Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za su bayyana a gare mu wacce ba ki taɓa ganin tamkar ta ba.
Da yardar tsafi abin dogaro sai kin cimma nasara.”
Koda jin wannan batu daga bakin ifritu Shammar sai bokanya Zulaima ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta mai kama da haniniyar doki, al’amarin da ya sanya baki ɗaya kogon dutsen ya kama girgiza tamkar zai tsaye.

Take ifritu Shammar ya ɓace ɓat! Daga kogon tamkar bai taɓa bayyana ba.
Ita dai bokanya Zulaima ta kasance gawurtacciyar matsafi da tayi shura a cikin bokaye har masu bincike da hasashe na duniya ke yi mata laƙabi da uwar matsafa,
Babban burin Zulaima shine ta mulki duniya baki ɗaya, bisa binciken da ta yi ne ta gano cewa dole sai ta mallaki ruhikan sarakunan duniya guda dubu shida ta tsafe su sun shiga jikinta, bisa wannan dalili ya sanya ta dinga farautar sarakunan tana hallaka su ta ƙarfin sihiri.
Wannan shi ne abin da ya wakana tsakanin uwar bokayen duniya bokanya Zulaima tare da sarkin matasan ifritai na duniya.

A can dajin Baitul-Shazwas kuwa kamar yadda bawa Himlas ya tsara haka al’amarin ya kasance wato a daren wannan rana suka kammala sanya dukkan tarkuna a dajin cikin kyakkyawa shiri, ta yadda komai kallon ƙurillar mutum ba zai iya gane an sanya abubuwa masu cutarwa a dajin ba.
Kashe gari tun da duku-dukun safiya aka hango ƙura ta turnuƙe sararin samaniya tamkar hadari zai gangamo a kece da ruwa. Koda ganin hakan sai kowa ya miƙe ya kimtsa jikin shi, Sulairat shigar kayan fata tayi tun daga ƙasa har sama a gadon bayanta tana rataye da wata rantsattsiyar kwari da baka, a gwiɓin cinyarta kuwa tana ɗauke da takobin Saiful-imfal wacce a daren jiya zakanya Juraima ta yi mata jagora izuwa inda takobin take ta ɗauko, a wuyanta kuwa tana rataye da sarƙar tsafinta kuma ta raba gashin kanta gida biyu ya zuba akan kafaɗunta.
Shigar ta yi matuƙar yi mata kyawu da kwarjini, bawa Himlas da Sunaila tare da Suhaimat shigar tufafi iri ɗaya suka yi sak gaba ɗaya sun rufe fuskokinsu da baƙin yanki idanuwansu kaɗai ake gani.
Cikin hanzari kowanne ya tsaya a matsayar shi kamar yadda aka tsara.
Sulairat ta tsaya a ɓangaren gabas tana zaune bisa kan zakanya Juraima, Suhaimat a yamma, Himlas kudu sai Sunaila a yamma.
Tsawon daƙiƙa ɗari aka shafe a cikin wannan hali sai daga bisani ne duhun dake sararin samaniya ya ye sai aka jiyo ƙarar takun sawaye haɗe da haniniyar dawakai ta cika dajin baki ɗaya.
A can bakin gaɓar shigowa dajin Baitul-Shazwas kuwa sarauniya Abidat tare da tawagar ta na ƙara kusantar dajin, lokacin da ya rage saura taku arba’in tsakanin su da dajin sai Abidat ta ɗaga hannunta sama aka tsaya can! A wannan lokaci Abidat tana sanye cikin baƙin sulken yaƙi tun daga ƙasa har sama kanta sanye da hular ƙarfe a gadon bayanta tana rataye da wata rantsattsiyar takobi a cikin kubenta, sanye a jikinta akwai makaman yaƙi fiye da guda ashirin, kaico! Haƙiƙa babu wani gwarzo da zai yi arba da Abidat a cikin wannan hali face ya razana domin shigar da tayi, shiga ce ta tawagar mutuwa.
A gefen hannunta na dama sarkin yaƙi ne cikin shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro.
Abidat ta ƙarewa dajin kallo tana nazarin shi zuwa can sai ta dubi sarkin yaƙi ta ce “ya dirkar birnin Sin kana ganin cewa su Sulairat ba su san da zuwan mu ba, ko kuwa wani tanadi suka yi mana domin su yi mana mamayar bazato?

Koda jin wannan tambaya sai sarkin yaƙi ya dube ta cikin ladabi ya ce “ya shugabata haƙiƙa abokan gabarmu sun shirya wani tuggu domin su mamaye mu, na tabbata cewa suna cikin wannan daji domin babu wani waje da zamu ɓuya da huce nan, sannan koda a ce ba su san da zuwan mu ba ai bayyanar mu ta zo masu domin hakan dole mu fara kai farmaki na somin taɓi.”
Koda jin wannan batu sai sarauniya Abidat ta ce “zancen ka dutse ya kai dirkar birnin Sin dole ayi hakan, sannan kasancewar ba ni da ikon shiga dajin Baitul-Shazwas dole ne mu tura dakarun mu su kai hari da yadda dole su Sulairat za su fito mu yi GABA DA GABA da su.”
Ya yin da sarauniya tazo nan a zancen ta sai sarkin yaƙi Hunaifu ya risina kawai sai ya yiwa waɗansu dakaru mutum dubu inkiya ta wutsiyar idanu, tamkar dakarun sun fahimci abin da yake nufi sai kawai suka sanya hannayensu suka ciro kibbau daga cikin kwarinsu suka tsoma su a cikin wani kuttu mai ɗauke da guba, kana suka sanya a cikin bakansu suka ja suka ɗame sannan suka harba. A lokaci guda kibban suka tafi cikin matsanancin gudu suka durfafi dajin, duk inda suka sauka sai wuta ta kama koda korran tsirrai ne sai wutar ya ƙonamu. Nan fa hayaƙi ya turnuƙe dajin wuta ta kama ci ganga-ganga.
Tsawon daƙiƙa ɗari ana cikin wannan hali al’amarin da ya fusata sarkin yaƙi Hunaifu kenan ya fara wasi-wasi ya fara tunanin shin ko su Sulairat sun yi nisa a cikin dajin.
Kawai sai ya dakawa dakaru dubu uku tsawa da ke nuna ba su umarni suka afka cikin dajin.
Cikin hanzari dakarun suka zaburi dawakansu suka durfafi dajin.
Kaico! Haƙiƙa rashin sani ya fi dare duhu kuma tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka inda ace waɗannan dakaru sun san abin da zai faru da ba su gangancin kutsa kai ba.
Lokacin da suka isa ciki nan take suka fara faɗawa tarkuna suna hallaka tare da dawakansu. Nan fa ihu da kururuwar mazaje ta cika dajin baki ɗaya
Sa’adda sarauniya Abidat taga yadda dakarunta ke yin mutuwar wulaƙanci sai takaici da baƙin ciki suka turnuƙe ta ta ji tamkar ta kunna kai izuwa cikin dajin amma da ta nuna babu halin hakan sai ta haƙura,
Kafin shuɗewar daƙiƙa hamsin fiye da mutum dubu na dakarun sun baƙunci barzahu, cikin hanzari sarkin yaƙi Hunaifu ya yi umarni a ja da baya, kamar taku goma sannan aka tsaya cak aka yi cirko-cirko.
Sai da ƙura ta lafa sannan aka jiyo ihu da gurnanin zakanya Juraima daga can sai ga su sun ratso ta duhuwar bishiyun sun bayyana a fili.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin ɓangarorin biyu cikin matuƙar ƙiyayyar juna da mugun tanadi.
Daga can dukkan ɓangarorin biyu suka yunƙura izuwa kan juna gami da falfalwa da azababban gudu, suna ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAƘA, lokacin da ya rage saura kamar taku shida tsakani sai sarauniya abidat ta dako wawan tsalle daga kan dokinta tun a sama ta zare takobinta ta kaiwa Sunaila wawan sara.
Cikin baƙin zafin nama irin na GAWURTACCIYA ta zare takobin Saiful-imfal ta kare harin, koda takubban suka haɗu da juna nan take aka kwantsama wata tsawa gami da walƙiya marar daɗin sauraro wacce ta sanya bishiyu karairayewa suna haɗu izuwa kan mayaƙa da dama suka faɗi ƙasa matattu.

Sannan Abidat ta sauka ƙasa cikin gwaninta bisa diga-diganta.
A dai-dai lokacin ne bawa Himlas ya tari sarkin yaƙi Hunaifu, baiwa Sunaila da Suhaimat kuwa suka kutsa izuwa cikin abokan gaba.
A lokaci guda duka ɓangarorin suka haɗu da juna aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini muni daban tsoro,
Kaico! Haƙiƙa duk wanda bai ziyarci filin yaƙi ba to bai ga maƙurar tashin hankali ba. Domin yaƙi shine ke sanyawa a rasa rai, dukiya, da mutunci baki ɗaya.
Wohoho! Idan gwani ya haɗu da gani a filin fama dole yaƙi ya zamo gwanin sha’awa da tashin hankali.
A ɓangaren manyan giwaye biyu Sarauniya Abidat da jaruma Sulairat kuwa gaba ɗaya sun ɗauki hankalin duk wata halitta dake filin yaƙin, domin kuwa suna artabun ne cikin gwaninta da ƙwarewa tamkar na’ura ce ke sarrafa su, jikkunansu ba su kasance na jini da tsoka ba, ita kuwa zakanya Juraima aiki biyu yake tana kaiwa sarauniya abidat hari tare da farmakar dakaru tana yi masu ɓarna.
A ɓangaren Bawa Himlas da sarkin yaƙi Hunaifu kuwa sun wanzu suna kaiwa juna hare-haren cikin JURIYA DA BAJINTA irin ta ‘yan MAZAN JIYA, duk sa’adda takubbansu suka haɗu da juna sai kaga tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara marar daɗin saurare.
Suhaimat da Sunaila kuwa duk inda suka sanya a gaba sai dai kaga dakaru na zubewa ƙasa magashiyan waɗansu matattu.
Wohoho! Haƙiƙa komai hassadar mutum idan ya ga yadda Waɗannan zaratan mataye ke ragargazar ‘yan maza suna maishe su mataye, dole ne ya jinjina masu ya tabbatar cewa tabbas sun cika mataye masu kamar maza kuma zaratan mayaƙa.
Sai da aka shafe tsawon sa’a ɗaya da rabi ana wannan ɗauki ba daɗi.
Nan fa ƙura ta turnuƙe sararin samaniya tamkar hadari ya gangamo, ƙarar karafniyar ƙarafa, ihu da kururuwar mazaje haɗe da haniniyar dawakai suka cika dodon kunne.
Haƙiƙa a wannan rana dakarun sarauniya Abidat suna ganin tashin hankalin da ba su taɓa ganin tamkar ta ba.
Ana cikin wannan karon batta ne sarauniya Abidat ta kaiwa Sulairat wani wawan sara da takobinta a kafaɗa da nufin tsinke mata wuya.
Cikin wani irin baƙin zafin nama Sulairat ta wurƙila da zillewa harin gami da mayar da martani, koda Abidat ta sanya takobin da nufin karewa take ta karya gida biyu ta faɗi ƙas.
Kafin ta yi wani yunƙuri Sulairat ta dunƙule hannunta ɗaya ta kirɓa mata wawan naushi a fuska, saboda ƙarfin naushin sai da Abidat ta yi sama ta sauka daga kan dokin ta tayi katantanwa sau biyu sannan ta faɗi ƙasa amma sai ta miƙe tsaye zumbur!
Tana mai gyara tsayuwarta, koda ta sanya hannunta ta shafa kumatunta nan take taga jini a inda Sulairat ta naushe ta ɗin.
Koda ganin hakan sai sarauniya Abidat ta cika matuƙar baƙin ciki, kawai sai ta taƙarƙare ta kwarara wawan ihu ta zare sabbin makamai biyu a jikinta ta sake afkawa Sulairat a karo na biyu, suka ruguntsume da sabon artabu.
Abu kamar wasa sai gashi dukkanin makaman yaƙin Abidat sun karairaye sun faɗi ƙasa.
Abin da bata sani ba shine har abada babu wani makami da zai iya yin tasiri akan takobin Saiful-imfal, bisa wannan dalili ya sanya makamanta suka lalace.
Nan fa taurarin biyu suka ja da baya suna haki da zufa, suna hararar juna tamkar waɗansu zakaru saboda yadda suka bawa hammata iska.
Ita zakanya Juraima sai ta dinga buga ƙafarta ɗaya a ƙasa tana gurnani domin shirin kar-ta-kwana.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga sararin samaniya ta yi duhu dunɗum! Tamkar dare biyu ne ya haɗu waje guda, sannu a hankali sai aka hango waɗansu irin halittu marasa adadi na ketowa daga cikin gajimare suna sauka a bisa turba, duk sa’adda ɗayansu ya saukan sai ƙasa ta amsa, ya yin da halittun suka kammala sauka sai suka yiwa dajin ƙawanya.

Nan fa dawakai suka firgice suka kama haniniyar suna zubar da mahayansu suna nausa cikin daji bisa arba da suka yi da halittun.
Su dai halittun suna matuƙar muni, kwarjini daban tsoro. Baki ɗayan su suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini, hannayensu ɗauke da miyagun makamai.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su Sulairat Abidat da tawagar halittun.
Daga can nesa kaɗan sai aka jiyo ƙarar takun sawayen dawakai haɗe da haniniyar su, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, sannu a hankali sai aka hango tawagar mayaƙa guda biyu mabanbanta sun durfafi sansanin.
Lokacin da yazamana tazarar dake tsakani bata huce kamu ashirin ba, sai dukkanin su suka yi turjiya suka tsaya cak!
Sa’adda zakanya Juraima taga abin da ke faru na bayyanar waɗannan baƙin rundunoni uku sai kawai ta yi wani gurnani. Ashe Sulairat ta fahimci abin da take nufi don haka sai kawai ta murza wannan sarƙar tsafi dake wuyanta.
Nan take su duka jama’arsu suka ɓace ɓat! Daga filin artabun tamkar ba su taɓa wanzuwa ba.
Cikin matuƙar takaici da baƙin ciki sarauniya Abidat ta taƙarƙare ta kurma wawan ihu a karo na biyu tamkar baza ta daina ba.

Mu haɗu a babi na uku domin jin cigaban wannan ƙayataccen littafi.

Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.

MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071Ƙarshen Zalunci book 3
Babi na uku
Mansur Usman Sufi
Kaico! Haƙiƙa a wannan rana sarauniya Abidat tayi matuƙar baƙin ciki da bata taɓa yin tamkar shi ba, kuma ta kunyata a idanun talakawanta.
Tsawon daƙiƙa goma tana cikin wannan hali sai daga bisani ne ta tsuke bakinta kuma ta turɓune fuska tamkar an aiko mata da SAƘON MUTUWA.
Ta dubi sarkin yaƙi a lokacin da ya so daf! Da ita ta dube shi ta ce “ya kai dirkar birnin Sin yanzu gashi a karo na biyu na sake yin rashin nasara, sai dai hakan ba zai sanya gwiwata tayi sanyi ba, zamu yada sansani a nan har izuwa lokacin da za mu sake yin nazari game da kai farmaki ga abokan gaba.”
Koda jin wannan batu daga bakin Abidat sai sarkin yaƙi Hunaifu ya risina ya ce “zancen ki dutse ya sarauniya mai duniya, amma wani hanzari ba gudu ba, shin Waɗannan tawagar sarakai da halittu mene ne manufar su na zuwa nan.
Shin sun zo ne domin farautar zakanya Juraima da Sulairat ko kuwa domin mallakar takobin Saiful-imfal?
Sa’adda Abidat ta ji wannan batu daga bakin sarkin yaƙi sai tayi shiru tana mai zurfafa cikin kogin tunani daga bisani ya dube shi ta ce “haƙiƙa maganarka akwai ƙanshin gaskiya a ciki, ai gamu ga su za muga abin da zai turewa buzu naɗi. Domin kuwa ba zamu lamunci kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi ba.
Yanzu sai kayi umarni ayi maza a kafa tantuna, tun da rana ta fara zafi ainun, akwai buƙatar mayaƙanmu su samu ƙwarin jikin da za su cigaba da kai farmaki.”
Da jin wannan furuci sai sarkin yaƙi ya ce”an gama ranki shi daɗe.
Cikin hanzari ya juya da baya tare da umartar dakaru su fara aikin kafa tantunan, kafin shuɗewar daƙiƙa hamsin sun kammala dukkan jama’a sun shiga ciki.
Al’amarin waɗannan halittu da suka sauka a wajen kuwa, ya yin da suka ga cewa su jaruma Sulairat sun ɓacewa su sarauniya Abidat kuma su Abidat sun kafa sansani, sai suma suka janye izuwa gefe guda nesa kaɗan da inda suke suka yada na su sansanin a bisa kan waɗansu dawatsu.
Haka al’amarin ya kasance ga sauran tawagar sarakunan biyu inda kowannen su yaja gefe guda nesa da ɗan uwanshi ya yada sansani.
Ba wasu ba ne waɗannan tawaga biyu face, ayarin sarki Nadiyar na kasar Madinatul-haiwan, da ya fito farautar zakanya Juraima da takobin Saiful-imfal, domin cika burin shi na samo maganin da zai bawa ɗaya daga cikin matanshi ta samu haihuwa.
Tawaga ta biyu kuwa tana bisa jagorancin sarki Damzaru ibn Gauras na birnin Salsalul-mahabba dake yamma maso arewacin duniya a gaɓar tekun nil.
Shi dai sarki Damzaru ya kasance matashin saurayi kyakkyawa, da masu hasashe suka tabbatar cewa a duka nahiyar babu namiji kyakkyawa tamkar shi, GWARZON ƘARNI mai tarwatsa dandazon mayaƙa a filin daga, ya shahara ainun a fagen ilimin tsafi gami da tarin dukiya dangin lu’ulu’u da dinare.

A rayuwar sarki Nadiyar bai taɓa soyayya ballantana aure, ‘ya’yan manyan sarakai da attajiran duniya sun rasa rayukansu bisa kamuwa da ciwon soyayyar shi.
Bakomai ne ya sanya sarki Damzaru bai taɓa ƙarɓar soyayyar wata ‘ya mace ba ko batun aure ba sai domin wata lalura dake damun shi.


A jikinshi yana ɗauke da halittar mace da namiji, tun ranar da aka haife shi bokaye suka tabbatar da cewa idan har likitoci suka yi masa aiki domin cire al’auran mace a tare da shi to fa za a rashi baki ɗaya. Kuma bokayen ba su gano inda wane magani zai magance lalurar ta shi ba.
Tun daga wannan lokaci dare da rana sarki Damzaru bashi da aiki face gudanar da bincike bisa halarar tsafin shi domin ya gano maganin lalurar shi amma bai taɓa samun wani bayani ba.


Al’amarin da yake matuƙar jefa shi a cikin damuwa kenan har takai yana zubar da hawayen baƙin ciki.
Wata rana yana zaune a turakarshi bisa kan ƙasaitacciyar tujera yana gudanar da bincike bisa halarar tsafin shi kwatsam! Sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar farin ciki tamkar na zai daina,
Al’amarin da yayi matuƙar bawa kuyangi da dakarun tsaro mamaki kenan domin yau tsawon shekaru goma rabon da aji sarki Damzaru ya yi wanan dariya.
Abin da basu sani ba shine bakomai ne ya sanya sarki Damzaru wannan dariyar farin ciki ba sai domin ya gano maganin da zai sha ya warware mashi lalurar shi.


Bakomai ne maganin ba face wata saiwar itaciya da ake kira da Shajarul-shifa’a dake ajiye a dajin fatalwa. Zai jiƙa saiwar Shajarul-shifa’a sannan ya sha ruwanta, da zarar aiwatar da hakan halittar ‘ya mace dake tare dashi zata fita ya dawo cikekken namiji,
Asalin Shajarul-shifa’a ta tsiro ne daga cikin tukunyar tsafin wani shu’umin boka da ya rayu a dajin fatalwa, saboda bishiyar na ɗauke da waɗansu muhimman ɗalasiman tsafi da a halin yanzu babu wani matsafi da yake da irin su a duniya.


Sannan muhimmin abin da sarki Damzaru ya gano shine burin shi ba zai taɓa cika ba na samun saiwar Shajarul-shifa’a face ya mallaki takobin Saiful-imfal wacce da ita ne kaɗai zai iya yaƙar halittun dake rayuwa a jikin bishiyar.
Su dai halittun sun kasance masu kama da tsuntsun batoyi, suna ɗauke da fuka-fukai irin jemage, bakunansu suna kaifi fiye da na takobi, duk abin da suka yanka da shi koda ƙarfe ne sai sun raba shi gida biyu, tsananin zafin naman su ya huce tunanin bil’adama.
Sai da sarki Damzaru ya shafe tsawon daƙiƙa goma yana wannan dariyar farin ciki, sannan ya tsagaita, nan take ya fito daga turakarshi ya dinga ɗibar dinare yana rabawa talakawa, al’amarin da yayi matuƙar ɗaure jama’a kai kenan suka ce a cikin ransu shin ko mene ne ya sanya sarki Damzaru sannan farin ciki haka? Ko kuma ya samu abokiyar rayuwarshi ne.
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan kawai suka zuba idanu.
Kashe gari tunda asubar fari sarki ya kammala shirin fita farautar takobin Saiful-imfal, bayan aiwatar da hakan sai ya yi bankwana da talakawan shi suna masu yi masa fatan samun nasara kasantuwarshi adali mai tausayin jama’arshi.
Wannan shine dalilin da ya sanya sarki Damzaru ya fito farautar takobin Saiful-imfal.

