshi bai huce kamu ɗaya ba, sai ta ji ta taɓo wani abu tamkar ƙarfe ya yin da ta ciro shi, sai ta ga ashe wata sarƙa ce fara sol da aka yi ta da ƙarfe jauhari, sai sheƙi take yi tana ɗaukar idanu.
Kawai sai zakanya Juraima ta yi mata nuni da ta sanya sarƙar a wuyanta.
Sannan Juraima ta yi wa Suhaimat ishara da ta ƙyale Sulairat ta ziyarci birnin Sin tana yi mata nuni da cewa wannan sarƙa da Sulairat ta sanya a wuyanta za ta bata kariya har ta je ta dawo lafiya.
Koda fahimtar hakan sai Suhaimat ta dubi ‘yarta ta ce “Na amince ki ziyarci birnin Sin kuma ina yi maki fatan samun nasara.”
Da jin hakan sai murna ta kama Sulairat ta yi godiya ga mahaifiyrta sai ta juya ta fice


daga kogon dutsen, sai da zakanya Juraima ta yi mata rakiya har izuwa gaɓar dajin Baitul-Shazwas sannan ta dawo bayan ta dora ta a kan hanya.

Kai tsaye Sulairat ta tasamma hanyar da za ta sadata da birnin Sin tun a kan hanya ta fara cika da matuƙar mamaki har ta isa birnin Sin domin sau tari za ta haɗu da miyagun namun daji amma sai ta ga sun ratse sun ba ta hanya, tamkar ba su ganta ba, ƙiri-ƙiri gashi masu gadin ƙofa na ganinta amma haka ta kunna kai zuwa ciki ba tare da sun yi yunƙurin afka mata da yaƙi ba, da shigarta zuwa birnin sai ta kama kalle- kalle da dube-dube tamkar dan ƙauye ya shigo birni.
Abin da Sulairat ba ta sani ba shi ne matsawar tana sanye da wannan sarka da zakanya Juraima ta ba ta, babu wani mai cutarwa da ya isa ya ganta, ya kusanci inda take ballantana har ya cutar da ita.
Haka dai Sulairat ta wanzu tana tafiya a cikin birnin Sin ta wanzu tana ratsa layuka da unguwanni, ba tare da ta haɗu da wani abu mai cutarwa ba.
Tana cikin tafiya a kasuwa ne sai kawai ta hango jama’a suna guje-guje da iface- iface, maza da mata yara da manya. Nan fa aka dinga barin kayan abinci, masu ƙarfi suka dinga bangaje masu rauni suna zubewa a kasa ana tattaka su.
Al’amarin da ya yi matuƙar bawa Sulairat mamaki kenan, kawai sai ta koma gefe guda ta ja ta tsaya, tana mai zuba idanu, domin ta ga abinda ya sanya jama’a suke GUDUN CETON RAYUKA.
Tana nan tsaye kwatsam sai ta hango dakaru masu tarin yawa shirye cikin matsananciyar shigar yaki sun shigo kasuwar su bisa tsakiyar dakarun wani
ƙasaitaccen keken doki ne da aka yi mata ado kayan kyale-kyale na sarauta.
Bisa cikin keken dokin wata budurwa ce a kishingiɗe sanye da tufafi na alfarma.
Budurwar ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance, ma’abociyar dara-daran idanuwa farare kal a cikin su akwai ɗigon baƙi, hancinta siriri ne gwanin ban sha’awa, tana da madaidaicin baki wanda leɓɓanshi suka kasance jajur, ƙirjinta a cike kuma ya tsaya kyam! Tamkar nunanniyar gwanda fatarsu
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment