Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd



*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*

*CHAPTER ONE*





Page_001


___K'arfe 7pm ne na daren ranar juma'a, tana zaune kan er kujerar dake gaban mudubin ta hannun ta rik'e da waya er k'arama wadda wasu ke kira da rakani kashi, sassanyan murmushi ke tashi daga kyakykyawar doguwar farar fuskar ta, tana nan zaune har zuwa lokacin da wata mata wadda kana ganin ta kasan mahaefiyar tace, saboda tsananin kama da suke yi, ta yaye labulen d'akin ta lek'o tana kallan ta

"AYRAH wae har yanzu jiran Abban kike?" Murmushi ne ya sake wanzuwa akan fuskar wadda aka kira da Ayrahn wanda hakan ya bawa dimple d'in dake gefen kowanne kumatun ta lotsawa sosae sannan tace cikin muryar ta me dad'in saurare

"Ehh Umma.." ta6e baki Umma tayi tace

"Ae se kiyi ta jira.." daga haka ta saki labulen ta koma tsakar gida. Tana nan zaune bayan wajen minti 10 ta jiyo sallamar mahaefin nata daga tsakar gidan su, seta ajjiye wayar da sauri akan gadon sannan ta mik'e ta yaye labulen d'akin ta fito, hasken farin wata da kuma na k'wan fitilar da suka kunna ya sanya ni ganin kyakykyawar fuskar ta da har zan iya kwatanta muku ita, matsashiya ce er kimanin shekaru 19 doguwa ce fara sosae, me idanu manya manya da dogon siririn hanci, se d'an k'aramin red lips d'in ta, sanye take cikin doguwar riga bak'a babu d'an kwali a kanta dan haka ta yafa mayafin doguwar rigar akan ta

"Abba sannu da zuwa.." ta fad'a tana neman waje ta zauna

"Yawwah Ayrah" Abban ya fad'a yana neman waje ya zauna sannan da murmushi kan fuskar sa ya sake kallan Ayrahn bayan ya amsa sannu da zuwan da Umma ke masa

"Toh in gyara zama dae in sha labarin karatun kin nan, dan da alama akwae magana a bakin ki" murmushi ta sake yi sannan tace

"Abba ae tun d'azu kae nake jira nazo muku da wani babban albishir" Umma ta kalli Abba tace

"Ahh toh, tun d'azu tak'i fad'a min abinda yake ta sanya ta murmushi tace seka dawo.." Abba ya maeda duban sa kan Ayrah yace

"Toh muna jin ki, Allah yasa alkhaeri ne" gyara zama tayi daga inda take zaune sannan ta fara magana har lokacin murmushi yak'i barin kyakykyawar fuskar ta

"Abba na had'u da RAJ.." ta fad'a da mad'aukakin murmushi akan fuskar ta, cikin rashin fahimta dukkan su suka kalle ta, seta d'an tsaya itama tana kallan su kafin tace

"Raj fa nake nufi, Umma Raj d'ina fa, kun tuna?" ta fad'a tana d'an murmushi dan ita in dae akan Raj ne bata da wata kunya, kallan juna Umma da Abba suka yi kafin Abba ya runtse idanun sa sannan ya fara k'ok'arin magana

"Umma cewa yayi ma na fad'a tun wuri Abbun sa zasu zo wajen Abba" Ayrah ta fad'a kafin Abban ya fara magana, Umma dake lura da yanayin Abba ta furta a hankali tana kallan sa sosae

"Abban su lafiya dae koh?" jinjina kae yayi kafin cikin er dakiya ya furta

"Kina nufin Raj d'an gidan Kabeeru..?" seta jinjina kae cikin jin dad'in yadda Abban ya gane maganar ta ta tace

"Ehh Abba, bama mu ta6a tunanin.." d'aga mata hannun da Abba yayi ne ya sanya ta dakatawa daga fad'in maganar da take k'ok'arin fad'a, ta cigaba da kallan yadda lokaci guda k'wayar idanun sa ta sauya, haka zalika Umma ma tak'i kallan ta, seda Abban ya sake runtse idanun sa sannan ya bud'e ya fara fad'in

"Kar ki sake min maganar sa ko maganar wanda ya shafi ahalin su gaba d'aya.." Abba ya k'arasa maganar idanun sa na sake yin jawur, cikin rashin fahimta take kallan Abban nasu, ta kuma kalli Umma sannan tace a d'an rud'e

"Abba ko dae ka bayar dani ne ga wani bansani ba? Abba cewa nayi fa Raj ke so azo a nemar masa aure na.."

"Ayrah..ki tashi ki bar wajen nan idan baso kike zuciya ta ta buga ba" Fararen idanun ta dake d'auke da bak'a sid'ik d'in k'wayar idanu ta d'aga ta sake duban mahaefin nata, take wasu k'walla suka tarar mata tana jin yadda k'irjin ta ke bugawa da k'arfin gaske, "me yake faruwa ne?" ta tambayi kanta

"Abba Raj ne fa, Abba Raj dae wanda ka sani fa, akan sa nake magana.." Abba ya runtse idanun sa yana jin wani irin zafi a cikin ransa cikin 6acin rae ya furta

"Ki saka a ranki in dae ina raye, har abada ba zaki ta6a auren Suraj ba" da wani irin razana ta d'aga ido ta kalli mahaefin nata, tana jin yadda kalaman nasa ke sauka a cikin kunnuwan ta kamar saukar mashi, kafin takae ga cewa komae ta sake jiyo Abban nata yana fad'in

"Ki kawo koma waye a fad'in garin nan gaba d'aya amma dae_dae da minti d'aya kada ki sake ki yaudari kanki kiyi tunanin zan aura miki Raj, bama Raj ba duk wani daya dangance su bazan ta6a aura miki shi ba" kuka ne ya k'wace mata babu k'ak'k'autawa tana jin wani iri a rae da zuciya har ma da gangar jikin ta, a hankali taja k'afafun ta da rarrafe ta k'arasa gaban mahaefin nata ta rik'o k'afafun sa sannan ta fara magana cikin kuka, kyakykyawar fuskar nan ta ta tayi jajir

"Abba..ka tausaya min, Abba ka taemakawa zuciya ta, Abba ko da wannan ce zata zama alfarma ta k'arshe da zaka iya yi min a rayuwa Abba kayi min ita don Allah" ta k'arasa fad'a tana sake fashewa da wani sabon kuka, a hankali Abba ya zame k'afafun sa bugun zuciyar sa na k'aruwa ko ba'a gwada shi ba tabbas yasan ciwon sa na dab da tashi, ya d'an runtse idanun sa kad'an sannan ya fara k'ok'arin tafiya, ta sake rik'o k'afafun nasa tana kuka kamar wadda ranta ze fita

"Abba ina k'aunar Raj, zuciya ta zata iya bugawa idan kace zaka rabani da shi, Abba kace wani abu don Allah" juyowa Abba yayi yana kallan ta kana a fusace yace

"Ko mutuwa zaki yi ba zaki ta6a auren Raj ba.." daga haka ya wuce d'akin sa, mik'ewar da Umma tayi ne ya sanya ta d'ago fuskar ta da tayi jajir tace

"Umma ya zaki tafi ki barni cikin duhu, Umma me Raj ya muku da Abba zece bazan aure shi ba, Umma Raj fa ko har yanzu baku gane wanda nake magana akansa ba.. Umma kiyi wa Abba bayani don Allah" ta k'arasa maganar sanda wani kukan yaci k'arfin ta, ko kallan inda take Umma ba tayi ba ta wuce cikin d'akin da Abba ya shiga.. A hankali ta cigaba da rera kukan ta, seda tayi me isarta sannan taja k'afafun ta zuwa cikin d'akin ta har lokacin hawaye yak'i dena sintiri akan kuncin ta, wayar ta dake ajje ta d'akko ta danno wata number ta kira...



... A hankali ya sako k'afafun sa farare tass dake cikin takalmin wanka, seda ya cire su daga k'ofar toilet d'in sannan ya sako kansa zuwa cikin kyakykyawan bedroom d'in, k'arasawa yayi bakin k'aton mudubin sa ya sanya hannu ya d'auki comb ya fara taje sumar kansa data sha gyara sosae, banda ruwan daya ta6a ta a gyara take tsaf se tashin k'amshi me dad'i da take yi, yanayin yadda yake d'auke da towel ne ya sanya ni ganin yadda k'ak'k'arfan jikin sa yake, dogo ne me k'ak'k'arfan jiki, fari ne sosae wanda hakan ya sanya bak'ar sumar dake kan k'irjin sa ta bayyana kan ta sosae kan farar fatar sa wadda ke kwance luff luff kamar wadda ake kwantar da ita da Comb, yana da dogon hanci me tsayi, fuskar sa d'auke da bak'in sajen daya zagaye bakin sa, ringing d'in da yaji wayar sa nayi ne ya sanya shi sakin wani k'ayataccen murmushi ya ajje comb d'in kan stool d'in sannan ya mik'e ya k'arasa inda wayar ke ajje ya d'auka kana ya zauna ya jinjina da pillown dake kan tank'amemen gadon sa kana ya kara wayar a kunne bayan ya d'aga, da kukan ta ya fara cin karo cikin wayar, seya mik'e zaune yana bud'e manyan idanun sa yace

"Subhanallahi..Ayrah meya saki kuka?" ya fad'a cikin kulawa, cigaba da kukan tayi kamar ranta ze fita, daga inda yake zaune kuwa yana jin kamar ana watsa masa dalma ne, mik'ewa tsaye yayi ya murza goshin sa da d'ayan hannun sa yana lumshe idanun sa har lokacin bata bar kukan ba, ya kuma yin k'asa da muryar sa yace

"Ya isa haka don Allah, ya isa haka, pls kiyi shiru ki fad'a min why are u crying.." ya sake fad'a cikin rarrashi

"Raj.." ta fad'a cikin kukan, ya lumshe idanu yana jin muryar ta ta har cikin gangar jikin sa

"Na'am.. Ayrah, pls menene Uhmm?" daga inda take zaune ta d'an lumshe idanu tana sassauta kukan ta koma sheshshek'a se can ta fara magana tana yi tana d'an aje ajiyar zuciya

"Abba ne.."

"Me Abban yayi?" ya fad'a yana jin yadda ya k'agu yaji abinda ya sanya ta kuka haka

"Abba yace bazan aure ka ba.. Raj meka yiwa Abba?" cikin rashin fahimta ya sake bud'e manyan idanun sa kana yace

"Ni kuma?" kamar tana gaban sa ta jinjina kae, kafin yace komae kuma ta sake cewa

"Na yarda da kae Raj, kawae ka fad'awa Abbun ku yazo wajen Abba, ina tunanin be gane Raj d'in da nake nufi ba.." neman waje yayi ya zauna kafin yace

"Ohk..In Sha Allah, yanzu dae ki dena kukan kinji? In Sha Allah ni naki ne kema kuma tawa ce kinji?" jinjina kae tayi ba tare da tace komae ba, se kuma can tace

"Ehh.."

"Oh yah Smile.." ya fad'a daga inda yake yana d'an murmushi, goge fuskar ta tayi sannan ta d'an yi murmushin me d'an sauti wanda tasan hakan ze faran ta masa

"Awwnnn That's my girl..yanzu dae ki aje waya kiyi bacci zan je na samu Abbu da wannan maganar.. I luv u.." ya k'arasa fad'a idanun sa a lumshe, itama nata idanun ta lumshe kamin tace

"Tohm.." Tashi yayi ya k'arasa shiryawa cikin wata bluen shadda dan babu k'arya yayi missing manyan kaya, ba tare da ya d'ora hula akan sumar kansa ba ya d'auki wayar sa har lokacin be dena mamakin dalilin da yasa Abban nata yace haka ba. Kae tsaye parlourn k'asa ya sauko cikin nutsuwar data zame masa jiki, dae_dae lokacin da wata farar mata wadda ak'alla zatayi shekaru 45 zuwa 50, kyakykyawa ce kamar yadda d'an nata yake, tana sanye cikin wata atamfa me kyau d'inkin riga da skirt, jera warmers d'in data fito dasu daga kitchen akan dinning take, ta kalle shi da murmushi kan fuskar ta sannan tace

"Ka k'araso ka fara cin abinci koh?, semu zauna mu samu muyi hira.." d'an murmushi ya saki kad'an kamin ya shafa sumar kansa yace

"Tohm Ummee.. Amma inaso ne muyi wata magana me muhimmaci.." ya fad'a yana d'an lumshe manyan idanun sa kad'an, dae_dae lokacin Ummee ta gama jera kayan data fito dasu seta k'araso inda yake tsaye tace tana murmushi