***

Budurwa ce kyakkyawa ta gaban kwatance sanye da fararen tufafi masu yalwa tun daga ƙasa har sama. ta rufe fuskarta da baƙin rawani idanuwanta kaɗai ake gani a gadon bayanta tana rataye da wata sharɓeɓiyar takobi a cikin kubenta tana zaune bisa farar taguwa.
Tafiya take cikin hanzari a cikin wani ƙasaitaccen daji mai ɗauke da sahara.
Sai da shafe tsawon zango biyu tana tafiya babu sassauci, tana cikin wannan hali ne kwatsam sai ta hango ƙura ta turnuƙe a can nesa kaɗan da inda take, koda ganin hakan sai taja linzamin taguwarta ta tsaya cak!
Sannu a hankali ƙurar tana Kusanto inda take har yazamana tazarar dake tsakanin su bata huce kamu goma ba.
Lokacin da ƙurar ta lafa sai ga waɗansu irin karen daji uku masu matukar girma da kwarjini, sai gurnani suke sun durfafo inda take wani yawu mai yauƙi yana dalala daga bakunansu. Su dai waɗannan karnuka sun kasance na sahara masu cinyin naman bil’adama, yau tsawon kwanaki huɗu ba su komai ba, domin haka suna cikin tsananin buƙata, bisa ɗabi’ar kurayen suna jiyo ƙamshin bil’adama a tsawon nisan rabin zango.
Lokacin da kyakkyawar budurwar ta hango karnukan sun durfafo inda take cikin mugun nufizsai kawai ta dako wawan tsalle daga kan taguwarta ta dira bisa diga-diganta gami da zare takobinta suka shiga yin kallon-kallo.
Daga can kawai ta ruga izuwa gare su domin tarar juna tana mai furta waɗansu kalamai da ita kaɗai ta san me take nufi.
Sa’adda suka haɗu da juna sai suka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro.
Abin tambaya anan shine daga ina wannan kyakkyawar budurwa take kuma ina ta dosa?
Amsar hakan kuwa shine :-

Sarki Shaibat ibnu Abbas yakasance dattijo ma’abocin haiba da SADAUKANTAKA da tarin duniya, mutum ne shi mai son addini da kyautata al’ummarshi, baya nuna bambanci a wajen hukunci tsakanin talaka da attajiri, bisa hakan ya sanya al’ummarshi ke matuƙar tausayin shi, hakan ya samo asali ne kasancewar shi ma’abocin addinin Musulunci.
Yana da matan aure ɗaya da ta haifa mashi ‘ya’ya biyu.
Gimbiya Husnat da Hasinat, an haife su tagwaye masu matuƙar kama da juna tamkar an tsaga kara, sun tashi cikin gata da kulawar mahaifin su.
Wata rana kwatsam! Sai aka wayi gari matar sarki Shaibat tare gimbiya Hasinat sun ɓace an neme su an rasa, nan fa hankalin sarki da jama’a ya dugunzuma ainun aka shiga bincike saƙo da lungu amma tsawon kwanaki biyu babu labarin su, wani abu da ya ɗaurewa al’umma kai shine babu wani sahihin labari da aka samu na dakarun sumame.
Lokacin da sarki Shaibat ya tsananta da bincike sai ya fahimci cewa tabbas anyi aiki da sihiri a sace gimbiya da mahaifiyarta.
kuma babban abokin gabar shi ne ya aikata haka sarki Marwatu, kuma ya yi hakanne domin shirya mashi baƙin tuggu na shafe birnin sa da addinin musulunci a doron ƙasa.
Asali tsarkin sarki Marwatu da Shaibat sun kasance ba a ga maciji da juna, kuma gaba ce data samo asali tun iyaye da kakanni.
Amma rana tsaka sarki Marwatu ya yi mubaya’a aka yi sulhu, aka cigaba da hulɗar kasuwanci da auratayya tsakani, yazamana cewa wasu daga cikin al’ummar sarki Marwatu na barin bautar gumaka su karɓar addinin musulunci, batare da sun fuskanci wata tsangwama ko hukunci ba.
Lokacin da alaƙa ta yi ƙarfi sosai sai sarki Marwatu ya aikewa da sarki Shaibat cewa babbar ‘yarshi gimbiya maulut ta kamu da matuƙar ƙaunarshi kuma ta na so ta aure shi.
Lokacin da wannan labari ya riske shi sai ya kasa zaune ya kasa tsaye, yana nazari akan wannan al’amari inda daga ƙarshe ya yanke shawarar amince domin wata ƙila idan ya aure ta hakan zai janyo hankalinta da na mahaifinta zuwa addinin musulunci.
Bisa wannan dalili ya sanya sarki Marwatu ya auri gimbiya maulut har ta haifa masa ‘yan biyu mata gimbiya Husnat da Hasinat.
Abin da sarki Shaibat bai sani ba shine a daren ranar da matarshi ta haihu sarki Marwatu ya bayyana a turakarta cikin alƙalumman sihiri ya shayar da jaririyar Hasinat tsufin tsafi, bayan ya ɓace ɓat daga turakar ne da daƙiƙa goma aka haifo Husnat.
Bisa wannan dalili ne ya sanya gimbiya Husnat ta taso da son ibada da addini saɓanin ‘yar uwarta Hasinat.
Sirrin da aka ɓoyewa sarki Shaibat shine an aura mashi gimbiya maulut domin ayi amfani da ita wajen cin amanar shi da ganin bayanshi.
A halin yanzu ‘yarshi gimbiya Hasinat babu wanda ta tsana a duniya fiye da shi.
Wani abin takaici da sarki Shaibat ya samu labari shine, a halin yanzu sarki Murwatu ya tura gimbiya Hasinat izuwa dajin Baitul-Shazwas domin ta mallako takobin Saiful-imfal wacce da zarar ta mallaki takobin zata shigo har birnin Niyaƙul-kabir ta hallaka shi.
Daga wannan lokaci za ta cigaba da azabtar da dukkan Musulmi a faɗin duniya.
Lokacin da sarki Shaibat ya samu wannan bayani sai hankalinshi ya dugunzuma ainun ya kasa zaune ya kasa tsaye, bisa wannan dalili ya sanya ya yi ganawar sirri da manyan hakimanshi, inda daga ƙarshe suka yanke shawarar a tura ‘yar uwarta Husnat domin ta hana ta cimma burinta na mallakar takobin Saiful-imfal domin ta hallaka mahaifinsu.
Wannan shi ne dalilin da ya sanya wannan kyakkyawar budurwa ta fito farautar ‘yar uwarta Hasinat, kuma take so ta isa dajin Baitul-Shazwas.

Mu haɗu a babi na hudu na karshe domin jin cigaban wannan ƙayataccen littafi.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.

MANSUR USMAN SUFI
08137237071Haske ya bayyana duhu ya yaye...
ƘARSHEN ZALUNCI book 3 end
BABI NA HUDU ƙarshe
Rubuta labari
Mansur Usman Sufi
Sarkin Littafan yaki
Lokacin da waɗannan masifaffun karnuka da gimbiya Husnat suka ruguntsume da azababban yaƙi a tsakiyar sahara. Sai suka wanzu suna kaiwa juna miyagun hare-hare cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance.
Karnukan suka wanzu suna kai Husnat yakushi ya cizo cikin wani baƙin zafin nama da ya huce tunanin bil’adama, ita kuwa ta wanzu tana kare hare-haren gami da zillewa cikin gwaninta da ƙwarewar yaƙi.
Wohoho! Haƙiƙa duk wanda ya iya ya huta, komai hassadar mutum idan yaga yadda Husnat ke kaucewa hare-haren karnukan tare da mayar da martani cikin baƙin zafin nama JURIYA DA BAJINTA sai mutum ya yi tsammanin ko wata na’ura ce ke sarrafa ta.
Sai da suka shafe tsawon rabin sa’a suna kaiwa juna hare-hare cikin baƙin zafin nama, babu alamun nasara ga kowanne ɓangare.
Al’amarin da ya fusata dukkan ɓangarorin biyu kenan kuma ya fusata su ainun.
Abin da ya fusata karnukan shine a iya tsawon wanzuwar su a dajin basu taɓa haɗuwa da halitta mai matuƙar zafin nama da nacin tsakiya tamkar

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment