Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tarbiyya zan bata wanda nan gaba itama zata yi alfahari da kan ta” .

Shiru duka suka yi kana Ibrahim yace “haidar anan ɗin zaka iya ba Ma'eesha tarbiyya kar ka manta karatun soja fa muke yi wannan ce shekaran mu ta farko, dole mu maida hankali Tayaya zaka iya karatu da Raino? .

Zan iya Ali jarumi ne”! Komai nawa na daban ne , Rainon soja ake faɗa maka yasha ban-ban da sauran rainon da ka sani . Cike da bashi ƙwarin gwiwa Areef ya furta “ Yes of course Ali zaka iya yin fiye da haka , ai mu sojoji ne dole komai namu ya zamana daban dana Mutane,mu fa masu kare al'umma ne , Tayaya tun yanzu ba zamu iya kulawa da wannan yar yarinyar ba ?’. Komawa Aliyu yayi yana ƙwantar da kan sa bisa pillow kana yace“ that why you're always my Best friend ever ” . Ku miyi barci saboda 3:00am muke da fita training.

**
Mami meke damunki tunanin mene kike yi haka? . Muryar Jidderh ya katse Mami wacce take zaune bisa Dinning table ta kasa sarrafa tunanin ta bisa abun da Aliyu ya ɗauko mata a jiya ” . Mamiii”. Jidderh ta kai hannu tana taɓa Mami tare da girgiza ta tana langwaɓe kai tare da ƙara Cewa “ What's up? What are you thinking for...? ” . Humm no..no... Nothing . Mami tayi maganan Muryar ta na rawa , kana ta ɗan kalli jidderh dake sanye cikin shigar Sport wear na makaranta duba ga yau laraba ,ranan saka rigar Sport kenan a school din nasu . Murmushi Mami ta ƙaƙalo don bata son Jidderh tasan da labarin Aliyu da wannan Yarinyar da ya ɗauko , don tasan yanda jidderh ke zafin kishi da son yayan nata bata son taga kowa ya rabe su , to Taji labari bata babu sukuni kuma sai na kuka.

Sauke Ajiyar zuciya Mami tayi a zuciyar ta tana cewa “ Ai yaga ɓacin raina kuma ya fuskanci horo wurin babban don haka nasan tuni ya maida yarinyar nan , bani da lokacin ma ɓata shi a kan bibiyar wani hali suke ciki , don tuni ya fitar ma kansa da maslaha. Hannun ta takai tana shafa kan Jidderh kana tace “ Are You ready for school now” . Gyaɗa mata kai Jidderh tayi kana ta zauna a bisa kujeran ta inda nan ne wurin zaman ta permanent dama. A h natse mami ta fara bata breakfast ɗin ta , Duk da itama sauri take zata wuce Wurin aikin ta na police amma sai ta sauke jidderh a school sannan zata wuce. Ganin yanda take feeding ɗin Jidderh da hannun ta tamkar jaririya ya sani cewa“ Lallai Mami anya lamarin ki babu .....🤔to muje dai gaba muji yanda zata ƙare.

Ture kan ta Jidderh tayi daga ƙoƙarin da Mani take yi na kai mata soyayyar Irish din da take yi . Cikin sauri tasa hannun ta tana Fiddo da Wani white pepper warware shi tayi a bisa jikin ta tana nuna ma Mami zanen ta na jiya da tayi . Wow that's very nice my baby 💃🏻 Wannan zane haka mai kyau? . Yes Mami see daddy here, While Boo mie seating in front of Dad kinga yanda yake haɗe giran nan da ya saba. Tayi maganan tana sakin dariya tare da nuna fuskar Aliyu Haidar , ta zana shi giran sa a haɗe , Gyefe kuma mami ne sai Yaya Khaleel dake sakin fara'a . Mami have you remembered any little thing about this? . Kin iya tunawa da wani abu ko kaɗan gami da Wannan zanen?. A'a baby na ban tuna da komai ba .

“Hinmm , wannan fa zanen shekara ɗaya da ta wuce ana gobe birthday din ya Aliyu ne muka zauna a haka yana fushi mara dalili , shi kuma yaya Khaleel na tsokanan sa baki ga dukan mu muna dariya ba ,shine kaɗai fuskar sa babu annuri?. Kallon zanen Mami tayi tana sakin dariya irin na Polisawa😹 don ita komai nata haka zaka ganshi woman like a boss . Haka take bata da wasa.

Girgiza kai tayi cikin sauri tana cewa “ Ohhhh Yes ”. Na tuna fa haka ya faru . So yau boo mie ɗina yake ranan zagayowar haihuwar sa haka ne mami atleast muyi surprising ɗin shi na yau. Mami ina so mu zauna a haka mu Biyar,bana son ko wacce baƙuwar fuska ta kutso mana cikin Ahali. Muna jin daɗin rayuwar mu a haka . Ina son Ya Aliyu Sosai,amma shi bai damu dani ba , ya Khaleel yafi shi Sona shi yake kulawa dani Sosai .

“Shiru ya isa haka babyn Ya Haidar , Wane ya faɗa Miki bai damu dake ba , ko jiya yazo kuma nasan don ya ganki yazo sai dai baku hadu ba. Mami ya Aliyu yazo? A'a ba don Ni yazo ba koda kuwa ya faɗa Miki hakan, yaushe zai dawo . Hannu Mami tasa tana lankafe takardar kana tace “ ki kwantar da hankalin ki , ai wannan ce shigar su ta farko 4 mount za su yi su dawo gida hutu . Kuma Kinga a yanzu sun yi kusan 3 mount nan ba da jimawa ba. Miƙewa Jidderh tayi tana daukar lunching box ɗin ta tare da cewa " Mami na shirya mu tafi yanzu.....!


Ɓangaren Aliyu kuwa ƙarfe Uku na asuba suka fara shirin fita training exercise da suke yi na awa biyu kullum , Kallon Ma'eesha yayi da take barci yana ƙara rufa mata bargo kana yace dasu Areef mu tafi ko?. Fitowa duka suka yi su kusan shida suke rayuwa a babban Ɗakin kowa da gadon sa da kuma wurin mu'amalar sa .

Sojoji na hanga birjik dukan su da kayan exercise suna running round tare da ɗaga ƙafafun su , Hango Aliyu Yasa Khaleel saurin isowa inda suke cikin Muryar sauke nishin wahala ya furta “ Haidar ina ka shiga tun jiya? ” . Kallon sa Aliyu yayi yana fara training exercise ɗin ba tare da yaba Khaleel amsan tambayar sa ba sai cewa yayi “ morning ya Khaleel ”. Shafa kan ƙanin nasa yayi yana wuce shi tare da cewa " ka kula yau Please kaji ban son ka sake wani laifi kaji? . Running up and down ya fara yi ba tare da yace da Khaleel komai ba...Kusan 5:30am sannan suka koma Wurin ƙwanan su . Don haka suke yi 7am su shiga class don karatu. Suna komawa Aliyu ya nufi Toilet ɗin su alwala yayo yana sallah kana ya juya yana kallon inda Ma'eesha ke ta barci har a lokacin. Miƙewa yayi yana ɗaura Towel a Kugun shi tare da nufar Toilet don ya watsa ruwa ya fito yayi shirin shiga aji kuma .

Mintuna Sha biyar ya dauka ya fito hannun sa ɗauke da ƙaramar Towel yana tsane suman kan shi . Areef ya gani da Ibrahim sai Adam suna zagaye da Ma'eesha da ta buɗe idanun ta tana Kallon su duka , Kaman mai tunanin wani abu akan su ,su kuma sai murmushi da wasanni suke yi mata suna kiran sunan ta “Ma'eesha , Areef na wasa da hannayen ta , don kuka ne basa so tayi . Ganin haka yasa Ali sakin Murmushi yana saurin ƙarikowa inda Suke. Da hannun sa ɗaya ya ɗagota yana Girgiza ta tare da yin wani tambul yana juyata sama zuwa ƙasa kan ta na kallon ƙasa yana dariya tare da cewa “ Kema Bara kiyi naki morning exercise ɗin ”. Innalillahi...Aliyu Meye haka? Bafa ƙashi a jikin ta”. Muryar Su Ibrahim ya katse shi a tare . Kallon su yayi yana kallon Ma'eesha dake ɓaɓɓaka dariyar ta babu alamun Taji tsoro . A'a dole itama zata rinƙa yin morning exercise sannan sai nayi mata wanka.................!




*Wani aiki sai soja😱💃🏻Rainon soja zamu sha kallo🤍🤣 to masu karatu kar ku manta littafin rainon soja na kudi ne masu ɓukatar fara payment ga yanda tsarin yake. Regular group ₦500 vip group ₦1000 special payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne ta wannan number 09061466409 yan Niger zaku turo da katin Airtel na 500f ...kar ku manta wurin yi mun sharing zuwa ga masoya baki daya🙏🏻🕊️.*
[12/15, 1:59 PM] Abu~ammar: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story .*




Free page 5



________________________
MAMAN TEDDY
Marubuciyar
My Lady boss
Walijaam
Siyasata
Yar maula
Kwaryar sama
The virgin maid
Gidan Ƙwarata
The Sexy Boss
Yar aiki
Bafullatanan Ruga
X world duniyar shahara
Mr romantic
Dijama
Kwarton manya
Yar tsakar gida
Zuma da maɗaci
Sadaka yalla
Yar waye
Gidan zaurawa
Taɓarah
________________________
"Da sauran su💃🏻 a yanzu kuma gata ɗauke muku da sabo mai ɗauke da sabon Salo na musamman wato Rainon soja , niko da kaina nace za'a sha duka😹soja da raino ai abun ba'a magana 🤣labarin sai wanda y karanta shi kar ki bari ayi babu ke Hajjaju...labari ne mai tafe da rikirkirteccen Al'amura wanda da fari sai kunce ya abun yake , Gaban yafi farkon🕊️dadi tun a yanzu ina sauraren comments din ku da masu fatan alheri na gode sosai . Sannan masu buƙatar daga farko don Allah kuna rinƙa tambaya ne a wasu groups da kuke ciki , idan kuka biyo Ni ayyukan da hidimomin nawa suna da yawa , bana samun damar turawa ta private 🙏🏻. Gare ku masu buƙatar fara payment na littafin Rainon soja ga yanda tsarin yake ; Regular group ₦500
Vip group ₦1000
SPC payment ₦1500
Via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 Vtu transfer number 09061466409 Yan Niger zaku turo da katin Airtel 500f free page ya fara nisa a page 10 Free zai ƙare maza ku hanzarta wurin biyan naki ana ta payment💃🏻Ni kuma ina ta adding😹🤗 to kar a barki a baya, ko kiyi tunanin samun na bulus mutane na yan amana ne..........!


•••••

Ganin haka yasa Ali sakin Murmushi yana saurin ƙarikowa inda Suke. Da hannun sa ɗaya ya ɗagota yana Girgiza ta tare da yin wani tambul yana juyata sama zuwa ƙasa kan ta na kallon ƙasa yana dariya tare da cewa “ Kema Bara kiyi naki morning exercise ɗin ”. Innalillahi...Aliyu Meye haka? Bafa ƙashi a jikin ta”. Muryar Su Ibrahim ya katse shi a tare . Kallon su yayi yana kallon Ma'eesha dake ɓaɓɓaka dariyar ta babu alamun Taji tsoro . A'a dole itama zata rinƙa yin morning exercise sannan sai nayi mata wanka na bata break ɗin ta kamin mu wuce class .

Humm to yanzu a ina ne zamu bar Ma'eesha kasan ba zai yiwu mu bar ta anan ita kaɗai ba , sannan kuma ba zai yiwu mu tafi da ita class ba. Areef ya katse Aliyu Haidar da a wannan lokacin yana cigaba da tambula Ma'eesha yanda yake mata kaman ɗan namiji....Itako gani take wasa yake mata dariyar ta take yi abun ta . Ƙwantar da ita yayi bisa gadon nasa yana kama hannayen ta biyu tare da ɗagota sama yana maida ta kusan mintuna biyar yana mata wannan salon motsa jinin nasa , yayin da bai Bama Areef amsar tambayar sa ba. Jin shirun nasa na wasu mintoci babu amsa yasa Areef juyawa yana nufar Toilet shima don ya fito ya kimtsa sannan sai su cigaba da maganan.

A haka nan dukan su suka shirya cikin shigar su ta uniform ɗin sojoji duka layi ɗaya suke wato Sojojin Airforce ne. Wannan yasa komai nasu tare suke yi .

Miƙewa Aliyu yayi yana sauke Gwauron numfashi kana ya kalli Ma'eesha da take bin sa da kallo War War War ta yara . Ina zuwa ma'eesha. Ya furta yana nufar inda yake jin maganan masu kawo masu breakfast.

“uhm common baby ”. Ya furta a lokacin da yake dawowa hannun sa ɗauke da basket dake shake da kayan karin kumallon su . Maganan yayi yana sakin mawa ma'eesha murmushi wanda nan take naga yarinyar ta juya da sauri tana miƙewa tare da rarrafowa zuwa inda yake. Tea ya fara haɗa mata tasha sosai, kana ya fara kokarin bata shinkafan da mai ne ta ture kan ta don bata buƙata . Murmushi yayi yana cewa “ Ok bari Nima nayi break fast sai mu wuce aji tare 😱” . Humm da rabon yau ma ya ƙara amsar wani horon 🥴 Allah dai ya kiyaye Ali” .

Yana tsaka da fara break fast din ne dukan su sauran abokanan nasa suka iso don sun kammala shirin su suma , zama suka yi suna fara nasu , wanda kamin su gama ne suka ga Aliyu ya miƙe yana kai hannun sa zuwa inda Ma'eesha take , ɗaukar ta yayi yana nufar Toilet da ita . Da ido Areef ya bishi , yayin da Ibrahim yace “ Aliyu fa ba zai iya yi mata wanka ba , Mene ya iya , nifa mamaki ma nake yi yanda yarinyar har take dariya da nuna so idan ta gannshi , bai iya komai ba Wallahi , Don Allah ku dakatar dashi Bara na kira Joy tayi mata Wankan just give me 1 minute I'll be back ”. Yana Ida maganan yana miƙewa cikin sauri tare da nufar ɗakin da su joy suke. Suma tare suke duka a wannan shekarar suka fara karatun duka .

Miƙewa Areef yayi yana biyo bayan Aliyu tare da shiga Toilet ɗin , kallon kallo suke yi don zaune ya tadda Aliyu ya tasa Ma'eesha yana kallo ya rasa ta ina zai fara wanke ta . Wani dariya ne ya taho ma Areef amma sanin halin Fushin Ali da jarabar sa yasa shi danne ta don dole . Aboki ka dakata yanzu joy zata taho sai tayi mata wankan . Areef ya furta yana ƙariƙawa zuwa ga Aliyu. Kallon sa Aliyu yayi kana juya yana kallon Ma'eesha, ba tare da ya kalli Areef ba idanun sa na kan ma'eesha yace “ Ai matsalar baka gani ba , bafa baf ɗin wanka duba ka ga , to a ƙasa ne za'a yi mata wankan? .

Eh mana yo shi yasa Nace ka kawota mu kai ma mummyna nasan zata kula da ita sosai.

Please stop saying that..”! Ni zan iya kulawa da Ma'eesha tun da mami ta wulaƙantani akan ta , dole da kaina zan raine ta kuma zata girma cikin kulawa ba zata mutu ba . Cikin sauri Areeef ya ware idanun sa a zuciyar sa yana cewa “ Ai ko indai kai ne zaka raini ma'eesha har girma to ko bata mutu ba ,zata ɗanɗana azaba . Ni kaina azabtar dani kake yi bare kuma ita dakake iƙirarin zaka raine ta ka bata tarbiyya . Sorry for you ma'eesha ”. Yana tsaka da wannan tunanin ne Ibrahim da joy suka shigo Toilet ɗin . Wata irin gabjejiya ce a tsaye take kaman namiji, Ya ne mutumin ? How are you?. Tayi maganan tana kai hannun ta tare da kama hannun Aliyu wanda yayi kinini da rai . Ali ya kake ?”. Ta kuma tambayar sa a karo na biyu wanda a daƙile yace “ Lafiya” . Wannan ce yarinyar ? Wow cutie😻 . Kyaƙyƙyawa ta furta tana kai hannun ta tare da amsan ma'eesha. Wasa ta fara yi mata tana cire yagalgwalin rigar jikin ta irin ƴan gobe sunan nan , da gani kasan yarinyar ta taso ne in a poor condition sai dai duk da haka kyawunta bai ɓoyu ba don tun a yanzu kyaunta mai fuzgar hankali ne ƙwarai . Sauke ta tayi ƙasa tana fara takawa da ƙafafun ta kana Joy ta sauke heater tana sirka ruwan. Skirt ɗin jikin Ma'eesha ta sauke , yayin da su Aliyu suka ja daga baya suna jiran ta kammala ko nace yana jiran ta kammala ya saɓa kayan sa .

Muryar Joy yaji tana dariya tare da cewa “ Oh my God, this girl she's beautiful...Areef kaga yarinya tun tana ƙara da shape da hips ? Jikin ta luwai........Keeeeee.....!!! “muryar Aliyu ya katse ta cikin doka mata Wani irin tsawa mai kama da saukar Aradu sai da joy ta firgita , ba ita kaɗai ba ma Har ta ma'eesha kuka ta saka cike da tsoro tana ƙanƙane hannun joy.

“Dama ku Arna babu wanda ya kai ku Iskanci, to amma ke naki iskancin yafi na kowa , yar iskar banza ...wasu irin ashar yake Aunata mata tamkar wanda yayi zaman tasha, yanayin sa kaman wanda zai buge ta , don jikin sa har tsuma yake yi . Shi kan shi bai san mene ya hasala shi bisa kalaman nata ba . Fice mun daga nan kar ki sake dawowa.

Kuma malamai duka ku fita Nine zan rinƙa mata wankan ta da koman ta bana buƙatar taimakon kowa , tun da abun ya koma harijanci🙊😹 . Gimtse Dariya su Ibrahim suka yi don yanda joy take kyarma daga taimako sai ta baka dariya . Da sauri ta fice bata ce dashi komai ba . Haka suma suka fita ,suna barin sa daga shi sai Ma'eesha.

Hannun sa yakai yana ɗago Ma'eesha tare da fara cire ƙaramin Pant ɗin jikin ta. A kan ƙafafun sa ya zaunar da ita yana fara Wanke mata jikin ta don yanda ake ma yara wanka bai fa sani ba . Sai da aka gama wanke jikin ne ya fara zuba mata ruwan ɗumin yana mata Wasa da ruwan tana dariya, a haka ruwan da ya ƙarar mata a jiki yafi ƙarfin bokiti babba uku , yanda take dariyar shi yake sanyaya zuciyar sa .

Kallon Areef Ibrahim yayi kana yace " saura mintuna biyar fa mu makara ”. Shiru Areef yayi kana Adam yace “ Leka kace masa yayi sauri ”. A'a kai dai kaje . Hahahahaha....suka fashe ma Areef da dariya . Ibrahim ne yace “ Wai tsoron Ali kake yi ne ?”. A'a bana ce ba ,amma kai zaka iya zuwa ”. Ok ya furta yana kama hanya tare da kutsa kan sa cikin Toilet ɗin . Wasa yaga yana yi mata da ruwan suna dariya , Dariyar da bai taɓa ganin Aliyu yana yin irin shi ba . Shi da ko murmushi ne sai yaso yake yi. Amma yau dariya har da kyakyatawa da ƙaramar yarinya . Aliyu saura mintuna biyar mu makara ”....Wani ɗauke wutaaa Aliyu yayi cikin fushi da ɗan ɗaga murya ya furta “ Dole sai dani zaku tafi , zaku iya tafiyar ku abin ku ”. Jin haka yasa Ibrahim juyawa har yakai ƙofa Yaji Muryar Ali ya katse shi da cewa “ Daga yau kar wanda ya sake shigo mun Toilet indai ina tare da Ma'eesha 🤗 . Saurin kallon sa Ibrahim yayi kamin yayi magana Nan Take Haidar yace “ Yessss haka nace kar wanda ya sake shigowa ko baku ga mace Bace ita , Idan ina mata Wanka kar wanda ya ƙara shigomun ka faɗa masu ”. Sakin baki Ibrahim yayi yana ficewa daga Toilet ɗin tare da isa inda Su Areef suke yana mai labarta masu yanda suka yi da Ali yanzu a Toilet .


Wani irin dariya Areef keyi har da buga ƙafa kana Adam yace “ Ok to shi ba namiji bane kenan, me zamu kalla a wannan jaririyar yarinyar? Kai nifa Ban gane ba ne ma🥴 . Ya furta yana kama ƙwiɓin sa . Fashewa da Dariya Ibrahim yayi kana yace “ Kasan halin Aliyu fitina ce kawai irin nashi yake neman kan wa zai sauke ,kaga kuwa ba Dani ba , Ni nayi na class kuma zaku tsaya ne ko na tafi Ni kaɗai .

A'a mu jira shi ya fito sai mu tafi duka.

Adam ne ya kalli Areef kana yace “ Ok tom mu jira shi kaga ikon Allah yana fitowa zaice mu fita daga waje ya shirya Ma'eesha 🤣 kar a ga mata jiki . Yarinya kaman kazar turawa wata can ƙasa da ita gata fa gijib. Dariya suka saka baki ɗaya cikin sauri suna ficewa tare da nufar inda ajijiwan karatun su yake.

Shi kuwa Aliyu koda ya fito yaga babu su bai damu ba ,don dama ya kuɗurta a ransa indai ya fito ya gansu sai yasa sun fita sannan zai shirya ma'eesha su tafi aji tare ....jama'a kuji mun Bala'i, ta ina zai yi karatu da yarinya abun da ba'a taɓa yi ba kenan.

Kallon ta yayi yana tunanin to wani kaya ma zai sanya mata ? Palmers oil ya shafa mata yana ɗaukar kayan da ya cire mata yana mai da mata . Idan kina buƙatar wani Abu Kice Uncle Zan sha ruwa ? Ko zanci abinci idan fitsari zakiyi sai ki mun magana kinji Ma'eesha? Yayi Maganan yana kallon ta , da itama take bin sa da kallo ganin babu alamun ta gane Hausan nasa ne yasa shi cewa “ Bata ma fahimta ba ,muje ”...ya furta yana kai hannun sa tare da goya ta a bayan sa , hannun sa ɗaya yana ɗaukar jakar bayan sa .

**
Shigar sa ajin yasa duka kowa kallon sa tare da bin bayan sa da kallo ganin kyaƙyƙyawar yarinya tayi lamo kan ta ko hula babu , gashi a warware yanayin tsayin gashin ta da cikar shi kaman yarinyar larabawa yafi komai tafiyar da hankalin su gare ta. Hango Su Ibrahim yayi da Areef Adam a can sama Captain Isma'il yana basu horo , wani kallo Ali yayi masu yana kauda kan sa a Zuciyar sa yana cewa “ Taɓ ashe duk ma saurin da suke yi sun makara ,aikin banza kenan”. Nufar mazaunin sa yayi yana aje Ma'eesha kana ya dawo gaban inda Captain Isma'il yake yana ƙamewa tare da cewa “Morning sir” .

Ya akayi ka zo a makare? Me yasa baka kai yarinyar section ɗin su ba ? . Captain yayi maganan yana kallon Aliyu don a tunanin sa Ma'eesha makarantar yara na cikin NDA ɗin take yi. Magana ce ta fara tashi ƙasa² . Ai ƙanwar Aliyu ce . Joy ne tace “ Eh nima naga suna kama sosai ”. Ɗauke ta ka kaita idan ka dawo kayi joining ɗin abokan naka . Captain Isma'il yayi Maganan tare da kallon ɓangaren da su Areef suke .

Ok sir . Aliyu ya furta yana isa inda Ma'eesha take , taho ma'eesha ”. Hannun sa yakai yana ɗaukar ta tare da ficewa da ga class ɗin.

“Khaleel dake can nesa mamaki yake yi a ina Aliyu ya samu yarinya? Gaba ɗaya kan sa ya kulle , Ya rasa wane zai tambaya ,gashi abokanan sa sai tambayar sa suke yi wai dama bayan Jidderh suna ƙanwa ce? . Shi dai ya

5 Comments On RAINON SOJA
avatar
hauwa-u-2

11 months ago

Reply

Beyin download

avatar
taskar

11 months ago

Reply

Replying to hauwa-u-2

dole sai kin yi subscription sannan zai downloading

avatar
taskar

11 months ago

Reply

Replying to hauwa-u-2

dole sai kin yi subscription sannan zai downloading

avatar
taskar

11 months ago

Reply

dole sai kin yi subscription sannan zai downloading

avatar
taskar

11 months ago

Reply

dole sai kin yi subscription sannan zai downloading

Please Login or Register in order to submit comment