Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

guda
ɗaya a wajenka.
Ina son kayi wannan tafiya tare
da ni domin idan na sadu da boka Hulumul Makahur zan sami ƙaruwa mai yawa a cikin ilimin tsafi bare kuma ace an sami nasarar shiga kogon Maddarul ikisina tare dani."
Yarima Yauhana yayi murmushi yace,
"Na amsa wannan buƙata taka."
Ba tare da ɓata wani lokaci ba boka Karluz ya kimtsa nan take ya kira wani basamuden aljani waishi Labagaza ya baiyana gabansa.
Bayyanar Labagaza keda wuya sarki da 'yan majalisarsa suka zube kasa sumamnmu saboda tsananin razana.
Boka Karluz da yarima Yauhana kaɗai suka rage a tsaye ƙiƙam su kansu zuciyoyinsu na rawa.
Aljani Labagaza ya kasance ƙatoton gaske kuma mummuna ne na kwatance.
Faɗin tafin hannusa guda yakai zira'i ɗari,hancinsa kuwa wawakekene tamkar ƙofar gari,idanunsa manya-
manya ne kuma ɓalo ɓalo kamar za su faɗo ƙasa.
Idan ya wangame bakinsa sai kaga harshensa ya zazzago ƙasa har yana shafar ƙasa saboda tsawonsa,girman haƙorinsa guda ya ninka ɓauren giwa uku.
Yana da fukafukai guda ɗari,hamsin a kuiɓin dama,hamsin a kuiɓinhagu,idan ya bushe da dariya sai kaga ƙasa ta kama girgiza tamkar za'a kifar da duniyar.
Labagaza risina gaban boka Karluz yace,
"Ya shubana gani gareka me kake buƙata daga gareni?
Ina mai tunasar dakai cewa a halin yanzu saura aiki uku kacal tsakanina da kai,idan nayi na ukun shi kenan mun rabu har abada bazan sake yin bauta a garcka ba."
Boka Karluz yayi murmushi yace,
"Zancen ka dutsene,ya kai Labagaza kayi sani cewa ban kiraka nan ba sai don ka ɗaukemu ni da yarima Yauhana ka kaimu dajin dulmas inda boka Hulumul makahus yake a cikin abin da bai wuce sa'a huɗu ba wato kafin yarima Sammaru đan sarki Alyasil Bubus ya isa gareshi."
Koda jin wannan batu sai aljani Labagaza ya ƙyalƙyale da dariyar mugunta al'amarin da ya janyo rugujewar turakar kenan ƙasa ta kama girgiza,gaba ɗaya birnin na Rum ya kama tambal tambal. Ba don aljani Labagaza yayi sauri ya ɗauke su boka
Karluz dasu sarki Jamshul ba da tuni sun rufta cikin ƙasa ta binnesu.
Koda ganin wanna ɓarna ta aljani Labagaza yayi.
Boka Karluz ya daka masa tsawa yace,
"Ashe bana haneka da yin dariya a nan ba?"
Labagaza ya sunkui da kansa ƙasa yace,
"Tuba nake ya shugabana,haƙiƙa na sha'afane saboda jin bautar da na yiwa Bil'adama a doron ƙasa zan iya kai ku gaban boka Hulumul
lakahur a cikin abin da bai wice sa'a daya da rabi ba."
Boka Karluz ya sake yin murmushi a karo na biyu sannan ya watsawa su sarki Jamshul ruwa suka farfaɗo daga dogon suman da sukayi,kafin ɗayansu ya buɗi baki yace wani abu tuni boka Karluz da yarima Yauhana sun kama hawa kan aljani Labagaza tamkar masu hawa gini mai matattakala dubu,cikin gudu suka isa tsakiyar gadon bayansa suka zauna.
Zamansu ke da wuya aljani Labagaza ya buɗe fukafukansa gaba daya đarin ya tashi da su sama.
Yarima Yauhana ya rinƙa ɗagawa sarki Jamshul hannu har suka ƙule a cikin gajimare.
Kamar yadda al'amura suka kasance a birnin Rum haka suka kasance a birnin Ƙisra da Farisa tamkar haɗin baki,sarkin Ƙisra na da ɗa guda kuma Jarumin gaske sunansa Lubaika.
Yanzu haka Lubaika ya nufi dajin Dalmus don riskar boka Hulumul Makahur bisa kan wani
aljani wai shi Karakainu.
Shi kuwa sarkin farisa yana da 'ɗa' mai suna Larbuz wanda ya kasance gwarzon shekara acikin birnin Farisa domin shi kaɗai ya fatattaki waɗansu dodanni da suka addabi ƙasar da kawo sumamen bazato suna đauki ɗai ɗai cikin dare.
Ance yawan dodannin ya kai dubu ashirin da bakwai kuma suna da matuƙar girma da ƙarfi amma da yake yarima Larbuz ya kasance sadauki mai tsananin zafin nama koda ya tarbasu cikin daji inda suka yi sansani sai ya zame musu alaƙaƙai yayi ta ragargazarsu,sai da ya kashe guda ɗari tara da saba'in da bakwai daga cikinsu.
Koda sukaga yayi musu wannan ɓarna kuma sun kasa cimma masa sau suka ranta a ana kare amma duk da haka bai ƙyalesu ba sai da ya bisu ya rinƙa kifar dasu,da ƙyar guda ɗari biyar suka tsira da rayuwarsu. Wannan jarumtaka da yarima Larbuz yayi ba ƙaramar ɗaukaka ta jawo masa ba a wajen mutanen ƙasar Farisa.
Sai da ya zamana kowa na ƙaunarsa maza da mata yara da
manya,kai duk wata budurwa da ta isa da kanta a fagen kyau bata da burin da ya fi ta auri yarima Larbuz.
A ranar da aka shirya gagarumin taro a
fadar birnin Farisa don zaɓar budurwar da yarima Larbuz zai aura sai bokan ƙasar ya bayyana wanda a kewa laƙabi da Sharudul Bahabul.
Nan boka Sharudul Sababul ya sanar da sarkin Farisa labarin masifar da zata faɗo kansa da kuma 'yan majalisarsa.
Haka kuma ya zaiyana musu yadda zasu kuɓuta ta hanyar samo wannan tsumin tsafin dake can taskar tsafin bokanya
Tazibul Luhucul.
Bugu da ƙari yayi bayanin cewa babu wani boka da zai iya faɗin hanyar da za'abi aje wannan wuri face boka Hulumul Makahur.
Duk wannan bayani boka Sharudul Bahabul yayi shine acikin bainar jama'a.
Koda ya ƙare jawabi sai gaba ɗaya wajen ya ruɗe da iface iface,masu kuka nayi masu surutai nayi.
Sarkin Farisa kuwa da 'yan majalisarsa tuni sun fita haiyacinsu tamkar wađanda suka shekara suna cutar ajali.
Koda ganin abin dake faruwa sai yarima Larbuz ya daka tsawa cikin kakkausar murya. Take wajen yayi tsit kai kace mutuwa ce ta gifta.
Yarima Larbuz ya hau kan wani mumbari dake ajiye a tsakiyar fadar ya waiga gabas da yamma,kudu da arewa yaga ko'ina jama'ane rututu babu masakar tsinke amma kowa ka dubi fuskarsa sai kaji tamkar ka fashe masa da kuka
domin alamun tsorone da fargaba ƙarara zaiyane a fuskarsa.
Yarima Larbuz yayi gyaran murya yace,
"Yaku mutanen bimin Farisa kuyi sani cewa ni yarima zan tafi
Larbuz na rantse da martabarku zan tafi wannan wuri inda tsumin bokanya Tazibul Luhucul yake ba kuma zan dawo ba sai da shi.
Lallai na yi alƙawarin kare lafiyar sarki data 'yan majalisarsa,kamar yadda na kare rayuwar jama'ar ƙasar nan daga harin muggan dodannin
nan."
Koda yarima Larbuz ya zo nan a zancensa sai wajen ya cika da shewa ana yi masa jinjina.
Ba tare da ɓata lokaci ba boka Sharudul Bahadul ya ajiye sandar tsafinsa a ƙasa sai ta rikiɗe ta zama wani ƙaton shaho mại girman gaske,wanda idan ya kaɗa fukafukansa sai ka ga iska na neman kwantar da jama'a.
Sharudul Bahabul ya dubị shahon yace,
"Ya kai wannan tsuntsu na umarce ka da ka duƙa ƙasa domin yarima ya hau bayanka ka ɗauke shi ka kại shi dajin Dalmus inda boka Hulumul Makahur yake."
Ai kuwa tamkar da mutum yayi magana,sai shahon nan ya durƙushe ƙafafunsa ƙasa.
Cikin hanzari yarima ya haye bayansa ya zauna.
Kafin tsuntusn ya tashi sama sai boka Sharudul
Bahabul ya matsa gaban yarima Larbuz yayi masa raɗa a kunne yace,
"Da zarar kun dira a can wannan tsuntsu zai rikiɗa ya zama sandata ta tsafi sai kaɗauka ka riƙe ta har ku je taskar tsafi ku dawo.
Lallai ka dawo tare da wannan sanda tawa."
Yarima Larbuz yace,
"Tabbas zan kasance mai cika alƙawari zan dawo maka da sandarka."
Boka Sharudul Bahabul ya bugi bayan shahon kawai sai ya buɗe fukafukansa ya yi sama.
Shahon ya yi ta lulaƙawa cikin gajimare,tun jama'a na iya hangensa har ya ɓace ɓat.
Su kuwa 'yan matan da suka zo wannan gagarumin taro don a zaɓi ɗaya daga cikinsu a matsayin wacce yarimna Larbuz zai aura sai suka fashe da kuka,suka kamu da tsananin baƙin cikin rabuwa da abin begensu dare da rana.
Wannan shine abinda ya faru a birnin Farisa.
A can birnin Misra kuwa sarki Usman ne ke mulkí.
A wannan lokaci mutanen birnin Misra gaba ɗayansu ma'abota addinin Musulunci ne.
Sarki Usman na da kyakkyawar 'ya' guda ɗaya wacce saboda tsananin kyawunta ba a bari ga fuskarta,koda yaushe fuskar ta ta a rufe take da baƙin kyalle mai shara-shara.
Ita dai wannan
'yar' sarki sunanta Fauwaza.
Fauwaza ta kasance budurwa 'yar shekara goma sha takwas mai cikakkiyar sura tamka ita ƙera kanta.
Haka kuma ta taso da kaifin basira da kuma ilimin addini ma yawa.
Wata baiwa wadda Allah yayi mata shi ne tana da ilimin fassarar mafarki.
Duk irin mafarkin da mutum yayi in dai ya faɗa mata take zata fassara shi,kuma duk abin da ta faɗa sai an ga faruwarsa walau na farin ciki ne ko na baƙin ciki.
Yayin da sarki Usman ya ga mutane na girmama Fauwaza bisa lamarinta na fassarar mafarki har na suna neman su maishe da ita abin dogaronsu sai ya hanata fassara mafarkin kowa face na sa,don gudun kada mutane su kauce hanyar Allah su shiga saɓo.
A wani dare sarki Usman na kwance yana barci sai yayi mafarki da wäsu irin baƙaƙen tsuntsaye guda talatin da bakwai suna shawagi a sararin samaniya,amma kuma wasu halittu biyu ne ke yi musu jagora.
Halittun kuwa ɗaya mutum ce đaya kuma aljana ce.
Tsutsayen da halittun suka rinƙa zuwa kan wasu manyan turakan gini guda shida suna watsa wata guba.
Nan take turakan ginin suka rinƙa rugujewa suna faɗuwa ƙasa.
Al'amarin da ya janyo rugujewar gaba ɗayan
gidajen shida waɗanda ke ƙarƙashin manyan turakan nan har ma wuta ta kama gidajen zasu ƙone ƙurmus.
Kawai sai sarki Usman ya tsinci kansa a gidajen guda shida.
Koda yaga wuta na ƙoƙarin ƙone su gaba ɗaya sai ya fara ƙoƙarin kashe wutar dake cikin gida na ƙarshe,kuma yana kiran taimako cikin ihu da ƙaraji.
Haka dai ya yi ta ƙoƙari bai samu mataimaki ba,har ya zamana wutar ta kama gefen rigarsa kafin ya ankara gaba ɗayan rabin rigar ɓangaren hagu ya cinye gaba ɗaya,amma wani abin mamaki shine ko kaɗan fatar jikinsa ba ta ƙone ba.
Yana cikin wannan hali ne wata ƙanƙanuwar tsuntsuwa fara sol ta bayyana gare shi tace,
"Ya kại adalin sarki na san cewa daga cikin abubuwan daka mallaka a duniya babu abin da ka fiso sama da wata kurciya guda ɗaya wadda ka keɓeta,ka hana kowa kusantarta,inda zaka saki wannan kurciya da ta zo nan ta kashe wannan wutar gaba ɗaya wadda ke shirin ƙone gidajen nan guda talatin da bakwai,sannan ta yaƙi masu yi musu jagora wajen aiwatar da wannan mummunan ɓarna ya zamana labarin suma ya gushe har abada."
Farar tsuntsuwar na gama faɗin haka sai
sarki Usman ya farka daga wannan mummunan mafarki mara kan gado,da wuyar fahimta.
Gaba đaya jikinsa ƙyarma yake haka kuma fuskar sa cike take da zufa.
Haƙiƙa sarki Usman ya razana da wannan mafarki.
Nan dai ya karanta waɗansu addu'o'i ya koma ya kwanta da niyyar cewa da safe zai kira 'yarsa Fauwaza ya sanar da ita
wannan mafarki don ta fassara masa shi.
Kashe gari kuwa sarki ya aika a gayawa Fauzawa cewar yana gaiyatarta kalaci turakarsa.
Al'amarin da ya matuƙar baiwa Fauwaza mamaki kenan,domin rabonta da barin ɓangaren da take an kai shekara huɗu.
Kullum a tsare take kamar 'yar fursuna sai dai sarki da mahaifiyarta su kawo mata ziyara da kan su.
Babu mai shiga inda take face barori da kuyangi masu yi mata hidima.
Fauwaza ta fara saƙe-saƙe a ranta cewar anya kuwa ba batun aure sarki zai yi mata ba.
Ai kuwa idan har bayar da ita za'a yi ga wani wanda bata taɓa gani ba zata kasance cikin tsananin baƙin ciki.
Haka dai ta yi ta saƙe-saƙe a ranta,ta ƙulla wannan,ta kwance wannan,har aka turo 'yan rakiya suka shige gaba don kaita turakar sarki.
Sarki Usman na zaune shi kaɗai a ƙasa,
bisa wata ƙatuwar dadduma an ajiye kalaci a gabansa,irin wanda kowanne talaka zai iya ci a gidansa,sai ga gimbiya Fauwaza ta shigo cikin ɗakin da sallama.
Cikin fara'a da murmushi ya ɗago kai ya dube ta yana mai amsa sallamar.
Cikin ɗari-ɗari Fauwaza ta zauna tana mai fuskantarsa.
Sarki Usman ya dubeta cikin
nutsuwa yace,
"Haba 'yata,ki saki jikinki mana ki tuna fa cewa nine mahaifinki,kuma babu abin da nake so a duniyar nan sama dake.
Na unmarce ki da cin wannan abin tare da ni."
Koda jin haka sai farin ciki ya lulluɓe Fauwaza domin tana jin daɗin kasancewa tare da mahaifinta,a kowanne lokaci.
Nan take ta yaye ƙyallan da ya rufe mata fuska,kuma ta saki jiki
suka fara cin abincin cikin kwanciyar hankali.
Sai da suka sha ruwa,a sannan ne sarki Usman yayi gyaran murya yace,
"Yake 'yata ki yi sani cewa ban kiraki ba nan domin komai sai don na labarta miki wani mafarki wanda nayi,ya firgitani kuma ya jefani cikin rashin fahimta da ruɗani.
Ina son ki fassara mini wannan mafarki don na gane ma'anarsa."
Ba tare da ɓata wani lokaci ba,ya zayyana mata wannan mugun mafarki da yayi.
Bayan ya gama sai yaga gimbiya Fauwaza ta shiga yanayin damuwa cikin alamun karayar zuciya tace da shi,
"Yakai Abbana ina son ka sani cewar fassarar wannan mafarki naka a bayyana take.
Waɗannan baƙaƙen tsuntsaye
guda talatin da bakwai daka gani ba komai bane face hadiman wata ibilishiyar bokanya,waɗanda duk sun kasance baƙaƙen aljanu,kuma
kafirai marasa tausayi da imani. Waɗannan halittu biyu dake wa baƙaƙen aljanun jagora kuwa bokanyar ce da uwargidanta,wata aljana muguwar gaske.
Wannan mafarki naka yana
bushara ne da cewar waɗannan kafirai zasu jehowa manyan sarakunan duniya wata irin muguwar cuta.
Sarakunan guda shida ne,kuma sune waɗannan turakan gini daka gani a cikin mafarkinka.
Wannan guba wacce tsuntsayen ke zubowa akan turakan gini ita ce nuguwar cutar.
Rugujewar turakan ginin da faɗuwarsu ƙasa na nufin cewa waɗannan sarakuna guda shida zasu kamu da ciwon ajali har ya kaisu ga kushewa,idan baka manta ba akwai gidaje guda shida ƙarƙashin turakan,waɗannan gidaje sune
manyan ƙasashen duniya dake ƙarƙashin manyan sarakuna.
Waɗannan ƙasashe sun haɗa
birnin Sin,Hindu,Rum,Ƙisra,Misra da Farisa.
A cikin mafarkin an nuna maka cewa gidajen shida sun ƙone ƙurmus,sakamakon rugujewár turakan ginin guda shida. Wannan yana nufin cewa da zarar cutar ajalin ta gama kashe sarakunan waɗannan ƙasashe shida za'a cisu da yaƙi gaba ɗaya.
Kà tuna cewa wutar data kama gidajen ta kama rigarka har ta ƙone rabinta ɓangaren hagu,amma ko kađan bata ƙona fatar jikinka ba,wannàn yana nufin cewa babu makawa kaima sai kamu da cutar mutuwar ɓarin jiki,amna ba zai taɓá imaninka da addininka ba.
Wannan farar tsuntsuwa kuwa data zo maka da bushara ba komai ba ce face Addinin Musulunci.
A cikin wannan mafarkin naka farar tsuntsuwar data gaya maka cewa inda za ka saki wata kurciya guda ɗaya wadda ka keɓeta ka hana kowa kusantarta da fa kashe wutar dake ƙoƙarin ƙone gidajen shida kuma ta káshe baƙaƙen aljanun nan guda talatin da bakwai da iyayen gidansu.
Wannan kurciya ba komai bace face ni ɗin nan gimbiya Fauwaza."
Koda gimbiya Fauwaza tazo nan a zancenta sai sarki Usman ya cika da tsananin mamaki.
Hankalin sa ya dugunzuma fiye da
kowanne lokaci.
Kawai sai yayi ajiyar zuciya ya dubi gimbiya Fauwaza cikin alamun karayar zuciya da sallamawa yace,
"Yake 'yata haƙiƙa fassarar wannan mafarki ta tayar mini da hankali.
Na sani cewa ba ki taɓa yin ƙarya ba,kuma duk abin da kika faɗi yana faruwa a zahiri.
Lallai ni da sauran waɗannan sarakuna muna cikin mummunan tashin hankali.
Tabbas ya zama wajibi in baki dama ki fita yin jihadi a doron ƙasa,domin kawar da maƙiya addinin Allah,kuma ki kawar da zalunci ki shimfiɗa adalci.
To amma abin tambayar anan shine ke ba jaruma bace,kuma baki taba yin yaƙi ba,ta yaya zaki iya fuskantar waɗannan manyan azzalumai masu tsananin karfin damtse da ƙarfin tsafi?"
Yayin da gimbiya Fauwza ta ji wannan batu na mabaifinta sai tayi murmushi tace,
"Yakai Abbana ina son na tuna maka cewa wanda duk yayi dogaro da Allah,haƙiƙa Allah zai iya masa bisa dukkanin abin da yasa a gabansa.
Abin da nake so da kai shi ne kasa a shirya mini runduna ta mayaƙa kimanin mutum dubu saba'in,ni kuwa nayi musu jagora izuwa cikin waɗannan manyan ƙasashen duniya,duk inda muka je za mu yi musu wa'azi bisa addinin Allah
cikin masalaha da nasiha,idan sun karɓa hannu shikenan Alhamdulillah,idan kuwa suka bijire sai na yaƙe su da ƙarfin tsiya na kafa tutar Musulunci a ƙasar.
Tabbas in dai ka lamince mini hakan Musulunci zai rinjayi kafirci kuma cutar da zata kamaku sai na zamo sanadiyar warkewarku."
Lokacin da gimbiya Fauwaza tazo nan a zancenta sai hawaye ya zubowa sarki Usman.
Koda ganin haka sai hankalinta ya tashi ta matsa gare shi ta riƙe hannayensa biyu tana mai cewa,
"Yakai Abbana ina dalilin zubar wannan hawaye a idanunka?
Ka yi mini gafara idan har maganganuna sun ɓata maka rai,don kada na shiga cikin fushin Allah."
Cikin alamun tausayawa dana nuna tsantsar kauna,sarki Usman ya kama kafaɗun gimbiya Fauwaza yace,
"Yake 'yata na rantse da sarki makaɗaici wanda bashi da abokin taraiya baki taɓa faɗin wata kalma ba guda ɗaya wadda ta ɓata mini rai,tun haihuwarki kawo iyanzu,ki yi sani cewa ba komai ba ne ya haddasa zubar hawaye a idanuna ba face sanin cewa
lokaci ya zo wanda zamu rabu tsawon lokaci alhalin kin sani cewa a duk duniya babu abin da nake so sama da ke.
Daidai da rana guda ban son
rabuwa dake,saboda tsananin so da nake yi miki ne na hana kowa kusantarkı,na hanaki yin aure,kuma na ɓoye kyawun nan da Allah ya yi miki.
Yau gashi za ki tafi ki barni,kyawunki zai bayyana a duniya kowa ya gani."
Sa'adda sarki Usman ya zo nan a zancensa sai jikin gimbiya yayi sanyi.
Tausayi da ƙaunar sarki Usman suka baibaye zuciyarta.
Kawai sai ta rungumeshi,ta fashe da kuka tana mai cewa,
"Da yardar Allah duk inda na je zan dawo gida lafiya.
Albarkacin wanda aka yi duniya da lahira dominsa,ajali ba zai zamo sanadin rashin sake saduwar mu ba.
Zan cigaba da roƙon Allah da yasa mu yi tsawon kwana har ka ga ranar aurena kuma kaga jikanka da idanu ka."
Sarki Usman ya janye jikinsa daga na gimbiya Fauwaza suka fuskanci juna sosai,yana mai share hawayen idanunsa yace,
"Yake 'ya ta,ki dube ni da kyau ki gani fa haƙiƙa tsufa ya riske ni domin a ƙallah shekaruna sun haura casa'in,anya kuwa zan iya kai wannan lokacin?"
Cikin sauri ta tari numfashinsa tace,
"Kada ka ƙara faɗin haka ya Abbana domin kuwa rai da mutuwa duk a hannun Allah suke,kuma babu wanda ya san gawar gobe."
Cikin yanayin nadama sarki Usman yace,
"Allah na tuba ka yafeni,kuma na roƙe ka daka sakawa wannan 'ya tawa da lada mai yawa,domin ta kasance mai sani akan tafarkin shiriya.
Allah na roƙeka da kayi mata jagora bisa wannan gagarumin aiki da zata yi dominka.
Ka kareta daga dukkan tsautsayi,asara,mugun ji da mugun gani,ka bata nasara bisa maƙiyanka.
Ka ɗaukaka ta,ɗaukaka irin wacce ka yiwa bayinka na gari magabatanmu."
Haka dai sarki Usman yayi ta yiwa gimbiya Fauwaza addu'o'in alheri.
Bai gushe ba yana yi har sai da itama ta karɓa,tana mai yi masa fatan alheri.
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin sarki Usman da 'yarsa gimbiya Fauwaza kyakkyawar budurwar da babu kamarta a duk faɗin duniya a wannan zamani a cikin birnin Misra.
Al'amarin bokanya Tazibul Luhucul,aljana Saubatu Azwas da hadimai talatin da bakwai kuwa kafin su rabu kaso biyu don tafiya aiwatar da wannan mummunan aiki dake gabansu saida süka tsaya suka tattauna gami da yin shawara bisa inda ya kamata su fara zuwa.
Tazibul Luhucul ce ta fara magana yayin data dubi Saubatul Azwas tace,
"Yake ƙawata
ina son ki sani cewa sarkin Misra da sarkin Hindu dana Farisa sune mafiya jajurcewa akan yawaita bauta da ibada,don gudun kada su ɓata mana lokaci zai fi kyau mu fara zuwa kasar Rum da Ƙisra don aiwatar da wannan aiki in yaso daga baya sai mu je Misra,Hindu da Farisan."
Koda jin haka sai Saubatul Azwas ta ƙyalƙyale da dariya tace,
"Yake ƙawata haƙiƙa maganarki gaskiya ce,don haka ni yanzu zan kwashi rabin hadimanki mu tafi kasar Rum ke kuma sai ki kwashi rabin ku tafi kasar Ƙisra."
Tazibul Luhucul tace,
"Ƙwarai kuwa wannan shawara tayi kyau,kuma koda na haɗu da wata matsala zan neme ki a cikin madubin tsafina na sanar dake don ki kawo mini đauki."
Saubatul Azwas ta sake ƙyalƙyalewa da dariya a karo na biyu tace,
"Wannan ba matsala ba ce."
Ba tare da ɓata wani lokaci ba Saubatul Azwas da bokanya Tazibul Lubucul,suka kwashi hadiman nan suka kasu gida biyu.
Saubatul Azwas ta nufî ƙasar Rum,ita kuwa Tazibul Luhucul ta nufi kasar Ƙisra.
Lokacin da bokanya Tazibul Luhucul tare da
rabin hadiman ta suka nufi ƙasar Ƙisra basu fi sa'a uku da rabi ba suna tafiyarsu suka iso bayan birnin.
A daidai wannan lokaci ne rana ta faɗi,wato Magariba ta doso kai.
Tazibul Luhucul ta ciji yatsanta,sannan ta dubi hadimanta cikin alamun takaici tace,
"Kash babu damar mu shiga cikin wannan birni yanzu dole ne mu tsaya anan har dare ya
raba."
Koda jin haka sai wata hadima mai suna Lulaija tace,
"Ya shugabata mene ne hikimar
hakan?"
Cikin fushi da harara Tazibul Luhucul ta dubi Lulaija tace,
"Amma dai duk yadda aka yi
ƙwaƙwalwar ki ta kifi ce,mara basira da mantuwar tsiya.
Ashe har kin manta da bayanin
da mai girma Saubatul Azwas ta yi mana kenan cewar lallai ba zamu ziyarci sarakunan nan ba sai da tsakar dare,kuma kada mu kusance su yayin da suke aikin bauta ko tsafi."
Lulaija ta duƙar da kai tace,
"Ki gafarce ni ya shugabata haƙiƙa zancenki dutse ne,lallai na sha'afa."
Kafin Lulaija ta gama faɗin haka tuni Tazibul Luhucul ta nuna gaba ɗayan hadiman da sandar tsafinta har dama ita kanta.
Ai kuwa nan
take suka bace ɓat,a lokaci guda tamkar dama can babu su a wurin.
Bayan kamar rabin sa'a sai Tazibul Luhucul ta murza sandar tsafin nata suka sake bayyana gaba ɗaya a wajen.
Bayyanarsu ke da wuya Lulaija ta rusina a gaban Tazibul Luhucul cikin alamun girmamawa tace,
"Ya shugabata mene ne ya faru kika ɓoyemu gaba daya?"
Tazibul Luhucul tayi murmushi, tace,
"Ba komai ba ne ya sa na ɓatar damu ba face na jiyo ƙamshin aikin bokayen garin nan suna son su san da zuwanmu.
Abin da ba su fahimta ba shine wanda duk ya riga ka kwana,dole ne ya riga ka tashi."
Cikin alamun mamaki Lulaija tace,
"To saboda me suke son su san zuwanmu?"
Tazibul Luhucul tace,
"Saboda su san matakin da zasu ɗauka wajen hanamu aiwatar da abin da ya kawo mu. Na rantse da ƙarfin tsafina yanzu ba su isa su ganmu ba,ko su ji muryarmu,domin na tsafance mu mu da ƙarfin sihirin tsafina.
Kowannen ku ya zauna cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,da zarar dare ya raba zan baku izini ku tafi izuwa gidajen 'yan majalisar garin nan ku barbaɗa musu hodar tsafin nan wacce zamo sanadiyar
kamuwarsu da cutar ajali."
Kamar yadda Tazibul Luhucul tayi wannan batu haka al'amarin ya kasance,wato basu shiga cikin birnin Ƙisra ba,sai da dare ya raba tsakiya.
Hadiman na ta suka kasu gida goma,suka tafi izuwa gidajen 'yan majalisar.
Cikin sa'a kuwa duk gidan da suka je sai su iske maigidan na kwance yana ta sharar barci. Nan take sai su watsa masa wannan hodar tsafi,su wuce gaba.
Gida ɗaya ne suka sami matsala,wannan gida kuwa na wazirin garin ne,shi dai wannan
waziri ya kasance yayan bokan birnin wanda ake kira Garfas.
Boka Garfas ya sanar da waziri cewa idan har ya daina barci a cikin dareren wannan shekara to tabbas wannan sihiri na cutar ajali ba zai hau kansa ba.
A bisa wannan dalili ne ya sauya lokacin barcinsa gaba ɗaya,ma'ana ya daina yin barci da daddare sai dai da rana.
Lokacin da hadimai suka zo gidan waziri sai suka iske shi a zaune yana ta aikin bautar gunkin da suke bautawa mai suna Gulmakuru.
Koda suka riskeshi a cikin wannan hali sai suka ja da baya da sauri suka koma bayan katangar gidan suka zauna,suna haki da dafe ƙirazansu,cikin yanayin tsoro da tashin hankali.
Daga can
sai Lulaija tace,
"Kai amma fa wannan shegen waziri da nacin tsiya yake,lallai ku sani cewa mun tsallake rijiya da baya,ba don mun yi sauri mun koma da baya ba da tuni gaba dayanmu mun zama gumaka.
In kuwa muka zama gumakan babu wanda ya isa ya dawo damu ainihin halittarmu,shi kenan tamu ta ƙare."
Yayin da Lulaija ta zo nan a zancenta,sai wata hadimar mai suna Kamtura tace,
"Tabɗijam ai kuwa in dai haka ne babu wawaye a duniyar nan kamarmu yanzu saboda tsananin kwaɗayin abin duniya muka jefa kanmu cikin irin wannan mugun aiki,mai mugun haɗari?"
Lulaija tace,
"Eh, to haka ne,amma ai kin san cewa faɗan da yafi ƙarfinka dole ne ka mayar da shi wasa.
Duk mun sani cewa ko muna so,ko bama so dole ne mu zama bayin Tazibul Luhucul,in kuwa muka ƙi bin umarninta hallaka mu za ta yi."
"Kunga yanzu dai ba hira ce mafitarmu bà yaya zamu ɓullowa wannan shegen wazirin mai naci.
Kun sani cewa idan fa lokacin da aka ɗiba mana ya cika dole ne mu bar wajen nan,kuma idan muka tafi ba tare da samun biyan buƙata ba gawa ma sai ta fi mu jin daɗi da kwanciyar hankali."
Wata hadima ce mai suna Faltu,tayi wannan furuci.
Gaba ɗayansu suka yi shiru suna tunani aka rasa wanda zai ce wani abu tsawon daƙiƙa sittin.
Gaba ɗayan waɗannan hadimai
su goma sha bakwai ne,amma namiji ɗaya ne tak a cikinsu,ana kiransa da suna Murkubalu.
Cikin alamun mamaki Murkubalu ya dubi waɗannan hadimai 'yan uwansa ɗaya bayan ɗaya yayi tsaki,sannan yace,
"Amma dai kun bani mamaki a matsayinku na mata iyayen kaidi a ce kun kasa tunano hanyar da zamu hallakar da
wannan mutum.
To idan kun sallama mini ni

2 Comments On MATSATSUBI Book 2
avatar
idris-idris-abubakar

1 year ago

Reply

Hausa

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to idris-idris-abubakar

Eh na hausa ne

Please Login or Register in order to submit comment