Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dalili, Abba ma yasan hakan zata iya faruwa yasan sai DON ya kore'ta, da gangan yake aika ta daman dan yasan duka dai DON bazan duketa ba tun da yamasa gargaɗi a kan haka, dawo da kallansa Abba yayi kan su Yusuf yayi yace "kai ina ruwan ku da ita zoki zauna ki chigaba da chin abinchi ki kinji my daughter, ɗaure fuska Aunty Amarya tayi dan taso jin me DON yawa hiyana take numfashi haka ko marin'ta yayi,

Zama hiyana tazo tayi awajen da ta tashi ta ɗauki spoon a hankali tafara chin abinchin ta, shiru shiru DON bai zoba da har suka gama chin abinchin, Abba ya dubi Khalid rai a ɗan bace yace "kai baba tashi kaje ka chewa Safras nifa na haife shi ba shi ya haifeni ba da zai ajiye'ni ina jiran sa, Khalid na kokarin mikewa, sai ga DON ya shi go sanye chikin jallabiya fari, yana taku irin na jaruman maza, fuskar san nan kamar bai san menen dariya ba sai wani kakkau da kai yake, gaba ɗaya su Aunty Maryam kowa ya shiga taitayin sa, har da Aunty amaryan, kujerar dake fuskantar Abba yaje ya zauna da sauri kannen nasu suka fara ɗaga masa gaisuwa, bai ko kalli inda suke ba bare ya amsa musu gaisuwar sai ma kara ɗaure fuska da yayi, sai da suka gama gai suwar nasu sukayi shiru kowa ya nitsu suna sauraren suji abun da Abba zai che.

A hankali DON ya buɗe ɗan karamin bakin nan nashi kamar bai san motsa lallausan lips nashi, ya fara gaishe da iyayen nasu, fiska ba yabo ba fallasa Abba ya amsa haka Aunty amarya da Ummi, Ammi kuwa ɗaure fuska tayi sosai kafin ta amsa masa,Shiru yayi san nan ya sun kuyar da kai, shiru palon yayi gaba ɗaya Abban ne ya katse musu shirun da chewa "Zahra kutashi kuba mu waje, tun bai kai karshen maganar ba Zahra hiyana diyana lamrat amrat suka miƙe suka bar palon,

dawo da kallansa kan su DON Abba yayi yafara Magana "abun da yasa na taraku a nan shine, duk kanku lokachi yayi da zakuyi Aure, a sukwane DON Aryan Fahad haidar Aiman da kuma Ahmad suka ɗago kai a tare suna kallon Abba kamar zasuyi ihu musam man DON Aryan Fahad Aiman,su nasu ɓachin ran na da ban ne kamar wayan da aka chewa uban su ya mutu, Khalid Yusuf Umar kam ko ajikinsu, Aunty farida ma ɓata rai tayi sosai dan tasan wan nan maganar da Abba yayi ba karamin ɗagawa su DON hankali zai yiba, dan babu hakan a tsarin su, tafiso a barsu sunemi mata chikin nitsuwa, dan idan akache za'a tilasta musu wlh duk wadda aka aura musu tashiga uku,

"No Abba No gaskiya kabar wan nan maganar ni babu mace a tsarin rayuwa kamin wani hukunchin dai amma banda batun mace pls Abba, chewar DON, ya karisa maganar chikin wata iriyar voice wadda da kajita kasan tsantsar kiyayyar macece a ranshi,ga fiskar nan kamar an aiko masa da sakon mutuwa, shiru Abba yayi ya zubawa DON ido har yakai karshen maganar tashi, shi kanshi Abba yasan chewa mawuya chin abune DON Aryan su yarda da batun Aure, domin babu hakan a tsarin da sukayi wa rayuwar su,shiyasa ma bai takura musu ba tsawon lokachi ya bar su, to amma yanzu yazama dole suyi Aure dan chika sunnan ma aiki, kuma yafi son su kawo matan da zasu Aura da kansu dan idan yace zai Aura musu zaɓin sane, yasan matan sun shiga uku

sosai Abba yashiga tunani, gaskiya bai kamata nayiwa DON dole ba idan yayi haka tofa akoi babban matsala tsabar tsanar mace dayayi ne jiba agaban kannen sa yau ya buɗe murya haka yana magana har da chewa sorry mutumin da magana wahala yi take masa, lallai bai kamata na takura masa ba idan kuwa nayi haka zanyi dana sani mai girma, addu'a kawai ya kamata na masa.

Ganin Abba yayi shirune yasa Aryan chewa "Abba pls kabar maganar auren nan wlh ba muso babu mace a tsarin rayuwar mu pls my Abba kaji ya karisa maganar yana ɗan dafa hannun Abba, chikin fushi Ammi tace "babu mace a tsarin rayuwar ku ko, to ku chiremu muma a tsarin rayuwar ku tunda muma matane tana kaiwa nan ta miƙe ta fiche daga palon chikin fushi da ɓachin rai, dafe kai DON yayi a zuchiyar'sa yana faɗin jiya nayi ɗaya yau kuma na biyu am so so sorry Ammi ammafa aure kam ba zan yi ba gaskiya sai dai duk abun da zai faru ya faru, miƙewa Ummi tayi itama tana faɗin "ranka ya daɗe idan kun gama zaman ka kira malam mai rukiyya yazo ya musu dan ga dukkan alamu aljana che ta auri ƴa'ƴan nan, a sukwane suka juyo gaba ɗayan su suna kallon Ummi, ɗaure fuska tayi kafin ta juya ta fice daga palon, kallan Aunty amarya Abba yayi tun bai yi magana ba ta miƙe ta fita tana ɓata rai dan taso jin me Abba zai che musu wani amsa zai basu, "Maryam salma mardiya kutashi ku bamu waje,chewar Abba yayi maganar yana kallon su, jiki ba kwari suka miƙe suka fita.

Palon ya rage daga Aunty farida, DON Khalid Yusuf Aryan Aiman Ahmad Umar haihar da kuma Fahad

Dawo da kallansa Abba yayi kansu DON ko'wannen su sai faman ɗaure fuska yake sai wani chi chijewa suke, ɗan gyaran murya Abba yayi kafin yafara Magana "ke farida na barki ne saboda bakin ku ɗaya dasu ke che sirrin su basu taɓayin wani abu batare da kin sani ba dan haka ku saurareni, "ni bazan tilas ta muku kuyi Aure ba, wani dauyayyar ajiya zuchiya DON Aryan Fahad, suka sauke a tare, har da ɗan sakin fuska, ganin hakan yasa Abba murmushi yachi gaba da chewa "bazan takura muku kuyi abun da baku so ba, saboda farin cikin ku nake bukata, amma dai burina shine naga kunyi aure kun haifamin jikoki shine babba burina a duniya kuma farinchiki na, ni ina san farin chikin ku ban sani ba ko kuma kunason nawa, ban sani ba ko zaku iya chika min burina tun ina raye, ɗan dakatawa Abba yayi yana satar kallon fuskokin su,a ransa yana faɗin nina haifeku ai baku kuka haifeni ba a chikin ruwan sanyi zanyi maganin ku, nan take fuskar DON da Aryan ya sauya sosai dan sun gano tarko Abba ke neman yima'su da kalaman sa, Fahad kuwa sai murna yake Abba bazai yimasu dole suyi aure ba, shiru Aiman yayi ya ɗora hannu a gemun sa yana kallon kasa yana nazarin magan ganun Abba, Khalid da Yusuf kuwa ɓata rai sukayi sosai dan su gaskiya Aure suke so kuma suna da matan da zasu aura, amma DON da Aryan suna neman watsa musu farin chiki, Aunty farida kuwa jikinta ne yayi sanyi sosai jin kalaman Abba, tabbas Abba na da gaskiya yakama suyi aure amma banso Abba yabi musu ta wan nan sigar ba da an bi a hankali an bisu da addu'a inshaa Allah komai zai tafi dai dai

Ganin sunyi shiru kowan nan su yatafi tunani yasa Abba chewa, "nifa ban takura'wa kowa daga chikin kuba, burina da kuma farinchiki na kawai na faɗa muku, kuma ban che dole sai kun chika min burina ba koma me ni zan zama mai chika muku burin,kuma mai saku farin chiki a ko da yaushe, kuje ku zauna kunitsu kuyi tunani yana kai karshen maganar yamike ya shige betroom ɗin sa,

chikin fushi da ɓachin rai DON ya furta "never Abba aure fa, wlh I cannot do it I cannot do it gaskiya bazan iya chika maka wan nan burin nakaba, a fusache ya miƙe ya bar palon, da sauri Aryan ya miƙe zai bi bayan sa "ina zakaje Aryan Aunty farida ta tambaya, "Aunty farida baki ganin ɗan uwana yana chikin ɓachin rai ne ai bazan iya zama ba, yana kai karshen maganar batare daya jira amsar taba ya fiche da sauri, a fusache Aiman ma ya mike yaja tsaki yana faɗin "nima dai ba zan iya chika'wa Abba wan nan burin na shi ba sai dai in ku zaku iya bani da lokachin mace yanzu, yana kai karshen maganar ya juya da, sauri ya nufi hanyar fita dan bai dan Aunty farida ta. dakatar da shi

Girgiza kai Khalid yayi kafin yache "gaskiya a wan nan gaɓar ya kamata mu chika wa Abba burinsa, domin duk wani abun da mukeso yana mana yanzu ki duba Aunty babba saboda bama son mulkin nan, Abba ya hakura da bamu mulkin duk dan muyi farin chiki, tun muna yara har muka girma har izuwa yanzu bamu taɓa chewa Abba muna bukatar abu kuma yaki yi mana ba, to meyasa mu kuma zamu rinƙa kin abun da yake so, yache zai bamu mulki munki ya hakura yanzu kuma kin fa ji auren mu shine kaɗai burin daya rage masa a duniya da yake san mu chika masa,to why bazamu chika masa burin sa ba. ɗan daka tawa Khalid yayi da magana yana mai da numfashi "Kana da gaskiya Khalid amma a hankali Ya kamata abi abun tun da kaga dukkan ku ba soyayya kuka taɓayiba babu wata alaka da ta taɓa haɗaku da wata mace idan ba mu yan uwan ku na gida ba, SO kaga abune mawuyache lokachi ɗaya a che zaayi muku maganar aure garama kai dasu Yusuf da sauki, amma kafini sanin halin DON da Aryan, basu san wani abu wai shi soyayya ba, bai da che amusu zuwa ɗaya haka ba a hankali za'a shawo kansu, yanzu dai zanje in same'su dan musan abunyi tana kai karshen maganar ta miƙe tanufi hanyar fita, shiru Khalid yayi yana tunani, miƙewa Fahad ma yayi yabi bayan Aunty farida, haidar da umar ma suƙa miƙe suka fita suka nufi ɓan garensu palon ya rage Khalid Ahmad Yusuf.
[6/15, 8:07 PM] Princess Teema Yola: *💫STAR LADY💫*


💖The Talent Troupe Writer's 💖




*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star Lady*



Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai



*Episode 2️⃣6️⃣*


Misalin karfe 7 na safe Ammi na zaune a bakin katafaren gadon ta sanye take da wata ɗankareriyar lace baki mai zanen flower manya manya ajiki jaa, ɗinkin bubu gawn, ta sanya wani dan kareren sarkan gold a wuya ka wasu manya manyan abun hannu masu kyau da tsada a hannunta, sai kamshi take zubawa,kamar anyi ɓarin turare ajikinta

da sallama ɗauke a bakin sa BGS ya shigo, kauda kai gefe Ammi tayi tana amsa sallamar, ganin hakan yasa BGS ya kariso chikin ɗakin da sauri a gaban ta ya zauna saman lallausan karpet na alfarma dake shinfiɗe a ɗakin, chikin sanyi murya ya fara magana "ina kwana Ammi, kara ɗaure fuska sosai Ammi tayi kasa kasa ta amsa masa da lfy, kwantar da kansa yayi kan chinyar ta ya riko hannunta cikin ladabi da girmamawa yafara Magana "kiyi hakuri Ammi na, kinji nasan nayi laifi dayawa amma pls ki daina fushi dani kinji, kin fa san idan ki na fushi da ni, ina cikin fushin Ubangiji kuma kome nasa a gaba bazan yi nasara ba pls my Ammi for give me, ɗan daka tawa yayi yana sauraron yaji me zata che

..... Hannu Ammi tasa ta fara shafa lallausan gashin kansa kafin tace "ni ba fushi nake da kai ba kuma ba zan iya fushi da kai ba saboda na san idan iyaye suna fushi da ƴa'ƴansu, wache bala'i mai girma suke jawa ƴaƴan nasu, kawai dai abun da ka keyi ne baya da chewa, "zan daina Ammi na duk wani abun da baki so ki faɗa min zan dai na "kayi alkawari "na miki alkawari Ammi na keche fa farin chikina lokachin da bana kasar nan kin ta ɓa ganin nayi 2 hours ban kira ki ba, kome aikin da nake sai na daka tar na kira ki koda na 5mnt ne, saboda kawai inji ya kike, "eh hakane na sani kuma kana da gaskiya

.... yanzu dai abu biyu ne kake yi a gidan nan yake ɓatamin rai, kuma nake son ka daina yi, da sauri BGS ya ɗago kai yana kallan ta, murnushi kaɗan Ammi ta sakar masa, shima wani cool murmushi wan da bai ta ɓayi ba ya sake har sai da dimple nashi ta lotsa, chigaba da magana Ammi tayi "ina son ka rage tsawar da ka kewa su hiyana abun yana damuna kaga marayune ba uwa ba uba pls ku jasu ajiki dan ku mantar da su marai chin nasu, kannen kane kai yaka mata kafi kowa sakar musu fuska da jansu ajiki,

..ɗaure fuska BGS yayi,bai che komai ba yayi shiru yana tunani, yanzu dai sulhu nazo nema wajen Ammi bai kamata nayi wani abun da zai sake ɓata mata rai ba gaskiya bari dai na bita a yadda take so for now, in yaso daga baya na koma normal, ɗan murmushi gefen fuska ya saki a hankali ya motsa ɗan karamin bakin nan nashi ya furta "daga shi sai mai kuma Ammi, ajiyar zuchiya Ammi ta sauƙe kafin tace "sai batun kannen ka su Umar, inajin ɓachin rai idan suka gaishe ka baka amsa ba, sai kache wasu abokan gaba, ai ko bazaka amsa gaisuwar mutane a waje ba to fa ya zama dole ka rinƙa amsa na kannen ka "to shike Ammi na i will try my best kinji daɗi " kwarai kuwa naji daɗi "Thank God, my Ammi haka nake so in ga kina chikin farin chiki, zame hannunta Ammi tayi daga gashin kan nashi tana faɗin "nima ina son naka farinchikin ai, yanzu dai katashi kaje ka shirya kuje ku raka Ahmad fada "a'a Ammi ni bazan je ba "what Ammi ta faɗa tana kara waro fararen idon ta "baka isa ba ka tashi kuma Allah idan ban ganka a fada ba.. bai bari ta karisa maganar ba yace "a'a my Ammi yanzu ma zanje na shirya yayi maganar yana miƙewa, san nan yanufi waje

Nauyayyar ajiyar zuchiya Ammi ta sauƙe, a fili ta fara magana, Alhadulillah Allah na godema da ka bani ɗa mai kauna ta mai jin tausayi na mai gudun ɓachin rai na, ya Allah ka tai makeni nima na rinƙa faran ta masa kamar yadda yake min ya Allah ka nunamin ranar da zaiyi Aure, bana son na chigaba da ta kura masa a kan batun Aure, yana min biyayya iya gorgidon iyawar sa yana son farinchiki na, bai kamata ni kuma ya dage wajen sashi abun da baya so ba zan rinƙa taya shi da addu'a har Allah ya karkato da hankalin sa kan Auren, karisa hayewa saman gadon tayi ta kwanta da kyau ya lumshe ido tana ta tunani

Misalin karfe 9:30 gaba ɗaya family sun haɗu a faɗa sun sha kwalliya sosai Abba na zaune kan kujerar mulkin su Ammi suna gefe gefensa, ga wata ha ɗaddɗiyar gujera a gefen na Abba ba kowa a kan gujerar, su Aryan suna kujerun dake jere gefe guda kujerun su Aunty farida na fuskantar nasu Aryan, ga manya manya baki kamar su sarkin zaria sarkin gombe sarkin yola da dai sauran su,

Miƙe Wa Abba yayi daga kan kujerar da yake zaune, yayi tattaki izu tsakiyar fada san nan ya fara magana "kai Ahmad tashi ka hau kujerar mulkin ka, jiki ba kwari Ahmad ya mike ya nufi kujerar, yana zama su wajiri suka miƙe suka nufoshi, nan take suka ɗauko farin kyalle suka fara naɗa masa rawani a kai, shidai kamar zai yi kuka haka aka naɗa masa rawanin sarautar,bayan su waziri sun gama na ɗawa Ahmad rawanin ne, Abba yace "salati goma ga annabi yayi maganar yana nufar gujerar kusa da Ahmad,

...zama Abba yayi san nan su kafara yiwa annabi salata bayan sun gama salati, Abba ya ɗago ido yana kallan BGS "Safras ka rufe mana da addu'a, BGS bayasan yin magana ko kaɗan amma yana gudun ya sake ɓatawa Ammi rai Allah badan Ammi na wajen nan ba da ba zanyi addu'ar nan ba, slowly ya buɗe ɗan karamin bakin nan nashi, da wani zazzakar Muryar sa ya fara zuba addu'oe, gaba ɗaya palon sunyi shiru suna sauraron'sa slowly hiyana ta ɗago blue eyes nata ta sauke su a kan shi chikin ranta tana faɗin "wow dama haka yake da voice mai daɗi? shi yasa baya magana dan kar murinƙa ji hmmm sosai take kalansa, har ya kai karshen Addu'ar yana kai karshe ya mike da sauri ya fice daga fada

sai sauri yake yana taku irin na jaruman maza, yazo dai dai zai shiga ɓangaren kamar daga sama yaji murya daga bayan sa tana faɗin "baka jiba, batare daya juyaba yayi shigewar sa, kai tsaye betroom nashi ya nufa yana shiga ya nufi katafaren gadon sa, ya haye ya kwanta ya lumshe ido yana jan tsaki

A hankalin ta turo kofar ɗakin ta shigo kwas, kwas, kwas, take takawa har gaban gadon nashi ta zo, kashe murya tayi tafara magana "haba mana shine ina maka magana a waje ka shareni, kasan wacece ni? nifa yar Autan sarkin zaria che pls kyakkyawa katashi mana muyi magana wlh ni bana barin abu a rai na da abu ya burgeni nake faɗe, wlh ka tafi da ni tun da kafara addu'a a fada nake kallon ka, kuma SON ka nake da dukkan zuchiyata, ko motsi BGS bai yiba bare tasa ran zai yi magana "haba mana kyakkyawa nasan ba kayi barchi... Bata kai karshen maganar ba taga BGS ya mike batayi auneba taji saukar wani gigitatchiyar ma haukachiyar mari,a kan kunchinta wani ihun azaba ta saki

.. a fusache ya zaro belt daga ma zaunin sa ya fara zuba mata ta ko ina a jikin ta, ihu take kamar ranta zai fita,shiko ko ajikinsa rai ambachi yake zabga mata belt ɗin, data ga dai BGS zai iya kashe ta ba wan da yaji ihun data ke bare yazo ya taimaka mata yasa ta miƙe da kyar tanufi hanyar fita, damko atachimen ɗin datayi chikon gashi da shi yayi ya daga ta da kai, yayi wurgi da ita gefe hakan yayi dai dai da shigowar Aryan ɗakin, a fusache BGS ya sake nufar ta, ko motsi batayi da alama ta suma chigaba da bugunta yayi

Da gudu Aryan ya karisa chikin ɗakin ya sa hannu biyu ya damko damsen BGS yana faɗin "haba blood kisa zakayi ne, chikin tsawa BGS yace "sakeni Aryan nache kasake ni "bazan sake ka ba BGS bazan sake ka ba nache, ida kuma nima zaka haɗa har dani ka bugane to Bismillah, a fusache BGS ya ya kwache hannunsa daga rikon da Aryan ya masa ya fice daga ɗakin sai huchi yake, bin yarinyar da kallon Aryan yayi a ranshi yana faɗin ko wacece wan nan kuma ko me ya haɗa su, wayar sa ya chiro daga aljihun wandon jeans dake jikin sa ya fara kiran layin Aunty farida,

....Bugu ɗaya Aunty farida ta ɗaga tare da faɗin "hello bro "Aunty farida kizo ɗakin BGS ki ɗauki wata yarinya "wata yarinya kuma? Aryan "eh nima yanzu shigowa na ka nan, na samu yana bugun wata yarinya gashi da alama ta suma "Allah dai yasa ba diyana ko hiyana bace "aa Aunty babba basu bane wan nan ma ba yar gidan nan bache "to ke nan a chikin baƙin nan ne, me tamasa zai bugi yar mutane, "to nima dai ban sani ba idan kinzo kya tambaye shi yana gama faɗin hakan ya katse kiran, ya juya ya fice daga ɗakin

Misalin karfe 2 na rana gaba ɗaya family Abba sun haɗu a babban palon Abba dan chin abinchin rana ban da ƴanma tan Ammi sune kaɗai basa nan sai BGS wadda daman ba tare suke chin abinchi da shi ba, "kin san me Safras ya aikata yau kuwa? Chewar Abba yayi maganar yana kallan Ammi "aa me kuma yayi chewar Ammi "hmmm yar sarkin zaria ya kama ya rinƙa bugu yanzu haka tana asibiti wlh bakiga yadda mahaifinta ya bata rai ba da kyar na bashi hakuri "kai wan nan yaro to me ya haɗa su Ammi ta tambaya tana kokarin ajiye spoon ɗin hannunta, da sauri Aunty Farida tace "aa baruwan DON ita taje ɗakin sa ta same sa ai, shiru sukayi dan Abba ya gane dalilin daya sa BGS ya bugi yarinyar


wai ina yan mata nane chewar Abba "suna ɗaki kasan diyana sarkin kwalliya che tana chan wai sai ta gama kwalliya, zata zo chin abinchin, su hiyana kuma suna jiranta chewar Ammi, murmushi Abba yayi kafin yace "ai tana da gaskiya gara ta rinƙa kwalliya sosai dan ta samu miji da wuri na aurar dasu, a sukwane Aryan ya ɗago ash eyes nashi karaf, idon nasa, ya sauka chikin na Abba dan kuwa shi Abba ke kallo mayar da kansa yayi ya sun kuyar ya ajiye spoon ɗin dake hannun sa ya ɗauki wayar sa ya fara latsawa,

...... Aure kuma Abba Aunty farida ta tambaya da mamaki, "eh mana my daughter yanzu su diyana basu kai Aure bane, ai da diyana hiyana Zahra sun kai Aure kuma nan ba da jimawa ba zan musu, wani dogon tsaki Aryan yaja wadda yasa gaba ɗaya mutanen palo suka ɗago suna kallon sa "Aryan lfy Ummi ta tambaya tana kallan sa daga sama har kasa, rai a ɓace yace "lfy Ummi, kau da fuska Abba yayi daga kallon Aryan ya chigaba da chewa "ita kam diyana ma ai tana da masoya ga yaya bellon ta, na Yola ga kuma malamin makarantar su duk da naji anche an karya masa kafa, baya tafi to in dai diyana na son shi zan fiddashi kasar india amasa aiki, "oh my god Aryan yafaɗa chikin tsawa yana dafe kai, wadda sai da gaba ɗaya jama'ar palon suka tsorata, "Aryan kana lfy kuwa Aunty farida ta tambaya da mamaki a fiskar ta, ban za yayi dasu ko sannu bai cheba, Abba kuwa chewa yayi "kai ku kyalesa mana tun da ba ya son magana, mikewa Aunty farida tayi daga nata kujerar tana faɗin "aa Abba wan nan irin tsawa haka ba lfy ba ta karisa maganar tana karisawa wajen da Aryan ke zaune, hannu tasa tana shafa kansa kafin tace "me nenen bro, ɗago ash eyes nashi yayi wadda suka sauya sukayi jaa ya buɗe ɗan karamin bakin nan nashi zai yi magana ke nan, sai sukaji yar siririyar muryan diyana tana doko sallama tun daga bakin kofar palon

Mai da kallon su gaba ɗaya mutanen palon su kayi izuwa bakin kofar palon, anko su kayi gaba ɗayan su chiki jalla biya pink colour Zahra hiyana lamrat amrat duk sun yafa mayafin rigar amma ban da diyana, ita kam ta tasaki wan nan bakin lallausan dogon gashin nan nata har gadon baya, a nitse suka kariso chikin palon kowan nan su na zauna a kujera table ɗin,

Wow my daughter kinyi kyau sosai chewar Abba yayi maganar yana kallan diyana, dan ita kaɗai che a chikin su tayi kwalliya, "laaaa Abba kasan me ranan ma yaya yusuf yace nayi kyau haka yaya Aryan ma da na kai masa coffee yace nayi kyau dana ɗan kwali, asukwane matasan gidan suka juyo da kallan su kan Aryan,

ɗaure fuska sosai Aryan yayi kamar bai taɓa dariya ba ya chigaba da latsa wayar sa, ita kuwa diyaba ko ajikin ta sai murmushi take tana bawa Abba lbr, ganin Aryan ya ɓata rai sosai ne yasa Yusuf yace "eh mana my sister ai dole kowa yace kina da kyau, to ke ba sis ɗin mu bace idan bamu yabe ki ba, waza mu yaba, wani murmushi diyana ta saki tana faɗin "Allah yaya Yusuf idan nayi kwalli ina kyau? "kai sosai ma kuwa may sis ai duk gidan nan kin fi kowa kyau kuma kin fi kowa...

Please Login or Register in order to submit comment