"Shikenan Raj, ni dama daga yadda na ganka nasan akwae magana a bakin ka" shima murmushin ya maeda mata sannan dukkan su suka wuce zuwa cikin k'aton parlourn daya k'awatu da had'ad'd'un kujeru, suna zama Alhaji Kabeer ya shigo cikin d'akin da sallama sanye cikin manyan kaya da babbar riga, dukan su suka amsa masa ya k'araso yana kallan su su duka kuma a lokaci guda yana amsa sannu da zuwan da suke masa, akan kujera ya zauna, yayin da Raj ya sauko daga kan kujerar yana shirin zama a k'asa Alhaji Kabeer yace

"A'ah kayi komawar ka ka zauna, yau ae hira zamuyi.." murmushi ne ya wanzu akan kyakykyawar fuskar sa seya koma ya zauna yana kallan Alhaji Kabeer yace

"Barka da dawowa Abbu.."

"Barka kadae Raj"

"Ko dae a kawo maka abincin nan ne?" Ummee ta fad'a tana kallan Abbun, girgiza kae yayi kafin yace

"A'ah fara kawo min dae juice na sha.." mik'ewa Ummee tayi ta wuce inda ze sadata da dinning area, yayin da Abbu ya dawo da duban sa kan Raj yace

"Ya hanyar dae? Kuma ya karatun?"

"Alhamdulillah Abbu..ina tafe da wani albishir fa.." ya fad'a da murmushi kan fuskar sa, dae_dae lokacin da Ummee ta k'araso hannun ta d'auke da juice d'in ta ajjiye sannan ta fara k'ok'arin zubawa a cikin tambulan

"Toh ko zamu bari mu fara cin abinci?" Abbu ya fad'a yana kar6ar juice d'in da Ummee ta mik'a masa kana ta nemi waje ta zauna, hannun sa ya kae kan sumar kansa ya d'an shafa sannan yace

"A'ah Abbu.. Na k'agu na sanar daku ne.." Ummee ta kalli Abbu tana murmushi tace

"Ae kawae ka k'yale shi ya fad'a dan tun d'azu ya kasa komae har abincin ma shima beci ba.."

"Ohk ina jin ka.." Abbu ya fad'a yana kae juice d'in bakin sa

"Abbu na samu matar aure.." dukkan su suka kalle shi cike da mamaki da kuma farin ciki duka a lokaci guda, mutumin da suka san kwata kwata baya kula wasu mata amma yau shine ke fad'in ya samu matar aure? Toh ta yaya?

"Wacece wannan Raj?" Ummee tayi k'arfin halin fad'in haka, wani k'ayataccen murmushi ne ya su6uce masa sannan yace bayan ya lumshe idanun sa ya bud'e

"Ayrah.."

"Wacece Ayrah?" Ummee ta fad'a tana kafe shi da idanun ta

"Ayrah dae wadda kika sani Ummee, kada kice min har kin manta ta, Ayrah dae tawa wadda kika sani.." k'warewar da Abba yayi ne ya sanya su duka suka kalle shi, babu k'ak'k'autawa ya shiga yin tari sosae, da sauri Raj ya mik'e ya isa fridge ya d'akko ruwa ya kawowa Abbun, da k'yar ya iya kar6a yasha ruwan, ya shiga sauke ajiyar zuciya kamar wanda yayi gudu

"Sannu Abbu..sannu.." shine abinda Ummee keta maemaetawa amma Abbun bebi ta kanta ba ya kalli Raj yace

"Ya..akayi ka had'u da ita?" yayi maganar a rarrabe yana kallan Raj, sosae Raj ke binsa da kallo yana so ya gano abinda ya sanya shi lokaci d'aya ya zama wani iri

"Abbu.."

"Ya akayi ka had'u da ita? Ko dama kuna tare tsawon lokacin nan?" Abbu ya katse masa maganar da yayi niyyar yi, girgiza kae Raj yayi har lokacin idanun sa nakan Abbu

"Tun wuri ka rabu da ita Raj, ka rabu da ita dan auren ku baze ta6a yiwuwa ba, tun wuri ma ka cire ta a ranka zefi maka.." Abbu ya fad'a yana mik'ewa yayi hanyar d'akin sa, da kallo yabi Abbun sannan ya maeda duban sa kan Ummee yana jin yanda k'irjin sa ke bugawa

"Ummee.." ya fad'a yana kallan ta, seta mik'e kawae tabi bayan Abbun a ranta tana sak'a yadda zasu 6illowa al'amarin, lallae idan ba suyi wasa ba suna cikin matsala.. Runtse idanun sa yayi har lokacin yana jin yadda bugun zuciyar sa ke k'aruwa, me yake faruwa ne? Yakae wajen minti 5 zaune a wajen yana sak'awa da warwarewa sannan ya d'auki wayar sa ya lalubo number ta ya danna kira. A 6angaren ta kuwa har lokacin tana kwance kan madaedaecin gadon d'akin, kanta d'ore akan pillow hawayen da suka k'i tsayawa se zuba suke akan pillown, kanta babu d'an kwali hakan ya bawa sumar kanta damar bajewa akan pillown, dae_dae lokacin da kiran wayar tasa ya shigo wayar ta yayi dae_dae da lokacin da Umma ta yaye labulen d'akin ta shigo, ringing d'in da taji ya sanya ta kallan wayar, Ayrah ta tashi zaune tana kallan Umman lokaci guda tana maeda duban ta kan wayar

"Mik'omin wayar.." Umma ta fad'a tana mik'a hannun ta, lumshe manyan idanun ta tayi wasu hawaye masu d'umi suna zubowa akan kuncin ta, ganin bata da niyyar mik'o mata wayar ne yasa Umman ta k'arasa da kanta ta d'auki wayar ta kashe ta gaba d'ayan ta sannan ta kalli Ayrah data fashe da wani irin kuka tace

"Kiyi shiru ki dena kuka, ki tsaya ki saurare ni, base kin tada hankalin mu muma mun tayar da naki ba.." kafin Umman ta kae k'arshen zancen ta Ayrah tace cikin kuka tana girgiza kae

"Umma meyasa haka? Shin baku san wanene Raj ba? Baku san halin sa ba? Ko kuwa iyayen sane baku sani ba.." K'arasawa Umma tayi ta zauna akan gadon kana ta kamo Ayrahn cikin jikin ta, bata fara magana ba seda taji ta fara sauke ajiyar zuciya, sannan ta kama dogon gashin Ayrahn ta d'aure a tsakiyar kanta kana ta fara magana a nutse tana jin zuciyar ta na mata wani irin zafi...

B'angaren sa kuwa runtse idanun sa yayi bayan ya sake kiran layin Ayrah yaji shi a kashe, yaja wani dogon numfashi sannan ya mik'e akan k'afafun sa yana daedaeta nutsuwar sa a ransa yana jin ya zama dole yasan aenahin abinda yake faruwa kafin k'wak'walwar sa ta tarwatse, dan kuwa tabbas akwae rina a kaba, me yake faruwa haka?.....





_*TUSHEN LABARI*_




ZARAH AUTA (Mhiz Innocent) ✍️



https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd



*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*

*CHAPTER ONE*


✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨


Page_002



____kyakykyawa ce fara sol me manyan idanuwa, haka zalika kuma me k'aramin jiki da dogon hanci, a kallan farko zaka iya k'iyasta shekarun ta, san haka baza ta wuce shekaru 4 ba, tana sanye cikin Uniform dake a goge fes fes dasu, hannun ta d'auke da basket d'in ta dake d'auke da flask d'in abinci na yara en makaranta da kuma rubber ruwa, da d'an gudun ta take fitowa daga cikin d'akin daya kasance mallakin ta, fuskar ta d'auke da murmushi, seda tazo dab da Abban nata sannan tace cikin muryar ta da bata gama fita sosae ba

"Abba na shirya.."

"Yawwah..Ayrah" Abba ya fad'a yana jan kumatun ta kafin ya d'ora da fad'in

"Ina yayan naki?" d'an k'aramin bakin ta ta tura gaba kad'an kana tace

"Abba Yah Sadeeq fa be shirya ba" kafin Abban ya sake cewa komae sega Sadeeq d'in ya fito, fari ne se dae ba can ba, amma kamar su d'aya da Ayrahn, wanda hakan ze alamta maka da cewar yayan tane, shima yana sanye cikin Uniform d'in kamar nata, sedae akwae d'an banbanci a Uniform d'in nasu wanda hakan ke nuni da ita a primary take yayin da shi kuma yake a secondary, shima nasan a wanke suke tass kuma a goge hannun sa rik'e da jaka yana k'ok'arin goyawa a bayan sa yace sanda yazo kusa da Abba bayan ya watsawa Ayrah harara

"Abba ka ganni fa a shirye nake.." mik'ewa Abba yayi yana rik'e da hannun Ayrah dae_dae lokacin da Umma ta fito daga kitchen tana kallan Sadeeq tace

"Ba zakayi break bane?" kallan Umman yayi kafin ya saci kallan Abba

"Wato so kake ka janyowa kan ka wata cutar koh?" sosa kansa yayi kana yace har lokacin kan nasa a k'asa

"A'ah fa Abba, ae ina siyar wani abun a school.."

"Toh yayi kyau, amma ko tea ne ka dinga sha ko ka samu hanjin ka ya warware"

"Toh Abba.." ya amsa a hankali

"Toh Allah ya tsare, ya bada sa'a.." Umma ta fad'a tana binsu da kallo su duka, suka amsa da "Ameen" sannan suka fice daga d'akin... Kae tsaye fire service suka wuce inda Abban ke ajiye motar sa k'irar Civic Honda, suka jira shi a bakin wajen, ya shiga ya d'auko sannan suka shiga ya wuce dasu zuwa makarantar kamar koda yaushe, a bakin makarantar ya ajiye su bayan ya sallami kowannen su sannan shi kuma ya wuce wata makarantar government da yake koyarwa a cikin garin nasu.. Hannun Ayrah cikin na Yah Sadeeq har suka k'arasa bakin ajin su Ayrahn, sannan ya sakar mata hannun yace yana kallan ta

"Ayi karatu sosae, banda k'iriniya"

"Toh" ta fad'a kawae tana yin cikin ajin nasu, seda yaga ta shiga sannan ya wuce nasu ajin.. Wajen k'arfe 10 aka fito break, kamar koda yaushe ita da k'awayen ta kan fito harabar makarantar suyi wasa bayan sun gama cin abincin, yau ma hakan ce ta kasance, dan kuwa suna gama cin abincin suka fito wajen suka fara wasan su irin na yara.. A hankali idanun ta suka sauka akan sa kamar koda yaushe yana zaune akan wani d'an dandamalin dake k'ofar wani aji, yayi shiru wani lokacin yana d'an kallan abinda ke faruwa a cikin makarantar, wani lokacin kuma idanun sa na kallan k'asa ko wani wajen, cigaba tayi da wasan ta sedae lokaci zuwa lokaci takan juya ta kalle shi har zuwa lokacin da aka koma break d'in suka koma aji bayan sunyi butu butu da Uniform d'in nasu. Suna zaune cikin ajin wani malami na musu karatu, seta d'an saci kallan tagar su da take kallan k'ofar ajin, kamar yadda ta tsammata kuwa seta hange shi d'an nesa kad'an yana lek'owa cikin ajin yana kallan malamin, cigaba tayi da kallan sa ba tare da ta cigaba da saurarar malamin ba

"Ayrah!!" taji malamin ya ambata, seta juyo da sauri tana gyara zaman ta, idanun ta da suka yi rau rau akan malamin, maeda duban sa yayi kan inda take kalla, ganin haka ya sanya yaron saurin yin k'asa da kansa dan kar a gansa, hakan yasa malamin bega komae ba, da mamaki ya tako zuwa inda take yace yana kallan ta

"Me kike kalla acan?" kamar zata fashe da kuka tace

"Ba komae.." ta fad'a d'an k'aramin bakin ta a gaba, sake kallan wajen malamin yayi sannan ya dawo da duban sa kanta yace

"Ohk toh me muke cewa?" ita sam bama ta gane tambayar da yake mata ba dan haka kawae ta bishi da kallo, ya girgiza kae kawae sannan ya koma ya cigaba da abinda yake yi, bata sake kallan wajen ba ta bada hankalin ta wajen karatun da ake musu, dan kullum ne idan ta koma gida se Yah Sadeeq ya sanya ta a gaba ta masa bitar abinda aka koya musu.. K'arfe 2 da en mintuna Abba yazo ya d'auke su a motar sa kamar
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment