Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Bismillahir rahmanirrahim godiya ta tabbata ga Allah wanda ya ara mana aron lokaci har nafara rubata wannan littapi mae albarka littapina na biyu kenan dafatan xae samu karbuwa
Marubuciyar littapin
QANGIN MASAURATA
Yanzu kuma
ABU MAHEER
By fatima Audi
PAGE 1 _5
* Wallahi acikin gidannan babu wanda ya isa yarabani dake harni xan daura maki talla kidawo mani da kwantae wani bugu takae mata abaki wanda yayi sanadiyar fashewar bakin ta
* Wata kara tasaka wallahi inna ba asan raena hakan takasance ba naxaga ko ina babu wanda yasiya duk wanda yace xae siya sae suce saena bisu dakinsu nikuma tsoro nake
*Lallae yarinya wuyanki ya isa yanka kamata tayi da bugu tako ina har saeda taga bata motsi sannan tasake ta tana maeda numfashi wlh abakin abincin ki don baxan bauta ma katuwar banxa ba kuma kitashi yanxu kitapi rafi dibo ruwa
*Dakyar ta iya dafa bango ta Mike tashiga dakin da yake mallakinta wato dakin da suke aje shirgin buhun hatsinsu wata bako tajanyo wadda ke dauke da kayan sawarta wanda baxasu wuce akirasu da tsummokara ba wani atamfa tadauko wadda tasha dinkin zare da allura duk abunda takeyi kukane takeyi maecin xuciyar mae sauraro
*Wae bazaki fitoba sae naxo nakara maki wani akan wanda maki yanxu yer iskar yarinya tambadaddiya mae halin uwarta munafuka gaki sumu² amma sae munafinci cike da ciki
*Wannan kalaman suna matukar kona mata rae tarasa dalili duk sanda xatayi mata fada sae ta sako mahaefiyar ta wadda bata taba gani ba koda taganta to ba lallae ta iya tunawa ba
*Fitowa tayi tana bin bango saboda yadda kafarta tayi mata tsami daukar tulun ruwan tayi sannan tapita a hanya tahadu da kawarta
*Yana ga kina dangyashi kowani abune yasameki domin nasan dik sanda xaa ganki to damuwa ce shimfide asaman fuskarki don ma Allah yayoki kina da boyan abu acikin zuciyarki
*Kedae bari ASiYA akullum gani nake babu wanda yake cikin damuwar danake ciki aduniya shin ni miye laepina da har ake mani gori? kiduba kigani tunda nike kalma daya mae dadi bata taba fitowa daga bakin INNA ba kullum aebuna take gani takare maganar idon na nazubar da hawaye masu radadi
*Kamar kullum abunda xan kara fada maki shine kiyi hakuri domin shine mafita ga dukan al'amarin rayuwa
*Nagode sosae kawata shiyasa nake kara kaunar ki saboda yadda kike share mani kuka na ina godiya agareki, da wannan firar suka isa zuwa rafin da xasu dibo ruwa
*Bayan sun debo ruwan sun taho suna firar su irinta kawaye kamar daga sama taji anbangaji tulun dayake saman kanta yafadi kasa yatarwatse
*Kirji tadafe nashiga uku ni SALMA mika aekata mani haka tafada tare da kae dubanta saman fuskarshi a iya sanin ta bata taba ganin fuskar mutumin daya sakata acikin tashin hankali basae yau kuma a wannan lokacin kuka tafashe dashi
*Kasan irin asarar daka mani kuwa kafasa mani tulunnan wlh akanshi bansan irin cin mutumci daxaayi mani ba amma kaeko ajikinka yanxu da wane ido xan kalli INNA in fada mata yafashe wani kukan takara saki wanda yake tabbatar da tana cikin tashin hankali
*Dik wannan abunda take fada bae tanka ba bare har tayi tunanin zae bata hakuri yadae dago idonshi yakalleta sannan yakauda kwayar idon shi saboda tunda yaganta gabanshi ke faduwa
*Bawan Allah kayi shiru bakace mata komi ba sannan kuma ko alamun kaga abunda yafaru bakayi ba haba don Allah murinqa ma rayuwa adalci ASIYA tafada ranta abace
*Kitaho mutafi kawae watakila ma kurmane shiyasa baeyi magana ba saboda haka babu komi haka Allah yatsara sae yafashe koda kau bae bigeni ba tafada tana share hawayen tausayin kanta da kanta
*Wannan magana datafada sae yaji taburgeshi sannan kuma ranshi yabashi tana cikin matsin rayuwa minene ke faruwa da ita da har tafadi haka?
*Tafiya suka farayi har suka tafi bae furta masu komi ba hakan yasa suka tabbatar da zargin su cewa kurmane shi amma ko kurmane ae yakamata yamana nuni
*Yanxu SALMA mixaki cema INNA akan fashewar tulun kinsandae baki mata laefi bama tabige ki inaga kinmata laefi gashi ni banda hanyar da zan taemaka maki
*Zuwa zanyi in fada mata dik abunda yafaru koda kuwa zata kasheni da dae inyi mata karya domin wani karin zunubi ne dahaka suka isa gida gaban SALMA sae faduwa yake domin batasan mixeje yadawo ba
*Assalamualaikum tayi sallama inna tanajin ta amma tayi banxa da ita saboda batasan matsayin sallamar a musulunci ba (y Allah karabamu da jahilci Ameen y Allah 🙏)
*Wae yanaga kina sando kamar wata munafuka hala wani halin kika aekata dabaki son asani ta laelayo wani ashar tawatsa mata wanda ni hannuna baxae iya rubata shi ba
*Daman tulun danatapi dashi dibar ruwane wani yabugeni yafadi kasa yafashe kiyi hakuri nima baason raena hakan takasance ba tafada cikin saduda
*Ehyeeee lallae yarinya wuyanki ya isa yanka wato yawon bin maxan naki haryakaeki ga fasa mani tuluna yau kau xaki kwashi jakar tsabar runbun gidanku ko ubanki bazae hanani cin ubanki ba tafada bakin ta har rawa yake
*Tuni jikin SALMA yafara rawa domin tasan kashin ta yabushe batayi laefi bama andake ta inaga tayi laepin kila kasheta za'ayi tafada cikin zuciyarta
Writing by Fatima Audi
Marubuciyar littapin QANGIN MASAURATA
ABUMAHEER
PAGE 5_10
* Wani icce tadakko tayo kanta zata buga mata kenan taji anyi sallama daga kofar gida dakatawa tayi daga abunda tayi niyar aekata mata baewar Allah itakau tayi shiru tanajiran saukar duka amma taji shiru
*Ki wuce kigano wake sallama a kofar gida tafada tana aeka mata da harara wadda ke nuna zallar tsana da kyamata atsakanin su fita tayi domin taga wanene yaceceta daga hannun ta domin da badanshi ba da yanxu sae dae wata ba ita ba
*Mutumin daya fasa mata tulu shita gani hannunshi rike da bokiti fuskarnan tashi kamar daxu babu alamun faraa miko mata yayi batare daya tanka mata ba juyawa taga yana niyar yi tayi saurin magana
*Bawan Allah zaka tafi bakayi magana ba ko dagaske kae kurmane kamar yadda muka dauka tsayawa yayi batare da ya juyo ba
*Kirinka dibar ruwa yafada a takaice kuma batare da yajuyo din ba yakama hanya yayi tafiyarshi cikin takun kasaeta kamar ba wanda yake rayuwa a kauye ba
* Shikuma wannan halin shi haka yake Allah mae banbanta mutane da mutane kowa da halinshi shi kuma wannan halin shi dagin kae toni dae koma minene yafitar dani daga matsala kiran da INNA kemata shiya dawo da ita hankalin ta
*Wannan bokitin sabo kuma daga ina INNA tafada tana duba bokitin kamar shi xae bata amsar tambayar ta
*Wanda yafasa mani tulune yakawo mani amaemakon shi yace inyi haquri wancan ma tsautsayi ne kum......
