Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai sa ta zama mutum ba, dan mu sittin da takwas ne a jikinta, mu sitti duka macizai ne kowa da yaren da yake ji, ita ma a karan kanta wacce ta yi mata aiki sawa ta yi a maidata macijiya, mu kuma aiki muke yi a kanta, ko da mun fice daga jikin Samima ba shi zai hanata zama macijiya ba, har sai wacce ta yi sanadiyyar komawarta macijiya taje ta fasa kaskon da muka bata, ta daina haɗa siddabarun tsafin da asirin da muka bata, sannan ta je ta tone maganin da Shugaba Ogiduwa ya bata ta binne da gashin Samima da matacciyar katuwar macijin tsafin da muka bata,kuma mun bata sharaɗi, wanda idan wannan aiki ya kare zata haɗu da gamonta ta ce mana ta amince, dan haka ko da mun fita a jikin Samima ita karan kanta Samiman macijiya ce, tunda ba a haƙo asirin da aka binne da gashin kanta ba,balle ma ba zamu fita ba, tun da Shugaba Ogiduwa ya bamu umarnin zama a jikinta ne" nan aka hau drama babu yadda Malam Abba bai yi ba akan su fita amma firrr sun ƙi fita, ga dare ya tsaƙa sosai, Baba da Umma sun ga tashin hankali wanda ba a saka masa rana, Suhail kuwa tuni numfashinsa ta daina aiki tun sadda Samima ta koma macijiya ya suma a tsaye, dan shi tun da aka haifesa bai taba ji ba ko a kanun labarai ba, balle ya gani, sai ga shi yau ya gani da idonsa, babu wanda yasan halin da Suhail yake ciki sai Malam Abba wanda da ya lura da hakan ya aike Nuren waje da ya kira masa almajiransa guda biyu, ko da suka zo ya basu umarni su dauki Suhail su tafi da shi, su tabbatar kuma sun ba shi rubutu ya sha, dan ya dawo hayyacinsa, suka amsawa malamin nasu cikin girmamawa kafin suka ciccib'i Suhail, ruwan magani mai zafin gaske Malam Abba yake watsawa macizan dake jikin Samima, wani ɗumi mai fitar da zafi gami da turiri ne yake tashi a ɗaki, daga karshe ma Malam Abba ya cewa su Baba da Umma su fita, aka bar shi daga shi sai Nuren, Malam ya yi iya yinsa inda a karshe ya fara tari, da kyar ya samu ya ƙona ɗaya ya kori biyu, macijin da ya yi magana a jikin Samima da ya ji azaba ya cewa Malam Abba.
"Zan je na dawo, zan je na sanarwa Shugaba Ogiduwa halin da ake ciki, amma karka sakawa ranka cewa mun rabu da Samima kenan dan zamu dawo" da haka ya yi wani juyi na maciji sannan ya zube ƙasa, kamar da minti ashirin da biyar Samima ta fara komawa mutum, har ta zama mutum, ba zato ba tsammani sai ga hawaye na bin fuskar Malam Abba wanda yasa Nuren shiga Babban damuwa, a kiɗime Nuren ke tambayar Malam Abba akan me ya saka shi kuka, kallonsa Malam Abba ya yi ya ce.
"Muje muyi sallar asuba dan lokaci ma har ya gota"
"To Malam, Samiman fa, a bar ta a nan?"
"Eh ka bar ta, babu abun da zai sameta"
Nuren ya gya ɗa kai, Malam ya yi gaba shi kuma ya bisa a baya yana waigen Samima cike da tausayawa, ko da suka fita aka raka Umma cikin gidan wajan Matan Malam, mahaifin Samima da Nuren suka yi alwala suka wuce Masallaci a tare da Malam, har aka yi sallah aka idar Nuren bai ga Suhail ba, tambayar wa inda suka fita da shi da dare ya yi, suka ba shi amsa da yana can a kwance ya kasa tashi yace sallar ma a daki zai yi, tsaki Nuren ya yi mai cike da haushi, sai karfe bakwai da rabi kafin suka koma ɗakin Malam, su na shiga suka samu Samima zaune sai aikin zare ido take yi da sauri Nuren ya karaso ya ɗuka a gabanta ya ce.
"Ƙanwata!? Kin ganeni!?" ta gya ɗa masa kai ba tare da tayi masa magana ba, Malam Abba ya ce.
"Samima matso nan" a hankali ta matsa gaban Malam Abba, ya ce.
"Kina jin wani abu a jikinki?" nan ma ji ta yi ta kasa magana, dan kamar an rike mata baki haka ta ji, Nuren ya ce.
"Innalillahi!! Malam ba dai sun mai da min da Ƙanwa kurma bane?"
"A'a Nuren, ba su mai da ta kurma ba, amma a cikinsu akwai kurame mutum uku, akwai baibaye mutum uku, akwai gurgu mutum ɗaya,akwai kuma kuturu mutum ɗaya, shaiɗanu sittin kuma dukkansu manyan shaiɗanun macizai ne, yanzu haka ma ba ita bace, kurman ne a jikinta shine ya hau,amma su wannan ba wani gagarumar matsala ba ce, sittin din nan su ne wasu ƙaramin yaƙin da zamu yi, yanzu ga wannan ruwan maganin ka bata da bismillah ta sha" Nuren yasa hannu biyu ya karba ya tallabo Samima ya bata ta ƙi karba, sai da ya matse mata baki ya ɗura mata kafin tasha, nan ta hau jera masa attishawa guɗa uku, kafin ta sake sulalewa a jikinsa, zafafan hawaye ne masu matuƙar tururin gaske Nuren ya hau yi, dan ƙaramin tausayi Samima ta ba shi ba, tun jiya take shan wahala, Allah ne kadai yasan abun da take ji, amma dai Allah ya isanta wa Asabe wallahi, yake faɗi a cikin ransa, yan mintina da basu gaza sha uku ba, a hankali ta fara buɗe idanunta wanda suka mata nauyi sosai ta ɗora su a fuskarsa, muryarta wanda da ka ji za ka san cewa ta wahala ta furta.
"YAYANA?" Nuren kasa magana ya yi illa gya ɗa mata kai kawai da yake yi, Malam Abba ya ce.
"Samima?" a hankali ta juyo ta ɗukar da kanta kasa ta amsa a sanyaye cikin girmamawa.
"Na'am Malam"
"Kina jin wani abu a jikinki"
"Malam, jikina ciwo yake min sosai, ko wace gaba ta jikina kamar an canzo min ba nawa bane"
Girgiza kai Malam Abba ya yi, ya ce.
"za ki iya tafiya?"
"A'a Malam" Malam Abba ya ɗaga waya ya kira ma'aikatan Matansa, suka zo ya basu umarnin su taimakawa Samima su kai ta cikin gida wajan Matansa da mahaifiyarta, suka amsa masa da to sannan suka kama Samima suka yi da ita gida, ko da suka shiga Umma ta rungume ƴarta suka sha kukansu, Matan Malam Abba su uku mata nagari wanda basu ruwansu, nan su ma suka din ga tayasu kukan, ruwan mai zafi aka hadawa Samima sai ka ce wacce za ayiwa wankan jego, Malam Abba ya aiko da garin magani yace ayi mata wankan da shi, Umma ce da kanta ta yiwa ɗiyarta wanka da ruwa mai zafi sosai ta gasa mata jiki, har ta ɗan ji dama-dama, abinci mai rai da lafiya aka shirya musu, amma na Samima daban kasancewar an saka mata magani a ciki, Malam Abba tare dasu Baba suka yi karin kumallo, inda Nuren sai aikawa Suhail harara yake yi, Suhail kuwa ya yi kamar bai san Nuren na yi ba, bayan sun gama karyawa ne Malam Abba ya ce, ya yi magana da Malam Habibu zasu taho yau shida Baba Malam, da wasu hazikan almajiransa wanda zasu yiwa Samima addua, fatan samun narasa suka yiwa juna, Malam Habibu su ma basu samu damar shigowa maiduguri ba, sai dare, a daren suka hau aiki akan Samima inda suka ci bakar wuya,ita kuma tasha baƙar azaba, da kyar da suɗin goshi aka samu ashirin suka bar gangar jikinta,kuma a hakan duka magana ɗaya suke maimaitawa akan cewa ko da sun fita jikin Samima, ba shi zai sa ta zama mutum ba har sai an tone sihirin da aka binne, inda Baba Malam ya ce a kamo Asabe a kawota maidugurin idan ta ji azaba dole ne ma ta tona sihirin, Malam Abba ya girgiza kai ya ce.
"Wannan yasha bambam da sauran sirihin da ake yiwa mutane, karku manta ɗayan biyun ne, wajan ganin kamo Asabe a tilasta mata haƙo wannan sihiri idan ba muyi a hankali ba zata ita kashe Samima" mu bi komai a sannu mu dage da addua, ai Allah ba azzalumin bawansa bane sai dai bawa ya zalunci kansa.





🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀



Ihu Asabe ke yi a daki sakamakon marin da ake dauketa dasu, ga amo na tashi a cikin dakin, gargaɗi ake yi mata akan cewa karta sake ta mance alkawarin da ta dauko, idan kuma wannan sihirin ya karye kar ta manta da abun da zai sameta, sannan sun gaya mata kuma ta amince hako wannan sihirin tamkar ta tono ramin kabarinta ne da kanta mai macizai, tace ta amince, marin da suka din ga dauketa dasu kuma na azaban da aka gana musu ne suka rama, dan haka ta yi a hankali, dan Malamai sun hadu akan Samima su na yi mata adduoi da magani, sannan yaron nan Nuren a shirye yake dan ya bada rayuwarsa wajan ganin Samima ta samu lafiya, dan haka tasan abunyi dan ko da wani lokaci komai zai iya ce'be mata, da haka suka tafi suka bar Asabe da fuska a kumbure baki ya koma gefe dan kuwa ta maru, mari ba a hannun aljanu ya mutum zai koma? Nan Asabe ta kudirtawa ranta ko sama da ƙasa zai haɗe ba zata taba tono sihirin nan ba,kuma Nuren sai ya auri shalelenta Sha'awanatu, kuma abun da ya mata akan abokinsa zata rama, dan sai ta kashe *SUHAIL* shi ba zata yi kashesa ba, tin da Sha'awa tana son shi, amma sai ta dauki fansar canza mata kamannin da yasa aka yi, duk a zuciyarta Asabe ke shan wannan alwashi, ta miƙe da kyar idanunta basu gani sosai, ta ja ruwa ta haɗa ruwan zafi ta yi bandaki.




🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀




_KUYI HAKURI JINA SHURU KWANA BIYU, LAMARIN BA A CEWA KOMAI SAI ADDUA ALLAH YASA MU DA CE._



KARKU MANTA LITTAFIN SAMIMA GAJERAR LABARI NE WANDA YA ZO MUKU DA SABON SALO, NI DAI BA ZAN FASA GODIYA DA GAISUWA GA MASOYANA BA, NA GODE.



*UMMU AHLAN TA KU CE*👍🏻
[02/09 à 08:47] 🌹🌹Flower 🌹 🌹: *SAMIMA* 🐉🐍
( _macijiya ce_)

Na
*ZAHRA ABDUL*
(MOMYN AHLAN)

Gajeran labari.


SHAFI NA TAKWAS. ✍🏻


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*




Yau kwanan Samima biyu bata san a wace duniya take ba,sakamakon maganin da ake mata na fidda mata shaiɗanu, su Malam Abba Albany sunyi matuƙar kokari dan kuwa a kwana biyu sun fatattaki shaiɗanu arba'in da takwas a jikin Samima inda ya rage saura shaiɗanu ashirin, sunyi-sunyi su sake fidda wasu amma abun ya gagara inda Baba Malam ya zo zai mata magani ya duba taurarinta ya ga haɗe suke da na *NURAIN* dan haka ya sanar dasu Malam Abba da Malam Habibu, akan cewa su ne mi Nuren ayi masa magana, indai ana so su kara samun nasara, tunda taurarin Samima haɗe yake da na Nuren din, ke nan zanen kaddararsu ɗaya ne, kuma Baba Malam ya yi bincike sosai idan har Nuren ya auri Samima wani duhu zai bayyana ga Asabe, hakan zai sa ta samu tawaya a wajan wani sihirinta, dan haka Malam Abba da Malam Habibu suka ce zasu ne mi Nuren da wannan maganar tun da ya ce zai iya bada rayuwarsa akan Samima ta samu lafiya.


Malam Abba da Malam Habibu ne suka kira Nuren, nan Malam Abba ke magana kamar haka.
"Nuren, a gaskiya zai fi kyau ace ka auri Samima, sabida wani magani da zamu yi mata, kuma mun ga zanen kaddararku daya ne da Samima, amma kai ya kake gani?" shuru Nuren ya yi yana nazari kafin ya ce.
"Malam, bazan ƙi Samima ba, kuma a shirye nake da na auri Samima, amma ina so na gayawa iyayena, dan su na da hakki a kaina a matsayina na ɗansu, duk da bana shakka a kansu zasu amince" Malam Habibu ya ce.
"Tabbas ni shaida ne akan iyayenka, Alhaji Ibrahim da Hajiya Amina mutanen kirki ne sosai, ka ne me su kuyi magana idan ya so sai mu ci gaba, In sha Allah nan da kwana biyu abubuwa zasu ɗan iya dai-daita da yardan Allah" Nuren ya jinjina kai ya fice, ko da ya fita Suhail ya fara gaya ma wa, inda Suhail ya ce.
"Allah yasa haka shi ne mafi alkhairi" dan kwana biyun nan Suhail baya jin dadi,kwata-kwata ya kasa gane kan shi, kallonsa da kyau Nuren ya yi, ya ce.
"Suhail? me yake damun ka ne kwana biyu duk ka canza, ko sabida ka ga Samima a macijiya ne?" girgiza kai Suhail ya yi ya ce.
"Nima ban san meke damuna ba, haka kawai wani lokaci zan din ga jin kaina na min ciwo sosai ga faɗuwar gaba"
"To me ya sa hakan?" cewar Nuren, maƙe kafaɗa Suhail ya yi alamun bai sani ba, kyalesa Nuren ya yi, dan ya danganta hakan da tsoro ne irin na Suhail, waje ya fita ya ba wa Suhail waje ganin baya son magana, Nuren na fita kuwa Suhail ya kwanta yana dafe kansa tare da karanto kalmar "Innalillahi wainna ilayhirrajiun!!" sakamakon sarawar da kansa ke masa, ko da Nuren ya kira iyayensa ya shaida musu, Abba ya fahimcesa inda ya nuna masa amincewarsa ya musu fatan alkhairi tare da yiwa Samima adduar Allah ya bata lafiya,amma nan Momy ta tubure ta ce sam bata ji ba, bata gani ba, ace ɗanta ɗaya tilo aurensa na fari ya fara da macijiya, ba shagali biki ba komai, ina sam ba zata amince ba, bata lamunta ba, Abba babu yadda bai yi da Momy ba, amma ganin da gaske take yi nan shi ma ya rufe na shi idon ya kalleta cikin b'acin rai ya fara magana.
"Amina kin ban mamaki wallahi!!! ashe son da kike yi wa Samima bai kai zuci ba?" cike da masifa Momy ta ce.
"Ya kai zuci mana, amma Ɗana ƙwalli ɗaya ne ya auri macijiya ne ban amince ba, duk son da nake mata kuwa, haka kawai ya aureta ta zo ta kashe min shi na shiga uku, nan fa a gabanka ya kiramu yana kuka akan cewa Shaiɗanun sun ce ko da sun fita a jikin Samima, Samima Macijiya ce? Ko ba haka ya ce ba? Tun da Gwaggonta ta tirje ita ba zata mai da ta mutum ba, ga shi bata rikiɗewa sai dare, sai su na kwance kawai ta sare min shi? Tabbb!!!! Sammm!!! Ban amince ba in dai ni ce Uwar Nuren wanda na sha wahalar ɗaukar cikinsa na sha wuyar nakuɗarsa ban amince ya auri Samima ba, na dai yarje masa ya taimaketa amma ban da aure" sosai Abba yake bin Momy da kallo kamar yau ne ya fara ganinta, ji yake yi kamar an canzo mi shi Aminarsa wannan ba ita ba ce, amma kasancewar tunowar da ya yi ɗan adama tara yake bai cika goma ba ya saka shi kama hannunta suka zauna cikin sanyin murya ya ce.
"Amina? Yanzu misali ace ke ce kike da Samima, ace Samima ƴarki ce, Nuren kuma Ɗan Zulaiha ne, ga dai ƴarki Samima tana fuskantar jarabawa, aka zo maganar taimako a matsayinki ta Uwa Mahaifiya idan Nuren ya ce ba zai auri ƴarki ba, domin ya taimaka mata ya za ki ji a ranki? Ki faɗa min gaskiya tsakaninki da Allah ya za ki ji? Karki manta duniya da faɗi, idan ka taimaki wani a yau, kai baka san wanda zai taimakeka a gobe ba, ina so ne ki fahimceni da kunnen basira, babu wanda yafi karfin jarabawa, ki amince ɗanki ya auri Samima dan ba ki san iya tarin ladar da Allah ya ba wa yaronki ba, ta sanadiyyar taimako, Allah yana son mutane masu taimako, karki kasance da son kanki da yawa Amina, son kai babbar illa ne ga rayuwar ɗan adam, sabida yana kai sa ga hallaka, fatan za ki yiwa maganata muhalli ki karbeta hannu biyu?" jikin Momy ne ya yi sanyi idanunta ya taru da hawaye ta tashi da sauri ta bar Abba,murmushi Abba ya yi dan yasan ya samo kanta.




🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀



Magana kamar wasa, a kwana biyu aka ɗaura auren Samima da Nuren a garin maiduguri, Abba shi da Momy sun zo in da manyan malamai suka halacci ɗaurin auren, Samima bata so auren Yayan nata ba, sabida tsoron laluran da take ciki, bayan an gama ɗaura aure Suhail na tsaye a gefe take ya ga gilmawar wani baƙin duhu wanda ya yi sanadiyyar faduwarsa ƙasa, da sauri Nuren ya ɗagosa yana jijjigasa yana ambatar sunansa cikin tashin hankali, nan aka cika akan Suhail, Malam Abba ya sa hannu ya dafe kan Suhail, sannan ya dafa ƙirjinsa, da sauri Malam Abba ya furta "Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!!" tuni zufa ta shiga wanke wa Nuren fuska ya ce.
"Malam, me ya faru? Me ya samu Abokina!!?" Malam Abba bai tsaya ba wa Nuren amsa ba, ya bada Umarnin a dauki Suhail a kai sa daki, da sauri almajiran Malam suka karbi Suhail da kyar daga hannun Nuren, aka wuce da shi, Nuren na biye da su a baya, nan aka rufu akan Suhail dan kuwa jinkiri kadan za ayi Asabe ta kashesa, adduoi Malamai ke yi wa Suhail ana bunka shi da hayaki, tun safe karfe sha ɗaya har yamma ana abu ɗaya da kyar da suɗin go shi aka samu Suhail ya farfado, kafin wannan lokacin idon Nuren sun kumbura suntum dan gani yake Suhail ya mutu, ga shi an hanasa shiga ya ga Suhail din, lokacin da aka gaya masa Suhail ya farka da gudu ya shiga ya rungumesa yana tambayar me ya sa me shi, nan ta ke Baba Malam ya ce.
" *ASABE CE*"
da sauri Nuren ya kalli Baba Malam.
"Asabe kuma? Asabe fa? To me Suhail ya mata?"
"Kashesa ta so yi" daga Nuren har Suhail idanu waje suka kalli Baba Malam, Malam Abba ya ce.
"Dama na faɗa muku zai yi wuya a gama ba tare da an rasa rai ba, sai dai wani ikon Allah"
"Innalillahi wainna ilayhirrajiun!!! wai me Asabe ta ke son zama ne?" cewar Nuren da jikinsa ke b'ari, Baba Malam ya ce.
"Ka dai ka bar mutum din da ya kauce hanya, idan har bawa zai din ga amfani da zugin zuciya tana ingiza shi zai iya zuwa ya aikata abun da ya fi haka, Allah ya rabamu da b'ata, ya tsaretar da imaninmu" aka amsa da ameen, Nuren ya ce.
"Ina ga zan koma Adamawa gobe dan na haɗa Asabe da hukuma" girgiza kai Malam Habibu ya yi, ya ce.
"Hakan ba mafita bane dan ba case din hukuma bane, mu kwantar da hankalinmu komai ya yi farko yana da karshe, wata rana sai labari, kuma Allah yana bai wa bayinsa masu aikata mugun nufi lokaci su ta aikata b'arna a ɗoran ƙasa, idan suka ƙi gyarawa Ubangiji shi yasan yadda yake yi da bayinsa, ko ba komai yanzu na tabbata Asabe ta samu tawaya, abu na farko auren Nuren da Samima dan mun rushe baƙin bangon sihirin da ta kulla a tsakanin Nuren da Samima, kuma shaiɗanun sun ra gu zuwa goma, a hankali komai zai dai-daita" jinjina kai suka yi, amma Nuren a zuciyarsa ya kudirta idan ya koma adamawa sai ya yi wa Asabe shegen duka.



@@@@@


A dayan bangaren kuwa Asabe ta ƙone a hannun sabida bata samu nasara akan Suhail ba, kuma ta sake tabbatar da duk sharrin Malaman da suke yi wa Samima magani ne,a madadin ta saduda sai kawai ta kwashe kayanta da ƴarta suka koma wani gida ba tare da kowa ya sani ba, baƙin ciki ya mata yawa ga aljanu sun fara addabarta, sabida sihirin da yake tsakanin Nuren da Samima ta rushe, tana so ta koma wajan bokanta a enugu dan ya sake yi mata aiki mai zafi wanda ya fi wannan, inda ta yanke shawarar ba zata sake yiwa Samima komai ba har na tsawon kwana biyu,ta inda zasu baro maiduguri su dawo adamawa ta samu ta kara aikata kudirinta akan Samima,kuma dole Nuren ya auri Sha'awa, dukiyar mahaifinsa ya dawo hannunta, da wannan shawarar da zuciyarta ta bata ta yi na'am da shi, kwana biyu ta ɗagawa Samima kafa, sosai kuma Samima ta ji sauki bata jin komai, da dare zata yi baccinta, ganin haka ya sa ta cewa ita fa ta ji sauki, Malam Abba ya yi murmushi ya girgiza kai shi kadai ya ga abun da ya gani, ya ce.
"Samima kina son komawa Adamawa ko?" ta yi dariya ta ce.
"Malam, na ga na ji sauki ne bana jin komai, duk da ance ba zan koma mutum ba, watakila a haka zan mutu, nayi tawakkali na karbi kaddarata, kuma muna da wani show ne yau saura kwana hudu shi ya sa"
Shuru Malam ya yi dan maganarta ta ba shi tausayi, da haka Malam ya kira Malam Nasiru mahaifin Samima akan cewa zasu iya komawa gida a gobe inda aka haɗasu da magani kala-kala, dama su Abba da Momy basu zauna ba,ranar da aka ɗaura aure da washe gari suka baro maiduguri, sosai shaƙuwa ta shiga tsakanin Umma da Matan Malam dan su na da matukar kirki, da washe gari asubanci su Nuren suka yi suka kama hanyar Adamawa, sai yamma lilis suka isa, a gajiye suke, Nuren ya ajiye su Umma a gida sannan ya ajiye Suhail, kafin shima ya wuce gida, ya watsa ruwa kafin ayi magriba ya zauna yana tattaunawa da Momy akan maganar ko Samima ta tare, ya ce.
"A'a baya so adamawa a san ya auri Samima sai ta ji sauki gaba ki ɗaya, sabida idan Asabe ta sani zata iya kashe Samima dan babu burbuɗin imani a zuciyarta" da haka suka ajiye magana.



🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀




Yau kwanar su Samima biyu da dawowa adamawa, yau kuma ta kama lahadi, haka kawai ta ji tana sha'awar shiga skull shiryawa ta yi ta gayawa Umma zata je makaranta Umma ta ce.
"Samima har ga Allah bana son fitarki, dan ni kam idan kika fita baya zame min alkhairi" murmushi Samima ta yi ta ce.
"Wallahi nima Ummana bana son fita, yanzu Sauda ta kirani take gaya min wai na b'ata b'at ba'a jina, kuma anyi paper dayawa bani nan kuma sun yi min,shi ne nake so na je karba na duba tun da sun ce su na cikin makaranta, gwanda naje mu haɗu mu gaisa" Umma ba sabida ta so ba ta ce.
"To shi kenan, ina fatan dai kin gayawa Nuren ya amince? Dan kinsan da da yanzu ba ɗaya bane ko?" dan yatsine fuska a boye Samima ta yi ta kwakulo yaƙe dan ba za ace dariya ko murmushi ta yi ba ta ce.
"Haba Umma, ke ma kinsan bana komai sai da izinin Yayana, ai na gaya masa kuma ya amince" cike da gamsuwa Umma ta ce "to a dawo lafiya" dan Samima yawancin shawararta da Nuren take yi, amma yau a zahirin gaskiya bata gaya masa ba dan bai san cewa zata fita ba, fita ta yi gabanta na faduwa tana adduar Allah yasa kar yazo Umma ta ce masa bata nan kuma ta gaya mata akan cewa ta tambayesa, neman napep ta tsayayi, kamar daga sama ta hango Sha'awanatu tana tafiya bazar-bazar tana lafcen ƙura, ko daga ina take oho sai kace almajira, girgiza kai Samima ta yi ta hau ɗaga mata hannu, Sha'awa tana ganin Samima ta ja dogon tsaki, kamar zata yi kuka, dan ganin Samima sai kace balarabiya, ita ma Samiman abun hawa ta hau ta kama gabanta ganin kallon wulakancin da Sha'awa ta yi mata, kar taje ta yi mata magana ta kama yi mata tijara a unguwa ga shi dama nemanta ake yi ruwa ajallo, dan har kwanar gobe kisan da ta yi akwai masu nemanta su kasheta,duk da ita ko kyankyaso bata taba kashewa ba, tana isa skull dinsu, a department dinsu ta iske su Sauda Sarah Sally Hidayan Abbas cikin murna ta miƙa musu hannu suka gaisa, ita ma ta zauna, Sally ta ce.
"Kee Samima kin ga yadda kika yi wani kyau kuwa?"
"Hummm Sally bana son tsokana, ni da nake ta fama da jinya bani da lafiya" Sarah ta ce.
"Gaskiya kam kin rame sosai Samima"
Hidaya ta ce.
"Amma me ke damunki haka Samima? Wannan ciwo ya ƙi barinki ki huta, wani irin ciwo ne?" Samima ta ce.
"Cutar sirri ne" suka kwashe da dariya su na tafawa hira suka ɗan taba na dan wani lokaci kafin suka fara yi mata bayanin abun da aka yi

Please Login or Register in order to submit comment