*Kedalla rufe mani baki cae⁴ sae xuba kikeyi kamar wadda tayi gobara a kae kin gama iskancin naki xaki xomani da bokiti a hannu wato ke ribar iskancin ki bokiti
* Wallahi INNA hahaka bane tafiya muke yabugeni yafadi kasa amma babu abunda ke tsakanina dashi tafada domin ita de tanajin kalmar iskanci batare da tasan ma'anar kalmar iskanci ba
*Wato ina fada kina fada don ubanki wuyanki ya isa yanka cakumota tayi takaemata mari da bayan hannunta sae da hancinta yafashe
*Wayyo INNA kiyi hakuri wallahi baxan kara ba natuba don Allah
* Au ashe harkin sami bakin daxaki iya bani hakuri wallahi baxan hakura ba sae naci ubanki wannan kyawun na fuskar ki naga alama shike rudar maza yaukau zan dakusheshi kowa ma yarasa
*Wata katuwar wuka tadakko tayo kanta takamata tana kokarin yimata bille sae akasamu akasi ta sami gefen wuyanta wata uwar yanka tamata sae ga jini yafito har tsartuwa yake
*Uwar karar data daka sae da makwafta sukaji wata iriyar radadine yaxiyarci kwakwalwa da ilahirin jikinta ita kanta INNA sae da gabanta yafadi domin batasan hakan xata kasance ba
*Jikinta ne yafara rawa saboda jinin dake zuba ajikinta wayyo Allah INNA kiyi hakuri nima baason raena ba kiyi hakuri natuba don Allah idon tane yafara rufewa
*Kunnuwanshine sukajiyo mashi kamar karar yarinyar dayakae ma bokiti akidime yajuyo xuwa hanyar daxe karasa kofar gidan kararta yasake jiyowa wanda hakan yatabbatar mashi da ba lapiya
*Ae da gudu yayi cikin gidan wanda lokacin har makwafta suma sun fara taruwa acikin gidan hankalin INNA yatashi daganin abunda ta aekata
*Wannan wane irin rashin imanine kika aekata wato abunnaki har yakae haka dik saboda bake kika haefi yarinyar nan ba shine zaki rika axaftar da ita ko dayake bakisan zafin haehuwa ba shiyasa kike haka cewar wata mata cikin matan da suka shigo gidan
*Miyake faruwa ne acikin gidannan yafada yana karasowa cikin sauri domin ganin SALMA kwance acikin jini gashi babu wadda tasamu damar taemaka mata kowa taxuva ido tana kallo bae saurari kowa ba
*Kubani dan kwali yanxu domin musamu jinin yatsaya kowace daga cikin ku babu abunda ta iya tsinanawa sae surutu dan kwalin aka bashi yadaure mata wurin raunin
*Ina za'a samu abun hawa wanda xae kaemu asibiti yafada yana kallonsu domin shikanshi hankalin shi yatashi daganin ciwon dake cikin wuyanta
*Sae dae aema dan liti magana saboda yana da abun hawa shine maekae mutane asibiti inbasu lafiya
*To ku kira mana shi mana kuntsaya sae kallon mu kukeyi ae kafin yagama rufe baki wata daga cikin matan harta pita tayo ma mae motar magana
*Daukar ta yayi suka pita yasata sannan yashiga shima direct emergency aka wuce da ita aka wanke mata ciwon tare da dinki
*Likitannane yapito domin yayi magana dasu yawwa kaene kakawota ko to agaskiya tana bukatar jini domin ciwon dataji jini yafita sosae don haka sae akira wadanda xasu bata jini
*Babu damuwa adiba nawa nasan zaiyi mata saboda zan iya bama kowa jini ba ita ba saboda haka muje ku auna
*To shikenan amma xamu duba sauran ciwo wanda xae hana kaba wani jini saboda haka muke
*Bayan an auna aka dibi jini laeda daya aka kara mata bayan anyi komi sannan yabar asibitin
*Bangaren INNA kuwa hankalin ta yatashi yanxu mi ta aekata haka idan takashe ta yaxatayi wurin yan sanda pa zata kwana karshe ma sukaeta koti kae zuciya batayi ba da takitsa mani mugun abu tagumi tarafka zuciyarta cikin zullumi
*Kayan dayasan za'a bukata a asibitin su yanemo sannan yadawo direct wurin likitan yashiga saboda yanaso yaga halin datake ciki tura kofar yayi yashiga
*Assalamualaikum daga ciki likitan ya amsa sannan shi kuma yakaraso cikin office din gaesawa sukayi sannan
*Likita yajikin nata ina fata tasamu sauki sannan tadawo cikin hankalinta?ya tambaya yana jiran ansar likitan
*Alhmdllh tasamu sauki munyi mata allurar bacci saboda haka tasamu bacci dama yanxu nake shirin in nemo ka saboda akwae tambayar da nakeso nae maka domin a gaskiya yarinyar nan tana cikin matsin rayuwa
ABUMAHEER
Writing by Fatima Audi
PAGE 10_15
*Inajin ka dr mike damunta bayan wannan abunda yafaru kamani bayani domin gabaki daya kaena yakulle
*Agaskiya tana dauke da ciwon ulcer wanda sanadiyar yunwa datake xama da ita takawo mata wadda hartaso ta taba mata hanji amma in sha Allah xamu dorata akan magunguna indae takiyaye shansu to zata samu sauqi
*Innalillahi wainna ilaehi rajiun wannan wacen irin cutace yarinya karama amma take fama da irin wannan matsananciyar damuwar hasbunallah, dama akwae matan da basu da tausayi?
*Shikenan bbu damuwa dr karubuta mana maganin in sha Allah za'a nemo kudi sae asiya maganin amma zuwa yaushe xa'a iya sallamar mu daga nan
*Agaskiya xamu riketa nadan wani lokaci kamar nanda kwana biyu saboda tana bukatar kulawa ta musamman daga garemu yanxu bara inbaka takardar maganin kaje ka anso
*To shikenan bbu damuwa mun gode likita bashi hannu yayi suka gaesa sannan yapita domin anso maganin da aka rubuta yana dawowa daga ansar maganin dakin da aka kwantar da ita yanufa
*Bacci takeyi hankali kwance ga jinin da akasaka mata yana diga a hankali wani tausayinta ne yaratsa zuciya da gangar jikinshi ita yarinyar nan wane irin laefi tayima matarnan datake axaftar da ita haka
*Motsi ta farayi alamun ta tashi INNA kiyi hakuri wlh niba yar iska bace tuluna yafasa mani kar ki kasheni wayyo Allah xata kasheni kuceceni abunda taketa fada kenan cikin tashin hankali
*Sae yanxu yafara kamo bakin zaren wato saboda bokitin daya kawo mata tae mata wannan ta'asar agaskiya barin irin wadannan matan a duniya hadarine
*Likitan dayake dubata yakira yaqara dubata domin kuwa har yanxu surutun take don ma maganar tadaena pita ahaka bacci yakara kwasheta
*INNA hankalin ta kara tashi yake duk sanda zuciyarta ta buga to da fargabar mixaeje yadawo take ga lokacin dawowar malam yakusa domin da yamma yake dawowa daga kasuwa kuma tasan idan yadawo babu SALMA agidan kashin ta yabushe danma tawani bangaren yana shakkarta daba tasan mixae faru ba
*Sae karfe 10:30 ta tashi daga baccin datayi wuyanta ne taji yamata tsami sae asannan ta tuna da abunda yafaru da ita kallon inda take tafarayi ganin ba agida bane yasa tafara kalle² idonta bae sauka ako ina ba sae kan mutumin da yafasa mata tulu to miyakeyi anan sannan waya kawoni nan? Sanin babu mae bata amsa yasa dakyar ta tashi xaune
*Sae asannan yaga halin da take ciki na farkawar da tayi tashi yayi daga inda yake xaune yakarasa gefen gadon nata domin jinin yakare har ancire mata shi sae dae cannular datake a hannunta har lokacin
*Inaso inyi sallah tafada tana kallon fuskar shi hannu kawae yamiko mata takama yataemaka mata tashiga bayin sannan yadawo yaxauna
*Sae da tagama abunda xatayi sannan tafito tana dan dafa bango gani tayi ya ajemata darduma da kuma hijab xuwa tayi tadauka tayi tasaka tayi sallolin da ake binta sannan taxauna
*Shayi yahada mata mae kauri yabata domin tasha cikin ta yawarware don yasan tana bukatar abu mae zafi takau sha sosae don saeda yahada mata kofi biyu sannan tayi gyatsa zufa ce tafara karyo mata
*Minakeyi anan sannan waya kawoni naga banga INNA ba tana ina tafada tanajiran amsar shi
*Bae bata amsa ba sae tashi dayayi nixan wuce sae da safe gobe inasaran za'a sallame mu saboda haka kikiyaye saboda ciwon da ke jikinki
*Ko babu komi tasamu sauki acikin ranta domin kulawar daya nuna mata kadae yawadace ta shikenan Allah yabamu alkaeri nagode da kulawarka agareni Allah yasaka maka da alkaeri tafada tana share kwalla
*Harga Allah yaji dadin adduar datayi mashi domin ko babu km ya yaba da natsuwar ta dik da kasancewar ta karamar yarinya
*Tambayar ki nakeyi ina kika kaemani yarinya ta wato abunda aka tareni dashi daga waje gaskiya ne nacewar kin kusa kashe mani yarinya to wlh idan har bata dawo gidaba kema saekin bar gidannan
*Don Allah malam kayi qoqari wlh sharrin shaedanne kagafarceni don Allah malam kada katona mani asiri tafada cikin zallar nadama afuskarta amma cikin zuciyarta jitake dama SALMA tabata
*Wannan baedameni ba diyata kawae nake bukata wato ke bakison intona maki asiri amma ni kike tona mani dik garinnan zagina ake cewar nakasa rike amanar ubangiji na daya bani to wlh indae bata dawo ba abakin auren ki
*Gabantane yayi mummunar faduwa dajin furucunshi nakarshe domin batae tunanin abun zaekae haka ba lallae akwae aeki agabana yau ni malam ke daga ma murya kan diyar shi xama baeganni ba dole indauki mataki tafada cikin zuciyarta
*A asibiti kuwa sae da SALMA tayi kwana biyu sannan aka sallame ta kuma har sannan INNA bata xo gaeshe ta ba saboda ita batasan asibitin da aka kwantar da ita ba
* Da baeso yamaeda ta gidan ba amma sanin babu inda zae nufa da ita yasa ya nufi hanyar kauyen su da ita domin hakan shine mafita
*Wlh LARAE kifita kinemo mani yarinya ta wannan ma ae iskanci ne ke hankalin ki akwance amma yarinya ta ban san halin da take ciki ba aekema kinsan bakiso axauna lafiya ba yafada yana nufar kofar fita daga cikin gidan axaure yayi kacibus da SALMA tana shigowa bayanta kuma wanda yayi jiyarta ne yatsaya domin tayi mashi iso zuwa cikin gidan nasu
ABUMAHEER
By Fatima Audi
PAGE 15_20
*SALMA ina mika shiga inata nemanki nadauka bazaki dawo ba yafada yataba wurin da aka saka mata bondage
*Wash da zapi ABBA mushiga daga cikin gida sae kaji komi kagama mutumin daya taemaka mani nan gurarin shine yayi komi da kudin shi tafada tana nunashi da hannun ta
*Allah sarki bawan Allah shigo daga ciki Allah yasaka maka da alkaeri ashe dama har yanxu akwae irin wadannan bayin Allahn masu halin annabawan farko yafada yana share hawayen fuskarshi
*Karasowa sukayi cikin gidan INNA naganin SALMA tayi fiki² tana raba idanu kamar tayi karya domin batae tunanin xasu dawo
*Duk abinda ya faru ya sanar masu sannan yace likita yace akiyaye da cinta domin tana fama da lalurar gyanbon ciki (ulcer) kada arinƙa barinta da yunwa hakan zai iya haifar mata da matsala babba
*Nagode sosae bawan Allah da taimakon da kamani Allah yabaka abinda kake nema duniya da lahira Ameen
*Babu komi baba amma don Allah akiyaye kar arinƙa barin mutane marasa imani suna azabtar da ita yafada yana kallon gefen da INNA take
*Tsuru² tayi da idanu domin tasan da ita yake to amma wannan ae wata dama nasamu babba tunda har takamu da wata lalura aeni kakata tayanke saƙa tafada aƙasan zuciyarta
*Babu damuwa yaro za'a kiyaye in sha Allah sae dae har yanxu bamusan sunan ka ba ita kanta SALMA tana buƙatar tasan miye sunan shi
*Sunana ABU yafada kanshi a ƙasa batare da yakalli kowa ba domin shi ba mutum bane mae son magana ba sallama yayi masu sannan ya tashi ya tafi godiya suka dinga mashi tace babu komi yima kaene
*To kingani kinso ta mutu Allah bae baki dama ba to wannan idan ke mae hankali ce to sae ki natsu kisan Annabi yafaku domin wallahi inda batadawo ba saekin bar gidannan sha³ kawae mtsssss yaja dogon tsaki yakara gaba
*Don ubanki duk akanki ake Mani wannan furucin to wallahi sae bafanshe kuma sae kinpi da ƙuntatuwa banza kawae mae halin uwarta tsinanna tafada tana dungurin kanta,washhhhh wuyana tafada tana dafe wurin ciwon ta
BAYAN SATI GUDA
*Awannan lukacin INNA tayi sauƙi akan takurawar datake ma SALMA saboda gargadin da baban SALMA yayi mata amma tadau alwashin xata koma wurin malamin ta jira take komi yalafa
*Yau tashirya domin zuwa wurin malamin ta domin yamaeda asirin jikin baban SALMA saboda taga alama matsala yakeso yabata domin ko halshe bae iya daga mata amma wae an wayi gari yana cewa zae sake ta kae wlh bata yiwuwa tana tafiya take wannan zantukan
*Tafiya tayi mae nisan gaske kafin taƙarasa dajin da bokan yake wayyo Allah wlh koda kudi aka hada mutum domin yaxiyarci wurin baxe iya ba amma saboda bushewar zuciya haka take ratsa ko ina sannan tashiga bukkar bokan
*Ran aljanu yadade shine abinda tafada amaemakon sallama kishigo da kafar hagu kishigo kina tsaki aka faɗa daga cikin bukkar bokan
*Yadda yafada haka ta aekata taƙarasa ciki tana doka tsaki kamar wata tsaka xama tayi tabude baki xatayi magana kenan yaɗaga mata hannu
*Tun kafin ki iso aljanu sun sanar mana da abinda kikaxo saboda haka babu wani karin bayani da muke bukata ga wannan kixuba masa a abincin daxaeci daga xaran taci to aekin ki tabiya komi kikeso xaeyi
*Godiya nake taxaro kudi ta ajiye sannan tapita tana tsaki kamar yadda tashigo (ya Allah ka kare mana zuciyar mu kasa mufi karfinta ameen 🙏)
*Ahaka takoma gida zuciyar ta fari kal saboda tasa aranta aekin ma har yaci saboda haka sae yadda tayi da wannan matsiyaciyar yarinyar
*SALMA kau baewar Allah batasan abinda yake faruwa ba ganin kwana biyu tadaga mata kafa tadauka duk wata azabtarwa datake mata to takare ashe akwae sauran rina akaba
*Koda INNA tagama tuwon dare haka ta aewatar da duk abinda boka yabata cikin farin ciki tanayi tana yan waƙoƙin ta nae nuna tana farin ciki
*kawo masa abincin tayi ya amsa yana ci sanda yagama ana kiran sallar isha'i saboda haka masallaci kawae yatapi saboda ya sauke farali
*Allah sarki SALMA baewar Allah tana daki tarasa mike mata daɗi ga ciwon ta dayake mata azaba tasha maganin amma yaki bari gashi rabonta da abinci tun na safe shima don Abba yananan tabata
*SALMA SALMA kina ina maza kipito yanxu inason ganinki fitowa tayi da gudu saboda karta jama kanta wani masifar kuma durkusawa tayi agabanra cikin girmamawa tana jiran taji dami taxo
*Yawwa inason in fada maki yanxu duk wasu ayyuka dasuka rataya akanki to yanxu xan linka maki su shara sau uku arana


ABUMAHEER
Written by Fatima Audi
PAGE 20_25
I love you so much my fans

*Yawwa inason in fada maki yanxu duk wasu ayyuka dasuka rataya akanki to yanxu xan linka maki su shara sau uku arana wanke² koda kwanoni basuyi datti ba to sae kin sake wankesu dibo ruwa kuma rafi basaena fada ba tashi yanxu kije ma kifara aekinki banza jaka tadaka mata tsawa
*jikina rawa ta tashi domin tafara aekin da akace tayi duk kuwa da wuyanta dake da ciwo bokiti tadauka wanda ABU yakawo mata tafita daga cikin gidan duk kuwa da dare yayi batada wata mafita sae baya aewatarda abunda akasakata
*Mtsssss ae yanxu muka fara talla kau babu dare babu rana kingama jindadina Kodayake dama ba daɗin kikeji ba irin tsiya kawae ta cigaba da cin tuwo abunta hankali kwance
*Allah sarki SALMA haka ta tapi rapin cikin darennan duk kuwa da tazara tsakanin gidansu da rafin amma haka tamiki hanya tana tafiya tana kuka
*Da yanxu mahaefiyata tananan duk da banga wannan wulakantar ba da yanxu zata share mani kukana ko kina ina bansaniba tafada cikin kuka
*Addu'a xakiyi mata bawae kuka ba domin kuka baya magance komi taji anfada daga bayanta waegawa domin taga waye kemata magana rugawa tayi da gudu tarungumeshi tana kara ƙarfin kukanta
*Yayana ina kashiga kabarni Ni kadae bakasan halin da nake ciki ba kamanta dani ko tafada tana kara makaleshi tana cigaba da kukanta
*Shafa bayanta yacigaba dayi ahankali

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment